UMMI CHAPTER 5

UMMI CHAPTER 5

MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Wuraren qarfe goma na safe tana cikin sitting room din shi yayinda take mopping floor. kamar kullum tana yi tana yaba kyan tsarin komai da yake cikin sitting room din. Allah ma ya sani komai na gidan MK birge Ummi yake yi. Ummi dai dama a daidai wannan lokacin ne take shiga sashen shi tayi ‘yan gyare gyaren ta kamar dai yadda Maleeka ta sa ta. Ta tabbatar a lokaci kamar hakan kuwa baya nan. Haka kawai ta ji zuciyarta ta fara bugawa yayinda take jin qamshin wani turare mai dadin gaske. Bata ankara ba ne ta ji motsi a bayanta. Aikuwa tana juyowa ta gan shi tsaye riqe da wayar shi. Sanye yake cikin three quarter sweat da farar T-shirt… Gashin shi a bit rough, da alama ma bai dade da tashi daga bacci ba don ba sai an fada ba ko wanka bai yi ba. MK wanda yake tsaye ne ya sa mata idanuwa cike da tsananin mamaki… the last person he expected to see.. that too in his sitting room!! Ji nayi yace “hey… me kike yi anan??” Ummi wadda qafafuwanta suka yi sanyi gani nayi ta jefar da mopping stick din hannunta yayinda ta juya zata gudu. MK ne yayi saurin fadin “hey tsaya mana…” Ko kafin ya rufe bakin shi sai ji yayi ta sa ihu yayinda ya ga ta zame ta fadi a qasa. Runtse idanuwa yayi ya bude yayinda ya girgiza kai. Yana nan tsaye yana kallonta ne ya ga ta yunqura zata tashi yayinda take kuka tana fadin “wayyo Allah naawalla..” Shafa kan shi yayi yace “what is she saying??” Gani nayi ya fara dosowa inda take yayinda ta fara ja baya, kanta a duqe tana fadin “don Allah kayi haquri… yanzu zan tashi in bar maka…” the sweet voice.. Gani nayi ya sa yatsar shi a baki yayinda yace “sssshhhhh…” sannan ya miqa mata hannu yana kallonta. Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda ta kasa dagowa ta kalle shi.. ita dai Ummi ko kadan bata son kallon MK.. A duk lokacin da ta kalle shi wani iri zuciyarta take yi mata. Gani nayi ta girgiza kai alamar a’a yayinda take share hawayen fuskarta. Har a wannan lokacin kuwa kanta a duqe ne. Ji tayi yace “idan baki kawo hannun ki ba zan dauke ki…” Aikuwa tun kafin ya qarasa magana tayi saurin cafko hannun shi.1 A lokacin da ta riqe hannun shi kuwa sai da gaban su ya fadi a dalilin wani mugun shocking da suka ji.3 Da sauri Ummi tayi qoqarin qwace hannunta daga nashi amma kuma ya riqe gam. Dago ta yayi ta tashi da qyar sannan ya zaunar da ita akan three seater kujera. Jikin Ummi sai rawa yake yi yayinda ta runtse idanuwanta gam. MK dai tsayawa yayi a gaban ta yayinda ya kafa mata idanuwa yana mamakin abinda yarinyar take yi a gidan. STORY CONTINUES BELOW Tunda Maleeka ta tafi yake cikin tsananin damuwa da tashin hankali amma kuma abin mamaki yana ganin yarinyar nan a yanzu sai ya ji zuciyar shi tayi sanyi. Ya rasa dalilin da ya sa yarinyar take affecting rayuwar shi haka..5 Gani nayi ya latsa wayar shi ya kai kunnen shi yace “hello Dr. Davis..” Murmushi yayi yace “I am fine.. please can you come over to my house..” Ita dai Ummi sauraron shi take yi amma har ya gama wayar bata san me yace ba. Bayan ya kashe wayar ne ya ji tace “hamma kayi haquri bazan qara shigowa nan ba..” Ummi dai har yanzu idanuwanta a rufe suke. Cike da mamaki yace “ban gane bazaki qara shigowa ba… na kore ki ne??” Bai jira amsar ta ba ya cigaba da fadin “….me kike yi a gidan nan?? tun yaushe kika zo??” Sossai zuciyarta take bugawa a dalilin tsayawa daf da ita da yayi.. ga qamshin turaren shi da ya cika ta wanda ya ruda ta gaba daya. Muryarta tana rawa tace “tun bayan da kuka dawo daga tafiya ne Adda ta dauko ni..” Yace “what??? kina cikin gidan nan all this while kuma ban taba sani ba??” Gani yayi ta miqe tace “Hamma insha Allah bazan qara shigowa nan din ba idan kana nan.. don Allah kar ka fadi ma Adda” Tana taka qafarta ahankali ta nufi wurin kayan mopping dinta zata dauka ta tafi. Jin muryar shi tayi yana fadin “idan kika bar nan ba tare da nayi miki izini ba sai na fadi mata” A razane ta juyo ta kalle shi.. hakan kuwa sai da ya sanya zuciyarshi ta buga. Sossai ya hango tsoro hade da damuwa a tattare da ita…. Ita kuwa Ummi gani nayi ta duqar da kanta yayinda qafafuwanta suka yi mugun sanyi. Ji tayi yace “Zo ki zauna..” Da sauri ta koma ta zauna a qasa yayinda ta bi ta takure. Gani nayi MK ya zauna akan kujera kusa da ita yayinda ya sa mata idanuwa. Dukda kan yarinyar a duqe ne bai hana shi ganin kyakyawar fuskarta ba. what a beautiful and cute face he thought.. Yau itace rana ta farko da MK ya yaba kyan wata mace wadda ba Maleeka ba.. infact zai iya cewa yarinyar da yake kallo a yanzu is the most beautiful creature he has ever seen in his life..8 Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “meye sunanki??” Cikin qaramar muryar ta mai dadi tace “Ummi” Murmushi yayi yace “toh meyasa kike rufe idanuwan ki ba kya son kallo na?? ko nayi kama da dodo ne??” Da sauri tace “a’a Hamma..” Wayar shi ce tayi ringing yayinda yayi answering.. Ji tayi yace “okay I am coming” Bayan ya kashe ne ya kalle ta yace “ina zuwa yanzu kuma kar ki sake ki tashi daga nan” Bayan ya fita ne ta bude idanuwan ta. Gani nayi ta dafe qirjinta tare da sakin numfashi wanda da alama tana riqe da shi for long. Tana nan zaune ta ji shigowar su. Ita dai Ummi ta ji yana ta magana da mutumin cikin harshen turanci.. ko da ta dan kalli mutumin ta gane cewar likita ne. Gani nayi ta zaro idanuwa a ranta tace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… meye haka??..” STORY CONTINUES BELOW Bata ankara ba kuwa ta ji muryar MK yana fadin “ki nuna mishi inda ke yi miki ciwo..” A hanzarce Ummi ta miqe tsaye wanda hakan ya sanya qafarta ta amsa yayinda tace “wayyo Allah” MK wanda yake kallonta ne yace “ke ina wasa da ke?” Da sauri tace “a’a Hamma… don Allah kayi haquri ni wallahi tsoron shi nake” yayinda ta nuna likitan. Duk maganar nan da take yi kuwa har yanzu bata kalli MK directly ba. Shi kuwa a bangaren shi bala’in jin dadin sauraron muryar yarinyar yake yi.. he just love her voice.. Dr. Davis dai yana tsaye yana kallon ikon Allah yayinda MK ya dan matsa kusa da ita yace “idan baki zauna kika nuna mishi ba zan fadi ma Adda..” Aikuwa nan da nan ta zauna a qasa yayinda ta nuna musu ankle dinta tace “nan ne Hamma..” Murmushi MK yayi sannan ya kalli Dr. Davis yace “go ahead doc” Komawa yayi kan wata kujera nesa da su ya zauna yayinda yake latsa wayar shi. Ni da na leqa gani nayi yana dialing number din Maleeka wanda take amfani da shi idan ta je England amma switched off. Fuskar shi ce tayi displaying tsananin damuwa yayinda na ji yace “where are you babe??..”2 Nikuwa nace ga wata babe din nan a gaban ka🤣10 Bai ankara ba ya ji ihunta. Yana nan zaune ya hangota tana ta qoqarin qwace qafar ta daga hannun likitan. Shi dai daga inda yake zaune ya ji tana ta wasu maganganu cikin yaren da bai gane ba… ba sai an fada ba ya san zagin likitan take yi. Fuskar yarinyar kawai yake kallo yayinda take bashi dariya amma kuma ya matse.. Gani nayi Dr. Davis ya tashi yayinda shima MK ya tashi ya nufi wurin shi. Dr. Davis wanda ya gyara glasses din idanuwan shi ne yace “its nothing major Mr Muhammad Kabir..” ya fiddo wani ointment daga cikin jakar shi ya miqa mishi yace “she will need to apply this three times daily and she will be just fine” MK ya karba yayi mishi godiya. Bayan ya raka likitan ya tafi ne ya dawo ya tarar da ita inda ya barta. Har a wannan lokacin tana share hawayen fuskarta. Murmushi yayi sannan ya miqo mata Ointment din. ba tare da ta kalle shi ba ne ta karba. Ji tayi yace “ki dinga shafawa sau uku a rana.. idan kuma kika qi qafar ki zata rube sai a yanke” Zaro idanuwa tayi tace “na’am…” MK wanda yake matse dariya ne yace “nace idan qafar ta rube sai a yanke ta ki zama mai qafa daya…” Da sauri tace “wallahi zan sa Hamma.. nagode” Girgiza kai yayi yana murmushi ya nufi hanyar dakin shi. Aikuwa yana shigewa ne Ummi ta miqe ta ja qafarta ta kwashe kayan mopping dinta ta bar falon. ************* MK ne tsaye a gaban dressing mirror dinshi yayinda yake shirin shiga wanka. Gani nayi yana ta murmushi wanda daga baya na ga ya fashe da dariya. Abubuwan da Ummi tayi ne suke bashi dariya. Shi kam haka kawai ya tsinci kanshi cikin tsananin farin ciki. Ya rasa yadda aka yi yake jin yarinyar a ranshi.. sossai yake son sauraron muryarta mai dadin gaske. Gani nayi ya runtse idanuwan shi yayinda ya sa hannuwan shi ya rufe fuskar shi. Hoton kyakyawar fuskar yarinyar yake gani.. da sauri ya bude yayinda ya saki ajiyar zuciya yace “what a beautiful soul..” *************** Ummi dai komawa tayi dakinta ta rufe qofa ta sa key sannan ta haye kan gadon tare da rungume pillow. Idanuwanta a rufe yayinda take tuno abubuwan da suka faru a while ago. “toh meyasa kike rufe idanuwan ki ba kya son kallo na?? ko nayi kama da dodo ne??” Ji nayi tace “ya ma za’ayi kayi kama da dodo Hamma.. ai duk duniyan nan babu wanda ya kamo ka a kyau”1 Murmushi tayi sannan tace “Hamma yana da kirki… dama ace kai Hamma na ne dagaske”3 🤔🤔🤔2 **************** Ummi dai bata qara fitowa ba tunda ta shige daki domin kuwa bata so ko alama su qara haduwa saboda wannan abun da take ji a cikin zuciyarta. Wanne abu kenan?6 Shi kuwa MK gaba daya ma tunanin yarinyar ya hana shi yin komai a yau. he kept thinking about her- from her beautiful face to her sweet voice to her little drama… he feels totally connected with the girl!! why??2 Tuni damuwar da yake ciki akan tafiyar Maleeka ta fara warwarewa..9 Ni kuwa nace toh fa… ♧♧♧♧♧♧♧♧ ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Tsaye yake a gaban Vanity mirror na dakin shi wuraren qarfe tara na safe yayinda yake brushing gashin kanshi. Wayarshi ce tayi ringing ya nufi inda take a kan gadon shi ya dauka. Gani nayi yana murmushi yayi answering yace “Hello Mamyna ina kwana” A dayan bangaren ne Mamy tace “lafiya lau, ya jikin naka??” Yace “Alhamdulillah..” Tace “Madallah… Abban ku yace kunyi waya jiya da daddare ko?” Yace “yes Ma” Tace “dazu mukayi waya da Maleeka…” Zuciyar shi ce ta buga yayinda ya cigaba da sauraronta. “……tace kunyi waya da ita wai kace tayi zamanta ta qarasa abinda takeyi” Sossai MK ya cika da tsananin mamaki. the lady that has refused to listen to him at all shine take fadin haka.. me ke damun ta ne?? Gyaran murya yayi sannan yace “eh Mamy.. zan kira su Mummy in fadi musu don nasan they will be against it” Tace “hakan ma yayi daidai ai… toh yanzu me kake buqata a kawo maka??” Yace “nothing Mamy, Chefs suna dafa abinci ai. tunda kun hana ni zuwa office I will just eat, watch and sleep… i am definitely going to be bored kam amma ya zanyi da ku” Mamy tana dariya tace “lafiyarka ake jiye maka MK.. kayi haquri ka ji??” Yace “it’s okay Mamy.. thanks for being a sweetheart.. I love you so much. ki ce ma Chubby nace idan bata zo ta duba ni ba zan warware deal din mu” Mamy tana dariya tace “aikuwa yanzun nan ta tafi school.. wai tana da test” Yana murmushi yace “ayya.. Allah ya bata sa’a” Tace “ameen” Bayan sunyi sallama ne yayi dialing lambar Maleeka. Har ta gama ringing bata amsa ba. Gani nayi yayi typing message ya tura mata. ************** MK ne ya fito daga sashen shi riqe da wayar shi a hannun shi. Dinning ya nufa inda aka jera breakfast. Gani nayi ya bubbude yayinda ya ga abinci masu rai da lafiya kala-kala. Ji nayi yace “Coffee first” sannan ya juya ya nufi Kitchen. Yana daf da shiga ne na ga ya tsaya cak yayinda ya natsu yana sauraron muryarta. Ummi ce zaune a qasan Kicin din yayinda take karatun Al-qur’ani mai girma. Ummi dai bayan Chefs sun gama hada breakfast ne ta gyara ko ina yayinda ta zauna zaman jiran lokacin da MK zai tafi ofis don ta je ta gyara sashen shi. Tana zaune ne ta fara kawo haddan da ke kanta kamar dai yadda take yi a duk lokacin da bata yin komai. a cikin karatun ne ya ji tace “..Yaaa ayyuhal lazeena aamanoo laa yaskhar qawmun min qawmin…” Da sauri ya qarasa shiga kicin din yayi gyaran murya. Hakan kuwa ya razana ta yayinda ta miqe tsaye a firgice. Gani nayi ta juya da sauri zata fita ta qofar bayan kicin din yayinda yayi saurin fadin “dawo nan Ummi..” Tsayawa tayi cak dafe da qirjinta yayinda zuciyarta take ta bugawa. STORY CONTINUES BELOW Bata ankara ba ta ji yayi bisimillah yayinda ya fara karatu kamar haka “Yaaa ayyuhal lazeena aamanoo laa yaskhar qawmum min qawmin ‘asaaa anyyakuunuu khairam minhum wa laa nisaaa’um min nisaaa’in ‘Asaaa ay yakunna khairam minhunna wa laa talmizuu anfusakum wa laa tanaabazuu bil alqaab, bi’sal ismul fusuuqu ba’dal eemaan, wa mal-lam yatub fa-ulaaa’ika humuz zaalimuun”1 Da sauri ta juyo tana kallon shi, ganin shi tayi zaune a kan daya daga cikin kujerun Island na kicin din. Ganin shima ita yake kallo ne na ga tayi saurin duqar da kanta yayinda zuciyarta ta cigaba da bugawa. Shi kam MK gani yayi ma kamar yarinyar ta qara kyau a yau. As always sanye take cikin hijabi dogo har qasa. Ji tayi yace “Yaaa ayyuhal lazeena aamanuu laa yaskhar qawmum min…” Ummi tana sauraron shi ta ji ya cigaba da fadin “meemun ce ba nunun ba… sannan haduwar meemun din guda biyu zai sa ki shigar da daya a cikin daya… ana kiran wannan Idgham shafawee ko kuma idgham meem saakinah..”3 Ita dai Ummi tunda ya fara yi mata bayani ya birge ta matuqa… haka kawai ta ji ya qara shiga ranta. Bata ankara ba ta ji yace “zo ki zauna ki cigaba da karatun in ji” Muryar ta tana rawa tace “don Allah kayi haquri Hamma..” MK dai mamaki yayi na yadda duk ta bi ta rude. Girgiza kai yayi sannan yace “idan baki zauna ba zan fadi ma…” Da sauri ya ga ta zauna a qasa tace “zanyi Hamma…”5 Murmushi yayi yana kallonta cike da mamaki. MK dai ya kula yarinyar tana bala’in tsoron Maleeka.. ya kula da zarar yace zai fadi mata tayi laifi duk sai ta bi ta rude. hehehehe… Haka ta cigaba da yin karatun yayinda yake ta sauraron muryar ta mai dadi sannan ya cigaba da yi mata gyara a wuraren da tayi kuskure. MK dai sossai yarinyar nan ta gama birge shi. Sossai ta qara shiga ran shi… sossai yake jin wani connection a tsakanin shi da ita.. Ni kuwa nace the feeling is mutual…2 Gyaran murya yayi yace “ina kika tsaya a karatun ki??” Tana wasa da yatsun hannun ta tace “Suratul Saba’ na tsaya” Yace “that’s good… kin iya karatu Ummi. kawai kina buqatar qara sanin hukunce-hukuncen Tajweed ne and you will be just fine” Ita dai Ummi ta ji abinda yake fadi amma fa bata wani gane ba tunda ya sanya turanci a maganar. Ji tayi yace “ya qafar ki?? ta daina ciwo?” Tace “eh Hamma ta daina” Addu’a ta fara yi akan Allah yasa ya tashi ya fita daga kicin din amma kuma abin mamaki sai gani tayi ya tashi ya nufi wurin Coffee maker. Tana kallon shi ta ga ya zuba ruwa a jug din coffee maker din yayinda yayi setting dinshi. Daga nan kuma ya dauko Coffee din ya zuba a sama ya rufe yayinda ya kunna. Ummi dai tana ganin abun a kicin din amma bata taba sanin me ake yi da shi ba. Juyowa ya dan yi ya ga tana kallon abinda yake yi wanda suna hada idanuwa ne tayi saurin kawar da kanta yayinda ya girgiza kai yana murmushi. Ji tayi yace “taso ki ga yadda ake yi don daga yau ke zaki dinga yi mun da safe sannan da dare har zuwa ranar da Addar ki zata dawo..”1 Gani nayi ta miqe da sauri ta nufi wurin shi yayinda ya dinga nuna mata komai. Ita dai Ummi tunda ta ji yace zata dinga yi mishi ta ji dadi a ranta domin kuwa ji take yi babu abinda bazata iya yi mishi ba a rayuwar nan.5 STORY CONTINUES BELOW A lokacin da yake shirin zuba ruwan Coffee din a cikin cup ne ya dan zubar mishi a hannu yayinda ta ji yace “ouch” Hankalinta ne yayi mugun tashi yayinda tayi saurin riqe hannun shi tana hurawa tare da fadin “ka kone ne?? sannu Hamma… ai da ka bari na zuba maka…”1 MK dai freezing yayi a tsaye yana kallonta, sossai yake mamakin tsananin damuwar da ta bayyana a fuskar yarinyar. Ya tabbatar hankalinta baya tare da ita shiyasa ta riqe hannun nashi. Gani yayi ta ja shi zuwa sink ta bude famfo tace “bazai yi maka zafi ba idan an sa ruwan sanyi…” Shi dai MK zuba mata idanuwa yayi yayinda yake ta mamaki. Bayan dan lokaci ne ta rufe famfon sannan ta cigaba da hura mishi tace “ya daina zafi??” Yana kallonta yace “nace miki yana mun zafi ne??” Da sauri ta dago kanta sannan ta saki hannun shi ta matsa baya. Muryarta tana rawa tace “don Allah kayi haquri da na taba ka Hamma.. ban san..” Murmushi kawai yayi sannan yace “nagode Ummi” Sossai jikinta ya dinga rawa yayinda ta juya zata bar kicin din. Muryar shi ta ji yace “dawo nan… bamu gama ba” Jiki a sanyaye ta dawo ta tsaya a gefenshi ta cigaba da kallon abinda yake yi. Gani tayi ya dauko cream ya zuba a coffee din. Bata ankara ba ta ga ya kai cup din saitin bakinta yace “sha ki ji..”2 Matsawa baya tayi da sauri tace “bazan sha ba” Cike da mamaki yace “meyasa?? kin taba sha ne kika ji babu dadi ko me??” Kanta a duqe yayinda take kallon yatsun qafafuwan shi wanda ke sanye cikin wani designer slippers mai kyan gaske ne tace “Hamma ya za’a yi in sha daga kofin ka??? kuma ma idan na sha kai wanne zaka sha??” Gani nayi MK yayi murmushi yayinda yace “da ni da ke waye mahaliccin mu??” kai tsaye tace “Allah” Yace “good.. da ya halicce mu ya bambanta mu?” Girgiza kai tayi alamar a’a. Yana murmushi yace “toh da ni da ke daya muke sannan ai ban ce ki shanye mun ba balle in rasa.. kawai dandanawa zakiyi idan yayi miki dadi sai ki dinga yi mana da ni da ke” Ya dan yi shiru sannan yace “sai dai idan kuma kyama ta kike yi toh..” Da sauri ta dago kai ta kalle shi wanda suka hada ido. Wani abu ne ya soki zuqatansu wanda kuwa ya sanya su yi pause na dan lokaci.2 Gani tayi ya qara matso da cup din saitin bakinta. Hannunta na rawa ta karbi cup din yayinda ta kai bakinta. Dan kadan ta sha sannan ta miqa mishi tana squeezing fuskarta. Ko da ya karba kallonta yake yi yana murmushi yace “akwai dadi” Daga kai tayi alamar “eh” Hararar ta yayi yace “ban ce kiyi mun qarya ba.. da ganin yadda kika bata fuska nasan bai yi miki dadi ba..” Gani tayi ya juya zai bar kicin din yayinda yake shan Coffee dinshi. ‘Yar qaramar muryarta ya jiyo a bayan shi tace “Hamma nagode” Ya juyo yace “da me??” Ta duqar da kai sannan tace “komai..” Murmushi yayi yace “nima nagode Ummi”. Daga nan ya juya ya fita.3 **************** Da yamma MK yana zaune a lawn din sashen shi yana duba business news a I-pad dinshi ne wayar shi tayi ringing. STORY CONTINUES BELOW Ganin sunan abokin shi ne yayi murmushi sannan yayi answering. Fahad ne yace “haba abokina… ya na ji ka shiru ne?? you didn’t even call to ask how far da office..” nikuwa nace ina fa zai kira🤣🤣…1 MK yana murmushi yace “yi haquri my friend.. I was carried away ne” Fahad cike da mamaki yace “carried away by what?” Yace “hey guess what… the girl” Fahad yace “what girl??” can kuma yace “wait.. you mean the maid??” Da sauri MK yace “point of correction abokina… Ummi sunan ta” Fahad wanda ya fashe da dariya yace “whoa… abokina yi haquri… UMMI. a ina ka ganta??” Anan ne MK ya ba abokinshi labarin abinda ya faru tsakanin shi da Ummi. Ji nayi yace “I swear abokina I feel completely connected to this girl… I really wanna help her in every possible way that I can” Fahad dai sossai ya ji dadin abinda ke faruwa. Yana murmushi yace “if you want to help her just marry her..”13 Da sauri MK yace “what??? haba don Allah… dadi na da kai idan ana maganar arziki sai ka sako shirme.. ta ya zan auri wannan yarinyar?? I mean she is a small girl fa besides who told you cewar sonta nake yi?? kawai fa…” Fahad ne ya dakatar da shi inda yace “yi haquri abokina.. ya labarin Maleeka? ta kira ka??” MK ya saki ajiyar zuciya sannan yace “wallahi bata kira ni ba..” Anan ya bashi labarin yadda tayi da su Mamy yayinda ya fadi mishi cewar ya riga ya sanar da Daddy kuma sun amince akan ta zauna har sai ta gama abinda take yi. Fahad wanda yake cike da mamaki ne yace “abokina is Maleeka okay??.. as in who does something like this? kenan sai yaushe zata neme ka??” MK yace “I really am confused at the moment… matsala na ma shine ta qi sauraro na..” Fahad ne ya katse shi tare da fadin “Ka qyale ta abokina… she will look for you duk lokacin da ta ga dama.. ni kam ina nan zuwa gidan in ga Ummi” MK ya girgiza kai yace “wato baka zo ganin matar gida ba lokacin da take nan sai yanzu zaka zo gulman ganin wata ko?” Fahad ya fashe da dariya yace “eh din.. na ji” Daga nan kuwa suka cigaba da hirar su na office. **************** Da daddare wuraren qarfe tara ne ta shigo falon shi cikin sallama. MK dai kwance yake a kan kujera yana kallon NXT a TV. Asali dai wrestling din da yake kallo cikin dare ake yin LIVE amma dayake yana recording din su shi sai at his convenient time yake kallo. Aikuwa tunda ya ji muryarta ya sa mata idanuwa. Sanye take cikin hijabi dogo har qasa kamar kullum. Sossai yarinyar tayi mishi kyau. Riqe take da tray wanda yake dauke da coffee cup. Ko da ta qaraso ta ajiye a kan side stool ne ta duqa har qasa tace “ina wuni Hamma” Gani nayi ya tashi zaune yayinda ya lanqwashe qafafuwan shi a kujerar yace “lafiya Ummi” Muryarta tana rawa tace “ga abinka nan na kawo maka.. amma don Allah Hamma idan baiyi dadi ba ka gaya mun sai in je in yi maka wani” MK yana murmushi ya janyo Cappuccino din ya kai bakin shi. Sip daya yayi na ga ya bata rai. Ummi kuwa tana ganin haka ta miqe da sauri cike da tsananin damuwa tace “don Allah kayi haquri.. bari in je in sake yi maka wani” Gani tayi ya fashe da dariya yayinda yace “me nace?” Kai tsaye tace “Hamma ka bata rai.. nasan bai yi dadi..” Yace “ban taba shan mai dadin wannan ba Ummi..” Zaro idanuwa tayi tace “dagaske Hamma??” Ya girgiza kai sannan yace “zaki dinga yi mun kullum??” Tana murmushi tace “eh Hamma” yace “nagode Ummi” Gani yayi ta tashi sannan tace “sai da safe Hamma” Da sauri yace “tsaya mana” ya miqe tare da ajiye cup din yace “Jira ni ina zuwa” Gani tayi ya nufi hanyar dakinshi yayinda ta saki ajiyar zuciya. Mamaki take yi na dalilin da ya sanya yace mata ta jira shi. Ummi dai daga kai tayi ta kalli TV sai gani tayi wasu mutane suna ta dukan junan su sannan duk sun gaji. Da sauri ta kawar da kanta cike da damuwa yayinda na ji tace “meyasa yake kallon irin wannan?” hahahaha… MK ne ya fito riqe da kwalin waya. qarasowa yayi wurinta ya miqa mata yace “ga wannan” Ummi dai matsawa tayi baya tace “Hamma na waye??” Yace “naki ne..” ko kafin ya rufe bakin shi ne tace “ni bana so” Bata rai yayi yace “ni kuma nace sai kin karba..” tace “don Allah kayi haquri” Yace “bazan yi ba” Kanta a duqe kawai sai ji yayi ta fashe da kuka. MK wanda ya cika da mamaki gani nayi ya dan duqo ya kalli fuskar ta yace “Ummi saboda na baki waya shine kike kuka??” Tace “toh ni nace bana so Hamma” Yace “kin san abinda ke ciki da har zaki ce baki so??” Da sauri ta dago kai ta kalle shi yayinda ya cigaba da fadin “karatun Al-Qurani na sa miki a ciki saboda ki dinga ji kina qara koya..” Da sauri ta share hawayen fuskarta tace “kayi haquri Hamma… ban sani bane” Yayi murmushi yace “it’s okay Ummi.. zo ki zauna in koya miki” Ko da ya zauna a kan kujera sai gani yayi ta zauna a qasa.. Ba tare da yace mata komai ba shima ya sauka qasan a gefenta ya zauna. Ni kuwa da na kalli kwalin wayar da kyau sai na ga iphone11 pro.8 Nace what??? for a maid??🙄4 Haka ya fara nuna mata yadda zata yi operating wayar wanda da alama tana ganewa. Sossai yayi mamakin yadda yarinyar take saurin gane abu. Ya tabbatar da Ummi tayi karatu she would have being a good student domin kuwa qwalwar ta tana daukar abu da wuri. Yace “akwai abinda baki gane ba??” Ta dan yi shiru sannan tace “na gane duka…” Murmushi yayi ya miqa mata wayar sannan yace “toh ga wayar ki” Hannu biyu ta sanya ta karba sannan tace “nagode Hamma.. Allah ya saka da alkhairi” Miqewa yayi ya koma kan kujera sannan ya dauko coffee cup dinshi wanda har yayi sanyi. Yana kallonta yace “kin ga har Cappuccino dina yayi sanyi ma…” Da sauri tace “bari in je in hado maka wani Hamma…” Girgiza kai yayi alamar a’a yayinda yace “kar ki damu Ummi, zan shanye a hakan… je ki kwanta ki huta..” Ta miqe sannan tace “sai da safe Hamma… nagode sossai… Allah ya qara budi” Cike da jin dadin addu’o’in da tayi mishi ne yace “sai da safe Ummi” Haka ya bi ta da kallo har ta bar falon. ♧ ,MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO, ABUJA Zaune yake a dinning yana breakfast yayinda take zaune a qasa. MK dai kiran yarinyar yayi ta zo ta zauna anan. Shi kam haka kawai yake jin dadin zaman ta kusa da shi. Dukda ba wata hira suke yi ba amma having her close to him gives him plenty of joy. Babu yadda bai yi da yarinyar akan ta zauna kan kujera ba amma ta qi. Abincin ma da yace ta zuba ta ci sai ce mishi tayi ta riga ta ci nata. Bayan ya gama ne ta miqe ta kwashe dishes din sannan ta gyare ko ina tsab. Har ta gama yana nan zaune yana kallonta. Ko da ta shiga kicin don wanke dishes din bin ta yayi ya zauna a kan kujerar Island ya cigaba da kallonta.6 Ita dai Ummi bata son hakan domin kuwa ruda ta yake yi. Ita bata san meyasa ya daina zuwa office ba. Ji nayi kawai tace “Hamma meyasa baka zuwa aiki??” Kai tsaye yace “saboda likita ya hana ni” Da sauri ta juyo tana kallon shi cike da tsananin damuwa tace “baka da lafiya ne??” Muguwar damuwar da ya gani a fuskar yarinyar ce ta sa yayi mamaki matuqa. Yana murmushi yace “hey relax.. na warke” Ajiyar zuciya ta saki cike da tausayawa tace “sannu Hamma.. Allah ya qara baka lafiya” Yace “ameen” Wayar shi ce tayi ringing yayinda yayi answering. Ji nayi yace “hey chubby how are you.. how was your test yesterday??” Shiru ya dan yi sannan yayi murmushi yace “Allah ya so ki kuwa… na so in fasa abun nan…” Gani nayi ya tashi yayinda yake murmushi yace “one minute Hafsah..” Ya matsa kusa da Ummi yace “idan kin gama ki zo falona” Tace “toh” Haka ya cigaba da magana da Hafsah yayinda na ji yana fadin “ki zo mun da Ice cream please..” ********** Kwance yake a kan kujerar babban falon shi yayinda idanuwanshi suke a rufe. Ummi wadda take zaune a qasa ce take karatun Al-qur’ani kamar yadda ya sa ta. Shi kam MK sossai yake jin dadin sauraron sautin muryar yarinyar. Haka ya dinga sauraronta wanda idan ya ji kuskure sai ya gyara mata. Hafsah ce take ta sallama cikin falon. Daga MK har Ummi basu ji ba. Gani nayi ta tsaya turus yayinda take kallon Ummi wadda take ta karatu cikin muryarta mai dadin gaske. Sossai tayi mamakin ganin yarinyar a gidan. A lokacin da ta qarasa shiga ne Ummi ta ganta. Da sauri ta russuna tace “ina wuni Adda” yayinda ta miqe ta karbi qatuwar ledar da ke hannunta. A wannan lokacin ne MK ya bude idanuwan shi yayinda ya ji Hafsah tace “lafiya lau” Ta kalle shi sannan tace “Hey bro.. what is she doing here?? ba maid din gidan Mummy bace wannan??” MK wanda ya tashi zaune yayinda ya lanqwashe qafafuwan shi a kan kujera ne yace “Hafsy she has a name… its Ummi” Hafsah dai ta cika da mamaki a yanzu. Gani nayi ta zauna a gefen shi yayinda ta ga Ummi ta tashi zata tafi. STORY CONTINUES BELOW MK ne yace “Ummi zo ki bani ledar ice-cream dinnan” Ta dawo ta dauko ta miqa mishi. Gani suka yi ya bude ya dauki roba daya sannan ya miqa mata ledar yace “je ki shanye wannan.. idan bazaki iya shanyewa ba ki sa a freezer sai anjima ki shanye” Ummi dai ta so tace bazata sha ba amma sanin halin MK na kafiya ne ta russuna ta karba sannan tace “nagode Hamma” Har ta kusa fita ne ta ji yace “Ummi ga wayar ki kin bari anan” Hafsah dai sossai ta cika da mamaki a lokacin da ta ga iPhone 11 pro a kan centre table.2 Jiki a sanyaye ta dawo ta dauki wayar sannan ta fita. Hafsah kuwa kafa ma MK idanuwa tayi yayinda ta ga ya bude robar ice-cream din shi ya fara sha. Ko da ya dago kai ya kalle ta gani yayi ta zuba mishi idanuwa. Hararar ta yayi yace “what???” Hafsah wadda take cike da mamaki tace “Ya MK what is happening?? me yarinyar nan take yi a gidan nan? and the phone.. how can she be using an iPhone 11 pro when yours is just an ordinary 11??” Murmushi yayi yace “Maleeka ta daukota.. I gave her the phone and nothing is happening” Hafsah cike da mamaki tace “amma meyasa ka..” Bai bari ta qarasa maganar ta ba yace “… na bata babbar waya?? she is human too Hafsah and kin fi kowa sanin I dont discriminate between people..” Anan dai ya bata labarin dalilin da ya sanya ya bata wayar and how he feels connected with the girl. Hafsah dai sakin baki tayi tana mamakin yayanta. Wai yau shine yake labarin wata wadda ba Maleeka ba har haka.. unbelievable!! Kai tsaye Hafsah tace “Ya MK are you in love with her??” Da sauri ya kalle ta yace “what the hell Hafsy… how can I be in love with the girl??” Tana murmushi tace “toh meye Ya MK?? from yadda kayi mun bayani ai tana da duk wani quality da kake so a mace… qualities din da har Ya Maleeka bata da su and we both know that..” Ta dan yi pause sannan ta cigaba da fadin “wait.. kar kace mun kana tunanin tayi maka qarama ne?? I am sure ta kai seventeen and she is just perfect..”2 Bata qarasa maganar bane ta ji ya bugi kafadarta yace “just shut up.. na dauki Ummi a matsayin qanwa ta just like you” Fashewa tayi da dariya yayinda yace “yi haquri bros.. I was just teasing you ne besides Ya Maleeka bazata taba bari kayi mata kishiya ba.. kishiyar ma ‘yar aiki” Hararar ta yayi yace “kar ki qara kiranta ‘yar aiki Hafsy… her name is Ummi please” Turo baki tayi tace “hmmm… I am jealous fa! na ga kamar zata qwace mun position a wurinka” Murmushi yayi tare da jan kumatunta yace “no one can take your spot my dearest chubby..” Murmushin jin dadi tayi tare da riqo hannun shi tace “yauwa bro… ya maganan deal din mu??? I swear I need the car…” Hafsah dai wata sabuwar Mercedes Benz AMG-GT ce da ta fito take so a siya mata. Dayake Abba yace bazai siya mata ba a dalilin tana da manyan motoci har uku shine ta dawo wurin MK wanda kuwa ya amince zai siya mata. Motar dai bala’in tsada gareta.. a cewarta ma idan za’a siyo mata ita a qwace sauran motocin toh she is okay.. shi kuwa MK he promised to buy her the car sannan ta hada da sauran ta cigaba da hawa… afterall she is his only sister and she deserves every happiness a rayuwar nan!! STORY CONTINUES BELOW Girgiza kai yayi yace “anjima za’a kawo miki” Zaro idanuwa tayi tace “dagaske Yaya??” Yace “anything for my sweet chubby” Turo baki tayi sannan kuma tace “toh yanzu Abba fa??? ka san zai yi fada..” Yana murmushi yace “kar ki damu zanyi mishi bayani” Cike da murna tayi hugging dinshi tare da fadin “thank you very much bro… You are the best kuma Allah ya azurta ka da yara wadanda zasu yi gadon halinka..” Ji nayi yace “ameen my dearest Hafsy..” a ranshi kuwa yace “cant wait for the day she will agree to give me a child” Ni kuwa nace kana da aiki… ah toh!!3 *************** Da yamma ne Fahad ya zo gidan bayan yayi closing daga aiki. Suna zaune a falon MK suna ta hira ne Fahad din yace “abokina tana ina??” MK yana murmushi yace “dagaske dai Ummi ka zo gani ba ni ba kenan?” Fahad yana dariya yace “ku biyu na zo gani” MK ya girgiza kai ya dauki wayarshi yayi dialing number din Ummi. Cikin qaramar muryar ta mai dadi tayi mishi sallama wanda ya amsa tare da lumshe idanuwa. Allah ma ya sani muryar yarinyar na bala’in yi mishi dadi. MK bai qi ace ya zauna ba yayi ta sauraron muryarta 24/7. Ji nayi yace “akwai baqo a falonta ki hada abubuwan motsa baki ki kawo yanzu” Tace “toh Hamma” Fahad yana murmushi yace “na ji ka kira ta a waya… you didn’t tell me har waya ka bata ai don dai nasan batada waya” MK yana dariya yace “zan baka wannan labarin abokina..” Fahad dai yana ta mamakin abubuwan da suke faruwa da abokin shi a game da yarinyar. The MK he knew before is definately not thesame MK sitting in front of him right now.. abinda dai ya sani shine he is happy with the present situation and he is hoping something good comes out of this.4 Suna nan zaune ne tayi sallama ta shigo falon. MK ne ya amsa sallamar yayinda Fahad ya kafa ma yarinyar idanuwa. Bayan ta ajiye tray din ne ta duqa har qasa tace “Hamma ina wuni” Fahad yana murmushi yace “lafiya qalau..” Daga nan ta miqe ta juya ta bar falon. Aikuwa tana fita Fahad ya kalli MK yace “kai abokina… she is pretty fa, haba no wonder..” MK yana hararar shi yace “no wonder what??” Murmushi yayi yace “nothing abokina..” Ya gyara zaman shi yace “toh wai yanzu idan Maleeka ta dawo ya kenan?? ka dai san she won’t let her anywhere close to you ko??” Ajiyar zuciya MK ya saki sannan yace “I swear I dont know.. abinda dai na sani shine I want this girl close to me..” Hmmmm… **************** Da daddare bayan MK ya dawo daga sallar Isha’I ne ya nufi dinning don cin abinci. As usual gani nayi ya bubbude warmers din ya ga abinci kala-kala. Har ya zauna sai na ga ya tashi ya nufi hanyar kicin. Da alama Ummi yake nema. Gani nayi ya tsaya bakin qofa yayinda ya hango ta zaune a qasa tana cin abinci cikin natsuwa. Gyaran murya yayi wanda ya sanya ta zabura yayinda yayi murmushi yace “yi haquri na baki tsoro” Ummi dai zuciyarta ce take ta bugawa yayinda ta duqar da kanta tace “ina wuni Hamma” STORY CONTINUES BELOW Ya fara dosowa inda take ne yace “lafiya.. abinci kike ci babu tayi??” Kafin ta amsa ne ya kalli kwanon nata. Gani nayi ya zaro idanuwa sannan yace “what!!” Da sauri ya qarasa ya dauki kwanon nata yayinda yake fadin “wa ya baki wannan abincin Ummi??” Da sauri ta miqe a rude tace “Hamma ni..” Kafin ta qarasa maganar kuwa sai gani tayi ya zauna kan kujerar island ya sa hannu zai fara ci. Da sauri ta qarasa wurin shi tare da riqe hannun shi tace “Hamma kar ka ci..” Cike da mamaki yake kallonta yayinda yace “meyasa?? kin kuwa san tuwo da miyan kuka shine abincin da na fi so??? ai ko magani kika zuba a ciki sai na ci” Ummi tace “don Allah kayi haquri Hamma.. ka ga na riga na fara cin wannan kuma ma babu nama a ciki sannan…” Ji tayi yace “sssshhhh… sakar mun hannu”4 Sai a lokacin ta ankara da hannun shi da ta riqe wanda tayi saurin saki tare da matsawa baya tace “yi haquri” Yana murmushi yace “ke komai sai kin bada haquri ne? je ki dauko mun ruwa” Ummi dai ko da ta nufi wurin fridge tana kallon shi ta ga ya kai loman tuwo a bakinshi yayinda ya lumshe idanuwan shi yace “hmmmm… this tastes great” Da sauri ya waigo ya kalle ta yace “gaskiya wannan tuwon yayi dadi..” Ko da ta kawo ruwa da cup ta ajiye mishi ne ta ji yace “daga yau idan kika yi don Allah ki ajiye mun kin ji??” Muryarta qasa-qasa tace “Hamma ai Adda bata so…” Shi kam bai bi ta kanta ba ta ga ya cigaba da kwasar tuwon. aikuwa nan da nan ya cinye shi yayinda ya dago kai yana kallonta yace “akwai saura??” Ta girgiza kai alamar a’a. Bayan ya sha ruwa ne yace “meyasa babu nama??” Kanta a duqe tace “Hamma ni bana son nama sossai ne..” Cike da mamaki yace “meyasa?? Adda ta hana ki ci ne ko me??” Ta girgiza kai alamar a’a sannan tace “ni kawai na fi son kifi ne..” Gani tayi ya tashi sannan yace “kar ki manta da Cappuccino dina anjima” Bayan ya fita ne Ummi ta saki ajiyar zuciya tare da dafe qirjinta. Sossai halin MK yake bata mamaki. Mamaki take yi yadda baya qyamarta a matsayinta na ‘yar aiki.. a kullum qara birge ta yake yi sannan qara shiga ranta yake yi. Ita kam Allah ya sani tunda ta fado duniya banda iyayenta da Goggon ta bata taba samun wanda yake kyautata mata ba kamar shi. A yadda take jin shi zata iya sadaukar mishi da komai nata… toh amma me take da shi da zata sadaukar mishi??8 Nothing I guess!!! ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ DORCHESTER HOTEL LONDON-ENGLAND Zaune take a kan daya daga cikin Sofas na lounge din dakin. Maleeka dai kusan awa daya kenan da ta dawo daga wurin fashion show din da aka yi. Wayarta ce a hannunta yayinda take karanta messages din da yake aiko mata. Gani nayi ta bude wani kamar haka: “Babe please answer my call ko sau daya ne.. I need to talk to you. kar ki bari abinda ya faru yayi affecting auren mu.. just come back and I promise you zamu warware komai… I love you” Gani nayi ta jefar da wayar yayinda ta fashe da kuka. Jameela wadda take karatu ce ta ajiye littafinta tace “lafiya Leek?” Cikin kuka tace “meyasa abubuwa suka zama mun haka?? I swear I love him but..” Jameela tayi tsaki tace “but girman kanki na bala’i ya hana ki sauko ki bashi haquri ku cigaba da zaman auren ku. A dalilinki fa har accident yayi kuma kin sani amma ko kiran shi bakiyi ba balle ki ji ya jikin shi… I swear Leek kina da babbar matsala. Ni kam ki daina yi mun kuka ki bar ni inyi karatu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *