UMM ADIYYAH CHAPTER 8 BY AZIZA IDRIS GOMBE

 UMM ADIYYAH CHAPTER 8 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Kwarai ba ta san mugun halin Yaya Zaid ya kai haka ba. Kwarai dole ya gwada min abin da ban gane ba, amma baya ga haka, ni bai taba yi min aikina ba. Amma tunda ka ce haka…” Hannu kawai ya ga ta sa ta janyo kwamfutar gabansa, cikin minti biyu ta rattaba takardar barin aiki. Ta tura masa gabansa, sannan ta miKe hadda bude jakarta ta ciro katin shaidar aikinta dinta ta ajiye kan teburinsa.
Sam bai yi tsammanin za ta dauki wannan matakin da gaske ba, ya yi mata hakan tun farko don ya razana ta, ya kuma gwada mata bai son yawan huldarta da
Musa, sai ga shi ta bashi mamaki. Ba ta jira komai daga gare shi ba, ta koma ta dauki abubuwanta a ofis, sannan ta yiwa kowa sallama. Kwarai sun ji mamakin tafiyarta farad daya haka. Hatta Ayo
cewa ya yi, “Hajiya, muje mu roKi Oga, na san zai sauko.” “A’a kar ku damu, wasu kebantattun al’amura ne, amma da zaran an warware zaku ganni.” Jikinsu duk a mace suka yi sallama, har mota Oga Musa ya rakota da jakarta na komfuta a hannunsa, kamar ya yi kuka saboda yadda suka saba da ita cikin watanni ukun da suka yi suna aiki tare.
Cikin turanci ta ce masa ta gode, shi ya sa hannu ya bude mata Kofar motar ta shiga. Daga saman hawa na uku ya saki labulen kararen (blinds) din ofis din nasa, zuciyarsa kuwa kamar za ta fashe don haushi da takaici, kai bai ma san me yake jiba a wannan lokacin. Musamman da wannan Dan Ibiran ya wani bude Kofar mota, sai ka ce wani linzami, sai bare-Dare yake yi. Sai a lokacin yaji da ma shi ya sallama, koda yake yana da amfani sosai a kamfanin.

ZAMU TASHI 

A hankali kuma ya koma tunani. “Zaid me yake damunka ne kake tunani irin wannan?”

*****

Tana fita gate din ta faka a gefe, sai a lokacin wani abu ya taso mata ta fashe da
kuka, kawai da gangan Yaya Zaid ya yi mata wannan wulaKancin, dan ma bai san yadda take ji game da shi ba, da ya sani kam, bata san me zai mata ba.
Don haka tunda ko ta haka ya bullo, sai dai ta yi addu’ar Allah ya sa hakan ya fi


mata. Babban damuwarta, yaya za ta fuskanci Abba, tace masa ta bar aiki? Har ta kai gida ta gaza sanin bayanin da za ta yiwa Abba, sai can yamma dabara ta fado mata. Suna cin abinci ne da dare ita da Maami da Abba, samarin kuma suna zaune suna kallon Kwallo a falo wurin kujeru, ta ce, “Abba daman ina so na fada maka, last week ECN sun kirani batun Documentation, wai na kai takarduna, sun karbeni aiki.” Abba ya ajiye cokalinsa, yana Karewa Umm Www.bankinhausanovels.com.ng Adiyya kallo, duk da kasancewarta marar hayaniya da surutu, yana saurin gano abin da take ciki, saboda kusan halayyarsa daya da nata. “To nan fa wanda kike yi da su Zaid?” Ai Abba ganin daman na karbi wannan zuwa wancan ya fito ne, shi ya sa yau na
rubuta masu Resignation.” Maami kam kallon tsaf! Ta bita da shi, “Ka ji min zancen shirme, kuma sai da ki ka yanke hukunci, za ki zo neman shawara?” “Maami, Allah na san Yaya Zaid da dadin baki, yanzu zai ce maku ku bar masa ni a wurinsu. Shi ya sa tun kan ya Www.bankinhausanovels.com.ng roKeku ma na yi Resigning, saboda nafi son can din,
kin ga Adda Zubaida kullum tana can ita kadai, shirun yana mata yawa, sai idan wani ya bi a kan hanyarsa ta zawa Gombe.” Justice Khadija ta hada idanu da Bldr. Zubair sannan ta kalli ‘yarta, “To kuma sai aka
ce miki tabbata za ki yi a gidan Zubaidan, ke ba za ki yi aure ba ko?” A’a Maami ba haka bane ba.” Ta fada cikin in ina, don ita ta tsani ayi mata maganar aure a gaban Abba, duk sai ta ji kunya ta kamata. To yaya ne? Wannan karon ba zan bi bayanki ba. Umm gaskiyar Maami, ba inda za ki je, daga garin nan har sai kin nuna min zabinki, na fara bincike a kansa tukuna, idan ba haka ba, to aikin ma an fasa yin sa.”
A razane ta dubi mahaifinta, cikin wani tashin hankalin da ba ta iya kwatantawa, dama Abba zai iya mata haka? Yaya za a ce rana tsaka ko ta fidda miji ko ta bar aikinta da take matuKar so? “Abba gaskiya ni ba na son kowa kuma ba mai sona.” Da Kyar Maami ta iya gintse dariyarta, tsabar yadda fuskar ‘yarta ya turbune cikin rigima. To banda rigimar Ummu, yaya za tace ba a sonta, ba ta son kowa, bayan
irin yadda take gani ake sintiri a kanta, tunda
Dai kaf! Gidan ita kadai ce ‘ya mace, bayan ita ko wa zai zo hira wurinta? Wasu ma fakewa suke yi da sun zo wurin SaadiK, idan yana gari, amma Ummun suka zo gani. “To ke tunda ba a sonki ba ki son kowa, ai shi kenan sai mu nemi mai son sadaka ko
kuwa? A hakan kuma idan ki ka Kara shekaru wa Zai ce yana so?” Ta san Abba zolayarta yake yi, hakan ne ya sa ta yi ‘yar dariya. “Maganar gaskiya
na ke fada maku, ki je ki yi shawara da Maaminki, ku san na yi, domin nan da watanni biyu ina son na ga Www.bankinhausanovels.com.ng mijinki Inshaa Allah. Idan ba haka ba kuma ki bar zancen wani aiki. Zuwa lokacin za ki iya zuwa ki fara Documentation, zan sa a kai ki Bauchin ko gobe ne. Inshaa Allah.” Yana fadan hakan ya mike ya bar kan teburin, yayin da Umm Adiyya ta kai wani
mummunan kallo ga Keyar Zaid da ya ba su baya, inda yake wani aiki a komfutarsa, kamar wani maye, sam baya hutawa, koda yaushe idanunsa kan Screen. A ranta kuwa cewa ta yi “Dama ni ce Ifrah ta littafin (SHAMAKIN RAYUWA), na tashi da safe
kawai na ga na mance komai, na rasa tunanina.” Don a ganinta duk shi ya janyo mata, da zuciyarta ba ta so shi, alhali shi baya sonta, da tuni ta tsufa da yin aure. To Yanzun ma jiran tsammanin warrabbuka za kiyi ne, har sai yace yana sonki ko kuwa har sai randa ki ka ga an aura masa aure da wata? Wani juyi cikinta ya yi, da gudu ta tashi a kan teburin ta yi hanyar dakinta a sama. Nan ta bar Maami da mamakinta.

***********

BABI NA BAKWAI

Ba tare da wani Data lokaci ba, ta kammala duk abin da ya dace a Bauchi, akan zata fara zuwa Litinin mai zuwa. “Walid, sauko nan kaci.” Allah Anti Ummu, ni ba na so, ni dai ki soya min Chips shi na ke so, ba zan ci tuwo ba.” “Na ga dai shi Mamanka ta ci ta girma, come on, sauko ko nayi maka dure.” Da gudu ta ga ya nufi Kofa har yaso ya bata tsoro, ta juya da kwanon abincin a hannunta, domin ta bi shi ne, suka ci karo, ai kuwa ta kwara masa miyar kuka a farin yadinsa.

Rufe idanu kawai ta yi cikin takaici da rashin sanin abin yi. Da sauri ta ajiye kwanon Www.bankinhausanovels.com.ng

ta zaro tissue paper, a kan Center table, ta ma manta kayan a jikinsa suke, don kidima, kawai ta shiga goge masa rigar, ga shi da manja aka yi miyar. Kallonta ya
tsaya yi, yadda hankalinta ya tashi. Idanunta suka Kara girma, gashin idanunta suka kwanta tamkar bargo a saman kuncin ta, ga kumatunta masu lobawa ko ba tayi dariya ba. Fatarta kuwa bai yi tsammanin Kurji ya taba ziyartar fuskarta ba. Sumul yake kamar na jarirai. Da Kyar ya shiga hankalinsa, ya bar Kare mata kallo, gyaran murya ya yi, ya sa
hannu ya karbi tissue din daga hannunta ya cigaba da gogewa. Don Allah, Uncle TJ. Ka yi haKuri, ban ji shigowarka ba, sannan Walid… Walid!” Tasa baki ta hau kiransa, ba don komai ba. Sai don ta gudu daga abin da ta aikata yanzu. Murmushi kawai ya yi, ya bita da kallo. Kafin ya ce, “Ki rabu da shi, dama dai kin lallaba shi ne da ya yarda, amma da tsumewa da barazana ba suyi aiki a kan yaro.” Da gudu ta wuce falon Adda Zubaida, domin kuwa duk sai ta ji kunya ta kamata. Ajiyar zuciya ya yi, shi dai ya rasa har rana mai kamar ta yau, bai taba jin son ‘ya
mace ya shige shi farad daya ba irin yadda ya shige shi lokacin da ya fara ganinta a Kofar gidansu, tun daga wannan lokacin kuwa bai sake ganin wata ta burge shi ba, baya ga Umm Adiyya. Ga hankali ga ilimi, ga natsuwa, ga zaKin murya, ga ta ‘yar dadas da ita kamar a sace ta. Amma kuma ya rasa me Zai yi, ta ji tana sonsa? Domin kuwa ya yi magiyar, ya yi lallabar, ya yi iya nacinsa, amma duk a banza, ko kadan ba ta taba yabawa ba, hakan har ya janyo rabuwarsu, ga shi yanzu bayan shekaru. Amma ya gaza manceta, har yanzu, sannan kuma an takura shi da batun aure, amma ya kasa ganin yarinyar da za Www.bankinhausanovels.com.ng ta iya cike gurbin Adiyya a zuciyarsa. Kakkafe rigar ta sa ya yi, bayan ya wanko ta daga bandakin da ke manne da falon Yayan nasa, shi kwata-kwata kwara masa miyar da ta yi bai bata masa rai ba, illa ma dadiin da ya ji, saboda ko ba komai. Ya samu kulawa daga gareta.

*********

Tun shigarta daki kuwa ranar ta Ki ta fito, saboda gudun haduwarta da TJ. Gaba daya nauyinsa take ji, tunda ta fito fili ta nuna masa rashin Kauna, koda yake ta waya suka rabu. Tun wancan lokacin kuma Al
lah bai sa za ta sake ganinsa ba, sai yau. Ga shi irin haduwar da suka yi, ta sake masa laifi, don yanzu kam ko ya rama ba za taga laifinsa ba. Saboda ita Allah kadai ya san irin wulaKancin da ta yi masa, bata taba kallon idon mutum, ta kira shi Sarkin naci ba, sai a kan TJ. Duk da kuwa ya kasance mai haKuri da ita, ita ba taji ya kwanta mata a rai bane, duk da kuwa ya hada duk wani abin da ran ‘Ya mace zai so a mijin aure. Adda Zubaida ce ta shigo dakin tana Www.bankinhausanovels.com.ng dariya ta ce, “Ummu, Ho! To sai ki je ku gaisa ai, TJ. Ne yake kiranki a falo, wai kin kwara masa miyar kuka kin gudu.”Lah! Adda Zubaida. Allah ban san yana bayana ba ne, shi ya sa, ni kuma ina juyawa miyar ta kwabe, don Allah ki ba shi haKuri.” Ta fada tana zazzaro idanu kamar wacce aka ritsa a tsakiyar yin sata. Cikin saibi ta dawo falon, wannan karon da lullubinta, ita sai yanzu ma ta tuna yadda ta hau goge masa jiki, gaba daya, sai abin ya Kara sa ta ji kamar ta nitse cikin Kasa. “Haba Ummu A. Ke kuma daga yin kuskure, sai guduwa? Ehn? To ni zan ma bar
gidan ki dawo falon, ki zo ki sake abinki.”
Ba haka bane fa Uncle TJ… Kawai dai…” Ta fara magana kuma sai ta yi shiru, tana ta faman murza hannayenta cikin juna. Yaa subhanAllah! Yarinyar nan komai tayi burge shi take yi, ji irin alkunyarta.
“Yaya wurin su Maami?” “Lafiyarsu Kalau.” “Tunda kin Ki yarda na je na gaishesu, zan je on my own, don yanzu aiki na ya dawo Abuja.” Ji ta yi gabanta ya yi wani mummunar faduwa, yau ta banu, ta zaci fa ya manta da wannan maganar. “Uncle TJ, don Allah kar kaje.” Ta so ta ba shi dariya, yadda ta yi maganar cikin sauri, “Kar ki damu wancan maganar ta wuce, by the way, na ji an ce aurenki ya kusa?” Har yanzu kallon razana take masa, “Wa ya fada maka?”Tunda bikin na rowa ne, sai mu ce Allah ya bada zaman lafiya. To ni zan shige, yaushe za ki koma Abujan?”
“Ni kam ina nan, don na gama Documentation, saboda haka zan fara aiki gobe Inshaa Allah.” “To Allah ya taimaka.” Ya fada kamar zai ce wani abu kuma dai ya yi shiru, don haka ya mike ya bar falon. Ta yi minti biyu a wurin, kanta duk ya bi ya kulle, shigowar Adda Zubaida ne ta ganta a wannan yanayin. “Kar ki Www.bankinhausanovels.com.ng damu, in dai TJ ne ya mance komai, domin kuwa muddin ya yiwo halin Baban Walid, to ina da tabbacin abu guda. TJ. Ba zai taba riKe ki da abin da ki ka
masa ba. Don haka ki kwantar da hankalinki, kin ji?”
“To yaya na iya Adda Zubaida? Ke da danginki kin fi ni saninsu.” “Yawwa ko ke fa.” Sai dai a wannan daren ba tunanin haduwarta da TJ Bane ya hanata barci, tunanin Yaya Zaid ne ya cika mata zuciya, amma a karo na farko ba muradin Kaunar sa bace ya dameta, sai tsantsar haushinsa da ya cika mata zuciya, ko akan wane dalili ne ya Sa hakan ya faru. Ita ma ba zata ce ga shi ba.

***********

Hankalinta kwance, yau satinta biyu a Bauchi, kullum kuma sai ta yi waya da Maami saboda ta yi kewarsu sosai, tamkar ba ta taba barin gari ba, zuwa wani wurin, bayan rabin rayuwarta a wasu garuruwan ta yi su, a dalilin makaranta.

Keke Napep yana ajiyeta a Kofar gidan Adda Zubaida, gabanta ya yanke ya fadi, saboda motar da ta gani a Kofar gidan. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke da ta shiga falon, ba ta ga kowa ba, amma ta ji mamaki Kwarai. To waye ya zo da motar? Tunda ba ta ga alamar baKi a gidan ba. Wanka ta yi ta zura doguwar rigar Cotton mai dan aiki a wuya, sannan ta samu Adda Zubaida a kitchen, turus! Ta tsaya, saboda aikin da ta gani a kan durowar kitchen
iin, tabbas an yi baKi, duba da yadda aka jere Www.bankinhausanovels.com.ng Warmers bayan na Mai-gidan. “Adda Zubaida lafiya na ganki wujiga-wujiga cikin aiki?” “Ai shigo ki gyara min kajin nan, zan yi marinating ne, ina son wancan hadin da ki ke yi. Sannan ya ce yana son kunun semo. Meye kuma kunun semo? Anyways, ya ce kin iya, za ki masa, kin san yadda yake so.” Zaid Abdur-Rahman, ba za ka share abin da ka ke min ba. Ka sani a gaba a kamfaninka, na yi shiru. To ba za ka biyoni inda na ke, kuma ka sani a gaba ba. “Na manta yadda ake yi Adda Zubaida.” Zubaida kallonta kawai ta yi, tun ba yau ba ta kula da Adiyya sam ba ta sa kanta a cikin lamarin da ya shafi Zaid. “Don Allah ki yi haKuri ke ma kin san halin rigimar Yaya Zaid, ba zan iya masa ba, ki duba cloud kawai. Ko Google ki hau, amma don Allah ki nemo yadda ake yi ki masa. Musamman ya ce wanda ki ke yi, don haka idan kin yi zai fi, ni tunda na kema, sai yau na san ana yin kunun semo.” Adda Zubaida ta so ta ba ta dariya, wannan ya sa kawai ta wuce, kai tsaye ta bude Cupboard ta fiddo tukunya madaidaiciya, sannan ta dauki gwangwanin madarar gari. Ganin haka Adda Zubaida kam ta rasa abin cewa, amma tabbas ta san koma me yake tsakanin Yaya Zaid da Umm Adiyya, ba Karamin abu bane. Ita ta shirya komai a wurin cin abinci, su hudu suka shigo daga masallaci, bayan Issha’i. Zaid ne da Baban Walid, sai Salisu abokin Yaya Zaid da kuma…
Numfashinta ne ya tsaya cak! Ganin TJ. Yana jawo Kofa. Yau yaya za ta yi da rayuwarta? WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Da sauri ta sa kai ta wuce cikin gida. Hannunta har gumi yake yi, ta san dai ba ta yaudari kanta ba, bare TJ. Tun farko ta fito ta fada masa akan abinsu ba mai dorewa bane, amma yau ganinsa da Yaya Zaid, ya sa cikinta duran ruwa, yanzu idan ya fadawa Yaya Zaid yana sonta, koda wasa ne. Yaya Zaid zai fadawa su Abba, yana fada kuwa shi kenan, daman Abba kiris! Yake jira. Hira suke yi a wurin cin abincin, amma hankalinsa kwata-kwata baya wurin, tun dazu
yake zuba idanun ganin ta fito. Amma shiru bai ganta ba. Haka dai ya daure bai tambayi Zubaida ba da ta shigo don su gaisa sosai. Har dai Salisu ya nemi ya kai shi masaukin sa, don haka suka wuce hade da yiwa Adda Zubaida sallama. Sai da ta ji falon tsit! Sannan ta koma kwasan kwanuka. Nan ta zauna tana kallon
labarai don T.V din falon Adda Zubaida ya samu matsala. Karar Kararrawar falon ne ya dawo da ita kalinta zuwa ga Kofa, a hankali ta ajiye
Safiyya da ta yi barci a kan Kafafunta, ta yafa mayafinta, sannan ta isa zuwa Kofar.
Kasancewar Kofar ta glass, tun kan ta bude ta ga waye ne, wannan ya sa suka tsaya kallon-kallo.
Za ki bude Kofar ko sai Karfin tabarau dinki ya Kare?” Tura gilas din idanunta ta yi saman hancinta, sannan ta yi saurin bude Kofar. Me yake damunki Ummu A. Yaya za ki bari ya rinKa kamaki ki na masa irin wannan kallon, ai zai dauka ke mayya ce.
Baya ta matsa, bayan ta bude Kofar, tana shirin daga Safiyya ne ya ce, “Saboda kin bar KarKashina a wurin aiki, ki sani ba wannan bane zai sa kiga mutane ki shiga masu raini ba, a garin nan ba a gaida na gaba da mutum ne? Ko kuwa dai wannan ra’ayinki ne? Kamar yadda _ Irresponsibility yake cikin dabi’unki?” Hawaye ne kawai ta ji sun cika mata idanu, kamar za ta yi kuka don ciwon

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *