WANENE SHI
CHAPTER 13Nanne ta k’ifta idanunta a hankali tana kallonsa, idanunsa na kallonta, kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik’onsa, ta tashi ta bar d’akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad’aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi.
Amma ta kasa ko motsi, idanunta na kallon nasa wanda ke cike da matsanancin rok’o irin na yaro k’arami sanda ya maka laifi, bayan hakan kuma akwai hanqoro na jiran abinda zata fad’a, a hankali ta shak’i sassanyan k’amshin dake fitowa daga jikinsa, wani k’amshi mai sanyi da dad’i, Taji zuciyarta na ayyana mata cewa k’amshin zai iya kwantar da hargitsin dake cikin kanta, saboda haka ta matsa a hankali ta cusa kanta cikin wuyansa sannan ta fad’i abinda yake gaskiyar zuciyarta.
“Bana jin tsoronka…!”
Da gaske ne ko kad’an babu d’igon tsoronsa da kalamansa suka sa mata, sai dai tarin mamaki fal da kuma rud’ani, gani take yi kamar a mafarki ko labari ne kad’ai abinda yake gaya mata zai faru, ta ture tunanin dake shirin kawo mata tsoro ta janyo b’arin zuciyarta dake cike da tausayinsa, tausayin irin rayuwar bautar da yayi a baya, wani abu da kwakwalwarta ta kasa hasko mata.
“I’m so sorry Noory, dan Allah kiyi hak’uri.”
Muryarsa ta fad’a daga saman kanta amma bata ce komai ba, sai yayi shiru kamar me jira. Zuwa can ta d’ago da kanta ta kalle shi, idanunsa har a lokacin basu canja daga launin silver, Ta yaya ne suka koma haka? akwai tambayoyin da yawa a cikin kanta a lokacin, saboda haka ta saka wannan ma a cikin jerinsu.
“Wace irin halitta ce ALBIE? ni ban tab’a jin sunan ba ko a tarihi.”
Ya kalleta sosai kafin ya amsa.
“Akwai tarin jinsin halittun Ubangiji a duniyar nan Sa’adha wanda tunanin d’an Adam bai sansu ba. abinda kowa ya sani kawai sune manya-manyan halittun; Mutane, Aljanu, Tsirrai da kuma Dabbobi.
Amma a k’arkashin kowannensu akwai jinsi kala-kala, idan kika d’auki dabba misali, akwai su da yawa, na k’asa da cikin ruwa, kuma ba kowanne irin jinsi kika sani a cikinsu ba ko aka ambata a alqur’ani ko hadisi, akwai wanda ma wanda baza’a tab’a saninsa ba har duniyar ta ka’re.
Ko a cikin ku mutane akwai jinsin k’abilu fal! wanda ba wanda ya san yawansu kuma ba kowanne aka ambata ba, toh haka a cikin jinsin Aljanu ma akwai irinmu da yawa da ba kowa ya sani ba. Mu ba Aljanu bane amma za’a iya danganta jinsinmu dasu tunda bama cikin mutane ko dabbobi.”
“Kuma kuma musulmai ne?”
Ya d’anyi guntun murmushi yana kallonta.
“Yadda addini yake kala-kala a cikin mutane da aljanu, haka yake ma a wajenmu, bayan musulunci akwai wasu da yawa, sai dai a nahiyarmu, musuluncin shi yafi k’arfi.”
Tayi shiru tana motsa yatsunta a hankali kafin tayi tambayar da take ganin itace jigon komai.
“Me yasa ka aure ni?”
Ta fad’a tana kallon labulen dake can bayansu, it was difficult for her ta fad’i kalmar aure tsakaninsu a fili.
“Saboda ina sonki Sa’adha.” kalaman suka fito cikin muryarsa mai taushi, muryar da sai a yanzu Nanne ta lura cewa tayi dad’i da yawa ta kasance ta mutane. Mutane musamman maza basu da irin wannan taushi da zurfin muryar. It was so velvety-husky!
Ta dawo da kallonta kan fuskarsa, cikin d’an guntun tunani tace.
“Ban gane ba, nayi tunanin kazo yin aikin da aka turo ka ne ba wai kayi rayuwa a cikin mu ba.”
Yayi shiru kafin ya k’ifta idanunsa a hankali.
“Ta yaya zan miki bayani ba tare da na tsorata ki ba…”
Story continues below

Sanda ya fad’i hakan yaji hannunsa d’aya da baya rik’e da nata yayi sanyi, saboda haka ba tare da ya nemi izini ba ya lalubo d’aya hannun nata yayi sliding nasa a ciki, nan da nan kuwa tunaninsa ya zama distracted.
“Hannayenki suna da laushi, ina son d’uminsu.” muryarsa can k’asa tare da yin ajiyar zuciya. Bata ce komai ba shima yayi shiru kamar mai jera tunaninsa.
“Kin tuna ranar dana fara ganinki kin dawo daga islamiyya?” Ta d’aga kanta.
“Zuciyata ta fara sonki tun a wannan ranar Sa’adha, tun a ranar dana fara shigowa cikin bil’adama, a lokacin da ban san komai ba kuma ban san ya rayuwar zata tafi dani ba, sannan ban san ko ke wacece ba amma zuciyata ta karb’e ki wholheartedy, duk da cewa ban fahimci hakan ba a lokacin nayi zaton kawai abinda kika yi ne ya burge ni don ban tab’a ganin hakan ba.
A ranar jaamil ya gaya min cewa wannan gidan na layinku ba zaiyi min dad’in zama ba saboda yawan mutane a wajen, saboda haka na canja wani a can wata unguwa, bayan nayi settling komai kuma na fara bibiyarki ta hanyar zuwa layinku, a haka na gano lokacin da kuke fita makaranta da safe, sai inzo in wuce ku kamar na dawo daga morning training don in ganki, da kuma sanda kuke tashi daga makaranta, sau da yawa zanje a siffar da bazaki ganni ba, in tsaya a parking lot d’in da ake zuwa d’aukarku, don in saurari dukkanin hirarki…”
Nanne taji k’arar wani abu kamar murmushinsa can k’asa, ta d’ago daga kallon hannayensu da take ta kalle shi, murmushin kuwa yake kyallin siver idonsa ya haska a cikin nasa.
“…Na san duk wata fitinarki a lokacin Sa’adha, kin tuna ranar da kuka tsayar da wani tsoho mai turmi?”
Ta maida kallonta k’asa a hankali, ta tuna lokacin sarai, ita da Amina ne da kuma wata Aisha, suka tsaida tsohon nan suka yi ta cinikin wani k’aton turmi daya d’auko, kusan minti ashirin yana ja suna ja har dai ya sallama musu akan wani farashi mai sauk’i, sannan suka ce wai ya dawo gobe zasu taho da kud’in, ai kuwa ya d’auki turminsa ya tafi yana zaginsu tare da Allah ya isa.
She smiled, and he smiled ruefully back.
“Bayan haka Noory kullum da yamma lokacin dawowarki daga islamiyya zanzo in tsaya daga wajen wasu samari da mafi yawa suke taruwa daga jikin mota a sigar da ba mai ganinna.
Sai dai a kullum ina gayawa zuciyata cewa abinda nake ba daidai bane, zai iya zama min matsala musamman idan Naani taji, amma kuma duk sanda na kwana biyu bai ganki ba, bana iya focusing akan aikina, Saboda haka a kullum zan cewa kaina daga ranar ba zan k’ara zuwa wajenki ba, amma gobe zan dawo.
Ban ankara da cewar abinda nake yi da gaske zai zame min matsala ba sai ranar dana ga cewa kina iya ganinna bayan kuma ina zuwa ne a sigar da idon mutane ba zai iya d’auka ba. Sau da yawa zaki juyo kamar kin kalle ni sai kuma kiyi saurin juyawa ki kalli Rahma da kuke tafiya tare. Tun daga wannan lokacin ne na takura kaina na daina bibiyarki kusan watanni biyu, shine wannan lokacin da kika ce kin daina ganina.”
“Me yasa a lokacin dana tambayeka wajen wa kake zuwa ka min k’arya?”
Ya d’ago hannayensu yana kallo sannan yace.
“Ta yaya zan gaya miki a lokacin cewa ba wanda ya san ni saboda ina zuwa ne a siffar da ba wanda ke ganina?”
“Toh me yasa ni kad’ai nake iya ganinka? kana tunanin inada wata matsalar ne?”
“Nine nake zuwa a siffar da mutane basa ganina, and you’re worried that kice mai matsala?”
Imran ya fad’a da d’an guntun murmushi a fuskarsa, ta fahimce dukkan manyan abubuwan da ya fad’a amma wannan kawai ya sata tunani? ya kalli fuskarta, wani abu kamar damuwa etched deep between her eyes, sannan tana ta tauna lebb’enta.
“Karki damu, ba wani matsala bane, ina tunanin alama ce na cewa ni dake are meant to be together.”
Ta sake tauna lebb’enta sannan tace.
“Shi yasa na tambayi Sadiq a lokacin yace min bai sanka ba.”
Maimakon ya bata amsa sai ya zare hannunsa daga cikin nata ya kaishi kan bakinta, ya janyo lebb’en daga cikin bakinta.
“Zaki ji wa kanki ciwo…” Kalaman suka rataye a iska kamar ba iyakar abinda yayi niyyar fad’a ba kenan.
Nanne ta kalli cikin idanunsa har yanzu suna kyallinsu na silver ga wannan sassanyan numfashin nasa yana kad’a fuskarta a hankali, zata iya zama tare dashi haka zuwa tsawon lokacin da baza ta iya tantancewa ba, amma a halin yanzu akwai tarin abubuwa da take son sani, labarin bai kai k’arshe ba saboda haka ta d’an matsa baya kad’an sannan tace.
“Bayan nan ban k’ara ganinka ba sai ranar daka fara min magana.”
“Right… lokacin da nake zuwa ganinki, jaamil ya lura da abinda nake yi, saboda haka ya dawo daga Muzzaffar lokacin dana riga na daina zuwa wajenki yayi min gargad’in cewa in daina abinda nake tun kafin Naani ta sani, ganin yadda ya d’auki abin da zafi yana ta b’ata rai, sai nayi tunanin in k’ara tsokanarsa saboda haka a ranar muna tare dashi na hango ki nazo nayi miki magana don ya gani, sai dai wannan maganar ta rushe duk wani tarin k’ok’arin da nake na avoiding d’inki, naji cewa ba zan iya sake nesanta kaina dake ba, saboda haka na dawo da zuwa ganinki.”
“A wannan ranar na kwana da wani irin ciwon kai, hakan yana da alak’a da kai?”
“I’m afraid yes, saboda na tab’a jikinki a karo na farko.”
Ta kalle shi da mamaki, idonta na nuna tambayar da bata furta ba.
“Sanda nazo baki handkerchief d’in nan, yatsana ya tab’a naki kad’an yadda ke baki ji bama.”
Ta had’iye wani abu a mak’ogwaronta kafin tace.
“A lokacin nayi tunanin handkerchief d’in Babba ne, amma daga baya dana d’auko sai na ganshi d’an karami.”
“Mhmm Mhmm…” Ya girgiza kansa yana kallonta.
“That’s not something important…Ki gaya min ciwon kan naki ya dad’e a ranar?”
Ta girgiza kanta a hankali.
“Dana tashi da safe babu shi.”
A cikin kanta, ta tuna mafarkin da tayi da muryarsa a lokacin, muryarsa mai taushi data ambaci sunanta.
“Bayan wannan ranar na kasa daurewa da daina ganinki, na cigaba da zuwa duk da irin magiyar da jaamil yake min, a sannan ne kuma nayi wani abu da ban tab’a yi ba tunda nake a rayuwata…”
Ya tsaya a lokaci d’aya sannan ya kawar da kansa daga kallonta. Itama bata ce komai ba ta cigaba da kallonsa har zuwa sanda yayi deciding cigaba da magana.
“Naje makarantarku lokacin da kike gayawa k’awarki kina son aljanu su shiga jikinki don ki mari wani malaminku…i was instantly jeleous! da naji kina neman aljani a tare dake, kuma na san a wannan lokacin da an sami aljanin da ya jiki zai shiga jikinki ne da hujja and i don’t think i can stand that… ba zan iya jure ganin wani tare dake ba, alhalin nima zan iya taimaka miki ta wannan hanyar, saboda haka ba tare da nayi shawara da kaina ba na shiga jikinki a islamiyyarku.”
He sounded ashamed, kamar yana admitting wani rauninsa. Nanne taji kanta ya d’aure, tunaninta ya hasko mata Malam Mukhtar, sanda yazo k’ofar gidansu yana gaya mata cewa Malam Murtala ya rantse cewa yaga aljani a jikinta, ashe Imran ne? Ta yaya ya ganshi a matsayin aljani? Ta yaya ma ya iya shiga jikinta? Common sense d’in kwakwalwarta na gaya mata cewa kamata yayi ta tsorata amma tambayar da take son yi ta ture hakan.
“Nayi zaton kace kuna da jiki, nayi zaton kace an canja maka jikin ne zuwa na mutane, ta yaya toh ka iya shiga jikina?”
“Na fad’a miki muna possesing wasu qualities irin na aljanu kuma mun fisu k’arfi ma a wasu b’angaren, muna iya b’atar da jikinmu yabi iska a wasu lokutan amma ba frequently ba kamar yadda aljanu suke a kullum.”
Ya k’arasa yana kallon yadda tayi shiru tana jinsa, yatsunta dake cikin nasa suna motsawa a hankali, kowacce kalma dake fita daga bakinsa ji yake kamar wani nauyi ake sauke masa, he felt free! Saboda tun daga lokacin da aka kawo ta gidansa yake son fad’a mata wannan gaskiyar daya lullub’e da k’arya, yana son ta ainihin shi waye kamar yadda itama ta bud’e masa zuciyarta ya san komai game da ita.
“Tun daga wannan ranar, na san cewa nayi wani babban kuskure saboda haka na kasa samun nutsuwa tare dani, jaamil bai san me ya faru ba, amma sai ya zab’i wannan lokacin ya kai k’arata wajen Naani, A karo na farko tun bayan zuwana na koma Muzaffar, na durk’usa a gabanta nayi mata rantsuwa ba cewa ba zan k’ara zuwa kusa dake ba.
Bayan sati biyu da hakan, jaamil yayi tafiya nemowa mahaifiyarsa maganin ciwon kanta, a wannan lokacin ne na had’u dake kin fito daga wani gida da k’unshi a hannunki, banyi miki magana ba saboda alk’awarin dana d’auka na nesanta kaina dake, amma bayan na koma gida sai naji cewa ba zan iya sawa rabuwarmu aya daga nan ba, saboda haka na dawo na baki hak’urin wannan zafin dana gani a cikin idonki, if not…i knew they will hunt me forever!
Nanne tayi shiru tana jinsa, ya gaya mata b’arin wannan gaskiyar sanda take masa tambayoyin nan, abinda kawai ya b’oye shine dalilin da yasa baiyi mata magana ba, a wancan lokacin yace saboda ya san bata kula kowa a waje ne, sai yanzu take jin ainihin gaskiyar.
“Daga nan kuma na takura kaina na goge komai naki daga cikin zuciyata don a tunanina hanyata da taki sun rabu kenan har abada, ashe wata k’addarar bata ma soma ba saboda ba’afi sati d’aya ba na tashi da wata matsananciyar rashin lafiya da ban tab’a yin irinta ba, da kyar na iya k’arasa meeting d’in da nake dashi a ranar, wani meeting mai muhimmanci kan abinda ya kaini kamfanin.
Na kira jaamil yazo yayi jinyata, muka yi ta k’ok’arin gano abinda ya same ni muka kasa, sai daga baya wani tunanin yazo masa, amma bai gaya min ba sai da yaje ya tabbatar tukunna sannan yazo ya sanar dani cewa kema baki da lafiya.”
Ya d’anyi shiru kafin ya cigaba.
“Kuma wai rashin lafiyata da taki ta faru ne saboda na shiga jikinki na bar b’arin ruhina tare dake.”
Yaji wani abu ya fad’a zuciyarsa sanda ya fad’i hakan, sannan yaji hannun Sa’adha dake cikin nasa yayi rawa, amma bai tsaya ba ya cigaba.
“Ransa ya b’aci sosai daya gano cewa har na shiga jikinki amma na b’oye masa, ya kasa karb’ar dukkan uzirina da hujjar cewa bana tab’a wasa da duk wani abu mai muhimmanci da Naani ta sani saboda haka ina sane nayi komai, bai san cewa tun lokacin da kika shigo rayuwata na rasa wannan confidence d’in ba, bai san cewa tun daga lokacin da nayi failing wajen controlling zuciyata akanki komai ya zame min sa’a ba.”
Idanunsa suka lalubo fuskarta a sannan, ta sunkuya kad’an tana kallon hannunsa dake cikin nata, so yake ya gaya mata itace abu mafi muhimmanci yanzu a rayuwarsa amma ya kasa samun k’arfin
yin hakan, yana fata ta fahimta a kowacce kalma da yake fad’a. A nutse muryarta ta fito.
Story continues below

“Nasha wahala lokacin, abubuwa suka yi ta tsoratani kala-kala, ya zama bana iya wani baccin kirki a kullum, sannan na tashi k’afafuna sun rik’e bana iya tashi, sai da Baffa ya kira wasu malamai suka yita addu’a sannan na samu sauk’i.”
“Bayan taimakon addu’arsu Nima na taimaka wajen d’orar da sauk’inki Sa’adha.”
Ta d’ago da idonta ta kalle shi.
“Lokacin da jaamil ya gane dalilin rashin lafiyar, ya gano cewa d’aya b’arin ruhin dake jikina zai iya kwantar dana jikinki zuwa wani lokaci, saboda in har suna tare ba abinda zai faru, sai sunyi nesa da juna ne sannan jikinki zai kasa rik’e wanda yake tare dake hakan yayi resulting a abubuwan dake tsorata ki. Saboda haka muka je gidanku a wannan daren kina bacci.”
Nanne ta zare idonta lokacin da kwakwalwarta ta hasko mata wannan mafarkin da tayi na farko, wanda taga siffofi biyun nan tsaye akanta, da sanda d’aya daga cikinsu ya d’ora hannunsa akan goshinta taji gabad’ya ciwon jikinta yabi iska. Kafin ta iya samun damar tambaya Imran ya cigaba.
“Bayan wannan lokacin, ina zuwa in kwantar da ciwonki duk sanda ya fara k’ok’arin tashi yana tsorata ki yayin da jaamil ke can yana kokarin gano yadda zamu ciro b’arin ruhina daga jikinki, sai duk sanda naje na kwantar da ciwon naki ina rasa k’arfi sosai a jikina wanda har hakan yake shafar kuzarina a wajen aiki.
Jaamil ya k’are bincikensa, amma bai iya samo hanyar da zamu iya ba tare da taimakon Naani ba, kuma a lokacin ta shiga bautarta na tsawon watanni biyar saboda haka ya kawo shawarar cewa in aure ki, saboda in har b’arin ruhin yana tare da d’an uwansa zai zauna ne kamar sanda yana jikina ba tare da wani abu ya faru ba.
A lokacin da naji haka nak’i yarda Sa’adha saboda girman da zancen yayi min, dukkan intrest d’in da nake dashi akanki bai tab’a gangarawa kan maganar aure ba, saboda haka nak’i yarda da shawararsa shi kuma yayi ta bina da ita, daga k’arshe har ce masa nayi ni ba sonki nake yi ba don ya kyale ni amma sai ya k’ara kafa hujjar cewa dama ba zan aure ki bane don ina sonki, zan aureki ne don in gyara kuskuren dana jawo, a haka har yaci galaba akaina na amince cewa zan iya.
Daga nan muka fara tunanin yadda auren zai yiwu, na kawo shawarar cewa dole sai kin amince dani haka ma ‘yan uwanki sannan komai zai tafi daidai, saboda haka jaamil ya bada shawarar na kad’e ki lokacin da kika je tsallaka titin nan siyo magani, ta haka na samu dukkanin wani contact dake da ‘yan gidanku, kowa ya sanni kuma muka yi healing k’afarki ta yadda baki ji zafin ciwon jikinta ba ko kad’an.
A lokacin da hakan ke faruwa, jaamil yaje yayi controlling tunanin Malaman da suka yi miki addu’a, suka je suka gayawa Baffanki cewa bak’aken aljanu ke shirin shiga jikinki kuma aure ne kawai hanyar samun sauqinki.”
Tunanin Nanne ya k’ulle a wannan lokacin, kallonsa kawai take yayin da maganganunsa ke shiga kanta kamar an tara bokiti a bakin famfo.
“Baffanki bai so yi miki aure a yanzu ba ko kad’an, don duk da k’ok’arin da jaamil yayi wajen sa zuciyarsa ta yarda da hakan, sai da yayi ta bin malamai kala-kala kuma kowannensu jaamil yana sawa su k’ara tabbatar masa da maganar dana farko suka fad’a.”
“Baffan…..” Muryarta ta fito involuntarily cikin rawa.
“We didn’t hurt him Sa’adha…wallahi ba abinda muka yi masa, jaamil yayi controlling kwakwalwarsa ne ba tare ma daya sani ba, kamar yadda kike jin tunaninki yana canjawa a cikin kanki haka komai ya faru.”
Ta kifta idanunta a hankali, tunaninta ya hasko mata sanda aka kaita wajensa sallama, sanda yake ta nasiha yana kuma bata hak’uri, Allah kadai ya san yadda yake ji a lokacin.
Imran yayi shiru don ya bata damar da zata wanke tunanin cikin kanta, yana murza hannunta a hankali cikin wani salo na rarrashi.
Nanne taji jinin dake cikin jijiyoyinta na gudu da wani irin sauri, wani irin saurin da taji dama tana da ikon da zata iya tsayar dashi, saboda hakan dad’a sawa yake taji komai ya had’e mata, sai dai yadda hannunsa ke motsawa akan nata a hankali ya shiga taimakawa wajen calming condition d’inta.
Bata san iya dad’ewar da suka yi a haka ba, zai iya yiwuwa kusan awa d’aya kafin ta iya samu dukkan maganganunsa su shiga kwakwalwarta. Bai motsa ba shima balle yayi magana yana rike da hannunta kawai, ta san a wannan lokacin bayan k’ok’arin yarda da maganganusa da tayi kamata yayi kuma taji tsoro, tsoron yadda rayuwarta ta gaba zata kasance ko abinda zai faru da ita, amma kwakwalwarta ta kasa hasko hakan, she couldn’t think of anything except that he’s touching her! hannunsa yana tab’a nata.
“Ka cigaba…” muryarta ta fito a hankali.
Taji sanda yayi ajiyar zuciya kafin shima muryarsa ta fito.
“Bayan Baffa ya tara ku ya fad’a muku cewa ya yanke shawarar aurar dake kuma ya baki wata d’aya ki gabatar masa da wani – sai naje wajensa bayan sati d’aya, Na fad’a masa labarin da kika sani kamar yadda muka tsara tun farko ni da jaamil, cewa ni d’an bauchi ne aiki ya kawo ni nan kuma iyayena sun rasu a hannun k’anin mahaifina na tashi.
Yayi maraba dani sosai sannan ya buk’aci in bashi lokaci cewa zaiyi bincike akan lamarina, bayan sati d’aya sai ya sake kirana ta hanyar yayanki Sulaiman wanda muka saba tun sanda kina asibiti, dana je ya buqaci in turo da iyayena suyi magana saboda haka jaamil ya sake yin aikinsa, ya turo dattijan mutane irin wanda ya san Baffa zai ga girmansu ta hanyar rufe masa ido amma a zahiri babu kowa, babu wasu mutanen da suka je.
A wannan lokacin na d’auki hutu naje Maldives. Wajen da tunda naje ba abinda nake iya tab’ukawa sai tunaninki Sa’adha, duk da cewa inata ture hakan daga zuciyata amma na kasa, tunanin yadda zaman mu zai kasance kawai nake, yadda zan iya rayuwa dake a matsayin matata alhali ba jinsinmu d’aya ba, tsoron cewa zan iya cutar dake ne yafi yawa da kuma tunanin yadda zanyi controlling zuciyata akanki.
Saboda a lokacin ina kokarin sawa zuciyata ta yarda da kalaman jaamil ne, na cewa sai na ture dukkan intrest d’ina akanki don zamana dake ba mai d’orewa bane, zai k’are a duk ranar da Naani ta dawo ta raba ruhina dake.”
A daidai nan, yayi shiru yana shak’ar kamshin jikinta da kuma na gashinta wanda ya fito ta k’arshen d’ankwalinta, a lokaci d’aya kuma yana sauraren bugun zuciyarta, wani lokacin sai ya buga da k’arfi wani lokacin kuma ya tsaya gabad’aya, bayan wani lokaci sai ya koma daidai ya cigaba da bugawa a normal rate d’in da ya saba, a wannan lokacin ya fahimci cewa bugun zuciyarta shine sauti mafi muhimmanci a rayuwarsa.
Duk cikin wannan lokacin bata motsa ba, saboda haka bayan ya tabbatar kwakwalwarta ta gama absorbing kalamansa na baya, ya cigaba.
“A sannan jaamil ya kira ni da cewar lokaci yayi, saboda haka hutuna bai k’are ba na tattaro na dawo. Bayan dawowata na sake zuwa na sami Baffa, shi ya bani ranar da zanzo in same ki, saboda haka na kira ki na tambaya, amma dana zo kika hana ni ganinki.
A wannan lokacin na fahimci cewa bayan had’in kan Baffa da muka samu, dole ne kuma sai na nemi naki in har ina so abubuwa su tafi mana daidai, ba tare da son ran jaamil ba na dinga kiranki a waya da duk wata hanyar dana san zan shawo kanki, har na fara koya miki yadda zaki so ni kamar yadda na fad’a miki.”
“Saboda me?” Ta tambaya.
Imran ya kasa gane dalilin da yasa ta tambaya, bata san cewa b’acin ranta koya yake can cause him physical pain ba? Bata fahimci cewa yana k’aunarta fiye da tasa rayuwar ba?
“Sa’adatu.” Ya kira full name d’inta yadda zata fahimci cewa he’s so serious, ya d’ago da d’aya hannunsa da baya rik’e da nata ya kamo gefen fuskarta.
“Ba zan tab’a iya rayuwa mai kyau ba in har na zama sanadin abinda zai dame ki, you don’t know how it tortured me to see you hurt.”
Nanne ta sake damk’e hannunta dake cikin nasa tana kallonsa, ya lumshe idanunsa a hankali by the pleasure, zai sake magana tayi saurin tsayar dashi ta hanyar d’ora yatsunta akan lebb’ensa, Bayaninsa bai kai k’arshe ba, akwai sauran abubuwan da suka rage itama kuma akwai sauran tambayoyin dake cikin kanta, amma wannan kalaman nasa ya ture komai, taji iya su kad’ai sunyi convincing zuciyarta sun ture duk wani sauran duhu dake cikin kanta game dashi.
A hankali tana kallon idanunsa da suke kyallin silver har yanzu tace.
“You are the most important thing to me too! the most important thing to me ever Ulfat!”
“Kin gansu koh?” Inna ta tambaya daga falo zaune akan dardumarta.
“Eh na gansu, ashe suna da d’an yawa ma.”
Nanne ta amsa sanda ta dawo cikin falon ta zauna a kusa da ita.
“Toh na nan ne masu yawan kenan, ai na zata na wajen Azumin sune suka fi yawa.”
“Au wai da akwai wasu ma a wajen mama Azumi?”
“Akwai mana, wad’annan ai ina jin na wajen Nuratu ne da suka kawo ran d’aurin aure da kuma na sauran mutanen da suka dinga kawowa daga baya, toh na wajenta kuma ina jin sune ragowar wanda su Nafisa suka je kasuwa aka manta ba’a kai ba.”
Nanne ta mik’a hannu ta d’auki sala d’aya na lemon dake gaban Innan kafin tace.
“Wallahi dama an barsu anan kawai, ki dinga yin gudunmawa dasu tunda a can d’in ma fa sai kiga wani abin har guda biyu iri d’aya.”
“A’ah, d’iban kayanki zaki yi ki tafi dasu ni yaushe zan d’ebi kayan kitchen in tafi kai gudunmawa, ai duk wanda zan bawa gudunmawa yanzu kud’i yake zato daga gurina.
Kuma kayan har fa da wanda su Nuratu suka kawo, me zai kaini tab’a su? a ranar ma da zasu tafi har tambayar su maryamah suka yi wai ko su tafi dasu ne tunda zasu je gidan naki kafin su wuce tace musu su barshi za’a kai, nayi ta fad’a da tazo ta gaya min anan, nace don me zata hana su, su kwashi tarkacensu mana suyi gaba idan gani suke zamu rik’e wani abin zamu yi, in banda ma…..”
Nanne kawai murmushi take tana kallonta, tayi missing hirar nan tata kamar me? yadda zasu zauna irin yanzu wajen k’arfe d’aya kafin tafiyarta islamiyya suna ta hirarrakinsu, na ‘yan uwa da kuma yanayin zamantakewar yau.
Tun wajen k’arfe tara na safiyar yau da Imran ya ajiyeta a k’ofar gidansu take jin wani canji a zuciyarta, gani take kamar ta dawo duniya ne daga can wani baqon wuri da aka kaita, sanda ta shigo taga inna kuma sai kewar komai ta dad’a kamata, ta rungumeta da k’arfi su mama Azumi da suka rako ta tun daga tsakar gida suna ta fad’in wai zata b’allata, amma itama innan bata damu ba, ta rik’e ta sosai tana ta lale maraba da Amarya.
Da kyar ta iya barin d’akin ma taje ta gaishe dasu hajiya Babba, kowa sai fara’a yake mata ana kuma bata wani girman da a da bata san dashi ba, don mama rabi wai harda rako ta bakin kofa, matar da a da kanta a d’age take amsa gaisuwarta.
Babban abin mamakin data gani shine daga wurin yayyenta maza, duk wanda ya lek’o yiwa Inna sallama zai fita, in ya ganta sai ya tsaya su gaisa, a baya kuwa wani ma hamb’are kafarta zaiyi ya shige wajen innan.
‘Yan biyu ma da suka shigo bayan sun tashi daga baccin asarar su Saleem da murmushinsa yayi ta tambayarta ya sabon waje da kuma mijinta, Suraj ne kawai ya d’an mata wani guntun murmushi daya d’auke in second sannan yace ‘kin zo dama.’
“Yanzu Inna to ke kad’ai kike kwana a d’akin nan?”
Ta tambaya sanda take taya innan rarraba goron da take bayarwa a kai masallaci sadaka duk ranar juma’a.
“A’ah bayan tafiyar su maryamah ai Azumi nan ta dawo, tare muke kwana kiga mu sha hirar mu ma har dare ya raba.”
“Kai Inna, wai harda kusha hira…irin kin samu wadda ta fini d’in nan.”
Ta fad’a kamar zata yi kuka.
“Yo kiji min ‘ya, ke ba wanda ya fini d’in kika samu ba? yanzu da za’a ce kizo ki kwana biyu ai ba yarda zaki yi ba.”
“Haba dai Inna, wallahi ba’a fad’a d’in bane.”
Ta fad’a tana d’aukar wani lemon, sai dai me? duk yadda ta kai ga d’okin gidan ana yin sallar la’asar taji ta fara tunanin sanda Imran zai zo su tafi, sau da yawa tana irin wannan dad’ewar bata ganshi ba in yana wajen aiki, amma yau da banbanci, a wani waje take da ba inda zai dinga tuna mata da abubuwansa, inda ya zauna yayi wani abin, inda yayi magana, abinda ya d’auka ko kuma inda ya tsaya yace mata wani abun.
Story continues below

Rahma ma tazo sun sha hira amma duk inda ta kai ga jin dad’in hirarsu ita da Inna, tunaninta yana zamewa wajen hasko mata wad’annan kyawawan idanun nasa da yake yawan lumshe mata su, ko muryarsa, ko yadda yake rik’eta, dama sauran tarin ‘yan k’anan abubuwan da bata san tana lura dasu ba.
Da gaske ne ta yarda cewa rayuwarta ta canja, tun daga lokacin da aka d’auketa aka kaita gidansa, rayuwarta ta canja ta hanyar da baza ta iya fassarawa ba sai dai kawai wanda ya san irin hakan ya gane.
Wajen k’arfe biyar, Sadiq ya shigo d’akin da tsokanarsa yana fad’in.
“Yan mata ta zama matar aure…!”
Nanne ta juya idonta tace.
“To ya ranka? girma ne dai dole yanzu Allah ya riga ya bani kuma inda mutunci ma kamata yayi ka dinga kirana da Aunty, tunda yanzu ka san na wuce ajinka.”
“Wallahi ba matsala…” ya fad’a yana zama a kujerar da take kai.
Suka kyalkyale da dariya har Inna kafin ta d’auki filo ta maka masa.
“Toh ina d’an handsome mijin naki? Kin san kwanaki su Abubakar d’in bayan layin nan suka tare ni wai dan Allah in gaya musu a ina kuka had’u, wai sun san gayen tun zuwansa unguwar na ba wadda yake kulawa, maza ma sallama ce kawai ke had’a su.”
Tace. “Toh me kace musu?”
Nanne ta sake kyalkyalewa da dariya.
“Kuma sun yarda?”
“Wallahi sun yarda, harda cewa wai zasu sa rana in raka su suma, na bisu da toh kawai.”
A cikin hirarsu Inna ta tambayeta sanda zasu dawo daga tafiyar da tace mata zasu yi.
“Inna wallahi ban sani ba don bai fad’a min ba, kawai yace in gaya muku zamu yi tafiya.”
“Ina zaku je?” Sadiq ya tambaya.
“Nifa ban sani ba, amma tunda da waya duk inda muka je zan kira ai.”
“Kaga hajiya Amarya, wato honeymoon d’in ma baza’a fad’i ina ne ba don kar a dame ku.”
Ta sake d’aukan filo ta maka masa.
“Ni nace maka honeymoon zamu je.”
Inna tace.
“Duk inda dai zaku ya kamata a sani, tafiya irin wannan da zata iya yin nisa.”
Sai bayan sallar isha sannan Imran yazo, ya d’an dade tare da Inna suna hira sannan yaje ya gaishe da baffa, kamar yadda yayi ta addu’a da sawa Nanne albarka haka shima yayi tayi masa, tare kuma da kallon da Imran ya fassara da cewar Ka kula da ita.
I will, da dukkan iyawata Baffa! Shima ya amsa da idanunsa.
Aka lodawa Nanne kayanta a mota sannan suka tafi bayan Inna tasa tabi su hajiya Babba duk tayi musu sallamar tafiyar da zasu yi.
“Kayan meye wannan?”
Imran ya tambaya sanda suka hau titi.
“Kayan ka ne.”
Ya juyo sosai ya kalleta.
“Ni kuma? a ina na sami wannan kayan?”
Tayi dariya kafin tace.
“Wasa nake yi fa, wai ragowar kayan da ba’a kai min bane, yawanci ma na amfanin kitchen ne.”
Yana jin haka ya maida idonsa titi, fuskarsa ba alamun murmushi balle dariya, Nanne tayi sensing wani abu na damunsa saboda haka tace.
“Ka san cewa kafi kyau in idanunka suka zama so light.”
Kafin yayi magana tunaninta ya dawo mata da amsar daya bata kwanaki biyu da suka wuce, sanda ta tambayeshi game da idonsa dake kyallin silver.
“Shine na farko da kika fara gani Sa’adha, a yanayin halittar mu, mood d’in mu yana reflecting ne a idonmu, I’m being myself aroud you now, zan dinga sakewa duk sanda ina tare dake akan k’ok’arin b’oyewar da nake a baya, Saboda haka zaki ga yanayin idona na canjawa a lokuta da yawa.”
A yanzu kuma taga sanda ya ciji lebb’ensa kafin yace.
“Wane color yayi yanzu?”
“Dark. So dark!”
Ya sake datsa lebb’ensa.
“Ban san me nake ji bane Sa’adha, I don’t know what I’m feeling, ‘yan gidanku sun yarda dani da yawa alhalin ina yaudararsu ne…kowannensu yana min kallon wani mutumin arziki, Wallahi bana son abinda nake Noory.”
Nanne ta maida kanta gefe tana kallon titi, ita kanta a lokacin da Inna ta tambayeta game da zancen ‘yan uwansa, da kyar ta iya lalubo karyar da tace mata sun zo basu dad’e bane suka koma garinsu.
Zuciyarta tayi nauyi da tunanin, in har su Inna suka ji gaskiyar WAYE Imran ya zasu yi? ya zasu ji in suka san wa suka aura mata? in har akwai matsalar da take hangowa a zamanta da Imran, bai wuce yadda zasu yi ta lullub’e komai ga iyayenta da ‘yanuwanta ba, amma ita ta riga tayi deciding zuciyarta, ta tsaida ita a waje d’aya…zata zauna da Imran a kowanne hali in har ba zai cutar da ita ba.
Tana son shi, kuma tana sonshi har cikin zuciyarta!
********
“At least ka d’an bani hint mana, ko don in san irin kayan da zan d’auka.”
Nanne ta fad’a tana kallon Imran dake kwance akan gado yana cafe kayayyakin da take jefowa daga cikin wardrobe, ya d’ora kafarsa akan d’aya, sannan hannunsa d’aya cikin gashinsa.
“Hint kike so? toh dogwayen rigunan ki ma zasu yi, akwai musulmai a inda zamu je.”
“Musulmai? wane yare suke yi?”
“Kala-kala, amma karki damu za’a samu wanda kika iya.”
Ta matso kusa da gadon tace.
“Toh farare ne ko bak’ake mutanen wajen?”
Ya d’age girarsa d’aya yace.
“I think suna da haske.”
Nanne ta tsuke baki tana kallonsa sanda durk’usa a gefen gadon rike da wani pink mayafi.
“Toh wajen zafi ne dashi ko sanyi?”
Ya d’an tsaya yana kallonta.
“Wai wayo kike son yi min?”
Ta karkata kanta kad’an.
“Ta ya zan maka wayo so nake kawai in sani…”
“Mhmm-Mhmm baby girl, wannan k’ifta idon ba zaiyi tasiri akaina ba…”
Ya karb’e mayafin hannunta sannan ya jawo ta kan gadon.
“…In kina son ki san inda zamu ki bari gobe insha Allah zaki fara gani.”
“Fara gani ba waje d’aya bane kenan?”
Imran ya juya idonsa, sannan ya mik’a hannunsa sama ya kashe switch d’in d’akin.
“Enough talking for today, in ba haka ba zaki sa in fad’a miki komai da komai yanzu.”
“Ban k’arasa had’a kayana ba fa.” Ta fad’a a cikin duhun.
Ya lalubi gefen kunnenta ya rad’a mata a hankali.
“Wanda ya shiga cikin akwatin sun isa Sa’adha, beside bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can.”
Ta lumshe idanunta tana shak’ar k’amshin jikinsa.
“I give up Ulfat! na hak’ura da sani Allah ya kaimu goben.”
“Ameen Habibty.”
Bayan kamar minti talatin, har Imran na tunanin tayi bacci, yaji muryarta ta kira shi a hankali.
Can k’asa-k’asa ya amsa shima kamar ya fara bacci. Ta b’alle buttun d’in gaban rigarsa a hankali sannan tace.
“Naani ba yanzu zata dawo ba, kuma kafin ta dawo we will figure a way out, ba abinda zai faru insha Allah Sa’adha, kuma ba zan tab’a rabuwa dake ba.”
Wannan sune kalaman Imran na jiya da suka kwantar da hankalin Nanne kuma suka bata kwarin gwiwar tashi a yau ta kammala komai na tafiyarsu, ta gyara gidan ta rurrufe komai da ta san zaiyi k’ura. Karfe goma sha biyun rana tayi musu ne a cikin airpot, har Imran ya gama duk wasu shige da ficensa tana tsaye bata san inda zasu ba, sai da suka shiga cikin jirgin ne sannan ta tambaye shi.
“Zamu dad’e bamu dawo ba?”
Maimakon ya bata amsa sai ya kamo hannunta cikin nasa ya murza a hankali.
“I love you!”
Hakan ya tabbatar mata cewa ba zata sami amsarta ba, saboda haka ta kwantar da kanta a gefen kafad’arsa kafin a hankali tace.
“That’s why we’re here.”
*******
“Lagos..?”
Nanne ta tambaya sanda suka sauka daga jirgin bayan tafiyar kusan awanni biyu.
“Itace hanyar da zamu bi ta farko.”
Ya fad’a da murmushi sanda yaja hannunta suka nufi hanyar building d’in terminal, anan bayan wasu cike-ciken da kuma b’ata wani lokacin suka k’arasa international counter inda suka yi boarding wani flight d’in.
“Australia?” Ta sake tambaya sanda ya karbi tickets d’in suka mik’e wata hanya.
“Itace hanyar da zamu bi ta biyu.” ya fad’a da wani murmushin.
Tafiyar daga lagos zuwa Australia awa bakwai ne, but it was comfortable tunda suna zaune ne a fad’ed’en seat d’in first-class. Abinda ya sata tunanin irin kud’in da Imran ke dashi.
Ta kira a hankali tana kallon hannunsa dake nannad’e a cikin nasa, Babbar hanyar communication d’insa, sau da yawa zasu zauna suyi shiru amma in har hannunsa na cikin nata, sai taji kamar magana suke yi.
Sai da Imran ya d’anyi shiru sannan ya fahimci sabon sunan da ta kira shi dashi, wani dad’i ya ratsa shi, yayi murmushi kad’an sannan ya amsa.
“A ina kake samun kud’i, na zata tunda baka dad’e da shigowa cikinmu ba, bai isa ka tara kud’i da yawa ba.”
The question is so silly, Yayi k’ok’arin kar yayi dariya amma ya kasa hana kansa.
“Na gaya miki Naani ta tanadar min komai kafin zuwana, akwai account guda da dimbin kud’i wanda a lokacin ban san adadinsu ba, sannan tunda na fara aiki, ina samun kud’i a kowanne wata da har wani amfani nake dasu sosai ba.”
Ta gyada kanta alamun ta fahimta. Ya matso da bakinsa dab! da kunnenta sannan a hankali yace.
Tayi murmushi tana b’oye fuskarta a jikinsa. Zuwa can ta d’ago ta kalle shi.
“Ka tuna ranar da ka maida ni gida da daddare?”
Ya d’anyi shiru kafin ya amsa.
“I dont want to talk about it, bana son tuna wannan ranar habibty.”
“Saboda me?”
Saboda mutanen nan. Ya amsa a cikin kansa, mutanen daya kasa d’aukan wani mataki akansu saboda ita, saboda kar taji tsoron da zai sa mata wani zarginsa a lokacin.
Amma yaso ko da motarsa ne ya take su, ko kuma ya shak’e wuyansu ta yadda k’ashin wajen zai kakkarye, ko yayi ta marin su har sai jinin jikinsu ya gama fita ta baki. He wanted to kill them so bad, yadda duk sanda ya tuna hakan sai yaji kamar zai danne hak’oran bakinsa har sai sun marmashe. Bata damu da rashin bata amsa da yayi ba ta zarce da tambayarta.
Story continues below

“Ranar ma yana cikin tsarinku?”
Ya girgiza kansa da sauri.
“Baya ciki ko kad’an, i swear to you k’addara ce kawai ta had’a ni dake a ranar, naje gidan wani d’an office d’inmu ne a hanyar daya takura mana da gaiyata ni da sauran mutanen office d’in, tun yamma ma muka je muka kai har bayan maghrib, ni na riga su fitowa shine lokacin da na hango ki a hanya…”
Ya kasa k’arasawa saboda tunanin wad’annan mutanen.
“Lokacin da ka kaini wannan chemist d’in? k’arfe tara da minti goma sha biyu amma har na koma gida tara da minti ashirin, ta yaya hakan…”
“I was driving so fast…” Ya katseta.
“…Na kare idanunki ne kawai daga gani amma sauri nake yi sosai, saboda bana so hankalin Inna ya tashi duk da cewa Sulaiman ya fad’a mata.”
Ya fad’i kalaman da gaskiya har cikin zuciyarsa, ya riga yayi wa kansa alk’awari ha zai sake b’oye mata komai ba a zamansu zai fad’a mata dukkanin amsar da take nema da dukkanin gaskiyarsa sai dai banda abu d’aya.
Abu d’aya daya san cewa yafi k’arfin tunaninta, abu d’aya da in ta sani zai zama sanadin rasa nutsuwarta, abu d’aya da zai sa ta daina sakewa dashi, ba zai tab’a iya fad’a mata cewar Naani ta dawo kuma baza’a iya raba ruhinsa da nata ba tare da a rasa ransa ko nata ba.
Tun tana masa tambayoyi kala-kala na wasu ‘yan k’ananan abubuwan da bata fahimta game dashi ba har tafiyar ta mik’a bacci ya kamata, wani bacci mai nauyi da bata ko farka ba sai lokacin da suka isa k’asar Australia, da daddare ne lokacin saboda haka bayan sun sauka da kyar take iya bud’e idonta a cikin hasken fitulun dake dallare a ko’ina, kwata -kwata bata san abinda Imran keyi ba, kawai janta yake yi tana binsa a cikin hayaniyar Airport d’in mai cike da yare kala-kala a lokaci d’aya kuma tana k’ok’arin bud’e idanunta.
Bayan kamar minti talatin suka yi connecting to wani jirgin da bata san ina ya nufa ba don suna shiga ta sake k’udundunewa a jikinsa ta koma baccinta.
Sai bayan kusan awa biyu sannan ta farka, har a lokacin basu sauka ba, ta tsakuri abinda zata iya ci a cikin abincin da a kawo, sannan ta shiga tambayarsa inda zasu je kuma, amma yak’i fad’a mata kuma ya hanata ganin takardun airport d’in dake hannunsa.
Haka ta hakura ta sake langab’ewa a jikinsa tana jin kowacce gab’ar jikinta na amsawa sakamakon kusan zaman awa goma a jirgi, ta tabbata yanzu a Nigeria tsakar dare ne su da suka taso tun wajen karfe biyuna rana.
Lokacin da jirgin ya sauka bayan tafiyar awa uku da ‘yan mintuna, Nanne ta ware idonta ganin k’aton signboard mai d’auke da haken fitilu dake ta dallare ta yana walk’a kalmomin.
“Ina ne kuma Male?”
Ta tambaya sanda aka gama X-ray d’in kayansu wani bature mai uniform ya d’ora su akan gurney ya biyo bayansu.
Yayi murmushi yana kallonta kafin yace.
“Itace hanyar da zamu bi ta uku!”
Daga haka bai k’ara mata magana ba ya rik’e hannunta har suka fita daga cikin airpot d’in, wannan mutumin na ta binsu ture da gurney d’in.
Nanne in banda zare ido tana kallon mutane ba abinda take, jinsi ne kala-kala na dangain fararen mutane ke ta harkokinsu, tsilli-tsilli kawai take hango bak’ar fata shima ba irin wanda ta saba gani ba, don fararen ma gani take kamar ba’a gaske take ganinsu ba, das-das dasu, ga gashi yala-yala daga mazan har matan.
Da yawansu sanye suke da dogwayen riguna irin na jikinta, wasu matan ma harda Niqab so she didn’t felt so different in banda fuskarta data kumbura sakamakon baccin data sha. Ta tuna maganar Imran a jiya ne ko shekaranjiya.
Story continues below

“…dogwayen rigunan ki ma zasu yi, akwai musulmai a inda zamu je.”
Saura kad’an tayi tuntub’e ba don yana rik’e da ita ba sanda ta hango wata ‘yar yarinya fara tas! mai bak’in gashi dogo, kayan jikinta masu kyau harda wata ‘yar karamar jaka ta goya a bayanta, ita da mamanta ne maman nata waya ita kuma tana tsaye a kusa da ita sai ‘yan juye-juyenta take, taji kamar ta koma ta d’auko ta ace ma an bar mata ita har abada.
Sanda suka fita can harabar airport d’in, Imran ya d’auko wayarsa data lura ya canja sim tun a cikin jirgin ya kira waya cikin wani yare da bata idea wanne ne. baifi minti biyu ba, wata shuttle bus ta k’araso inda suke, mai gurney d’in nan ya saka musu kayansu Sannan suka shiga, babu kowa sai driver da yake kamar bafaranse don ta tsinci wasu ‘yan kalmomi a maganar da suka yi shida Imran, mamaki take yi na adadin yaren daya iya.
“Mun kusa insha Allah Noory” Ya fad’a yana kamo hannunta, bata ce komai ba sai murmushi kawai data masa.
Motar ta cigaba da tafiya ta cikin manya-manyan titunan masu d’auke da fitulu rutu-rutu da kuma mutane, mutanen da Nanne ke gani wasu iri a idanunta, a hankali kuma yawansu dana gine-ginen ya ragu har suka k’araso edge na titin, a gabansu duhun wani k’aton ruwa ne daya mamaye gabansu gabad’aya.
Motar ta tsaya a k’arshen wani titi daya tsaya a daidai hanyar da zata d’auke ka zuwa port d’in dake gabansu, ‘tashar jiragen ruwa’ gasu nan fal manya da k’anana, wadu daga can nesa a cikin ruwan wasu kuma a tsaitsaye.
Nanne taji ta had’iye yawu sanda ta d’aga ido ta hango wani tafkeken jirgin a tsaye cikin ruwan, taji wani imani ya ratsa ta ganin yadda duk girmansa yake tsaye a cikin ruwan ba tare da nutsewa ba. Imran ya rik’e hannunta zuwa wata doguwar hanya ta katako data kaisu can bakin ruwan, yana ta magana da mutane kala-kala cikin yaren da bata ganewa. Daga k’arshe suka ka’rasa wajen wani d’an madaidaicin jirgi fari tas dashi, sai kyalli yake alamun sabunta, aka saka kayansu da wani ya d’auko lokacin da matukin jirgin ke warming d’insa.
Ya juyo ya kalleta a hankali tare da mik’o mata hannunsa d’aya.
“Bismillah…”
Nanne ta jiya ta kalli k’aton tekun dake gabansu, bakikirin ba wani alamun haske, ga manya-mayan jirage a cikinsa ga kuma iska na kad’awa kota’ina, sanna ga tarin fararen mutanen da bata taba ganin irinsu ba. Ina zasu je a cikinsa? Sai kawai ta girgiza kanta da sauri.
“Ba zan iya ba, ba zan iya shiga cikin ruwan ba, ina zamu je a cikinsa?”
A hankali take taka marbles d’in cikin gidan mai wani irin santsi da barefoot kafafunta, Saboda ta ajiye takalminta tun a cikin jirgin nan, sanda ta fara fitowa ta nutsar da k’afarta a cikin yashin beach d’in da aka sauke su mai sanyi, a haka ta k’araso har cikin d’an k’aramin gidan da Imran ya nuno mata a matsayin inda zasu zauna bayan ya fito daga reception d’in da yayi musu booking.
Tana tafe tana barin d’igon yashin a duk inda ta taka sannan tana kunna fitulun kowanne corridor, mamaki take na yadda gidan yake da girma fiye da yadda ta ganshi ta waje, tana ganin komai kamar a irin mafarki ko irin tunanin yadda take hango Aljanna a idonta, saboda haka yadda zuciyarta ke bugawa cike da d’oki yasa komai ya zama blurry a idonta.
Dogowar hanyar data bi daga inda yayi kama da falo mai d’auke da luntsuma luntsuman kujeru guda biyu da k’arama d’aya, ya kaita wata k’atuwar k’ofa data ganta ‘yar mitsitsiya a gabanta, tasa hannunta a hankali ta tura ta sannan ta kunna switch d’in fitila dake jikin bango a gefe.
D’akin k’ato ne kuma komai na cikinsa fari ne tas! daga kan furnitures d’in har carpet din dake gaban gado, bedsheet, labulaye da kuma fentin komai fari ne, sannan bangon k’arshe dake gefen gado na glass ne gabad’aya dake nuna glistening view d’in waje, amma bata lura sosai da nan ba hankalinta yafi tafiya kan k’aton gadon dake tsakiyar d’akin, ta matsa ta tab’a lallausan bargon dake kai sannan ta danna hannunta ciki, she wanted to be sure everything was real!
Bata jin ko a hoto ta tab’a ganin waje mai kyau irin wajen nan, ta dinga zagaye d’akin tana tab’a komai cikin mamaki, akwai tarin kayan electronics harda wanda bata san amfaninsu ba, ta tura k’ofar inda ya mata kama da toilet ta shiga, toilet din ne kuwa, sai dai cikin wata irin haduwa da bata taba gani ba, drawers koina kamar kitchen sannan wai harda wani center carpet a tsakiya, abu d’aya idonta ya gane da wuri shine bathtub, amma sink ma da kyar ta iya lalubo shi tsakanin drawers d’in.
Akwai wasu irin dogwayen tagogi daga gefe, ta bud’e guda d’aya a hankali, hasken wata daga sama ya haske beach d’in dake can gabansu da kuma ruwan tekun, yashin wajen yayi wani haske a idon mai kallo sannan ga wata iska mai dad’i tana kad’awa.
A sannan ne ta jiyo maganganun Imran shida Room service d’in daya d’auko kayansu daga can reception din, ta rufe windon sannan ta fito daga cikin toilet d’in.
Daidai sanda shima ya bud’e k’ofar d’akin ya shigo.
“Do you like white?” ya fad’a yana k’arasowa dab da ita, ta d’aga fuskarta kad’an tana kallon tasa.
“Kai kayi choosing colour?” Numfashinta ya busa a fuskarsa, tana ganin yadda ya lumshe idonsa kafin ya amsa.
“Na zata kina son fari.”
“Ina son kowacce colour Ayunie, white is great, also this place is great.”
Gefen kumatunsa ya lotsa alamun yaji dad’in maganarta.
“Baki ga komai ba Noory, zan nuna miki duk sauran abubuwan da nayi wancan karon.”
“Ka tab’a zuwa dama?”
“Na tab’a zuwa lokacin dana d’auki hutu sau d’aya, amma tun a lokacin ba komai na iya yi sosai ba saboda tunaninki.”
Sai ta sunkuyar da kanta k’asa tayi murmushi.
“Yanzu kije kiyi alwala muyi Sallah.”
Magriba da Isha, abinda take tunani itama kenan, tunda sunyi azahar da la’asar tun a Nigeria da zasu taho. Kafin ta motsa taji ya lankwaso da kansa cikin wuyanta, lips d’insa suka yi brushing a gefen mak’ogwaronta daidai k’asan kunnenta, ta rufe idonta sannan ta damk’e yatsun k’afarta da k’arfi, kamar ya gani sai yayi dariya a hankali numfashinsa mai d’umi yana busawa akan fatarta.
Story continues below

Da sauri ta d’an ture shi ta juya ta koma cikin toilet d’in tayi alwalar, akwai dogwayen hijabanta guda biyu a cikin akwatinsa da tasa saboda nata ya cika, d’aya daga cikinsu ta d’auko ta saka yayi musu jam’in sallolin guda biyu .
Bayan sun idar order d’in abincin da yayi daga can reception d’in da suka fara tsayawa ya iso, akwai abubuwa da yawa amma in banda snack d’in samosa da fried naman kaza ba abinda Nanne ta gane a ciki toasted bread da ta gani guda uku.
Sai dai duk sauran abubuwan nan da bata gane ba, haka Imran yayi ta d’ura mata su yana cewa taci shima k’arin experience ne, wani ta had’iye da kyar wani kuma ta fito masa dashi, haka zai sa hannunsa ya k’arb’a bai ko damu ba.
Ita dai har a lokacin dad’a kallon wajen take tana gayawa zuciyarta cewa ta yarda ba mafarki take ba.
********
“No…!”
Nanne ta fad’a tana zare idanunta.
“Yes.”
Imran ya fad’a tsaye daga bayanta, suna tsaye daga wani balcony da ya fito ta cikin falon inda akayi wani d’an karamin pool da aka jawo ruwansa daga cikin tekun sannan ga grass carpet mai taushi da kuma flowers da fitilu masu haske kala-kala a wajen, wajen yayi kyau it felt like a dream to her! Har yanzu gani take kamar ba da gaske itace a wajen ba, kamar zata iya bud’e ido a kowanne lokaci ace mafarki take yi.
Dazu taga k’ofar amma bata tab’a tunanin cewa wani wajen ne ba, tayi zaton toilet ne ko kuma d’an store kawai. Bata san sanda ta juyo da sauri ta kalle shi ba tace.
“Please Ulfat zamu zauna anan har abada?”
Ta fad’a tana kifkifta masa idonta alamun rok’o.
Yayi dariya mai zurfi yana kallonta.
“In kina so me zai hana, amma me zaki cewa su Inna?”
Inna. kiran sunan da yayi ya sata tuna cewa bata kira su ba.
“Ya salam! Ayunie ban kira su ba, ya kamata ace na kira su na fad’a musu inda muke tunda muka sauka.”
Yayi saurin rik’ota sanda take kokarin komawa ciki.
“Kin san k’arfe nawa yanzu?”
Ta janyo d’aya hannunsa dake rik’e da wayarsa ta kalli agogon.
“K’arfe tara fa ai bata kwanta ba yanzu.”
“Wannan setting d’in k’asar nan ne saboda na canja Sim amma k’arfe hud’u na asuba yanzu a Nigeria.”
“Huh..?” Ta ware ido tana kallonsa.
“Ko so kike tayi tunanin wani abun?”
Ba tace komai ba ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta.
“Zamu kira ta first thing zuwa gobe, yanzu kin gaji da yawa Sa’adha, kije kisa ruwan zafi a jikinki kizo mu kwanta.”
Ya Allah, kunya ta kamata sanyin iskar wajen gabad’aya yasa ta manta da wani abu wai shi wanka. Ta d’aga kanta a hankali ba tare da ta kalle shi ba.
A minute alone would be perfect!
“Ko muje ne in taya ki?”
Bata san sanda ta kalle shi da sauri tana zare ido ba, ya sake yin dariya cikin husky voice d’insa, sannan yasa kansa cikin wuyanta, wani waje dake fitting d’insa perfectly.
Ya rad’a mata wani abu da muryarsa data koma can k’asa yadda taji kamar yana lasar fatar jikinta ne, taji k’afafunta sun daskare a wajen kamar k’ank’ara, tunaninta ya gwamutse a lokaci d’aya kuma kwakwalwarta ta kasa tab’uka wani tunanin.
A haka yaja hannunta suka koma ciki har bakin toilet d’in.
“I’m waiting for you.” Yaja saman hancinta sannan ya juya ya koma ciki.
Tabi bayansa da kallo kafin ta tattaro dukkan k’arfinta taja numfashi cikin k’irjinta, sannan ta kalli kafad’arta don taga ko ta kama ne da wuta, don hakan wani abu ne da Imran bai tab’a mata ba, kullum tana jikinsa amma tun lokacin da ta tashi da wannan marks, ya daina mata irin wannan abubuwan. Taji a cikin ranta cewa wajen zai k’ara kusanci a tsakaninsu.
Babu wutar a kafad’arta, atleast babu a fili sai ta cikin fatarta da take jin wajen kamar an d’ora gaushi, ta lalubo jakar toiletries d’inta sannan ta koma toilet d’in, sai dai tana bud’ewa taga ta manta brush dinta, saboda haka ta shiga bud’e drawers din anan wani mamakin ya kamata, akwai komai da aka san d’an adam na iya buqata a harkar toilet, brands kala-kala masu kyau bama irin na Nigeria ba.
Saboda haka ta zuge jakarta ta ajiyeta a gefe, don ba ta yadda za’a had’a kyan kayan da nata, ta d’auko wani shampoo mai ainihin k’amshin extract d’in strawberry ta wanke gashinta tsaf sannan tayi wanka, shi kansa ruwan wani irin santsi ne dashi akan fata, bayan ta gama ta d’auko wani katon towel a cikin drawer ta nannade jikinta sannan tasa wani karami ta tsane ruwan kanta, ta jona hand dryer ta taje gashinta, yayi d’umi ya kwanta smoothly har gadon bayanta.
Sanda ta fito ta bud’e akwatinta, wani mamakin ya kamata, gabad’aya kayan da ta san ta jera da hannunta babu su, instead kayan da bata tab’a gani bane, k’ananan riguna da three-quarter skirts da wando, bayansu sai kayan bacci kala-kala masu mutuk’ar kyau.
Undies d’inta da kuma wasu dogwayen riguna uku na material sune kad’ai abinda ta sani nata. Ta fiffito da kayan, gabad’ayansu sababbi ne da tag d’insu, bata san yaushe ya siyo ba kuma bata san yaushe ya canja su da kayanta ba, ita kad’ai amma kunyar kayan ta kamata, ta tuno da abinda ya fad’a mata a gida.
“…bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can.”
Da kyar ta iya zab’ar wata rigar mai gajeren hannu kalar Pitch da kad’an ta wuce gwiwa ta saka, Ta juya wajen mirrors d’in dake kan wani dogon counter a gefenta, ai kuwa tana kalla ta juya da sauri ta juyawa mudubin baya, gaskiya ba zata iya fita a haka ba, ita da ta saba kullum cikin dogwayen rigunan barcinta…ta koma cikin akwatin ta d’auko doguwar rigar material d’inta guda d’aya, toh ai kuma yanzu dare ne, ta yaya zata zumbula wannan rigar ta kwanta?
Sai kawai ta zauna akan sassayan tiles d’in d’akin ta cusa kanta a tsakanin k’afafunta, tana ji ne kamar zata fita cikin dubunnan jama’a wad’anda suke jiranta ba tare da ta san me zata fad’a ba.
K’ofar d’akin ta bud’e a lokaci d’aya, ta d’ago da kanta da sauri ta kalle shi.
“Sulaiman ya kira ni yanzu, ban san ke da inna wa yafi…”
Maganarsa ta katse lokacin da idonsa ya gano ta, kyawawan idanunsa suka sauka akan nata, sannan a hankali suka soma sulalewa zuwa jikinta, sai ya tako a hankali ya k’araso gabanta, ya zube gwiwoyinsa a gabanta sannan yasa hannayensa ya nannad’o ta cikin jikinsa. Tana kallon yadda mak’ogwaronsa ya motsa alamun ya had’iye wani abun.
“Kinyi kyau.” Ya rad’a cikin kunnenta.
“Kinyi kyau sosai Mine!”
Ta k’ifta idonta hankali tace.
“Yaushe ka siyo kayan?”
Maimakon ya amsa mata sai ya d’ago hannunsa zuwa gashinta ya warware Bun d’in data k’ulle shi.
“I preffered your hair loose!” Ya fad’a cikin husky voice d’insa, muryarsa mai taushi dake d’auke hankalinta.
Zuciyarta ta buga da k’arfi sanda ya sunkuyo daidai fuskarsa yayi pressing lips d’insa a gefen bakinta.
Ya Allah!
Tunaninta ya d’auke gabad’aya, taji bakinta ya bushe sannan numfashinta ja fita da sauri, kamar zai janye gabad’aya ta suma, a cikin haka kwakwalwarta ta jiyo masa sanda ya fad’i wani abu, bata tabbatar ba amma taji kamar yace ne “Please” Sannan ya d’an tsaya kamar mai jiran wani abu, amma ta gaza yin komai, ta tsaya cak kawai hannayenta rik’e dashi ba tare da ta san me zata yi na, bayan wani d’an lokaci taji yana shirin d’aga kansa.
No! not so soon…!
Duk wani sauran tunaninta babu shi a lokacin, saboda haka tasa hannayenta dake rik’e da rigarsa ta janyo shi ya dawo…daga nan ta daina gane komai.