UMM ADIYYAH CHAPTER 81 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Suna gama jin bayanin Saadik, Nas aka koma
kurawa idanu, “Tana hutawa yanzu,
amma za a gyarata a mayar da ita (Side
Ward).”
Lokacin ne suka sauke ajiyar zuciya. Maami
ko ta mika baby wa Babansa, ta duba
Zubaidan sama-sama, sannan ta ce da Abba za
ta je gida ta ga me suke ciki.
“Su kadai ne a gidan.” Kasancewar duk a
masauki suka sauka, wannan ya sa kowa
ya riga ya wuce ta can daga gun walima.
Su Umm Adiyya aka bari don su ga yanayin
Adda Zubaidan, kafin Maami ta je
gidan. Faruk ne ya tuka Abba da Maamin, aka
bar Zaid da Baban Walid a asibitin.
Koda Maami za ta taho asibitin ma da su
Walid ta taho. Da ta tashi zuwa wurin
Www.bankinhausanovels.com.ng
Saudah kuwa Umm Adiyya ta ce ta bar su asi-
bitin za a sake dawowa da Saudan.
Ana mayar da Adda Zubaida dakin gefe, aka
ce za su iya shiga su ganta. Baban
Walid ne ya yi gaba.
Asma da Umm Adiyya aka bari da leke ta
yi.