WANENE SHI
CHAPTER 8
Nanne ta tsirawa fuskarta ido a mudubin toilet tana nazari. A cikin sati d’aya kawai ta wani irin zabge kuma idanunta sunyi fari fat! sun d’ashe, kamar masu shirin fad’awa duk wanda ya kallesu irin adadin hawayen da suka zubar, ta kai hannu ta tab’a wuyanta a hankali inda wani rami ya fito tsakanin k’asusuwanta biyu. +
Watakila na rashin cin abincin da bata yi ne, ko kuma na yawan tunanin dake faruwa a cikin kanta. A sati d’aya kawai, kwakwalwarta tayi sak’a da warwara akan dubunnan abubuwan da a gabad’aya shekarunta na baya bata yi ba. A kullum zata tashi da fatan cewa wannan zaman da akayi na falon baffa bai faru ba, amma cikin awa daya kawai fatanta zai ruguje saboda irin hada-hadar da inna keyi kamar a satin ne za’a d’aura mata auren.
Aure. A kullum ta fadi kalmar ta sake maimaita ta tasan cewa bata shirya masa ba, don wani abu ne da kwakwalwarta bata taba hasko mata shi nan kusa, bama haka ba, ba zata iya tuna ranar da wai ta hango kanta a gidan aure ba. Balle kuma yanzu da akace za’a tura ta cikinsa nan kusa.
Kwallar da ta taru a idonta d’aya ta ziraro kan kumatunta, tasa bayan hannunta da sauri ta share. Ta riga ta yiwa inna alkawarin daina kuka, tayi mata alkawarin karbar al’amarin nan hannu biyu tun ranar data tasa ta a gaba da rok’on ta taimaka ta dawo da rayuwarta kamar da.
Don tun bayan fitowarta daga falon baffa a waccan ranar komai nata ya canja, ta daina magana, ta daina dariya, ta daina shiga mutane, bata da aiki sai ta dukunkune kanta a gado tayi ta turkar kuka. Ba irin magana da bin bakin da kowa a gidan bai mata ba amma bata ko fahimtar abinda suke fad’a.
Sai da inna taga abin nata na neman d’orewa ne yasa ta sameta ita kadai ta ajiye duk wani fad’anta a gefe ta rok’e ta akan ta taimaka ta yiwa mahaifinta da ita biyayya, tace su iyayenta ne, bai kamata su nemi abu a wajenta ba amna da sunan baffa da kuma ita yau tana neman alfarmata da ta basu had’in kai wajen gyara rayuwarta, don abinda suke k’ok’arin yi d’in taimako ne ga ita kanta.
Abin ya bata tsoro ganin innan na shirin durk’usa mata, a lokacin sai ta manta da komai tayi mata alkawarin cewa ta amince baza ta sake nuna damuwarta ba, tana hawaye itama innan nayi. Kuma tun daga wannan ranar, take kokarin ture duk wata damuwarta ganin ta farantawa innan. Bata k’ara kuka ko nuna b’acin ranta ba, sai dai kuma ta koma wata sabuwar halittar daban.
Bata magana, sai bada amsar abinda aka tambayeta kawai, bata dariya bata kuka, abinci ma tana cin iya wanda ta san zai hana ta galabaita ne kawai. A kullum zuciyarta cikin tarawa da d’ebe tunani kala kala take kawai.
Tunanin yadda zata yi ta fad’akar da kowa cewa ita ba wasu bak’ak’en aljanu dake shirin shafarta, rashin lafiyarta cuta ce kawai ba komai ba. Musamman baffa, tasha had’a irin kalaman da zata je ta tsugunna a gabansa ta fada masa ya gane cewa ita lafiyarta kalau, ya taimaka ya janye maganganunsa rayuwarta ta koma daidai, amma a kullum ta tashi taga wannan farin cikin na fuskar inna, sai tunani ta ya karye ta shiga lalubar wata hanyar da zata fitar da ita.
“Yanzu Nanne har yanzu kina cikin band’akin nan?”
Muryar inna ta dawo da ita cikin zahirin da take.
Da sauri ta bude fanfaon sink d’in sannan ta taba butar dake gefe da kafarta, jin k’arar yasa innan tace.
“Toh Allah kuwa ya sawwake miki. Kiyi ki fito Rahman tun dazu take zaman jiranki, ga dare nayi.”
Jin sunan Rahma yasa ta tuna da cewar yau zasu je can gidan malaman ta karbo magunguna, abinda yasa dole saida ita saboda akwai wani turare da malamin yace za’a dinga mata duk sati, kuma matarsa ce take yi. Sunje wancan satin anyi mata saura na yau kenan. Ta ja tsaki a k’asan numfashinta. Allah ya sani bata ko son ganin mutanen nan. Don a tunaninta, sune silar duk wani hali da take ciki a yanzu.Ta d’auko sabulu ta wanke fuskarta sannan ta fito. Ta d’auki hijabi milk dogo mai hannu ta zura akan kayanta kafin tayi falo. Tana fita inna ta kalleta tace.
“Koma ki d’auro dankwali.”
Bayan abinda da bai kai minti d’aya ba ta sake fitowa ta d’aura dankwalin, bak’i irin na abaya.
“Toh ungo nan…ance idris ya fita da motar kuma yayyenki ba wanda ya dawo, ku hau adaidaita sahu kuje ku dawo kuma dan Allah kar ku dade, ana gamawa ku taho, ko sadiq za’a kira ya raka ku ne ma?”
Rahma tace.
“Inna kin manta sun tafi kaduna. Ba komai zamu iya zuwa mu dawo, ai ba nisa sosai.”
Har suka fita bakin titi, Nanne bata yi magana ba, sai da suka hau adaidaita sahun sannan Rahma ta kalle ta tace.
“An kawo irin takalmin nan da kika ce kina so, wanda ake siyarwa a mak’otanmu.”
Ta kalleta kawai sannan tace.
“Mhmmm.”
Kamar Rahman zata sake magana kuma saita yi shiru. Haka kawai sai Nanne taji ba dadi, babu laifin rahma ko d’aya a cikin halin da take, bai kamata ta canja mata haka ba. Ta tuno yadda ta damu sosai lokacin da take ta kukan nan, a kullum zata shigo d’akin ta dubata sau ba adadi kuma bata tab’a gajiyawa ba akan bata hakuri. Sai ta juya ta kalleta tace.
“Kuma akwai kalar wanda na gani a wajenki d’in?”
Jin haka yasa ta amsa da sauri.
“Akwai mana, ba dai kamar baby pink ba? Har na d’aukar miki ma.”
“Kiji zumudi, to da na fasa siya fa.”
“Sai in karbo kud’in a wajen inna in sai miki.”
Taji wani abu kamar murmushi zai fito ta gefen bakinta. Wanda a ‘yan kwanakin nan ta manta cewar fatar baki na da wani aikin sab’anin magana da kuma karbar abinci. (Gimbiya ruwaila- daga d’aya labarina na komai Nisan Dare!) 1
Basu wani dad’e a gidan ba suka gama abinda zasu yi suka fito. Sai dai har sun kai bakin titi, Nanne ta tuna ta manta purse d’inta da kud’in motar ke ciki a gidan. saboda haka tayi sauri ta koma Rahma kuma ta tsaya jiranta a kofar wani shago.
A inda gidan malamin yake, cikin wani k’aton gida ne irin na mutanen da, irin Family house d’in nan dake d’auke da waje-waje, kuma gidan nasa na daga tsakiya ne, saboda haka da kyar ta iya ganewa, sai dai kafin ta shiga ciki ma wani yaro ya fito rik’e da purse d’in nata da gudu, da alama cewa akayi ya biyo bayansu.
Ta karb’a sannan ta juya, sai dai kuma ta kasa gane hanyar data biyo, kawai sai tayi ta bin lungu-lungu har ya fitar da ita ta wata k’ofa daban da bata nan suka saba shiga ba. Amma sai tayi tunanin ai duk titi ta zata kaita saboda haka kawai ta fita ta nan.
Sai dai me? Layin ya zama daban da wancan, kamar ta koma cikin gidan kuma taga k’ila ta sake b’ata gwara kawai tabi hanyar ta fitar da ita titi inda rahma take.
Layin babu wani haske dake fitowa daga dukkan gidajen wajen kuma babu mutane sosai, saboda haka ta k’ara sauri ta nufi inda take tunanin zai fitar da ita titi, a lokacin ne ta hango wasu mutane biyu su kad’ai sun karyo kwanar dake gabanta. Suna tafe suna magana da karfi tare da kyalkyala dariya.
Gabanta ya fad’i, sannan zuciyarta ta buga da k’arfi.
Tayi saurin matsawa gefe don ta basu hanya. A lokacin suma suka ankara da ita sabada haka tayi saurin sunkuyar da kanta.
“‘Yanmata..!” d’aya daga cikinsu ya kira sanda suka zo dab da ita, ta san da ita suke tunda babu kowa a wajen amma sai tak’i d’agowa ta cigaba da tafiya.
“Yanmata tsaya mana.” mutumin ya sake fad’a sanda ta wuce su, suka juyo suka biyo bayanta. Ta k’ara damk’e purse d’inta sannan ta k’ara sauri.
“Tambayarki kawai zamu yi.” muryan d’ayan ta fada da alamun dariya yake yi. Ta juya baya ta hango suna binta, ga gidan data baro daga can bayansu ba yadda za’ayi ta koma, sai tayi kwanar gefenta kawai da sauri tana jin takunsu a bayanta.
Ta hango wani haske kamar na mota ya tahowa, wani dad’i ya ratsa zuciyarta sai dai a lokaci d’aya tafi kasancewar motar bata ko tsaya ba ta karya wani layi ta b’ace.
“Idan kika tsaya ba abinda zai same ki, zaki koma gidanku lafiya.”
Ta sake jiyo muryarsu daga bayanta, sai kawai ta nufi kwanar da motar ta shiga da sauri idanunta kuma na lalube a hanyar, ko zata gaga wani abin da zai iya taimaka mata wajen kare kanta, katako, dutse, k’arfe ko duk wani abu da zai zame mata a matsayin makami. +
Ba tsammani kawai taji hannu ya fizgo kafad’unta ta baya, ta dawo tangal-tangal sannan tayi yunk’urin fizge hannunta, bata san cewa ba da karfi aka rik’e ba saida taji tayi baya ta daki ginin wani kango.
“Haba ‘yanmata, tambayarki fa kawai zamuyi.”
Katuwar muryar mutumin ta fada. Ta damk’e purse dintama hannayenta na rawa sannan idonta na kallonsu d’aya bayan d’aya.
A daidai sannan ne fitilun mota suka haske wajen gaba d’aya, motar ta taho da sauri kamar zata bige su gabadaya kafin a taka wani irin birki da k’ararsa ta karad’e wajen!Nanne ta k’ara ware idonta ganin wanda ya fito, mamaki ya kusa cinyeta amma kuma sai taji duk wani tsoronta da fargaba sunbi iska, taji kamar ta riga ta kub’uta ne daga hannun mutanen, sannan taji bugun zuciyarta ya dawo daidai.
“Lafiyarki kalau? Ba abinda ya same ki? Ba abinda suka yi miki?”
Wannan muryar mai taushi ta jefo tambayoyin a lokaci guda. Maimakon ta bashi amsa sai ta juya inda mutanen ke tsaye, ga mamakinta sai kawai ta hango su daga can gaba suna gudu.
“Ba abinda ya sameki?” Imran ya k’ara fada tsaye kusa da ita.”
Ta juyo ta kalle shi, sannan motarsa dake gefe k’ofa a bud’e.
“Ta yaya kazo nan? Ta yaya ka san ina nan?”
“Kin tabbata ba abinda ya same ki?”
Ya tambaya kamar baiji me tace ba, sai kawai ta d’aga kai har a lokacin tana damk’e da purse d’inta.
“Mu bar wajen nan.”
Ba musu tabi bayansa ta bud’e k’ofar gaba ta shiga, wani sanyi da kamshi ya ziyarci koina a jikinta. Ya tada motar sannan yayi kwana ya bi hanyar data baro a baya. Har a lokacin hannayenta rawa suke saboda haka bata ce komai ba, Bayan sun fita titi ya juyo ya kalleta.
“Kin tabbatar ba abinda ya same ki?”
Ta daga kanta da sauri.
“Baki buge ba? baki fadi ba? bakya jin jiri ko…”
“Bana jin komai.” ta katse shi a hankali idonta na kallon titi.
Kawai sai ya rage saurin motar sannan yayi parking a gefen titin, kusa da wani shagon saida robobi. Ta juyo ta kalle shi, shima ita yake kallo.
“Sa’adha kin tabbata mutanen can ba abinda suka yi miki?”
“Ba abinda suka min, ta yaya ka san ina can? Me ya kaika wajen?”
“Na wuce ne ta hanyar sai na hango kamar ke, shine na dawo in tabbatar.”
Idanunta suka hasko mata wannan motar da ta wuce ta gabanta. Har a lokacin da mamaki a fuskarta tace.
“Me ya kaika wajen toh?”
“May be ke ya kamata in fara tambaya, ni namiji ne zan iya zuwa koina kuma ina da mota, amma ke a daren nan, sannan wannan wajen….”
Taji idanunsa sun mata nauyi saboda haka ta juya sannan tace.
“Hanya ce ta b’ace min bayan na fito daga wani gida.”
Ya gyada kansa.
“Okay, toh ta yaya kika zo unguwar ke kad’ai?”
Amsar da zata bayar ya tuna mata da Rahma, ta kalle shi da sauri.
“Ba ni kadai bace nida rahma ne, tana can tana jirana.”
“A ina?”
“Ban san wajen ba, amma….” Ta juya ta kalli yanayin wajen.
“Ina tunanin mun wuce shi a baya.”
Ya juya kan motar a hankali sannan ya sauka daga kan titi, suka koma baya tana ya zare ido har suka zo daidai shagon nan da Rahma ta tsaya.
“Ga wajen nan…amma kuma bata nan.” ta k’arasa a hankali tana kallon koina a wajen. Tayi nufin bude k’ofar motar amma yayi saurin danna lock din gefenta.
“Ki zauna a ciki, bari inje in duba.”
Duk da zuciyarta ba’a nitse take ba a lokacin amma ta kasa hana kanta kallon yanayin takun tafiyarsa da kuma yadda kafadunsa suke a k’ame kamar ba motsi yake ba. Ya k’arasa cikin kantin suka gaisa da mutumin ciki, tana kallon yadda mutmin keta masa bayani har sanda ya fito bakin kantin ya dauko waya ya kira sannna dawo cikin motar.Bata nan, ta koma gida.” +
“Kamar yaya? Ya akayi ta tafi?”
“Ta koma gidan da kuka je ta tarar bakya nan sai mutanen wajen suka ce mata watakila kin b’ace hanya ne kika tafi gida saboda haka ta tafi.”
Nanne ta jingina kanta da seat din tare da yin ajiyar zuciya. Ta riga ta tsira daga koma me wadancan mutanen ke shirin yi mata amma zuciyarta ta kasa nutsuwa, tambayoyi da yawa ne ke yawo akanta na yadda akayi imran yaje wajen a lokacin, ta kasa yarda da abinda yace d’azu, don motar data wuce da farko ba itace wannan da take ciki ba sannan ita ko kad’an bata tsaya ba balle na ciki ya ganta.
Idonta ya kai kan titi, a lokacin ne ta lura da yanayin garin, kamar mutane sun fara raguwa sakamakon daren daya fara yi. Ta kalli agogon kan dashboard, karfe tara da minti goma sha biyu. Ta san dole Rahma ta koma gida yanzu kuma hankalinsu zai tashi.
Me yasa ne a cikin kwanakin nan take zama silar tashin hankalin kowa?
Kamar ya karanci damuwarta sai taji yace.
“Karki damu na kira sulaiman yanzun nan nace masa muna hanya.”
Jin an ambaci ya sulaiman yasa ta juyo da sauri ta kalle shi. “Bai tambayeka a ina ka ganni ba?”
Haske fitilar wata motar ya haska mata fuskarsa sanda yayi murmushi a k’asan numfashinsa.
“Bai tambaya ba, watakila yayi tunanin ko na k’ara kade ki ne.”
Abin yaso sata murmushin itama amma sai tace.
“Wannan ranar ma tsautsayi ne amma ko keke bai taba buge ni a hanya ba, sannan a lokacin ma na…..”
Sai ta kasa k’arasawa saboda yadda idonta ya hango mata titin a wancan lokacin, sai da ta riga ta tabbatar babu mota a kusa sai wani babur daga can nesa sannan ta tsallaka, toh ta ina motarsa ta taho da bata ganta ba? Abin yaso yi mata shige da wanda ya faru yanzu.
“Ya kika yi shiru?” ya tambaya a hankali sanda taji suna k’ok’arin sauka daga kan titi.
“Ba komai.” Ta fad’a sannan da sauri ta juya ta kalli window, sai dai sab’anin k’ofar gidansu sai taga sun tsaya ne a wani k’aton chemist mai cike da hasken fitilu. Ta sake dawo da idonta kansa.
“Me zaka yi anan? Dare yana yi ban koma gida ba.”
Ya kashe motar nan sannan yace.
“Ke na kawo.”
Ta kalli chemist d’in sannan ta sake kallonsa.
“Me ya same ni? Na fad’a maka lafiyata….”
Ta kasa k’arasa zancen sakamakon juyowa da yayi ya kalle ta, idanunsa masu kyau suka tsaida duk wani tunaninta.
“You don’t look fine to me sa’adha, its like you are kind of distracted.”
“Abinda ke damuna daban.” Ta ayyana a ranta. Amma a fili sai tace.
“Dan Allah ka maida ni gida.”
Minti uku bayan hakan, wata mace na tsaye a kanta a cikin chemist din. Daga ta zura mata wani abu sai ta gwale idonta kamar zata ciro tsakuwa a ciki. Duk abinda ake yi, idonta na kan agogo da kuma shi da yake ta zagaye a cikin wajen daga kanta zuwa kanta, yana kallon magungunan dake zube akai.
“Kina jin jiri?” matar ta tambayeta bayan ta zaro wani abu kamar tsinke data sa mata a baki.
“Ba abinda nake ji, lafiyata kalau.”
Tayi murmushi tana kallonta.
“Kar ki damu madam, lafiyarki kalau.”
Sai ta jawo wata ‘yar takarda tayi rubutu sanna ta zagaya d’ebo magunguna. Daidai sanda imran ya dawo hannunsa d’auke da k’atuwar robar yoghurt guda biyu.
“Tace ba abinda ya same ni, mu tafi yanzu?”
Lebb’ensa ya motsa cikin murmushi.
“Ko in zauna ne a gwada ni a tabbatar miki cewa bana cin mutane?”
Kafin ta amsa matar ta dawo da ‘yan maguguna a hannunta. Ta nufi inda yake tsaye.
“Yawwa ga wannan su zata sha, na duba na gani lafiyarta k’alau, kawai fargaba ce da kuma gajiya a jikinta.”
Daga inda take zaune, Sa’adha ta san matar nan karya take, kawai dai tana son samun hanyar da zata ci kud’insa ne. Ya mika mata robobin yoghurt d’in yace ta had’a har dasu ta fadi kud’in. Ai kuwa abinda ta fad’a ko waye zaiji ya san ko kusa kud’in abubuwan basu kai haka ba. 1
“Zan iya ganinki gobe?”
Ya tambaya bayan sun koma motar.
“Me za’ayi?”
Itama ta tambaya a hankali idonta na kallon titi. Taji wani abu kamar k’arar murmushinsa kafin yace.
“Karki damu ba nan zamu dawo ba, akwai abubuwa da yawa da nake son i tambayeki ne.” +
Taji kamar ya karanci zuciyarta ne, don watakila ita tarin tambayoyin ma dake k’ulle a kanta game dashi sun ninka nasa. Saboda haka ba tare da tunanin komai ba tace.
“Allah ya kaimu.”
“Ameen. Amma da yaushe zan same ki?”
“May be da yamma?” Ta amsa kamar tambaya.
Ya sake yin murmuushi yana kallon titin.
“Baki tabbatar ba?”
Tun lokacin da ta fara sabawa dashi a asibiti, ta lura yana da yawan murmushi, amma bata yi tunanin yawan ya kai haka ba.
“Na tabbatar. Allah ya kaimu.”
“Ameen.” ya sake amsawa.
Taji wani iri, yadda d’an wannan alkawarin yasa jikinta yayi sanyi bayan duk gwagwarmayar data sha a daren. Sun shigo layinsu a lokacin, komai yana nan kamar yadda yake, fitulun k’ofar kowanne gida sun haska tar! masu gadi na waje da ‘yar rediyonsu sannan tsilli-tsillin mutane na wucewa.
Sai taji kamar duk abinda ya faru a mafarki ne, yanzu ta farka.
Yayi parking a k’ofar gate d’insu amma bai bud’e lock d’in ba. ya miko mata ledar magungunan.
“Ki tabbata kinsha maganin kafin ki kwanta.”
Ta kalli ledar sannan shi, abinda ke idonta ya nuna masa tana shirin k’in k’arba ne saboda haka ya sauke muryarsa k’asa yace.
“…Don Allah.”
Hakan ya tuna mata da ranar daya fara mata magana, lokacin da yake tambayar ta sunanta. Sai ta sauke gashin idonta kan ledar sannan ta karb’a.
“One more thing….” ya katse godiyar da bakinta ke shirin yi. Muryarsa ta canja, ta zama so serious.
“Zaki iya min wani alkawari?”
Ta gyada kanta, a lokaci d’aya kuma tayi dana sanin hakan, ta san me zai tambayeta ne? in kuma wani babu ne da bazata iya ba fa?
“Kar ki sake zuwa inda baki sani ba ke kad’ai.”
Ssi tayi ajiyar zuciya, wannan ai ba wani abu bane.
“Insha Allah, sai da safe.”
“Allah ya kaimu.” ya amsa sannan ya bud’e lock d’in.
Ta juya ta bud’e k’ofar motar, sai dai tana zura k’afarta d’aya waje, ya sake tsaida ita.
“Sa’adha….”
Me yasa ne muryarsa ta saba fad’ar sunanta, watakila don bai san yadda hakan ke sawa taji bane. Ta juyo da sauri ta kalle shi. Saboda shirme wani b’angare na zuciyarta na fatan zaice kar ta tafi ne.
“Sleep well.”
Amon muryar tasa ya amsa a kowanne lungu da sako na jikinta, taji zuciyarta ta buga kamar tana neman hanyar fitowa daga kirjinta. Ba shiri ta fita daga motar ta tura k’ofar gate d’in ta shige.
Babu kowa a harabar compound d’in amma duk fitilun d’akunan mazan a kunne suke alamun ba wanda yayi bacci. Da sauri ta shige ciki kar wani ma ya fito ya ganta. Akwai ‘yan aiki da d’an yawa a kicin din amma bata bari kowa ya ganta ba tayi hanyar sama da sauri.
Tana shiga d’aki ta tarar inna na zaune akan sallayarta.
“Alhmdlilahi, har kin dawo?”
Ta fad’a bayan ta amsa sallamarta. mamaki ya kamata.
“Inna har ne? Ban dad’e ba?”
“A’ah baki dade ba, yanzun nan fa sulaiman ya bar d’akin nan yake ce mana wai kin b’ace hanya ne, amma kin had’u da d’an albarkar yaron nan zai maido ki, itama rahman fitarta kenan ta tafi gida.”
Nanne ta juya ta kalli agogo, karfe tara da minti ashirin, tun kafin su tsaya a chemist d’in nan taga k’arfe tara da minti goma sha biyu, ta yaya za’a ce duk sauran abubuwan da suka faru a minti takwas ne kawai? 1
“Inace ba dai abinda ya same ki koh?”
Ta girgiza kanta da sauri.
“Ba komai inna, dana koma gidan ne sai na fito ta wata k’ofar, na kasa gane hanya, sai Allah ya had’ani dashi ya dawo dani.”
“Toh Alhmdlilahi, ai baki ji yadda naji ba da Rahma tazo min da zancen wallahi, wannan bawan Allah dai Allah ya saka masa da alkhairi…”
Tayi cikin d’aki ta bar innan nata sa masa albarka. Ta ajiye ledar hannunta a kasan gado sannan ta shiga toilet, ta tara ruwan zafi tayi wanka, ta fito tasa kayan bacci tayi sallah sannan tayi wa inna sai da safe ta kashe fitulun ko’ina sannan ta dawo d’aki.
A yanzu ita kad’ai take kwana don Inna ta koma da shimfid’arta falo, ta jawo ledar nan ta fito da magungunan, guda uku ne daga wani pain reliver sai paracetamol da vitamin C, ta san ba abinda take ji a jikinta amma ta d’auko ruwa ta tura su bakinta, sannan ta sa vitamin C d’in a baki.Idan bata sha ba, zata yi ta tuno muryarsa ne sanda ya miko mata ledar. Ta d’auko robar yoghurt din nan tana juya ta, abubuwa da yawa game dashi suna d’aure mata kai, amma gobe ta san komai zai warware, don in har zai mata tambayoyi, itama zata yi masa tambayoyin da zasu sa ta san WAYE SHI. +
Ba zata b’oye komai ba, zata tambayeshi gabad’aya abubuwan da bata fahimta ba, tun daga ranar data fara ganinsa har zuwa yanzu. Ta koma cikin bargon ta dunk’unk’une jikinta rik’e da robar a hannunta.
Wani irin dad’i da fresh take ji a jikinta, kamar an sauke mata nauyin wasu abubuwa, ta manta da halin da take ciki, ta manta da maganganun Baffa, ta manta da abinda ke shirin faruwa da ita, ta manta da wa’adin da Baffa ya bata, ta manta da duk wani zumud’in Inna.
Ta janyo tunanin Imran da duk abinda ya faru a yau da kuma fatan ganin gobe kawai tasa a ranta, goben da take fatan sanin…
WAYE SHI?
Bai san me ya same shi ba, bai san me yasa tunda ya dawo zuciyarsa ta kasa nutsuwa ba. ya san ya riga yayi kuskure tun a jiyan, kuskuren fad’a mata cewa zai ganta a yau, abinda ya san ba zai tab’a faruwa ba. Watakila ko don ganin yadda ta tsorata da mutanen nan ne. +
Shi kansa har yanzu da ya rufe ido su yake hangowa, musamman d’ayan, wanda yafi matsawa kusa da ita sosai yana dariya. Da ace Allah bai kawo shi a daidai wannan lokacin ba, baya jin zai iya tsayawa abinda zai faru.
Daga office ne suka je gidan wani abokin aikinsu daya takura musu da gaiyata tun wajen watanni uku a baya da yayi aure, sai a jiyan Allah ya k’addara zasu je, kuma ya riga sauran da suka je tare tahowa, ganin dare ya fara yi amma su basu da niyyar tashi.
Saboda haka yayi musu sallama ya taho, sai dai tunda ya shiga motarsa ya fara jin gabansa na fad’uwa sannan zuciyarsa tana bugawa, ya rasa dalilin hakan tunda ya san ba abinda ya same shi kuma ciwon Sa’adha a lokacin bai isa ya tashi ba.
Abin ya cigaba da k’aruwa bayan ya fita daga layin yabi hanyar da zata kaishi titi.
A hanyar ne idanunsa suka hango masa wasu mutane daga gefe sannan bugun zuciyarsa ya k’aru a daidai wannan lokacin saboda haka ya juyo da kan motarsa ya dawo.
Anan ne ya hangi abinda ya sashi mutukar mamaki, wasu maza biyu suna kokarin ritsa Sa’adha a jikin wata kantanga, mamaki ya kamashi na ganinta a wajen, kenan abinda yasa shi fargaba kenan? Saboda daya b’arin jikinsa na cikin matsala? Bai san lokacin daya k’arawa motar gudu ba yayi kansu gabadaya.
Abu d’aya ne ya hana shi bin bayan matasan nan lokacin da suka gudu. Idanunta. wad’annan idanun nata da suka cika da d’imbin tsoro, yaji ba zai iya tafiya ya barta ita kad’ai a wajen ba, don bai yarda cewa in har ya tafi wasu irinsu baza su sake zuwa ba.
A zahiri da kuma yadda ta fad’a masa, ba abinda suka yi mata amma har suka hau titi fad’uwar da gabansa yake da kuma bugawar zuciyarsa basu canja ba, alamun har a lokacin tana cike da tsoro, saboda haka yayi tunanin ko sunyi mata wani abun ne ta b’oye masa. shi yasa a lokacin daya tabbatar k’awarta ta koma gida yanke shawarar tsayawa a wannan chemist d’in.
Sannan bayan matar ta gama dubata ta zagaya d’ebo magunguna, ya tsaida duk wani abu dake motsi na cikin chemist d’in ya isa gurinta ya kalli idanuwanta, ya lalubo cikin tunaninta daga sanda suka shigo chemist d’in har zuwa lokacin da ta gama duba ta.
Babu wani abu data gani a jikin sa’adhan, hasali ma tunaninta baya cike da komai sai k’ok’arin ganin meye a tsakaninsu. Tayi tunanin sa’adha k’anwarsa ce ko cousin, don a cewarta ba zai yiwu ace ita matarsa bace, he’s too classy for her. (ya girmewa ajinta.)
Yayi murmushi sanda ya tuna hakan.
Daga baya kuma sai ta koma tunanin yadda zata karbi kud’i da yawa a wajensa, tana tunanin idan ta k’ara akan wanda take dasu zasu isa ta samu ta kai ‘yarta asibiti gobe. 1
Ganin ta bar zancen sa’adhan yasa ya juya ya nufi can k’arshen ginin, wajen da aka jera fridges sannan ya murza hannunsa komai ya dawo daidai.
Ya lura har suka koma cikin mota, bata da nutsuwa sosai, tunaninta ya rabu kashi-kashi sannan hankalinta ya tafi gida, kamar tana ganin wani abu zai faru in bata nan,
Yayi tunanin yi mata magana don hankalinta ya kwanta ko shima ya sami nutsuwar zuciyarsa.
“Zan iya ganinki gobe?”Bai san abinda ya tambaya kenan ba sai da tace
“Me za’ayi?”
Yayi murmushi a hankali saboda yadda muryarta ta fita kamar tana tsoron zai sake dawo da ita chemist d’in ne, saboda haka yace mata kawai yana son yi mata tambayoyi ne
Kuskuren da yayi kuma kenan, na neman kauce tsarin da suka yi shida jaamil. Don a yadda suka tsara ba zai k’ara ganin ta ba sai nan da wani lokaci, lokacin da zata shigo cikin rayuwarsa ya k’arasa daga inda jaamil ya tsaya.
Tsarinsu ya tafi ne a cewar ta riga ta fara sonsa, don haka zata yarda dashi in har komai yazo a k’urewa amma shi bai yarda ba. Ya san Kawai tana cikin Delusion ne irin na mata da yawa da yake gamuwa dasu. Bata san WAYE SHI ba, bata san komai game dashi ba, toh ta yaya zata so shi?
Soyayya shine a lokacin daka yarda ka kuma amince da mutum a kowanne irin hali na rayuwa. Don haka baya tunanin akwai wanda zai so shi, SHI d’in dake bayan wannan fuskar.
Ya san zata shiga damuwa a yau d’in na rashin zuwansa amma ba yadda zaiyi, yayi kuskure da yawa a baya ba zai so ya cigaba da lalata musu abubuwa ba, alhalin jaamil yana iya k’ok’arinsa wajen gyarawa. Ko ganinta a jiyan ma, ba zai taba bari ya sani ba.
Ya kalli had’dd’en agogon dake facing d’insa a saman TV.
K’arfe hudu da rabi.
*******
“K’arfe hudu da rabi.” Sa’adha ta fad’a tana mikawa inna wayar. Inna ta karb’a ta kara a kunnenta tana fad’in.
“Toh ni kuwa ina suka tsaya haka? ace kasuwa tun safe har yamma…” Tayi saurin katse maganar sakamakon d’aukar wayar da akayi daga d’aya gefen.
“…Maryama yanzu Allah baza ku taho ba sai wannan ruwan ya sauko a kanku, kuna ganin wannan hadari haka…”
Nanne ta mik’e a hankali ta isa jikin taga inda iska ke kad’owa ciki kamar zata taho da labulen, garin yayi bak’ik’irin kamar da magariba sakamakon hadarin daya game sararin sama baki daya.
A kusa da tagar akwai fridge, sannan a cikin fridge d’in akwai wannan robobin yoghurt d’in guda biyu, ta bud’e ta d’auko d’aya, sannan ta jingina da tagar tana wasa da ita a hannunta, babu d’ankwali akanta sakamakon ‘yan k’ananan kitson da Rahma ta gama yi mata wanda ya dameta da zafi, saboda haka iskar ta shiga d’aga gashinta tana turo shi kan fuskarta.
Ta tuna murmushin da yayi lokacin daya rik’o robobin a hannunsa.
“Ko in zauna ne a gwada ni a tabbatar miki cewa bana cin mutane?”
Taji kamar itama zata yi murmushin amma ya mak’ale daga wuyanta, akwai abinda yake ba daidai ba yau, duk da ta saba a kwana biyun nan bata da walwala amma yau tana jinta ne kamar tana tsaye a k’arshen wani abu mai tsawon gaske, k’arshen da zata iya fad’owa a kowanne lokaci.
Ta sake hasko gabad’aya tambayoyin data shirya tun jiya a cikin kanta. Bata da matsala ta riga ta had’a komai da zata tambayeshi amma ita bata san me zai tambayeta ba kuma ta matsu taji ya nasa tambayoyin zasu kasance.
Ba irin tunanin da bata yi hasashensa ba tun daga jiya har zuwa yau. Ta hasko cewar imran zai zo wajenta, kuma zai cigaba da zuwa har su saba. Watakila ma har suyi sabon da zai iya neman aurenta kafin adadin lokacin da Baffa ya d’ibar mata.
Don in bashi ba, bata tunanin zata tab’a saurarar wani, balle har a zuciyarta ta yarda dashi tace zata kaishi wajen Baffa. Waye ma zai yarda a yanzu daga fara zuwa wajenta a fara zancen aure? In har dama ba ya shirya bane.
Sai kuma wata zuciyar ta tambayeta game da Imran, meya banbanta shi da sauran? Me yasa take tunanin in shi d’in ne zai yarda a d’an k’ank’anin lokaci ya aureta?
Tayi saurin ture wannan tunanin kar ya b’ata ranta.
Ta maida robar cikin fridge sannan ta dawo ta zauna akan kujera, a lokacin inna ta gama wayar, kuma iskar da akeyi ta k’aru, sannan gari ya dad’a duhu alamun a kowanne lokaci ruwan zai iya sauka, ta dunk’ule a cikin kujerar tana sauraron zancen inna da take mita akan dad’ewar su Aunty maryama.
Kowacce kalma tana shiga kunnenta, amma bata fahimtar komai.
Har aka d’auke ruwan dab! Da maghriba akayi sallah, babu Imran ba alamun zuwansa. Zuciyarta tayi nauyi, sannan jikinta yayi ba dad’i. A
Amma kuma sai ta dinga bawa kanta uzurin cewa watak’ila ruwan ne ya hana shi zuwa. +
Washegari rana ta fito har ta fadi, babu alamun zuwansa. Kwana d’aya, kwana biyu.
Sai ta fara tunanin ta karb’i shawarar da d’aya b’arin zuciyarta ke bata, na cewar ta cire imran daga ranta, yaci ace ta gane cewa shi bai dauketa a matsayin data dauke shi ba. Watakila ya riga ya manta da abinda ya gaya mata tun a daren nan. Koma ya manta da ita ya shiga harkokinsa.
Ya isa ta gane cewa duk sanda suka had’u chance d’in k’ara ganinsa yana sake mata nisa ne. Kuma bai kamata ta cigaba da damuwa dashi a ranta ba. Damuwa da mutumin da bata san waye shi ba.
Ya isa ta gane cewa ba daga Baffa yayi mata maganar aure bane imran zai zo yace zai aureta.
Akwai abubuwa da yawa yanzu a gabanta, su ya kamata ta fuskanta ba wani abu da ba zai taba yiwuwa ba. Sai dai a duk sanda ta tuna tarin taimakonsa gare ta sai wani b’arin na zuciyarta ya sake rik’e fatan cewa zai zo a ranar ko gobe.
Amma bayan sati d’aya sai ta hakura ta cire wannan fatan.
Komai na gidan ya sake dawo mata kamar da, shirye-shiryen inna ya k’aru, zancen aurenta kuma ya biye gabad’aya danginsu, sannan a kullum kwanakin da Baffa ya d’ibar mata k’ara matsowa suke, komai ya sake cakud’e mata. Fatan da zuciyarta ta samu game da Imran a dare d’aya kawai yayi mata nisa ya zama kamar bai tab’a faruwa ba.
BAYAN SATI DAYA.
BAYAN SATI BIYU.
BAYAN SATI UKU.
BAYAN SATI HUDU.
Baffa ya kirata!Lokaci yana tafiya a kullum kuma a kodayaushe. Walau cikin farin ciki ko bak’in ciki. A duk motsawar agogo guda daya, lokaci ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba. +
Sau da yawa kuma, d’an adam baya fahimtar saurin zuwan lokaci sai ya tsara wani abu yasa masa rana. Anan ne zaka ga kamar ansa igiya ne ana jawo wannan lokacin. Hakan ce ta faru da Nanne, adadin kwanakin da baffa ya d’ibar mata ya k’are saboda haka a kowanne lokaci ta san tana iya samun kiransa.
Muryar Inna ta kutsa cikin kanta.
“Ni na gaji wallahi, had’a kayanki zaki yi ki tafi can wajen babar taki, watakila tunda ita ta kawo ki duniya ita kya iya hak’ura ki sake a wajenta, duk randa aka saka ranar auren kya dawo.”
Nanne ta d’ago daga juya abincin hannunta da take yi maimakon ci ta kalle ta, kwata-kwata ta manta magana innan ke mata balle har ta iya rik’e abinda take cewa ko wanda ta fad’a a karshe.
“Inna me nayi?”
Ta tambaya a lokaci d’aya kuma taji kunyar tambayar. Ita kanta ta san ko makaho ne yake tare dasu ya san cewa ta canja daga Nannen da kowa ya santa zuwa wani abin daban. Wani abu da ita kanta bata sanshi ba. Ta zama kamar wani gunki dake tafiya a doron k’asa, tayi losing duk wasu emotions d’inta.
“Ba abinda kika yi, kuma matsalar kenan, ba abinda kike yi Nanne!”
Ta rufe idonta a hankali, a cikin wata d’aya da ‘yan kwanakin da suka wuce me nene bata yi? bata tab’a fashin makaranta ko sau d’aya ba, karatun da a da bata yi yanzu a kullum cikinsa take, anyi jarabawar first term tazo ta shida a maimakon na goma sha da take d’auka a baya, sannan a iya wannan lokacin ta had’a haddar izu bakwai a islamiyya.
Sai dai bata hira, bata dariya, bata kuka sannan bata tsokanar da kowa ya santa da ita, ta koma kamar wancan lokacin da baffa yayi meeting akanta, lokacin da imran baizo yasa mata wani fata a dare d’aya kawai ba.
“Inna me kike so nayi?”
“Au tambayata ma kike yi? Da lokacin da kike harkokin ki ni kike tambaya me zaki yi?”
Tayi shiru tana cigaba da juya abincin, kafin a hankali kuma tace.
“Kiyi hakuri.”
“Ni ba hakuri nake so ki bani ba.”
“Toh me kike son inyi?”
Har ta bud’e baki kamar zata yi magana kuma sai tayi ajiyar zuciya sannan tace.
“Nanne, kin san dai ba’a kanki aka fara zancen irin wannan auren ba koh? Ba akanki aka fara aure a irin wannan shekarun ba sannan kin san ba’a kanki aka fara aure kafin a kammala makaranta ba koh?”
“Na sani.”
“Toh me yasa zaki sa kanki a cikin damuwa irin haka? Koh auren ne kwata-kwata bakya so?”
Tambayar tasa ta d’ago da kanta da sauri ta kalleta. Tunda aka fara zancen nan ba wanda ya tab’a bata zabi, ba wanda ya tab’a tambayar ra’ayinta. Kowa yaji zancen ko aka gaya masa, fatan alkhairi kawai zaiyi wasu ma su fara binta da shawarwarin da suka danganci auren.
Amma yanzu ga inna na tambayar ra’ayinta, innar da’a yanzu in ta bude baki tace bata amince ba shikenan an rufe babin zancen sai wani kuma. Zuciyarta tayi zurfi cike da rokon Allah yasa ta fahimce ta. Ta gyara zama a hankali sannan ta d’aga kai.
A lokacin taji inna ta rafka salati sannan ta ka’rashe da…
“Na shiga uku ni saudatu, wallahi yau na dad’a tabbatar da zancen malaman nan, dole akwai abinda ke faruwa tare dake Nanne amma banda haka ni ina na tab’a jin macen data bud’i baki tace bata son aure? Sannan don har ance za’a yi mata ta fita haiyacinta ta shiga kunci tana wannan ramar?
Toh wallahi tun wuri ki fita idona in rufe kafin in sassab’a miki…”
Bata bari ta k’arasa ba ta d’auki plate d’in tayi cikin d’aki. Wani k’ololon abu ya makale mata a wuya, taji ina ma kuka zaizo mata a lokacin, watak’ila in ta samu tayi zata samu sauk’i a ranta.
Sai kawai ta zube a k’asan gado sannan ta kwantar da kanta a gefe, ta jawo wayar inna dake kusa da filo, one missed call ya nuna akan screen d’in, ta bud’e ta a hankali sannan ta shiga cikin call log d’in. Sunan Addano ya nuna tar akai, yadda tayi saving number Nuratu dashi.
A cikin sakan d’aya kawai, tunaninka da yawa suka faru a cikin kanta. Ta tuno da zancen da suka yi da ita a wannan zuwan nata na k’arshe, zancen da a lokacin ta d’auke shi ta ajiye a gefe tana tunanin ba na lokacinta bane. +
Ta tabbata yanzu idan taji abinda ke faruwa zata fi kowa cikin farin ciki, watakila ma har tafi inna. Sai kuma ta tuno da zancen d’an yayarta da tayi mata, wanda tace har yana aiki a cikin adamawa, kwakwalwarta tayi k’ok’arin tuna sunansa amma ta kasa.
Idan har abubuwa sun cakud’e mata a yanzu ana shirin aurar da ita ga wanda bata sani ba, me yasa ba zata bi shawarar Nuratu ba ta yarda da wanda take tunanin had’asu? Tunda kamar yadda tace ne ko ba komai zata shiga cikin dangin mahaifiyarta.
Amma kuma ta san wane irin mutum ne shi? Ta san halayensa? Sannan zai yarda ya aureta a iya lokacin da Baffa ya fad’a? Idan ta aure shi adamawa zata koma kenan? Zai barta ta cigaba da karatunta? Wace irin rayuwa zata yi a can?
Tambayoyi da yawa suka dinga yawo a cikin kanta har ta kwanta a ranar, komai ya cakud’e mata, tana ganin kamar an d’ora rayuwarta ne akan faranti dake hannun k’aramin yaro yana gudu. kuma a kodayaushe zata iya fad’owa.
Ta san in har tayi kuskure guda d’aya a yanzu zai shafi rayuwarta ne har abada. Don zai iya yiwuwa tayi kuskuren barin baffa ya zab’ar mata mijin da ba lallai taji dadin aurensa ba, sannan zai iya yiwuwa ita da kanta tayi wannan kuskuren.
Ta rufe idonta a hankali sanda ta sake k’udundunewa cikin bargonta. Kanta cike da tunani fal! Wanda bayan ta farka washegari ta takura kanta ta samu matsaya d’aya.
Ta d’auko wayar inna ta turawa da Nuratu sak’on text. Abu mai muhimmanci a ciki shine.
“Addano na amince da zancen, ki turo SHI!”
BAYAN SATI DAYA!
Baffa ya kirata!
*******
“Naji dad’i kwarai da bin maganata da kika yi Sa’adha. Haka ya tabbatar min da cewa baki d’auki fushin da wasu ‘ya’ya ke d’auka da iyayensu ba a irin wannan lokacin.
Kin kab’i kaddararki da hannu biyu ba tare da kin bari ta tauye ki ba, sanda naga result d’inki nayi farin ciki sosai fiye da yadda zan misalta miki.
Amma a lokacin da mutanen da kika turo suka zo min da zancen neman aurenki, a ranar nayi sallah ta musamman ga Allah Sa’adha, na godewa wa Allah sannan nayi alfari dake fiye da koyaushe.
Kin d’auki hanya mai b’ullewa wadda zaki ga amfaninta, kinyi min biyayya duk da cewa hakan zai tauye abubuwa da yawa na tsarin rayuwarki, amma ina tabbatar miki zaki yi tutiya da abinda kika yi nan gaba, biyaiyarki baza ta tab’a cutar dake ba.
Nayi bincike akan yaron da kika turo, kuma daga kowanne b’angare ban samu aibinsa ba, saboda haka zamu zauna da iyayensa, mu yanke duk abinda ya dace. Tashi kije Allah yayi miki Albarka.”
Nanne taji kwalla na taruwa a idonta bayan ta fito daga falon baffa a lokacin, kwalla ce wadda ta manta yaushe rabon da taga irinta a idonta, kwallar dake tabbatar mata komai yazo k’arshe kenan, ta rufe idonta a hankali sanda d’uminta ya gangaro ya taho kan kumatunta.
Shikenan abinda take wa hangen nesa ya kusa faruwa, Baffa ya yarda da mutumin da a yanzu ta san sunansa Nura. Mutumin dake shirin zama wani b’ari na rayuwarta!
******