UMMI CHAPTER 2
MANDARIN ORIENTAL HONG KONG – CHINA+ A yau satin su daya a Hong Kong. Kwance yake a kan Sofa a suite din da suka sauka yayinda yake ta hira da ita a waya. Wayar dai ajiye take a gefen shi yayinda ya sa ta a handsfree. Fahad yana zaune a kusa da shi yana wani aiki a laptop dinshi yayinda yake sauraron hirar tasu. Ji yayi Maleeka tana fadin “…wallahi Honey sai ka ga yadda mutane suka so designs dina. do you know that I have sold 85% of my new collection??” MK wanda idanuwan shi suke a rufe muryar shi qasa-qasa yace “haba?? it’s great news and I am so proud of you” Tace “thanks my love, yanzu ma akwai change of plan.. dole sai na je America because I have to go do some re-stockings idan har ina so in zuba kayan a boutique dina” Ji tayi yace “zan tura miki kudi sai ki qara..” Cike da murna tace “yeeeeey… thank you so much Honey. I think zanyi doubling production din kawai…” Haka dai Maleeka ta cika MK da labarin business dinta har tsawon awa daya da minti talatin biyar. Shi kam haka nan ya cigaba da sauraronta yayinda yake responding where and when necessary.6 Bayan sunyi sallama ne na ji ya saki numfashi yayinda ya dafa kanshi. Fahad wanda yake kallon shi ne yace “MK like seriously??…” MK dai shiru yayi yana sauraron abokin nashi, ya sani sarai criticizing din Maleeka zai yi. Fahad ya cigaba da fadin “….Yanzu fisabilillah tunda kuka fara wayar nan ban ji ta tambaye ka jikin ka ba.. kana nufin bata san kana fama da ciwon kai ba tun jiya??” Shi dai MK ya sani sarai Fahad is right. kuma dagaske ta sani cewar yana fama da ciwon kai.. from all indication ta manta kenan… but why??6 Tunda yake da Maleeka bata taba tambayar shi ya yake ba ko ya aikin shi da sauran su… all she cares about is herself and things that are happening in her life. Lokutta da dama hakan na damun shi- yadda bata damuwa da al’amuran shi.. abinda ya sani shine Maleeka is just a young girl that is overwhelmed by abubuwan da suke faruwa a rayuwarta. Business dinta irin wanda ke buqatar 100% attention dinta ne… don haka ne yayi mata uzuri.3 really?? MK dai ji yayi Fahad ya cigaba da fadin “Gaskiya MK I have to tell you the truth.. Maleeka bata damu da kai ba. she is your cousin sister fa, ko da babu soyayya a tsakanin ku ai yakamata ta damu da wellbeing dinka.. trust me you deserve someone better”3 MK wanda idanuwan shi suke a rufe ne yace “abokina the most important thing is I love her kuma itama tana sona…” Fahad yayi murmushi yace “kana nufin zafin kishin da take nunawa akanka?? the way she slaps and hit girls yadda ta ga dama don kawai ta gan su a kusa da kai?? Allah sarki poor Nayla… I heard ta mare ta on the day we left Nigeria…” MK yace “it was just a misunderstanding kuma tayi realizing mistake dinta…” Ya tashi zaune dafe da kanshi yace “abokina nasan cewar baka son Maleeka but I beg you kayi qoqari ka ga good side dinta.. dagaske she is a nice garl” Fahad ya rufe laptop dinshi yace “Ni kam addu’a zan taya ka da shi akan Allah ya hada ka da soulmate dinka.. someone that will love you unconditionally, wadda zata damu da kai fiye da kanta..”6 STORY CONTINUES BELOW MK yayi murmushi yace “Nope abokina, bazan auri more than one woman ba kuma Maleeka is surely the one and only”1 Fahad yace “toh abokina, dukda dai ba alqawari ka dauka ba..” Murmushi yayi yace “but I give you my word” Fahad ya girgiza kai yace “I rest my case… Ya kan naka?? ya sassauta??” Yace “yeah, Alhamdulillah.. Insha Allah zuwa gobe idan na qara warwarewa sai mu koma Nigeria next tomorrow” Fahad ya miqe tare da fadin “Okay.. let me get you your Cappuccino.. amma please idan ka sha just retire to bed ka manta da kallon Smackdown dinnan da kake fadin kana so ka kalla… remember you should stay away from excessive light and sound har sai kanka yayi subsiding completely.. you need to rest MK”1 MK wanda ya koma ya kwanta kan Sofa yana murmushi ne yace “Yes sir” ♧♧♧♧♧♧ BAYAN SATI UKU ALIYU SODANGI RESIDENCE Zaune suke a dinning din gidan harda MK suna Dinner. Abinci ne kala-kala wadanda chefs din gidan suka shirya. Maleeka dai tana nan maqale a gefen MK tana ta buga mishi shagwaba.. Abincin ma shine ya zuba mata wanda take so. Maleeka dai kwanan su biyu da dawowa daga trip dinsu. tunda ta dawo MK yana Lagos don haka ne yana dawowa yau ya zo gidan don ganinta. Daddy ne ya kalli MK yace “Yaushe ne zaka je Germany din?” Yace “Daddy sai Sunday insha Allah… appointment dina da likita is on monday” Maleeka ce tayi saurin fadin “honey Migraine dinka ya tashi ne??” Murmushi yayi yace “yes babe… I was down before I travelled to lagos..” Cike da mamaki tace “shine kullum sai munyi waya amma baka fadi mun ba??” Yace “Yi haquri Babe… bana so hankalin ki ya tashi ne” Mummy ce ta harari Maleeka tace “does he have to tell you?? Ai da jin muryar shi a lokacin yakamata ki gane… ke kam ban san lokacin da zaki natsu ki dinga aiki da qwalwar ki ba” Turo baki tayi yayinda MK da Daddy suka yi murmushi. Suna gab da qarasa cin abincin su ne Maleeka tace “Honey kar ka manta gobe zamu je muyi pre-wedding pictures din” Yace “okay babe..” Daddy da Mummy dai suna ta sauraron su. Tace “zan turo maka da list na colors din kayan da zaka sa” Yace “okay.. you should do just that” Shi kam MK don dai kawai tayi insisting ne amma baya son irin wadannan abubuwan. Haka dai suka kammala dinner sannan suka koma falon Daddy suka dan taba hira. *********** Tsaye yake a jikin motar shi yana latsa wayar shi yayinda yake jiran ta. Maleeka dai ta tsaya kwaso mishi tsarabar shi ne. Yana nan tsaye ya hangosu sun fito. Tafe take sanye cikin dogon hijabi riqe da shopping bags dayawa yayinda kanta yake a duqe. Da ganin yadda ta riqo kayan ka san sunyi mata nauyi. Maleeka ce biye da ita. MK wanda ya kafa mata idanuwa kuwa haka kawai ya ji tausayinta. He instantly felt the urge to help her. Gani nayi ya qaraso wurinta yayinda ya miqa hannu zai karbi kayan. A wannan lokacin da ya matso daf da ita kuwa sai da zuciyar shi ta buga, ji yayi kamar he found something he has lost a long time ago…5 STORY CONTINUES BELOW why??3 Ko da ya sa hannu ya karbi kayan hannuwan su ne suka taba juna yayinda tayi saurin sakin kayan wanda kuwa duk suka watse a qasa. A dai-dai wannan lokacin ne Maleeka ta qaraso wurin su yayinda ta dauke ta da wani irin mugun marin da har sai da ta duqe qasa ta fashe da kuka. Gani nayi MK ya runtse idanuwan shi yayinda hankalin shi yayi mugun tashi. A yadda yayi freezing zaka rantse shi ne aka mara. Kukan yarinyar kuwa sai dukan qwalwar shi yake yi yayinda zuciyar shi take ta zafi tana tafasa. why??3 Ji yayi Maleeka tana fadin “Dan ubanki kin San nawa wadannan kayan da zaki zubar??” Cikin kuka ya jiyo ‘yar qaramar muryar ta mai dadin gaske tana fadin “Adda don Allah kiyi haquri…” Maleeka cikin masifa tace “just shut up… stupid girl” MK Wanda gaba daya hankalin shi yake a tashe ne ya kalli Maleeka da sauri yace “Babe it’s okay.. she has apologised so please let it be… after all laifi na ne..” Tuni yarinyar ta fara tattara kayan da suka zube yayinda MK yayi sauri ya duqa yana fadin “hey.. leave it..” Ita dai yarinyar bata san abinda yace ba don haka ta cigaba da kwashewa yayinda suka ji Maleeka tana fadin “haba Honey, ka qyaleta ta kwashe mana… ba ‘yar aiki bace??”1 Yarinyar wadda har a lokacin take kuka ce ta dago kai ta dan kalli MK. Gani nayi daga shi har ita sunyi freezing yayinda suke kallon juna. wani yanayi suka shiga na daban.4 Yarinyar ce tayi saurin ankara yayinda ta duqar da kanta. MK kuwa sa mata idanuwa yayi babu ko qyaftawa. Muryarta tana rawa tace “don Allah Hamma ka bari in kwashe..” Shi kam gaba daya tunanin shi yayi mugun nisa. Abinda ya ji game da yarinyar kuwa bai taba jin shi ba a rayuwar shi… why??5 Da ya ankara ne yace “bar shi kawai… tashi ki koma cikin gida” Ita kanta yarinyar gani nayi jikinta yayi mugun sanyi. Da sauri ta tashi ta wuce yayinda Maleeka ta bi ta da harara tana ta masifa. MK dai yana ta tattara kayan yayinda Maleeka take ta masifa.. shi kam gaba daya ma hankalin shi baya tare da ita. Bude mota yayi ya zuba bags din a ciki sannan ya juyo ya kalle ta yace “Babe don Allah nace kiyi haquri” Turo baki tayi tace “but honey…” Yace “please Babe… do me a favor” Tace “what?” Yace “don Allah kar kiyi ma yarinyar nan komai.. tunda ta baki haquri just forget about it” Ita kam Maleeka ta so idan ta koma sai ta ci qaniyar yarinyar dukda kuwa she is her best employee a gidan. Ji tayi MK yace “promise me you wont scold her..” Shiru ta dan yi sannan tace “I promise you” Murmushi yayi sannan yace “nagode Babe” ♧♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD KABIR SODANGI RESIDENCE MAITAMA, ABUJA Zaune yake a falon shi yana kallon NXT a TV. A zahiri dai kallo yake yi amma a badini hankalin shi gaba daya baya tare da shi. MK dai kusan awa daya da rabi kenan da ya dawo daga gidan su Maleeka. Gaba daya ya shiga damuwa a dalilin yarinyar nan. Marin da Maleeka tayi mata ne ya tuno yayinda yayi saurin runtse idanuwan shi. Sossai zuciyar shi take zafi. Gani nayi ya kashe TV din ya wuce dakin shi yayinda yake addu’a Allah yasa kar Maleeka tayi ma yarinyar wani abu. Ko da MK yayi shirin bacci ya hau gadon shi kasa runtsawa yayi.. da ya rufe ido sai ya ga kyakyawar fuskar yarinyar a lokacin da take kuka. Gani nayi ya tashi zaune yayinda ya dafe kai. Ji nayi yace “MK what’s wrong with you??” Wayar shi ya janyo yayi dialing number din Maleeka. A kira na biyu ne ta amsa cikin muryar bacci. Ji nayi tace “Honey ya akayi ne??” Shiru ya dan yi sannan yace “lafiya lau babe, bana jin bacci ne shine nace bari in kira ki don in ji muryar ki.. but kamar kin fara bacci ko??” Cike da jin dadin kalaman shi tace “yeah na fara amma kuma ya tafi da na ji muryar ka” Murmushi yayi sannan yace “thanks Babe..” Ji yayi tace “ka duba kayan nan?? kana son su??” Shi kam gaba daya ya ma manta bai duba kayan ba. Hankalin shi baya tare da shi at all. Gyaran murya yayi yace “na duba babes.. I love them but most importantly I love you so much and thank you very much” Murmushi tayi tace “I am glad you liked it… I swear na qagara a daura mana aure in dawo wurinka..” Dariya yayi sannan yace “can’t wait to have you my dear, bala’in sonki nake yi… Uhm, ban tambaye ki ba… yarinyar nan hope dai baki yi scolding dinta ba ko??” Maleeka tayi dariya sannan tace “wallahi I didn’t Honey, ba kace in qyaleta ba??? toh I did just that” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “thank you my babe” Ji yayi tace “ni kam ban san meyasa kake daukar mutanen da ba kowa ba da muhimmanci… the girl for example, she is just a maid fa” Da sauri yace “remember what I told you… in Quran 2 verse 213…” Da sauri tace “yeah yeah… And mankind is naught but a single nation” Murmushi yayi yayinda yace “Good girl.. I am glad you are learning.. Allah ya kai mu ki haifo mun yara kyawawa masu kama da ke” Da sauri tace “Honey ka fara ko?? Ni fa na fadi maka bazan haihu anytime soon ba kuma ma ni na fi so mu yi rayuwar mu daga ni sai kai”3 MK dai ba tun yau ba yake jin wannan maganar daga bakin Maleeka. Asali bata son yara kuma ta sha fadi mishi bazata haihu da wuri ba. Shi kuma wani ikon Allah a duniyan nan baya da burin da ya wuce ya ga dan da Maleeka zata haifa mishi. One thing is ya sani cewa idan ta zo zai canza mata ra’ayi tunda dai he has always succeeded in making her do whatever he wants. Hakan yana tabbatar mishi da lallai Maleeka tana son shi. Ji nayi yace “Babe we will discuss this idan kin zo kin ji??” Shiru ta dan yi sannan cikin shagwaba tace “toh Honey”ALIYU SODANGI RESIDENCE+ Wuraren qarfe biyu na dare tana zaune a bisa katifar da ta kasance ta dakin su a matsayin su na ma’aikata. Kuka take ta yi babu sassautawa. Ummi dai ta kasa bacci a yau. Da ta kwanta ta rufe idanuwan ta sai ta dinga ganin fuskar shi. Sossai take jin shi a ranta.. ji take yi kamar ta gano wani abinda ta rasa a rayuwarta tun da dadewa.4 Inno wadda suke zama dakin tare ce ta ji sautin kukan ta a cikin bacci. Ko da ta bude idanuwa ganinta tayi zaune ta kifa kanta bisa gwiwarta. Da sauri Inno ta tashi zaune yayinda ta janyo ta tace “Ummi lafiya kike ta kuka??? ba dai akan marin da Hajiya qarama tayi miki bane??” Girgiza kai tayi alamar ba wannan bane. Cikin kuka tace “Dada ni fa wallahi ba laifi na bane. Kin ga shine ya taba ni kuma sai na ji kamar wuta ta ja ni… Dada na shiga uku.. ya hana ni bacci”1 Ta qara fashewa da kuka tace “ni bana so ina ganin shi a bacci na… zuciyata tana yi mun wani iri.. don Allah ki taimaka mun…” Inno wadda duk ta bi ta rude tana shafa kanta tace “ki daina kuka Ummi.. na tabbatar saboda kin sa abin a ranki ne shiyasa kika damu.. itama hajiya qarama kiyi qoqari ki qara bata haquri gobe kin ji” Ummi tana share hawayen ta tace “toh Dada.. nagode” Inno tayi murmushi tace “babu komai Ummi, ni na dauke ki a matsayin ‘ya wadda na haifa da ciki na. Tunda kika zo gidan nan na kula da lallai kina da hankali da natsuwa. Ki cigaba da haquri Ummi, ni ina ji a jiki na cewar rayuwar ki zata yi haske nan gaba, Allah bazai barki haka ba Bi’iznillahi ta’aalaa” Ummi tace “gettaɗɗo Dada” Inno ta harare ta tace “kin fara fulatancin naki kenan ko?? ni kam ban san abinda kika ce ba..”2 Murmushi Ummi tayi sannan tace “Haba Dada… sau nawa zan koya miki wannan?? kawai fa ina nufin nagode ne” A haka dai Inno ta lallaba ta suka koma bacci dukda dai ita Ummi bata koma ba domin kuwa ta kasa. Fuskar MK kawai ke dawo mata da zarar ta rufe idanuwa… Why??4 ♧♧♧♧♧♧♧ Washegari wuraren qarfe goma sha daya na safe tana kwance a kan makeken gadon dakinta yayinda Jameela take zaune a gefen ta. Jameela ce tace “yanzu jibi Layla Hayat din zata iso??” Maleeka tace “yes Jay, Mummy tace jiya sunyi waya da ita tace jibi zata baro Egypt” Jameela tace “gaskiya matar ta iya aiki, na tabbatar she will do wonders on you..” Maleeka ta turo baki tace “ni duk ba wannan ba Jay, takura ni da za’a yi ne bana so. Mummy fa tace idan aka fara gyaran jikin nan bazan qara fita ba… ai wannan punishment ne”2 Jameela ta Harare ta tace “meye punishment anan?? hutawa fa zakiyi Leek besides bikin ki ya matso so you need to reduce all these your to and fro movements” Maleeka ta turo baki tace “wallahi Jay don dai bani da anything to take care of a fanin business dina but I swear har ranar auren zan iya tafiya..” Kafin ta qarasa maganar kuwa Jameela tace “what?? is your business more important than your wedding da kike fadin haka?? duk shirin da kika yi??” Maleeka tace “No Jay, My wedding is more important but the business is equally important.. aure na da Honey can take place even if we are not present amma kuma business dina can’t survive without me..”8 STORY CONTINUES BELOW Jameela wadda take cike da mamaki tace “a taqaice dai kina qoqarin gwada mun business dinki ya fi Ya MK kenan…” Maleeka tace “no qawata.. bazaki gane…” Kafin ta qarasa maganar ne suka ji sallamarta. Jameela ce ta amsa sallamar yayinda ta shigo riqe da tray na kayan motsa baki. Har qasa ta duqa ta gaishe da Jameela sannan ta ajiye tray din. Kallon Maleeka tayi cike da girmamawa tace “Adda don Allah kiyi haquri akan abinda ya faru jiya… Insha Allah bazan qara ba” Jameela ce take kallon ta cike da confusion yayinda take sauraron abinda Maleeka zata ce. Maleeka wadda take latsa wayarta ce tace “Na ji.. na haqura. Tashi ki tafi” Ummi tace “nagode Adda” sannan ta tashi ta tafi. Bayan Ummi ta bar dakin ne Jameela wadda take kallon Maleeka tace “hey me tayi miki ne??” Maleeka ta ba qawarta labarin abinda Ummi tayi jiya. Jameela tace “Ayya baiwar Allah… Ni kam ina son yarinyar wallahi. She is beautiful and cool sannan I like her fulani accent. abinda yake qara birge ni kuma yadda kullum zaki ganta tsab tsab dukda ‘yar aiki ce…” Maleeka wadda take ta latsa wayar ta tace “it’s the reason why she is my Fav…” Jameela tace “shin yau ne zaku je yin pre-wedding pix dinku ko??” Tana murmushi tace “yes Jay.. bari ma in tura mishi kalolin kayan da zai sa don wallahi idan banyi haka ba yana iya kwafsa mun.. na riga na san halin abina” Jameela ta dinga yi mata dariya. ♧♧♧♧♧♧♧♧ Bayan kwana uku… MK-TECH SOFTWARE COMPANY Zaune yake a ofis din Fahad yayinda suke wani aiki. Tunda suka fara aikin kuwa Fahad ya kula hankalin abokin nashi baya tare da shi. Gani nayi Fahad ya ture laptop din da take gaban su yayinda ya kalli abokin nashi yace “MK what’s wrong?? Na ga kwana biyu duk ka dan canza.. you seem lost all the time these days… Maleeka ce??” Girgiza kai yayi yace “it’s not her abokina” Fahad yace “then tell me already..” Ya miqe tare da komawa kusa da window yana kallon waje yayinda yace “abokina there is this girl…” Kafin ya qarasa maganar shi kuwa Fahad ya miqe cike da mamaki yace “whaaat?? a girl??” MK ya juyo ya kalle shi tare da fadin “hey it’s not what you are thinking…” Fahad yace “then tell me because as far as I know you MK maganar mace daya kawai kake yi.. Maleeka. idan har ka ambaci wata wadda ba ita ba toh akwai bayani kenan…” Komawa yayi kan kujera ya zauna yana kallon abokin nashi sannan ya bashi labarin abinda ya faru five days ago.. Ji nayi yace “I swear abokina when she slapped her I really felt it.. I felt our souls connected on a level so deep that it is completely unexplainable. I kinda feel it’s my responsibility to protect the girl a rayuwar nan but I dont know how… like am I even making sense?? ban san yarinyar ba, ban taba ganinta ba sai ranar… what is my connection with her?? meyasa nake ji kamar she belongs nowhere but close to me?…”2 Fahad dai shiru yayi yana kallon abokin shi cike da tsananin mamaki. MK wanda yake ta jiran abokin nashi yayi magana ne yace “guy say something mana..” STORY CONTINUES BELOW Fahad yayi murmushi yace “me kake so in ce?? kace qaramar yarinya ce kuma mai aiki.. if it were vice versa da nace qila soyayya ce..” Da sauri MK ya miqe yace “what the hell abokina… I have one and only true love in this life- Maleeka”3 Fahad yace “idan haka ne toh why is this girl stuck in your head?? why do you feel she belongs nowhere but close to you??” MK ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu yace “I dont know… abinda nake so in gane kenan” Fahad ya janyo shi ya zauna yayinda yace “abokina ka manta da yarinyar.. ka ga fa dama idan aure ya matso shaidan yakan shiga zuqatan mu ya birkita mana tunani..” MK ya girgiza kai yace “bazaka gane bane.. wannan yarinyar jin ta nake yi kamar she is a part of me.. ko bacci na kwanta sai in dinga ganin scene din.. her voice echoes in my mind peacefully… I just feel mentally inseparable with the girl” Fahad yayi murmushi yace “toh ni dai nasan you wont believe me but gaskiya irin wannan feeling din akan wani is simply the type you feel for a soulmate sannan ina mai tabbatar maka cewar idan har haka ne toh lallai yadda kake ji itama yarinyar haka take ji” MK wanda ya zama so confused ne yace “No my friend… Maleeka is my one and only soulmate. ban taba son wata mace ba a rayuwa ta banda ita..” Fahad ya girgiza kai yace “shiyasa nace maka just forget about the girl and focus.. You are getting married to the love of your life, your Cousin Maleeka and that is all that matters right now” Shi kam Fahad is extremely happy da jin wannan zancen domin kuwa shi dama baya son Maleeka.. Addu’a yake yi Allah yasa somehow qaddara ta hada abokin nashi da mai aikin.. idan ma auren ta zaiyi ya aure ta ya hada su biyu.10 Ni kuwa nace Fahad mugu…5 Wayar MK ce tayi ringing. ko da ya duba sunan Maleeka ya gani. Gani nayi yayi murmushi sannan yayi answering yace “amaryar MK how are you??” tace “fine angon Leek” Cike da jin dadin maganarta yace “ya hidima?? how is everything going?? hope dai ba kya stressing kanki??” Cikin shagwaba tace “not really my love.. anjima zaka zo??” Yace “idan kin ce in zo zan zo babe… remember your every wish is my command” Tana murmushi tace “toh don Allah ka zo… I want to see you before you travel to Germany gobe..” Kai tsaye yace “an gama my Babe… zan zo anjima insha Allah” A haka suka cigaba da hirar soyayyar su kamar kullum yayinda Fahad ya miqe ya bashi wuri domin kuwa a yadda suka dauko hira sai su shafe awa biyu basu sani ba. ♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE Zaune suke a falo suna ta hira kamar kullum idan ya zo gidan. MK Wanda ya sa mata idanuwa ne yace “Babe kin ga yadda kika qara kyau kuwa?? tell me.. what’s the secret??” Tana murmushi tace “Honey this is the work of Layla Hayat.. kasan gyaran jikin da nace maka an fara yi mun?? result din ne ya fara bayyana” Kafin yayi magana ne suka ji sallamar Inno wadda ta qaraso ta ajiye kayan motsa baki sannan ta gaishe shi. A bangaren MK dai yayi zaton zai ga yarinyar amma kuma kash.. sai ya ga sabanin hakan.1 Har Inno ta bar wurin bai sani ba domin kuwa yayi nisa a tunani.. Maleeka ce ta dan taba shi sannan tace “Honey lafiya?? na ga maid din tana ta gaishe ka but you didn’t answer..” STORY CONTINUES BELOW Shafa kanshi yayi yace “wallahi babe my mind wasn’t even here..” Ya dan juya yayinda ya hango Inno tana fita daga falon. Ji nayi yace “ayya she left already??” Maleeka tayi murmushi sannan tace “yes honey..” Wayarta ta janyo tace “hey our fotos are ready” ta matsa daf da shi yayinda ta fara nuna mishi hotunan wadanda suka yi bala’in kyau. MK wanda yake kallon hotunan yace “wow.. babe this is beautiful. it wasn’t a bad idea afterall” Tana murmushi tace “ai na fadi maka George Okoro issa great guy honey… dama fa nace mishi sai munyi vetting sannan zan bashi greenlight na yayi posting a social media”6 MK ya dan bata rai sannan yace “wai dama baza mu za’a yi a ana kallon mu??” Fashewa tayi da dariya tace “toh da me kake tunani?? kawai munyi ne for just ourselves?? No honey.. ai wadannan pictures din sai sun zagaye duniya Insha Allah.. I really want everything about our wedding to be grand..” Shafa kai yayi yayinda yace “MK is so in trouble..” Maleeka dai tana dariya tace “Honey haka fa ake yi” ta dan Harare shi tare da fadin “kai dama fa Baqauye ne dagaske” Dariya ma ta bashi. A haka dai suka cigaba da kwasar hirar su yayinda ta tura mishi hotunan a wayar shi. *********** MK dai bai bar gidan ba sai da yayi sallama da su Daddy dayake flight dinshi zuwa Germany washegari da sassafe ne. A lokacin da Maleeka ta rako shi wurin motar shi kuwa yana tsaye jikin motar yayinda take ta kallon shi. MK wanda shima kallonta yake yi yace “Babe na qagara in mallaki ki a matsayin mata, I really am dying to have you with me kullum..” Bai qarasa maganar shi bane ya ga ta matso kusa da shi sannan ta rungume shi. Yana shirin banbare ta daga jikin shi ne tace “please Honey.. allow me. I am going to miss you” MK dai kasa magana yayi yayinda duk ta bi ta kashe mishi jiki… shi bai rungume ta ba sannan for the first time ya kasa janyewa daga gareta. Kamar ance mishi ya daga kai sai ya hango ta tsaye a jikin window tana kallon su. Zuciyar shi ce ta buga yayinda ya sa mata idanuwa. Haka kawai ya ji bai kyauta ma yarinyar ba. why??8 Da sauri ya sa hannu ya banbare Maleeka daga jikin shi tare da tura ta baya yace “babe ba yanzu ba… saura kadan Insha Allah.” Murmushi tayi tace “cant wait Honey… I love you so much…” Yana murmushi yace “I will miss you alot” yayinda ya daga kai don ganin yarinyar amma kuma bai ganta ba. Gaba daya bai ji dadi ba… why???3 ************ Ummi ce kwance a kan katifar dakin su yayinda take ta kuka.2 Ita ta rasa dalilin da yasa take jin abinda take ji a game da wannan mutumin da yake zuwa wurin Maleeka.4 ●● Ummi ta sani sarai mutumin ya zo gidan wanda ko da aka sanar musu su kai mishi abin motsa baki qin zuwa tayi yayinda ta roqi Inno ta kai mishi. Ita dai bata son ganin shi saboda bata son abinda take ji game da shi.2 A lokacin da ta shiga dakin Maleeka don gyara mata kamar kullum ne tsautsayi ya kai ta wurin window yayinda ta hango lokacin da Maleeka tayi hugging dinshi. Ummi dai a wannan lokacin ji tayi kamar ta mutu wanda ta rasa dalili. Abinda ya qara tayar mata da hankali shine lokacin da ya dago kai ya hangota yayinda yayi saurin ture Maleeka.3 Matsawa tayi daga jikin window din yayinda ta cigaba da leqen shi. Tana ganin shi lokacin da yake ta dago kai yana kallon window din amma bai ganta ba. Har lokacin da Maleeka ta shiga cikin gida yana ta kallon window din. Sossai ta ga alamun damuwa a tattare da shi. shin shima yana jin abinda take ji ne a game da shi?? ●● Ummi tana ta kuka ne Inno ta shigo dakin. tsayawa tayi turus yayinda ta cika da mamaki. Da sauri ta qarasa wurinta ta janyo ta jikinta tare da rungume ta tace “ke ‘yan nan lafiya kuma kike kuka??? me akayi miki?” Cikin kuka Ummi tace “Dada ni gaskiya bazan zauna a gidan nan ba..”5 Da sauri Inno tace “meyasa kike fadin haka Ummi?? lafiya??” Kuka ta cigaba da rusawa yayinda ta bata labarin abinda ya faru. Ita dai Inno shiru tayi tana mamakin wannan al’amari. Ta rasa dalilin da ya sanya MK ya tsaya ma yarinyar a rai.. Inno dai ta kula ko da ta kai mishi kayan motsa baki kamar bai ji dadin ganinta ba.. kamar a ranshi ya so ace Ummi ce domin kuwa ta kula ko gaisuwarta ma bai amsa ba.2 Abinda ta sani shine idan ma soyayya ce bazata taba yiwuwa ba tunda dai Maleeka zai aura kuma ma ina shi ina ‘yar aiki sannan qaramar yarinya.. ai kowa ma ya san cewar hanyar jirgi daban sannan ta mota daban. Tana rungume da Ummi ne tace “kiyi haquri ki daina kuka kin ji… shi wannan mutumin da kika gani dan uwan Hajiya qarama ne kuma tuni an sa ranar bikin su wanda a yanzu haka saura ‘yan satuttuka kadan… idan anyi auren zaki daina ganin shi a gidan nan” Tana shafa kanta ta cigaba da fadin “banda abinki baki dade da zuwa gidan nan ba kuma sai ki ce zaki tafi?? Kiyi haquri ki manta da shi” ♧♧♧♧♧♧♧ Haaa… My people Me ke faruwa ne?? Weeks Later…+ ALIYU SODANGI RESIDENCE A kwana a tashi babu wuya.. Tuni an kai lefen Maleeka wanda dai ita ta hada kayan ta da kanta. Kaya ne na bala’i masu kyan gaske. Kusan zamu iya cewa ba’a ga kayan lefen masu yawa da tsada kamar wannan ba a garin Abuja da kewaye. Sossai Maleeka ta zama talk of the town (abinda take so). A lokacin da satin bikin su Maleeka ya shigo kuwa sossai gidan ya cika da mutane, sossai ake ta hidima iri-iri. Gaba daya garin Abuja labarin bikin su Maleeka ake yi. Maleeka dai ta shirya shagulgula da yawa, sati guda cir ta dauka wanda a kowacce rana akwai event din da za’a yi. Kudaden MK dai sunyi kuka domin kuwa sossai ta shirya events na gani na fada. ********** A yau ranar qunshi, gaba daya qawayenta suna gidan yayinda Amaryadotcom tare da team dinta suke ta zirara lalle. Maleeka tana zaune ana yi mata lalle ne wayar ta tayi ringing. Ganin sunan MK ne na ga tayi murmushi yayinda ta kalli Jameela wadda tuni nata lallen ya bushe tace “Jay please…” Jameela tana murmushi tace “No Leek… yayi haquri” Zaro idanuwa tayi tace “what?? Noo… don Allah ki bari” Jameela tana murmushi tayi answering yayinda ta sa mata a speakerphone. Muryar shi suka ji yana fadin “hey babe.. and how is the most beautiful girl in this whole wide world doing??” Tana murmushi tace “I am fine my love.. ina ka shiga ina ta kiran ka dazu and you didn’t pick??” Yace “sorry ina meeting ne..” Turo baki tayi kamar yana ganinta tace “I swear kai workaholic ne” Dariya yayi yace “yi haquri my babe… I need to clear some things ne before we go for our honeymoon.. kin san yakamata in baki full attention dina…” Qawayen ta ne suka fashe da dariya jin maganar da yayi. Ji suka yi yace “guess what??” Da sauri tace “tell me” Yace “I just completed our reservation na trip dinmu zuwa Gold Coast…” Cikin ihu da murna tace “whaaaaat??? dagaske Honey??? Oh my God.. I cant believe this.. thank you very much My Honey… Finally our honeymoon will be on point… wallahi har na cire rai fa” Yace “nima haka babe.. Can’t wait to have a beautiful experience with you in Australia” Muryar Qanwar shi Hafsah ya ji tace “Ya MK ina jin ka fa..” Gaba dayan su suka fashe da dariya. MK wanda shima dariya yake yi ne yace “Eavesdropping on our conversation ko Chubby??.. its bad” Jameela tana dariya tace “ba laifi ta bane.. kana speakerphone ne kuma amaryar taka an lullube hannunta da lalle” Ji suka yi yace “Whoa Jay…. toh a gaya ma mai lallen tayi ma amarya ta lalle mai kyau..” Jameela tace “aikuwa tana jin ka” Yace “great… Babe ki aiko mun da hoto idan an gama” Maleeka tana murmushi tace “I will my love” STORY CONTINUES BELOW A haka suka cigaba da hira wanda kuwa dukda ya san cewar speakerphone yake bai hana shi fadin kalaman soyayya zuwa ga amaryar tashi ba. Ita kuwa sai shagwaba take buga mishi cike da salon soyayya. Sossai qawayen Maleeka suka dinga yaba ma salon soyayyar su. Da daddare ne akayi Bridal Shower anan gidan su Maleeka wanda kuwa yayi kyau sossai. George Okoro dai shi ya dinga kashe hotuna yayinda Fati Mamza ta tsantsara ma amarya kwalliyarta. **************** Ana gobe daurin aure ne aka yi lafiyayyen kamu a Bluevelvet Marquee.. Amarya dai ta sha kyau. Dinkin da ta sanya kuwa Galiafahad na qasar Dubai ne ya dinka mata. Fati Mamza ce ta tsara mata kwalliya. komai was perfect and on point.1 MK dai akan dole Maleeka ta tilasta mishi zuwa wannan taro kamar yadda ta tilasata mishi zuwa sauran da akayi. Tare da abokanen shi suka zo wanda kuwa sossai suka yi kyau. Duk inda ka ga Maleeka zaka ga MK biye da ita.. they made the perfect couple. Iyayen su kuwa sossai suke cikin farin ciki. everything was grand just the way she had planned… ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE Maleeka dai tunda suka dawo daga bikin kamun Layla Hayat ta sanya ta a gaba tayi wanka cikin turarruka, ko da ta fito ta hada ta da mayyuka iri-iri wanda kuwa ta dinga zabga qamshi yayinda qawayenta suke ta yabawa. Sallah kawai tayi sannan ta haye gado a gajiye. Jameela wadda take kwance a gefenta tana ta kallon hotunan bikin da ake ta bazawa a social media ce tace “Babe I swear bikin ku yayi masifar kyau… ni kam ban taba ganin yawan mutane a biki har haka ba” Wata qawar Maleeka mai suna Husna ce tace “Na tabbatar dinner din gobe zai fi kowanne event din da akayi yawan mutane” Maleeka wadda take rungume da pillow tana sauraron qawayen nata ce tace “I am glad my wedding turned out to be the kind I always dreamt of my friends” Jameela tace “hoping you’d build a happy home filled with joy and laughter Leek”5 Tana murmushi tace “I will Jay” will she???🤨8 Sallamarta suka ji yayinda ta shigo dakin sanye cikin hijabi kamar kullum. Da ka kalli fuskarta kasan ba daidai take ba. Ahankali ta qaraso ta tsugunna har qasa ta gaishe su sannan tace “Adda dama Hajiya ce tace in kira ki.. wai ta neme ki a waya amma baya shiga” Maleeka dai ba tare da ta kalli Ummi ba tace “ki ce mata ina zuwa” Jameela wadda take kallon Ummi ce tace “ya na ga kinyi wani iri?? baki da lafiya ne??” Kai tsaye tace “kai na ne yake ciwo Adda” Su kam sauran qawayen Maleeka da suke dakin ko kallo Ummi bata ishe su ba balle su sa hankalin su akan maganar da take yi da Jameela. Asali ma hirar bikin suke ta yi. Jameela ce tace “Ayyah.. kin sha magani dai ko??” Ta kalli Maleeka tace “I am sure stress ne..” Maleeka wadda ta tashi zaune ta kalli Ummi sannan tace “je ki sha magani ki je ki kwanta” Ummi tace “toh Adda…” sannan ta miqe ta bar dakin. Jameela tana kallon Maleeka tace “I swear I like this girl.. meye sunan ta ne wai??” STORY CONTINUES BELOW Maleeka wadda ta sauka daga kan gadon ta harare ta sannan tace “Wallahi Jay ban san sunan ta ba… ko wata uku bata yi ba da zuwa gidan nan fa..” Jameela ta girgiza kai tare da fadin “hmmm.. Leek I swear bakiyi ba.. Yanzu ace kina da house help amma baki san sunan ta ba?? Na fa ga duk hidimar ki itace…” Maleeka ta daga mata hannu tare da fadin “toh wai dole ne sai na san sunan ta?? ni kam ta ma yi sa’a bana samun matsala da ita…” Ta gyara nighty din da ke jikinta sannan tace “bari in je in ji kiran Mummy.. ina zuwa” ************** ●● Ummi dai tunda aka shigo satin bikin Maleeka ta kasa samun sukuni. Gaba daya ji tayi kamar za’a raba ta da wani abu da ya kasance nata. Haka kawai sai ta ji zuciyarta tana bugawa yayinda jikinta yake bi yana matuqar sanyi. Wasa wasa dai har ciwon kai ya kama ta wanda take kwana da shi tana tashi da shi. Dukda kuwa ta sha magani amma sam babu sassauci. Ga hidimar biki wanda ya hana su zama. Don ma tayi sa’a Inno tana taimaka mata da ayyukan nata. Asali dai gidan Alhaji Sodangi Ma’aikata kala-kala ne. Masu dafa abincin (chefs) gidan daban, akwai masu aikin wajen gida sai Inno da Ummi wadanda suke aikin cikin gida. Daga baya ma Ummi ta zama personal maid din Maleeka wadda ta aminta da natsuwarta da kuma qwarewar ta a dukkanin aikin da aka sa ta. ●● ************** A yau ranar daurin aure, Ummi dai ta shiga tsananin damuwa fiye da kullum.. Gaba daya rayuwarta bata yi mata dadi. Da ka ganta kuwa ka san akwai matsala.1 Inno dai batayi mamakin ganin Ummi a haka ba domin kuwa ta kula tunda satin bikin ya gabato yarinyar ta birkice. Inno dai ta sani sarai abinda yake damun Yarinyar, ta sani sarai a dalilin auren da ake yi a gidan ne, ta sani sarai damuwarta akan MK ne.. Abinda ta kasa fahimta shine meye hadin ta da shi?? meyasa yarinyar ta damu da har ta shiga tsananin damuwa haka?? ita dai a saninta dama ance akwai zuqatan mutane a duniya da suke gamuwa da juna ko da kuwa basu tare… shin abinda yake faruwa a tsakanin Ummi da mijin Maleeka kenan??? interesting!!2 ♧♧♧♧♧♧♧♧ Bayan sallan Juma’a ne aka daura auren Muhammad Kabir Sodangi da amaryar shi Maleeka Aliyu Sodangi a central mosque akan sadaki naira dubu dari.5 Sossai masallaci ya cika da manyan baqi. Direct Sheraton Hotel aka tafi inda aka shirya wani classy reception. Garin Abuja a wannan ranar ya ga yawan jama’a kai kace bikin diyar shugaban qasa ake yi. Alhaji Muhammad Sodangi da dan uwan shi Alhaji Aliyu Sodangi mutane ne masu jama’a don haka ba abun mamaki bane ganin yawan mutanen da suka halarci wannan daurin aure. ♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE Tsaye take a gaban Vanity mirror na dakinta yayinda take magana da shi a waya. Qawayenta kuwa suna sashen visitors na gidan yayinda suke ta shirin su na Yinin bikin da za’ayi a nan harabar gidan. Maleeka dai tuni Fati Mamza ta gama mata make up dinta. A dalilin wayar da take yi ne tace ma Hudayya ta bata few minutes sannan ta zo ta taya ta sanya kayanta. Hudayya da team dinta suka yi zaman su a falon Maleeka suna jiranta. Jameela dai tana nan a dakin tana ta qoqarin kammala shiryawa. A lokacin Ummi tana cikin closet din dakin yayinda take hada ma Maleeka wasu daga cikin kayanta kamar yadda ta umurce ta. Gani nayi Maleeka ta lumshe idanuwa yayinda tace “Allah nagode maka… I am officially Mrs. MK Sodangi. Ya Allah… buri na ya cika… I now own the cutest and most sweetest guy in this whole wide world”5 A dayan bangaren MK yana dariya yace “Yes my Babe.. Finally we belong to eachother. I love you so much and I cant wait for our honeymoon to begin…” Murmushi tayi yayinda ta ji ya cigaba da fadin “….babe ni fa I think idan an gama reception dinnan zan zo in tafi da ke..” Zaro idanuwa tayi tace “what??? don Allah ka rufa mun asiri… sai an gama dinner anjima sannan za’a kawo ni kuma ma fa na ji Mummy tace wai gidan Mamy za’a kai ni first…” Da sauri yace “What??? wai dama ba yau za’a kawo ki gida na ba?? Gaskiya bana son tradition dinnan da ake yi.. mutum da matar shi sai ayi ta ja mishi rai” Tana dariya tace “My love kar ka damu… flight din mu ba gobe da yamma bane?? idan mun tafi fa it will be just me and you… remember??” Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “yeah babe.. its gonna be just me and you and no one else har abada insha Allah” really??😏4 Kafin yayi magana ne ta ji muryar Fahad yana fadin “MK your attention is needed here please” Gani nayi Maleeka ta bata rai tare da turo baki yayinda ta ji MK yace “Babe let me get going.. ana nema na. will call you later and kar ki manta ki aiko mun hoto” Tace “Okay Honey.. I love you bye” Bayan ta kashe wayar ne ta juyo ta kalli Jameela tace “wallahi bana son Fahad dinnan… na rasa meyasa Honey yake ji da shi. ki duba fa kawai muna hirar mu ya zo yayi interrupting kuma na sani sarai ya san da ni yake waya..” Jameela wadda take kallonta cike da mamaki ce tace “na shiga uku da complain dinki Leek, baki son shi amma dole kiyi haquri tunda mijinki yana son shi. I really have to tell you this… kiyi qoqari ki so duk wani abinda Ya MK yake so… it’s the least you can do for him considering the unconditional love he has for you” Gani nayi Maleeka ta turo baki yayinda Jameela ta cigaba da fadin “kin dai san you are not perfect kuma kin sani sarai ba kya jin magana but dukda haka Ya MK sees each and every imperfection of yours to be perfect. Again, wannan girman kan naki yakamata ki rage shi don kuwa zai iya janyo miki matsala…”2 A daidai lokacin ne Maleeka ta bude wata drawer ta dauko wata leda zata kai ma Ummi ta hada mata cikin kayanta. Ledar ce ta kufce daga hannunta yayinda kwalayen maganin da ke ciki suka watse a qasa. Jameela wadda idanuwanta suka kai kan kwalayen magani ne tayi saurin duqawa ta dauki daya daga cikin su yayinda na ga ta zaro idanuwa cike da tsananin mamaki. Da sauri ta kalli Maleeka tace “Subhanalillah… Leek?? emergency contraceptive pills??? as in maganin hana daukar ciki???”1 A daidai lokacin ne Ummi tana shirin fitowa daga closet din ne ta ji wannan maganar yayinda ta tsaya cak cike da tsananin mamaki!!1 ♧♧♧♧♧♧♧ Hmmm…