UMM ADIYYAH CHAPTER 79 BY AZIZA IDRIS GOMBE
daukeki cikin farin-ciki da komai, na kai mata
ke fuska a turbune da busasshen
hawaye? Mu je na gyara miki fuskar. “
“An ki din, ka daina min magana, na yi fushi.”
Ta fada a shagwabe.
Ta kara tsumewa hade da danno bakinta gaba.
“Kin san Zan iya sumbatarki tsawon
wuni guda, idan ba ki gyara bakin nan ba, zan
dauke shi a matsayin gayyata.”
“Ya Salaam! Yaya Zaid me ya shiga kanka ne
yau?”
“Sonki ne kawai.” Ya fada yana dariya.
“Don Allah ka mayar da ni gida.”
“Na ki din, a nan za mu kwana.”
Ba shiri ta sauke goyon hannunta da ta yi, sai
ga ta a kan gwiwowinta. Da sauri ya
sa hannu ya dagata.
“Umm Adiyya, lafiyarki kuwa2”
Kai ta gyada masa, “Kawai gida na ke so.”
Duk wata alamar raha ta bar fuskar Zaid, ya
gyada mata kai. “Shi kenan yanzu zan
wasu a cikin lufayu. Sai da kowa ya
shirya, sannan Umm Adiyya ta shiga bangaren
Maami don ta yi mata sallama.
Saboda kamar yadda Zaid ya fada, shi zai kai
ta gidansa da kansa, haka Abba ya
fada shi ma ya ce daga wurin, duk hidimar da
za su je yi, ya wuce da matarsa
gidansa, shi ya gama nasa, ya kuma damka
masa ita amana, ita kuwa ce mata ya
yi.
“Dukkanku ku ne martabar gidan nan, duk
wacce ta wulakanta aurenta, ta ki bin
umarnin Allah, to tamkar ta zubar mana da
martaba ne.”
To ga kalaman Abba, ga kuma Maami tana
ganinta, ta sa Tissue tana goge gefen
idanunta, zuwa ta yi kan Maami kawai ta
rungumeta tana kokarin kar ta yi kuka,
amma sai da hawayen suka ci Karfinta.
Maamin ce ta daure ta tsayar da nata, ta ce.
“Bebina yanzu kam ki san fa kin girma, babuu
batun wasa, ki san zaman ibada ba
wasa bane, haka aljanna ba ta da arha. Ki rike
.