UMM ADIYYAH CHAPTER 73 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 73 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

shiririta ce sam ba na so. Don haka duk ku
tattara ku ba ni wuri, ba na son na saurari
kowa. Idan ita Ummu an warware baikon
can a kanta, to ni da na bada auren Ummu, ba
ni da labari, kai Zubairu kai ne
mahaifinta, ban sani ba ko kai ka samu labarin
hakan?”
A take Abba ya girgiza kansa, yanzu kam ba
tantama Zaid ya san iyayen sun hade
masu baki ne.

“Baffa ku yi hakuri, za mu san yadda za ayi ku

ji komai daga bakinsu, amma sam ba

zancen wasa da hankalinku muke yi ba.”

Ba wanda ya tanka shi, don haka ya dauka a

matsayin sun sallame shi ne, kansa ya

gama kullewa, a take ya danna wayar Salisu

yana fita.

“Dan group ka ji abin da muka sa kanmu a

ciki, ashe wancan dan Bauchin bai fada

masu ya janye ba, yanzu su a dole sun bada

Umm Adiyya, ba za su ma karbi batuna

ba.”Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Tijjani sunansa, lokaci ya yi kuma da za ku yi

magana ta fahimta da shi, domin dole

sai ya sa baki, kafin ka samu Umm Adiyya.”

A take wani gumi ya yanke a fuskar Zaid, han-

nunsa na hagu ya sa ya shafo

fuskarsa. Sannan ya sauke ajiyar zuciya.

*************

BABI NA ARBAIN DA BIYAR

Kallonsa take yi kamar ya fado daga sama, shi

ma kura mata idanu ya yi, “Yaya

dai? Bismillah.” Kallon wayar tata take yi a
hannunta, yau ita kam ya sa ta a tsaka
mai wuya, yaya za ayi haka kawai ta kira TJ.
Rana tsaka, bayan tun randa suka rabu
a asibiti, ba su sake magana ba, ba ta ma san
halin da yake ciki ba. Ba ta san ma ko
zai dauki wayarta ba, ko ya sa ta a reject list.
Ta yi kara biyar, a ta shida ta katse. “Yaya?”
“Bai dauka ba.”
“Wata kila baya kusa ne, sake kiransa, ki bada
minti goma a tsakani.” A cikin minti
na uku. Zaid ya gaji da sintirin da yake yi a
falon, ya ce, “Fada min lambar ta sa.”
Mika masa wayar ta yi jiki a sanyaye, sannan
ya daddana, ya mika mata wayarsa ta
yi amfani da ita.
Bugu uku ya yi, sannan aka daga, “Assalamu-
Alaikum.” Wani abu ne ya tsayawa
Adiyya a ranta, da gaske yana kin daukar ki-
ranta nee.
Daga idanu ta yi tana kallon Zaid, gyada mata
kai ya yi alamar ta yi magana.
“Wa’alaikumussalam. Ummu ce, don Allah kar
ka katse, ina son mu yi magana ne.”
“Na gane muryar, ki na lafiya?” Ya tambaya,
ba sai ya fada ba ta jiyo dacin da ke
cikin muryarsa.
“Lafiya, Alhamdulillah.”
“Ina sauraronki.”
“Uhm… Dama na yi magana da Abba ne kan
batunka, batun janyewar da ka yiwa
maganar aurenmu..”
“Uhum”.
“Shi ne ya ce su ba su san da batun ba, ka
fadawa Baban Walid ne ko akwai wanda
za ka wakilta ya sanar da su?”
Wani murmushi ya yi mai sauti, “Ummu ke
nan, you do it fast, aure za ki yi ne
maganar ta taso ko kuwa ki na Allah-Allah ki
warware alakar ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Runtse idanu ta yi, sai ga hawaye, ta san har
yanzu abin bai daina masa ciwo ba,
don haka ba ta ji zafin kalamansa ko daya ba.
“Aure zan yi, kuma ka ga bai dace ayi nema
cikin nema ba ko?”
“Kar ki damu, hakan ba zai faru ba, zan
fadawa Yaya Isma’il ya sanar da Abbanku…”
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu,
“Uncle TJ. Abinda ya faru ranar…” Katseta ta
ji ya yi.
“Ba komai, ni na ba ki damar hakan, ba sai kin
yi justifying kanki ba. Allah ya bada
zaman lafiya, ki gaida Yayan namu.”
“Na gode, a gaida Minaal da Mamanta.”
“Rahma.”
“A gaida Aunty Rahma.”
Sautin murmushinsa ta ji kafin ya datse wayar.
Dago da kanta da ta yi ne, ta nemi
Yaya Zaid a falon ta rasa, ko yaushe ya fita ba
ta sani ba.
Don haka ta fito harabar gidan, nan ta same shi
a zaune a daya daga cikin kujrerun
wurin. “Me ya faru?’ Ya fada a tausashe ganin
yanayinta.
“Ya ce zai yi magana da Baban Walid.”
Tsuke idanunsa ya yi, goshinsa ya tattare cikin
damuwa, lokacin da ya nufo inda
take tsaye, “Kina lafiya?”
Kai ta gyada masa, wata ajiyar zuciya Zaid ya
sauke, sannan ya juya zai fita, “Ga
wayarka.” Ta fada. Hannu ya sa ya karba.
“Na gode, na san na saka ki a wani irin yanayi.
Ina nufin kiransa bayan abinda ya
faru kwanan nan.”
“A’a abu ne da ya zamo lallai a aiwatar*
Lallausar murmushin da yayi mata ne, sai da
ya taba ta har cikin zuciyarta. “Ka
tsaya an gama abinci,”
“Ki ajiye min sai na dawo anjima.”
To, Allah ya bada sa’a.”
“Ameen, my Twinkle.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
%***********
Mahmoud ne ya dubi TJ. Wanda ya yi shiru ya yi
zurfi cikin tunani, “Me ya sa to ka
janye bayan ka san zai zo ya dameka?”
“Mahmoud, ba za ka gane bane, amma a gan-
ina hakan ya fi alkhairi, saboda haka
mu bari cewan kaddara ce kawai.”
“Ni yanzu duk ka sa na fara tunanin A’isha ma,
kar ayi irin naka, don sai na ke ganin
kamar ni na ke kidana na ke rawana.”
TJ Ya tattara tunaninsa ya adana a gefe, ya
fuskanci abokinsa, ya kula kwanan nan
ya fi maida hanaklinsa kan matsalolinsa, yana
nema ya mance mutanen da suke da
muhimmanci a rayuwarsa.
“Wani abu ya faru da A’ishan?”
“Haba Material, wancan watan na fara fada
maka yarinyar nan ta fara canza min,
gaba daya, yanzu sai caza min kwakwalwa
take yi.”
Wani takaitaccen murmushi TJ. Ya yi, “Zai iya
yiwuwa ka na kallon abin a baibai ne,
wata kila ka fassara tsoronka ga so a matsayin
so. Ka bada son da ka ke mata cikin
matsi, ba ka bada sararin ta dauki abin a han-
kali ba tukun. Sannan kuma ta iya
yiwuwa ya rasa asalin saka kai da jajirce-
wanka, ba ka karbe shi ka rungume shi da
dukkan zuciya daya ba, domin baida shamaki,
haka nan ba mai karewa bane.
Kuma ya kamata ka san da cewa, a so ba lalle
bane ka samu abinda ka so, sannan
a cikin irin wannan son, ba ka dagewa lallai sai
abin sonka ya zama mallakar ka.
Abin da ka fi so, masu shi ne ci-gaba a rayuwar
nan. Su samu abinda ya fi komai
daraja da muhimmanci.
Ka fi son su kasance cikakku, su kuma gamnu
da abubuwa mafi kyau a rayuwa,
sannan su samu daraja a cikin kawunansu. Idan
ba ka ba ta sar
arin ta zamaasalin
kanta ba, to an samu matsala daga nan, domin
kumfa kawai ka ke kamawa.
Asalin so yana son motsi ba kafewa wuri guda
ba, yana son farin-ciki, yana son
canjejeniya, ba dukkanmu bane aka yi mu
domin juna, ba kuma dukkanmu bane
muke gamewa a rayuwa. Saboda haka ka natsu
ka kula ka duba, kan ka so wata,
dole ka fahimci kanka, nan ne za ka gane mai
sonka na gaskiya. Wannan ya sa ni
ma na ke kara godewa Allah da ya sa na
fuskanci hakan akan Umm Adiyya, duk da
ya zo min a kurarren lokaci, amma… Ina tu-
nanin hakan shine yafi alkhairi.
Rahma ta ce na canja cikin kwanakin nan, ina
ba su lokacina fiye da da.”
“Allah ya saka maka da alkhairi, a bisa hakurin
da ka yi abokina, kuma ni ma Inshaa
Allah zan duba abinda ka ce da kyau, domin ba
na son gina gidana bisa kuskure, sai
dai tabbas ba ni da tantama ko kuma shakku a
cikin soyayar da na ke yiwa A ‘isha.”
“To, kar ka bari ta subuce maka idan ka
fuskanci lallai tana yinka, idan ba ta yinka ka
gudu sukan iya zama mummunar labari.”
Haka suka zauna cikin shiru kadan kafin TJ.
Ya numfasa ya ce, “Bari na koma gida,
na san suna jirana yanzu haka, ka san sai su yi
ta zama da yunwa suna jiran mutum
ya dawo cin abinci.”
“Da kyau mutumina, ka gane kanka Wallahi, ai
ni ma dai azumin bana kam ina sa
ran na yi shi a matsayin dan gata.”
Suna dariya suka watse, daga zaman nasu, a
can bakin masallacin da ke unguwar
da gidan TJ. Yake. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Duk da Baffa ya samu sakon wurin Baban Walid,
hakan bai sa ya canza batunsa ba,
don haka Zaid ya tafi gun abokan Baffa ya je
ya kwaso masa su yi masa magana.
“Alhaji a ganina ai tunda duka sun zauna sun
sasanta kansu, gwamma a bari su
koma din, abubuwa sai su fi gyaruwa, da ace
za su zauna suna jiran wasu kuma su
fito masu don neman aure. Sai ayi hakuri,
abinda ya wuce, ai ya riga ya wuce, sai
dai a kyautata gaba.”
“Ambasada, ba na ki ta taka bane, amma ga shi
nan ai ya fada maku da bakin sa,
ba yadda ba mu yi ba a nan gidan, a nan falon,
ba sai an je da nisa ba. Akan ya
maida matarsa, tun kan kowa ma ya sani ko a
zo ana mayar da zance, amma fir!
Suka ce su sun ji, sun gani, sun hakura suna
bukatar lokaci. To shi aure makaranta
ne da za a koma ayi kwanaki, ran hutu kowa ya
kwashi akwatinsa ya je gidansu don
ya huta? Ai ba haka bane rayuwar take aiki.
Allah Saini.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Duk dai mun ji uzurinka, kuma ba zai sake
faruwa ba, yanzun ma Inshaa Allah, ayi
mana hakuri, ni da kaina ma zan bada sadaki
da goro gudumawata kenan. Kai mun
bar ka da sa rana, kar ka zo ka min gori
gori
wataran ka ce ban maka kara ba.”
Dariya suka yi kafin Baffa ya ce, “To ai ga su
nan, yaran naka ne, duk yadda ka yi da
su, ka ji da kanka, idan su kayi maka halin
nasu.”
“Bare ma Inshaa Allah an wuce wurin, girma
ya kamasu ai, yanzu kam sai dai su
yiwa kannensu fada.” Zaid kam tsakani da Al-
lah yana gefe, amma farin-cikin da ke
cikin zuciyarsa bai misaltuwa har ya gaza
boyewa, sai shararo addu’a yake yiwa
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *