WALIJAAM CHAPTER 8 BY MAMAN TEDDY

WALIJAAM CHAPTER 8 BY MAMAN TEDDY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Koda ya isa barrack din gidan shi ya nufa ,tsawon kwana biyu baya da walwala sai dai kaman yanda yayi mawa mahaifin nashi alkawari bai sa6a masa ba domun kuwa tun ranan da ya sauka yasa aka fara sauya masa komai na gidan , Sam su Sadeq basu damu da ganin wannan sauyin yanayin daga gareshi ba don dama sun dade da sanin halin Anwar din ,sai ya kwana ya wuni bai ce mawa kowa komai ba indai ba kaine ka tanka shi ba, wannan kadanne na daga miskilancin Anwar .

Zaune duka suke kowa na abun da ya saba ,shi Sadeeq na can yana fira da mata Yayin da Anwar ke sana’ar sa Shikam Abbas sai wani murmushin nishadi yake yi don yau gurun shi ya cika ,ya jiyo labarin inda wannan yar fulanin take da zama ,a yanxu abu daya ya rage masa shine tayanda zasu na haduwa da ita .

Abbas lafiya sai wani murmushi kakeyi kana fara’a sai kace an maka albishir da gidan Aljjana?. Cewan Sadeeq yana mai datse wayan tashi hadi da kallon Abbas da har wannan lokacin murmushi yakeyi ,shikam Anwar sai a sannan ya lura da mood din Abbas din a yau hakan yasa shi bin shi da kallo da son jin mai zai fadi .

Hmm nisawa Abbas yayi har da dagowa yana mai gyara zaman shi kamin yace ” ba dole nayi farin ciki ba ,wacce na dade ina nema zuciyata tana marari allah ya kusa cikamun burina , nan take ya kwashe masu duk yanda zasukayi da wannan tsohuwar bafullatanan ya fada masu .

Mamaki ne ya kama Anwar Haushi ya ciyo zuciyar sa ,wai a yanxu fulanin ne Abbas ke so ,ta6 a da kam ba ruwan shi dasu ,amma sanadin wannan yarinyar yaji ya tsane duk wasu fulani . A miskilamce yace ma Abbas ” wai kai fulanin ne kakeso?? Abbas don allah ka rabu masu da yar mutane nasan halinka ,kana samun yar mutane wlh ko baka aureta ba ,kasamu kayi abun da kakeso da ita zakace ka janye ka dai na son ta, ka rabu masu da yar mutane plz… Yana mgnan ne hadi da lumshe lulun idon sa . Murmushi Abbas yayi yana lasan lips nashi na kasa kamin yace ” bana mawa kaina tsammanin irin wannan son nake mata Anwar . Ina son ta kuma duk idan na tunanota a zuciyata ina jin shaawar ta fiye da kowacce diya mace ,kaga ko ai hakan akeso ana son ayi aure tare da so da Shaawar juna ina son Aysha kuma zan Aureta ,babu mai hanani sai Allah sai kuma mutuwa ,amma indai ina raye da numfashi na wlh baxan yarda a rabani da Shatu ba .

Ikon allah Lamarin babba ne cewann Sadeeq dama shi dan zugo ne ,kamin ya saki wata irin dariya yana cewa ” Har ka san sunan ma diyar fulanin ,lallai nesa tazo kusa ,sai ya kuma bushewa da dariya harda tafa hannu yana buga kafa . Abbas Wai ahhh ni na ma rasa me zance ,like is not real kai ne zakace kanason yar kauye ,wai ma yar kauyen bafullatana , Amazing abun da mamaki kam ,kai dakace bazaka auri yar nigeria ba duk wayewan ta sai kuma a yanxu naji kana fadin Yar kauyen wai bafullatana …kawai Ya kuma bushewa da dariya . Kai oga sir ya isa haka ! Cewan Anwar don bashi yake mawa ba amma yagama kuluwa don shi Abbas baiga Auren nashi ba ,shiko yaga feture din nashi ,hmmm kana wani dariya gomma Abbas bai Aureta ba ,amma niko an aura mun fulani wife ,wanda nafi tsana a rayuwa ta na duniya na tsani fulani ,amma wai itace Dad ya auro mun kaiiii ,ya karke maganan yana dafe kai hadi da cije la66ansa na bakin ciki ,a lokaci daya idon shi ya sauya ya chanja daga fari zuwa ja.

Mamaki ne ya kamasu duka Abbas da Sadeeq ,Wai ban gane mai kake nufi ba Anwar ,plz yi mana bayani yanda zamu fahimta kaji “. Cewan Abbas yana fiddo da idon sa waje don mmki ,shi yama kasa fahimtar mgnan Abokin nasa .

Cike da dakewa Anwar yace ina nufin Daddy yy mun aure va tare da sani na ba ,kuma nan take yafara basu lbrn komai da yafaru da yanda Daddy ya aura masa matan don yakara masa bayanin komai da baiyi a gaban Dr Haula ba ,don tamaki tsayawa ta fuskance Alhji Jalingo din .

Inalillahi Anwar kaine Aka aura mawa bafullatanan??cewan Sadeeq yana fiddo da idanun sa waje kaman wanda aka kamasa yy karya .kai dallah malam Dan rufe mana baki ,a hamdalah zamuyi ma Allah domun ko samun Bafullatana a yanxu dace ne sai wanda Allah yaba . Cewan Abbas yana daukar cup din dake gaban Anwar yana shan ruwan giyan dake ciki .

Kallon Banza su duka suka watsa masa ,kamin Abbas ya cigaba da cewa ” ni wlh kaga ma faduwa tazo dai dai da zama ,idan zamuje dauko amarya sai na tsaya neman tawa matan ko ya kukace . Kallon shi Anwar yayi kaman zai masa mgn sai kuma ya ta6e baki don ma baida lokacin sa  yafara tunanin Abbas ba a hankalin sa yake ba . Uhmm mikewa Anwar yayi yana cewa kai kumu hade a wurin training yana fadin haka ya fice yabar Sadeeq da baki bude ,shi kuma abbas na cigaba da kwarara gear din sa .

**********

Bangaren Dr Haulat kam abun duniya ya dameta sam bata da walwala ko dariya ,fuskan ta kullum a daure yake babu fara’a sam ,abu daya take tunowa taji sanyi shine cewan da Zabeenart tayi a yanxu Anwar yana sakin mata fuska har suyi mgn amaimakon da baya .

Nisawa Mom Anwar tayi tana mgn a fili da cewa ” tun a sali ni najawo mawa kaina ai ,da na fadi abun da nakeso anwar yayi da tuni ya Auri Zabeena da yanxu ban zauna da tagumi ba mtsww taja karamin tsaki tana cigaba da bin ma’aikatan da take hango su ta haraban gidan a jikin windon ta kowa na aikin sa .

Ji tayi an hugging din ta ta baya an rungumeta sanyaayyar turaren ta na mamaye ilahirin falon Dr Haulan “. Murmushi tayi kamin ta juya tana jagayo da zabeena ta gaban ta tana mai fadada fara’ar ta ganin zabeena ta saki jikin ta fiye da kullum , sanye take cikin shiga lace riga da skirt blue da milk colour nasa sai karamar mayafin dake rike a hannun ta mai launin milk ,takalmin kafarta mai dan tudu .

Kissing din ta Dr Haula tayi kamin tace ” yau kuma Daughter na ina zataje ne da sanyin safennan ?. Murmushi Zabeena tayi tana far da ido kamin tace “Ai mom jiya na yanke shawarar zuwa zaria naje wurin Anwar acan gidan sa xan zauna don in shiga tsakanin su da wannan shegiyar yarinyar don Mom bazan dawo ba sai naga Aurennan ya mutu ,ya zama nice kadai a zuciyar Anwar sannan . Inaso naje mukara sabawa da juna sannan .

Murmushi Dr Haula tayi cike da jin dadin maganan Zabeena kamin tace ” kai da kyau Daughter na ,nima kaina ina nan inata tunanin ta yanda zan bullo mawa al’amarin ,kije ki zauna tare dashi ya ware maki dakin ki ,Komai da yake faruwa a gidan mu rinka communicate kinji diya ta . Yanxu kamin ki isa Zan kira Anwar din maxa allah shi tsare ya kiyaye mun ke Zabeena .

Ameen Mommy na tafi ,tayi mgnan ta na juyawa hadi da ficewa daga dakin tana barin mum tana sakin murmushin farin ciki don zabeena itace wacce zata sa ta lalata komai na wannan tsakin . A zuciyar ta tana mai kara jin tsanar Hajiya Rahamatu da ta dauki komai na ragamar kayan lefe . Tuni dangi aka dauka masu farin ciki nayi masu taya hajiya Haula bakin ciki nayi ,duk da masu farin cikin sunfi yawa ,don kowa yasan makirci na Hajiya Haula ,taki kowa a dangin mijin ta ,babu mai ra6ar arxikin ta na d’anta da mijin ta ,wannan dalilin yasa da yawa suke farin ciki da wannan auren ,dama shi Alhji jalingo mutum ne da bai damuwa da Talaka da mai kudi du
kka ya dauke su yan uwa kuma nashi ne .

*********

Tun da Anwar ya shiga barikin sojojin bai dawo gidan sa ba sai magriba don bai san da zuwan Zabeena ba .

Tun da ya shiga falon gidan nasa a saman cushunes din falon yaga jakar mace da mayafi . Mmki ne ke ciyosa a zuciya amma abunka ga muskili sai ya dake yana nufar bedroom din shi toilet ya fada hadi da watsa ruwa yana dauro alwala . Bai fito falon ba sai da yy sallan magriba kana ya fito sanye da jallabiya .  Muryar Zabeena yaji a kitchen ita da mai kulada komai na girkin sa daniel . Mamaki ne ya kamasa matuka sai ya nufi daya daga cikin kujerun falon yana zama dai dai Zabeena na fitowa.

Da gudu ta nufesa cike da kissa da yaudararriyar murya ta ke fadin oyoyo wlcm back dear tana hayewa saaman cinyan sa hadi da rungumesa . Tana manna masa kiss a saman lips din shi .

Wani irin yarrr yaji tsikar jikin shi na tashi ,wanda cike da murtike fuska yace ” Zabeena mai ya kawoki da wannan lokacin har a yaushe xaki koma gida ne “.

Yana mgnan hadi da rabata da jikin sa ta mike daga jikin sa badon taso ba .. Lokaci daya taji ranta ya baci ya kuma sosu ,murtike fuska yayi ganin yanda ta kafesa da ido ta rashin kunya ,don bayason raini sam .

Ba magana nakeyi maki ba?? Yayi maganan yana kare gimtse fuskar sa tamau . Abunka ga yar duniya ,tuni tafara matso kwallah tana jah da baya a hankali hadi da cewa” yo dama don na taho gidan ka shikenan nayi laifi ,baxan zauna gidan ka ba ,ai mom tace zata fada maka zan zo 😣, Amma shikenan tun da bakayi farin ciki da zuwa ba ba kaso ba ba damuwa kayi hakuri nayi laifi .

Tana fadin haka ta juya tana nufar dakin ta da tayada zongo da komai nata …dafe kanshi yayi don sai asannan ya tuna da Kwarai kuwa Mom ta fada masa zuwan ta . A hankali ya mike yana bin bayan ta don yasan yanxu kayanta zata hada tace xata bar gidan…!!

Abunko da yayi tunani hakan ta faru don kuwa har ta gama hada kayanta tana daukar jakarta .

Zama yayi zaman royal bed din yana kallon ta kaman bazai mata mgn ba sai kuma yace ” Ina ne kike hada kayanki zakije . Shiru tayi bata basa amsa ba don tukukin bakin cikin dake ciyota ,sai kuma a gajarce tace ” zan koma inda na fito gidan Mom nasan ita baxata wulakantani ba ko bayan ran iyayena bare kuma dasu a raye .

Tana maganan hadi da daukar jakarta tana takawa hadi da nufan kofa…bai tankata ba sai danna wani lock remote da ya rufe ko ina Bedroom din . Burda kofan tayi da zummar ficewa daga dakin nan taji ta a rufe .

Kara murdawa tayi nan ma taji a rufe yake hakan yasa ta juyowa don ta tayi masa mgn ,amma cike da mmki ta bude baki ne ta ganshi ,shi ya koma ma ya kwanta ne abun shi bama ya ta kanta ,sai idon shi dake akan wayan hannun shi fuskan shi na kallon sama.

Mu tare a page na 25 kuma na karshen free page inshaallh💃💃

Hazarta wajen biyan naki kudin littafin Kar ayi baki ,domun kuwa lbrn yanxu take yanxun zaa fara💃💃

_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_

_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_

https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Normal grp 200_

_Vip grp  500_

_Spc group 1k👌_

_Idan kati xaki turo MTN ne ._

_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_

_0028799846_

_Farida Hashim stanbic bank_

_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne na Airtel ta wannan number na kasa👇_

_+22797780373_

_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._

_*Maman teddy🧸*_

     08081202932

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *