UMMI CHAPTER 6
MK-TECH SOFTWARE COMPANY A yau thursday MK ya koma ofis. Zaune suke a conference room yayinda ake ta review na 3rd quarter of the year. Fahad ne yayi presentation na summary din komai da komai. A yadda kamfanin yake tafiya an samu growth na 18% compared to last year wanda kuwa a yanzu haka saura 3 months shekarar ta qare. Wannan ya nuna cewar zasu iya achieving more before year end. Sossai Mk yayi farin cikin wannan al’amarin sannan yayi ma heads na different units din kamfanin godiya na yadda suka jajirce akan aikinsu. A nan take yayi authorising din Head na account unit akan a ba dukkan ma’aikatan kamfanin bonus tun kafin shekarar ma ta qare. A cewar shi they deserve it kuma idan aka yi musu hakan they will work harder towards achieving more zuwa qarshen shekarar which will attract another bonus. Sossai aka yi murnar wannan al’amari. Haka aka dinga yi mishi godiya tare da yi mishi fatan alkhairi. Kyautatawa tana cikin dalilan da suka sanya MK yake da farin jini a rayuwar shi. sossai ma’aikatan shi suke jin dadin aiki da shi domin kuwa albashin su mai kyau ne sannan duk wasu allowances da compensation baya wasa wurin tabbatar da an biya su haqqin su. Afterall without their dedication and hardwork, the company wouldn’t have gotten to where it is a yanzu haka!! ************ Zaune suke a ofis din Fahad yayinda Fahad din yake fadin “gaskiya abokina kana shan addu’o’i wurin mutane… kai kam babu abinda zamu ce sai Allah ya saka maka da gidan aljannah” Murmushi yayi yace “ameen abokina” Gani nayi ya kalli agogo ya ga qarfe sha biyu ta wuce. Da sauri na ga ya dauki wayar shi sannan yace “subhanalillah.. I was supposed to call her and I forgot..” Fahad ya gane wa yake nufi amma don neman tsokana yace “who?? your babe??” Yana dialling layinta ne yace “no my friend.. Ummi” Fahad yayi murmushi tare da girgiza kai ya mayar da idanuwan shi bisa laptop dinshi.. a ranshi yace “look at this guy.. he has a thing for the girl amma kuma yana denying.. zamu ga for how long MK” A kira na biyu ne ta amsa wayar cikin sallama kamar kullum. Yana amsa sallamar kuwa ya ji tace “Hamma ina ka shiga ne yau?? na hada maka Cappuccino dinka amma ban gan ka ba??” A yadda ta kira Cappuccino din zaka rantse dama can ta iya ba wai koya tayi ba just yesterday… Abinda yake qara birge shi yadda take daukar abu a kanta da sauri. wani lokaci yakan yi tunani ma kamar ta iya turanci and she is only pretending ne.3 is she???🤔🤔🤔🤔… I guess not!!! Yana murmushi yace “hey relax.. lafiya na qalau. Na koma office ne kuma na manta ban gaya miki ba… ina azumi..” Shiru tayi bata ce komai ba yayinda ya cigaba da fadin “…ke kin ci abinci??” Tace “a’a, nima azumi nake yi” Da sauri yace “haba??? yaushe da yaushe kike yi??” tace “litinin da alhamis ne nake yi Hamma..” STORY CONTINUES BELOW Lumshe idanuwa yayi sannan yace “da kyau Ummi.. toh me zakiyi mana na bude baki?? tuwo??” Cike da mamaki tace “Hamma ya za’ayi ka kai azumi ka ci tuwo..” Fahad dai gani yayi ya fashe da dariya sannan yace “toh meye?? ni dai ki ajiye mun duk abinda zaki ci” Tace “toh ai masu dafa maka abinci zasu yi maka…” Kai tsaye yace “naki zan ci Ummi..” A sanyaye tace “toh Hamma” Yace “kar kiyi aiki dayawa yau.. ki kwanta ki huta tunda azumi kike yi kin ji??” Tace “nagode Hamma” Bayan sunyi sallama ya kashe wayar ne Fahad ya dago kai yana kallon shi yace “MK ka tabbatar ba son…” Da sauri yace “shut up…” yayinda ya miqe zai fita daga ofis din. Fahad yana dariya yace “nayi shiru abokina..” Har ya kai qofa ne sai kuma ya dawo yace “na manta please ka sa a kai kifi gida na..” Cike da mamaki Fahad yace “kifi?? as in Fish? me ya hada ka da kifi abokina??…” Kai tsaye yace “Ummi ce take so… don Allah ka sa a kai mata.. “2 Haka MK ya juya ya bar ofis din yayinda ya bar Fahad sake da baki yana mamaki.1 Ji nayi Fahad yace “who would have thought so… Alhamdulillah Allah nagode maka. Allah ya bayyanar da soyayya a tsakanin ku abokina”5 Hahahaha… Fahad dan adawar Maleeka!! ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Zaune yake a dinning yayinda take tsaye tana zuba mishi fruit salad din da tayi. Ummi dai bata taba yin fruit salad ba, asali ma a wurin chefs ta koya. Bayan ta zuba mishi ne ta tsaya yayinda ta sa mishi idanuwa tana jira ya sha ya ji idan yayi dadi. Sossai ta damu da ta ji comment din shi. MK dai bai jira komai ba ya kai cokalin fruit salad din bakin shi yayinda yayi saurin dago kai ya kalle ta. Gani tayi ya ajiye cokalin sannan yayi resting bayan shi a kujera. Ummi wadda ta damu a yanzu tana kallon shi tace “Hamma bai yi dadi ba ko?? don Allah kayi haquri dama fa ban taba yi ba sai yau… ina gani kamar ban ga yadda suke yi ba da kyau” Daga nan ya ga ta sa hannu zata fara kwashe bowl din yayinda yayi saurin riqe hannun nata yace “hey.. meye haka??” Cikin muryar kuka tace “zan tattara ne..” Yace “saboda me??”3 Ture hannunta yayi yace “kin ji nace bai yi dadi bane??” Tana share hawayen fuskarta ne tace “toh na ga ka ajiye cokalin ne Hamma” Fashewa yayi da dariya yayinda yace “toh meye abin kuka idan na ajiye??” Dago kai tayi ta kalle shi sannan tace “Hamma wallahi bana so inyi maka abu ba daidai bane..” Ya girgiza kai yayinda yace “interesting…” Ya nuna bowl din fruit salad din yace “yayi dadi sossai Ummi.. ban taba shan mai dadin wannan ba” Gani yayi ta zaro idanuwa yayinda tace “dagaske Hamma??” Yana murmushi yace “zuba naki kema ki zauna muyi bude bakin tare..” Matsawa baya ta dan yi tace “a’a Hamma.. zan sha nawa a kicin” Hararar ta yayi yace “ni kuma nace a nan zaki sha” STORY CONTINUES BELOW Daga nan ya janyo bowl ya zuba mata fruit salad ya tura gabanta yayinda yace “oya janyo kujera ki zauna” Gani yayi ta dauki bowl din sannan ta koma gefe a qasa ta zauna. A ranshi ne yace “tunda dai kin zauna kusa da ni ai shikenan”2 Daga haka kuwa basu qara yin magana ba. Ita dai Ummi tana ta shan nata tana kallon shi yayinda yake shan nashi cikin natsuwa da birgewa. Ko da ya shanye nashi gani tayi ya janyo bowl din gaba daya sannan ya juyo yace “idan zaki qara ki zo ki qara don shanyewa zanyi” Murmushi tayi tace “ya ishe ni Hamma… ka shanye” Ita dai sossai ta cika da farin ciki yadda ta ga MK ya shanye fruit salad din da tayi. Gani tayi ya tashi yayinda yace “bari in tafi masallaci.. an kusa kiran sallan Isha’I. idan na dawo sai a bani tuwo na” Murmushi tayi tace “toh Hamma sai ka dawo” Shima yana murmushi ya fita daga dinning din. ************* MK bai shigo gidan ba sai wuraren qarfe tara saura. Ya tsaya sauraron wa’azi ne a masallaci kamar kullum. A lokacin da ya dawo kuwa tana nan zaune a qasan dinning din tana jiran shi. Ji tayi yace “kin dai yi sallah ko??” Murmushi tayi tace “nayi Hamma” Ya girgiza kai yace “good girl” Miqewa tayi ta zuba mishi tuwo sannan ta sa mishi miya. Gani yayi ta bude wani pepper soup na naman kaza zata zuba mishi. Da sauri yace “ina kifin?? ko ba’a kawo miki bane??” Tace “an kawo..” Yace “toh meyasa bakiyi amfani da shi ba??” Kai tsaye tace “nayi amfani da shi..” Ya nuna pepper soup na kazar da take gaban shi yace “toh ni shine zaki bani wannan? bazaki bani kifin ba??” Da sauri tace “yi haquri Hamma, ban san kana ci ba ai. bari in kawo maka” Ko da ta tafi kicin ji nayi yace “tabbas bana ci amma dai yau zan ci.. we have so much in common Ummi, why not this too??”5 hmmmm… Ko da ta dawo ta zuba mishi peppersoup na cat fish itama ta zuba nata abincin sannan ta koma qasa ta zauna. MK dai tuwon ya fara ci.. tunda kuwa ya fara ci baiyi magana ba har sai da ya kwashe shi tas sannan ya juyo ya kalle ta yace “kin iya girki Ummi.. Allah yayi miki albarka” Murmushi tayi tace “ameen” Dago kai tayi ta ga ya janyo plate din peppersoup na kifin yayinda ya fara qoqarin ci. A yadda yake shirin sakawa bakin shi kuwa zaka tabbatar baqo ne wurin cin kifi. Gani nayi Ummi ta tashi da sauri ta nufi wurinshi tace “Hamma tsaya…” Cike da mamaki yace “saboda me??” Tace “baka cire qaya ba ai.. zai iya ji maka ciwo a baki” Kai tsaye yace “toh ki cire mun” Ummi dai shiru ta dan yi sannan tace “Hamma ya za’a yi in sa maka da hannu na..” Kafin ta qarasa yace “sssssshhhhh… cire mun ni dai” Haka ta sa hannu ta dinga zare mishi qayar shi kuma yana ci kamar dai yadda ake yi ma yara. Ummi dai tana ta mamakin yadda MK baya nuna mata qyama. Sossai MK ya ji dadin kifin don kuwa ya ci shi dayawa. Bayan ya gama ci ne yace “nagode Ummi, you are a great cook” STORY CONTINUES BELOW Tashi yayi ya cigaba da fadin “…yau kin cika mun ciki dayawa.. na tabbatar idan kullum ina cin abinci haka zan zama qato” Gani yayi ta fashe dariya yayinda yayi murmushi. Yana shirin barin dinning din ne yace “ina jiran Cappuccino dina” Tace “toh Hamma” ♧♧♧♧♧♧♧♧ Wani ikon Allah cikin qanqanin lokacin nan MK da Ummi suka saba da juna sossai. sun shaqu in such a way that they understand eachother better than anyone. Ba sai sunyi ma juna magana ba sannan suke communicating.. they feel and understand eachother even without talking. it’s like they share thesame mind, heart and soul.4 A yanzu dai Ummi itace mai dafa ma MK abinci.. duk abinda ta ci shima shi yake ci. Tuni ya hana chefs din gidan dafa mishi abinci. Ummi dai tana dafa mishi abinci irin su faten doya, jollof na shinkafa da wake mai man-ja, Alale, koko da qosai, masa da kuma tuwo kala-kala kuma sossai yake jin dadin su. Shi kam bai san akwai abinci (local dishes) kala-kala irin wadannan ba sai yanzu domin kuwa tunda ya taso a gida kullum continental dishes ake dafawa… wasu abubuwan ma duk ya rasa ko meye su. Tuni ya zama maciyin Kifi. A kullum ita take tsayawa tana cire mishi qaya yana ci kamar wani qaramin yaro. Tare suke cin abincin wanda shi yana kan table ita tana qasa. A kowanne safiya kuwa kafin ya tafi office sai ya ganta ya ji yadda ta kwana.. idan kuwa bai samu ganinta ba toh zai kira ta a waya. Har video call yake kiranta wanda suke shan hira. Lokutta da dama Fahad yana shiga ofis dinshi ya tarar da shi yana aiki yana hira da ita through video call. A irin wannan lokuttan kuwa zaka gan shi looking so happy. Fahad yakan yi mamakin hakan amma sai yayi shiru tunda dai yace he sees her only as a sister. A duk lokacin da basu ga juna ba kuwa ji suke yi kamar sunyi missing wani abu mai muhimmanci a rayuwar su. A kullum idan har Ya dawo zai kirata ta zo ta zauna tare da shi a falon shi. Lokutta da dama ma ba hira suke yi ba amma haka kawai yana so tana zama kusa da shi. Asali rashin maganan su ta fi maganan su yawa.. they feel so much connected. Matsala daya take da shi idan ya kirata ta zauna a falon. Wrestling din da yake kallo… ita dai Allah ya sani bata so ta ga ana dukan mutane anyhow… sossai hankalinta yake tashi. Ta rasa me ya hada shi da kallon kokuwa. Aikuwa a kullum idan yana kallon wrestling din juya ma TV baya take yi tayi ta buga game dinta a waya. Wasu lokutta kuwa sa ta yake ta zauna tayi ta yi mishi karatun Al-qur’ani yayinda yake zama yana sauraron muryar ta mai dadi. Haka idan yana aiki a study tare suke zama. Yana aikin shi ita kuma tana zaune a qasa tana buga game a wayarta. Idan har MK ya ji Ummi tayi shiru tana latsa wayarta toh fa ‘naughty bear game’ take bugawa. Bala’in son game din takeyi wanda shi ya koya mata. MK da Ummi feel secured and protected around each other. Sun dauki junan su a matsayin guardian Angel’s din junan su.1 Duk wani abu da MK yasan Ummi tana so sai ya sa an kawo mata. He pays attention to duk wani abu da take so da wanda bata so no matter how small or insignificant. Misali tunda ya kula tana son Ice-cream da grapes toh fa kullum sai ya sa an kawo mata. Freezer din gidan cike take da Ice- cream haka Grapes kamar na siyarwa. Ummi ta sha fadi mishi cewar akwai dayawa da bata sha ba amma kamar wanda yake mantawa sai dai kawai ta ga an kawo mata wasu. Wrestling din ma da bata so ya sani sarai. A kullum burin su bai wuce su faranta ma junan su ba. idan har dayan su yana cikin farin ciki toh hankalin dayan a kwance yake. Their happiness surely lies in eachother’s happiness. Tuni MK ya fita batun Maleeka, damuwar da ta sanya shi ya warware. Yawan kiranta da yake yi a waya ya ragu sannan text messages din ma da yake aika mata ya bari.4 Fahad dai ya fi kowa jin dadin wannan sauyin da abokin nashi yayi. A kullum dai addu’ar shi bata wuce na abokin nashi yayi ending up da Ummi ba.3 Shin hakan abu ne mai yiwuwa???4 ♧♧♧♧♧♧♧♧ Hmmm… Babu tantama Ummi holds a special place a zuciyar MK…. Shin dagaske a matsayin qanwa yake kallonta ko kuwa dai he doesnt want to admit cewar yana sonta ne??8 What is so special about Ummi??? She is just a Maid.. Meyasa a handsome, rich and sophisticated guy kamar MK yake bata so much attention??3 Soyayya ce?? tausayi ne?? what??? MK-TECH SOFTWARE COMPANY Zaune suke a office dinshi suna reviewing wani report a macbook dinshi tare da Nayla da Fahad. Bayan sun kammala ne na ji yace “okay Nayla.. please finish up BCOB” Tace “okay sir..” Ya zare hard drive din da yake jikin Macbook din nashi ya miqa mata. Nayla ta karba tace “excuse me” Fahad yayi murmushi yace “go ahead Nayla” Bayan ta fita ne suka fara hira. A cikin hirar ne MK yace “abokina na manta ban tambaye ka ba… ya jikin Fatima??” Fahad yace “Alhamdulillah… jiya da muka je asibiti likitan yace da zarar ta fita daga first trimester dinta wahala zata ragu” MK yace “Allah ya sauke ta lafiya… I am happy for you. atleast you are expecting.. yanzu look at me.. matar tawa ma ta gudu” Fahad wanda ya tausaya ma abokin nashi ne yace “amma abokina ka tabbata bazaka sanar da iyayen ku ba?? it’s already two weeks fa.. me take nufi?? a wane matsayi ta dauki auren naku?” Yace “the problem is I can’t tell them.. bana so inyi sanadiyyar sanya tension a tsakanin families din mu..” Ya girgiza kai ya cigaba da fadin “…ka san abinda ya fi bani mamaki? wai a bakin su Mamy nake jin halin da take ciki and she keeps telling them munyi waya blah blah blah..” Fahad ya girgiza kai yace “Allah ya kyauta.. things will fall into place insha Allah. Ban tambaye ka ba.. Ya Ummin ka?? hope she is good?” Gani nayi ya dauko wayar shi da sauri yace “wallahi abokina ban sani ba… na fito ban gan ta ba kuma fa na kira wayarta bata amsa ba… I thought maybe bacci take yi tunda yau monday..” Haka ya dinga kiran layinta amma babu response. Ji nayi yace “no response abokina.. do you think she is fine??” Fahad yace “eh toh tunda dai you are less busy yanzu kuma meeting dinmu is in an hour’s time why dont you go and check on her..” MK ya miqe tare da fadin “haka za’a yi.. bari in duba ta in dawo” Fahad yana kallon shi ya fita yayinda yayi murmushi yace “Oh my friend.. what could this be???”2 ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO MK ne ya shigo gidan yayinda ya fara zagayen neman inda zai ganta. A yadda ya tarar da gidan ya tabbatar Ummi bata yi aiki ba yau dukda ba wai datti gidan yayi ba amma akwai abubuwan that are not in their rightful places. Gaba daya ya zagaye inda yake sa ran zai ganta amma bai ganta ba. Asali dai MK bai san ina take kwana ba a gidan… bai taba sanin inda dakin Ummi yake ba. Tsaye yake a main falon gidan yayinda yake cike da damuwa. Ji nayi yana fadin “Ummi where are you?? where are…” Kafin ya qarasa maganar shi ne na ga ya shafa kanshi tare da fadin “ofcourse… the CCTV cams..” Gani nayi ya wuce sashen shi ya shiga study dinshi ya zauna ya kunna wani screen ya dinga bin cameras din da ke gidan don ganin movements din yarinyar a ‘yan kwanakin. Asalin gidan MK akwai CCTV cameras a ko ina amma banda bedrooms din gidan. MK dai yana ta kallo yayinda ya ga most times takan fito daga sashen visitors sannan da dare ma nan take shiga… meaning that is where she stays!! STORY CONTINUES BELOW Da sauri ya tashi ya fita yayinda ya nufi visitors side din. Haka ya dinga bin ko ina yana neman ta har Allah ya sa ya iso dakinta. Da farko dai qwanqwaso qofar yayi amma ya ji shiru. Ko da ya natsu ya dan saurara sai ya ji kamar tana kuka. Da sauri ya murda qofar dakin ya shiga ne na ga yayi freezing a tsaye. Kwance take a a qasa cikin hijabinta yayinda idanuwanta suke a rufe. Dafe take da cikinta yayinda take ta juyi.. ga hawaye da ke ta gangarowa daga idanuwanta. Da sauri ya qarasa wurinta hankali a tashe ya tsugunna a gaban ta yace “Ummi me ya same ki??” Da qyar ta bude idanuwanta wadanda suka yi Ja yayinda ta kasa magana. Sossai hankalin MK ya tashi da ganin yanayin ta. Ji nayi yace “tashi mu je asibiti..” Muryarta qasa-qasa tace “a’a Hamma… cikina ne kuma zai daina” Bai tsaya sauraronta bane na ga ya fiddo wayar shi ya kira Dr. Davis. Bai jira sun gaisa bane yace “Dr please can you send your gynecologist to my house?? it’s an emergency” Shiru ya dan yi sannan yace “okay thank you” Bayan ya kashe wayar ya kalle ta yace “sannu.. tun yaushe kika fara jin ciwon??” Idanuwanta a rufe tace “tun da safe ne Hamma.. ka koma wurin aikin ka zan samu sauqi zuwa anjima” MK wanda yake cikin tsananin damuwa a ranshi yace “ya za’a yi in koma office kina cikin wannan halin Ummi.. I will never be okay if you are not”5 hmmm… Da qyar ya lallabata ta tashi ta koma kan gado yayinda ya zauna a kan stool na Vanity mirror yana ta kallon ta tana ta juyi. MK yana kallon Ummi tana fama da ciwo amma babu abinda zai iya yi mata. How he wish he can take the pain away.. Yana nan zaune cike da damuwa ne aka kira shi a waya aka sanar da shi isowar likitar. Da sauri ya miqe ya fita ya shigo da Dr. Zeenat. Bayan Dr. Zeenat ta ajiye kayan aikinta ne ta fara examining dinta. MK yana ta kai da komowa a tsakar dakin yayinda hankalin shi yake a tashe. Ko da Dr. Zeenat ta fara yi ma Ummi tambayoyi Ummin dai ta so ace MK ya fita don ta samu privacy wurin responding. sossai kunya take ji ta fadi ainihin dalilin da yasa take fama da ciwon cikin a gaban shi. Muryarta qasa-qasa ta dinga amsa likitar ta yadda ta tabbatar MK bai ji ba. Ita dai Dr. Zeenat daga ‘yan tambayoyin da tayi ma Ummi ne ta gane cewar ba wani abu bane illa menstrual cramps wanda da alama yana ba yarinyar wahala kamar yadda yake ba wasu matan. Gani nayi ta miqe ta nufi wurin MK. Ummi dai bata ankara ba ta ji likitar ta fara yi mishi bayanin abinda yake faruwa. Hakan kuwa ba qaramin haushi ya bata ba. hahaha… Sossai kunya ta baibaye ta yayinda ta juya musu baya tare da runtse idanuwanta.. Ga cikinta da yake ta ciwo. Tana sauraron su ne ta ji MK yace “toh yanzu ya za’a yi… babu abinda za’a iya yi mata ta rage jin zafin??” Dr. Zeenat tayi murmushi tace “eh toh idan ta samu massage a lower abdomen it helps reduce the cramps gaskiya…” MK ya dan zaro idanuwa yayinda likitar ta cigaba da fadin “…alternatively, idan ta sha ruwan lipton ma it helps..” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “well I think the alternative is okay” STORY CONTINUES BELOW Tana murmushi ta nufi jakarta ta bude sannan ta fiddo wani pain reliever tace “zata iya shan wannan ma.. it will help alot” MK yace “thank you doctor.. but I have a question” tace “go ahead sir” Yace “yanzu whenever it’s coming haka zata dinga fama da wannan ciwon? babu wani abinda za’a iya yi da zai hana ciwon cikin kwata-kwata??” Ummi wadda take sauraron su dai ji tayi kamar ta bace daga dakin. A ranta ne tace “subhanalillah.. ta ya zan kalli Hamma bayan wannan abin da yake faruwa??” Ji tayi likitar tace “well most women get relief after marriage.. frequent release of sex orgasms relieve menstrual cramps faster tunda ka san menstrual cramps are a result of her uterus contracting to release its lining… when she has an orgasm, the muscles of her uterus also contract and then they release. That release should bring some relief from period cramps…” Gani nayi MK ya shafa kanshi tare da fadin “uhum.. I will have to come for that lecture nan gaba doctor.. I think the alternative solution should be adopted yanzu” Ita dai Ummi bata san me suke fadi ba sai ji tayi suna dariya. A ranta ne tace “na shiga uku gashi har dariya suke yi mun”3 MK dai tare da likitar suka fita daga dakin suna ta magana yayinda Ummi ta dinga Addu’a Allah yasa kar ya dawo. Bayan kamar minti goma ne ta ji qarar bude qofa yayinda ta jiyo motsin shi. Ya shigo riqe da tea cup a hannun shi. Qarasowa yayi ya zauna kan Vanity stool yayinda yace “Ummi tashi ki sha lipton din..” Shiru tayi ba tare da tace komai ba. MK dai ya gane dalilin da ya sanya ta qi juyowa.. ya sani sarai kunya take ji. Murmushi yayi yace “toh wai kunya kike ji ne saboda na san abinda ke damun ki?? toh meye?” Muryar ta qasa-qasa tace “don Allah Hamma ka tafi ka..” Katse ta yayi tare da fadin “ai idan kin ga na bar dakin nan toh kin shanye ruwan lipton dinnan sannan kin sha magani don haka kawai ki tashi..” A hankali ta tashi zaune yayinda kanta yake duqe ta miqa hannunta alamar ya bata. Shi kam hakan sossai ya bashi dariya. Bayan ya miqa mata ne ta fara sha yayinda ya sa mata idanuwa. Shi kam Allah ya sani duk abinda Ummi tayi birge shi take yi. Wayar shi ce tayi ringing ya duba. Sunan Fahad ya gani yayinda yayi answering call din. Yana kallon fuskarta yace “yeah abokina na ganta… she is actually not feeling fine ne but it’s nothing serious. zaku iya fara meeting din without me.. I will join you shortly” Bayan ya kashe ba tare da ta kalle shi ba ne tace “Hamma idan ana neman ka a wurin aiki ne ka tafi..” Ji tayi yace “sssshhhh… shanye shi” Haka har ta shanye sannan ya miqa mata maganin da ruwa ta sha. Ji tayi yace “yau babu azumi kenan..” Da sauri ta dago kai ta kalle shi yayinda ya kashe mata ido daya. Runtse idanuwanta tayi yayinda shi kuma ya fashe da dariya.1 Shi kam dama ya fadi haka ne don ya tsokane ta tunda ya san bata so. Aikuwa bai ankara ba ya ji ta fara sheshekar kuka wanda hakan ya sa shi saurin fadin “hey.. kuka kike yi? kiyi haquri.. wasa fa nake yi miki” STORY CONTINUES BELOW Ganin ta qi daina kukan ne yace “haba Babyn Hamma kiyi haquri don Allah… Hamma ba zai qara ba kin ji??”17 Da sauri ta dago kai ta kalle shi yayinda ta ga yayi mata fuskar tausayi. Sossai ta ji dadin sunan da ya kira ta da shi- Babyn Hamma.1 Bata ankara ba ta ji yace “Babyn Hamma ta haqura ko sai ya durqusa…” Murmushi tayi cikin shagwaba tace “don Allah ka daina Hamma…” Yana murmushi yace “okay okay na daina.. kiyi haquri kin ji?? Yanzu dai ki kwanta ki huta abinki.. kar kiyi aiki yau. idan kina buqatar wani abu ki kira ni a waya” Ya miqe tare da fadin “bari in koma office.. I will call you” Ta gane me yake nufi da yace ‘I will call you’ domin kuwa zama tare da shi ta fara jin wasu turancin da yake yi mata..2 Tana kallon shi tace “nagode Hamma.. sai ka dawo” Haka ta sa mishi ido har ya bar dakin. Gani nayi ta sauke numfashi tare da lumshe idanuwa. Ji nayi tace “Allah ma ya sani ina sonka Hamma.. kai kadai ne mai sona duk duniyan nan bayan Goggo.. Yanzu da zarar Adda ta dawo komai zai canza..”3 Ni kuwa nace tabbas… Ummi dai ta sani cewar Maleeka bata taba dadewa haka ba idan tayi tafiya… dukda tana mamakin yadda har yau bata dawo ba deep down within her bata so ta dawo din because dawowarta will keep MK faraway from her gashi kuma a yadda ta saba da shi bata so ko kadan tayi nisa da shi…!!8 toh ya kenan???? ************** Ummi dai ta samu sauqin ciwon cikinta tun bayan da ta sha ruwan lipton da magani don har wani bacci ya fizge ta wanda har MK yayi mata missed calls bata sani ba. A lokacin da ta tashi kuwa ta ji sauqi sossai. Bathroom ta shiga tayi wanka sannan ta kimtsa kanta. A lokacin da ta dauki wayarta zata fita don yin aikinta ne kiran MK ya qara shigowa a wayar. Ko da tayi answering call din muryar shi ta ji yana fadin “Babyn Hamma ta tashi daga baccin??” Cike da mamaki tace “ya akayi ka san nayi bacci??” Yana murmushi yace “na ji a jikina ne Ummi.. ya cikin ya daina ciwo??” Cike da kunya tace “ya daina..” Yace “toh masha Allah… me kike so in sa a kawo miki??” Tace “babu komai…” Yace “toh idan kina son wani abu ki kira ki sanar da ni kin ji” Tace “toh Hamma nagode” Ji nayi yace “ina zuwa…” Kafin tayi magana kuwa sai ta ji ya kashe. Call dinshi ya sake shigowa amma wannan karon da ta duba sai ta ga Video call ne. Tana murmushi tayi answering yayinda ta gan shi zaune a ofis dinshi.. Yana kallon ta ne yace “ina zaki je?? ba nace ki kwanta ki huta ba?? hope ba aiki zaki je yi ba??” Ummi wadda ta wayance ce tace “dama ruwa na je na sha… zan koma daki ne” Ya girgiza kai yace “okay” A haka babu shiri ta koma dakinta ta zauna a kan gado suka cigaba da hira. Suna hira yayinda yake ta aikin shi. Har Fahad ya shigo ofis din ya tarar da shi yana waya da yarinyar. Girgiza kai kawai yayi yana murmushi. Shi kam a halin yanzu ya gama tabbatar da cewar MK is in love with the girl.. he just doesn’t want to admit ne!! Really???3 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ DORCHESTER HOTEL LONDON-ENGLAND Tsaye take a jikin window na suite din dakin yayinda tayi zurfi a tunani. A yau kwanan ta Goma sha bakwai a England, kwanan ta Goma sha takwas rabon da ta gan shi. Kwana takwas rabon da ta ga missed call dinshi balle text message. Tun wannan abun baya damunta har ta fara shiga damuwa. Ga qawarta Jameela ta fita batun ta tunda dai tayi iyakar qoqarinta wurin bata shawara amma ta qi ji.. A yanzu haka tayi tafiyarta school. Maleeka dai a yau kwana goma kenan da suka gama event din da ya kawo ta qasar. A tunaninta MK zai biyo ta idan ya ji ta shiru amma a yanzu ta tabbatar ba zuwa zaiyi ba.. toh meyasa??? Ya daina sonta ne??8 Ji nayi tace “na shiga uku… me ke faruwa da ni ne? Anya bazan tattara in koma gida ba kuwa??”11 Wayarta ce tayi ringing. da ta duba kuwa kira ne daga Production team dinta na qasar America. Ko da ta amsa ji nayi tace “what is it Henry??” Can kuma tace “do I really have to be there?” Gani nayi ta runtse idanuwanta ta bude sannan tace “okay Henry… tomorrow. bye”9 Ajiyar zuciya ta saki sannan ta nufi closet ta fara hada kayanta. Ji nayi tace “I am going back home after this…”4 A yau kwana biyu kenan da MK yake wani important aiki wanda yake ta draining energy dinshi.. Asali dai wani program ne yake ta qoqarin debugging.. wannan program din dai ana ta qoqarin yin amfani da shi amma it keeps giving incorrect and unexpected result. Gashi program din is very important to the company, saboda wannan problem din operations na company din yayi slowing down. A yanzu haka qoqari yake yi idan yayi debugging zaiyi modifying software din gaba daya to avoid future occurrences.5 Tunda ya fara aikin nan baya hutawa. Dare da rana cikin aiki yake. Idan ya dawo daga office shigewa yake yi study dinshi ya duqufa. *************** MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO A yau dai kamar kullum Ummi tana zaune a qasa tana buga game dinta yayinda yake ta aikin shi. Tana yi tana kallon shi, ta kula da yadda yake cikin damuwa.. da alama he is finding what he is doing very difficult. Gani nayi ta miqe ta fita daga study din wanda kuma bayan dan lokaci sai gata ta dawo riqe da tray mai dauke da tea cup na Cappuccino. Bayan ta ajiye a kan table din da yake aiki ne ya dago kai ya kalle ta yayinda yayi murmushi yace “thanks Babyn Hamma..” Murmushi tayi sannan tace “Hamma yau dai kayi sauri ka gama aikin don ka kwanta da wuri.. yawan aikin fa zai iya janyo maka rashin lafiya” Ya dan yi sipping Cappuccino din ya ajiye cup din sannan yace “toh ai na kasa gamawa ne Ummi..” Bata rai tayi tana kallon Macbook dinshi tace “da na iya da na taya ka Hamma amma insha Allah zaka gama yanzu nan” Yana murmushi yace “nagode Ummi na..”3 Ya kalli agogo yace “kin ga qarfe daya saura yanzu.. je kiyi bacci” Girgiza kai tayi alamar a’a sannan tace “bana jin bacci Hamma” Shi kam ya sani sarai qarya take yi. Ya sani saboda shi ne ta qi tafiya.. shi kanshi baya so ta tafi domin Allah ma ya sani idan ya daga kai ya ganta a kusa da shi zuciyar shi sanyi take yi. Zaman Ummi kusa da shi a kwanakin nan biyu yayi mishi amfani mentally and emotionally. Haka kawai ya ji zaman ta tare da shi yana bashi motivation sossai. Haka Ummi ta cigaba da zama. A yanzu dai ta daina buga game din yayinda ta sa mishi idanuwa cike da damuwa.. Ta sani sarai he is exhausted amma da alama bazai bar abinda yake yi ba har sai yayi succeeding. Haka kawai ta samu kanta da yi mishi addu’a akan Allah ya bashi sa’a ya gama ya huta. MK dai wasa wasa bai gano kan software dinnan ba sai wuraren qarfe uku da rabi na dare. Ummi wadda take zaune tana kallon shi sai gani tayi yayi thumbs up tare da fadin “yes… finally” Da sauri ta miqe ta nufi wurin shi tace “Hamma me ya faru?” Dago idanuwan shi yayi wadanda suka yi Ja yace “na gama Ummi” Cike da tsananin farin ciki tace “Alhamdulillah.. Allah nagode maka” A yadda ta cika da murna zaka rantse ta san muhimmancin aikin. Bai ankara ba ya ji tace “toh tashi ka je ka kwanta kayi bacci…” Murmushi yayi kawai ya miqe dukda kuwa ya so yayi modifying software din.. but he just cant refuse her sannan atleast ko ba don shi ba, ko don ita dole ya je ya kwanta domin kuwa yasan itama ta gaji. sitting down idly ba qaramin aiki bane. STORY CONTINUES BELOW Tare suka fita daga study din. Har qofar dakinta ya raka ta sannan ya dawo dakin shi. ***************** Ko da gari ya waye Ummi dai sai qarfe goma sha daya na safe ta farka. Bayan tayi wanka ta kimtsa kanta ta fito ne na ga ta dauki wayarta tayi dialing layin MK. A kira na uku ne ya amsa. Ji tayi yace “hey Babyn Hamma kin tashi daga baccin??” Kai tsaye tace “Hamma kana ina?” Yace “office…” Zaro idanuwa tayi tace “meyasa Hamma?? meyasa zaka je wurin aiki bayan kasan cewar baka samu isashen bacci ba jiya?…” A yadda take magana kuwa zaka rantse wata mahaifiyar shi ce take yi mishi fada..1 Kallon Fahad yayi wanda suke zaune a office dinshi tare suna applying software din da suka yi modifying wanda shi MK din yayi debugging jiya. Dayake wayar a hands free take sossai Fahad yayi mamakin jin yadda yarinyar take yi mishi masifa. Ji sukayi tace “…Yanzu fisabilillah bazaka taba samun lokacin kanka ka huta ba? kullum sai kayi ta aiki baka damuwa da lafiyarka? ka san cewar rashin isashen bacci yana kawo rashin lafiya ko Hamma? yanzu idan kayi ciwo…” Ji tayi yace “sssssshhhhh… Ummi stop” Sai a wannan lokacin ne ta ankara da masifar da take ta yi mishi wanda tayi saurin fadin “yi haquri don Allah Hamma… wallahi ban san me nake fadi ba..” Ji tayi sun fashe da dariya wanda hakan ya tabbatar mata da ba shi kadai bane sannan koma waye a tare da shi ya ji abinda ta fadi. Fahad ne yace “Ummi kina so Hamma ya dawo gida ya kwanta yayi bacci ne??” Dukda bata gane ko waye ba sai tace “eh.. kace mishi ya dawo. Nasan kai ma ka ga yanayin shi ai. da ganin shi kasan yana buqatar hutu ko??” Fahad yana dariya yace “tabbas haka ne….” Ya kalli MK wanda yake kallonshi yace “toh Hamma.. Ummi tace ka koma gida” MK yana murmushi ya cire handsfree din yayinda ya kai wayar kunnen shi yace “idan na gama abinda nake yi zan dawo kin ji Babyn Hamma…” Fahad wanda yake kallon abokin nashi yana ta mamaki yayinda ya ji yace “dagaske zan dawo.. kiyi haquri kin ji?” Ya dan yi shiru yana murmushi sannan yace “toh sai na dawo… okay bye” Bayan ya kashe wayar ne ya ji Fahad yace “she cares alot about you abokina..” MK yana murmushi yace “how I wish Maleeka is just like her… I mean I never thought I would blend with someone wadda ba Maleeka ba the way I do with this girl.. I cant imagine life without her close to me..” Fahad ya girgiza kai yana murmushi yace “could it be love?” Kai tsaye MK yace “no my friend… its something else but definately not love”7 Ni kuwa nace hmmmm… ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Kwance yake a kan sofa na qaramin falon shi yayinda yake dafe da kanshi. MK dai tun da rana yake jin alamun kan shi zai matsa mishi. Dukda haka kuwa sai da suka gama resolving issue na software din sannan hankalin shi ya kwanta. Ko da suka gama gida ya wuce straight wanda kuwa ya shige dakinshi ya kwanta yayi bacci. Dayake ya sanar da Ummi cewar zaiyi bacci bata damu ba. Asali ma dadi ta ji da ya dawo zai huta. STORY CONTINUES BELOW A yanzu haka bayan ta idar da sallar Isha’I ne ta shigo falon riqe da tray na abincin shi. Dama akwai lokuttan da yakan ce mata ta kawo mishi abincin sashen shi. Ganin bata gan shi a babban falon shi bane ta wuce qaramin tunda ta san lokutta da dama can yake zaman shi. Ummi dai ko da ta hango shi kwance a kan kujera dafe da kan shi da sauri ta qarasa shiga yayinda hankalinta ya tashi. Ajiye tray din tayi ta matsa kusa da shi ta tsugunna a qasa tace “Hamma lafiya? me ya same ka??” MK wanda idanuwan shi suke a rufe muryar shi qasa-qasa yace “kaina ke ciwo” Cike da tsananin tashin hankali tace “subhanalillah… Hamma sannu. Ina wayarka?? bari in kira likita..” Da sauri yace “shiga dakina ki duba drawer na gefen gado ki dauko mun magani” Hankalinta a tashe ta miqe ta nufi dakin nashi. Ita dai Ummi bata taba shiga dakin MK ba sai yau. Ko da ta bude qofar ta shiga gani nayi ta tsaya cak yayinda take qare ma dakin kallo. Sossai dakin ya birge ta.. Mai karatu tsayawa baka labarin haduwar dakin bata lokaci ne.2 Gani nayi ta lumshe idanuwa yayinda take shaqar wani asirtaccen qamshi mai dadin gaske. Da ta ankara ne na ga ta ruga a guje ta nufi wurin bedside drawer ta bude sannan ta dauko maganin. Da sauri ta fito ta nufi wurin shi tace “ga maganin Hamma.. guda nawa zaka sha?” Yace “biyu” Nan da nan ta bare ta dauko goran ruwa tace “tashi ka sha” Dafe da kan shi ya dan tashi ya karba ya sha sannan ya koma ya kwanta. Tana nan zaune cike da damuwa yayinda ta kasa samun natsuwa. Gani nayi tana ta share hawayen fuskarta yayinda ta sa mishi idanuwa. Ummi dai sossai zuciyarta take zafi. Ji take yi kamar ta cire mishi ciwon kan ta mayar a kanta. Haka ta cigaba da zama cikin damuwa har wani dan bacci ya sace shi.. Bayan kusan awa biyu ne ta ga ya motsa tare da squeezing fuskar shi yayinda ya dafa gefe daya na kan shi yace “oouch” Da sauri Ummi ta miqe ta matsa daf da shi tace “Hamma kan ne?” MK dai kasa ma bude idanuwa yayi saboda hasken wuta da yayi mishi yawa. Gani tayi yana ta massaging gefen kanshi yayinda yayi magana amma kuma bata ji ba. Qara matsawa tayi daf da shi wanda har ya zama tsakanin kunnen ta da bakinshi bai wuce inch daya ba. Zuciyarta ce take ta bugawa, muryar ta qasa-qasa tace “me kace??” Ji tayi yace “kashe mun wuta ki je ki kwanta..” Ba tare da ta musa mishi ba ta miqe ta nufi wurin switch ta kashe wutan. MK wanda yayi tunanin Ummi ta wuce kuwa bai ankara ba ya ji hannunta bisa nashi. Ture hannun shi tayi yayinda ta fara yi mishi massage din ahankali. Gaba dayan su babu wanda yayi magana. Ji tayi kanshi yayi mugun zafi yayinda Zuciyarta take ta bugawa.. a yanzu dai damuwarta ta qaru. Bai ankara ba ya ji sheshekar kukan ta ahankali. Hankalin shi a tashe yace “Ummi kuka kike yi??” Girgiza kai tayi alamar a’a kamar yana ganinta. Ji tayi yace “ki daina kuka.. na riga na saba da wannan ciwon kan.. kawai ki dinga yi mun addu’a kin ji??” Tana share hawayenta tace “toh Hamma.. Allah ya baka lafiya” Daga nan babu wanda ya sake yin magana a cikin su. Tsawon minti talatin Ummi tana yi mishi massage yayinda yake samun sassauci. Sossai hannun yarinyar yake producing mishi magic. This is surely the best massage da ya taba samu a rayuwar shi. Wani ikon Allah kuwa addu’a ya dinga yi Allah yasa kar ta gaji ta daina domin kuwa wani irin soothing relief yake samu. A yanzu kam ya tabbatar Ummi is a reflection of him.. someone that can hold his hands and walk with him through darkness… he will forever be grateful for her kindness. MK dai tun yana samun sassauci har wani bacci mai nauyi ya kwashe shi. Ummi bata tashi ankara da yayi bacci ba sai kusan qarfe goma sha biyu. Gani nayi ta matsa daf da shi yayinda ta tofa mishi addu’a sannan ta koma gefe tana kallon shi dukda kuwa cikin duhu ne. ************* Wuraren qarfe uku ne MK ya farka. Tuni kanshi ya daina ciwo. A tunanin shi Ummi ta tafi dakinta don haka ne ya lalubo wayar shi yayi tapping screen din sannan ya kuna flashlight. Gani nayi ya zaro idanuwa yayinda ya ganta kwance a qasa dunqule cikin hijabinta tana bacci. Girgiza kai yayi sannan ya miqar da hannun shi zai tada ta sai kuma na ga ya mayar yayinda ya haska fuskarta yana kallonta. Gani nayi yayi murmushi yayinda yace “I have never in my life seen a beautiful creature like her.. why do I feel connected to her? why does our every conversation flow seamlessly?? why do I find everything she says enlightening? why do I care alot about her?? why do I feel I cant do anything without her close to me??… Ummi what the hell have you done to me???…”1 Ummi wadda ta ji muryar shi a cikin baccinta ne tayi firgigit ta tashi yayinda tayi saurin matsawa kusa da shi ta dafa kan shi tana fadin “Na shiga uku Hamma.. kan naka bai daina ciwo ba??”. Shi dai MK freezing yayi a dalilin dafa kan shi da tayi.. Da qyar ya saita murya yace “Ya daina ciwo Babyn Hamma… relax..” Zare hannunta tayi daga kanshi ta matsa baya da sauri tace “Alhamdulillah Hamma… Allah ya qara maka lafiya” Yana murmushi yace “Ameen… mu je in raka ki dakinki” Girgiza kai tayi alamar a’a sannan tace “baka da lafiya Hamma.. je ka kwanta ba sai ka raka ni ba kuma don Allah idan ka ji ba daidai ba ka kira ni a waya.. ka ji??” da kyau guardian angel din Hamma..2 Murmushi yayi yace “toh Babyn Hamma nagode…” Ummi dai qin tafiya tayi har sai da ta tabbatar yana bakin qofar dakin shi. Gani nayi ta zaro idanuwa sannan tace “Subhanalillah, Hamma baka ci abinci ba.. bari in je in dafa maka wani tunda wancan yayi sanyi” Da sauri yace “No Ummi bar shi kawai bana jin yunwa..” Tace “a’a Hamma don Allah..” Yace “hey relax.. nace bana jin yunwa. Je ki kwanta abinki kin ji” Tace “toh, bari in je in kwashe wancan din toh..” Yana kallonta ta koma ta dauki tray din abincin da ta ajiye mishi tun dazu wanda bai ci ba ta dawo tace “sai da safe Hamma..” Ta juya zata tafi ne ta ji yace “Ummi..” Da sauri ta juyo sannan tace “na’am Hamma..” Yana kallonta yace “nagode sossai” Murmushi tayi sannan ta juya yayinda ta bar shi a tsaye yana kallonta har ta fita… ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧