WALIJAAM CHAPTER 3 BY MAMAN TEDDY

WALIJAAM CHAPTER 3 BY MAMAN TEDDY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

*_Ga masu bukatar wannan littafi xasuna iya mgn dani ta wannan link din 👇_*

https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_FREE page na dab da karewa ,Ki tausaya ma yar mutan mallawa kar ki fitarmun da littafi idan kin siya ,kema kar ki karantamun idan ba biya kikayi ba don Allah._

*_SADAUKARWA GA DUK KANIN FULANI🐄_*

*Alheri writers asso.📚*

_________________________

” Shatu ne ta kai hannun ta tana shafan inda jinin ke zuba mawa yarinyar ,wanda bata lura dashi ba sai a wannan lokacin hannun ta tasa tana shafa inda jinin ke fita duk da bada yawa ne yakefita ba ,amma hankalin ta ya tashi matuka. Bata ankare da shigowar mareeya ba sai maganan ta da taji tana xama gyefen ta  kamin tace ” Shatu kiyi hakuri komai mai wucewa ne a rayuwa kum…wani wucewa ai wannan abun da ta jawo mawa kanta baxai ta6a bille mata ko ya haifa mata da mai ido ba ,kuma tayaya zai wuce mareeya? Ai sai kin fada mana inda kika dauko wannan diya sannan…Cewan Oumman shatu da shigowar su kenan bukan ita da Yawindo.

Aa Fatima kar ki manta da maganan liman mana komai fa kadara ce,kuma mun san wannan yarinya bata aikata wannan abun da ake zargin ta dashi ba…don haka mu bita ta lalama ne muji inda ta tsinto wanga jaririya.

Nisawa Oumman shatu tayi badon hankalin ta ya kwanta ba ,ta koma tana xama jarab a kasan tabarman kaba…amsan yarinyar Yawindo tayi tana kara gyarata hadi da nadeta cikin zani tana shafa mata mankade akan raunin da akaji mata garin dukan shatu da Oumma keyi . Sai da ta gama natsata sannan yawindo ta bata dafaffan kindirmo don ya dau cikin ta sosai ,sai wani yin nan nan da ita take kaman mejegon gskennan… Sai da Yawindo ta kammala ne sannan ta bar bukan hadi da nufan wurin liman . Wanda bata boye masa komai ba ta fadesa duk abun da ta gani akan Shatu da sanar masa cewan Wannan jaririya ba Diyar ta bace.

Hamdala Liman yayi kamin yayi saurin nufan Wurin sana’ar Baffa don ya sanar masa da komai .

Mutane ne tun daga nesan rumfan Baffa tankam ,dagani kasan sunyi babban bako . Amma da liman ya matsa kusa sai yaga abun da ranshi yayi matukar baci don mahaifin Hardo ne da shi kanshi hardon sun tsaya akan Baffa basuyi duba ga Mutanen da sukazo rumfar nasa ba suke tsitsaya tsiya da masifa hadi da cin mutumci .

Bazan Auri Shatu ba ni nama saketa ,taje ta auri wanda suka saba sheke ayansu har  yayi mata cikin shege ya Aureta. Nidai bazan auri ragowa ba ,kuma wlh banyafe ba abun da akamun…cewar Hardo yana wucewa fuuuu yabar mahafin shi yana cigaba da zagi da cin mutunci .

Shikam Baffa dukar ds kai kurum yayi ranshi na masa wani irin suya ,a zuciyar shi yana ayyanawa cewan daga yau Shatu tabar masa gida. Hakuri ake baimawa Baffa gyefe guda kuma wasu na janye Baffan Hardo da yake abu kaman xai bigi Baffa. Kowa a wannan wuri tausaya mawa Baffa yake da wannan iftilain abun kunyar da ya same shi ,wasu na cewa a zukatan su wannan ai shine baka jawo ba an jawo maka.

Liman kam wucewan da Baffan hardo yayi yana kumfar baki da zage_xage yasa shi zama yaana fuskan tar Baffa da hankalin shi sosai ya tashi . Kayi hakuri Malam Yakubu ,kar kayi fushi ko kullatan diyarka ,anan ne agaban sauran mutanen ya kwashe komai yanda ya faru da abun da Yawindo ta sanar masa ya fada masu . Hamdallah duka wurin aka dauka ,wanda har a wannan lokacin Baffa baiyi sauka ba ,budan bakin shi cewa yayi tom liman ita wannan yarinya yar wacece a ina ta samo….?? 

Malam Yakubu na lura duk gabaki daya hankalin ka yagaxa kwanciya ,ni ina rokon ka abaimawa Yarona Auren Wannan yarinya ta wurinka daman na dade inason mu kullah haalaka wacce babu rabuwa a tsakanin mu ta har abada. 

Wani irin tsit ne wurin ya dauka ,kowa yagaxa motsawa don jin mgnan da Alhji Jalingo ke fadi da bakin sa…. Cigaba yayi da cewa ” kayi mun alhairai maban banta na rokeka Malam yakubu kabaimawa dan dana haifa Aishatu ko nima auren nata zai xama silar shiriyar nawa yaron. Don duk wacce ya kalli shatu yasan iyayen ta sun bata tarbiya kwarai ,shiyasa nake roka…Haba Alhaji Ai Shatu ya ce a wurin ka ,wlh kamin komai nima ,basai ka roki wani abu daga gareni ba alhji ,indai wannan abun kuwa nawa ne kasa mawa ranka tamkar naka ne ,don haka ni Yakubu na bai ma Yarona na wajen ka Auren Shatu. 

Mashaallh Alhmdullillah…Abun da kowa ke fadi kenan a wannan wuri ,kamin Alhji jalingo yace ” Nagode kwarai malam yakubu ,ina nima alfarma idan babu damuwa….. Cike da yabawa da hali da dattijanta ka ga dattako irin na Alhji Jalingo da bai nuna banbanci tsakanin talaka da mai Arxiki Baffa yace munaji Alhji .

Nisawa yayi kamin yace” yanda suka saki wannan yarinya anan wurin sakin wulakanci inaso ne adaura wannan Aure anan wurin a take..!!

**********

Fitan Yawindo ke da wuya ne Umma cike da fushi tafara rufe Shatu da balai ,kun sun zuciya idan fushi ya turnukota ,sam Umma batasan lokacin da ta dubi Wannan jaririya ba tace ” idan baki fada mana inda kika samo wannan yarinya ba aradu sai nasa an dauketa an jefar ajeji can ta karata ko akaita gidan marayu bai wuce ai tsintota kikayi… Kuka Shatu tasa mai ta6a zuciya harda shashsheka gami da  fara mawa Umma magiyan kan ta rabu da yarinyar amma Umma cike da fushi a zuciye ta fice daga bukan .

Tsawon lokaci shatu ta dauka tana xubda kwallah ,kamin tunanin yaxo mata ,mikewa tayi tana sa6a jaririyar ,don a cewan ta baxata yarda a cutar mata da Wannan yarinyaba sam ,amanan tace ,kuma ta dauki alkawarin ba zata fadi mawa kowa wannan sirrin ba.

Fakaitan idon Umma tayi ta fice daga wannn buka tana nufan hanyar barin wannan Ruga. Tana tafe tana kuka takaici na rashin fahimta n ta dakowa yayi ,kowa yakasa barin ta da y’ar ta.  Ta daujika ta ke yankawa don koda an biyo bayan ta tayi badda hanya babu mai iya cin mata .

Tafiya tayi mai nisan gaske don har rana ta fara  faduwa sannan ta yanko wani Babban titi da batasan ta inace ba.

Yanda ta rufe yarinyar rigib a bayan ts bubu mai cewa ba diyar tace ba…haka itama tasa lullubi ta rufe kanta rijib da shi.

Tafiya take kanta tsaye batare da tayi aune ba taji an riko hannun ta caraf. Wani irin faduwa ne gabanta yayi wanda tsoro sai da ya fito a kwayar idon ta…. Wasu irin murda_murdan rikakkun sojoji ta gani wasu a gaban ta wasu baya ,kusan su 4 ,fuskan su daure babu imani ko baa ce maka ba.

Kasa masu magana Shatu tayi don ko ina na jikin ta rawa yake ,don Yagwalgwal ta fadi mata su waye soja a nigeria matsayin su da martabansu.

Duk da tsoron da ya kamata sam bashi ya hanata cewa” ku din su waye..? Me nayi maku?? Me kukuso dani?? Basu bata amsa ba ,sai daya daga cikin sune yace da ita” meje gurun Leutanant zamu kai ki. Yayi mgnan yana tasa kyeyarta . Mamaki ne ya kamata waye shi wannan leutanant din ne? Me xaiyi mata kuma? .

A tsaye ta taddasu su uku kamsn yanda kullum suke ,idan kaga daya sai kaga biyun ,Anwar ,Abbas da Sadeeq .

Murmushi Abbas ya saki kamin yace ” Anwar kaga yar fulani mai kyaukuwa ,a ina kika
samo wannan kyaun haka ?! Yayi mgnan ga Anwar da kallo daya yayi mawa Shatu ya gane fuskan ta don baxai manta da ita ba ,wani irin tafasa zuciyar sa yake masa lokaci daya ,kaman a wannan lokacin ne sukayi case din da yahadasu da Shatun .

Kauda kansa yayi gyefe yayin da Sadeeq ne ya amsa shi da Allah yaasa yanda take da kyaun fuskan nan nata har daga ciki ma hakan yake . Wani wawan dariya Abbas yayi yana kai hannun shi hadi kokarin riko Shatu . Saurin matsawa tayi tana bin sa da wani irin kallo .

Murmushi ya saki irin na yan iskan nan yana wani shafa sajen sa da ya tattara ya tara na rashin kunya . Zaki zo nayi abun da xanyi dake ne ko ko sai na sa miki karfi .

Kina wani jah baya kaman baki saba ba,bayan fualin nan babu wanda ya kaiku iskanci ku fake da saida nono kuyi ta iskanci a gari ,matsawa yayi kusa da inda take yana dukowa hadi da dan rage tsayin sa kadan yana saisaitawa da nata cikin wani irin murya ta tatattu yace ” koda akwai wanda bakyeso ya ganki ne anan wurin mu shiga daga ciki …yy mgn da murya mai kama da rada yana kashe mata idon daya….Wani irin mari Shattun ta dauke shi dashi wanda batasan xata iya shi ba .

Ba Sadeeq ne kadai ya girgixa da saukar marin ba Har da Anwar da ya kauda masu da kai ,don a zuciyar shi godiya yake mawa Allah da ya kuma hadasu da wannan yarinyar ,yana farin ciki don bai ta6a son Abbs da wannan harkar ba sai ayau…yana addu’ar Allah yasa yaci ubann Shatu ,shiyasa ya juyq masu baya ,amaimakon yaji Abbas ya jefata moto sai kuma yaji saukar mari a kuncin Abbas wanda baiyi zato ko tsaanin hakan  ba………………

_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_

_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_

https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Normal grp 200_

_Vip grp  500_

_Spc group 1k👌_

_Idan kati xaki turo MTN ne ._

_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_

_0028799846_

_Farida Hashim stanbic bank_

_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne na Airtel ta wannan number na kasa👇_

_+22797780373_

_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._

*Don Allah kimun mgn ne idan kin san biyan littafi xakiyi ,wlh banada lokacin amsa hlo ,hi banadashi ….kawai ki tura kudin ki kimun screen shorting evidence of payment naki ta wannan number 08081202932 ,idan kati turo mun kaawai xan saki a paid grp inshaallh….*

*Kar ku manta free page na dab da karewa….*

_________________________

_FREE PAGE na dab da karewa don Allah don maaiki kar ki fitar mun da littafi a bati idan kin siya ,ke kuma don Allah kar ki jira isowar littafin da aka sata ba tare da sanin marubuciyar ba ,idan kkyi haka kaman kin xama barauniyar xaune ce! Don ma’aiki badon niba kar ki fitarmun da littafi idan kin biya ,ku kuma idan baku biya ba kar ku karanta mun littafin WALIJAAM Don Allah👏_

_*Masoya makaranta littafan maman teddy a yau gashi ta zo maku da wata dama na karatun littafan nata kaman👇*_

_Yar Aiki na_

_Bafullatanan ruga_

_Gidan kwarata_

_Siyasa taah_

_Zuma da madaci_

_Kwaryar sama_

_Dijama y’ar fulani_

_Y’ar maula_

_Y’ar waye_

_Da dai sauran su…A yau sun bude hanyar da zaku na samun audio na littafan a youtube channel nasu mai suna HUMAIRA NOVELS TV_

_*Maman teddy🧸*_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *