UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 7 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 7 BY SHATU

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ni kaina nasan nayi karfin Hali, da har nasa hannuna na Mari Ismail, Amma ya zanyi banida wani option, tunda bazan iya fada da Ummaah ba to tabbas Zan samu abun da zanyi Mata warning dashi,ba tareda na jira maganar su ba ki na kalla yanayin da suke ciki nasa kaina nayi gaba, Likita ya take min baya. Yanayin dawowar mu ya banbanta da tafiyar mu, lokacin da muka tafi ban taba tunanin zanyi bacin Rai a wañnan ranar ba Amma se gashi within hours wasu sun Bata min Rai na. Tunda muka tafi Bai cemin komai ba, se da muka karaso kofar gidan yace min+

” Zan wuce?”

Na gyada kaina saboda nasan he needs space kamar yadda Nima nake bukatar space din. Ciki na shige ban ma jira ya tafi ba, Ammi na parlor tana waya taji shigowa ta Dan nasan Bata ji sallama taba saboda can kasan makoshi na nayi. Ta bini da kallo har na karasa gefenta na zauna, tayi saurin yin sallama a wayar ta aje tare da kallona cikin idanu, fuskata tayi ja ga shatin hannun Ummaah dake zaune a fuskar ta barin hagu, Ammi ta ciren hannu na dana dafe fuskar dashi shi ne ya bayyana. Take Naga fuskar ta ta Kara bayyana bacin Rai tace

” Waye ya mare ki?”

Ta fada tana zare min idanu, duk yadda nake da kwarin gwiwa da jin I’m strong se na saka Mata kuka tare da kwanciya akan kafadar ta, tasan babban Abu ke saka ni kuka tasan Akan karamin Abu bazan zauna Ina kuka ba.

” Sofy baki jina ki fada min me ya faru da kuka he gidan Gwoggo”

Ganin naki magana Kuma se kuka nake se ta fara rarrashina har nayi shiru sannan ne nace Mata Ummaah ce ta mare no

” Me Kika Mata? Rashin kunya ko?”

Na girgiza kaina, kafin nace wani abun ta Kuma cewa

” Zagina akai Kika Rama ko, shiyasa ta mare ki?”

Uwata tasan halina tasan zaginta kawai zaayi ya fito da halayena da suke a boye, nanma kaina na girgiza Mata sannan na fada Mata entire abinda ya faru, ranta ya baci tace min

” Me yasa Zaki Mari Ismail, sa’anki ne? Ba tarbiyyar da nayi muku kenan ba. Tashi ki wuce daki”

Haka na Mike a sanyaye na batta parlon, daga dakina na jiyo maganar ta a waya Wanda ya tabbatar min Baba ta Kira

” Ina son ka jawa Yan uwanka kunne, kada wadda ta Kara daukar min yata, nayi hakuri wannan Karan saboda shi ne Karo na farko Amma wallahi..”

Se tayi shiru kafin ta cigaba da fadin

” Ka Kira ka tambaye su!”

Daga haka ban Kara jin maganar ta ba, na shiga toilet na wanke fuskata sannan na dawo na sameta zaune alamar jirana take

” Shi Ina Bature take?”

Nace

” Ammi ya tafi! Kiyi hakuri”

Se ta janyo ni jikinta ta rungume ni, hakan se ya Kara Sagar min da gwiwa na cigaba da kukan, ba kukan abinda ya faru gidan Gwoggo nake ba, fact that na hadawa Ammi kasa a Ido ne ke saka ni kuka.

” Ya Isa kukan haka. Rayuwa baa Mata hakan, nasan tabbas bakya son Ismail, nasan akwai babban tabon Babar shi a zuciyar ki, Amma ba Zaki wulakan ta shi ba, babau Wanda yasan Maci tuwo har se Miya ta Kare. Ki dauke Yana sonki Ismail yayanki ne, it’s disrespectful of you ki daga hannu ki mare shi that’s very wrong, Ina son idan kin huce ki Kira shi ki bashi hakuri”

Na gyada kaina Dan nasan Bata son idan tana maka fada kana kokarin Kare Lanka ka Bari har se ta Gama ta huce se kayi bayani. Abinci ta zuba min naci tasa na fito parlor ta dakko min Quran tace na karanta, Babu musu na karba. Nayi karatun na wajen 20mins Sega Kiran Baba ya shigo wayata, Dana dauka naji muryar shi can kasa

STORY CONTINUES BELOW

” Are you ok?”

Nace

” Eh Baba, Ina wuni”

” Lafiya Lau daughter, tell me what exactly happened?”

Na Kai idanuna kan Ammi dake kallona sannan na fara Masa bayani, seda na gama yace

” Why did you slap Ismail?”

Cikin sanyin murya nace

” Baba taba ni yayi Kuma nace Masa ya daina taba ni bana so”

Yace

” Yayi kyau, kin kyauta but anjima ki Kira ki bashi hakuri yayanki ne, kada ki sake wani namiji ya taba ki kinji ko?”

Nayi murmushi nace

” Eh Baba!”

Yace

” Yauwaa Allah ya Miki albarka! I’ll handle the aftermath ki rarrashi Ammin ki”

Nayi murmushi Ina kallonta na gyada Kai mukai sallama, na Kara kallonta Bayan na sauke wayar ta tabe baki tace

” Halin banza yace kin burge shi ko?”

Nayi dariya kawai. Se yamma lis na Kira Bature nasan ya Isa Funtua zuwa lokacin, Yana dauka na fara bashi hakuri se ya fara dariya Yana cemin ai shi zai bani hakuri saboda he caused all this, daga haka se muka fara Hira abinmu har na manta abinda ya faru da Rana.

A gidan Gwoggo Ummaah na zaune itada Gwoggo da Anty Nabiha, ta dubi Gwoggo da tunda na fita take fada akan me yasa zata mareni, ta Kuma Bata mutuncin ta a idon sirikin ta

” Ni fa Gwoggo na fada Miki aure Ismail zai aureta Amma wallahi se naci ubanta da har zata mara Ismail a gabana, Banda ke ai wallahi se na bita har gaban uwarta na balla ta”

Gwoggo ranta na Kara baci tace

” Ke dai ba uwar kirki bace, me Ismail yayi ta mare shi, taba ta yayi, Kuma ga alamar wannan ba shi ne Karo na farko da yayi ba, tunda ke bazaki iya tankwara shi ba se ki Bari ita tayi”

” Kenan Gwoggo bayan ta ma kike bi ko? To shikenan!”

Daga haka ta Mike da kyar saboda ciwon kafa da take fama dashi, ga uban kiba da take dashi Wanda ya Kara taimakawa wajen munanta ciwon kafar. Mayafinta ta dauka zata fita Gwoggo dake zaune tace

” Ina Kuma Zaki je?”

Ba tareda ta juyo ba tace

” Gidan Babandi!”

Gwoggo Bata Kara cewa komai ba ta kyaleta, tana fita ta samu Ismail na zaune kan mota hannun shi rike da wayar shi, his favorite spot, shidai indai zaka ganshi to saman mota Yana Danna waya har se kana tunanin me yake dannawa ko Kuma tunanin baya gajiya ne. Yana ganinta ya duro, idanun shi har lokacin Basu washe daga Jan da sukai ba, saboda Marin Dana mishi,

” Ummaah Ina Zaki je?”

Ta kauda Kai tace

” Gidan Babandi zanje…”

Ya Dan zaro idanu yace

” Kawu Abdullahi wai? Ummaah dan Allah Kar kije. Bakiga ke Kika fara Marin ta ba”

Ta Masa wani kallo sannan tace

” Dan na mareta se nace ta mare ka, ita wacece?”

Ya girgiza kan shi dukda ba mutum bane me yawan surutu ba Amma kokari yake ya fahimtar da ita

” Ummaah wannan abun da kike bashi da kyau, beside tace na daina taba ta Kuma na taba Kinga laifi nane, Dan ta kawo saurayinta she’s every right ta kula Wanda take so, Dan Allah ki koma ciki. Kada ki Kara Bata Mata Rai”

Mamaki Karara akan fuskar Ummaah bayan ya gama magana tace

” Ismail akan mace? Ni uwarka kake cewa abinda nake bashi da kyau? Duk rayuwata komai saboda ku nake. Fada nake maka Dan ba zaka iya ba Amma kace Kar na Bata Mata rai..”

Yayi saurin katse ta Bayan ya fahimci ranta ya baci, ya kwantar da kai yace

” Nooo! Ba hakan nake nufi ba, Ina son ki gane idan Kika je gidan you’ll only upset her more, Kuma Kinga bazai taimaka ma aurenta da zanyi ba. Kiyi hakuri kawai ki koma ciki.”

Se ta koma ciki Dan tana jin maganar Ismail sosae cikin yaranta shi kadai namiji Wanda take ganin shi matsayin magaji. Bayan ya tabbatar ta tafi ya juya ya koma dakin shi, se Bayan maghrib sannan ya zo gidan mu. Na idar da sallar Isha na dakko novel Zan fara karantawa Ammi tace na aje nazo

” Wannan karatun ki dinga sararawa haka. Zo yau kallo zamuyi”

Na zauna gefen ta bayan na dakko zobo cikin tumbler na aje Ina kallon tsohon Indian movie Mard na Amitabh Bachan, mun danyi nisa naji sallamar Ismail Dan bamu riga mun rufe gidan ba. Na janyo hijab na saka na amsa shi ya shigo ya tsugunna har kasa ya gaida Ammi, da faraa ta amsa shi tana tambayar yadda Suka baro Gwoggo da kuma Ummaah. Ni na kawo Masa zobo na zauna na gaishe shi ya amsa Yana sunkuyar da Kai yace

” Ammi banci abinci ba!”

Ta kalleni tace

” Ki kawo abinci Mana”

Na Mike na zubo Masa abincin na aje gaban shi, na samu Ammi ta koma dakin hakan yasa na zauna na aje masa, Yana ci Yana kallona har yayi rabi se na bude baki a lokaci daya muka furta, ni nace

” I’m sorry for what happened dazun”

Shi Kuma yace

” Kiyi hakuri abinda Ummaah ta Miki!”

Se mukai dariya, ya Gama cin abincin sannan ya marairaice fuska yace

” Are you choosing him over me?”

Na gyada Masa Kai, se ya langwabar da Kai yace

” I’m hurt, zafi nake ji idan Ina ganin ki da wani fa. Me yasa bakya Sona? Na Miki laifi ne?”

Na girgiza Kai sannan nace

” Bana son auren gida”

Idanun shi ya Dan zaro irin Bai yarda ba yace

” Let’s assume bamu hada komai ba”

Na girgiza Kai nace

” It’s reality no assumption!”

Se yayi shiru a wañnan lokacin Kuma Likita nata Kirana so seda Ismail ya tafi looking broken kafin na samu na tadda calls dinsa da nayi missing. Zama nayi na fara kiranshi Amma har ya katse Bai picking ba Kuma Nima har nayi bacci Bai Kira ba.

Ban Kara Kiran shi ba nayi kwanciyata da niyyar nayi bacci amma hakan ya gagara saboda abubuwa da dama da suka dinga min yawo cikin kaina, Ismail yazo ya bani hakuri dukda cewar I wronged him Amma Bai dauka hakan a matsayin komai ba, wannan na nufin sincerely Ismail kaunata yake da gaske tsakanin shi da Allah, na danyi juyi akan gadon Ina kwabar zuciyata da tuna Mata Bature kadai zata tuna, Bature kadai zata so duk wani namiji dake kokarin shiga cikin zuciyar to zamu dauke shi matsayin abokin gaba. Da wannan consolation din na samu nayi bacci. Washegari da wurwuri Ammi ta rakani gidan Gwoggo na Mata sallama har lokacin Ummaah na nan Bata tafi ba Amma bacci take se yasa har muka gama abinda zamuyi Bata San mun zo ba, ni a raina naso ma ta tashi ta ganmu tayi masifa Ammi ta mayar Mata tasan cewar Ammin da da Ammin yanzun ba daya suke ba. Kamar yadda na fada muku har Zaria Ammi ta rakani seda na gama komai nayi settling sabon dakin nawa sannan Kuma ta shirya min Kaya muka fito, ta Mika min kudi tace na rike kafin Baba ya tura min ta account Dina. Na Mata godiya har na fara jin kewar ta. A gabana suka juya suka tafi sannan a hankali na koma hostel, na zauna bakin gado tareda karewa dakin kallo. Mu uku ne ciki dukda ban samu kowa ba da nazo, Amma daga yadda akai arranging beds din ya tabbatar min hakan. Wayata na janyo nayi dialing number Bature, Amma se ta katse da line busy, ajewa nayi Ina tura bakina Dan tun jiya bamuyi magana ba, se kawai ga Kiran shi ya shigo, na dauka cikeda dauki muka fara gaisawa seda muka Gama sannan na fara Masa korafin ya manta dani, se yayi dariya yace+
” Ni na Isa mantawa da gimbiya! Ai kamar na manta da kaina kenan”
I blushed sannan Kuma nayi shiru se yayi dariya yana fadin
” Jiya kin Kira ni Kuma i was in the ot shiyasa ban dauka ba, yau da safe Kuma nasan Kuna tareda Ammi and I left WhatsApp message for you”
” But se ka min message kace kana theater ai! Nima dai na fara makaranta zan dinga ce maka Ina lecture ne”
Yayi dariya da yasa nayi murmushi yace
” Nima na iya rigima fa! To dai kiyi hakuri”
Se muka Dan taba Hira sannan ya min fada akan sabuwar rayuwar mukai sallama.
Anty Nabiha ita ce autar su Baba, Kuma itama layin su daya dasu Ummaah, wato Ummaah ce ta rike ta Mata aure Dan haka se ta Zama yarinyar ta, you can mistaken her for yarta ba kanwar ta ba. Sede ita tana Kaduna tana aure hakan yasa baa fiya jinta sosae ba, plus mijinta Dan balai ne baya barinta tana zuwa ko da yaushe, se tafi shekara Bata zo ba. Tana komawa Kaduna bayan sun bar Gumel ta Kira Anty jidda ta fesa Mata abinda yake faruwa, tayi ihu Anty jidda tace
” Amma Nabiha Allah ya Miki albarka, nagode da wannan labarin. Anty Furairan ta dawo ne?”
Tace
” Eh ta dawo tun jiya”
Se sukai sallama, Anty jidda ta sakko ta shiga kwalawa Hanifa Kira, tana kwance daki tana kallo , ta fito tana yatsina fuska
” Mom kina ta Kirana kamar Zaki fasa min eardrums”
Anty jidda tayi murmushi tace
” Kina son Ismail ko kin hakura?”
Ta Dan zaro idonta sannan ta Dan Yi tsaki tace
” Nifa Mom kinsan bana son wulakanci, I can’t just throw myself akan mutumin da Bai san worth dina ba”
Anty jidda ta sake baki dukda tun asali ba Hanifa ke son Ismail ba ita ta fara instigating abin ta Kuma sakawa Hanifa hakan cikin zuciyar ta, ta fara kokarin cusa kanta Dan itama Ismail ya Mata, ba kowacce mace ce zata iya dauke kanta akan shi ba, Amma Bayan yadda ya yaba ta Bayan bikin Rayha da Kuma Nima abinda na Mata se ta fara ganin me yasa zata Bata lokacin ta akan namiji kwaya daya Bayan duk mazan da suke sonta, idan kudi ne,ilimi ko kyau.
STORY CONTINUES BELOW
” Kenan kina nufin kin hakura dashi, duk abinda nayi a banza kenan?”
Hanifa ta tabe baki tace
” Ni fa Mom ban taba ce Miki kije like musu ba, nifa gaskiya bana son abinda Zan aure shi baya Sona, Kuma kina kallon yadda wannan Sofy ta gaggaya min magana ranar”
Anty jidda kamar ta daura hannu a kanta tayi ihu, cikin daga murya tace
” Haneey, ki manta da Sofy wannan ba problem din ki bace, kina zancen baya sonki ta ya zai soki baki zauna kin kula dashi ba, yanzun yaushe rabon da ki Kira shi?”
Hanifa kawai ta girgiza kanta ta wuce daki tana fadin
” Dan Allah idan wannan maganar ce Mom karki Kara Kirana, inada abubuwa da yawa”
Ran Anty jidda ya baci ta bita daki ta same ta ta maida hankali kallon Joda and Akhbar, ta zauna tace
” Yanzun Hanifa ni kike fadawa haka?”
Hanifa ta Dan kalleta sannan ta maida kanta kan allon tvn tace
” To Mom kiyi hakuri. Shikenan?”
Anty jidda tace
” Ko kefa yanzun ki shirya muje race course din”
Ta girgiza Kai tace
” Kije kawai idan ya amince I’ll make a move”
To ya zatayi haka ta fito, ba tareda taji wai yarta rashin kunya tayi Mata ba, ita a lokacin babbar matsalar ta shi ne botsarewa da Hanifa ke Shirin Yi. Shiryawa tayi tsaf ta dauki key din motar ta, dama mijin Anty jidda hoto me shidai kawai Yana aurene Amma se yadda akace dashi, shiyasa Yan uwanshi basa sonta Amma Kuma tafi karfin suyi Mata abinda takewa Ammi. Irin me kudinnan ne Amma Kuma Yan uwanshi duk Yan kauye ne, Babu wayewa balle ilimi shi dinma hakan take, idan ka ganshi baxaka ce mijinta bane.
Dakin Hanifa ta leka lokacin Amira ta dawo, se fada suke wai Amira ta shigo batayi knocking ba, ita Kuma Amira tace ai dakin bana ta bane ita daya so Bata Isa tai knocking ba. Ko ta musu magana baji suke ba hakan yasa ta musu sallama ta wuce warta. Tun a hanya take kissima irin zugar da za tayiwa Ummaah idan taje. Tana Isa ta samu Ismail an rirriko shi daga mota zuwa parlor da sauri ta karasa ta samu an aje shi kan kujera. Ta shiga da Yanayin tausayi a fuskarta irin ace Bata ji dadin halin da Ismail yake ciki ba. Bayan sun gaisa ta shiga kitchen ta dama Masa oat kamar yadda Ummaah ta fada mata, tana fitowa ta samu an maida shi daki se kawai me aiki ta karba ta Kai Masa daki bayan ance ta tabbatar ya shanye, ban sani ba ko dura Masa zatayi oho!
Anty jidda Suka gaisa da Ummaah, tace
” Jidda yanzun nake Shirin kiranki kinsan me ya faru Dani kuwa”
Anty jidda ta gyara Zama tace
” Me ya faru Kuma? Me ya samu yarima”
Ita kadai ke ce Masa yarima saboda tasan haka Ummaah take so. Ummaah ta zauna ta fada Mata duk yadda ya faru a Gumel sannan tace Mata
” Tunda muka dawo bashi da lafiya, na kasa gane kanshi, jidda Kuma mirsisi Babandi yace shi bazai yiwa Yar shi auren Dole ba seda yardarta. Ban taba tunanin Zan nemi Abu na rasa ba”
Anty jidda ta kulu kenan Bayan duk abinda ya faru Ummaah kokarin hada auren take, ita kuma da ta shafe shekara da shekaru tana Mata fadanci se kawai opportunity ya wuce ta. Hakan yasa ta girgiza Kai tace
” Lallai Anty Furaira yanzun Bayan a gaban ki Sofy ta Mari yarima har kike tunanin aura Mata shi..”
” To ya zanyi jidda? Ya kafe ya nace se ita, da nayi kokarin hanashi shi ne ya fara wannan jinyar, ya zanyi?”
” Baki sani ba wallahi Kika Bari ya Shiga hannun su uwarta se ta Rama cin kashin da muka Mata, balle ma yadda yake sonta, karki damu ni Ina ganin inada mafita”
Ummaah ta gyara Zama tace
” Yawwa jidda fada min naji, tsoron da nake kenan kada Hajara ta maida min yaro se yadda tace. Ke meye shawararki?”
” Ki Masa aure kawai! Ki samu wata ki Masa aure shi ne kadai zaisa ya hakura”
Ummaah tayi shiru tana tunani kafin can tace
” Anya wannan shawara ce? Anya zai yadda”
Ganin haka Anty jidda tace
” Ba se ya yadda ba kawai ke zakiyi, dama Kika biyeshi a bazai yadda ba”
Se Ummaah tace
” To Zan gwada na gani, Amma wa Zan aura Masa ma dai”
Tayi Murmushin nasara tace
” Zan cigita Miki, balle shi Mai cousins gaba da baya”
Tasan idan ta kawo motion din Yar ta Ummaah zata harbo jirginta se kawai ta fuske Amma har ta Gama tsara yadda komai zai kasance.
Babu Wanda yasan abinda Anty jidda ke shiryawa cikin ranta, sede itama tana ganin lokaci ne da zata dauki fansar bauta da tayi shekara da shekaru tana yiwa Ummaah, ta bude wuta ta fara shirye shirye Babu Kama hannun yaro, kullum tana hanyar kasuwa ko kuma tace tayi order. A bangaren Ismail Ummaah ta tabbatar jikin shi yayi sauki sannan ta same shi da batun auren, yayi shiru yana kallonta kafin yace
” Ummaah kenan na hakura da Sofy?”
Ta girgiza Kai tace
” Ina son na maka aure kafin ita ta gama  makaranta, idan ta gama se ka aureta”
Se ya gyada kanshi saboda shi mutum ne me tsananin biyayya, suna Gama maganar ta Kira Anty jidda ta sanar Mata akwai progress, Dan haka Anty jidda tace wani satin zata shigo su Gama Shirin.
A hankali na fara karatu, bana bukatar wani yace min wai nayi karatu Dan hakan Bata baki ne, ko a fada ko baa fada ba ansan zanyi karatu, in fact se ma cemin ake in daure Ina hutawa. First two weeks ban Saba da kowa ba hatta room mates dina sede na gaishe su kawai na fita, Yar final year din ce ma Anty yusra ke komawa ta kaina, ita ce take Dan tambayata idan taga na Jima ban dawo ba, har ta karba contact dina. Tun ranar da na fara ganinta, she looks familiar, tana min Kama da wata Amma na kasa tuna a Ina ma nasan me Kama da fuskar ta,kawai zuciyata ta kwanta da ita, for unknown reason Ina sonta.
  A class dama kullum Ina gaba, zaiyi wahala a tsare front seat ban zo ba, tunda naje bana taba yin  girki ranar da nake da lecture, sede na siya kawai. So ranar Saturday ce da ya Kai wajen wata na guda kenan, na fita nayo cefane na zauna na gyara komai sannan naje inda ya kamata nayi girki na daura abinci, Ina zaune da wani novel hannuna har na Gama, na juye sannan na dawo daki na aje na koma nayi wanke wanke na dawo. Anty yusra da fitowar ta kenan a wanka tana zaune tana shafa Mai, se dayar Hussaina Hussy ita Kuma ta fita, dake mutum ce me kawayen so bata fiye Zama ba. bansan Ina taje ba. Abincin na zuba a Dan deep plate na kaiwa Anty yusra, ta kalleni sannan tayi murmushi tace
” A’a yau girki Kika Yi kenan?”
Nayi murmushi nace
” Na gaji da cin na waje”
Ta gyada Kai tareda cemin ai dama tana ganin kokarina, se Bata ci abincin ba wai ta koshi, ban damu ba na zauna na cinye abinci na sannan na dauka wayata na kunna data na fara chatting. Tunda Naga Rayha online se kawai na zauna muka ta fira har bansan lokaci ya tafi sosae ba. Na aje wayar kenan Sega Kiran Ismail ya shigo kamar bazan dauka ba, se Kuma na dauka, da wannan muryar tashi me sanyi yace min
” Darling ya kike?”
Nayi dariya kamar yadda nake Yi duk lokacin da ya kirani da wani sweet name, seda muka gaisa sannan yace
” Ummaah zatayi min aure..”
Cikin farin ciki nace
” Da gaske? Oh Allah ya Sanya alkhairi”
Ya Dan Bata Rai kafin yace
” To are you happy zanyi aure, kiranki nayi na baki hakuri don’t feel humiliated kinji, Zan aureki inshallah kinji?”
Na girgiza Kai nace
” Ina maka fatan alkhairi,Amma ka manta aurena kawai. Focus on the marriage you’re about to hold.”
” Shikenan rabuwa zakiyi dani? Kenan?”
Bance Masa komai ba Amma naji tausayin shi sosae cikin Raina, ba Kuma hakan ke nufin Zan karbe shi ba, uwarshi na ganin tayi amfani da hakan wajen Bata min Rai a yadda Ismail ya fahimta kenan, Bai San koami na gaba ba. Ya Jima Yana ta yimin complain akan baisan motive din Ummaah ba, Bai San me yasa take son Masa aure ba. Nidai sede na bishi da cewar yayi addua kawai.
STORY CONTINUES BELOW
Wajen azahar nayi sallah na dawo na kwanta, Anty yusra dake gefe naji tana fadin
” Hamma wallahi yanzun Zan fito, Dan Allah ka kirani”
Mikewa tayi ta janyo katon hijab a gefen locker dinta har zata fita se ta dubeni tace
” Sofy Zaki rakani, brother nane yazo”
Nima na gaji da zaman se kawai na mike, skirt da riga ne jikina na atamfa, na dakko veil na yafa sannan na dauki wayata na bi bayanta. Ganin yadda take sauri nace
” Anty yusra se sauri kikeyi”
Tayi dariya tace
” Baki San waye Hamma ba, Dada kawai yake iya jira Amma ko matar shi zai iya barinta ya tafi, balle ni”
Na gyada Kai na fahimta irin Wanda Basu son a Bata musu lokaci, wata mota muka nufa Ash anyi parking a gefe, se kafafun shi da ya zuro waje Suka bayyana slippers din dake kafafun shi. Jujjuyawa tayi tana fadin
” Ko Ina yake?”
Se muka ji honk daga wannan Ash din motar, gurin ta nufa tana min inkiya na taho, Muna zuwa ta rike kofar tana murmushi tace
” Hamma sannu da zuwa, ya Hanya?”
Banji yayi magana ba Naga tana murmushi tace
” Kuma Kai kadai ko su Afaf baka zo dasu ba”
” Kai Hamma! Safiyya taho ku gaisa”
Tana fadin Safiyya Naga yayi saurin lekowa, guess who? Usman Dikko ne. Idanuna nadan zaro na bude baki Amma words din se Suka makale, shi Kuma ya fito gaba daya daga motar yace1
” Sofy kece da gaske ko kuma I’m seeing things?”
Nayi murmushi tareda yin kasa da kaina, kamar na nutse saboda kunya, ban taba tunanin Zan Kara haduwa dashi ba, shiyasa da aka bani sakon shi bayan nayi graduation na kasa kiran shi, ni a zuciyata bashi da space din da Zan bashi shiyasa nake ganin kamar Bata masa lokaci zanyi ba, kallon Anty yusra nayi dake kallon mu baki bude se yanzun na fahimci da wa take Kama, sosae  suke Kama hatta skin color dinsu,
” Safiyya kin San shi ne?”
Kafin nayi magana yace
” Yanzun zata ce Miki Bata sanni…”
Nayi saurin katse shi da fadin
” Anty yusra na sanshi fa, he’s my teacher”
Ta kallemu sannan tayi dariya tace
” Hamma ko dai ko dai”
Ya dage kafadar shi tareda harararta yace
” Ina ruwan ki, Sofy zo”
Na sunkuyar da kaina, na kalle shi sannan na karasa gefen shi har familiar turaren shi Ina jin kamshin, se na tuna wannan lokutan da yake zuwa gurina a class, lokacin da zai tayi min hira Amma sede kawai nace uhmm ko a’a.
” Howwa you my dear, kwana da yawa”
Nayi murmushi nace
” Lafiya Lau inasu Afaf?”
Yayi murmushi yace
” Tana lafiya ai ita kadai ce, so wanne course kikeyi?”
Nace
” Vet medicine nakeyi”
Yace Allah ya taimaka sannan ya kalla Anty yusra yace
” Yusra ga amanata nan, take care of her”
Ta kalleni sannan ta kalleshi tace
” Inshallah Hamma”
Nayi tunanin zai karba phone number ta Amma Bai nema ba, se kudi ya Bata na Dan matsa gefe Suka Dan taba Hira sannan ya tako inda nake yace
” Sofy se na Kara dawowa, by the way Ina twin sister dinki”
Nace
” Tayi aure suna Qatar”
Yayi Mana murna sannan ya tafi, bayan mun juya ni da Anty yusra tace min
” A Ina Kika sanshi?”
” Fggc Bakori”
Se ta gyada kanta Bata Kara cemin komai ba, bayan mun koma daki ta Lalo kudi ta bani naki amsa tace se na karba tunda kuwa Hamma ya Bata ta bani, dole na karba nace ta Masa godiya se ta dauki wayata ta saka min contact din shi cikin wayata tace
” Ki Kira shi ki Masa godiya”
Na gyada Kai bawai Dan Zan Kira ba sede Dan bazan ja zance ba, tun daga ranar kuwa ta Shiga bani kulawa sosae kamar wadda aka kawo mu tare, idan na Mata complain se tace wai bansan waye Hamma a rayuwar ta ba. Ya zanyi Dole haka Zan hakura, se ya zamana hatta Ammi tasan Anty yusra Kuma suna waya da ita, Dana fadawa Bature se yace min wai campaign take yiwa yayanta, nayi dariya nace kishi yake kenan, yace wai shi ko a jikin shi. Lokaci zuwa lokaci idan ya Kira zai ce Mata Ina amanar shi, se ta kawo min wayar muyi Hira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *