UMM ADIYYAH CHAPTER 63 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Eh, tabbas laifi ne mai tsauri, zai iya yiwuwa
ya gaza danne kwadayinsa, zai iya
yiwuwa yana son ya balle ya gina nasa kam-
fanin ne. Har hakan ya janyo ya yi
abinda ya yi. Yana da iyali, matarsa kuma tana
kirana kaninta. So, ya biya tarar da
aka ci shi, ya dawo kuma da wasu daga cikin
kudaden da ya samu daga hannunsu.
Yanzu haka yana kirana duk karshen wata ya
fada min abinda yake ciki a sabon
wurin aikin sa.”
Yallabai gaskiya kun yi kokari, ba kowa ne
zai iya abinda ku ka yi ba. Allah ya saka
maku da alheri.”
Gefen labbansa ne suka motsa sama kadan,
alamar murmushi.
Suka ci-gaba da hada wayoyin da suka dace su
y.
A nan dai aka yanke shawarar washegari za su
gamu da kamfanin N-Bits.
**********
Hankalinsa gaba daya ya tafi akan wayar da yake
yi, ya bada dukkan natsuwarsa a
kai, lokacin da ya ji ana taba kofar ofishin nasa
alamar kwankwasawa, idanunsa ya
mayar kan komfutar da take dauke da hotunan
mutanen, Karamin falon karban
bakin sa.
Wayar Intakom dinsa ya daga ya yi magana da
Stella, “Ki bari su shigo.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana ajiye kan wayar ne, suka shigo cikin
ofishin, fara’ arsa ya fadada, hade da
mikewa don ya isa wurin kujerun zaman da
yake zama da bakin gida ko baki na
musamman. Hannu ya mika masu.
Suka karba daya bayan daya cikin musabaha,
suka gaisa da shi, “Fa’iz ai ban san
za ka zo ba, yanzu ko na ke shirin shiga (Meet-
ing), a (Conference Room), amma za
ku iya jirana, ban tsammanin za mu dade a ciki
ba.”Fa’iz yana dan yake ya sosa keya, sannan ya
dan taba abokin sa akan ya yi
Magana. Zaid ya kallesu ya kara mayar da
ganinsa wurin Fa’iz.
Yaya dai? Idan kuma ba za ku iya jira ba, zan
hadaku da Ceasar ya nuna maku
cikin kamfanin, duk da na san kai ka sha zuwa,
za ka iya nunawa abokinka ko ina,
ku shiga har Lab ma ya ga komai.”
“Uhm! Yallabai, dazu an kiramu aka ce mu zo
karfe sha daya.” Abokin Fa’iz ya yi
magana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Goshin Zaid ne ya tattare cikin tunani, yana
dubansu daya bayan daya. Akan Fa’iz
ganinsa ya sauka. “Waye ya kiraku?”
Ina ga ya ce idan muka zo mu kira shi
sunansa Charles, to sai Fa’iz ya ce ya san
wurin da ka ke zai fi kyau mu zo kai tsaye
wurinka, don mu yi magana.
Idanun Zaid a take suka fara kifkiftawa don
kansu, a hankali fara’ar da ta wadata a
fuskarsa ‘yan sakannin da suka wuce ya koma
tashin hankali. Ji ya yi kamar an sace
masa iskar Kafafunsa, yayin da gumi ya
ya
tsattsafo masa a goshinsa.
“Charles? Ya kiraku? Ya ce ku zo nan karfe
sha daya?”
Dukansu biyu suka shiga gyada kai, kamar
kadangaru.
“Uhm! Shin Fa’iz ka na da alaka da wani abu
da ake kira N-bits”
Fa’iz na murmushi kasa-kasa, ya sosa kai ya
ce. “Yallabai ni da aboki na din nan,
mu ne wadanda suka assasa kamfanin N-Bits.”
Wani numfashi Zaid ya zuka, take ya ji
wuyansa ya toshe, ruwan da aka ajiye masu, ya
dauka ya balle hancin gora daya, ya kai baki ya
shanye tas! Sannan ya goge
bakin sa. Duk kwakwalwarsa tana cikin tu-
nani.
Murmushi ya masu ya ce, “”I must say you’re
quite Impressive. Very impressive. So
za ku dan ban bayanin yadda aka yi ku ka kafa
kamfaninku, duba da yadda ku ka
fito da karfinku?” Kallon juna suka yi kamar
suna shawara. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bude coat dinsa ya yi, ya gyara, sannan ya
shiga makale aninan suit dinsa, ya koma
ya jinginu da kujerar hade da nade katfarsa
daya kan daya, safar kafarsa tana
lekowa a cikin dress shoes dinsa.
“Ku saki jikinku, kasuwanci za mu yi, sannan
ina bukatar na san abubuwa game da
kamfaninku, kamar yadda ni ma na tabbatar sai
da ku ka gama bincikenku, kafin ku
zo da hannun kasuwanci. Shin na fadi dai-
dai?
Ehm, Yaya Zaid, muna da wani wanda ya
dauki nauyin tallafa mana. Sannan kuma,
wannan sunansa Rufa’i yana da dan jari, kuma
dama yana dan harkalla haka, to ya
san kan komfutoci.”
Kamar yadda ka san programming.” Zaid ya
fada, hannunsa jingine da kansa,
yatsarsa manuniya na kansa, yayin da karamar
yatsarsa ke kusa da bakin sa.
Eh, to shi ne muka fara dan bincikenmu haka
akan encryption (marufin sirri) da dai
sauransu.”
Yanzu ina so ku fada min iya matsalar da ku
ka saka kanku a ciki, kafin mu je gaba
da bayanin.” Zaid ya fada hade da
rankwafowa gaba, ya sargafe hannayensa cikin
juna, yana kallon yadda Fa’iz ya hadiyi wani
abu. Rufa’i yana wulla idanu.
“Ba mu san yadda aka yi ba, lokaci na karshe
garin dan tattara bayanai, mun samu
yar matsala har dai wancan kamfanin suka
nemi su hadamu da hukuma. Yaya Zaid
da gaske, ba abu marar kyau muka yi ba, kawai
dai mu idan mun samu ne muke
decrypting mu sayarwa masu so. Kuma…”
Yaya ku ke so (AZIT) ya taimake ku a nan?”
Shiru ne ya dan ratsa kafin Rufa’i ya lashi
labbansa ya ce, “Mun ji labari kwanakin
baya, kun samu matsalar Data breach (Satan
muhimman takardu), shi ne muke so
ku taimaka mana wurin kulle Database dinmu,
yadda babu wanda zai iya samun Www.bankinhausanovels.com.ng
mashiga, saboda mu matakin tsaron da muke
amfani da shi, bai da karfin da za mu
toshe masu kawo mana hari ba.”
Murmushi Zaid ya yi, ya ce “Mhm! Hakan na
da kyau. Zan hada ku da Analyst
dinmu, sai ku tattauna abubuwan da ku ke
bukata ayi maku.”
Nan da nan Fa’iz ya washe baki. “Sai maganar
kudin aikinku, da za ku biya.” Zaid ya
fada yana kallon fuskokinsu.
“Ah, Yallabai wannan ba komai bane, ko nawa
ne za mu bayar kawai dai…”
Fees dinku shi ne ku tattaro duk bayanan da
ku ka san kun sa a kasuwa na (AZ IT),
sannan kuma wadanda ba ku gama sayarwa
ba, ku dawo mana da su, sannan ku
dawo mana da ribar da ku ka samu akai.
Daga lokacin zuwa yanzu. A madadin hakan
zan ba ku aikin yi a nan, Ina da ra’ayi
akan kamfaninku, za mu hade da namu mu ci-
gaba da bunkasa shi ta hanyar
habbaka ayyuka masu kyau bisa ka’ ida, ku
kuma ku samu riba, kuma ku sa iliminku
a yin aikin da yake kan yadda shari’a ta tsara,
ba sayar da kayan sata ba.”
Gumi ne ya jika fuskar Fa’iz, nan take han-
nunsa ya hau kakkarwa. Yayin da Rufa’i
ya matsa daf kunnan Fa’iz hakoransa a cije ya
ce masa, “Na fada maka zai gane.”
“Ba ku ce komai ba, shin mun samu yarje-
jeniya?”
A take Fa’iz ya zube a kasan kafet din gaban
Zaid yana kuka, “Don Allah, don
Annabi Yaya kar ka fadawa su Abba. Wallahi
ba da gangan muka yi ba, kawai mun
far
a da kadan-kadan ne, kuma..”
“Me ya sa ka ke kuka? Ba cewa na yi zan sa a
kulle ku ba, which by the way, idan Www.bankinhausanovels.com.ng
aka kulleku sai kun yi shekaru biyar, zuwa
bakwai, amma ba hakan na ke so maku
ba, saboda dukkanku har yanzu yara ne, you
have the potential, kawai kun zabi ku yi
amfani da shi ta gurbatacciyar hanya ce.
Idan kun amince za mu yi covering wasu legal
issues dinku, a canza komai na
kamfanin, na kuma dauke ku a aiki, don ba za
mu yi amfani da sunan kamfaninku
ba, kasancewar an riga anyi aikin sata akalla
sau hudu zuwa biyar da shi, kuma ina
tabbatar maku da ba (AZ IT) bane kawai suke
nemanku.”
“Mun amince Yaya Zaid, ba ma son ma ko-
mai.”
“Wato Mr Akim ko? Shawararka ce ko kuma
ta waye?A ina ka fara sanin Akim?”
“Ehm, Adda Ummu ta kan fada mana labarin
mutanen ofis dinsu, wataran idan na zo
wurinta, ina lura da shi, wannan ya sa da muka
fara kasuwancin da abokanmu, sai
muka tura wasu su je su ba shi offer, da farko
ya ki, amma muka matsa masa har
sai da muka ba shi kudin da mun san ba zai ki
amincewa ba.”
Naira miliyan talatin a kayyade. Ku kuma a
ina ku ka samu wannan makudan
kudaden?”
Kudin Rufa’i ne na gado, sai kuma wani dan
kasuwa da muka samu ya sanya mana
hannun jari.”
Zaid ya tabe baki yana kallon kasa, hade da
gyada kansa, kafin kallonsa ya koma
kan Fa’iz, “Ka san dai tamabaya kadai idan
kayi ya wadatar ko? Ka san ba abinda
ba zan yi wa Abba da Maami ba ko? Me ya sa?
A yanzu ina jin zafi da kunci a raina
da har na bari karkashin kulawata ka zama
abin da ka zama Fa’iz. Meye matsayin
Faruk a kamfaninku?”
Kan Fa’iz a kasa yana share hawaye, ya ce
Bai san muna yi ba.”
Zaid ya sa hannu ya tallafo kansa cikin matsan-
nancin damuwa. Yaya Abba zai yi
idan ya ji wannan mummunar labarin cewa da
hannun dansa aka hadu aka cuci
kamfaninsa daruruwan miliyoyin kudade.
Shi bai isa ya daure su ba, duk da abinda ya
dace ya yi kenan, abinda
kwakwalwarsa take fada masa kenan, amma
idan ya yi haka, ya bata goma ne,
daya ba ta gyaru ba, tabbas yaran suna da
fasaha, sai dai rashin samun kula mai
kyau da kuma saurinsu na son su yi kudi ta ko
wane hali, ya sa sun zama yan Www.bankinhausanovels.com.ng
yahoo yahoo.
“Banda hustling’ me ka ke sha Fa’iz?” Zaid
ya jefawa Fa’iz wannan tambayar., yana
Kare masa kallo.
*** *****
BABI NA ARBAIN
“Wallahi Yaya, banda sigari ban taba shan ko-
mai ba. Shi ma sau biyu kawai na taba
sha. Maami za ta tsine min idan ta ji abinda na
yi, don Allah kar ka fada mata.”
Fa’iz kam kuka yake yi wee-wee.
Yanzu abu na gaba, ya dace ina dakin taro
mintuna goma da suka shige. Ina
tattaunawa da ma’assasa (N-Bit Links). Abinda
na ke so da ku, shi ne za mu shiga
da ku wurin taron, za ku maimaita abinda ku
ka fada min yanzu, za kuma ku nemi
gafara da kuma yarjejeniya. Zan kira lauyanmu
mu tattauna, kafin nan ku je nan
Reception ku jirani.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG