WANENE SHI CHAPTER 4

WANENE SHI






CHAPTER 14










“Kayi shiru, I want to watch it quietly.”

Nanne ta fad’a a hankali idnunta na kallon can gabansu, inda rana ke shirin fad’uwa, Tana kwance a jikinsa daga k’asan wata dogowar bishiyar kwakwa a bakin tekun dake ta ambaliya wani har yana tab’o kafafunsa dake mik’e.

A can gabansu rana ce ke shirin fad’uwa, wani abu ne da bata tab’a gajiya da gani tun zuwansu wajen, wani abu dake k’ara mata jin kamar ba’a cikin duniya take ba sannan wani dake k’ara k’arfin imani a zuciyarta…ranar tayi wani irin ja sannan brightness d’inta yayi reflecting a kowacce kusurwa ta yadda ya bada hasken rainbow, tana kuma yin k’asa a hankali kamar tana lumewa cikin makeken tekun dake gabansu.

Rayuwa ce ta kwanciyar hankali da nutsuwa, ba ruwan kowa dasu don wajen ba mutane sosai…saboda haka yadda zasu farantawa junansu rai shine kad’ai a gabansu.

Sun ziyarci wajaje da yawa har da wasu island d’in dake kusa da nasu cikin irin speedboat da suka xo, a yanzu Nanne ta riga ta kware a shiga jirgin don har rige-rigen wajen zama suke ita dashi wajen da a karshe dai su biyun ne zasu zauna, har cikin ruwan sun shiga amma ba can zurfi ba, gefe kawai inda ‘yan k’ananan kifaye da kuma kunkurun ruwa suke amma sai da suka sa snokel tukunna, (Wani glass d’in ruwa dake rufe ido da hanci saboda shak’ar iska.)

Har da wani paddle na ruwa da ake tafiya a tsaye, abubuwa kala-kala yadda kullum suka fita sai rana ta fad’i suke komawa cikin cabin d’insu. Bayan fad’uwar rana kuma har fitowarta suke gani, Inran ya saka alarm a duk lokutan sallah saboda haka bayan sun idar da sallar asuba kullum zasu fito da overnight mat din da suka samu a cikin gidan su shimfidaa wannan balcony din na wajen pool, mat din na da laushi kamar katifa anan zasu kwanta suna facing fitowar ranar, yadda haskenta ke fitowa a hankali yana canja kalar duhun sama zuwa kamar royal blue da kuma shade d’in golden da kuma orange.

A yanzu bata da matsalar abinci don Menu guda suka kaiwa can wajen dake kawo musu abinci na irin simple-simple abubuwan da suka san zasu iya yi wanda su kuma zasu iya ci, don haka a kullum warmers d’insu cike suke da cima kala-kala, wani lokacin ma har sai an koma da wasu.

*******

Wajen k’arfe uku na rana, dawowarsu kenan daga waje, bayan sun bawa cleaning crew d’in wajen awa biyu na gyaran cikin cabin d’in nasu.

Nanne ta shiga wanka ta wanke fatarta tas! data k’ara wani sulb’i da haske a cikin kwanakin, bruises d’inta sunyi sauqi a lokacin sai dai basu tafi duka ba, har a lokacin akwai alamunsu a wani wajen, sunyi shade d’in pink kad’an.

Bayan ta fito ta saka wata ‘yar k’aramar riga mai kyau dark pink da d’an short da bai kai gwiwa ba, a yanzu ta riga ta saba da duka kayan nan, kullum su take saw kala-kala har gani take da ta taho da dogwayen rigunanta ba lallai ta iya sasu kullum ba, tunda wanda Imran ya bar mata ma amfaninsu in zasu fita ne kawai, amna duk inda suka je tattare abinta take tasha iska da dogon wandon da take sawa a ciki tunda ba wasu mutane a wajen.

Story continues below


Tayi k’ok’arin b’oye murmushinta sanda idanun Imran suka zare bayan ta fito daga toilet d’in, amma cikin wucewar second d’aya yayi k’ok’arin controlling fuskarsa sannan yayi gyaran murya kad’an.

“You look beautiful Noory, kinyi kyau da yawa, kamar kullum!”

Ya fad’i abinda take shirin tambaya.

“Awwn…” Ta dunkule hannayenta a k’irji sannan ta d’an turo bakinta tana kifta ido.

“Thank you Ayunie.” Ta fad’a sanda ta hau kan gadon da yake kwance yana karanta wata bussines magazine, ya mik’o hannunsa ya jawo ta jikinsa tayi hamma kad’an sannan ta d’ora kanta a kirjinsa.

“Yaushe zamu koma gida?”

“Har kin gaji? ke da kika ce mu zauna anan har abada.”

Tana murza idonta da hannu d’aya tace.

“Wajen da dad’i Ulfat, amma ina missing su Inna.”

“Kullum fa sai kunyi waya.”

Ta turo bakinta kad’an. “Yau bamu yi ba.” 

Sai ya mik’a hannunsa gefe ya jawo wayarsa yana fad’in bari a kira su toh, ta rik’o hannun nasa da sauri.

“A’ah ba yanzu ba sai anjima, bacci nake ji.” 

“Bamu ci abinci bafa…I’m afraid bana feeding dinki sosai.” 

“You’re trying, ka bari sai na tashi sai muci, na gaji yanzu.” 

Ya ajiye magazine d’in hannunsa ya sake kwantar da kanta a jikinsa. 

“shikenan, kiyi baccinki.” 

Muryarsa can k’asa ya fara mata humming wani lullaby a hankali yana shafa bayanta. 

“Ban san me yasa nake yawan baccin nan ba Ayunie…” Ta fad’a a hankali idonta na shirin rufewa. 

Yayi murmushi kad’an sannan ya cigaba da humming d’in. 

“Tunda nake ban tab’a irin wannan baccin mai yawa ba, kuma akai-akai haka.” 

Ta sake fad’a muryarta so low. Humming d’in nasa ya tsaya a lokaci d’aya. 

“Nima I was wondering, baccin naki yaso yayi yawa habibty, ba don minshirin da kike ba, har zato nake ko kin shiga Coma ne.” 

Da sauri idanunta suka bud’e, ta d’ago ta kalle shi. 

“Wallahi bana minshari.” 

Ya d’age girarsa duka biyun. 

Wani haushi ya cika mata wuya, bata san sanda ta wawuro pillon gefenta ba ta shiga maka masa, yana ta kyalkyaka dariya yana fad’in tayi hak’uri wasa yake yi! 

********* 

BAYAN SATI BIYU. 

“I’m sorry!” Jaamil ya sake fad’a karo na biyu yana kallon yadda tekun gabansu ke tambal-tambal cikin wani salo mai ban sha’awa. 

Ganin Imran bashi da niyyar amsawa yasa ya juyo gefe ya kalle shi, suna zaune a wata kujera dake facing bakin tekun. 

“Yarima.” Ya kira sunan sa a hankali, maimakon ya amsa sai ya gyara zamansa ba tare da ya kalle shi ba yace. 

“Ta yaya ka san muna nan?” 

“Saboda na sanka, na san duk wani possibilities d’inka.” 

“Amma ka ture wannan sanin kake son biyewa plan d’in Naani? kake kokarin yin abinda ka san zai cuce ni?” 

Story continues below


“Karo na uku kenan da nake maka bayanin cewa daga ni har Naani bamu yi wannan zancen don cutar da kai ba sai don kawai abinda muka tsara tun farko ya tafi daidai sannan a lokacin baka tsaya kaji ra’ayina ba yarima, ina fitowa ka shak’e ni da tambayoyinka.” 

Imran yayi ajiyar zuciya sannan yace. 

“Naani ta sani?” 

“I never told her, ta cigaba da tsarinta na yadda duk lokacin da ka kawo yarinyar zata raba ruhin da jikinta, a kwanakin baya ma ta kirani da saqon cewa in gaya maka zata nemeka nan gaba, saboda da farko ta gaya maka zata kira ka ne bayan sati d’aya. 

“Ba zan taba kawo ta ba.” Muryarsa ta fito kai tsaye. 

“Na sani, amma ta yaya zaka iya karb’ar dutsen in lokaci yayi? tunda ka san b’arinka d’aya ba zai taba iyawa ba.” 

“I’m figuring a way out Jaamil, ban san wace hanya zan samo ba amma definetly zan samo hanyar da zan kare Sa’adha, I will, surely!” 

Jaamil ya juyo ya kalle shi kamar mai karantar wani abun sannan ya koma da kallonsa kan tekun. 

“Sooo…” yaja maganar yana kallon yatsunsa. 

“Ta yarda dani.” Imran ya fad’i amsar tambayar da bai furta da dogon kalamai ba. 

“Na gaya mata komai kuma ta yarda dani jaamil, tace it doesnt matter ko ni meye, zuciyarta ta riga ta amince kuma zata zauna dani.” 

Jaamil ya d’aga kansa kafin yace. 

“Kuma ka fad’a mata abinda Naani tace?” 

“Ba zan iya fad’a mata wannan ba, ba zan iya karya zuciyarta bayan yardar data riga ta bani ba, saboda haka na gaya mata Naani bata dawo ba, kuma kota dawo zan san hanyar da zan kare ta.” 

“Insha Allah, zamu samo mafita yarima.” 

Sai a sannan Imran ya kalle shi cike da mamaki. shima ya juyo yayi focusing sosai yana kallonsa. 

“Tun tasowarmu tare muke komai yarima, bamu tab’a banbanta wani abu namu ba, sannan tare muka fara wannan abin, tare Naani ta turo mu yin aikin nan, tare muka samo mafitar waccan matsalar, me yasa kake tunanin don wani abu ya faru yanzu hakan zai canja?” 

Imran ya had’iye yawu kafin ya maida kallonsa kan tekun, a hankali muryarsa ta fito. 

“Thank you.” 

Jaamil ya juyar da kansa shima sannan suka yi shiru. Zuwa can yace. 

“And I like your wife, tana da kirki.” 

Imran yaji murmushin jin dad’i ya cika bakinsa, ya kasa daurewa har saida hakan ya fito. 

Daga nan suka shiga tattaunawa akan yadda zasu b’ullowa lamarin ba tare da Naani ta sani ba, sun dad’e sosai kafin su fitar da wani kwakwaran plan wanda babu makawa shi zai zame musu mafita. Kafin su rabu hirarsu ta dawo daidai kamar ba abinda ya tab’a had’a su, dama haka yake kowannensu baya iya fushi da d’an’uwansa. 

******** 

Mafarkin ya fara ne a wannan wajen, wannan filin mai tarin bishiyun da ta san cewa abinda tazo nema yana cikinsu, sai dai a wannan karon babu muryoyin su inna dake kiran sunanta daga can nesa. 

Sannan kamar wancan lokacin Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d’ago yatsansa guda d’aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun. 

Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab’anin tunaninta kamar wancan karon, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa. 

Story continues below


Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k’ugunta sannan ya d’ora hab’arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d’umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k’asan kunnenta. 

A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d’aya gefen. 

Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k’asa ta fad’i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa. 

Amma kafin komai ya d’auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye kamar lokacin baya akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sai dai wannan karon a gefensa akwai wani d’an karamin yaro fari tas! mai mutuk’ar kyau dake ta b’angala mata dariya, a hankali idonta ya dawo kan hannun Imran wanda ke ta faman d’igar da jini! 

Ta mik’e da wani irin sauri lokacin data farka daga baccin. D’akin yayi duhu sakamakon yamma data yi sosai kuma an saki curtains d’in gabad’aya harda na jikin glass wall din an zuge shi, akwai sanyi air condition kad’an, amma taji gumi na gangarowa ta cikin gashinta. 

Ta kai hannunta jikin bango ta kunna fitila, haske ya dallare koina, hasken daya nuna mata cewar Imran baya d’akin, a sannan ne kuma Idonta kan tarin takardun dake baje kusan koina a d’akin. 

Kan drawars, gado, mudubi, da duk wani abu da yake da space a d’akin, ta mik’a hannu ta d’auko guda da’aya dake gefenta akan side-drawer. 

I’m hoping ba zaki karanta takardar nan ba saboda ba dad’ewa zanyi ba, amma in har kina karantawa yanzu, wani abu ya rik’e ni kenan…but I ‘ll be back very soon, kiyi sallah kici abinci sannan ki koma baccinki kinjii…? Zaki ganni lokacin da kika sake tashi insha Allah. I love you… 

…like crazy! 

“I love you too.” 

Ta fad’a a hankali sannan ta maida ninkin paper ta rufe, ta mik’e ta tattaro dukkan sauran na d’akin da abu d’aya suke fad’a ta zuba su a handbag d’inta. Ta shiga toilet tayi alwala tayi sallar La’asar data nemi ta kub’uce mata sannan ta sake wanka, kamar wancan karon bata sa mafarkin nan a cikin kanta ba, abu d’aya ne kawai ya tsaya mata a rai…wannan kyakkyawan yaron dake tsaye a kusa da Imran yana b’angala mata dariya. 

Bayan ta shirya ta fito don samun abinda zata ci kamar yadda Imran yace, ba wai yunwa take ji sosai ba amma tunda ya fad’a dole ne taci, tana tafe tana kunna duk switches d’in data san shi ya kashe da zai fita. 

Ta k’ara jin gidan ya mata shiru fye da koyaushe sannan ta dinga ganin koina wani iri. 

A kan stool d’in jikin counter ta zauna tana ta kallon abincin dake cikin warmers d’in, haka kurum take jin bakinta ba dad’i saboda haka tayi tagumi tana tunanin me zata ci. Da kyar ta tsaida zuciyarta ta janyo wani bowl dake cike da potato soup yasha yankan vegetables round kala-kala. 

Yawu ya taru a bakinta tun kafin ma ta fara ci saboda haka ta ajiye cokalin data d’auko tasa hannunta ta fara, tana ci tana lashe hannu kamar wadda aka sanmata. Sai dai bata kai ga ko ci da yawa ba wani irin tashin zuciya dirar mata, bata san sanda ta ture kwanon ba ta matsa da sauri jikin sink ta shiga kwara amai. 

Sai da ta fito da duk wanda taci sannan ya tsaya ta d’auraye bakinta a hankali ta had’a har da fuskarta, tana d’agowa taji kuma kamar jiri ya kamara, gidan ya fara juya mata saboda haka ta lalubi kujera ta dunk’ule akai, a can d’aya side din kujerar akwai wani blanket, amma kafin ta iya d’auko shi ta lullub’a wani sabon baccin yayi awon gaba da ita

Story continues below


Sanda ta sake farkawa duhu yayi sosai, kuma Imran na zaune a gabanta, gaban kujerar da take kai. 

“I’m sorry, ya fad’a yana shafa fuskarta a hankali. 

“I’m sorry na barki ke kad’ai, wani uzurin ne…” 

Bata ji k’arshen zancensa ba ta ture hannunsa da sauri sannan ta tashi da gudu tayi wajen sink d’in, ta shiga kwara wani sabon aman kamar zai had’o da hanjin cikinta. 

“Noory me ya faru? me ya same ki?” 

He was there in an instant! ya rik’o ta yana janye gashinta daga fuskarta. sai da numfashinta ya dawo daidai, sannan ta kalle shi, idanunta sun ciko da kwalla tace. 

“Ka matsa daga nan, amai fa nake yi.” 

Bai ko kula ta ba ya bud’e fanfon aman ya wuce sannan ya d’auraye mata baki suka koma kujerar. 

“Abinci naci ya fara lallacewa.” 

Ta fad’a sanda ya zaunar da ita. 

“Wane iri ne?” 

“Gashi can akan counter.” 

Ya mik’e da sauri ya nufi wajen sai ta maida kanta kan pillow ta rufe idonta ta sake dukunkunewa. Bayan kamar minti ashirin ya dawo ya sake tashinta, ya tsugunna a gabanta ya d’ora hannunsa akan goshinta. 

“Ya kike ji yanzu?” 

Ta daure tayi murmushi tana kallonsa. 

“Lafiya k’alau.” 

“Zan kira likita yanzu ya duba ki.” 

Da sauri tace. 

“Amai ne fa kawai Ayunie, ba wai ciwo bane I’m fine, dan Allah kar ka kira su.” 

“Allura kike tsoro?” 

“Harda magani ma bana so.” 

Yayi shiru yana kallonta, ba yadda ya iya saboda haka yace. 

“Nasa an fitar da duk abincin an kawo sababbi, ki taso muje kici tunda ba komai a cikinki yanzu.” 

Da kyar ta samu taci meatpie guda uku, yana bata a baki yana tab’a jikinta da k’ara tambayar yadda take ji, tunda tana bashi amsar cewa ba komai, har in ya tambayeta sai ta lankwasar da muryarta ta fad’o wani k’aton ciwon, hakan ke sawa su kyalkyale da dariya. 

Bayan sunyi sallar isha, ya kunna t.v suna kallon wani funny American film na wasu teenagers, don shelf guda ne cike da movies kala-kala harda cartoons, tana zaton ma wajen yafi wani gidan saida CD’s d’in yawansu. Tun ita kad’ai ke dariyar yana karanta bussines magazine d’insa har dai ya ajiye shima ya biye mata. 

Kafin su kwanta, she was so happy da har ta manta da jirin da take d’anji. 

Sai dai k’arfe biyun dare, ta tashi da wani irin ciwon cikin da yasa ta amayar da dukka meatpie d’in nan. 

“Sa’adha….” 

Imran ya fad’a yana kwankwasa k’ofar toilet d’in don ta k’ulle wannan karon. 

“Open the door, ki bud’e min.” 

Bata ko motsa ba, idonta na kan cikin sink d’in wanda ya rine jawur da jini, aman nata ya had’o da wani rin jini mai yawa da har dunk’ulewa yake, kamar wani abu ya fashe a cikin ta, ta kunna famfo da sauri ya tafi sanda taji hannunsa ya rik’o ta. 

Ta juyo ta kalle shi, sannan k’ofar band’akin wadda handle d’inta yake a karye. 

“I’m calling a doctor now.” 

“Ayunie amai ne fa…” 

“I don’t care…” ya katseta. 

“…Baki da lafiya shine kad’ai abinda na sani.” 

Ta d’ora kanta akan k’irjinsa shi kuma yasa hannunsa ya rungume ta. 

“Aman da nayi harda jini.” Ta fad’a a hankali. taji yadda k’arar bugun zuciyarsa ya canja a lokaci d’aya sannan rik’on da yayi mata ya d’an saki, daga can yayi ajiyar zuciya sannan yace. 

“Abin yayi yawa Noory, dole ne muga likita…yawan bacci, tashin zuciya amai kuma har da…” 

Sai dai kafin ya k’arasa kwakwalwar Nanne ta ta tsinci wani abin, ta d’ago kanta da sauri tana kallon fuskarsa, kamar me shirin d’auko wani abu nata daya fad’i. 

“Me ya faru? Tunanin me kike?” 

Bata ce komai ba ta cigaba da kallonsa blankly, fatar goshinta na tattarewa alamun tunani. Ya d’ora hannunsa akan goshinta. 

“What’s wrong? Sa’adha….” 

Kafin ya k’arasa muryarta dake rawa tace. 

“Yau wane Date?” 

“25th…gida kike son tafiya?” 

Ta girgiza kanta da sauri sannan ta had’iye wani k’aton abu a makogwaronta. 

“Period d’ina yayi latti da kwana bakwai!” 

“Is it possible? zai iya yiwuwa?” 

Abinda Nanne ta iya fahimta a cikin kalaman Imran dake waya kenan kawai, wayar da yayi kusan awa d’aya yana yi da wani irin yaren da bata ganewa, bayan wannan hausar da yayi ta farko, sunanta kawai ta iya tsinta wanda ya had’o tare da gwamutsin kalmomin da bata san ma’anarsu ba. 

Mamaki take na shi dawa yake waya haka? me yake son tabbatarwa bayan likitan da ya kira yazo ya tabbatar musu cewa da gaske ne tana da ciki. 

CIKI. 

Ciki wai… 

Ta kai hannu ta shafa saman cikin nata a hankali, a yanzu halitta ce a jikinsa, halittar da take combination dinta ita da imran, halittar da zai girma zuwa wani lokacin ya fito a matsayin d’an baby, irin babies d’in da take hangowa a hannun mutane, itama zata samu nata…nata na kanta da zai zama cikin ikonta sannan nata itada Imran! 

A hankali kwakwalwarta ta shiga imagining yadda kammanin babyn zai kasance, ko mace ce ko namiji zata fi so ya d’auko kammanin Imran sosai, yadda duk sanda ta kalle shi zata ga abinda zuciyarta ke k’auna guda biyu awaje d’aya, don duniyarta ta canja daga lokacin da likitan nan ya furta cewa taba d’auke da cikin Imran, taji kamar zuciyarta ta k’ara girma ne ta fito da tsiron wata k’aunar sab’anin ta Imran, abu d’aya da take ji ba zata iya rayuwa babu shi ba a yanzu ya zama biyu. 

K’aunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan k’aunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri ne na son tabbatar da abinda kake so, Allah ya sani a lokacin tana son Babyn cikinta kamar yadda take k’aunar ranta, watakila ma fiye. She wanted him so badly! 

Hannun ta yana kan cikinta kuma zuciyarta nata sak’e-saken abinda zai faru nan gaba sanda taji hannun Imran ya dafa saman nata. 

“Ciwon yake sake yi?” Muryarsa ta fito da alamun tsananin damuwar da yake son kwantarwa. 

Ta girgiza kanta da sauri. 

“Bana jin komai.” 

Ta amsa idanunta na kallonsa cike da mamaki, fuskarsa was hard! babu wani emotion da zata iya tsinta a ciki, ita tayi zaton ganin farin ciki ko yaya ne a fuskarsa… for crying out loud ba’ayi ko awa d’aya ba fa da gaya musu sak’on da yafi kowanne muhimmanci a rayuwarsu, amma tun wannan d’an guntun murmushin da yayi wa likitan babu wata sigar farin ciki data gani tare dashi. Ta juyo da hannunta ta rik’o nasan tana cigaba da kallonsa, Kafin tayi magana ya rigata. 

“Ki kwantar da hankaliki dan Allah Noory, ba abinda zai faru kinji?” 

Ba abinda zai faru kamar yaya? itafa bata gane me yake nufi ba, anya kuwa ya fahimci ma me aka ce? ciki fa akace tana dashi, cikin dake shirin kawo d’a a tsakaninsu, ita ta zata daga fitar likitan zai k’ank’ameta ne saboda farin ciki ko ya d’auke ta ne yayi ta juyi da ita a cikin d’akin suna godewa Allah. 

“Me kake nufi? Ba abinda zai faru a ina?” Ta yanke shawarar tambaya. 

“Ba abinda zai same ki insha Allah ba abinda zan bari ya same ki, Nayi kuskure tun farko wanda ba zai gyaru ba, amma nayi miki rantsuwa ban taba tunanin cewa haka zai iya faruwa ba, da tuntuni na kare hakan…saboda waninmu bai taba shigowa cikin mutane ba, irin haka bata taba faruwa ba.” 

Kanta ya d’aure ta kasa fahimtar komai a cikin zancensa. 

Story continues below


Abu? d’an da zata haifa shine abu? 

Imran baya son Babynsu kenan? Baya son abinda zata haifa? Me yake nufi? Ta yaya d’an mitsitsin halitta zai cutar da ita? A lokaci d’aya tunanin dake cikin kanta ya canja, hoton da take gani Imran d’auke da ita yana murna ya juye zuwa shi da jaamil suna k’ok’arin kashe d’anta, d’an kyakkyawan Babynta, kunnenta ya karad’e da k’arar kukansa. 

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! tunaninta ya hargitse a lokaci d’aya, ba zata taba yarda ba, ba wanda zai rabata da d’an dake cikinta, ba zata taba bari a cutar dashi ba, ko waye kuwa, ko shi Imran d’in ne kansa! 

Taji sanda ya zame hannunsa daga cikin nata ya mik’e tsaye yana amsa wata wayar, cikin yare irin na d’azu, ta tabbata jaamil d’in ne suke sake tattauna abinda ba zai tab’a kasancewa ba. 

Juyowar da Imran zaiyi cikin wayar ya kula da hawayen da take yi, Ya salam! ba dai wani ciwon take sake ji bada sauri ya kashe wayar ya dawo gabanta. 

“Sa’adha me ya faru?” 

“Ayunie so kake ka kashe Babyn mu?” muryarta ta fito cikin rawa. 

Ya d’an tsuke ido yana kallonta, Baby? tunanin da take kenan? tunani take abinda ke cikinta Baby ne? 

“Sa’adha we don’t know what’s in there…na gaya miki irin haka bai tab’a faruwa da irinmu ba, sanda nake wannan kuskuren ban taba sanin cewa ciki zai iya shiga jikinki ba, so for all we know a yanzu abinda ke jikinki zai iya cutar dake.” 

Ta girgiza kanta da sauri. 

“Ta yaya zai cutar dani wai? ta yaya zai cuce…” 

“Kin manta ni ba mutum bane?” Yayi saurin katseta, ganin alamun bata fahimce shi ba ko kad’an. 

A lokacin d’aya fuskarta ta koma blank! idanunta suka zare kamar yaune rana ta farko data ji hakan, don har ga Allah ita mantawa take Imran ba mutum bane tunda bata tab’a ganin wata alamar hakan a tare dashi komai nasa irin na mutane ne sak! ba wata tangard’a. 

“Kin manta waye ni? ni ba mutum bane Sa’adha, saboda haka bana tunanin abinda ke cikinki zai iya zama mutum, zaki iya haifarsa da wata jirkitattiyar halittar or worse yazo a irin siffar mu… 

Look bama wannan ba, ba zaki iya ba,  jikin mutane da namu ba iri d’aya bane, halittarmu tana da k’arfin possesing abubuwa da yawa while mutane are weak, you’re not strong for this Noory!” 

Duk wannan bayanin da Imran yake yi, kwakwalwar Nanne ba fahimta take yi ba, abu d’aya kawai ta gane shine Imran baya son Babynsu saboda baya so ko kad’an a samu wata alama da zata tab’a nuna cewa shi ba mutum bane, amma ita bata damu da wannan ba, in har Imran ya kasance k’addararta toh zata rik’i wannan ma a matsayin wata k’addarar tata, zata yi k’ok’ari da dukkan iyawarta ta raini Babynta, tana ji a jikinta cewa hakan wani alkhairi ne nata… So atleast she would try! 

“Dan Allah ki fahimce ni.” Ya fad’a yana sake rik’o hannunta. 

Ta tsaida idonta sosai akansa sannan tace. 

“Na fahimceka Ulfat, kuma nima ina son ka fahimce ni, ina son ka fahimci cewa ba zan tab’a iya kashe shi ba.” 

A lokaci d’aya kalar idanunsa suka yi duhu sosai alamun b’acin rai. 

“Sa’adha, ba lallai irin Babyn da kike tunani bane a cikinki, for one second ki bud’e kwakwalwarki ki gane me nake nufi, abin nan zai cutar dake ta irin hanyar da baki sani ba, it’s not some pretty Babyn da kike tunani.” 

Itama nata ran ya b’aci, ta d’age girarta d’aya. 

“Zamu gani toh.” 

Tana fad’in haka ta mik’e tayi hanyar d’aki, ba tare da wani tunani ba Imran ya b’ace cikin iska ya baiyana a gabanta, a lokacin da bugun zuciyarta yayi wani irin bugawa cikin kunnensa, a lokacin yayi dana sanin abinda yayi, don ba sai ta fad’a masa ba ta tsorata sosai da hakan, amma tunanin zancen da suke yi ya danne wanda ke cewa ya bata hak’uri. 

“Me yasa ba zaki gane abinda nake nufi bane? i can’t stand to see you in pain,_Sa’adha abin nan zai iya kashe ki!”

Nanne ta had’iye tsoron dake kanta, yanzu ta k’ara fahimtar wani abin, yana tunanin zata iya mutuwa shi yasa ya damu kansa haka, baya son ya rasa ta, watakila sunyi daidai kenan a haka, itama tana tsananin son abinda ke cikinta baza taba iya bari ta rasa shi ba, saboda haka tace.

“Ba zai kashe ni ba Imran, I can do this.”

Tana fadin haka ta k’arasa cikin d’aki ta rufo k’ofar, yaji sanda ta murd’a lock d’in ta k’ulle alamun bata buk’atar company d’insa, amma ba wannan ne ya dame shi ba, the fact that ta kira shi da Imran, wani abu ne da ya kwana da sanin cewa duk sanda ta kira sunansa toh ko tana cikin rud’ani ko kuma fushi, wanda a yanzu ya tabbata fushin take ji, A hankali ya zame k’asa ya zauna akan dandaryar tiles d’in, bayansa ya jingina da bangon corridor d’in.

Ya kai hannunsa don ya share gumin daya fito masa, amma sai yatsunsa suka nutse kamar zasu d’ago da fatarsa, duhun kwayar idonsa ya sake haskawa cikin sockets d’insu sannan bakinsa ya bud’e kamar zai yi ihu amma ba abinda ya fito.

Sa’adha fushi take dashi? ta yaya zaiyi mata bayanin cewa ba zata iya d’aukar abinda ke cikinta ba, ta yaya zai zai fad’a mata ta fahimce shi su gyara kuskuren da yayi. Me yasa ne abubuwa basa tab’a zama masa daidai game da ita? me yasa baya iya controlling zuciyarsa akanta? Baya tab’a behaving rules d’in da suka dace… he’s just being himself around her! Saboda tana sawa yaji shi complete yaji shima wani ne mai iko, don tunda yake bai tab’a jin yana son abu kamar yadda yake son Sa’adha ba.

Yana zaune a wajen bai motsa ba har lokacin da alarm d’in wayarsa ya buga k’arfe d’aya lokacin sallar Azahar, bai san ya akayi tajibalarm d’in ba don bayan wani lokaci yaji karar zubar ruwa daga can toilet d’in d’akin hakan ya tabbatar masa yau jam’in da suke yi ba zai samu ba kenan, saboda haka ya fita can balcony yayi tasa alwalar sannan ya shigo yayi sallah, sai dai har wajen k’arfe uku Sa’adha bata fito daga cikin d’akin nan ba shi kuma yayi alqawarin ba zai takura mata ba, zai barta tayi dukkan irin tunanin cikin kanta wataqila hakan zaiyi knocking sense cikin kanta ta fahimci abinda yake nufi.

Yaji gabad’aya ya takura gidan ya masa wani iri, duniyar ta tsaya masa cak! sannan zuciyarsa ta matse na rashin sanin ainihin tunanin da take game dashi. Ya kasa yin komai, Jaamil ya sake kiransa fiye da sau goma amma yana kallo ya kasa d’auka.

There had never been something like you and sa’adha before, dole sai kayi hankali da kasancewarku tare…Banbancin halittarku shi zai iya jawo wata matsalar a zamanku, akwai abubuwa da yawa da sai kayi taka tsan-tsan game dasu, strong emotion d’inka zai iya kawo wani abun yarima.

Ya tuno maganganun da jaamil ya fad’a masa ana gobe d’aurin aurensa da Sa’adha, gashi bai kiyaye komai a ciki ba.

Sai bayan La’asar sannan Nanne ta fito daga cikin d’akin, ta same shi daga jikin counter saboda haka ta tsaya daga nan, Zuciyarta tayi wani irin nauyi sanda ya d’ago ya kalleta, da lumsasun idanunsa dake cike taf da damuwa.

Imran ya gyara zamansa sosai yana kallonta, tayi wanka ta canja kayanta zuwa wata ‘yar pink riga mai kyau iya gwiwa, ya tuna sanda ya hango rigar daga can sama bayan ya gama d’ebo sauran yazo biyan kudi, haka kurum tayi masa kyau yace a d’auko ta a had’a da ita. k’afarta ta dama a tsaye take, ta hagu kuma akan babban d’an yatsanta tana juyawa, kamar abinda yaro yake yi in zai tambayi abu yana kuma shakka.

“Ina so in tambayeka wani abu.”

Ta yanke shawarar magana lokacin da taga bashi da niyyar barin kallonta.

“Ina jinki habibty.” Ya fada shima daga inda yake zaune.

“I want to go home, ina son inje gida.”

Ya gyad’a kansa a take.

“Zan duba inda flight gobe zan mana booking.”

Ta gyad’a kanta a hankali, sannan ta juya ta koma ciki, Imran yabi bayanta da kallo yana jin kamar ya mik’a hannunsa ya jawo ta, _this is toture!_ bata san yadda rashinta a d’an lokacin nan ke azabatar dashi ba. Ya kifa kansa akan counter lokacin da itama ta buga k’ofar d’akin ta rufo.

Wasa-wasa har sallar isha Nanne bata da alamun fitowa daga d’akin, saboda haka bayan ya idar da salkar isha ya hada mata tea mai kauri sannan ya d’ebi wani abincin da wasu snacks d’in ya nufi d’akin, yayi niyyar b’alla k’ofar amma ga mamakinsa yana turawa ya ganta a bud’e. Ya shiga ya kunna fitilar dake kashe, a lokaci d’aya ya hango ta lullub’e daga tsakiyar gadon ta takure kanta.

Ya ajiye kayan da sauri ya isa gareta.

“Sa’adha me ya sameki? Ciwo kike ji?”

Ta d’ago da jikakkun idanunta ta kalle shi.

“Sai yanzu kaga damar zuwa? Ayunie tun d’azu nake jiranka.”

Bai san sanda ya janyo ta gabad’aya jikinsa ya rungume ta ba.

“I’m so sorry Noory, na zata kina buqatar lokaci ne ke kadai.”

“Wane lokacin nake buqata ni kad’ai ulfat? wane lokacin nake buqata da babu kai?”

Ya sake rungumeta yana shafa bayanta.

“Kiyi hakuri, na zata fushi kike dani.”

Ta dunk’ule hannunta ta shiga dukan kirjinsa.

“Fushi nake yi da kai mana, fushi nake yi da kai sosai, kuma tun d’azu nake jiran kazo ka bani hak’uri…”

“Toh ai kin k’ulle k’ofarki.”

“Ba ka iya b’allawa ba, jiya ba ka b’alla k’ofar toilet ba, ba sai ka b’alla ka shigo ba.”

Ya d’ago da fukarta daga jikinsa ya kalle ta.

“Toh Noory sai in ta b’alla musu k’ofofi?”

Ta sake kai masa wani dunk’ulallen naushi, shi kuma ya k’ara rungumeta a jikinsa!

A can cikin rigarsa ya jiyo muryarta.

“Ba zan mutu ba Ayunie, I will keep my heart beating, inada k’arfin da zan iya rik’e Babynmu insha Allah, ina son shi Ulfat…ina son shi sosai!”
You will be fine! 

******* 

“Ka tabbata da abinda muke shirin yi yarima? are you sure about this?” 

Jaamil ya tambaya sanda suka zagaya bayan gidan suka zauna akan wasu kujeru dake cikin d’an karamin wajen shan iska, wajen da ana iya fitowa ta k’ofar kitchen ta baya. 

Imran ya sunkuyar da kansa sannan ya fito da iska ta bakinsa. 

“I don’t know jaamil, wallahi ban san ya zanyi ba kome zai faru, kullum cikin magiya take min kala-kala ta safe daban, ta rana daban, ta dare daban duk akan a bar mata shi, ba irin bayanin da banyi mata ba tun muna can amma ta kasa fahimta ta, da farko ma zargi na ta fara yi akan wai zan kashe Babynta, yanzu kuma bayan duk taji komai tana ganin kamar ina underestimating d’inta ne, gani take kamar tana da k’arfin da zata iya.” 

“Baby? Tunani take Baby ne a cikinta?” 

“Haka take gani saboda har a yanzu mantawa take ni ba mutum bane sai na tuna mata tukunnan, yadda ka san tatsuniya kawai na bata a baya.” 

“Tana matawa ne saboda baka nuna mata what you’re capable of.” 

“Ba zan iya ba jaamil don koda ta yarda dani ita bil’adama ce, dole akwai tsoro irin nasu…ba zan iya dinga b’acewa a gabanta ba ko in dinga yin abubuwa da mutane baza su iya ba, ko in dinga baiyana mata ainihin halitta ta…I have to blend in for her sake!”   (I tynk na amsa wanda ke tambaya ta me yasa Imran baya nuna powers dinsa.😊) 

“Haka ne.” ya amsa curtly. 

Suka d’an yi shiru na wasu seconds kafin jaamil yace. 

“Bwama ta gaya min Naani ce kad’ai zata iya ganin ainihin abinda ke cikinta…” 

Story continues below


“And she will never be involved!” Imran ya katse shi sharply. 

Jaamil ya gyad’a kansa a hankali ba tare daya kalle shi ba, bayan wani lokaci ya sake magana. 

“The good news…itama bwama bata so a rabata dashi.” 

Imran ya juyo ya kalle shi da sauri. 

“Tana ganin cewa zai yiwu ne?” 

“Ba zata tabbatar in zai yiwu ba sai ta gama ganinta yanzu, amma ta fad’a min ne k’aunar uwa ga d’anta wani abu ne da babu irinsa a fad’in duniya, tace kowacce uwa tana son jininta komai irin munin halayya da siffarsa, so inaga ta fahimci abinda Sa’adhan take ji ne a yanzu, shi yasa ta matsa min a lokaci d’aya cewa sai mun taho don taga irin halin da take ciki.” 

Imran ya had’e tafukan hannayensa sannan ya d’ora su akan lebb’ensa, kwakwalwarsa ta tuno masa hirarsa da ita jiya da yamma. 

“Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab’a zama irin tunanin da kake ba…ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah.” 

A lokacin suna zaune yana bata yoghurt a baki, abinda a yanzu suka gano cewa shi kad’ai cikinta ke d’auka ba tare da ta amayar daga baya ba. 

“So habibty Babyn namiji ne?” Ya tambaya yana goge mata smudge na yoghurt d’in a gefen bakinta. 

A lokacin d’aya kumatunta suka yi blushing zuwa pink… wata kala mai kyau, mai kyau sosai da yaji kamar an caka masa wuk’a a cikinsa, wata wuk’a mai tsini da kuma tsatsa saboda zuciyarsa ta kasa tantance wace irin k’auna Sa’adha ke masa, he’d hurt her in so many ways amma har tana iya wannan farin cikin around him. 

“Yau ce rana ta farko daka fad’i wani abu good akan Babyn nan Ayunie…” 

Kafin yayi magana ta cigaba. 

“…ban sani ba ko mace ne ko namiji
, amma ni a mafarkina namiji nake gani.” 

“Har mafarki kike yi da Babyn?” 

A lokacin da ya fad’i haka zai iya rantsewa yaga giftawar wani abu cikin idanunta, kamar akwai wani sauran bayanin tattare da mafarkin nata da take k’ok’arin b’oye masa amma sai ta sake yin murmushi tace. 

“Zanso in iya nuna maka shi a mafarkin, yana da kyau sosai saboda da kai yake kama!” 

Kafin fuskarsa ta iya rik’e wani reaction d’in ta rik’e hannunsa dake shirin kai mata wani spoon d’in baki tace. 

“Kaci abinci?” 

Ya langwab’ar da kansa kad’an irin abin tausayin nan yace. 

“Noory ba abinda naci.” 

“Awwn…I’m soory na barka da yunwa, kaine kuma kak’i bari na in tashi.” 

Ta fad’a tana cupping fuskarsa a cikin hannunta, a lokaci d’aya kuma ta tashi ta nufi kitchen, bai b’ata lokaci ba shima ya rufe robar yoghurt d’in yabi bayanta. A gaban deep freezer ya same ta ta bud’e tana kallon kayan ciki, ya matsa a hankali ya juyo da ita, hannunsa d’aya zagaye da waist d’inta, d’aya kuma ya karb’e bowl d’in markadadd’en kayan miyan data d’auko. 

“Me zaki yi?” ya tambaya fuskarsa dab da nata. 

“Abinci zan dafa maka.” 

“Yaushe nace ina jin yunwa.” 

Ta d’age girarta d’aya. 

“Kace baka ci komai ba.” 

“Amma bance ina jin yunwa ba.” Ya fad’a yana kallon bakinta da idanunsa masu d’auke da emotions kala-kala da take hango su ta cikin maik’on idon. 

Story continues below


“Toh ai zaka nemi abinci anjima kuma sai mu zauna ba’ayi girki ba don ni ba zan…” 

Kafin ta k’arasa kawai ya had’e lips d’inta da nasa and just like that…ta manta k’arshen zancenta, kwakwalwarta ta tafi cloud 9 ta nutse can cikin duniyarsa. 

Ya k’ara manna ta a jikinsa yana jin kamar ya cusa ta cikin zuciyarsa ta gano yadda yake mutuqar k’aunarta, ita kuma ta rik’o wuyansa kamar tana tsoron zata fad’i. 

“Kasha tea Ayunie, bakinka na k’amshin madara.” Ta fad’a breathlessly sanda ta d’an ja baya kad’an. 

Yayi murmushi so soft idanunsa kusan a rufe, kafin ta k’ara magana ya sake sunkuyowa yana k’ara kissing d’inta, wannan karon itama ta taya shi, k’arar heartbeat d’insu ya had’e waje d’aya. 

“I want to tell you something, abinda zan gaya maka yana mutuk’ar muhimmanci.” 

Muryar jaamil ta jawo shi daga tunanin da yayi tafi, ya juyo a hankali ya kalle shi. 

“Mene ne?” 

Kamar bai ji ba, sai da yayi shiru kafin yace. 

“Ban san ta ina zan fara maka bayani bama.” 

Ya sake fad’a ba tare da ya juyo ba, Imran ya d’an tsuke gira yana kallonsa. 

“How about the begining?…ka fara ta farko.” 

Maimakon ya amsa, sai ya d’ora hab’arsa akan hannayensa duka biyu sannan yace. 

“Yaushe ne lokacin da Naani take jira?” 

“Jiya na koma company, sunyi fixing date nan da kwana goma sha shida, atleast dai sati biyu, so i was thinking zamu iya samun mafita kafin nan.” 

Jaamil ya girgiza kansa har a lokacin bai juyo ba. 

“Babu wata mafita da zamu nema yarima, Allah ya riga ya kawo mana sauk’i.” 

“Ka samo wata hanyar kenan?” 

“Ban samo ba, kuma ba abinda zan samo, hasalima ba zaka je karb’ar award d’in ba, wannan dutsen ba zai tab’a shigowa hannunka ba.” 

“Ban gane ba…” Da tsananin mamaki Imran ya furta reaction d’in dake kan fuskarsa. 

“Me kake nufi jaamil? ka san wannan dutsen shine dalilin duk abubuwan dake faruwa yanzu, shine dalilin shigowarmu cikin bil’adama kusan shekara guda kenan..ta yaya sai yanzu da komai ya kammala, Dr. turaki ya gama amincewa dani a matsayi wanda za’a bawa award d’in sannan zaka ce ba zan karb’a? 

Idan har matsalar b’arin ruhina dake jikin Sa’adha ne na san zamu iya samo wata mafitar kafin sati biyun, amma ba zamu tab’a k’in cikawa Naani alk’awarin da muka d’auka ba..she has sacrificed alot don a kawo wannan lokacin saboda haka zamu k’arasa komai ba tare da saninta ba, na san in dai har na iya karb’ar dutsen na kai mata, ba zata takurani akan matsalar Sa’adha ba tunda ta samu abinda take so…sai dai kuma in nemi yadda zanyi da sareefa don Allah jaamil a yanzu ba zan iya rabuwa da Sa’adha ba.” 

Har ya kai k’arshen zancen jaamil bai katse shi ba, sai da yayi shiru sannan yace. 

“Ban san ta yaya zan fara maka bayani ba yarima, amma abinda kake shirin ji yanzu zai karya zuciyarka.” 

Imran yayi focusing idonsa sosai yana kallonsa kwakwalwarsa na son tsinto yanayin da fuskarsa ke nunawa, yasha ganinsa cikin fushi, cikin b’acin rai, tashin hankali, mamaki, rud’ani da kuma ciwo… 

Amma yanayin fuskar tasa a yanzu wani abu ne daya girmewa tashin hankali ko rud’ani, a cikin idanun bil’adamansa yana iya hango ainihin kwayar idonsa da tayi jawur duk da cewar baya kallonsa, ya tsirawa wata ‘yar k’aramar flowerpot d’in dake gabansu ido ne kamar an cinna masa wuta, duk zagayen tunanin Imran ya kasa gano dalilin da zaisa jaamil cikin wannan yanayin. Naani ta yaudare mu yarima… bata turo mu samo dutsen nan don kariyar nahiyarmu ba kamar yadda ta fad’a.” 1

Imran ya k’ifta ido jin hakan, kwakwalwarsa ta maimaita zancen ta k’ara maimatawa amma ya kasa gane me suke nufi.

“Kamar yadda kaji zancenmu da Naani, haka nima naji zancensu da Sareefa jiya bayan ta kira ni da saqon cewa in gaya maka ka kai Sa’adha wajenta gobe.

“Gobe? Ta gama dukkan shirin da tace zata yi kenan na cire ruhin daga jikinta?”

“Ba wannan ne mai muhimmanci ba.” Jaamil ya fad’a yana ciro wani dunk’ulen abu daga aljihunsa, Imran ya riga ya san mene ne…HABLER, wani abu da suke recording murya dashi.

Ya bud’e shi a cikin tafin hannunsa, take wasu abubuwa kamar fuka-fiki biyu suka fito ta kowanne b’angare suka shiga kad’awa, a lokacin muryar dake ciki ta shiga fitowa.

Wannan muryar mai cike da kaushi da kuma k’arfin amo mai girgizarwa, kamar koyaushe Imran yaji sautin ta yana tab’owa har k’asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa.

“Na fahimce cewa zuciyarki ta fara karkata akaina sareefa, kina ganin kamar bana sonki, kamar ina fifita su yarima fiye dake…a yau zan shaida miki wani abu da babu mahalukin daya sani…ina amfani da yarima da jaamil ne kawai don cimma manufar da zata gyara rayuwarmu ni dake, shi yasa na d’auke su na nunawa al’umma su na fifita su duk don zuciyarsu ta amince dani suji zasu iya sadaukar da rayuwarsu don yi min komai…!

Kamar yadda tun tasowarki kike ganin suna yi min aiki kala-kala, haka a yanzu ma na tura su yin aikin da shine dalilin d’auko yarima da nayi daga kwararo na gyara rayuwarsa na bashi dukkan wata kulawa daya rasa a baya.

Na taba gaya miki a baya cewa ina neman dutsen Nil, wani dutse da zai bani k’arfin da zaisa zuri’ata ta d’ore wajen mulkar nahiyar nan…toh daga baya mun samo dutsen a cikin bil’adama, wad’anda basu san amfaninsa ba sai kawai kyau da yayi musu suke ado dashi a matsayin kyauta, a lokacin yana wajen wani mutumi dake shugabantar wani kamfani saboda haka nayi niyyar d’aukowa amma sai farme ya shaida min cewa kona d’auka dutsen ba zai tab’a min amfani ba, k’arfinsa yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta hanya mai kyau, ma’ana sai in har mai shi ya bani da yardarsa inba haka ba ba zai tab’a min amfani ba.

Tun a lokacin nayi niyyar tura dalak (Babban bawanta) a matsayin bil’adama yaje kamfanin mutumin har yayi aikin da zasu yarda dashi a bashi dutsen amma sai muka sake ganowa cewa ba kowa ne zai iya rik’e shi ba, sai irin d’aid’akun halittun cikinmu masu k’arfin ruhi, saboda haka nasa farme ya shiga nemo min irinsa.A sannan ne ya gano wani bawa dake can nahiyar Sabeel, saboda haka mu karkata zuciyar mai shi ya taho muzaffar da niyyar saida bayinsa ya samu kud’i, bana so ko kad’an matashin bawan ya san inada hannu a cikin lamarinsa don haka muka shirya komai ya tafi a tsare, Farme ya kashe ubangidansa a daren da suka shigo Muzaffar sannan ya taimaka wajen kwance sark’arsa ya gudo. Sai bayan sati d’aya da shigowarsa cikin muzaffar sannan na shirya had’uwa dashi, shine a ranar da muka fita cikin kasuwa har dake ya taimaka wajen cetona daga fad’awa rami da Farme ya shirya komai, ni kuma nayi amfani da wannan damar na ‘yanta shi na kawo shi cikin masarauta. 1

Ban tsara komai da jaamil ba saboda bana son cutar dashi a matsayinsa na d’an ‘yar uwata, amma daga baya na fahimci alaqarsu tayi karfin da ba zan iya raba su ba saboda haka na barshi a matsayi mai taimakonsa nake tura su yin abubuwa kala-kala duk don su saba da hakan, sai da na fahimci zuciyar kowannensu ta yarda dani sannan na bijiro musu da buqatar samo min dutsen Nil, kuma ba wanda yayi musu a cikinsu duk da cewa basu tab’a wani abu makamancinsa va wato canja siffarsu su shiga cikin bil’adama.

Na tsara komai ba tare dana gaya musu ainihin manufata ba, sannan na tura su da dukkan wani abu da zasu nema yadda komai zai tafi daidai su samo dutsen kuma su danqa minshi da yardarsu! sai dai gabad’ayansu sun sab’awa umarnina a yanzu sunyi wani abu da babu shi a cikin tsarinmu…wani abu da zan d’auki mataki akansa duk ranar da suka gama abinda na tura su.

Saboda haka ki kore dukkan wani tunanin dake cikin kanki game da ina fifita su yarima akanki, K’arshensu ya kusa zuwa kwanan nan , daga lokacin da suka kawo min dutsen Nil, daga lokacin zan shafe tarihinsu daga tunanin al’ummar nahiyar nan gabad’aya, don hatta aurenki dashi na yarda da baikon ne wai don in k’ara samun yardarsa game damu ba wai don hakan zai kasance ba.

Ke kad’ai ce d’iyata Sareefa, ke kad’ai ce zan iya sadaukar da komai akanki…kuma saboda ke kad’i nake duk wannan tanadin!”Toh kin gansu nan, kala biyu ne…wannan da nono zaki samu ki dama shi wannan kuma da ruwa kawai in kinga dama ma ki watsa shi a bakinki haka, cikin cokali d’aya ya isa.”

Nanne ta d’age hanci da gira tana kallon k’ullin magungunan da inna ke nunawa a gabanta, ita tunda aka bud’e k’ullin wani yellow taji cikinta ya juya, yoghurt d’in data sha na safe na shirin fitowa.

“Wai daga ina ma aka samo su?”

“Tun zuwan da nayi Niger na taho dasu a wajen malam na vonni.”

Mamaki ya kamata, ta saki baki kawai tana kallon inna, ta kasa yarda cewa tun sanda suka je Niger da zancen aurenta inna ta karb’o mata maganin ciki.

“In zaki sha tea da safe ma kawai ki saka shi a ciki tunda na san baki fiye son nono ba.”

“Inna nifa bana jin zan iya shan wannann abubuwan, ba komai ma nake iya ci ba.”

“Haka kuwa zaki sha, ko kina sha zasu dawo baza a rasa mai amfanin da zai tsaya ba, wad’annan d’in da kike rainawa sune masu amfani amma ku kunfi ganewa kwayoyin turawa da zaku yi ta sha ana haifar ‘ya’ya da cututtuka.”

Ta fad’a tana janyo manyan ledojin da aka shigo dasu na tsarabar kayayyaki masu kyau da Nannen tazo dasu, komai a rabe yake don kowa a gidan saida ta d’auko wani abu da sunansa,  hatta ‘yan aikin gidan su lami sai da ta d’auko musu mayafai irin na mutanen can, inna ta shiga warewa tana fad’in kuma ya biye miki kuka yita kwaso kaya haka, amma can k’asan ranta farin ciki ne fal! na ganin tarin alkhairin da  kowannensu baisa rai dashi ba, ta riga ta sani tun da Nanne bata da rowa ko kad’an, abin hannunta bai dame ta ba don bata k’i tayi kyauta da komai nata ba har kuwa ga wanda ba shiri suke ba, rashin kunyarta iya ta baki ce kawai.

“Ki d’auki fa magungunan kisa a jakarki.”

Ba yadda ta iya haka ta d’auka tasa a handbag d’inta ba da niyyar sha ba, don tun zuwanta a yau da inna fahimci cikin dake jikinta tayi ta tambayarta game da zancen sunje asibiti da kuma yadda take jin jikinta, ba sai an fad’a ba ta san murna ce tsantsa a can k’asan ranta don tana iya hango kyallin hakan daga cikin idanunta sanda take gayawa Mama Azumi data shigo.

STORY CONTINUES BELOW

Zuciyarta ta karye da tunanin yaya zasu ji a lokacin da suka san irin sirrin da take b’oyewa, kafin zuwan Imran cikin rayuwarta bata taba tunani akwai wanda zuciyarta zata amince har tayi sharing sirrinta dashi bayan Inna ba, sai gashi a yau innan take b’oyewa sirrinta, sirrin wani abu da take ganin ya zama jigon rayuwarta…take kareshi da karya kala-kala a wajen innar tata.

Don ko awa d’aya bata rufa da zuwa gidan ba ta fara tambayarta game da zancen ‘yan uwan Imran, ba yadda ta iya haka ta bud’i baki ta fad’i k’aryar cewa ai daga dawowarsu can bauchi suka fara sauka, sai da suka suka kwana biyu aka zagaya da ita cikin danginsa sannan suka taho. Jin haka yasa hankalin innan ya kwanta ita kuma nata ya karkasu waje da yawa.

A cikin wajajen harda wani waje mai kama da damuwa ganin cewar dukkansu basu san irin cikin dake jikinta ba kuma basu kawo zaton komai a ransu ba, mama halime ce kawai data shigo tace mata in ta koma asibiti tayi complain akan idanunta don k’asansu yayi rami kad’an, basu san cewa ko sau d’aya bata bi hanyar asibiti ba, kuma bata jin har lokacin haihuwarta zata nemi asibitin.

Bwama ta riga ta gama yi mata duk wani therapy da take buqata kuma ta gaya mata abinda a kwanakin baya take jin zata iya saida ranta don ta ji shi, Abinda ya zama dukkan wani fata da burinta a lokacin da Imran ya dasa ayar tambaya game da cikin nata.

Allah ya sani a lokacin da yake gaya mata b’arin ruhinsa yana tare da ita, taji tsoro kad’an don bata son sake experiencing abinda taji a baya, har wani part na zuciyarta yayi fatan dawowar Naani don a cire shi, amma daga sanda bwama ta dubata, ta ganocewar wannan b’arin ruhin shike rik’e da cikin nata, ta mik’a godiyarta ga Allah da har a lokacin ya kasance a jikinta, don tace ba don shi ba, babu ta yadda za’ayi cikin Imran ma ya iya zama a jikinta kona ‘yan mituna…jikinta is too weak d’in da zai iya rik’e shi!

Amma a yanzu tana fatan k’arfin zai iya rik’e shi har zuwa watannin da abinda ke cikinta zai fito, watannin da bwama ta tabbatar mata ba zai zamo d’aya dana mutane ba, don they grow so fast ba irin halittar d’an adam ba. +

Ta tuno yanayin Imran sanda ya shigo gidan bayan tafiyar Bwama, ga mamakinta emotion d’in fuskarsa was weak! zata iya fassara yanayinsa da kamar na d’an karamin yaron a lokacin da yaga mamansa bayan ya b’ata na kwana biyu.

“Come here.”

Ya fad’a a hankali yana bud’e hannayensa ba tare da ya bar tahowa wajenta ba, ai kuwa yana rufe baki ta ajiye sassak’en itacen da Bwaman ta bata ta tafi da sauri ta had’e distance d’in dake tsakaninsu, yadda ta cusa kanta cikin jikinsa ya tabbatar masa da kuka take shirin yi.

“Wani abu ya faru ne sweetheart?”

Ya tambaya daga saman kanta. Muryarsa kad’ai a lokacin ta tabbatar mata da dole akwai wani abu daya same shi a lokacin, akwai wani abu da suka tattauna jaamil bayan fitarsa, bata san ko meye ba amma taji zuciyarta ta sake tsinkewa, hawayenta ya k’aru har yana gangarowa kan kuncinta.

Ya jijjiga ta a hankali yana share hawayen da d’aya hannunsa.

“Me ya saki kuka?” Ya tambaya yana d’auke hawayen da yatsunsa masu taushi, amma raunin muryarsa da take ji yasa suka kasa daina fitowa.

“I’m so happy Ayunie, murna nake yi…”

Ta amsa muryarta a karye.

“…Bwama tace we can keep it!”

Ya fad’i abinda ya san zai zama next words d’inta, daga can saman kafad’arsa ta d’aga kai sannan ta k’ara rungume shi.

“Alhmdlilah.”

His voice was low again, saboda haka ta d’ago ta kalle shi, a lokacin ne zuciyarta ta girgiza sosai don ganin wani abu da bata tab’a zata ba, wani abu da tunaninta bai kawo mata ba.

TEARS!

*********

HAWAYE.

Wani abu ne da Imran bai san ya d’uminsu yake akan fata ba, wani abu da bai tab’a using ba tun shigowarsa cikin mutane.

Amma a lokacin da yake rungume da Sa’adha bayan tafiyar Bwama, a lokacin yayi experiencing yadda mutane keji sanda suke fitar da kwallar farin ciki da godiya ga Allah kan wata baiwa da yayi musu…

Ya k’ara yarda cewa itace shi a yanzu, itace dukkan wani hope da zaisa ya cigaba da rayuwa mai kyau a gaba, Sa’adha k’addararsa ce da Allah ya shigo da ita don ta tallafe shi a lokacin daya rasa kowanne gata…kamar yadda jaamil ya fad’a ne zuciyarsa ta karye gutsi-gutsi ta dagargaje bayan muryar Naani da ya gama ji, muryar data fallasa dukkan wani zargi da zuciyarsa ta fara d’arsa masa tun lokacin da Naani ta d’auko shi a matsayin wanda ta ‘yanta kamar d’anta, amma sai tarin alkhairinta suka ture masa komai a lokacin.

Sai a yanzu yake hasko dukkan abinda ya faru a baya tar! a idanunsa, kamar a da yana cikin wani d’aki ne mai duhu a yanzu kuma aka kunna fitila mai haske yake ganin komai a gabansa.

Ya godewa Allah da yasa komai ya baiyana a yanzu, a yanzun da abubuwa basu zame daga hannunsa ba, a yanzun da yake da Sa’adha…wata mace guda d’aya da ta san dukkan wani secrets d’insa but she still stood beside him, a woman who love and trust him da dukkan zuciyarta, wadda ta bashi hope d’inta 100% ba tare da ta tab’a zarginsa ba, macen data bashi wata irin kulawa da bai tab’a experiencing irinta a wajen wani mahaluki ba, a woman who had every reason d’in da zata guje shi amma bata yi ba, ta baro iyayenta da kowa tayi sacrificing rayuwarta da zata iya gyarawa a gaba and choose to stand by him! 1

Ya rantse da ubangijinsa zai so Sa’adha ya kula da ita, ya kare ta da dukkan wani iyawarsa a duniyar nan, saboda ya fahimci cewa iya abinda zai iya yi mata kawai kenan!

***
A cikin mota lokacin da yaje d’aukarta bayan ya shiga gidan ya karb’o godiya kala-kala a wajen kowa, Nanne tayi ajiyar zuciya mai nauyi, ya mik’o hannunsa da baya kan sitiyari yayi squeezing nata a hankali.

“Me ya faru? how did it went?”

“Ba abinda ya faru Ulfat, Inna ta fahimta tun kafin ma in bata slightest hint…kuma kowa da yaji yayi farin ciki komai ya tafi daidai.”

Ya gyad’a kansa  ba tare da ya kalleta ba idonsa na kan titi.

“Komai zai tafi daidai insha Allah Noory.”

“Insha Allah.” Itama ta amsa.

Ta san cewa ya fahimci akwai ‘yar damuwa a tare da ita amma bai tambaya ba, and she was glad that ya barta tayi keeping abun a cikin zuciyarta, in ba haka ba bata san ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta a tsinke take na ganin irin farin cikin da inna ke ciki game da Babynta ba alhalin ita tana b’oye mata wani babban abu da ya kamata ace ta sani, ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta ta dagargaje kamar irin yadda tasa tayi ranar da aka d’aura musu aure, ranar da yaga irin tarin al’ummar daya d’ora akan fake labarinsa.

Maimakon ya kaita gida a lokacin sai ya canja hanya zuwa wani k’aton mall dake d’auke da wajaje da yawa a cikinsa, watakila ya fahimci damuwar da take ciki ne a lokacin, ya fahimci yanayinta ya canja kamar yadda itama take gane komai nasa da duk wani slightest bit na motsinsa, cikin sa’a kuma sai frozen vanilla yoghurt din da suka siya ya taimaka wajen lifting spirit d’inta, taji sanyinsa har yana barin wani danshi a can k’asan zuciyarta.

Kusan minti talatin suna zaune a d’aya daga cikin kujerun park d’in wajen ba tare da sunyi magana ba, shiru da sanyin bishiyun wajen ya saukar da wani peace of mind a zuciyar kowannensu.

Sai da Nanne ta d’aga robar yoghurt d’inta taji ya k’are tas! sannan ta yar da ita a gefe, ta juya ta kalle shi sannan tace.

“Ayunie we need to talk…akwai abinda kuka tattauna da jaamil lokacin da Bwama tazo, You need to tell me, ina son inji me ya faru.”

Imran yayi squeezing robar chocolate ice-cream d’in da ya gama sha shima, he’d seen this coming…ya riga ya san Sa’adha ta fahimci damuwar da yake ciki tun wancan lokacin kuma ya dad’e yana jiran zuwan tambayarta dama, tambayar da ya riga ya shirya amsarta daki bayan daki.

Sai dai kafin yayi magana, idonsa ya hango masa text d’in da ya turawa jaamil a d’azu.

Komai zai cigaba da tafiya kamar yadda muka tsara jaamil, ba abinda zai canja ko ya tsaya, zanje in karbo dutsen Nil….zan kare Sa’adha dashi kuma zan d’auki fansa akan Naani dashi! 
“Naani ce ta dawo kuma ta san da dukkan abinda ya faru amma bata san da zancen cikinki ba…so mun tattauna yadda zamu b’oye mata sanin hakan ne har zuwa lokacin da zaki haihu, saboda in har ta sani ba zata yarda ba Sa’adha, ba zata yarda muyi abinda baya cikin tsarinta ba.”

Imran ya fad’i k’aryar da zata lullub’e ainihin gaskiyar da yayi niyyar gaya mata a da, ainihin gaskiyar da zata sa ya daina barinta a duhu game da al’amarin Naani, don a yanzu yana ganin ta cancanci ta san ko wane gutsiren al’amari game dashi, he can’t hide anything fom her! amma sai kalaman da Bwama ta fad’a masa suka hana shi furta mata ainhin gaskiyar…

“Kar ka tab’a bari ranta ya b’aci har ta shiga damuwa yarima, dole ne ka dinga b’oye duk wani abu da kasan zai takura zuciyarta…oum veri nah kour menku rajern! (stress will only make her more ill.) irtou nah kalabg daer waqatu harvil jourda gnawyer bayadda ferl…(Zuciyarta da duk wani k’arfin jikinta sun ta’allak’a ne yanzu akan abu guda, she can’t be distracted.) hazar fumerbe ferl don sartu nah, gzarde ser tah ngam!  (You have to he composed, you can’t make it harder for her.) 1

Wad’annan kalaman su suka hana shi fad’a mata ainihin yadda zuciyarsa ta dagargaje da kuma irin ciwon da take yi bayan yaji kalaman Naani daga cikin Habler nan, Amma kwakwalwar Sa’adha was so sharp than tunaninsa.

Ta tsuke idanunta kad’an sannan tace.

“Ayunie ka tabbata ba wani abu da Naanin take shiryawa da zai cutar dani ko kai?”

A lokacin data fad’i hakan wani abu a k’irjinsa ya tarwatse sannnan harshensa ya k’ulle… ta ya zai fara gaya mata cewa he just found out cewa Naani bata tab’a nufinsa da alkhairi ba, ta d’auko shine kawai don ta gyara rayuwarta daga k’arshe shi kuma ta tsaida tasa…

Daga yanayin fuskarsa Nanne ta fahimci cewa ba zai bata amsa ba, saboda haka ta kwantar da kanta a kafad’arsa sannan ta zuro hannunta ta cikin nasa.

“Koma meye Ulfat, na san I’m safe with you!”

Matsalar kenan! gabad’aya tunaninta akansa were all backwards… bata tab’a gane hatsarin da rayuwarta ke shiga akansa, a koyaushe tana bashi wata yarda ne da shi bai cancanta ya samu daga gare ta ba, maimakon guduwa tana k’ara cusa kanta ne wajen da yake da hatsari…watakila kuma laifinsa ne da tun farko bai nuna mata hakan ba.

Amma ta yaya zai kare ta daga kansa alhalin dukkan zuciyoyinsu basa son hakan?

Sai ya jingina kansa shima a saman nata a hankali, idanunsu na kallon k’ayatattun lilukan park d’in dake can gabansu!

****

BAYAN WATA UKU.

“Kina da popo pos?” Hidaya ta tambaya zaune daga kujerar island na kitchen d’in.

Nanne ta k’ara d’auraye bakinta daga d’an guntun aman da tayi a sink sannan ta juyo ta kalleta da murmushi, wani murmushi da ya fad’a can cikin ramin kumatunta kamar yadda idanunta da suka d’ashe suka yi zurfi a can cikin lungunsu.

A cikin watanni uku kawai wanda ya san Nanne a baya zai yi mutuqar wuya ya gane siffarta a yanzu, wata siffa da a kullum innarta ke kira da kwarangwal… don d’an karamin jikinta ya yamushe sosai cikin abinda za’a iya kira fata da k’ashi kawai, fuskarta ta sirance sosai ta yadda k’ashin gefen hab’arta ya fito k’arara yana haska idanunta da suka d’ashe tas!

Gashin kanta mai cika a yanzu duk ya yamushe ya kuma wani d’an yalolo sai tsawo ne kawai dashi…sai dai duk wannan canjin babu shi a cikin zuciyarta… zuciyarta da take b’ul-b’ul cikin k’oshin lafiya kuma cike da murnar sanin Babynta yana raye cikin k’oshin lafiya, don a kullum in banda k’ara girma ba abinda yake yi, girman dake tada hankalin ‘yan uwanta ganin yadda ita take k’arewa kullum a tsaye.

STORY CONTINUES BELOW

Sai dai tunda har bata jin wani ciwo ko kad’an sai inna ta kashe bakin kowa da cewar ko wacce mace da irin yanayin cikinta, ita nata laulayin a haka yazo mata… amma duk da hakan tana ganin tashin hankali kwance a k’asan idanun innar ko yaushe taje gida, tashin hankalin da duk girmansa bai kai na Imran ba, shi da a kullum suke kwana da tashi tare, ya san cewa bata cikin wani ciwo in banda rashin tak’amaiman abincin da bata iya ci…duk kuwa da duk irin k’ok’arin da Bwama ke zuwa bata na magungunansu kala-kala amma bata iya cin wani abun kirki, abinda ke bata mamaki kenan na ganin yadda kuma babyn ke ta girma a cikinta.

Babyn da har yanzu bata san ya yake ba, don taje asibiti sau d’aya, a wata rana da ya zama ya zama silar fad’uwar wani jigon a rayuwarta, taje gida ta had’u da ya Ahmad sunzo shida matarsa da ‘ya’yansa, tunda cikinta ya fara baiyana bata ganshi ba sai a wannan ranar…inda yayi mamaki ganin yadda duk ta k’are saboda haka yace zai dubata don bai tab’a ganin ciki irin nata ba, inna kuma ta bada goyon bayanta da cewar itama a lokacin taga ramar tata ta fara yawa, Ba irin hanyar da bata bi ba don ta zille masa amma sai da inna tasa ya d’auketa ya tafi da ita can asibitinsa. Inda wani al’amari ya faru daya jijjiga tunaninsa, gabad’aya injinan ultrasound na asibitin suka k’i aiki a jikin Nanne, ba abinda suke nunawa sai tarin wasu alamomi da suke fad’in…

The membrane is too hard!

Wato fatar dake lullub’e da babyn tayi karfin da ultrasound d’in ba zai iya ratsawa ya haska cikinta ba. A lokacin ne ya karb’i wayarta ya kira Imran da cewar yazo ya same su a asibitin, wanda kafin zuwansa ba irin magiyar da bata yi masa ba akan ya fad’a mata abinda ya gani amma yayi shiru kawai yana kallon hawayen da take yi, hawayen da ya kasa tantance na tsoro ne ko kuma na son kare abinda take b’oye musu.

Lokacin da Imran ya k’araso cikin asibitin a d’an k’ank’anin time, lokacin ya Ahmad ya bud’e baki ya fad’i abinda Nanne bata tab’a zata ba.

“Imran ka san cewa abinda ke cikin matarka ba mutum bane?”

Zata iya tuna yadda fuskar Ayuninta take hard a lokacin, wani emotion da ya tabbatar mata cewa abinda take tsoro ya faru, baiyi magana ba ko sau d’aya har sanda ya Ahmad d’in ya sake tambayarsa.

“You need to tell me, wane asibitin kuke zuwa suna yaudararku tun farkon samun cikin nata?”

“Ya Ahmad dan Allah….”

“Shshshsh….” yayi saurin katse ta idonsa cike da b’acin rai da kuma wani abu kamar tashin hankali.

“Da mijinki nake magana, kar ki sake kisa min baki.!”

Daga yanayin idanunsa da muryarsa ta riga ta san what he’s capable of a lokacin, ta san halinsa sarai, ta san babu abinda zai hana shi tunkarar Baffa a ranar da zancen, saboda haka ta juya wajen Imran dake zaune kamar gunkin da aka sassak’a ta rik’o hannunsa sannan ta kira sunansa… sunansa direct don ya san cewa abinda zata gaya masa da gaske take, hakan kuwa yasa ya juyo da kansa ya kalle ta, idanunsa were so dark! alamun feelings kala-kala a tare dashi amma bata kula da wannan sosai ba, abinda zata fad’a a lokacin shine priority… a hankali muryarta ta fito ta cikin fuskarta dake shab’e-shab’e da hawaye.

“Wipe his memory please!”

“What? Me kika ce?” Muryar ya Ahmad tayi ihu daga gefensu.

“Ka goge tunaninsa Ayunie dan Allah, in ba haka ba komai zai ruguje mana ne…za’a illata Babynmu.” Ta sake fad’a idanunta akan Imran.

“Nanne kina da hankali kuwa? me kike cewa? me ya same ki? me zai yi…”

He trailed of cike da tambayoyi kala-kala, amma bata juya ta kalle shi ba, idanunta na kan imran da take rok’o da dukkan wani senses na jikinta akan ya taimaka yayi hakan, daga yanayin idanunsa kad’ai ta tabbatar baya son aikata abinda ta fad’a amma kuma ba zai iya mata musu ba, don shi kansa ya san basu da wata mafitar data wuce hakan, ya Ahmad ya riga ya san wani b’ari na sirrinsu da ba zai tab’a rufuwa ba saboda haka ya gyad’a kansa a hankali sannan ya mik’e ya juya wajen ya Ahmad dake k’ok’arin lalubo wayarsa a lokacin.

STORY CONTINUES BELOW

Nanne ta juyar da kanta zuwa kallon k’ofa hawaye na bin idonta daidai sanda Imran ya tsaida duk wani abu dake motsi a cikin office d’in cak! har kuwa da nata tunanin…. Sannan irin abinda ya faru ga masu hoton nan ya kasance ga ya Ahmad, memory d’in abinda ya faru tas! ya d’auke daga cikin kwakwalwarsa. 2

Daga wannan ranar kuma suka tattara komai nasu suka bar cikin garin katsina zuwa Abuja, Nanne ta bar cikin mahaifarta don kare abinda take ganin shine rayuwarta a yanzu, kuma hakan yazo musu da sauqi tunda a yanzu Imran ya riga ya bar aiki a kamfaninsu, abinda ya kaishi ya riga ya k’are kuma ba zai tab’a iya cigaba da zama ba tun bayan abinda ya faru tsakaninsa da Naani.

Wani abu da ya zamo…..

“Baki da popo pos d’in?” Muryar ‘yar yarinyar d’azu ta janyo kwakwalwar Nanne daga tunanin data tafi, ta k’ifta idonta da sauri sannan ta kalleta sosai, tayi tagumi da hannayenta akan island table d’in kamar sanda take tunanin ita kuma ta tsaya ne tana kallonta. Sai data d’anyi gajeren tunani sannan ta gane me yarinyar ke nufi.

“Coco pops kike so?”

Ta d’aga kanta da sauri.

“Eh nawa ya k’are kuma Daddy bai shiyo ba.”

Yadda tayi maganar tana turo d’an plumpy lips d’inta ya burge Nanne ta shafa kumatunta ta hannunta d’aya sannan tace.

“Karki damu hidaya zaki sha coco pops yanzun nan, amma zaki yi game kafin a kawo?”

“Yey! kina da candy crush?” Ta tambaya with pleading eyes.

“Oww…bani da candy crush amna akwai garden scapes, yana da dad’i.”

“I’m in!”

Ta fad’a da sauri tana d’aga hannayenta, Nanne tayi dariya ta koma falo ta d’auko mata tablet d’in Imran, ta nuna mata yadda zata yi gane d’in sannan ta d’auko wayarta ta kira shi, zuciyarta na fatan ya amsa kafin ta tsinke, don wajen sabon aikinsa na yanzu, aiki yake sosai fiye da wancan tunda suka gano irin kwarewarsa a harkar advertisiment d’in nasu, abinda take gani ya taimaka wajen lifting spirit d’insa da bashi kwarin gwiwa wajen manta abinda ya faru tsakaninsa da Naani.

Wani abu da ya zamo…. 1

“Hello! sweatheart ta tashi?”

Muryarsa ta silalo ta cikin speaker wayar, tayi murmushi kad’an.

“Na tashi Ulfat, kuma gidan ba dad’i, na saba da kai a cikinsa, kana tunanin weekend d’in nan ya b’ata ni?”

Taji sautin murmushinsa kafin yace.

“Ina tunanin ni na b’ata ki baby.”

Ta ciji gefen lebb’enta tana danna hannunta cikin shinkafar data d’ebo a wani bowl zata wanke.

“Tell me how much you miss me Noory…ina nan inata ganin fuskarki akan screen d’ina, I kept checking time kowanne minute a wayana don inga fuskarki, (Picture d’inta was his wallpaper) And beleive me it’s getting out of hand don na kasa ko gama project d’aya.

So tell me naki storyn.”

Ya Allah! wai yaushe ne zata saba da irin wannan kalaman na Imran, maimakon ta biye masa sai tace.

“Dan Allah zamu samu Coco pops in zaka dawo?”

“Coco pops?”

Tana iya jiyo mamaki a cikin muryarsa.

“Are we talking Babies?”

Murmushinta ya k’aru, ta sake nutsar da hannunta cikin shinkafar.

“Ni dai in za’a samu dan Allah ka taho dashi.”

“Sure Babe kar ki damu… your wish  my command.”

Ta gyad’a kanta a hankali kamar yana ganinta sannan tace. “Come back soon!”

“I will habibty.”

Tana ajiye wayar ta koma kan girkin da take yi, tun dawowarsu gidan bata tab’a d’ora wani abun arzik’i ba, kullum girkinsu ‘yan kame-kame ne kawai, saboda haka a ranar tayi niyyar zama ta yiwa Imran girki sosai tunda ita ba iya ci take ba, sai dai tunda ta fara zuciyarta ke tashi tana ta yin k’ananan amai akai-akai, amma bata fasa ba don ta dake zuciyarta cewa zata yin.

Kusan minti talatin tana aikin suna ‘yar hirarsu jefi-jefi da hidaya tana mata tambaya game da kewayen unguwar da kuma makarantarsu, wata amsar ta gane, wata kuma ta had’e cikin jagwalgwalon gwarancinta…

Bayan wani lokaci ta tsinci muryar Imran daga k’ofar kitchen d’in lokacin ta gama sauke abincinta, tana had’a samosan da take yi, kafin ta k’arasa amsa sallamarsa taji hannayensa guda biyu sun zagaye k’ugunta.

“I’m back!” Muryarsa mai taushi ta fad’a dab da kunnenta, numfashinsa ya busa akan fatarta, taji tsigar jikinta ta tashi.

“Sannu da zuwa.” Ta fad’a a hankali tana k’ok’arin fitar da numfashinta.

“Mhmhmm.” Ya amsa softly yana grazing fuskarsa a cikin wuyanta, taji k’afafunta sunyi sanyi amma duk da haka ta karkata kanta kad’an don ta bashi more space.

“You feel warm habibty…”

Abu ne mai mutuqar wuya idan Imran na tab’a ta ta iya wani tunani mai kyau, saboda haka it took her a minute of scattered concentration kafin ta iya tuna cewa Hidaya na zaune a bayansu, da sauri ta juya game da d’an ture shi amma ga mamakinta ba kowa a zaune wajen island d’in nan, sai tablet dake kan table.

“Ayunie Hidaya tana ina?”

Girarsa biyu ta had’e waje guda.

“Hidaya? Wace ce ita?” 1

“Baka ganta ba, tana zaune fa anan.”

Kafin yayi magana ta kwance hannunsa dake rik’e da ita sannan ta bazama cikin gidan tana ta faman kiran sunan Hidaya.

Imran yabi ta da kallo cike da mamaki, wace ce kuma Hidaya, a ina ta samo ta? A ina ta sami wata yarinya mai suna Hidaya? yaji gabansa ya fad’i wani abu mai kama da zargi ya d’arsu a zuciyarsa, tun bayan abinda ya faru tsakaninsa da Naani, zuciyarsa bata tab’a hutawa ba, don wani abu ne da ya zamo….

“Hidaya…kina ina?”

Muryarsa ta katse tunaninsa, yana iya jiyo yadda bangwayen saman gidan ya d’auka da sound d’in muryarta. Ba shiri ya ajiye ledar Coco pops d’in daya shigo dasu har guda uku yabi bayanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *