UMM ADIYYAH CHAPTER 92 BY AZIZA IDRIS GOMBE
zogin da ke cikin kirjinta ya ragu.
****k*********
BABI NA HAMSIN DA HUDU
Washegari yana dawowa daga wurin aiki, ta
tarbe shi cikin kyakkyawar shiga da
fara’a a fuskarta kamar ba abinda ya faru a
jiyan.
“Hmm! Me ake shirya mana a gidan, sai
kamshi tun daga waje?”
Murmushi ta yi ta ce, “Surprise ne, ka kimtsa
kafin nan.” Daidai lokacin yaran suka
shigo kicin din da gudu kowa yana *Abbie!
Abbie!! Dukansu ya daga sama yana
masu cakulkuli. “Ehhhm! Waye ne wannan?
Mr. Chubby da Mr Chubbilee.”
Kyalkyalewa suka yi da dariya.
“Ku tafi ku ba ni wuri, na karasa aiki na, kun
cika min kunne.” Umm Adiyya ta fada
tana korarsu da matsamin hannunta.
“An fasa mana rakiyar ne?” Zaid ya fada,
lokacin da Saalim yake kokarin dare