UMMI CHAPTER 11
MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO+ Fatima ce zaune a main falon gidan yayinda take jiran fitowar Ummi. Tana nan zaune ne Ummi ta shigo falon sanye cikin doguwar Jallabiya wadda ta bala’in yi mata kyau. Ta yafa gyalen jallabiyar a kanta yayinda jelar gashinta wanda ta kitsa ya sauka har bayanta. Fuskar ta fayau amma fa tayi kyau sossai tunda dai dama Ummin ku kyakyawa ce.. Fatima dai tunda ta shigo ta sanya mata idanuwa yayinda take mamakin wai wannan itace aka ce ‘yar shekara Goma sha bakwai.. like how??? A ranta kuwa tace “lallai fa Maleeka is in trouble”1 Cikin fara’a Ummi ta qaraso tace “Adda ina wuni” Fatima tana murmushi tace “lafiya Babyn Hamma.. ya gida??” Tace “lafiya lau.. bari in kawo miki abun motsa baki..” Da sauri Fatima tace “yi zamanki ‘yar uwa…” Bayan Ummi ta zauna ne Fatima tace “ya fadi miki cewar zamu fita ko??” Tana murmushi tace “eh Adda.. amma ina zamu je?” Fatima tana murmushi tace “wurare dayawa…” ♧♧♧♧♧♧♧♧ Ummi dai tunda suka fita da Fatima shopping suka je suka yi na kayan sawa masu yawan gaske.. Kama tun daga dogayen riguna, English wears, night wears, inner wears da sauran su. Dukda anyi rigima sossai da ita wurin zaben kayan, Fatima bata bi ta kanta ba. Haka ta dinga kwasar mata kaya masu zafin gaske yayinda ita Ummin ta dinga kumbure-kumbure.1 Cosmetics ma ta zabar mata masu kyau da tsada, turarruka ma haka designers. Sossai suka kashe kudi. Bayan sun gama siyayya ne suka nufi plush beauty lounge (salon and spa). Ko da Ummi ta bude kanta gaba daya masu aikin salon din harda customers aka dinga mamaki ana yaba kyau da tsawon gashin ta.. Ma’aikatam wurin ma cewa suka yi basu taba ganin mai tsawon gashin Ummi ba.. Ganin ta fara sol suka dinga fadin ai da ganinta ma ba ‘yar Nigeria ba ce.. Dayake dai yawanci da turanci suke magana ita bata ma san abinda suke fadi ba.. Fatima ce take amsa su yayinda take ta kwasar dariya na rudewar da suka yi. Wasu lokutta ma Ummi ce take tambayar ta me suka ce wanda take fadi mata. Haka aka gyare mata gashinta yayi kyau sossai sai qyalli yake yi.. ga wasu mayyuka masu kyau, qamshi da tsada da aka sanya mata. Dayake anyi mata stretching sai gashin ya qara tsawo. Ita kanta tayi mamakin ganin yadda gashinta yayi tsawo.. abin har tsoro ya dinga bata. Masu wurin sun so suyi ma Ummi gyaran jiki domin kuwa sun iya sossai amma Fatima tace basu so. Sun dai yi mata pedicure da manicure.. Ummi dai nan da nan ta canza kamar ba ita ba. Straight gidan Fatima suka wuce wanda yake Maitama. A nan ne kuma Fatima ta fitar da wasu turarruka da mayyuka masu qamshin gaske kala-kala. Ta tara ruwa a Jacuzzi bath ta sanya turarrukan wanka masu qamshin bala’i a cikin bath din sannan ta umurce Ummi akan ta shiga ta zauna a ciki na tsawon lokaci. STORY CONTINUES BELOW Gaba daya bathroom din da dakin sai qamshin turarukan suke yi. Bayan ta fito ne ta hada ta da wasu mayyuka ta shafa a jikin ta tas. Ummi dai gaba dayan ta banda qamshi babu abinda take zabgawa. Ita dai dama tana son qamshi shiyasa MK yake birge ta.. a kullum zaka ji yana qamshi don haka ne ta ji dadi sossai.. Fatima ta zaunar da ita ta fara yi mata lecture akan zaman aure. Tun Fatima tana yi Ummi tana kunya har ta warware… wasu abubuwan ma da Fatima take fadi sossai Ummi take mamaki.. ita ya za’ayi ta tsaya a gaban MK kamar wata ‘yar iska.. ita fa ba wai tana so suyi abubuwan da ake yi idan aka yi aure bane… kawai sai tana so ta zauna da shi ne. Fatima dai gaba daya ta warware ma Ummi duk wani sirri da dabara na yadda zata tafiyar da MK… dukda ta kula Ummi is not interested ta tabbatar zata gane tayi fiye da abinda tace mata gradually… toh Allah yasa..1 ♧♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE MAITAMA Yinin yau MK yana gidan yana ta son ganin Abba amma sam Abba ya qi kula shi. Asali ma baqi yayi wanda suka dade suna discussing business… daga baya ma bayan baqin sun tafi shigewa dakin shi yayi abin shi. Mamy ma ko gaisuwar shi bata amsa ba. Babu shakka iyayen MK sunyi fushi da shi sossai akan auren Ummi da yayi. Gaba daya MK yana cikin tashin hankali.. ya rasa yadda zai yi da su… su saurare shi ma sun qi! Hafsah ce take qoqarin sanyaya mishi zuciya tare da bashi courage. Bayan sallan Isha’I Abba ya dawo daga masallaci wanda tare suka yi sallah da MK a masallacin amma ko da aka fito tafiyar shi yayi ya bar MK din sabanin yadda suke yi a baya (su jero suna hira har su iso gida) Yana zaune a falon shi tare da Mamy suna hira. MK da Hafsah ne suka shigo falon cikin sallama. Aikuwa suna ganin MK sai suka daure fuska.. Bayan sun zauna a qasa ne MK yayi gyaran murya sannan yace “Abba, Mamy don Allah kuyi haquri ku…” Abba wanda ya kalli MK directly ne yace “Kai Kabir.. wai ba na kore ka ba jiya? what makes you think nacin ka zai sa in saurare ka?..” Ya gyara zama ya cigaba da fadin “Yadda ka je kayi aure ba tare da izinin iyayen ka ba haka zaka je ka cigaba da rayuwarka without us.. just forget about us” Da sauri MK yace “Abba ya za’a yi in manta da ku?? you are my parents and I really am sorry for getting married without your permission wallahi I had no option ne but to…” Kai tsaye Abba ya dakatar da shi yace “you had no option at the time but you do have one now…” Da sauri MK ya dago kai yana kallon shi cike da fargaba yayinda ya ji Abba ya cigaba da fadin “…. ka je ka zauna da ita matar taka sannan ka manta da mu, ko kuma ka je ka SAKE TA and everything will be okay… the bottom line is ‘We your parents’ or ‘the girl you claim to be your wife’ …that’s final”15 Daga nan kuwa ya miqe zai bar falon yayinda ya juyo yace “and you have until tomorrow to decide..” ya juya ya fita. A nan ya bar MK cikin tsananin tashin hankali. Tunda ya fado duniya bai taba ganin tashin hankali irin wannan ba.. gaba daya ji yayi kanshi yayi mugun nauyi yayinda yake mishi azabar ciwo.. jikin shi ya riga yayi mugun sanyi. Dukda sanyin AC da take ratsa falon hakan bai hana shi zufa ba.. Me yasa Abba ya sanya shi a wannan tight spot din? why wont they just listen to him and understand? how can he choose between them and Ummi? For crying out loud they are both important to him in different ways.. STORY CONTINUES BELOW Su Abba iyayen shi ne wadanda suka haife shi suka bashi kulawa ta musamman suka bashi tarbiyya mai kyau wanda har gobe yana alfahari da kasancewar su iyayen shi, su suka bashi ilimi na boko da addini wanda a yanzu haka he has reached where he is because of them.. Ummi on the other hand is a reflection of him.. yarinyar da ta damu da shi fiye da kanta, yarinyar da take gane abinda yake damun shi without even asking, yarinyar da rayuwarsu ta kasance iri daya, yarinyar da idan ya rasa ta tamkar ya rasa tashi rayuwar.. he feels vulnerable without Ummi by his side.. she is like a guardian angel to him.. toh me yakamata yayi???2 Hafsah ce ta kalli Mamy cike da damuwa tace “Mamy don Allah ki sa baki a wannan maganar..” Mamy ta daga mata hannu yayinda tace “idan kika qara yin magana akan wannan zancen sai na ci mutuncin ki… Abban ku ya riga ya bashi zabi don haka komai ya rage nashi” Daga nan ta tashi ta nufi hanyar dakin mijinta ta bar su a nan zaune. MK dafe da kanshi sai zufa yake yi yayinda ya ji kan shi yana juyawa. Hafsah wadda take gefen shi ce ta dafa shi sannan tace “bro it’s time you tell them about what Ya Maleeka did… na tabbatar hukuncin nan da suka yanke a dalilinta ne. Suna gani kamar ka wulaqanta ta ne a matsayinta na ‘yar uwarka. I swear if not because I promised you cewar bazan fadi ma kowa maganar ba I would have told them…” Ajiyar zuciya ya saki sannan ya miqe yace “I still have until tomorrow Hafsah.. bari in tafi gida..”3 Hafsah wadda take kallon shi sossai take mamakin halin shi.. wato sai dagaske he is not ready to tell them about Maleeka? why?1 Ji nayi tace “Ya MK can you drive a halin da kake ciki?? mu je dai driver ya kai ka” Yace “dont worry Hafsy.. I will manage” ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Tsaye take a gaban Vanity Mirror yayinda take ta kallon kanta tana murmushi.3 Ummi tayi kusan minti talatin tsaye tana ta wasa da gashinta yayinda take cike da murnar yadda akayi transforming dinta.. har haske ta qara yi. Yanzu haka tana sanye cikin kayan baccinta na wandon three quarter da ‘yar qaramar T-shirt. Sai zabga qamshi takeyi… Fatima ta bata turarruka dayawa wanda ta fadi mata yadda zata yi amfani da su. Da na wanka da na fesawa sannan da mayyuka dayawa na shafawa. MK ne ya bude qofar dakin ahankali yayinda wani asirtaccen qamshi ya bugi hancin shi. Ganinta yayi a tsaye gaban mirror tana ta murmushi yayinda take wasa da gashinta. Sa mata idanuwa yayi yayinda ta birge shi matuqa. She looked so happy… A yanzu haka da ya shigo gidan hankalin shi a tashe ne amma kuma wani ikon Allah yana ganin fuskar yarinyar sai ya ji zuciyar shi tayi fayau.. Ummi is surely an angel in disguise!!1 Gashinta wanda yayi mugun tsawo ya bashi mamaki. Qamshin turaren shi ne da ta ji ya sanya ta juyo da sauri wanda hakan sai da ya sanya zuciyar shi ta buga… how can she be this beautiful??? Bai ankara ba ya ga ta fara dosowa wurin shi yayinda ya rude… she looked different. Composing kanshi yayi sannan cikin tsokana yace “wannan wacece??” Cike da mamaki tace “Hamma ni ce fa..” STORY CONTINUES BELOW Cikin rashin fahimta yace “ke wa??” Gani nayi ta dan kalli jikinta sannan ta kalle shi tace “Hamma ni ce Ummi.. wani abu ya samu fuska na ne da baka gane ni ba??”1 A rude ta koma gaban mirror tana kallon kanta yayinda tace “Hamma dagaske ni ce fa..” MK wanda ya qaraso wurinta yana murmushi ne yace “na gane ke ce Baby… kin canza ne sossai sannan kin qara kyau, you are beautiful..” Murmushi tayi yayinda tace “nagode Hamma…” Ita dai Ummi tana so idan MK yace mata she is beautiful.. ta sani sarai hakan yana nufin tana da kyau ne. Bata ankara ba ta ji ya rungumeta very tight ta baya yayinda ya kwantar da kan shi a kan kafadarta yana shaqar qamshin ta mai dadi… Ummi dai tunda ya rungume ta jikinta yayi mugun sanyi yayinda take ta kyarma. Gaba daya ta kasa motsi. Zuciyarta kuwa sai bugawa take yi. Ji tayi ya tura fuskar shi a cikin gashinta yayinda yace “Baby wannan duk gashinki ne haka?? ya akayi ya qara tsawo?? ko sun qara miki ne???” Muryarta qasa-qasa tace “Hamma ai babu kyau qarin gashi.. wani abu suka yi amfani da shi suka ja shi shine ya qara tsawo… yayi kyau??” Yace “sossai Baby…” Bata ankara ba ta ji ya juyota ta fuskance shi yayinda yayi hugging dinta very tight. Ita dai Ummi gaba daya ta sukurkuce domin kuwa wani yanayi ta shiga wanda bata taba shiga irin shi ba. A dalilin rudewa da tayi bata san lokacin da hannunta ya kai bisa gashin kanshi ba wanda kuma na ga tayi saurin zare jikinta daga nashi ta dafa goshin shi sannan ta shafa fuskar shi zuwa wuyan shi… Ji tayi kamar wuta saboda zafi. Hankalinta ne yayi matuqar tashi yayinda tace “subhanalillah… Hamma? jikinka yayi zafi sossai… baka da lafiya ne??” Bata ma bari yayi magana bane ta kamo hannun shi ta ja shi zuwa gadonta tace “zo ka kwanta..” Babu musu ya hau gadon ya kwanta yayinda ta zauna daf da shi tace “kan ka ne yake ciwo ko?? Hamma har yanzu su Abba basu amince da auren mu ba ko?? ka fadi mun gaskiya Hamma.. idan sun ce ka sake ni kawai ka sake ni in tafi don wallahi ko kadan bana so inyi sanadiyyar bata tsakanin ka da iyayen ka… iyaye suna da muhimmanci a rayuwar ‘ya’yan su don haka…” MK wanda yake ta kallonta a ranshi yace “ya za’a yi in rabu da ke Ummi?? ya za’ayi in rabu da yarinyar da ta fi kowa gane ni a rayuwar nan??” Cikin muryar kuka ya ji ta cigaba da fadin “…dama fa na san zai yi wuya su amince saboda ni din ‘yar qauye ce.. banyi karatu ba kuma ka ga dole zasu fi sonka tare da ‘yar uwarka..” Hannun shi ya dago ya toshe bakinta yayinda yace “Ummi stop… tabbas basu amince ba har yanzu amma kuma insha Allah zasu amince.. don Allah kar kiyi kuka kin ji??” Girgiza kai tayi tace “toh Hamma.. bari in kawo maka abinci sai ka sha magani…” Da sauri ya riqe hannunta yace “Bar abincin ki zo kiyi mun massage..” Da sauri ta matsa yayinda ta fara yi mishi kamar yadda yake so. Sossai yake jin dadin massage din yayinda asirtaccen qamshin da take yi yake ta ratsa shi. MK dai bai san lokacin da bacci kwashe shi ba. Ummi kuwa ko bayan da yayi bacci ta dade tana yi mishi massage din sannan ta daina.. Gani nayi ta sa mishi idanuwa tana ta kallonshi yana bacci. Allah dai ya sani tana son MK a rayuwarta.. idan su Abba sun qi amincewa da auren su kenan fa dole zata rabu da shi?? toh idan ta rabu da shi ina zata je?? ta sani cewar duk ranar da ta rabu da shi toh fa mutuwa zata yi. Gani nayi ta sa hannunta ta shafa gefen fuskar shi yayinda ta saki ajiyar zuciya. Ji nayi tace “Allah yasa kar su raba ni da kai Hamma..” Matsawa tayi daf da shi ta karanto addu’o’i sannan ta shafa a kan shi. Daga nan kuma sai na ga ta gyara pillow ta kwanta yayinda ta sa mishi ido har bacci ya kwashe ta. ************ Wuraren qarfe biyu na dare ne MK ya farka yayinda ya ganta kwance daf da shi. A yadda ta takure kuwa sai kace matsoraciya.. MK dai ya kula duk lokacin da yarinyar take bacci sai ta dunqule wuri daya… ko me yasa hakan?? Gyara kwanciyar shi yayi yayinda ya sanya mata idanuwa.. Hannu ya sa ya kawar da gashin kanta wanda ya rufe mata rabin fuskarta… as usual hular kanta ta dan zame yayinda tayi revealing gashin gaban goshinta da yake bala’in so.2 A kullum dai Ummi qara yi mishi kyau take yi. sossai ya shagala a kallonta. Kalaman Abba ne suka fado mishi a rai.. “ka je ka zauna da ita matar taka sannan ka manta da mu, ko kuma ka je ka SAKE TA and everything will be okay… the bottom line is ‘We your parents’ or ‘the girl you claim to be your wife’ …that’s final” Zuciyar shi ce ta buga yayinda ya runtse idanuwan shi ya bude.. A hankali na ji yace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… a bangare daya ga Ummi sannan a dayan bangaren ga su Abba” Ya qura ma Ummi idanuwa yace “bazan taba iya rabuwa da ke ba…”1 Ya dan yi shiru sannan kuma yace “su Abba???”1 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Kiran sallan farko ne MK ya farka ya ji ta maqale a jikin shi yayinda ta shaqe mishi wuya. Sossai ya cika da mamaki..+ this is the second time da take yi mishi haka.. toh ita haka take bacci?? ta maqale a jikin mutum sannan ta shaqe shi?? why?? A yau kuwa maimakon ya tada ta sai gani nayi ya qara matse ta jikinshi yayinda yake ta shaqar qamshinta… He never thought zai taba hada jikin shi da wata mace wadda ba Maleeka ba, he never thought zai kwanta a gado daya da wata wadda ba Maleeka ba.. Yau gashi tare da Ummi, a small girl wadda da alama she knows just a little or even nothing about married life… Kiran sallah na biyu ne ya dawo da shi daga duniyar tunani yayinda ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “hey beautiful, me kike yi a jikina yau kuma??” A firgice Ummi ta farka ta ganta maqale a jikinshi. Da sauri ta sake shi yayinda ta fara neman matsawa yayinda take addu’ar tashi daga bacci. Shi kuwa ya riqe ta gam.. Muryarta tana rawa tace “Hamma don Allah kayi haquri..” Ya dan bata rai yace “kuma dai??.. ni kawai ki gaya mun dalilin da ya sanya kike maqalewa a jikina kiyi bacci.. ko tsoro kike ji ne? gashi fa har shaqe ni kike yi” Shiru ta dan yi sannan ta kalle shi tace “Hamma wallahi gani nake yi kamar Daada zata zo ta zane ni idan ina bacci… ka ga kullum haka take yi mun idan ina bacci sai ta zo tayi ta zane ni akan in tashi inyi aiki shiyasa bana so inyi bacci ni daya a…” Daga nan kuwa sai ta fashe mishi da kuka. Allah sarki baiwar Allah… sossai ta bashi tausayi. Janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta yayinda yake bubbuga bayan ta yace “hey stop crying.. kin dai san dukkanin abinda ya faru a baya ya wuce ko? toh Daada bazata qara zuwa kusa da ke ba balle har ta taba mun ke kin ji?” Ya dago fuskarta saitin nashi yace “idan kina so daga yau ki dinga zuwa ki kwana a daki na har sai kin daina tsoron amma fa da sharadi daya..” Tace “wane sharadi Hamma??” Yace “bazaki dinga shaqe ni ba don yanzu haka ma wuyana ciwo yake yi…” yayinda ya fara stretching wuyan nashi. Da sauri ta matsa daf da shi tana taba wuyan nashi tace “don Allah Hamma kayi haquri ka ji..” Yana murmushi yace “toh kin amince?” Ita dai Ummi sau biyu kenan da tayi bacci tare da shi kuma har ga Allah wadannan kwanakin biyu suna cikin best nights dinta a duniya.. she feels secured and protected sleeping close to him don haka ba tare da wani tunani mai zurfi ba tace “na amince Hamma” ************* Wuraren qarfe takwas na safe yana tsaye a gaban mirror din dakin shi yana brushing kanshi yayinda yayi zurfi a tunani. The deadline is today.. wa zai zaba a cikin su??? UMMI ko IYAYENSHI??? Ya juyo ne zai dauki wayar shi a kan gado ya ganta a tsaye tana kallon shi. Ummi dai ta yi kusan minti biyar a tsaye yayinda ta kula kamar hankalin shi baya tare da shi. Murmushi yayi yace “baby ya aka yi ne??” Ta qaraso wurin shi tace “Hamma toh sai yaushe ne su Abba zasu amince da auren mu? ni fa ina jin tsoron kar a…” STORY CONTINUES BELOW Girgiza kai yayi yace “ssssshhhh…” Ya janyo hannun ta yace “insha Allah yau zasu amince… ki cigaba da yi mana addu’a” Ya bata side hug yayinda suka fito daga dakin. Ji nayi yace “wai wannan turaren naki wane iri ne haka??” Tana murmushi tace “Adda Fatima ce ta bani dayawa… kana son shi??” Yace “sossai ma Baby…” Cike da jin dadi tace “ka ga jiya da muka fita fa kaya dayawa muka siyo.. wai tace kai ne kace a siyo mun gashi na manta ban yi maka godiya ba.. nagode sossai Hamma, Allah ya saka da alkhairi” Murmushi yayi yace “Baby duk abinda nayi miki fa kamar kaina nayi wa… don haka ki daina godiya” Tace “amma fa Hamma kayan sunyi yawa..” Yana murmushi yace “Baby sunyi yawa fa kika ce.. toh ai har yanzu ma ban baki kayan lefen ki ba” Ta zaro idanuwa zata yi magana ne ya toshe bakin nata yayinda yace “sssshhhh” A haka ta ja shi zuwa dinning yayi breakfast wanda itace ta bashi a baki kamar yadda yake so. Bayan ya gama ne ya fita. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK-TECH SOFTWARE COMPANY MK dai bai yi niyyar zuwa ofis ba yau amma he needed to go out saboda zaman shi kusa da Ummi yana sanya shi ya manta abinda ke faruwa da kuma halin da yake ciki.. gashi he needs to do a very serious thinking as he is running out of time.. Yana kwance a daya daga cikin sofas na lounge din ofis din yayinda yake ta saqe-saqe a ranshi. Fahad ne ya qwanqwaso qofar ya shigo. Ganin abokin nashi a kwance ne yace “abokina ya haka?? ashe da gaske ka shigo.. I was just about to sign off some papers in zo in duba ka a gida tunda nayi ta kiran ka jiya baka picking” Ya zauna a kujerar gefen shi ya cigaba da fadin “… hey you dont look good.. kenan su Abba basu amince ba har yanzu??” MK ya tashi zaune yayinda yace “ko sauraro na sun qi yi…” daga nan ya ba abokin shi labarin komai da yadda suka yi da Abba. Fahad cike da mamaki yace “toh ya zakayi yanzu??” Kai tsaye MK yace “wallahi abokina ina son Ummi..”6 Zaro idanuwa Fahad yayi yayinda yace “wait what??” Yayi resting bayan shi a kujera yayinda ya rufe idanuwa yace “I swear I love Ummi very very much, Each time I touch my chest….” Ya taba qirjinshi yayinda ya cigaba da fadin “…I feel her deep in my heart. I feel solitude when I’m beside her, and I feel on top of the world when I hold her in my arms. Whenever I look at her cute face, I feel all the happiness in the world at once… I swear abokina In my thought, she has dominated my mind, and In my world, she rules my activities. I just cant live without her.. she is my life and I can never abandon her… not even in my wildest dreams..”5 Tunda ya fara wannan maganar kuwa babu abinda yake picturing sai UMMI, from her beautiful face to her beautiful long hair to her cute body to her sweet voice to her everything…. da kyau Romeo..2 Fahad wanda yake ta kallon shi cike da mamaki kasa ma magana yayi. MK ne ya bude idanuwan shi ya kalli abokin nashi wanda ya sa mishi idanuwa babu ko qyaftawa..1 Gani nayi ya harare shi yayinda yace “what?”4 Fahad ya fashe da dariya yace “nothing my friend.. na ji dadi sossai na yadda finally kayi admitting kana son Ummi.. I swear ni na san hakan tuntuni kawai dai kai din ne ka qi admitting” STORY CONTINUES BELOW Ya gyara zama yace “Yanzu dai with regards to zabin da Abba ya baka I think the only way out is to talk to Daddy then..” Da sauri MK yace “what?? Daddy fa kace.. ka manta shine mahaifin Maleeka?? haba abokina ai da kunya ace inyi mishi maganar.. ka ga fa ko gidan na kasa zuwa saboda…” Fahad ya dakatar da shi yace “haba MK, we both know cewar Daddy yana da sauqin kai sossai… Tun kana qarami Daddy has always been there for you a duk lokacin da Abba baya nan.. Ka zauna a gidan Daddy tsawon shekaru and he has been nothing but a good father to you… na tabbatar idan kayi mishi bayani zai fahimta. Again, I will still tell you this.. idan har abubuwa basu daidaita ba dole ne ka gaya musu abinda Maleeka tayi maka tunda it’s a serious issue. Yin hakan kuwa shine kadai zai sa su amince da auren nan da kayi straight up.. this is your last resort abokina”2 MK ya dafe kan shi yayinda yace “insha Allah it wont come to that… the last thing da nake son yi a rayuwar nan shine in tona ma Maleeka asiri..”2 hmmm.. Fahad ya girgiza kai sannan yace “it’s okay my friend.. try and talk to Daddy din… hopefully idan yayi ma Abba magana zai saurare shi” A haka dai suka cigaba da hirar yayinda MK ya dauki shawarar abokin nashi na yayi ma Daddy magana. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune yake a qasan falon Daddy yayinda ya gama basu labarin abubuwan da suka faru. Bayan ya gama fadi musu komai ne Daddy ya sa Mummy ta kira Maleeka. Wani ikon Allah tun kafin yanzu daga Daddy har Mummy basu ji haushin auren da MK yayi ba.. Sun tabbatar haka kawai bazai aikata hakan ba without a genuine reason. Allah ya sani sun yarda da halin MK 100% and at this point in time ma sunyi trusting MK fiye da ‘yar da suka haifa- Maleeka.4 Daddy ne ya kalli Mummy yace “wai tana ina ne? bata san ita ake jira bane?” Mummy tace “tace tana zuwa….” Kafin Mummy ta rufe bakinta ne Maleeka ta shigo falon. MK wanda ya dago kai ya kalle ta kuwa gani nayi fuskar shi yayi displaying tsananin mamaki. Rabon shi da ganin Maleeka tun lokacin da tayi confronting dinshi akan Ummi wanda ya sanya har ya shaqe ta tare da furta mata kalaman da shi kanshi bai so ya furta mata su ba. Maleeka tayi ma MK laifi amma kuma wani ikon Allah bai taba blaming dinta ba.. he blames himself because ya sani cewar he has played a major role all through her upbringing.. MK ya shagwaba Maleeka sossai.. he has always done duk wani abinda take so and it used to be very difficult for him to scold her idan tayi mishi laifi. Abubuwan da yake tilasta mata tayi ma ba da son ranshi bane sai don ya zama dole domin kuwa yawanci irin abubuwan da suka shafi addinin mu ne wanda babu wasa a ciki. MK still sees Maleeka as that little girl that he adores, yarinyar da ya girma da sonta a cikin zuciyar shi. A yanzu haka da yake kallonta he is blaming himself for all that she is going through. Maleeka ta rame, fuskarta ta kumbura tayi jajawur da alama ta ci kuka sossai.. she looks sick and it’s all his fault.1 Jiki a sanyaye ta qarasa shigowa falon yayinda ta samu wuri ta zauna a gefen mummy a qasa. Tunda ta shigo bata kalli MK ba domin kuwa wani azababben kishi ne yake ta addabar zuciyarta. Gaba daya ji take yi kamar zata mutu.2 Muryar Daddy suka ji yace “toh Maleeka, ga mijin ki nan ya zo ya fadi mana dukkanin abubuwan da suka faru…” Da sauri ta dago kai ta kalli MK wanda yake kallonta. Gani sukayi ta fashe da kuka yayinda tace “Daddy wallahi bazan qara shan pills din ba.. amma don Allah kace mishi ya sake ta.. ni wallahi bazan iya zama da shi tare da wata ba..”14 Gaba dayan su kallonta suke yi cike da mamaki yayinda MK yayi saurin fadin “Babe please stop…” Maleeka wadda take ta rusa kuka ta rarrafa gaban shi ta riqe hannun shi sannan tace “i promise you bazan qara shan pills din ba wallahi I am ready to give you a child Honey amma don Allah ka saki yarinyar nan..”3 Muryar Mummy na ji tace “what???” Daddy wanda yake kallon fuskar MK ne yace “me take fadi haka MK?? you didn’t mention this ai..” Cikin rashin fahimta Maleeka ta kalli Daddy sannan ta kalli MK tace “na shiga uku.. Honey dama ba abinda ka fadi musu kenan ba??”4 Mummy ce tace “you are very stupid Maleeka”4 Daga nan kuwa ta rushe da sabon kuka yayinda Mummy ta cigaba da fadin “dama can iskancin da kike yi mishi kenan a gida?? dama maganin hana daukar ciki kike sha???” Ta kalli MK wanda hankalin shi yake a tashe tace “kai kuma shine kayi shiru baka kawo zancen gida ba??”4 Da sauri MK yace “don Allah mummy..” Bata bari ya qarasa magana ba tace “shut up MK, dama kai a rayuwarka baka son ace Maleeka tayi laifi. yanzu akan wane dalili zaka kare mata bayan ta aikata mummunan abu kamar wannan??” Ta kalli Maleeka tace “Toh ai maganin ki kenan.. gwara da ya auro wata wadda zata zo ta Haifa mishi yaran tunda ke baki so.. da ba’a haihuwa za’a haife ki ne?? shashashar banza kawai”5 Maleeka ce ta rarrafa wurin Daddy wanda yake kallonta with disgust tace “Daddy don Allah kuyi haquri..”2 Daga mata hannu yayi yace “ai ba mu kika yi ma laifi ba Maleeka… mijinki kika yi ma laifi. Maganar ya saki matar shi kuwa bata taso ba. A yanzu tunda kin gane kurenki tashi zakiyi ki bi shi ku tafi gida ku cigaba da zaman auren ku” Cike da tsananin tashin hankali tace “wallahi Daddy bazan iya zama da kishiya ba…”3 Yace “toh sai ki cigaba da zama tare da mu a gida…” Ya kalli MK yace “maza tashi mu je gidan Abba.. ai kam dole ya amince da auren da kayi ko don wannan al’amari da ya faru”5 MK dai jiki a sanyaye ya miqe yayinda yake kallon Maleeka wadda take ta rusa kuka a falon kamar zata mutu. Sossai ya ji tausayinta. Ya sani sarai Maleeka bata son kishiya, bata so ta ga mace a kusa da shi.. Bai taba sa ran wata mace zata shigo rayuwar shi ba bayan ita but Ummi came all along.. the girl with a pure heart, yarinyar da ta damu da shi fiye da kanta.. Yarinyar da ta sace mishi zuciya lokaci daya. Ya sani cewar Maleeka tana bala’in son shi amma kuma sun samu bambancin ra’ayi. taurin kanta da girman kanta sun hana tayi making just one sacrifice for him.. Tabbas MK bai daina son Maleeka ba amma kuma bala’in son Ummi yake yi… at this point in time UMMI is his everything and he can never let her go for anything or anyone a rayuwar nan!!5 ♧♧♧♧♧♧ Tsaye take a gefen shi tana ta kallon shi yayinda yake gaban vanity mirror na dakin shi yana qarasa shirin zuwa ofis.+ Ummi dai tun jiya da ta ji labarin cewar su Abba sun amince da auren su ne take cikin tsananin farin ciki. A yanzu haka sunyi da MK idan ya dawo daga ofis zasu je gidan. MK wanda yake qoqarin zura agogo a hannun shi ne ya ga tayi saurin karba tare da fadin “bari in sa maka Hamma…” Yana murmushi yace “toh Baby nagode..” Yana ta kallonta har ta gama sa mishi. Bayan ta gama ne tace “saura takalmin ka, mu je ka nuna mun wanda zaka sa..” Janyo ta yayi da sauri yayinda ya rungume ta ba tare da yace komai ba. Kusan tsawon mintuna biyar suna a wannan position din. Bugun zuciyar juna kawai suke ji yayinda qamshin junan su yake ratsa su. Ummi wadda take manne a jikin shi ce tace “Hamma zaka yi latti fa..” Muryar shi qasa qasa yace “laifin ki ne ai.. ” da sauri tace “me nayi??” Yace “kin hana ni tafiya.. ban taba son kasancewa tare da wani abu ba kamar ke Ummi, meyasa kika shiga raina da yawa haka??” Dariya tayi tace “Hamma nima fa kana raina.. kullum fa ina cikin tunaninka. wallahi bana so ka fita kawai dai don aiki…” Kafin ta qarasa magana ne yace “shirya mu tafi tare…” Zaro idanuwa tayi tare da breaking hug din tace “dagaske Hamma??” Yace “eh.. ai dama baki taba zuwa ofis dina ba don haka ki zo mu je.. idan na gama meeting dina ma sai mu tafi gidan Abba daga can kawai” Cike da murna tace “toh Hamma bari in je inyi wanka..” A guje ta fita daga dakin yayinda ta barshi a nan tsaye yana murmushi. With each second that passes qara son yarinyar yake yi.. MK dai yayi ma kanshi alqawarin tarayya ta aure bazata shiga tsakanin shi da Ummi a yanzu ba domin he sees her as a small girl that is not ready for that.. Ya tsara akan sai nan gaba idan ta qara girma.. Shin zai iya???12 *********** Yana zaune a falon shi ta fito sanye cikin doguwar riga ta Jallabiya yayinda ta yafa gyalenta a kanta. Tunda ta fito MK ya sanya mata idanuwa. Babu kwalliya a fuskarta amma tayi bala’in kyau. Ummi is a natural beauty. Ta qaraso wurin shi sai zabga qamshi take yi. Tana murmushi tace “na shirya Hamma” Ajiyar zuciya ya saki sannan ya miqe yace “kinyi kyau Baby.. Yanzu haka zamu fita mutane suyi ta kallon ki?” Cikin rashin fahimta tace “Hamma baka so a kalle ni ne? meyasa??” Ya girgiza kai yace “zan fadi miki watarana” Tana riqe da jakar Macbook dinshi suka fita. ♧♧♧♧♧♧♧ MK-TECH SOFTWARE COMPANY Tare suka shigo kamfanin. Yana riqe da hannunta yayinda take riqe da jakar Macbook dinshi. MK yayi da ita ta bashi amma ta qi.. a cewarta wai bata so ya wahala. Shi kam sossai yake mamakin yadda Ummi bata bari yayi komai when it’s supposed to be the other way round.. how can he not fall in love with someone who cares about him more than herself?? STORY CONTINUES BELOW Ita dai Ummi tunda suka shigo take ta kalle-kalle. bata taba tunanin akwai wuri mai kyan haka ba a qasar nan. kusan komai glass ne.. hatta floor din da take takawa gani take yi kamar zai fashe. Ma’aikatan ne suke ta gaishe su yayinda MK yake amsawa. Ummi kuwa hankalinta yayi nisa yayinda take cike da mamaki. Haka ma’aikatan suka dinga bin ta da kallo suna yaba kyan ta dukda dai basu san ko wacece ba. A lokacin da suka shiga lift ne ta riqe shi gam yayinda tace “Hamma meye wannan muka shiga??” Yana dariya yace “lift sunan shi… zai kai mu sama ne inda office dina yake.. kin ga idan mun bi ta matakala zamu bata lokaci tunda kin ga office dina yana hawa na biyar ne” Kafin tayi magana lift din ya bude alamar sun iso 5th floor din. Ganin wannan floor din kuwa sossai Ummi ta rude. Ji nayi tace “amma dai Hamma wurin nan yana da kyau.. yanzu duk kai ka gina wannan??” MK dai ya san Ummi da tambayoyi kamar ‘yar jarida.. wasu tambayoyin ma idan tayi mishi sai ya rasa yadda zai amsa mata su.. A haka dai suka isa ofis dinshi yayinda take ta yi mishi tambayoyi yana amsawa. Suna shiga kuwa ta zaro idanuwa tace “laaa.. Hamma dama nan ne??” Dariya yayi yayinda yace “nan ne Baby.. yayi kyau??” Tana zagaye ofis din tace “sossai ma Hamma.. dama fa idan muna video call ina dan ganin wurin yana birge ni ashe ashe ma ban ga komai ba..”1 Ta nufi wurin table dinshi ta ajiye mishi jakar Macbook dinshi yayinda ta zuge zip din ta fiddo ta ajiye a gaban shi.. MK wanda yake zaune a kan kujerar shi yana ta kallonta sossai take birge shi.. ya kula idan ya biye ma Ummi bazai qara yi ma kanshi komai ba saidai ita tayi mishi. Yana murmushi yace “nagode Baby.. toh zauna..” Girgiza kai tayi tace “a’a Hamma.. ban gama kallon ofis dinka ba..” Ta juya yayinda ta cigaba da bin ofis din da kallo kamar wadda take inspection. Yana dariya ya kunna Macbook dinshi sannan ya fara duba mails dinshi. Yana yi yana dago kai yana kallonta. Ji yayi tace “wallahi Hamma komai naka yana birge ni.. duk wani abun ka mai kyau ne” Kai tsaye yace “harda ke Baby… kuma duk kin fi wani abinda na mallaka kyau” Tana murmushi ta juyo ta kalle shi tace “nagode Hamma” Wayar shi ce tayi ringing ya duba ya ga sunan abokin shi. Ko da yayi answering ji nayi yace “okay gani nan” Bayan ya kashe ne na ga yayi dialing intercom sannan yace “Nayla please come to my office” Nayla ce ta qwanqwaso qofar ta shigo tare da russunawa tace “morning sir” Yace “morning Nayla.. I will be having a meeting at the conference room… please get some ice cream for my wife” Cike da mamaki Nayla ta juya ta kalli Ummi yayinda ta juyo tace “okay sir” tana murmushi tace “congratulations sir” Ya gane me take nufi sai yace “thanks Nayla” Ita dai Nayla tayi mamakin yadda MK ya qara aure.. toh ya akayi Maleeka ta bari?? Da ta juyo zata fita ne ta qara kallon Ummi sannan tace “good morning ma’am” harda dan russunawa. Ummi wadda fuskarta tayi displaying confusion ce ta kalli MK tace “Hamma me tace???” STORY CONTINUES BELOW Yana dariya yace “gaishe ki tayi Baby..” Ita dai Nayla tuni ta fita daga ofis din yayinda Ummi tace “shine harda russunawa??? ai wannan ta girme ni” MK wanda ya tashi daga kan kujerar shi ya nufi wurinta yana dariya ne ya janyo ta jikin shi ya rungume ta sannan yace “girma take baki a matsayinki na matar Hamma.. ni zan shiga meeting amma bazan dade ba.. idan na fito sai mu je gidan Abba” Tace “toh Hamma… Allah ya baku sa’a. don Allah kar kayi aiki dayawa kanka yayi ciwo ka ji??” MK dai qara matse ta yayi jikin shi a ranshi yana fadin “You are surely my greatest achievement a rayuwar nan” Ummi dai jin ya qi sakinta ne tace “Hamma.. zaka shiga meeting fa kace” Ajiyar zuciya ya saki sannan yayi breaking hug din. Bata ankara ba ta ga ya duqo saitin fuskarta yayi mata peck a kumatu sannan yace “na tafi..” Ummi dai wani shocking ta ji a kumatun yayinda ta dafe daidai wurin tana kallon shi cike da mamaki har ya fita. Gani nayi ta lumshe idanuwa yayinda tace “na shiga uku da Hamma.. duk inda ya taba ni sai in ji kamar wuta ta ja ni… meyasa??”3 Nikuwa nace habwa Ummi, you never see anything🤣4 *********** After 2 hours.. Zaune take a kan kujerar shi yayinda ta sa Macbook dinshi a gabanta tana ta kallo tana murmushi. Idan ka gan ta a hakan zaka rantse kujerar ta ce dama. MK ne ya shigo ofis din tare da Fahad wadanda suke hira akan abubuwan da aka tattauna a meeting din. Ganin ta zaune a kan kujerar shi ne ya sanya su yin shiru yayinda Fahad ya fashe da dariya. MK kuwa da sauri ya qarasa don ganin abinda take yi… shi kam addu’ar shi kawai Allah yasa ba tampering mishi da files take yi ba. Yana isowa wurinta kuwa na ga ya tsaya yana mamaki. She wasn’t actually doing anything domin kuwa homescreen dinshi ya gani.. meaning bata shiga ko ina ba. Dago kai tayi ta kalle shi sannan tace “Hamma hoton nan naka yayi kyau sossai.. na kusa awa daya ina kallo.. idan ya bace sai in danna nan..” ta nuna mishi wani key a kan Macbook din2 MK ma bai san lokacin da ya fashe da dariya ba. Duqowa yayi saitin fuskarta yace “kina son hoton ne??” Tace “sossai ma Hamma” Yace “zan tura miki a waya..” Tana murmushi tace “nagode… amma meyasa hoton babu kala??” MK ya girgiza kai yana murmushi… a ranshi yace “ta fara kenan..” tambayoyi non-stop. Fahad wanda yake dariya ya qarasa shigowa ya zauna a kujera ne ya katse musu conversation yayinda yace “baka fadi mun tare da amarya ka zo ofis ba yau” MK yana murmushi yace “tare muka zo abokina.. dama ina so ne after the meeting kawai mu wuce gidan Abba” Fahad yace “I am glad they accepted the marriage abokina” Kafin MK yayi magana ne Ummi ta miqe tare da fadin “Hamma bamu gaisa ba… ina kwana” Yana murmushi yace “lafiya lau Babyn Hamma.. ya gida” Tace “lafiya” sannan ta kalli MK tace “Hamma zo ka zauna” yayinda ta matsa mishi. MK ya zauna ne Fahad ya miqe tare da fadin “abokina bari a gama hada documents dinnan kayi signing kafin ka tafi don Allah… don nasan zai yi wuya mu qara ganin ka yau” STORY CONTINUES BELOW MK yana murmushi yace “I will be waiting” Bayan ya fita ne Ummi wadda take tsaye a gefen shi ta ga yayi resting bayan shi jikin kujera yayinda ya dago kai ya kalle ta itama. Bai ankara ba ya ga ta zagaya ta bayan shi sannan ta fara yi mishi massage tana fadin “Hamma ka gaji ko??” MK wanda yake bala’in enjoying moment irin wannan kuwa ko magana bai yi ba yayinda ya lumshe idanuwa. Ji nayi yace “an kawo miki ice cream din?” Tace “eh Hamma… na sha guda hudu sai na ajiye sauran a cikin fridge” Yace “Baby hudu basuyi miki yawa ba?? bana so mura ta kama mun ke fa” Ta dan turo baki tace “Hamma hudu babu yawa fa” Yace “toh shikenan.. idan dai mura ta kama ki zan kira likita ya zo yayi miki allura” Da sauri tace “me kace Hamma? don Allah kayi haquri.. daga yau daya zan dinga sha” Dariya kawai yayi. Fahad ne ya shigo ofis din riqe da files yayinda ya ganta tsaye tana yi mishi massage. Murmushi yayi tare da girgiza kai yace “gaskiya abokina baka da matsala… wato har precaution ake dauka don kar ciwon kai ya tashi ko?” MK dai dariya kawai yayi, ya sani sarai abokin nashi akwai shi da zolaya. Ummi wadda take tsaye a bayan MK ne ta duqo kanta saitin fuskarshi tace “Hamma ai duk laifin shi ne ko?? ya san kan ka yana yawan ciwo kuma sai ya dinga baka aiki dayawa kana yi.. wallahi da na iya da na dinga yi maka duka aikin” MK da Fahad dai fashewa suka yi da dariya yayinda MK yace “kar ki damu zan koya miki sai ki dinga taya ni” Fahad kuwa yace “yanzu dai kiyi haquri Hamma yayi signing wannan..” ya tura files din gaban MK yayinda ya cigaba da fadin “….daga nan kuma mun bar miki shi” A haka dai MK yayi signing documents din sannan suka yi ma Fahad sallama suka tafi. ♧♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a falon Mamy harda Abba suna hira. Yawanci dai hirar bikin Hafsah suke yi Wanda yake ta matsowa. MK ne yayi sallama falon yayinda suka shigo tare. Ummi wadda take biye da shi sossai jikinta yake rawa yayinda zuciyarta take ta bugawa. Muryar Hafsah suka ji tace “Ga Yaaya da amaryar shi..” yayinda ta miqe ta qarasa wurin Ummi ta riqo ta tana fadin “oh my God Ya MK.. wai wannan ce wadda na gani a gida last time??” MK yana murmushi ya qarasa wurin Abba ya dan russuna tare da miqa mishi hannu sukayi musabaha. Ummi wadda suka qaraso tare da Hafsah ce ta duqa har qasa ta gaida su Abba yayinda suka amsa cikin fara’a. Mamy da Abba dai bayan sun ji abinda Maleeka tayi basu ji dadi ba amma kuma hakan bai zama reason da zai sa MK ya qara aure ba tare da ya sanar da su ba don haka suka tsaya akan bakan su na lallai sai ya saki Ummi… Da qyar Daddy ya fahimtar da su halin da MK din ya tsinci kanshi a game da yarinyar yayinda ya lallashe su akan su amince tunda dai haka Allah ya tsara. Babu yadda zasuyi dole suka amince da auren yayinda MK ya dinga yi musu godiya tare da qara basu haquri akan laifin da yayi musu. Mamy ce tace “zo nan ki zauna kusa da ni Ummi” Jiki a sanyaye ta qarasa wurin Mamy zata zauna a qasa amma Mamy ta riqo ta tare da zaunar da ita gefenta tace “Masha Allah… ya gida?” STORY CONTINUES BELOW Cikin ‘yar qaramar muryar ta tace “Lafiya lau Mamy” Hafsah wadda take kallon Ummi tace “hmm.. Ya MK duk ka tara kyawawan mata a gidan ka.. gasu farare sannan kai kuma baqi” Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Mamy tace “a’a wallahi.. yarona ba baqi bane. matan nashi ne dai hasken su yayi yawa..” MK yana dariya yace “nagode Mamy na” yayinda yayi ma Hafsah gwalo yace “ko banza kuma na fi wata haske..” Hafsah ta turo baki yayinda suke ta yi mata dariya. Ita dai Ummi tana nan zaune kusa da Mamy yayinda ta kasa yin motsin kirki.. gaba daya ma ji take yi kamar ta bace daga falon domin kuwa wani irin nauyin su take ji. Wani ikon Allah kuma su Mamy suna ganin Ummi suka ji ta kwanta musu a rai.. musamman Mamy wadda a yanzu take sa ran ganin jika daga wurin Ummin tunda Maleeka bata son haihuwa. Abba ne yace “Ubangiji Allah ya sanya albarka a auren ku..” Gaba daya suka amsa da ‘ameen’ Ya kalli MK yace “sai ka kula da ita sossai saboda a yanzu batada kowa idan ba kai ba.. always remember that she is an orphan and..” Wayar shi ce tayi ringing yayinda yace “excuse me.. we will continue this later..” ya miqe yayinda yayi answering call din yana magana ya bar falon. Hafsah ce ta girgiza kai tana dariya yayinda tace “mun shiga uku da business calls din Abba… yanzu ya sa pause kenan?” MK da Mamy suna ta dariya yayinda Mamy tace “ai ina mamakin yadda yake samun strength din da yake dealing da business dinnan nashi haka” Ita dai Ummi tana ta sauraron su amma fa ba komai da suke fadi take ji ba tunda dai suna hadawa da turanci. Wayar intercom ce tayi ringing yayinda Hafsah tayi picking. Daga kicin ne inda chefs ke tambayan abinda za’a dafa. Hafsah ce tace “hold on please” yayinda ta kalli Mamy tace “Mamy me za’a dafa wai??” Mamy tace “tunda Abban ku yana nan ai nasan zai fi buqatar tuwo” ta kalli MK tace “ga wani maciyin tuwon an qaro ma… in yaso sai su dafa any other continental..” Bayan Hafsah ta fadi musu ta kashe wayar ne Ummi ta dan yi gyaran murya yace “Mamy in je in taimaka musu??” Mamy tana murmushi tace “Haba dai Ummi, daga zuwa kuma sai ki hau aiki?? qyale su..” Ummi tace “don Allah Mamy..” MK ne yace “Mamy please allow her.. she likes cooking” Mamy tana murmushi tace “toh shikenan..” ta kalli Hafsah tace “Hafsah kai ta kicin din” Tare suka miqe yayinda suka tafi kicin din. MK kuwa tunda ta tashi ya sa mata idanuwa har ta bace. Mamy kuwa tana ta kallon shi tana murmushi.1 Bai ankara ba ya ji Mamy tace “you love her alot.. dont you??” Yana murmushi yace “wallahi I do Mamy.. I honestly never thought I’d fall for another girl aside Maleeka..” Tana murmushi tace “ai rayuwa haka take kasancewa.. Allah dai ya baku zaman lafiya” Yace “Ameen” ************ Ummi dai ko da ta shiga kicin sossai ta zage ta tuqa tuwo lafiyayye da miyan kuka. Ta hada farfesun kaza sannan ta bar ma Chefs din su jera a dinning. Ko da ta dawo falo ta tarar MK ya tafi masallaci tare da Abba. Umma ma ta tafi dakinta don yin sallah. Hafsah ce kawai a falon.. ganin Ummi ne ta miqe tare da fadin “matar yaaya mu je kiyi sallah” Haka ta janye Ummi zuwa sashen ta. ita Hafsah dayake tana fashin sallah sai tayi kwanciyarta a kan gado tana ta chatting a waya har Ummi ta idar. ************ Zaune suke a dinning gaba dayan su harda Abba yayinda Hafsah da Ummi suka yi serving abincin. Ummi dai ita ta zuba ma Abba da MK Tuwo yayinda ta zuba ma kanta dan kadan itama. Hafsah kuma ta zuba ma Mamy white rice da liver sauce yayinda ta zuba ma kanta. Ko da suka zauna gani nayi Ummi ta kalli MK wanda shima yake kallonta. Gani nayi ya kai bakin shi saitin kunnen ta yayinda yace “kar ki damu zan ci da kaina..” Murmushi tayi yayinda su Mamy ma suka kalli juna suna murmushi. Abba wanda ya kai lomar tuwo bakin shi ne yayi saurin dago kai yace “wa ya tuqa tuwon nan???” Zuciyar Ummi ce ta buga yayinda hankalinta ya tashi.. bata san lokacin da ta miqe tsaye ba cike da tsananin damuwa.. jikinta har rawa yake yi. Muryar ta tana rawa tace “Abba ni ce.. don Allah kayi haquri..” Abba wanda yake mamaki sai gani nayi ya girgiza kai yana murmushi yayinda yace “toh ai ni ban taba cin tuwo mai dadin wannan ba..”3 Zaro idanuwa tayi yayinda su MK suka fashe da dariya. Mamy ce tace “aah… lallai kuwa sirikar mu tayi qoqari tunda Abba ya yaba.. ” MK ne ya riqo hannun Ummi yana murmushi ya zaunar da ita yayinda su Hafsah suke ta dariya. Ji sukayi Abba yace “Allah yayi miki albarka Ummi..” Gaba dayan su suka amsa da ‘ameen’ yayinda Ummi ta cika da farin ciki. Haka dai suka cigaba da cin abincin yayinda Abba yake jin dadin abincin. Su Mamy ma sun kula da yadda ya ci tuwon dayawa, abin mamaki har qarawa yayi… hakan ya tabbatar musu da lallai tuwon yayi mishi dadi. Bayan sun kammala cin abinci ne Abba ya kalli MK yace “Ka tabbatar ka riqe yarinyar nan cikin amana.. ka ga yanzu you have added responsibility. Auren mata biyu kake yi a yanzu don haka ka zama mai kamanta adalci a tsakanin su, kayi qoqari wurin hada kawunan su.. kar ka fifita daya akan dayar..” MK yace “insha Allah Abba, I will try my best” Abba yace “I trust you will.. yau zaka dauko Maleeka ko??” Zuciyar Ummi ce ta buga yayinda hankalinta yayi mugun tashi. Nan da nan jikinta ya fara rawa… Ji tayi MK yace “yes Abba, idan mun bar nan gidan zamu je mu dauko ta….” Ummi dai saboda tsananin tashin hankali da fargaba da take ciki haka suka cigaba da magana amma sam bata jin abinda suke fadi..1 Lallai tunda Maleeka zata dawo qarshen ta ya zo kenan… she thought!!7 ♧♧♧♧♧♧♧♧ Toooooh Ummi tayi winning hearts din sirikan ta already!! Great abi???4 Hankalin ta kuma ya tashi a dalilin jin cewar Maleeka (her worst fear) is coming back!!7 Shin idan ta dawo ya zaman zai kasance?? MK, Ummi and Maleeka under thesame roof… shin kuna hango abinda nake hangowa kuwa??14