UNCLE NE CHAPTER 8 BY NIMCYLUV
Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya boka Saƙib yayi kafin ya daki wani ƙoƙo daga cikin ƙoƙonan dake gabansa,nan take photon Jalilerh ya bai yana tana zaune a gaban dressing mirror tana shafa lotion daga ita sai ɗan kuntun towel,
Tsora mata ido boka Saƙib da Mubarak Yahya cibo sukai ko wanne da abinda yake saƙawa a ransa,can boka Saƙib ya ƙara dukan ƙoƙon nan take photon ya ɗauke,kana ya ɗago kai ya kalli Mubarak Yahya cibo yace
“Wannan tana da muhimmanci a gareka,idan ka sameta ba governor har shugaban ƙasa sai ka zama”
Baki ya washe domin nan take ya fahimci wacce yarinya ce domin har abada bazai manta da ita ba,numfasawa yayi cikin hanzari kuma yace
“Mene muhimmanci ta a gareni?”
Miƙewa boka Saƙib yayi yace
“Ba yanzu ba sai nan gama kaɗan zan sanar dakai muhimmanci ta,da kuma abinda za’ai mata,zaka iya tafiya duk sanda na kiraka ranar zan gabatar da ƙudiri na a kanka,kada ka manta da jaririran da kuma idanuwan”
Yana faɗin haka ga shige cikin wani ɗan ma dai-dai cin ɗaki, farin ciki fal fuskarsa ya fita tunda a hanya ya sanarwar da Lamir ya kira masa p.a ɗin sa..
Da daddare Jalal ya na zaune a parlour’n sa shida Jafar yana masa bayanin abubuwan da Prince Hassan ke yaɗawa a media ya wanci duk yaɗa manufa ne da kuma tunasar da al’umma muhimmanci al’ƙawari,da kuma gaya masu irin nagartarka, ajjiye glass cup ɗin hannunsa yayi,a hankali kuma ya kalli Jafar yace
“Me kake harshashe akan wannan zaɓen?”
Wayar hannunsa Jafar yayi kafin yace
“Eh to,da alama bamu da magauta, sannan kuma ya maɗiɗi da ake dakai akan abinda ya faru yay sanyi domin yanzu ba’a maganar,abu guda mutane suke yawan surutu akai wanda nima shi yake ban mamaki da kai boddy,kuma koni ina son na san mene yasa hakan?”
Lumshe idanunsa yay kafin ya buɗe su akan Jafar,cikin ƙasa da murya kuma yace
“Mene?”
Jafar ya maida hankalinsa akan Jalal sosai kafin ya numfasa yace.
“Tayaya wanda bashi da iyali wanda bai son yadda ake mulkar iyali ba har yake tunanin mulkar dubban jama’ar gari?” Wasu ana gane adalci ne a lokacin da suke adalci a cikin iyalansu,uwa uba idan mutum ya kasance yana da zuri’a masu yawa, Jalal nima yanzu ina son nasan mene yasa aduk lokacin da akai maka maganar aure saika bauɗe? Afuwa bawai ina saka maku ido a cikin gidanku bane,amma ina kula da komai kuma ina fahimtar ka,ka girman sosai amma a yanzu ace da ba Nihila nake jira ba dana manta dayin aure,kana da dukiya,kana da ilimi,kana da kyakkyawan tsohe asali kuma nagarta,babu wata ƴar mace da zata kalleka tace bata sonka,kai ko a matan ka rasa wa zaka ɗauka, aƙwai matan da dayawa zasu kawo maka tayin soyayyar su,bama ni ba maganar da ake yanzu Aryan ma shirin yin aure yake”
hannunsa ya tura cikin sumarsa ya ɗan birkita ka ɗan kafin ya saki wani guntun murmushi yace
“ALLAH ya sanya alkairi”
Jafar ya kalli Jalal cikin serious magana yace
“Meye damuwarka?mene yasa baka son yin aure ina son sani indan har da gaske kallo aboki nagari kake min kuma wanda yake da kusanci dakai”
Miƙewa Jalal tare da nufar cikin bedroom yana tafe yace
“Ina sharing damuwata ne da iya zuciyata”
Yana faɗin hakan ya shige cikin bedroom ɗinsa.
Da ido Jafar ya bisa yana son fahimtar abinda yake zuciyar Jalal ta hanyar ƙurawa fuskarsa ido amma bai fahimci komai ba,domin fuskar bobo wasai take. Abu alamar damuwa ko guda.
Agogon hannunsa ya duba yaga 9 saura, miƙewa yayi shima ya fice daga cikin part ɗin Jalal
A main parlour ya tarar da Mama hannunta riƙe da mahaifi gefenta kuma Nihila ce tsaye itama sanye da Orange ɗin abaya tayi rollig kanta da vail ɗin abayar, Mama ta kallesa tace
“Kai Allah dai yay wadarar rashin ƙiba,ji yadda kake tafiya babu masali,ohhh ƙilan durune ko?”
Ɗan haɗe rai yayi sabida ganin Nihila tsaye yace
“Ke kuma sa’ido Mama,banda haka mene naki da rashin ƙibata dan Allah?”
Taɓe baki tayi tana gyara zaman kalbin kanta tace
“Kaga bana da lokacin surutu yanzu, ni ba asa rariya bace maza jeka kira min Jalalu ya kaini shufin”
Waje ya nema ya zauna yace
“Tab ai sai dai kiji da kanki,nidai aka gama yiwa ba’a”
Da sauri ta juya tace
“Waye yay maka ba’a kuma? a’a wlh babu ƙyau ai haramun ne,kamar wani yay maka jikin ba Ubangiji ba”
Kusan a tare Jalilerh da Aryan suka fito daga parts ɗinsu,da sauri Mama ta washe baki tace
“Yawwa takwarar Jalalu ki kiramin malamin naki”
Aryan dake tsaye yay saurin faɗin
“Malami kuma Mama?”
Ta gefen ido ta kallesa tace
“Ehmn,ba ankul naji tana faɗa ba?duk da dai ba makaranta nayi ba amma nasan ai malami ake faɗawa”
Jafar ya miƙe tsaye yana kallon Nihila kafin ya maida direction ɗinsa zuwa ga Mama yace
“Kin faɗi gsky da kikace maki makaranta ba,wanda yay yasan ma’anar ta”
Bata kulasu ta kalli Jalilerh wacce har yanzu take tsaye da riga da wando sai vail da tasa ta yane sumar kanta tace
“Maza jeki kinji yarinyar kirki,na maki alƙawarin wannan lemon na zuƙa”
Kanta a ƙasa jikinta kuma sanyaye ta nufi hanyar da zata kaita part ɗin,da hanzari kuma Aryan yace
“Mama bari na kira maki shi,ita aƙwai abinda zata”
Haɓa Mama ta riƙe tace
“Kaji kinibibi,to ba sallamammiya bace ni,maza ban waje”
Bisa dole ya matsawa Jalilerh hanya ta shige ya bita da ido yana mai jin wani raɗaɗi a ransa,musamman da yay duba da kayan data saka.
Zama Mama tayi a saman kujera ta tattauna dakakken goran data zuba a bakinta, Nihila tayi dariya tace
“Me yasa kike daka goro ne bayan ya haƙora nan a bakinki?”
Harara Mama ta watsa mata kafin tace
“Sabida ban samu haƙori ba ina uwarki, yooo inama ruwanki danine ba dai ni kikaiwa ruwan dubulan ba,kawai dai nafi jin daɗin cinsa a haka,ba kiga har ƙashi nake taunawa ba”
Nihila ba tace komai ba saboda alama da Jafar yay mata da hannu da tayi shuru
Ƙwance ta samesa ya ɗaga kansa sama yana kallon silin dake cikin bedroom ɗinsa,tunani ne fal cikin ransa akan abubuwa da suke faruwa dashi,wato bayan ahhalinsa dake ƙwalla fa ran yay aure yadda al’ummar gari,to duk mene yasa hakan ke faruwa ne? Shi kaɗai ne namiji wanda bai da aure?ko kuma mulki da yake nema yasa duk hankali mutane ya dawo kansa? Yasan da ba’ai masa wannan surutu,to inama za’ai masa tunda gaba ɗaya ba’a ƙasar yay rayuwa ba,rabin rayuwarsa a yanzu haka a Paris yayi ta sai dai kuma nan gaba,kuma yasan cewa abune mai wahala yakai adadin shekarun da yay a Paris da ransa,yasan bashi yake tsara rayuwa ba amma yana roƙan Allah ya ɗauki ransa akan ya ƙara adadin shekarun da yayi a Paris,mene a duniyar da har za kaji daɗin zama a cikinta? Aure! Aure! Aure bayan da yawan mutane ba kowa yasan darajar aure ba…,”
Daga ƙofa yaji ance
“Kayiwa aure mummunar fahimta,duk ba sanin al’adun ku na sani ba da kuma yanayin zaman aurenku,amma da yadda su Mummy ke rayuwa a nan gidan zaka fahimci ba duk aka taro aka zama ɗaya ba,ko anamu Yaren ya nuna mana yadda ake zaman aure da kuma yadda ake daraja auren kuma na tabbatar da hakan wajan Ammi na”
Lumshe idanunsa yay kafin ya sauke numfashi a hankali yace
“Me kika sani akan auren ke?”
Duk yadda zcyarta ke bugawa akan abinda yake addabar ta a ƴan lokutan nan bai yana tace
“Ban san yaya aure yake ba,sabida bana da tabbacin zanyi sa,amma yadda Ammina keyi duk da ba komai take ganewa ba nasan aure a wajan hausawa yana da daraja”
Miƙewa zaune yayi kafin ya ɗan kalleta da hannu yay mata nuni data ƙarasu ciki,hannu tasa ta danne saitin zcyarta,kafin tayi ƙarfin halin shiga ta ƙarasa inda yake zaune,a gefen ƙafarsa ta zauna saman carpet tace
“Uncle Mama tace kaje”
Zamuwa yayi daga saman bed ɗin ya ɗura kansa bisa shoulder ɗinta yace
“Meyasa ke baza kiyi auren ba tunda kin isa?”
Runtsa idanunta tayi da ƙarfi ka ta ɗan ware bakinta tace
“Tayaya wani zai ganni a halin da nake a yanzu har yayi sha’awar aure na, muna da saɓanin addini kuma babu wani na mijin da zai sha’awar aure na,koda yayi danginsa ba lalle su aminta ba,kuna Sallah,azumi,kuna sadaka kuna bada zakka kuna ziyartar ɗakin ALLAH,uwa uba wanda babu yadda dashi ba ku kun yarda dashi,kaga muna da banbanci mai yawan gaske,wazai yarda ya ajjiye guba cikin abu mai ƙyau,na sani koda na amshi musulunci wata rana zan haɗu da fushin uwa sundu,zan fuskanci zalunci wajan jama’ar birninmu, mutum biyu zasu samin garkuwa a birnin”
Ta ƙare maganar muryarta na rawa,wajan 10seconds yace
“Su waye?”
Cikin rawar murya tace
“Uncle Jabir da Ammi”
Ta ƙare maganar tana sakin kuka,a hankali yaja idanunsa ya lumshe kukan nata da yaji ya tsananta yasa ya jawo ta jikinsa tare da rungome ta ya shiga bubbuga bayan ta,shuru sukai gaba ɗaya kafin ta miƙe da sauri daga jikinsa tace.
“Uncle ina son komawa gida, Please ka mai dani kaji”
Hannunsa yasa ta tallafo haɓarta tare da cewa
“Look at me”
Kasa kallonsa tayi sai idanunta dake zubar da ƙwalla, murmushi yay dan yasan daban ba zata kallesa ba,komai nata ya sauya saɓanin da,tana da kunya hankali nutsuwa,komai nata daban yake kallonsa a yanzu, ƙasa yay da murya yace
“Why kike son haka? Ko kin mata da saurayin naki na can me jiran ki?”
Turo baki tayi tana ƙara sautin kukanta, baya yayi ya jingina da jikin bed jin tare da zuba mata shanyayyun idanunsa,
Ajjiyar zuciya Aryan ya sauke da sauri lokacin daya gama kallonsu,tunda ɗazo ya shigo da Mama tace taji shuru yaje ya duba,fita yayi daga part ɗin yana tafe yana dailing wata number kana yay kira, ɗauka akai daga can ɓangaren Lamir yace
“Lafiya kira a wannan daren?”
Aryan kamar zai sanya kuka yace
“Aƙwai matsala Daddy Lamir”
Lamir ya kalli p.a dake kusa dashi tana driving yace
“Yanzu ina hanya,amma meke faruwa ne haka?”
Aryan ya kwashe komai ya faɗawa Lamir,shuru yayi yana sauraran abinda Lamir ke faɗa masa,cike da murna yace
“Ngd sosai Daddy Lamir”
Camerar wayar ya kunna tare da komawa ɗakin
Jalal yace
“Iya jeki ƙwanta”
Kanta a ƙasa tace “me zan cewa Mama to?kasan masifa zatai min”
Ɗan haɗe rai yayi yace “kakar tawa take masifa Jaalilerhhhh”
Da sauri ta ɗaga kanta dan rabon da taji ya kira sunanta ta manta,da mamaki tace
“Uncle kasan sunana daman?” Juyawa idanunsa yayi yace “a’a”
Ta kwaɓe fuska tace “gashi ka faɗa yanzu” hankalinsa akan agogon ɗakin yace “a’a” turo baki tayi tace “Amma Mama tace sunanmu iri guda ne” ɗan waro idanunsa yay cike da mamaki yace “laaa haba!? Ni meye nawa sunan” sunkuyar da kanta tayi a cinyarsa tana dry ƙasa-ƙasa,hannu yasa ya ɗago ta yace “ohhyaaa out” turo baki tayi tare da marairai ce fuska girgiza kai kawai yayi kafin yasa hannu yaja lips ɗinta,baki ta buɗe zatai kuka yayi sauri bata light kiss a gefen lips ɗinta a dai-dai nan kuma yaga haske kamar na wuta ya bai yana a ɗakin.
Tafiya take a hankali daga ita sai wando da kuma ƴar ma dai-dai ciyar riga iya guiwa kanta sanye da hula,sosai take tafiya lokaci zuwa lokaci tana duba bayanta sabida babu wanda yasan fitowar ta,bata wani buri daya huce taje inda ake kiranta,domin tayi amana kiran alkairi ne,tunda ance mata UNCLE NE ke kiranta,dukkan abinda aka haɗa da Uncle ɗinta tasan alkairi ne,tsayawa tayi bakin wani layi inda akai mata ƙwatance dashi,tana tsaye tana rarraba idanunta,wata dalliyar mota ce ta tsaya a gefenta,baya taja kaɗan,zuge glass ɗin motar akai wani matashin mutum ne age mate ɗin Uncle ɗin ta,ya leƙo da kai waje yace
“JALILERH KO?”
Kai ta ɗaga masa alamar “eh” murmushi yayi yace “ok shigo to, Yallaɓai Jalal yace akai ki wajansa yana gidan gunarsa” cikin murna ta buɗe murfin gaban motar ta shiga reverse yayi yaja motar da gudu,sosai yake tafiya tun tana ganin abin wasa harya tsallake tunaninta sbd ganin sun fara shiga cikin daji,kallon mutumin tayi tace “a ina Uncle ɗin yake?”
Murmushi yay mata yana kara giyar motar ba tare da yace komai,sosai tsoro ya kama JALILERH,cikin tsakiyar wani daji yay parking tare da fitowa daga cikin motar, buɗe mata yay ta fito lokacin idanunta harya fara zubar da hawaye,hannunta yaja tana tirjewa tare dayin ihu amma ko kaɗan bai raga mata ba,juyawa tayi taga dajin babu alamun mutane ko guda ɗaya ga yadda dajin yake da duhun gaske,ahaka harya shigar da ita wata bukka, wani matashin saurayi ne zaune daga shi sai three gaiter ko riga babu jikinsa,sai facemask daya sanya ya rufe fuskar gaba ɗaya,kallonsa ta shiga yi tare da ƙarewa fatar jikinsa kallo,ganin hakan yasa wancan mutumin yay saurin fita tare da rufe ƙofar bukkar,tana tsaye sai ihu take har muryarta bata fita sbd kuka, mutumin ya miƙe tare da ɗaukan wata igiya ya nufi inda take tsaye,yana zuwa ya fincikota ta faɗa saman tabarmar kabar bukkar bai tsaya jiran komai ba ya ɗaureta da igiyar hannu da ƙafa yadda ko mutsi ba zata iya ba, idanunta ta rufe sabida sam ba zata iya kallon abinda yake ba tana a ƙwancen taji ya faɗa kanta tare da tura kansa..,wata razananniyar ƙara ta fasa tare da kiran sunan UNCLE….!!
Kai tsaye kujera dake can gefe da ita ya zauna tare da juya mata baya,a hankali yaja idanunsa ya rufe tare da fesar da iska mai zafi daga cikin bakinsa,sai lokacin kallon da Nusaibat dake masa ya faɗo masa, ɗan ƙaramin tsaki yaja haka nan yaji yarinyar bata ƙwanta masa ba,bata iya ɓoye abinda ke ranta tana abu tamkar wata zautacciya,yasan cewa rayuwa mai sauƙi ce kowa yana da ƴan cin yin abinda yaga dama,amma shi mene yasa bashi da wannan ƴan cin,mene yasa komai yake zuwar masa a baibai ba kamar yadda yake tunani ba,ji yake inama bai nemi wannan kujerar ba,inama bai tsaya takarar governor na ba,da duk hakan bai faro ba,da yanzu jama’a basu saka masa ido ba,yanzu haka dukkan abinda yay idanun jama’a na kansa wani abin kafin yay an samu wani ya fitar dashi,tayaya hakan ke faruwa? suwaye suka sanya rayuwarsa ido har haka? ƙara gyara zamansa yay yana mai jin yadda kansa ke juya masa,tafin hannunsa ya sanya a saman forehead ɗinsa ya fara murzawa a hankali, Jalilerh na gefe tunanin mafarkin da tayi ya hanata sakat,a mafarki ma mutum ɗan uwanka na neman cutar da kai bare a zahiri? Abinda ke ɗaure mata kai yadda akai amfani da Uncle wajan ganin an tarwatsa rayuwarta,mene yasa komai idan zai faru da ita ake haɗawa da Uncle ɗinta?a wancan karan ansa ta muzan tashi,taci zarafinsa ba,a wannan karan kuma an nemi aci zarafin ta ta hanyar amfani da sunan Uncle ɗinta,me yasa a iya kanta kawai hakan ke faruwa?meyasa ba’a amfani da sister ɗin sa? Mene yasa ba’a amfani da wata matar?ko dan ta kasance mara addini hakan take faruwa da ita? Bata da wata addu’a da zata zame mata makami akan maƙiya ko abokan gaba,shuru tayi tana tunanin maganar Nihila inda take cewa *_kiyi tunani da zuciyarki,abinda ta amince maki shine dai-dai_* ajjiyar zcya ta sauke domin zuwa yanzu ta gama yarda da abinda zuciyarta ta amince mata,ta amince da aminda take kwaɗai ta mata tana ganin shine abinda yafi dacewa da ita a yanzu,wanda zai zama garkuwanta,mutsin da taji a bayanta yasa ta juya da sauri,mamaki fal fuskarta take kallonsa, yaushe ya shigo? Tana wanne tunanin? Shin ya ganta daya shigo ko a’a? Meyasa bai kulata ba? Jiki a sanyaye ta miƙe tare da nufar inda yake zaune,tana zuwa ta zauna gefen ƙafafunsa daga ƙasa,sosai bobo yaji idanunta a kansa amma yay kamar bai ganta ba domin a yanzu yana so ya kasance shi ɗaya babu takura,yana buƙatar yay tunani,tunani mai zurfi a kan rayuwar sa yanzu da kuma wacce zai fuskanta nan gaba,suna zaune babu wanda ya iya cewa komai kowa da abinda yake tunani,ita tana buƙatar sanar masa abinda ta yanke, shi kuma yana tunani akan zaɓen dazai gaba a sati mai zuwa, ƙafarsa data zauna akai ya ɗan mutsa kaɗan da sauri itama ta janye jikinta,ganin bashi da niyar tambayarta abinda ya kawo ta wajansa yasa tayi ƙasa da kai tare da kiran sunansa a hankali “Uncle” lumshe idanunsa yay kafin ya fesar da numfashi,bai amsata ba kuma bai mutsa ba,wajan 5minutes ta ƙara kiran sunansa “Uncle” murya can ƙasa yace “uhm”kanta ta ɗaga tana ɗan turo baki gaba,ido biyu sukai dashi kasancewar kansa a ƙasa yake dai-dai lokacin data ɗago kai a dai-dai lokacin shima ya ware manyan gajiyayyun idanunsa,da sauri ta janye nata,shuru yayi mata still yana ƙara ware manyan idanunta a kanta,a zahiri kuma bawai ita ɗin yake kalla ba, fararen ƴan yatsunsa na ƙafa ta zubawa idanu,ko wanne yatsa gargasa tayi ƙwance a samansa,cikin muryar ta mai rauni tace “Uncle nayi tunani kamar yadda baby tace nayi,kuma na amince da abinda Zuciyar tawa take faɗa min,amma bazan samu cikar muradin zuciyata ba sai ta dalilinka”tunaninsa gaba ɗaya ya tattaro zuwa gareta kafin yace “uhm inaji” cikin muryar kuka tare kuma miƙa wuya da kuma yadda da amincin zuciyar ta tace “Uncle ina son kalmar shahada,ina son yadda da annabi Muhammad Rasulullah (S.a.w), Uncle ina son rabauta da addinin musulunci” ta ƙare maganar hawaye na bin fuskarta,kamar saukar ruwan sama haka yaji saukar Muryar ta,da saurin da bai san yana dashi ba,yayi sauri sanya hannunsa ya ɗaga ta zuwa saman kujera, haɓarta ya tallafo idanunsa na yawo saman fuskarta yace “Are you sure? Kin tabbatar da abinda kike faɗa gasky ne?” Cikin kuka tace “na yarda Uncle ba tare da faɗar wani ba,ko kuma tursasawar wani ba,na yarda da hakanne sabida yarda da Annabi Muhammad Rasulullah,kuma da yarda da addinin musulunci shine addini guda kuma mafi suyowa, musulunci shine addinin gsky,kuma shine garkuwan ko wanne ɗan adam” sabida murna da farin cikin kasa cewa komai yayi sai kallonta yake da ido, miƙewa yayi tare da kallonta yace “muje ciki” a ƙofar shiga parlour suka haɗu da Nihila da ido take kallonsu, musamman bobo wanda fuskarsa take ɗauke da matsanancin farin ciki,wanda ta daɗe bata gansa a ciki ba,ganin yadda ta tsaya take kallonsa ya saka yasa hannu ya matsar da ita gefe kana ya shige cikin parlour’n, kusan gaba ɗaya jama’ar gidan na nan hadda Jafar wanda zuwansa ke nan, Mama ce tace “kai kuma lafiya kake farin ciki kamar wanda akaiwa ƙyauta da kujerar Makkah?” Lumshe idanunsa yay few seconds ya buɗe su a kan Mama yace “ko aikin hajji bai kai darajar wannan abunba”jin haka yasa Mummy ta gyara zama tace “bobo bamu musha mana” hannu yasa yaja gefenmu fuskarsa kafin ya sauke tagwayen ajjiyar zcya yace “gaya masu” ya faɗa yana sauke ganinsa akan Aryan kafin ya janye idanunsa,jiki a sanyaye ta faɗa masu the same abinda ta faɗawa Jalal,farin ciki ya sanya kusan gaba ɗaya wajan suka miƙe tsaye,cike da jin daɗi Abbou yace “me ake jira, Muhammad maza bata kalmar shahada, wannan ai abin farin ciki ne”gyara tsaiwa yay dan baya jin zai iya zama, Mameey miƙewa tayi ta rufe wa Jalilerh gashinta da wata red ɗin hula, cikin taushi murya yace “kin yarda kin amince zaki shiga addinin Musulunci ba tare da takurawar wani ko wata ba?” Jiki a sanyaye ta ɗaga masa kai, girgiza kansa yay kana yace “da baki zaki amsa” cikin rayuwar murya tace “eh” jinjina kai shima yayi alamar “good” kana ya ɗura da faɗin “kinyi hakanne bisa rafin kanki,tare da amincewar zuciyarki?” Nan ma tace “eh” cike da farin ciki ya ƙara sakin murmushi,wajan fridge ɗin dake parlour’n ya ƙara gorar ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle murfin gorar ya sanya cikin bakinsa,sai da yasha fiye da rabi kafin ya sauke gorar ruwan yace “kafin nan zanyi tsokaci akan ADDININ MUSULUNCI” gaba ɗaya wajan suka miƙa masa hankalinsu,banda Aryan da yake latsa wayarsa cikin tsaftacciyar muryarsa ya fara da faɗin.
MUSULUNCI
addinin Musulincci yazo ne daga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi, shine manzon da Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki daya kuma na karshe annabawa a duniya domin yasake jaddada addinin Allah ayi imani da Allah daya wanda Ya halicci kowa da komai. Addinin musulunci na da mabiya a duk fadin Duniya kuma mafiya yawan su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin Afirka ta arewa wadanda mafiyansu Larabawa ne masu bin adiinin musulunci, sai dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci ako’ina a fadin Duniyar mu, Ma’anar Addinin Musulunci shine ” Yarda da Mika wuya ga kadaituwan Allah Madaukakin Sarki, wato Shaidawa babu abun bautawa da Gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzonsa ne (Ma’aikinsa ne), bayan haka ka yarda da dukkan abubuwan da ya kebanta dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai”Allah Madaukakin Sarki shi ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al Kur’ani Mai Girma domin yazamo shiriya da Rahma ga Halittu baki daya, an bayyana musulunci a matsayin addinin dake da saurin karin yawa a duniya a kullum wanda ke da Adadin musulmai na Duniya sun kai kusan kashi 24.1% na dukka mutanen Duniya wato fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari takwas (1,800,000,000) a fadin duniya.
tsit wajan yayi banda ƙarar a.c babu abinda kake jin mutsinsa a wajan,hatta Mama zaune take ta tafka tagumi tana jin abinda Jikan nata yake faɗa tamkar balaraban Makkah wanda yake jan sallar ashan yayin azumi, Jalal kam shuru yayi yana jin yadda maƙoshinsa ke suya sabida yawan maganar da yayi,gefe guda kuma yana jin yadda yake samun nutsuwa a cikin zcyarsa,a hankali kuma ya juya ya kalli Jalilerh wacce kanta ke sunkuye sai zubar da hawaye yake, ɗan haɗe rai yay sabida kallon da yaga ana masa,kafin ya sauke idanunsa zuwa ƙasa haɗi da kama hannunta ya sanya cikin nasa ya ɗura da.
Dukkan addini na gaskiya ko na karya, dukkan jam’iya mai anfani ko mai cutarwa, dukkan kungiya mai alkhairi ko mai sharri‿
Dukkan wadan nan suna da akidodin su da kuma ginshikai da manufofin manufofin su, manufofi da ke zama kamar kundi ga mabiyan su.
Idan mutun yana son shiga cikin ko wane daya daga ababen da suka gabata, abu na farko da yake dibawa shine wadanan akidodi da gimshikai, idan ya yarda da su, kuma ya kudurcesu ba tare da shakku ba, bayan ya fahimci abinda suka kumsa, sai ya mika wuya, ya kuma zama daya daga ma biya wanan kungiya ko addinni. Bayan haka sai ya kasance wajibi akan shi ayukkan da ke wajibi akansu, ya kuma nisanci ababen da shi wanan kundi ya kumsa tare da ikhlasi a cikin dukkan ayukanshi a kowane lokaci, ya na mai kira zuwa gare shi.
Kasancewar mutun a cikin wanan kungiyar yana nufin ya san dokokin wanan kungiyar, ya kuma kudurci manufofinta, bayan haka ya yarda da hukunce hukuncen ta, tare da bayyana wadannan dokoki da hukunce hukumce a aikace. haka ne Muslunci ma.
Wanda yake son shiga cikin muslunci ya zama wajibi a kansa yayi imani da kudurce kudurce na muslunci dan ya kasance ya na akida ta muslunci.
Wanan akida ta kunshi imani da kasancewar wannan duniyar da muke gani ba ita ce kway ba, akoy abubuwa wa ‘ynda ba ma ganinsu, akoy kuma wata rayuwa bayan wannan rayuwar ta duniya.
Dan adam bai samar da kanshi ba, bayan haka wani abun halitta bai samarda shi ba, ba wanda ya samarda shi banda ubangijin da ya samarda halittu gaba dai bayan babu su, wandake bada rayuwa ko mutuwa, shine Allah wanda ya halicci kowa da kome, idan kuma yaso sai ya kasha su gaba daya, wanda babu mai kama da shi, babu wani abu da yake buya gareshi, shine na farko babu wani abu gabaninsa, shine kuma na karshe babu wani abu bayansa, shine mai ikon da ba shi da iyaka, shine mai adalcin da bay a kama da adalcin ababen halitta.
Shine ya saka ka idodi na dabi ia da rayuwa ke tafiya a kai , ya kuma sanya kome a matsayin sa da ya cancanta tun fil azal, ya kaddara motsi ko aiki da rashin su, yakuma baiwa da adam hankali da yake gane abubuwa da yawa da shi, wanda kuma da shine Allah ya bashi damar zabin abin da yake so a cikin rayuwa.
Bayan wannan rayuwar takaitatta ya sanya wata rayuwa wadda take mai dorewa ita ce lahira domin ya sakauta wa masu biyayya gare Shi a kan ayukkan su nagari da aljanna, wadanda suka ki biyayya kwa da jahannama.
Allannan shi daya yake ba shi da abokin tarayya, bai sanya tsani tsakanin shi da bayin Sa ba, babu mai ceto agurin Sa ba tare da izinin Sa ba, Shi kadai ake wa bawta, ko wan irin bawta ne.
Ya nada ababen halitta wadanda muke ganin su kamar yanda yake da halittu, masu motsi da wadanda ba sa motsi, da ba ma ganin su.
Halittun Sa sun kasu kishi uku:
Masu alkhairi kadai ( su ne mala’ iku ).
Masu sharri kadai ( su ne shaidannu ).
Wadanda suka hada alkhairi da sharri ( aljani da mutun ).
Allah ya na zaben wasu mutane wadanda mala’ ikun Sa ke sabkar da shari’ a gare su domin su isar da ita ga al ‿ ummomin su; wadannan mutane su ne manzonni.
Shari’ a ta karshe daga cikin Shari’ o’ in nan ( shari’ ar musulunci ) ta shafe dukkan Shari’ o’ in da suka gabace ta, dan haka littafi na karshe da Allah ya sabkar shine Alkur’ ani , wanda ya kore dukkan litattafen da suka zo gabanin shi, domin litattafen nan an cancanza su, wadan su kuma sun bace, wasu kuma an manta su; Alkur’ ani kadai ne ya kubuta daga ababen da su ka gabata.
Kuma hake ne muhamad ( tsira da rahama ta musamman su tabbata a gare shi, shi da dukkan annabawa ) shine manzo na karshe da ALLAH ya aiko, shi kwa dan kabilar kuraishawa ne a cikin larabawa, dan haka da shi aka cika annabci; babu wani annabi bayan shi.
Alkur’ ani shine kundi na Muslunci , dukkan wanda ya gaskata cewa daga Allah yake shi wannan al kur’ ani, ya kuma yi imani da shi gaba daya, to wannan ana kiran shi mumuni.
Imani ko da wannan ababe da suka gabata babu wanda ke ganin shi a cikin zuciyar mutane banda ALLAH; domin shi kadai ne ya san abin da zuciya ta kumsa, mutane sun san abinda ke zahiri ne kadai.
Domin haka ana dauka mutun musulmi idan ya yi firici da shahadar cewa babu wani abin bauta wanin ALLAH, kuma muhamad ( tsira da rahama ta musamman su tabbata a gare shi, shi da dukkan annabawa ) manzon ALLAH ne.
Idan ya firta wannan shahada lalle ya zama daya daga cikin musulmi, ya nada hakki kamar dukkan musulmi, haka kuma dukkan abin da ke hawan musulmi ya na hawan shi.
Wadannan abubuwa da ke rataya a kan shi abubuwa ne masu sauki, kuma ba masu yawa ba, daga cikin su:
1- sallah; zai yi ruku’ u ga ALLAH so biyu da safe, wannan ruku’ un kwa ganawa ce da ubangijin shi domin ya nemi rahama da tsarinshi daga dukkan sharri.
Gabanin wannan ganawar zai yi alwala ( tsabtace gabban shi ), ko yayi wanka idan akoy janaba a tare da shi.
Sa’ annan idan rana ta kau da tsakiya sai yayi raka’ a hudu.
Idan kuma inuwar shi ta lunka tsayin shi so biyu sai ya yi raka’ a hudu.
Ya kuma yi raka’ a uku yayinda rana ta fadi.
Da dare zai cika sallolin shi da raka’ a hudu.
Wannan sune salloli da ke wajibi a kan shi, ko wace daya daga cikin su bata wuce minti goma ba, ba’ a kuma kayyade su da wani guri na musamman, ko wani mutun wanda dole za’ a yi ta da shi, ba kuma wani tsani a cikin ta tsakanin mutun da ubangijin shi.
2- a cikin shekara akoy wani wata wanda musulmi yake azumta; a cikin wannan wata yana nisantar abinci da abin sha, ko saduwa tsakanin namiji da matar shi, daga safe har faduwar rana, wanan ko dan ya tsarkake zuciyar shi, ya kuma futar da tubin shi, ya kuma gyara halayan shi.
Sa’ an nan wannan watan wata ne dake karantar da musulmi game da haduwa akan aikin al kheiri.
3- idan dukiyar musulmi ta haura bukatar shi da ta iyalin shi, ta kai wani haddi da shari’ a ta kayyade, ta kuma shekara ba tare da ya bukace ta ba, ya na zama wajibi a kan shi ya fitarda wani kaso kankane ( biyu da rabi cikin dari ), ya bayarda shi ga mabukata da talakkawa ‿ abin da zai kawo hadin kai tsakanin al ‿ ummah da rike juna.
4- Muslunci ya tanadarwa musulmi haduwa na lokaci zuwa lokaci; haduwa biyar a ko wace rana a lokacin sallah, inda suke dada jaddawa ubangijinsu bautar su da bukatuwarsu gare shi a tsayuwarsu gaban Shi; hakan kuma zai sa mai karfi a cikin su ya kasance ya na mai taimakawa wanda ba shi da karfi, masani ya sanar da wanda ba ya da sani, mawadaci ya taimakawa wanda ba shi da shi.
Wannan salloli kwa ba su hana mutun gudanar da ayukan shi na yau da kullun, domin ba su daukar lokaci mai yawa.
Haka ne kuma Muslunci ya tanadar da haduwa ta mako a sallar ranar juma’a dake wajibi akan maza, wadda ita ma bat a daukar fiye da awa guda.
Bayan haka akoy haduwa so biyu a shekara a idin layya da na azumi, wadannan haduwa biyu ko halartar su ba wajibi ba ne ba, tare da cewa ko wace daya a cikin su ba ta daukar fiye da awa guda.
Sa’ annan a karshe akoy haduwa ta shekara a guri na musamman, a lokaci kayyadadde.
Wannan haduwar wada ke farali ( dole ) so daya a rayuwar musulmi idan ya na da iko, hakika taro ne na karantarwa da fuskantarwa, tare da motsa jiki da kolluwa; wannan taro shine hajji.
Wadannan sune ibadodi da ke wajaba a kan musulmi a asali.
Yana kuma cikin ibada barin wasu ayukka kayyadaddu, wadanda kuma masu hankali na duniya sun hadu a kan cewa sharri ne, tamkar kisan kai bad a hakki ba, ko ta’ adi a kan dukiyar mutane, ko zalunci, ko giya, ko riba, ko karya, ko zina, ko karya, ko al gush, ko rishin da’ a ga iyaye, ko rantsuwa a kan karya, ko shaidar zur, da abinda ya yi kama da haka na daga ababe munana wanda dukkan masu hankali sun san cewa sharri ne.
Idan musulmi ya gaza bayar da wasu daga cikin ababen da ke wajibi a kan shi, ko ya aikata wasu daga cikin ababen da aka hane shi, sa’ an nan ya tuba, ya koma ga Allah , ya kuma nemi afuwa shi, ba sakka Allah zai masa afuwa, idan kuma bai tuba ba zai ci gaba da kasancewa cikin musulunci, tare da cewa shi mai sabo ne, wanda yake cancantar ukubar Ubangiji ta wani lokaci, ba kamar ta kafiri ba.
Musulmi zai iya samun kan shi a halin barin wasu hukunce hukunce na musulunci ba tare da ya yi inkarin daya daga cikinsu ba, wannan ko ba zai fitar da shi daga da’ irar musulunci ba, face dai shi mai sabo ne.
Amma imani baya rarrabuwa, inda mutun zai yi imani da dukkan akidu na musulunci sa’ an nan yayi inkarin akida guda zai kafirta.
Mutun zai iya kasancewa musulmi amma ba ya da imani, kamar wanda ya shiga cikin wata kungiya tare da cewa bai yarda da ka’ idodin ta ba a hakika, kuma bai gamsu da ingancin ta ba, abin da ke da kwai shine kawai ya danganta kanshi gareta, domin leken asirin ta, ko bata ta.
Wannan kwa shi ne munafiki; wanda ke firta shahada da bakin shi, yake kuma aikata ayuka na Muslunci a zahira, tare da kunshe kafirci a cikin zuciyar shi, domin bai yi imani ba. Mutane suna masa hukuncin cewa shi musulmi ne; domin su ba su san abin da ke kumshe a cikin zukata ba.
Idan mutane suka yi imani da Allah, imani na hakika, suka kuma tsarkake Shi daga shirka ko tsani, tare da yin imani da mala’ iku, da annabawa, da litattafai, da rayuwar lahira, da kuma kaddara, bayan firta shahada, suna kuma masu sallatar salloli na farilla, da azumtar watan Ramadan, suka kuma kasance suna masu fitar da zakka ta dukiyoyin su, da kuma aikin hajji da umra inda hali, tare da nisantar ababen da aka hane shi, to hakika wannan musulmi ne kuma mumini ne, zai kuma samu dandanon musulunci muddun ya rungumi hanyar musulunci da gaskiya.
Wannan hanyar kwa manzon tsira yayi muna bayaninta cikin kalimomi takaitattu wanda suka hada al khairi na duniya da lahira.
Wadannan kalimomi sune: ya tuna a ko wane lokaci cewa Allah yana ganin shi, ya kuma san abin da zuciyar shi ta kunsa, dan haka kar ya saba mi Shi; saboda yana ganin shi, kar kuma ya fudda kauna soboda yana tare da shi, kar kuma ya samu kawaiti tare da cewa ya na ganawa da shi, kar kuma ya bukaci wani tare da cewa yana rokan Shi .
Idan ya saba masai ya komo zuwa gare Shi; domin mutun daman mai sabo ne, Ubangijin Shi kuma mai karbar tuba ne.
Wannan duka a cikin fadar manzon Allah yayin da ya ce: « kyautatawa shine: ka bautawa Allah kamar kana ganinshi, idan kai ba ka ganin Shi, to, lalle Shi yana ganin ka ».
Wannan shine musulunci wanda ya zo da shari’ a mai sauki, wadda mai ilimi da wanda ba shi da shi duka za su iya fahinta, ta kuma dace da kowa da kowa; ba ta dora wa kowa face abinda zai iya, tana tabbatar mishi da incin shi ba tare da sabawa Ubangijin shi ko cutar da wani ba.
Dan haka shi ne addini na jin kai da koncin hankali tare da salama.
Wannan shine addinin musulunci a takaice.
An ciro wannan bahasi ne da ga littafin sheik: Ali Dandawi (Allah ya ji kan shi ) mai suna: kitab ta’arifun a’m bi dinil islam.
Wata wahalalliyar ajjiyar zcya ya sauke tare da runtsa idanunsa yana mai karato sunayen ALLAH tsarkaka a cikin zcyarsa,a hankali kuma sautin kukanta ya ƙara cika ɗakin,ba tare daya buɗe idanunsa ba,ya ƙara matse hannunta ya ɗura da faɗin..Jalal kallon Abbou’nsa yay ta gefen ido ba tare kuma da yace komai ba yaci gaba da sauraran abinda Abbou ke faɗa,koda cewa Aryan ƙaninka ne,yana da ƙyau ka mara masa baya akan abinda yake so,kafi kowa sanin yarinyar kai kazo da ita,amma hakan ba yana nufin dole saika zaka bada aurenta ba,kaima aƙwai wanda suke da iko dakai” shuru Abbou yayi yana kallon Jalal wanda kansa yake a ƙasa yace “dakai nake Muhammad” ajjiyar zcya ya sauke kafin yaja numfashi yace “ita tana so ne?” murmushi Abbou yay yace “ko bata so nasan ai baza taƙi jikinka ba,daman dalilin daya sanya na kiraka kenan,ka dinga ƙarfafa mata guiwa akan Aryan,koda ba taso idan taga kana so ina da tabbacin zata ƙauna ci ɗan uwan naka”jidai kawai Jalal yake ba tare daya amsa Abbou har Abbou ya kammala yace “zaka iya tafiya”miƙewa yay yana tafe yana ambaton Allah a zuciyarsa,yana fita yay kwana zai shige part ɗin Mameey yaji Mummy tayi kiran sunansa, juyawa yay sukai ido huɗu,yana kallonta ya janye idanunsa yana jiran abinda zata ce masa,daga ƙofar part ɗinta tace “zo nan” tana faɗin hakan ta shige cikin part ɗinta,bayanta yabi da kallo kamar suko yana tsaye har wasu seconds suka shige,a hankali kuma ya ja jikinsa zuwa part ɗin mahaifiyar tasa,zaune ya same ta saman kujera 1seater da,tana ganinsa ta nuna masa kujerar dake farcing nata tace “zauna”babu musu ya zauna idanunsa a kanta, gyara zama tayi tace”me Abbou Jalal yace maka?”da mmki ya kalli mummy baice mata komai, ɓata rai tayi tace “ba photo bace ni da zaka zauna kana kallo na,nace mai mahaifinka yace maka?”ɗauke kansa yay,gaba ɗaya ya kasa gane mai iyayen nasa suke nema dashi,wannan yace kaza ita kuma ga a inda take tambaya,idan wani abu suke buƙata ai yana da ƙyau su fito fili su gaya masa,amma sai magana suke masa a tufke wacce baya gane inda maganar tasu ya dusa, numfashi ya sauke kafin ya ware laɓɓansa yace “babu komai” da ido ta kafesa tana son ta gane gskyar abinda ya faɗa,amma yadda ya haɗe ransa yasa bata fahimci komai ba, tace “bawai ina son nasan a abinda mahaifinka ya faɗa maka bane,nasan aƙwai sirri tsakanin ɗa da Uba,amma taza iya yiwuwa abinda kake tunani ba haka bane,domin nasan abinda baka sani ba Muhammad,a kullum ganinka kake babba akan sauran ƴan uwanka,amma mu muna sama dakai zamu iya yin abinda baza kai ba”jinjina mata kai yay alamar yana fahimtar zancen ta, murmushi tayi tace “daman zan faɗa maka tun safe Jalilerh ke fama da fever and headache,ko magani taƙi sha,nayi tunanin gayawa Abbou Jalal sai kuma na fasa nace idan ka dawo na faɗa maka” miƙewa tsaye yay ba tare da yace wani abu ba ya fice daga cikin part ɗin nata,a dwonstrais ya samu Nihila da Jalilerh, Jalilerh na ƙwance a saman soma idanunta rufe sai Nihila wacce ta sauya channel ɗin daga wacce take kalla zuwa sunna t.v,bai kalleta ba yace “kee! Tashe ta and kice ta sameni a part ɗina lrt”har ya nufi part ɗinsa yaji zaman gidan ya damesa gaba ɗaya ransa a ɓace yake ya rasa dalilin haka,fita yay zuwa compound ɗin gidan a wajan wasu kujeru ya zauna wajan an masa ado da wasu manyan flowers masu ƙyau sun kewaye kujerun,zama yay kana ya ɗura ƙafafunsa a saman ɗaya kujerar,a hankali kuma ya fara Musa bakinsa tare dayin bisimillah ya fara karanta suratul YAASIN…
Bayan sallar issha’i Mummy ta shiga part ɗin su Jalilerh ta samu Nihila zaune tana duba littafin Physics, Jalilerh kuma tana ƙwance tana rawar sanyi da alama zazzaɓin ne ya tashi,tana shiga cikin bedroom ɗin tana faɗin “bobo baizo ya dubata bane?” Nihila ta juya idanunta tace “aikam yace nace taje wajansa na kowa manta” juyawa Mummy tayi tace “kamarya kin manta Baby?bayan kinsan cewa dubata zaiyi” turo baki tayi tana shigewa bathroom tace “to Mummy karatu nake lokacin fa”tana faɗin hakan ta shige bathroom Mummy tace “shirme dai” zama tayi gefen Jalilerh tana yaye duvet ɗin data rufe jikinta dashi,daga ita sai half vest da wando 3gauter,ta ɗaure dugun gashin kanta da ribbon,jin jikin da zafi sosai yasa Mummy ta miƙar da ita tsaye tare da faɗin “ayya daughter haka jikin yay yanzu?maza jeki wajan Uncle ɗinki”cikin zafin zazzaɓi da shagwaɓa ta langwaɓar da kanta a saman shoulder ɗin Mummy tace “Mummy allura zai min fa”rungome ta Mummy tayi tace “a’a bazai maki ba tunda baki so” idanunta ne ya kawo ruwa tace “Mummy haka ranar nan kikace min”shafa kanta tayi tace “idan yay maki ki faɗa min”cike da ƙuruciya ta ɗagawa Mummy,dugun hijabi Mummy ta saka mata kafin ta mata bedroom silefers ta sanya a ƙafarta,har dwonstrais mummy tazo da ita tana sauka ta haɗu da Aryan ya fito daga cikin kitchen hannunsa riƙe da cup ɗin tea yace “Mummy jikinne?” Mummy ta miƙa masa hannun Jalilerh tace “wlh fa, Please kaita wajan bobo ya dubata”ba tare da komai ba ya riƙe hannunta dan rabon data tsaya ya ganta ya manta, Juyawa Mummy tayi shi kuma ya nufi side ɗinsu da ita,yana tafe ya kalleta yaga ta ƙara masa ƙyau a idanunsa ga wani girma data ƙara ƙwana biyu yace “Cutie ni kike gudu ko?”shuru tayi masa yana jin yadda take ƙoƙarin zame hannunta cikin nasa yace “never mind,Zaki daina da zarar mun zama ɗaya” tana jinsa amma bata fahimtar komai sai zazzaɓin daya fara cin ƙarfinta,ganin sun kusa isa part ɗin Jalal ya tsaya yana mai ɗan jawota zuwa jikinsa kafin ya ƙarasa shigar da ita jikin nasa bobo dake tsaye tun ɗazo yay gyaran murya kaɗan “uhm..ehem..” da sauri Aryan ya saketa kana ya shige part ɗinsa,wani murmushi takaicin halin ɗan uwan nasa Jalal ya saki,kafin ya haɗe rai ya kalli Jalilerh yace “me kike nan?” Lokacin har hawaye ya gama wanke mata fuska,kasa magana tayi ganin halin da take ciki yasa shima bai takurata ba, ya nufi inda take tsaye jikinta sai rawa yake,yana zuwa yasa hannu ya ɗaga ta cak ya nufi cikin part ɗinsa da ita, Aryan murmushi fal fuskarsa ya shige part ɗinsa sbd murinsa yana gaf da cika,komai zaizo masa cikin ruwan sanyi ba tare da wani wahala ba,akan 3seater Jalal ya sauketa yana ajjiye ta ya shige cikin bedroom ɗinsa,kai tsaye wani ɗan ƙaramin ɗaki ya shiga inda yake ajjiye kayansa masu muhimmanci,yana shiga ya ɗauki wata frist aidbox,ya fito daga cikin ɗakin wajan fridge ya ƙarasa ya ɗauki fresh milk mai sanyi da kuma go fresh, parlour’n ya dawo tana ƙwance inda ya sameta,inda ta ɗura kanta ya zauna,yana ta miƙe tsaye idanunta fal hawaye tace “Uncle Mummy tace kada kai min injection”kallon cikin idanunta yayi yaga da gaske take, murmushi yay mata kana ya zare hijab ɗin jikinta, ba tare da wani abu ba ya ajjiye gefe guda, lumshe idanunta tayi tana ɗan rufe ƙirjinta,dry ce ta subuce masa baki ta saki tana kallonsa sbd wani sihirtaccen ƙyau da yay mata, bata taɓa ganin wanda dry taiwa ƙyau kamarsa ba,gaba ɗaya ya sauya tamkar bashi ba, beauty points ɗinsa duk sun luma kusan rabin cheeks ɗinsa sune,kodan kar aga ƙyansa yasa baya yin dry? Ta tambaya a ranta,bayan yay dryarsa ta wasu seconds yace “me kike rufewa kuma?” Ƙasa tayi da kanta wata kunyarsa ta kamata ba tayi tunanin ya fahimci abinda take ba, ƙasa yay da muryarsa dai-dai kunanta yace “UNCLE NE fa?and kina ƙwaila kike tunanin za’a ga wani abu” turo baki tayi tana kai hannunta saman kirjinsay ta ɗan dakesa kaɗan tace “uhm..uhm”gefe yay da kanta ya ɗura a ƙirjinsa yana mai ɗan hura mata iska kaɗan kaɗan cikin kunnuwanta kafin yace “ina ke maki ciwo?” Ƙara shigar da fuskarta tayi cikin faffaɗan ƙirjinsa tace “mara na kemin ciwo” lips ɗinsa ya ɗura saman forehead ɗinta yana ƙara ƙwantar da ita yace “sorry en matan Uncle” kafin tai magana taji saukar allura a jikinsa yana sakawa ya zare,ihu ta fasa tare da saurin ƙanƙamesa ta shiga kuka kamar yarinya,wani killer smile ya saki ya rungome ta sosai a jikinsa yana shafa kanta yace “sorry Uncle ne ko?” Kai ta ɗaga masa tana ƙara sautin kukan ta,kansa ya ɗura a shoulder ɗinta yace “ohhyaaa shuru,and ki rama idan baki yafe ba”kamar jira take ta shiga cizonsa a ƙirjinsa duk inda tasa baki ta ciza sai ya lumshe idanunsa sbd zafi,ita tsakanin ta da Allah ramawa take,sai ta gaji dan kanta rabu dashi,kanta ya ɗaga ya kalli yadda fuskarsa ta caɓe da hawaye yace “kin rama” kaita ɗaga masa, haɗe fuska yayi yace “ban son haka” kamar zatai wani kukan tace “bapiii” ɗauke kansa ya ƙara shigar da ita jikinsa sbd yadda jikinta ya ɗauki zafi sosai da kuma yadda yaga tana ware hannayensa tana shigewa jikinsa,yasa ya ware duka hannayensa tana ganin hakan ta shige cikin jikinsa shi kuma ya maida hannunsa samanta,shuru gaba ɗaya sukai kowa da abinda yake ransa,can ya sauke numfashi yace “yaya kike wankan tsarki?” Idanunsa a lumshe tace “mene tsarki?” Waro idanunsa yayi cike da mamaki kafin yace “ok muna da shika-shikan musulunci guda biyar kuma a cikinsa akai maganar sallah ita kuma sallah bata yiwuwa sai da tsarkiyake” bacci na fusgarta tace “su waye biyar ɗin?” Lumshe idanunsa yay yana ja baya kaɗan ya ƙwanta jikin kujerar shima yace “shika-shikan musulunci sune.
Rukunnan Musulunci Biyar (arkān al-Islām, larabci أركان الإسلام; ko arkān al-dīn, larabci أركان الدين, Rukunnan addini, Shika-shikan addini) abubuwa ne ko ayyuka wadanda ginshikai ne, guda biyar a Musulunci, wadanda wajibai ne akan kowane mai imani, kuma sune farkon ginshikin rayuwar Musulmi. Suna nan tattare a shahararren hadisin nan na mala’ika Jibril.[1][2][3][4]
Shia, da Ahmadiyya, da Sunni dukkanin su sun yarda da muhimman bayani da ayyukan wadannan abubuwan,[5][2] amma Shi’a basa kiransu da irin wannan sunan (see Ancillaries of the Faith, na Twelvers, da kuma Seven pillars of Ismailism). Sune suka hada rayuwar musulmi, sallarsa, taimakawa gajiyayyu, tsarkake kai daga zunubbai, da aiki hajji,[6][7] ga wanda yakeda ikon zuwa.[8]
Shahada: (Imani) Gyara
Shahada itace mika wuya da tabbatar da Imani da bada gaskiya dake yarda da cewar babu wani abun bauta inba (Allah) ba, kuma Annabi Muhammad Manzon Sa ne, Kalman shahada dai rukuni ne na farko daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar, wanda wajibi ne sosai mutum ya kiyaye ta , tana shigar da mutum cikin Musulunci in har ya furta , kuma ya kudurce a zuciyar shi ,kuma yayi aiki da ma`anan abinda ya firta, kuma tana fitar da Mutum daga Musulunci idan ya saba ma`anar kalman ta hanyan yin sabo ko shirka ko ya aikata wani aiki dake fitar da mutum daga Musulunci
Salah: (Sallah) Gyara
Sallah (ṣalāh) itace bautar musulmai, Sallah ta kunshi yin salloli biyar kamar yadda Sunnah yazo dasu; sunayensu akan lokutan Amfani: Fajr (Subhi), Dhuhr (rana), ʿAṣr (Yamma), Maghrib (Almuru), da kuma ʿIshāʾ (dare). Sallar Fajr ana gudanar da ita ne kafin fitowar(tasowar) rana, Dhuhr kuma ana yinta ne a tsakiyar rana, bayan rana yayi zawali, Asr kuma da yammaci ake yinta kafin faduwar rana, Maghrib da almuru bayan rana ya fadi, sannan sai sallar Isha’i da akeyinta acikin dare. Duk wadannan salloli anayinsu ne ta hanyar kallon Kaaba a Mecca daya samar da muhimmin ginshiki a cikin alumman Musulmi. Musulmi sai sun wake jiki kafin yin Sallah; wannan wankin akekira da wudu
Zakāh: (Zakkah) Gyara
Zakkāh Zakka rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ana bayar da wani sashi ne na dukiyar mutum idan dukiyar ta kai nisabi.
Sawm: Azumi Gyara
Azumi rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar , ana kin cin abinci ne da kuma kin shan abun sha tin daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana , haka za`a tayi har sai anyi wata daya na watan Ramadan tukunnan aka sauke nauyin farillan. [11] ref>Al Kur’ani 2:196</ref> .[12][13] ⁶⁸_⁶⁹