UMM ADIYYAH CHAPTER 7 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
san manufarsu ba. Sai Oga Akim, wanda shi ne shugaban bangaren da take. Dadinta dai daya sun mata kyakkyawar tarba, sannan Jamila ita ma tana da faram faram. Hakan ya sa ta dan ji sauKi, zuwa washegari ta fahimci Oga Musa mutum ne mai
tsannanin tsabta da tsantseni, don baya sayan komai yaci. Daga gida yake kawo abincinsa, yawanci kayan marmari a yanke a robar take away. Minti kadan kuma zai murza man kariya daga Kwayoyin cuta (Hand sanitizer). Bai cika magana ba, wannan ya sa tasu tafi zuwa daya. Sai Ayo wanda maye ne wurin tsare-tsaren kwangila, don idan ya ritsa komfuta ko Charles Babbage (Mutumin da ya fara kirkiro komfuta) iyakaci, ance wataran a ofis yake kwana.
Kwanakinta hudu tana zuwa, kuma ba laifi ta fara gane kan komai, minti kadan wani daga cikin manyan zai leKo ya tambaya ko tana buKatar wani abu. Ko yadda suke mata, ta san hala Yaya Zaid ya fada masu ita Kanwarsa ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai dai duk yadda take son danne lamarinsa a cikin ranta ta boye, bai hanata jin kewarsa ba na tafiyar da ya yi tun ranar Asabar, yau kwanaki shida kenan. Yau kam da motar Maami ta fito ofis, ta zo shiga ne. Sai ga Oga Musa ma ya sauko ya bude tasa motar, ya yi mata murmushi sannan ya ce, “Have a nice Juma’‘ah.” Godiya ta yi masa ta shige cikin murmushi. Ba kasafai ya faye magana ba, sai ta kama dole.
Duk da kasancewar yau ba su yi wani aiki so
ZAMU TASHI
sai ba, amma a gajiye take lis! Ga shirye-shiryen bikin Adda Asma’ da suke kai. Don koda ta bar office, sai da ta wuce shagon Alhaji Manniru da ke kasuwar Wuse, saboda karbar wasu kayan da ya kawo masu.
Isarta Kofar gida ne, ta samu kanta cikin faduwar gaba, a natse ta shiga, yayin da masu gadi suka shigo da kayan da ta zo da su daga kasuwa, ai ko tana shiga falon. Maami ta same shi zaune kan kujera. Gaisuwa ma suke yi, da alama yanzu shigowarsa. Maamin ma ba ta dade da dawowa ba.
“Sannu da dawowa.” Ta fada kawai ta sa kai za ta wuce daki. Ummu!” Ya sa baki ya kirata, ta dawo ta zauna a gefen Maami, “Har kin fara zuwa aikin
ne?”
Shiru ta yi tana kallonsa, bayan tun shekaranjiya ta ji sun yi waya da Fayemi yana fada masa ta fara. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Eh.” Tsareta ya yi da idanuwansa yace, “Ya yi kyau, sai ki dage banda wasa. Allah ya taimaka.” A ranta cewa ta yi, “Kamar ni na ce ina son aikin daman.” Ba tare da ta amsa ba, ta mike ta bar falon. Maami ta bi ta da murmushi. Duk da cewa ta san da zuciya daya ya ce wa Abba ta yi aiki da kamfaninsu, ita haushi ya ba ta, don me ya sa ba za a barta ta bi ra’ayinta ba. Uwa, uba ga shi yanzu duk randa ta je aiki, sai sun hadu, wata Kila, ba ta san yaya
za ta Karke da HALIN ZUCIYARTA ba. Wayyo ni Umm Adiyya!
********
BABI NA SHIDA
Bikin Asma’ dai sai gabatowa yake yi, don an sa rana yanzu kam sati daya kacal! Ya rage, ko aiki ma da wuri take guduwa, saboda yadda abubuwan suka cabe mata. Umm ke bin ta da kallo ta ce, “Yawwa gwamma wannan, ina ga a kan dayan, ki yi amfani da shi don dinkin ya fi fasali, idan ya so wancan din, sai ki sa a budan kai tunda da shi za a lullube ki.”
Asma’u ta harareta, “Wato munin Cinkin nawa ma ya kai ga har sai na lullube shi ko?” Turbune fuska ta yi ta ce, “Haba, Umm A. Na kiraki ne fa don ki ga yadda
Dinkunan suka yi, kin zo kin wani haKiKance, ki na kushe min kaya.” Dariya ta yi sannan ta ce, “Ah to, ba gwamma ni na fada miki gaskiya ba a kan ki
saka, a Zo ana cewa ‘yar Justice ba ta iya ado ba? Ko dai ki kai a gyara miki wuyar rigar ko kuwa ki haKura da sakata.” Umm Adiyya kam sai gani kawai ta yi Asma’u ta wurga kayan a akwati. “Na fasa amfani da shi, tunda ni ina son kayana, sai bayan auren ma na saka.” Umm Adiyya kam ba abinda take yi sai Www.bankinhausanovels.com.ng dariya, wayarta ce ta hau Kara, wannan ya sa ta daga da sauri, don ganin lambar Oga Akim ne. Bayan sun gaisa ne, ya ce ana nemanta a wurin aiki. Bata rai tayi, sannan ta kashe wayar, ta kalli lokaci ta ce, “Allah mutanen kun nan suna da gulmar tsiya, meye za su kama su kirana yau Asabar da ba aiki za ayi ba, ba komai ba.” Ki ka san ko aikin ne ya taso? Ki shirya ki je ki gani mana, bari na je Maami ta tayani zabe.” Murmushi kawai Umm Adiyya ta yi, don da Maami ta zaba maka kaya, gwamma ka zaba, saboda irin zabinta kam sai ita. Tun a hanya banda guna-guni ba abin da take yi, tana zuwa kuwa ta tadda harabar kamfanin motoci Kalilan ne, ba kamar a ranakun aiki ba. Ayyukan da suka fara jiya ne, aka nuna mata wai an matso da lokacin buKatar aikin
kusa, don haka dole su sa rarar lokaci, saboda a same shi zuwa lokacin da aka dibar masu. Duk da ba ta so fitar ba, babu yadda ta iya, haka ta zauna ta sa kai sai aiki, dukkan su sun fito aikin, don haka tana carkewa ta fadawa Oga Musa, don shi ne mai kula
da ita (Supervisor). Teburin sa ta koma da komfutar suka duKufa aiki, ko awa biyu ba su yi ba, ya shigo
wurin, duk da ta ji shigowarsa, gaishe shi kawai ta yi Sama-sama ta koma kan aikinta, yayin da shi kuma ya Kara nunawa Akim abinda yake buKata. Tana kula da ko kallon inda take bai sake yi ba, ya fice a ofis din. Sai wajen Karfe uku suka kammala, ta koma gida a gajiye lis!
************
“Gaskiya Umm A. Ya kamata ke ma ran Litinin ki bada excuse, ai wannan za su gajiyar da ke. Yaya suke son na yi! Oho? Ga shi Laraba Inshaa Allahu na ji Abba yace za mu tafi Gombe mu duka.” Zan gwada Www.bankinhausanovels.com.ng tambaya. Allah dai ya sa su bar ni, yadda ki ka san sun samu jaka haka suke min. Na gaji ma Wallahi.” Asma’u ta ce,Ki yi haKuri, za ki saba, ni ma da haka na saba.” Tun ranar Lahadi aka je aka shiryawa amarya gidanta da yake Kaduna, kasancewar
Zunnurain ya koma bangaren ofis dinsu na Kaduna da aiki, a can za su zauna. Umm Adiyya kam ba ta bisu ba, ta san da wuya ta iya zuwa har ta dawo ta koma kan aikinta, ba tare da ta janyo wa kanta laifi ba.
Su Adda Zubaida ne kan gaba a komai da kuma ‘yan-uwan Maami da Abba. Ranar Laraba ko aka dunguma gabaki daya zuwa Gombe. Nan ne suka samu biki ya kankama, domin Maami ta rigasu tafiya da kwana guda, haka suka samu gidan tirim! A cike da jama’a. Sai lokacin ne ‘ya’yan Baffaninsu da suke Gombe suka sa masu hannu, don ganin shirye-shiryen ya tafi yadda ake so. Alhamis da safe, mai yin lalle ta zo ta yiwa amarya. Nan fa ta dage tace da Umm
Adiyya, “Ke fa ba za ki saka lallen bane? Na ga tun dazu da Kawaye ke ta ribibin saka lallen, banda ke.”
Bar ni kawai ko na saka, wani abu zai taso, kuma ni za a nema, na rasa inda Adda Zubaida take bacewa bat! Duk da dai ta yi nauyi, amma ta bar min kusan ayyukan gaba daya.” “Kar ki damu, ki yi aikinki, da dare ai ina nan sai na zauna na shirya miki lalle, ga shi zai miki kyau, yadda ki ke jazur kamar ‘yar Indiyan nan.” Umm Adiyya ta yi dariya, jin yadda mai lalle take ta Kwarzanta farar fatarta. Ai ko ba ayi minti goma ba. Maami ta aiko ta zo za a je kasuwa.
(Family Dinner) aka shirya na amarya kawai da danginta mata, sai ko abokan taya farin-ciki. Ya Kawatu sosai inda dangin amarya suka sha ankonsu na jan kaya, bangaren ango suka sha nasu, (Golden Yellow), tuni wurin taro ya bada kala. Haka aka ci aka sha, baki suna ta jin dadi, kowa da ya zo ya miKe Kafa, sai dai a miKo abinci. Ummu A, ba ta san ana wannan miKe Kafafun ba, kowa ita ya sani, idan ana buKatar wani abu, to ita da Adda Zubaida ne.
Ranar Juma’a ana gobe daurin aure ne, ta samu ta sulale falon Abba, ta jawo Kofar Www.bankinhausanovels.com.ng
ta sa makulli ta ciki ta zauna a kan kujera, hade da saka kanta a wuyar kujerar, tana kallon sama, tana maida numfashi. “Za ki fadi, idan ki ka biye masu.”
A razane ta dago kanta tana duban inda ta jiyo zuzzufar sumul din muryar. “Yaya Zaid? Ka bani tsoro.” Kun tara jama’a kam dole ku yi haKuri, amma ba ace kar ku huta ba kuma.” Yana daga zaune akan kujerar karatun falon Abba, wanda yake girke a wani kebabben wuri a cikin falon yake magana. “Saura kadan a gama, ai ba wani abu.” “Meye wannan kuma?” Ya fada yana kallon hannunta. Da sauri ta boye hannun, ba shi kadai ya tambaya ba. An fara mata lallen jiya kawai ta Kwace hannunta, ta je ta yi barcinta, haka ta wuni, take yawo da lalle hannu daya da rabi. “Style ne.” Ta fada tana rufe idanu.
Jinjina kai ya yi yace. “Idan kin tashi ki rufe Kofar ni zan fita, hayaniya ta yi yawa a gidan nan, na je gidan Baffa ba masaka tsinke, na zaci a can ake bikin da na zo nanma, na ga abin duk daya.”
“Na kawo maka abinci?” Ta tambaya a sanyaye.
“A’a na ci da aka fitar da na su Abba. Na gode.” MiKewa ta ga ya yi, har ta ji ba dadi, saboda ta samu suna ‘yar hirarsu. “Sai da safe.” Ya fada daidai lokacin da ya bude Kofar, da kai ta amsa masa,
saboda ba ta yarda da kanta wurin bude baki ba, cikin tsoron kar ta saka ihun dadi, ya zaci ko ita mahaukaciya ce. Washegari kam shagali ya kankama, ana ta harka dai irin na al’ada, an hada kayan
amarya, an gama fidda doke, an ware kayan uwar ango. An daura aure ana kuma yiwa amarya nasiha a falon Abba, kamar yaKi za a tafi. Ana ban-kwana. Kodayake dama an ce aure yaKin mata.
Ummu Adiyya dai ba ta ga amfanin yin nasiha randa za a kai yarinya dakinta ba, da kukan barin gida za ta ji, ko kuma da sauraren hudubar da ake mata? Nasiha kam ai tunda take girma a gaban iyaye, ya kamata ace ta tsinci nasihu kala-kala a shekarun. Ko kuma kafin ranar auren. Cikin natsuwa da jaddada ababe masu muhimmanci. Yadda Asma’ take kwanda kuka, sai ta rantse ba ta son auren ne, ba ta yi tsammanin ta ji me ake fada mata ba na daga nasihar ma. Da aka fiddo da ita har da su wayyo Allah take fadi Umm Adiyya ta zo kusa da ita ta ce, “Adda Asma’ banda gulma dai. Abba yace ya fasa, idan ki ka yi kukan over, za ki shide, a kai ki asibiti, sai ace an fasa kai ki yanzu.” Harararta Asma’u ta yi ta ja hanci, idanun nan sunyi ja tace, “An wuce fasawa kam. Umm Adiyya ta yi dariya sosai, sannan ta rufe mata Kofa inda Antin gidan Baffa Abdu ta shiga gefen amarya, a daya gefen kuma kakarsu ce Hajja Kubitto ta shiga ta harde. Biki dai ya yi armashi,Www.bankinhausanovels.com.ng kowa ya watse yana yaba kyawun tarba na mai shari‘a, ana yaba yadda aka samu kyakkyawar tarba da kulawa a bikin, duk da sha’ani ne na jama’a mai yawa. Haka Umm Adiyya ta ja jiki ta koma ranar Lahadi. Litinin kuwa aka dora a inda aka tsaya
Alhamis aka yi masu waya Adda Zubaida ta haihu, an samu ‘ya mace, Umm Adiyya kamar ta fire take ji, amma ba hali, wannan aiki na jaraba yasa ba zata tafi ba, sai Karshen mako, ta san zai yi wuya ta samu bikin sunan. An sanyawa yarinya suna Safiyya.
**********
Yau ma suna tsara yadda za su gudanar da aikinsu ne, ita da Oga Musa da Jamila a teburinta. Zaid din ya shigo ofis dinsu, ta kula kamar ya zamo masa dabi’a kullum sai ya bi ko wani Department sama-sama ya kula da abubuwan da suke yi, wataran
baya magana, wataran kuma sai ya tambayi matsayin ci gaba na ayyukansu Yana fita ko minti biyar bai yi ba, sai ga wayarsa, “Ki sameni a ofis.” Iya abin da ya ce da ita kenan, don haka ba tare da kawo komai a ranta ba, ta miKe ta nufi matakalar da zai kai mutum dakunan taro (Board room) da kuma ofis-ofis na shuwagabannin kamfanin. Tana shiga, ta samu ya sa hannayensa saman tebur din gabansa ya hard Www.bankinhausanovels.com.ng yatsunsa cikin juna hace da Kurawa Kofar ido. “Gani Yaya Zaid…” “Zauna.” A darare ta zauna, don ta gaza karantar yanayinsa, sai dai ko kadan ta san babu wasa a cikin idanunsa. Komfutar gabansa ya tura mata yace, “Ki rubuta.” Kallon fuskar na’urar ta shiga yi a razane, bayan ta karanta kanun da ke kai. Takardar barin aiki? A kidime ta dube shi, akan me zai sa ta rubuta takardar barin aiki ana zaune Kalau? “Yaya Zaid, ban gane ba?” “Na ga alama kin gaji, ko kuwa dai ki na da abubuwan da suka fi aikinki
muhimmanci, mu kuma a nan muna mu’amala ne da masu Kwazo da suka san abinyi suka san kuma abin da ya kawo su, don haka idan ki na ga baki da sukunin bin
Ka’idojin kamfaninmu (Work Ethics), za ki iya tafiya.”
Dariya ma ya so ya bata, amma ta kasa yi, don abin ya ma wuce tunaninta, “Zan so na san laifin da ake tuhumata da aikatawa, idan har hakan kuma ba zai samu ba, shin ina buKatar na tunatar da kai cewa, nan kamfaninka ne za ka iya korata kai tsaye, ba sai kayi wata kwana-kwana ba?“ Shiru ya yi yana kallon dan tsurut din bakinta da ke ta zazzage bayani.
Ni dai na ba ki zabi, idan ki na son aikinki, dole ki mayar da hankalinki gaba daya akai, idan kuma har kin gaji ne, To, Bismillah.” A iya sani na, ina aiki na dai-dai gwargwado, idan kuma ba ka amince ba, duk
lokacin da na gama, zan rinKa bada rahoton abin da nayi, na miKa hannun Oga Musa, tunda shi ne Supervisor na.” Balla mata harara ya yi, “Yaya zan san cewa ba zai ba ki lambar yabo haka siddan ba?”
“Akan me ya sa zai ba ni abin da ban cancanta ba? Idan ka gaji ne, za ka iya cewa kawai na tafi.”
Na sani? Saboda na ga kwanan nan shi yake miki ayyukanki.” Ita dai a yanzu a matsayin shugaban Www.bankinhausanovels.com.ng kamfanin da take aiki ta dauke shi, amma
Kwarai ba ta san mugun halin Yaya Zaid ya kai haka ba. Kwarai dole ya gwada min abin da ban gane ba, amma baya ga haka, ni bai taba yi min aikina ba. Amma tunda ka ce haka…” Hannu kawai ya ga ta sa ta janyo kwamfutar gabansa, cikin minti biyu ta rattaba takardar barin aiki. Ta tura masa gabansa, sannan ta miKe hadda bude jakarta ta ciro katin shaidar aikinta dinta ta ajiye kan teburinsa.
Sam bai yi tsammanin za ta dauki wannan matakin da gaske ba, ya yi mata hakan tun farko don ya razana ta, ya kuma gwada mata bai son yawan huldarta da
Musa, sai ga shi ta bashi mamaki. Ba ta jira komai daga gare shi ba, ta koma ta dauki abubuwanta a ofis, sannan ta yiwa kowa sallama. Kwarai sun ji mamakin tafiyarta farad daya haka. Hatta Ayo
cewa ya yi, “Hajiya, muje mu roKi Oga, na san zai sauko.” “A’a kar ku damu, wasu kebantattun al’amura ne, amma da zaran an warware zaku ganni.” Jikinsu duk a mace suka yi sallama, har mota Oga Musa ya rakota da jakarta na komfuta a hannunsa, kamar ya yi kuka saboda yadda suka saba da ita cikin watanni ukun da suka yi suna aiki tare.
Cikin turanci ta ce masa ta gode, shi ya sa hannu ya bude mata Kofar motar ta shiga. Daga saman hawa na uku ya saki labulen kararen (blinds) din ofis din nasa, zuciyarsa kuwa kamar za ta fashe don haushi da takaici, kai bai ma san me yake jiba a wannan lokacin. Musamman da wannan Dan Ibiran ya wani bude Kofar mota, sai ka ce wani linzami, sai bare-Dare yake yi. Sai a lokacin yaji da ma shi ya sallama, koda yake yana da amfani sosai a kamfanin.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG