WANI AURE
CHAPTER 30
Ki Ki daina furta kalmar mutuwa nan nablah addu’a kawai shine mafuta .
zeenat wacce gabadaya tagama rudewa sbd ganin halin da nablah take ciki tasoma zariya a dakin tana Kai kawo da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
A rude ummi tace kamamin ita zeenat mukaita dakin kasa .
+
Zeenat dake tsintitin acikin dakin takaraso da sauri .
Takai hannuta jikin nablah ita da ummi zasu kamata.
nablah tayi saurin girgiza kanta tana dukan Tear’s da tafin hannunta .
kibari akai ki dakin kasa nablah zai fi sauki akan nan din.
uhmmmm ummi uhmmmm takasa cewa komai sai uhmmmm da murkususu ciwo .
take wani irin gumi me zafi shiga tsaftsafo mata takoina jikinta.
Jikinta ke wani irin kirma Dan azabar radadin ciwo.
ta dinga cizan lip’s dinta da karfi tsabar tashin hankali .
kuka take da idanunta tana kokarin kamo hannu ummi ‘aiko Allah yabata sa’a ta damke hannun ummi ‘cikin nata da karfi tsiya .
nishi take hankali sbd numfashinta dake sizing yana dawo .
zeenat dibo min ruwa a cup kikawo nayi mata addu’a.
hk zeenat ta fita jikinta Na rawa biyu biyu ta dinga taka step taje takawo ummi ruwa acikin cup .
ummi takarba tayi mata addu’a tabawa nablah tasha Amman still ciwon Bai ragu ba .
Sai abunda ya Karu Na naxaba wani irin murdawa cikin nata yayi da karfi aiko ta saki wata irin razananniyar kara wanda Yasa zeenat fashewa da wani irin matsanancin kuka jikinta yacigaba da rawa .
Tana kuka tace ummi Dan girma Allah mukai yarinyar nan asibiti karfa Yar mutane ta mace mana mushiga uku Daga taimako ..
bazata mutu ba inshallahu .
Duk wani taimakon da ummi tasan anayiwa me nakuda tayiwa nablah shi Amman Sam bbu wata alamun zuwan bby wanda hkn ya nuna ummi cewa doguwar nakuda gareta.
Daman km dayawa anasamun hk wani zaga alokacin rainon ciki basashan wahala sai gurin haihuwa wasu km tun gurin daukar ‘cikin suke shan wahala har zuwa haihuwa wasu ma kwata kwata basu San da wannan matsalar ba zasuyi renon ciki lafiya Haka ma haihuwar ‘cikin sauki zasuyi ta .
kuka nablah keyi tana kiran mutuwa zatayi itama zeenat kuka take tana cewa ummi kinga abinda nake gudu da jin tsoro ko……..
ummi kalli yadda yarinyar mutane ke shan wahala kalli yadda numfashinta keyi ni dai wlh tsoro nake ji wani abu yasameta ‘cikin wani irin kuka zeenat takarashe zancenta da wallahi ummi bazan iya haihuwa ba ban zan iya ba wallahi Na hakura da haihuwar gabadaya .
‘Cikin fushi ummi ta buga mata tsawa Dan Allah kiyiwa mutane shr duk kinbi kin cikawa mutane kunne ba’a haihuwa ke uwarki ta haifeki.
zakizo ki ishi mutane da surutan banza da wofi shasha kawai ‘aiko kowace da yadda haihuwa take zuwa mata kamamin ita ni mukaita kasa .. .
Haka suka kama nablah zuwa dakin kasa ummi ta kwantar daita tunda tun dazu a tsugunne take a sama har garin Allah yawaye ciwo yaki ci yaki cinyewa banda murkususu ciwo bbu abinda nablah keyi da ikin kiran sunan mamata da mutuwa zatayi .Wani daren yashigo nablah Na kan abu daya , tayi firifiri daita tayi mugun fita haiyacinta iya jigatuwa tayi shi har tasoma gajiya tana janyo numfashi da kyar tana fitawar da kyar km still ummi da zeenat Na tsaye akanta Amman haihuwa shr.
Gashi km sosai nablah ke jin wata irin azababen azaba har tasoma fezgar gashin kanta ….
ta daina gane suwaye akanta ta dawo bbu karfin komai ajikinta bakinta ya bushe sannan Yayi fari fat.. idanunta suka bushe .
hawayen dake idanunta suka kafe suka bar xuba bakinta ne kawai ke motsin ahankali tana karanto duk wata addu’ar tada iya ji taje da zata iya data fizge ‘cikin jikinta ta huta da radadin azabar ciwon datake ji …
Daren ranar bbu shiri ummi ta da zeenat suka cucibi nablah tamkar wata Yar bby suka sakata abayan mota batare da sanin kowa ummi ta zauna baya tare da nablah zeenat ta shiga gaban mota ta tayiwa motar key sai wani asibiti kudi me zaman kanshi da shegen kyau. +
suna xuwa hospital doctor yana dubata yace haihuwa ce Amman km da saura Dan yanzu ma tasoma nakudar domin har lokacin jikin nablah Bai bude.
ba jin Haka Yasa zeenat sadaukarwa da mutuwa zatayi duk wannan azabar data kwana tana Sha .
Ace km yanzu taka fara nukuda ita kam tunda take arayuwarta bata taba ganin irin ciwon nan ba.
shi Yasa tasawa ranta ta nablah takare ..
Tun daren jiya jikin mahaifiyar nablah yake a tashe takasa runtsawa sakamakon gabanta daketa aikin faduwa tamkar ana buga mata guduma wanda batasan dalilin faruwar Hakan ba Dan Haka ta Mike jikinta a sanyaye Daga kwanciyar datayi tazo ta dauki buta tayi alwala tashiga jero nafiloli da addu’oi neman tsari .
Shi can bangaren deeni tun daren jiya jikinshi yabashi gidanshi bbu lafiya sbd mafarkin barkatai daya kwanayi km duk akan nablah ne Dan Haka tun da asuba yashiga neman layin zeenat dana ummi Amman shr bbu wanda ya dauka acikinsu ,Bai hakura ba Yacigaba da neman layin Daga karshe ma daya Kira yaji wayar akashe .
nan fa hankalin shi yayi mugun dagawa yakasa yin komai sannan Kuma rasa jin dadin zuciyarsa kawai yaga gara ya dawo gida .batare da bata lokaci ba yabada Umarni siyan Tiket kawai yana shirya jikinshi yana neman layin ummi dana zeenat Amman har lokaci shr swchoff ake ce masa . Wani tashin hankali ma sai jirginsu ya sauka a Lagos gabansa ya tsananta faduwa zuciyarsa Na tsinkewa Allah Allah yake yaganshi agida kawai ..
Yana shigowa ‘cikin gidan da zeenat yasoma cin karo ya sauke ajiyar zuciya da karfi yana dubanta tana sauri tana hada kayan bby Na haihuwa Dan jiya daddare basu tafi da kayan haihuwa ba sbd a rude suke.
tana ganinsa duk ta dabirce tasoma kuka muryasa Na rawa yace Ina nablah da ummi ‘cikin sharar hawaye tace suna hospital prioucion s .
Tun jiya batada lfy amman doctor yace nakuda ce ….inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana tafiya yana furta hakan acikin zuciyarsa atare suka shiga mota gabadayansu a rude suke .sanda ya iso asibiti nablah ta jigata iya jigatuwa bbu kowa agurinta sai nurse nurse ne tare daita.
deeni ko gaisawa bai tsaya yi da ummi ba. +
Hankalinsa a matukar tashe yace Ina nablah take ?
Suka nuna mishi dakin haihuwa Kai tsaye yashige ‘cikin labour’ room din wata doctor ce tace please sir kayi hakuri ka Dan jiramu awaje hankalinsa a matukar tashe yace madam Dan girma Allah kiyi hakuri nima Ina son naga matata .
Ai yana dora idanunshi akanta Bai san sanda hawaye suka shiga siyayo masa .
ya mannata ajikinshi ya rungumeta yana kuka da aikin jero mata sannu bbu kaukautawa addu’a kawai yake mata yana zubda hawayen tausayinta ya dinga jin daana kar bar wa mutun nakuda daya karbarma ta huta tun daren jiya ake abu daya har yanzu . tamkar shi nakudar take jira ta tashi zanga zanga Amman haihuwa shr bbu labari .
Hankali likitoci Suma yayi matukar tashi sosai tun daren jiya suke tsaye akanta , zeenat kuwa a ranta tace tun dai shekaranjiya Dan dai bamu gaya muku gsky bane .
.. likitoci suka tabbatarwa deeni zata haihu zuwa karfe goma shabiyu ranar Amman gashi har yanzu shr Ga dai ‘cikin Na motsa alamun bby ‘cikin Na raye.
Sosai hankalin deeni yakai karshe gurin tashi tsigar jikinshi har tashi suke tsabar tausayin yarinyar .
ganin har biyu tayi ta wuce bbu sauki sai wahala datake Sha Yasa Shi cewa doctors din suyi mata aiki su cire mata abinda yake ‘cikin ta huta .
tunda sauran karfinta yazamo yanzu ko nishin bata iyawa sai shanyayyun idanunta datake jujjuyawa wal wal dasu .
Hudu daidai aka yi mata shirin aiki sai addu’a ummi keyi ita ko zeenat kuka take sosai har da shesheka .
A dakin tiyata sabon ciwo yatashi ‘cikin zafi zafi ta dinga jin bayanta tamkar ana Sara mata da ada jikinta wani irin rawa har gadon datake kwance akai shima sheking yake .iya wahala nablah tasha sai dai Allah sauketa lafiya ..
Deeni rike da hanuta yana kuka yana mata addu’ar .Shi yanzu bata ‘cikin jikinta yake ba ,ita din yafi bukata .domin duk yadda yakai da son haihuwa sai daya ji ta fita aranshi tausayinta da kaunarta ke zariya a gangar jikinshi.
wani irin uban nishi tayi da karfi sai Ga kan yaro ya fito fit .
Jim kadan wani kadan wani yaron ya sake fitowa sororo deeni yayi yana kuka yana kallon ikon Allah Wani sabon kukan farinciki ya kufce masa ya rike hannuta gam yaki saki sai sumar kanta yake shafa ahankali yana mata sannu can km sai Ga wani sabon ciwo nakuda take doctors din suka gane Yan uku ne suka taimaka mata aka fiddota agalabaice duk tafisu shan wahala Dan ko kuka batayi.
nan suka fita da yaran duka uku Dan gyarasu ummi tayi matukar farinciki da saukarta lfy an shirya yara ummi nata murna .Shi kam deeni bbu wanda yake son Gani kmr nablah doctors sukace masa kada ya damu ana kimtsa ta ne suka mata allurar bacci sannan suka kaita dakin hutu bacci take sosai Dan batasan irin hidimar da’akeyi daita ba .koda zeenat taga bbys sai kirjinta ya buga sbd tsabar kamanin da suke da deeni sak sak komai Nasu Na deeni har ma gara ta mace ta dauko kamanin uwarta sai sai farin Na deeni ta debo .’aiko take tasoma yiwa ummi mitar kamanin yaran .Kai zeenat wlh Kin fiyye matsala Wani kama yaran nan sukayi da deeni kawai idanunki ke ganin hk Amman ni Banga hk ba ..
+
Tun asibitin ummi ta dinga kiran dangi tana sheda musu zeenat ta haihu sauka lafiya tasamu yan uku .
Sannan ta tilasawa doctor kan sai ya sallamesu a ranar doctor yace a’a sbd uwar tana bukatar hutu .ummi tace bbu damuwa abar uwar anan zasu wace da yaran doctor yacika da mamaki Amman dayaga ai sune suka kawota yace shikennan .
Suna komawa gida nan dangi sukayi matuka murna da farinciki saukarta lfy kowa sai albarkaci bakinsa yake fada Kai Kai zeenat gsky kin iya haihuwa tamkar bake ce kika haifi yaran nan ba.
Kai Masha Allah Yara sak ubansu takoina deeni yaran nan suka dauko ita dai sai dai tayi murmushi kawai tana duban yaran dake kwance masu tsantsar kamanin da mijinta tun asibitin gabanta ke faduwa sbd tsabar kamanin da yaran ke yi da deeni ..
ita kam nablah tana can hospital batasan hidimar da’ake da bbys dinta a gida ba.
Dan batama San yan uku ta haifa ba .
Tana farkawa idanunta suka sauka akan deeni ya taso da sauri sannu nablah kin tashi ?
Kallonsa kurum tayi .
Ta kauda fuskarta gefe ya wanke mata baki ‘cikin wani dan karamin kwanan siliva tare da tayarda ita zaune yaje ya ajiye kwano ya hado mata tea me kwari yazo yana bata da kanshi ..idanunta kawai ta tsura masa tana kallonsa tana tea din .
ahankali ,shi kanshi yagane mgn take son yi .. ‘cikin sanyi jiki ta kauda bakinta Daga cup din . alamun takoshi .
Ya ajiye cup ya dawo gefenta ya zauna ya kamo tafin hannunta ‘cikin nashi yana mammatsa mata magana take son yi Amman bakinta Yayi mata nauyi ..
Ya kafe da rikitattun idanunshi gabadaya tayi wata irin muguwar rama acikin kwana biyn din datayi tana nakuda muryarsa a sanyaye yace kina son wani abu ne akawo miki ?
Ta girgiza masa kanta. ahankali .
Ok kimin mgn mana naji muryarki ko wani guri Na miki ciwo ne,?
Nan ma ta girgiza masa kanta ..can km muryarta a raunane tace Ina abinda Na haifa ?
Gabansa yayi Wani irin tsalle Dan baiyi tunanin zata tambayi abinda ta haifa ba .take
Zuciyarsa tashiga harbawa da sauri da sauri muryarsa can kasa kasa yace Suna gida gurinsu ummi .
ta runtse shanyayyun idanunta da suka sake shanyewa tsabar wahala dataci .
yabita da wani irin kallo tunhuma Haka kawai yaji gabansa Nacigaba da dukan uku uku sautin muryarta ya sake ji nima Ina son zuwa gida .yace Ok bari nasamu doctor . Ya Mike tsaye ya sumbaci goshinta kana ya fice da sauri yana waigenta .
+
Byn deen yasamu doctor yayi masa bayanin ko za’a iya sallamarsu bbu wata matsala doctor yace bbu komai ai zasu iya wucewa ..
Sai yamma liss suka shiga estate din ta kofar baya deeni yashiga daita sbd taron mutane dake ‘cike da gidan.
Yan taya murna bai samu damar kaita dakinta ba .
ya nufi dakinsa na kasa daita zuwa lokacin da jama zasu tafi ..
misalin karfe tara Na daren deeni yaje gadon kwanciyar yaran ya dauko mace da namiji ya rungume yaran yana jin matukar son yaran nabin jiki da jinin jikinshi yana mamaye ruhinsa da zuciyarsa .. ummi ta dauko daya suka nufi dakin da nablah take .
Da sallama suka shigo dakin nablah .
suka zauna tare da saka nablah a tsakiyarsu muryar deeni cike da farinciki yace nablah kinga arzikin da Allah Ya …wani irin kallo ummi tayi masa yakasa karasa abin zaice take km yagane ashe yaso ya kwabsa ne..kwantar da yaran sukayi akan bed .wayanda suka Sha wasu haddun kaya sanyi masu shegen kyau da tsada da daukar hankalin farare tas tas dasu tamkar ya’yan turawa ,sosai ta tsurawa bbys din ido tana masu Wani irin.kallo kamanin yaran take kallo ‘cikin tashin hankali taki dauke idanunta akansu yanzu itace ta haifi wayan nan kyawawan bbys din masu kyawun kyau hk ganin yadda yake kallon baby’s din Yasa ummi tashi ta fice shima can deeni ya Mike tsaye yana amsa wayar Yan taya Shi murna ya bar dakin .
Dakin ya saura Daga nablah sai bbys dinta da suke kwance reras akan gado abin sha’awa. kallon yaran tacigaba tana jin Wani irin sanyi Na bin jikinta take km taji Wani irin mugun son yaran yashiga ranta tare da ratsa kowane shashi Na gangar jikinta tundaga tafin kafafunta har ‘cikin kwalkwaluwarta nan take taji idan dukiya zata taru bazata iya rabuwa da yaranta ba ,daidai da daya Daga cikinsu bazata iya bayarwa ba ballanantana dukansu kawai ta fashe da wani irin matsanancin kuka tare da rungume yaranta tasoma sabatu , wallahi tallahi bazan iya rabuwa daku ba yarana Ina sonku ina kaunarku km zan rayu daku.
koda kuwa duniya zatakini .ta zageni akanku Ina sonku takarasa fadar hkn tana sakin Wani irin kuka me cin rai ahankali take cigaba da kallon baby’s dinta hawayenta Na tsaya ahankali tasa hannuta ta goge tana sakin ajiyar zuciya ‘ta daura mazan duka a saman cinyoyinta mace km ta daurata akafadarta tana jin Wani irin dadi mara misaltuwa aranta tare da jin duk abinda zai faru sai sai ya rafu Amman bazata rabuwa dasu ba ….’Cikin wannan halin datake ciki deeni ya km shigowa dakin fasukarsa dauke da wani irin maganadisun murmushi .ta koina ka kalleshi kasan yana ‘cikin tsantsar farinciki da murna samun wayan nan kyawawan bbys din masu matukar kyawun da daukar hankali . +
Ahankali yakarasa inda take zaune rungume da ya’yanta duka .
ya tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta da jin Wani irin mugun sonta da yaran yana tasoma masa .
Yanayin daya ganta ciki yasashi shan jinin jikinshi .
zama yayi kusa daita sosai har cinyoyinsu Na gugar juna ya amshi ta mace Daga hannuta ya daurata saman cinyarsa yana kallonta yana kallon fuskarta nablah dayaga gabadaya ta canza ta dawo wata iri . muryarsa a sanyaye ya Kira sunanta nabeelah ….bata amsa masa ba sai ma juyo da tayi inda yake zaune tayi masa kallon second 2 kana ta dauke idanunta Daga kanshi.
ta maidasu kan yaranta dake cinyarta .
,sautin muryarsa taji a matukar sanyaye fiyye da farkon shigowarsa dakin .. nablah kinga kyautar da Allah Yayi mana ko?
Adakike ta amsa masa da uhmmmm . gsky kin iya haihuwa.
arayuwata bantaba ganin macce data iya haihuwa kmr ki ba .
Gsky kinyi kokari sosai . nan ma tayi masa banza ta sharesa gabadaya ma taki cewa dashi komai .
yanzu mekike bukata akawo miki ?
muryarta can kasa kasa tace babu tare da kamo lips dinta Na kasa tana cizawa ahankali ahankali tana Dan jijjiga kafarta daya akasa .
Gabadaya deeni ya rude yarasa abinda ke masa dadi tunda ta haihu yarasa gane kanta sai wani shashsharesa take tana basar dashi da ciccin magani wanda yarasa dalilinta nayin hk . runtse rikitattun idanunshi Yayi sosai .
ciki Mutuwar jiki sakamakon tuno da kyawawan bbys dinsu data haifar masa masu tsananin kamadashi km yake tare dasu ahalin yanzu.
To me zai dameshi da duk abinda zatayi arayuwa tagama masa komai tunda tabashi abinda yafi so da kauna a rayuwarsa ta duniya . sumbar bby girl din yayi yana jin wata irin natsuwa ta daban tana ratsa kowane shashi Na gangar jikinshi sosai yake son yaransa Amman yafi jin kaunar mace fiyye da sauran acikin zuciyarsa .Jikinasa cike da rauni soyayyarta yakamo tafin hannuta ‘cikin nashi yasoma murzawa ahankali ahankali ‘hade da shaukin kaunarta yace meke damunki nablah naga duk kinyi wani iri hk ? +
Ki sanar da deeni abinda ke damunki banason ganinki ‘cikin wannan damuwa da tashin hankalin please …
yanzu kin zama wata bangare Na rayuwata da farincikina gabadaya sbd wannan kyawawan bbys din dakika bani ..
Kimin abinda wata matar takasa jura ta min arayuwa .
Kin bani kyautarsu alokacin danafi bukata . akan wayan nan yaran bbu abinda bazan iya miki Shi ba , matukar Bai shafi addanina ba .
ban ji dadin yadda naganki ba yanzu.
idan akwai wani abu dake damun zuciyarki ki fito ki sanar min.
ni km nayi miki alkwarin zan yi miki maganinsa kowani iri ne .. yakarasa fadar hk yana matse laulausar tafin hannunta ‘cikin nashi yana jin yadda sonta ke fizgar zuciyarsa gareta ..
So take tayi mgn Amman maganar taki fitowa sakamakon wani yanayi data tsinci kanta ciki ,ita fa bbu abinda ke damunta s halin yanzu wanda ya wuce son rabata da ya’ya za’a yi.
ta lumshe shanyayyun idanunta kana ta budesu ahankali ta zubesu ‘cikin nasa still takasa tabuka komai shima lumshe rikitattun idanunshi Yayi sannan yace Ok kingama ganin yaran zan maidasu kasa sbd masu zuwa ganin bby ..
take zuciyarta ta buga da matsanancin karfi har sai data taji zubowar gudan jini Daga kasanta . afrigice ta zare hannuta ‘cikin nashi tana kallonsa a tsorace bakinta da alamun son yin mgn .
kanshi ya girgiza mata yana kokarin mikewa tsaye .
Muryarta cike da inn inna ta fizgo mgn da kyar tace nifa.. nifa ..ban bada ya’ yana.
what ? Bai San sanda yakoma ya zauna ba .yana kallonta da matukar mamaki .Wallahi wallahi deeni idan duniya zata taru akaina idan sama da kasa zata hade idan za’a yi ruwan jini deeni bazan iya bada ya’ya nan ba.
kai ni daya Daga cikinsu ma bazan iya bayarwa ba ballanantana duka .
deeni koda duniya zata kini ciki kuwa har da mahaifana dakai deeni koda zan dawo kwanan akan bola Ina tsince tsince in ciyar da kaina da ya’ya Na ,bazan iya bada ya’yan nan ba wlh. duk da Allah yasani bansan waye mahaifinsu ba Amman Ina ji ajikina mahaifinsu ba wulakantacce mutun bane duba Ga yanayin ya’ya.
take gaban deeni ya fadi rassss rassss rassss yashiga bugawa da karfi karfi .zuciyarsa tashiga tsalle da kururuwa neman dauki da agaji . +
muryarta ahankali ‘cikin sanyi jiki tacigaba da mgn tunda Na kalli fuskar ya’yan nan narasa meyasa naji Ina mugun kaunarsa wanda bansan dalili ba narasa meyasa tun sanda Na daura idanuna akansu kawai naji bazan iya rabuwa dasu ba .
takarasa mgnr tana fashe masa da wani irin matsanancin kuka me cin rai da Daga hankalin .
Jikinta Na matsanancin rawa ta kwantar da yaran daya byn daya akan gadon.
da kyar ta sauko Daga kan gadon datake ta zube masa a gabansa ta dinga kuka Dan Allah deeni karku rabani da ya’yana Ina son su ko zan rasa raina bazan iya rayuwa bbu su ba.
Wallahi bazan iya rabuwa da yarana ba aduk yanayin da suke Wallahi azim bazan iya rayuwa bbu su ba ni Ina son su a Haka .
kuka take sosai tana rokonsa akan kada surabata da yayanta .
Gabadaya jikin deeni yayi Wani irin mugun tsayi km ilahirin jikinshi suka mace murus yarasa abinda ke masa dadi a zuciyarsa .
Ga koshi Ga kwana yunwa.
hankalinsa ya Kai kololuwar gurin tashi gabadaya yarasa abinda yakamata Yayi ahalin dayake ciki .
kukan farinciki zai yi ko haushinta zai ji Na sabon salon iskanci data tsiro … sai kallon bbys din yake yana kallonta tsugunne agabansa tana risgar kuka tana rokonsa .
shima ajiye bby’ girl din dake hannunshi yayi .
ya tsura mata rikitattun idanunshi da kyau yana cigaba da kallonta hade da nazarinta wato dai da gaske mutuwar son yaran take kmr yadda shima yake matsanancin son su .
duk Shi a tunaninsa yafita son su da bukartasu arayuwarsa ..
a zuciyarsa yaji wani irin matsanancin sanyi ya ratsashi tundaga tafin kafafunshi zuwa kwanyarsa , kennan idan yace zai isar da sakon zuciyarsa gareta bazai Sha wata wahalar shawo kanta ba adalilin wayan nan yaran ..
take km burin mahaifiyarsa ya fado masa .
yaya zaiyi da ummi wace oready tagama gaya duniya da shelar cewa zeenat ta haihu ?
..yaya zata ji idan tasamu wannan mummunar labarin ?Kuka take Sosai ta rike kafafunshi gam deeni kayi hakuri nasan ban kyauta ba akan abinda nayi Amman Ina son ya’yana duk da kasancewarsu shegu wlh ba zan iya kyauta dasu ba kmr yadda nayi maka.. shiiiiii Karki kara kiran ya’ya Na da she.. shegu ni..Ni..ne …sai km yayi shr ya datse harshensa da hakorinsa gam jikinsa Na wani irin matsanancin rawa idanunta dake cike da ruwan hawaye ta xuba masa tana kallon bakinsa .. zuciyarsa gabadaya gaskiya take son fada mata Dan ta daina danganta ya’ yansa da kalmar shegu Amman yana jin matsanancin tsoron tashin hankali dazata shiga fiyye da wanda take ciki ahalin yanzu.. Shi dai yasan xuwa yanzu ya Mika duk rayuwarsa gareta sbd kaunar dayake mata ita da yayanta … +
‘Cikin wannan halin zeenat da ummi suka shigo dakin atare turus sukayi ganin nablah durkushe gaban deeni rike da kafafunsa tana risgar kuka da iyakacin karfinta .
Da sauri suka karasa garesu suna tmbyr deeni lafiya meke faruwa ?
‘cikin rawar jiki nablah ta Mike tsaye ta nufi gurin ummi tana layi tana kuka muryarta cike da kuka tace Dan girma Allah ummi ku min rai wallahi bazan iya bada ya’yan nan ba kumin abun alkhari nasani km Na gode da karamcinku gareni Amman kada Ku rabani da ya’yana …..
A zubure zeenat ta dafe kirjinta tare da cewa what ke kina da hankali kuwa ?
Ke wace irin mahaukaciya ce yaza’a yi kice bazaki iya bada ya’yan ba …..
take nablah ta fuskanceta sosai a fusace tace gaki nan babbar mahaukacirya da batasan abinda takeyi ba da sanin ciwon Kanta ba.
ke kinsan zafin haihuwa ne?ko kinsa zafi ya’ya ke kinsa wahalar dana Sha akan wayan nan ya’ya? +
to nace bazan bayar ba km idan sama da kasa zata hade bazan bada ya’ya nan ba ke ni akan ya’yan nan banki duniya takini ba ciki km har da iyayena wallahi wallahi dana bada ya’yan nan gara narasa rayuwata gabadaya.
ke indai kika ga nabada ya’ya nan sai dai idan bana numfashi a doron kasa .
rassss rassss gaban ummi yayi wani irin matsanancin bugawa da karfi ..Hk ma deeni gabansa ya km bugawa zuciyarsa tacigaba da rawar datake tun kafin shigiwarsu ummi ..
Zeenat tace Wallahi wallahi baki isa ba nablah kinyi kadan km sai kin bada yaran nan tunda tun farko ke kika amince km kinyi alkawarin zaki bada su muryar zeenat Na rawa takarasa fadar hk .
Wani irin kallon tababbiya nablah tayi mata sannan muryarta Na rawa rawa tace to..to.. yanzu nafasa badasu sbd nima Ina son abuna dama can danayi kyautar su bansan zafinsu bane yanzu kuwa sai dai nabawa wasu labari .
Baki isa ba wallahi sai dai kuwa ki rasa ran naki dakike ikirarin rasawa akansu Amman kmr kin bada ya’ya kingama .. Ok zanga wanda ya isa dazai rabani da ya’yana ..
ke nifa nafiki zafin Kai da rashin mutunci akan yaran nan zan iya miki duk abinda yazo zuciyata inji cewa zeenat .
baki nablah ta saki tana kallon zeenat da mamakinta hakan yabawa zeenat damar cigaba da maimaita kalmar dole abasu yara tunda tun farko an rigada anshirya hk da surutai kala kala tayi kan baby’s cike takama zata dauka nablah tayi kuka kura ta dire gabanta cike da maseefa tace ubanwa yabaki damar taba min yara ?
Ubanki da km uban Yayi miki ciki a gidan nan .
a fusace ummi tashiga tsakaninsu tana jan zeenat baya.
ummi ta dinga mamakin abinda nablah tayi duk da tasan Yar tatace da fadan rashin gsky Amman batayi tunani nablah zata iyawa zeenat rashin kunya da tsiwa Haka ba .
Ni zaki kawo danyen Kai da ranshi kunya ta fadi Haka tana nuna nablah da yatsan hannuta Dan girma Allah ummi ki matsa Na canzawa wannan Yar iskar yarinyar halitata dama Ina da ciki daita Ina takaici ta wlh.
kallon kasa da sama nablah ke bin zeenat dashi ahankali wanda ke nuna alamun bata isa ba .
Kina takaicina ai sai kixo ki kasheni ki huta banda mijinki daya nace akan zai taimakamin da tuni ban san inda dare Yayi min .
zeenat tayi sororo tabi deeni da wani irin kallo tana jiran taji yakarya mgnr yarinyar .
Amman taji Yayi shr yana binsu da idanu kawai .
my hrt ummi kuna jin fa abinda yar iskar yarinyar kecewa ko.ummi tace munji ai zance nata duk shirme ne bakya ganin duk abinda take bata ‘cikin haiyacinta tasoma jijjga zeenat din kiyi shiru mu yanzu bawannan shirme bane agabanmu yadda yara zasu zama naki shi kawai .kiyi shr ki natsu asan abin yi .
+
nablah najin Haka ta buga kafarta daya a kasa ta nufi gurin da bbys dinta suke kwance gadan gadan tasa wani irin mahaukatan kuka tana cewa wllahi tallahi ban bada ya’ya Na .
ya’yan guda uku ta rungumesu ajikinta tana sake sakin wani irin matsanancin kuka me ban tausayi da taba zuciyar ma aboci saurare ..
Tashin hankali wanda ba’a saka masa ranar zuwa .
zaune kawai deeni yake yana kallon sarautar Allah.
Yana mamakin daman zafin kan yarinyar nan yakai hk Shi Bai sani ba ….abu kmr a film yarinya tana kokarin birkice musu da dagula musu lissafi.
hatta ummi tsaye kawai take sake da baki tana kallon ikon Allah da yadda nablah ke nuna reaction dinta akan bby din da batasan taka maimain wanda yayi ma ‘cikin su ba .
,to wannan idan km tasan ya’yan deeni ne km jikokinta me zai faru ? Tayi wa kanta tmbyr tana cigaba da kallon nablah rungume da yara tana kuka .
tamkar wata zautaucciya .
Gabadaya Daga deeni har ummi kasa tabuka komai suka yi sai idanu da suke bin nablah dashi …
Wani irin tausayinta ne me gyaraye da tsansar soyayyarta ke sake huda kirjinsa da mamaye gangar jikinshi da zuciyarsa .
alahakikanin gaskiya Bai taba tunani yarinyar zata canza salo irin Haka ba.bai dauka zata so ya’yan da ta dinga hauka akan acire mata su ba .
Wani irin gumi ne me zafi ya shiga tsaftsafo masa ta koina ajikinshi yazama tamkar wani mutun mutumi a zaune yana kallon nablah kwakwume da bbys ajikinta duk tayi firi firi tafita haiyacinta .
Take zeenat ta dinga jin zuciyarta tamkar zata fashe ta tarwatse kan takaicin nablah.
ita kanta wani irin mugu mugun son bbys din ne yashiga ranta tun sanda suka zo duniya ta daura idanunta akansu taji sun shiga ranta.
duk da duk sanda ta kallesu gabanta Na tsananta faduwa akan tsananin kamanin da yaran keyi da mijinta.
Dan ko mahaukaci ya kalli yaran yasan kamarsu daya da deeni babu wani bambanci launi ko sura daidai da yatsun kafafun yaran dana hannusu irin na deeni ne sak .bakinsu da hanci komai Nasu irin nasa ne .
sosai take taji wani irin mugun son yara Na sake ratsata har ‘cikin zuciyarta tana jin bazata iya rayuwa bbu su ba ….
+
Amman Ga tashin hankali da uwarsu tazo mata dashi wanda take jin bazata iya jurawa ba .. Amman duk da Haka durkusawa wada ….
gabadayan ilahirin jikinta yayi mugun sanyi jikinta banda kirma bbu abinda yake tsabar tsoro da rudani .
Ga mamaki deeni da ummi har nablah.
suka Ga zeenat ta zube a gaban nablah tana kuka tare da rike kafafunta tana rokonta Dan girma Allah nablah ki rufa min asiri kada ki min Haka wannan ita kadai ce damata da zata min katanga tare da yi min shingi da kishiya arayuwa ta.
Dan girma Allah kibar min yaran wallahi nafiki bukatarsu zan kular miki dasu fiyye da tunaninki .
zan basu gatan duk duniyar nan .
zan kaunace su fiyye da ke kanki da kika kawo su duniya ..
Dan Allah kibar min su Karki fasa kyautar mana dasu kmr yadda kikace ummi Dan Allah kisa baki tabar min su .. my hrt kaima kayi shr kaki cewa komai please kuyi mata mgn kozataji nafita bukatarsu takarasa mgnr tana fashewa da wani irin matsanancin kuka.
kuka zeenat take tana rokon nablah akan tabar mata yaran … ahankalin deeni ya Mike tsaye Daga zaune dayake yaje har gaban nablah ya mika mata hannunwansa duka alamun tabashi yaran Amman taki .
Yayi yayi tabashi yayan taki sai ma matsawa da tayi Daga kusa dashi tana jijiga yaran da zuwa yanzu hayaniyarsu tasoma tayar dasu .
da kyar deeni ya shawo kanta ta hanyar ce mata bbu inda zanje da yaran nan nablah zan kwantar dasu ne kawai ko bakiga yadda kika matsesu ba ajikinki ba kar wani abu yasamesu .
sannan ta Mika masa mace da Na namiji zuciyarta cike da tsoro da fargaba yaje ya kwantar dasu .
ya dawo ya amshi dayan ma ya kwantar dashi kusa da yan’uwasa kana ya janyo hannuta ciki sanyi jiki Ya zaunar daita akan gadonta ya tsura mata rikitattun idanunshi yana kare mata kallon tsanake .
sannan yasoma magana ‘cikin sanyi rai da zuciya… Nablah ki natsu ki dawo ‘cikin haiyacinki muyi mgn ‘cikin tsanake da fahimtar juna da farko kin amince da zaki bamu abinda zaki haifa wanda har muka sanyawa rayuwarmu son abinda ke cikinki.
” to meyyasa yanzu kika canza ra’ayinki alhalin duniya tagama sannin wayan nan ya’yan ya’yanmu ne nida matata ? +
Ilahirin jikinta da bakinta wara suke gurin cewa nidai kawai ji nake a halin yanzu bazan iya kyautar dasu ba.
. saboda kinsha wahala gurin haihuwarsu shiyasa bazaki iya badasu ko me ?
Kai tsaye taji ya ‘aiko mata da tmbyr datasa ta tsura masa shanyayyun idanunta da suke cike da ruwan hawaye taki ce masa komai sai kallonsa kawai take ..
“jikin deeni Yayi sanyi sosai sbd ganin yadda yanayinta ya sauya . yarasa ta inda zai bullo mata.
ta kalleshi sosai Yayi matukar bata tausayi Amman har ‘cikin zuciyarta bata jin zata amince tabashi yayanta kyauta .
” tacigaba da dubansa can km yace kina jina ko kiyi hakuri kibar mana yaran nan nida matata nayi miki alkwarin zan raba tarin dukiya biyu Na baki rabbi akansu kije kicigaba da rayuwarki .
Sosai ta sake tsareshi da shanyayyun idanunta tamkar zata cinyeshi tana mishi wani irin kallon rainin wayo.
hakan Yasa gabansa cigaba da faduwar dayake .
shima kallonta yake yana jira Daga gareta tare da mamakin canzawarta a’cikin zuciyarsa .
idan wani ya fada masa zata rikide ta dawo masa Haka wallahi zai rantse da Allah yace karya ne ranta a matukar bace tace Kai dukiya ta dama km take rudarka har kake jin Kai wani ne .
Amman ni bbu abinda za’a bani a duniyar nan da zai Saka Na iya kyautar da ya’yana har UKu ba daya ba.
ko mahaikaciya ce Ni bazan soma yin wannan dayin aikin ba ballanantana Ina ‘cikin haiyacina, yakarasa fadar hk tana nuna brain dinta da yatsan hannuta.
kana tacigaba nidai Dan girma Allah Na rokeku daku barmin ya’ya Na Ina sansu nima a duk yadda suke.
deeni ya runtse idanushi gam tare da furta ya Allah akasan zuciyarsa ….yasoma cizan lips dinsa da karfi .
gabadaya komai Na ‘cikin duniyar nan yasoma tsaya masa Bai taba tunani sanadiyar yarinyar zai taba shiga ‘cikin tashin hankali irin Haka ba.
ya dauka rashin son ‘cikin jikinta datake tun farko zai tsaya a Haka ne .Amman a kalmomin bakinta na yanzu komai ya sauya agareshi yagane shi din bakomai bane a duniya nan .
sannan ya soma fahimtar Bai isa yace zai ma kaddarsa wayo ba .
Yau din nan tazo masa da tarin abubuwa da daya farinciki dake tattare da tashin hankali mara misaltuwa . +
Shin yanzu ya zaiyi da kaddarar data fada masa ?
Ya’yan da zai fara samu a duniya sunzo masa da wani irin salo na daban .
yanzu mezai cewa danginsa da yan’uwa ?
Hakika Komai yagama dagule masa ahankali ya juya saitin da zeenat take tsaye surusuru tana aikin barin jiki da marairaice wa .
yana aika mata da wani irin matsiyacin kallo me frigita zuciyar wanda akawa sannan muryarsa a fusace yace kinga ni ko ?
Kinga irin abinda sakacinki ya haifar mana ko ?
Me kike tunani zai faru gaba idan har taki amincewa tabada yaranta ?
Zeenat da jikinta ke mugun kirrrrrrma ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka tana yarfe hannuwa .
yanzu dakin yi hakuri kin haifi wanda Allah yabaki da duk hk Bai faru ba.
da km baki samu ‘cikin tsaka me wuya ba. Amman bbu komai duk ‘cikin wannan lamarin ni akafi cuta yakarasa mgnrsa yana jin kunar rai acikin zuciyarsa yayinda kirjinsa ke wani irin buguwa da karfi .
Shi kanshi kuka yake son yi ko zai daina jin radadin azabar ciwon zuciyarsa keyi .
banda kuka bbu abinda zeenat keyi ita kanta tasan ta cuci kanta da kanta.
Ta ruguza rayuwarsu sbd sakacinta da son zuciyarta ta Mike Daga inda take ahankali tana layi ta rungume ummi ajikinta tana matsanancin kuka.
Ummi kiyi hakuri a rayuwa nasan Na cutar daku Amman ko daidai rana daya ummi baki taba kina ba .
Sai ma sabuwar kulawa da kike bani hakika ke uwace guda har da rabi samun irin Ku ahalin yanzu zai yi wuya ummi kiyi hakuri abida nayi ki ya femin Na cutar dake domin ba irin tarbiyya da kika bani ba kennan ta sake tsanata kukanta.
ummi itama ta rungumeta sosai tana zubda hawayen tausayin diyarta arayuwa ta tsani abinda zai saka zeenat dinta zubd hawaye matukar tana da yadda zatayi.
kasa cewa komai tayi Sai aikin rarrashita datake tana shafa bayanta ..Ahankali deeni ya dauke idanunsa akansu ya juyo sosai tare da gyaran zamansa yana fuskantar nablah da kyau ya kaskantar da kanshi da muryarsa agabanta yana nuna mata shin din bakomai bane facce me nema agurinta .
a wannan fani har ya mance dako su waye tsaye akansa.
Domin Bai San sanda ya kamo tafin hannunta ‘cikin sanyi jiki ba yana kallon ‘cikin kwayar idanunta muryarsa cike da rauni zuciya tare da mayyen sonta ya Kira sunanta.. nabeelah …kiyiwa Allah ki mallaka mana bbys din nan.
badanmu ba Sai saboda Allah ki duba tashin hankali da zanshiga akan yaran nan .
sannan ki duba halin da mahaifiyata da matata zasu shiga ki tausaya nablah ki duba yadda mahaifiyata tagama gayawa duniya akan nida matata muka haifi bbys din nan .Kinsa idan akaji sabanin hk zatashiga tashin hankali da rudin rayuwa ..
nablah nasan kina da saukin Kai da sanyi hali hade da hakuri akan komai Na rayuwa .
Na rokeki da Allah kibarwa zeenat bbys din nan .
Allah zai duba lamarinki ya sake baki wasu da yardarsa …
a fusace ta fizge hannuta ‘cikin sauri Daga nashi tana jin takaicin mgnrsa . .. +
Kana ji har mara hankali matarka ta kirani dashi akan ya’yan dani kadai nasan kalar wahalar dana Sha akansu tunda Daga cikinsu har zuwa haihuwarsu.
idan har nabar mata yaran nan wallahi azim Na tabbata mahaukaciyar gaske deeni .
zeenat ta bar jikin ummi tamatso gareta sosai tana kuka tana rokon nablah.
ZUCIYAR deeni tasoma rawa yasoma jin Wani irin ajikinshi hakika ya tausayawa zeenat duk da yasan itace silar rugujewar rayuwarsu da yi musu katangar karfe da burin ransu km farincikinsu Amman fur nablah taki amincewa tare da cewa aunty kiyi hakuri wlh nima Ina son ya’yana.
idan nabaki su ni km yazamanto su kadai ne ya’ya da zan haifa a duniya ni km Sai nayi ya’ya ?
Kiyi hakuri kawai kema Allah zai baki naki da yardarsa Amman zance nabar miki ma su yanzu bbu shi .kibar min nawa nayi rayuwa dasu , sune duniyata ayanzu bazan iya rayuwa bbu su ba . +
deeni ya juyo a tsukwane ya kafe zeenat da idanushi yana kallon yadda ta dawo wata kala abar tausayi bbu wuya tashin hankali ya canza mata kammani .
Ummi takaraso ahankali itama ta zauna kusa da nablah ta dinga bata hakuri da yima dabarunsu irin Na manya da siyasa iri iri Amman fur nablah taki Sai ma fashe musu da sabon kuka datayi ni kibarni Haka Dan Allah Dame zanji .
yanzu zan bar muku gidanku akan na bada yaran nan gara na komai
kan bola Na rayu dasu ‘cikin kulawata .
gabadaya deeni yasoma tsorata da yanayinta har yasoma aikawa kwalkwaluwarsa tmbyr Anya kuwa wani abu Bai samu brain dinta ba kuwa gurin haihuwa ?
Sosai Ya xuba uban tagumi tare da jefa Dan karamin yatsansa ‘cikin bakinsa yana cizawa da karfi yana kallonta yana nazarin reaction dinta ..
sosai ya jima yana kallonta kafin Daga bisani yace first love barta kawai akawo mata abinci yaci da alamun tana jin yunwa tun da muka shigo gidan nayi nayi daita taci abinci taki ci a she rigima take ji shiyasa.
jikin ummi a matukar sanyaye tace zeenat goge Hawayenki ki natsu kada mutane su gane Muna ‘cikin damuwa da matsala.
muje maza ki kawo mata abinci ni zan Dan tsaya saboda kauda idanun mutane akanmu.
Tare suka fita .
ummi Na sake rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta ..
Suna fita deeni ya juyo gareta ya hade da jikinshi ya rungumeta zuciyarsa Na harbawa da sauri da sauri .
tare sa sakin naunauyen ajiyar zuciya bakinsa yakai daidai saitin kunneta sosai.
Yace Na yaba da jarumtarki Na yaba miki da yadda kike son baby’s dinmu .
daman Haka yakamata duk wata uwa tayi akan yayanta .
km hakan da kika yi ya sa naji kin birgeni sosai. Sai dai me zai hana ki tausaya kibarwa zeenat dina baby’s din please zata kular miki dasu ..ki tuna sanda kike kuka kike rokona akan azubar da ciki Na hana batare da saninki ba .
ki tuna irin taimakon dana miki akan ni zan karbi ‘cikin da bansan wanda Yayi miki ba domin gujewa kunyar duniya
Da karfina da dukiyata duk sa sadaukar akan Na inganta ‘cikin jikinki da rayuwarki .
Amman kirasa abinda zaki sakayyar min dashi .
Sai hanani bbyn dana gama wahala akansu.
Meyasa zaki min hk ? Yakarasa mgnr da
Ki bar mata sake of me please nablah zanji dadi idan har zaki iya min hk .kina jin yadda zuciyarata ke bugawa da karfi akanki .
,akanki zan iya yin komai ciki har da fallasa sirrin dake boye wanda hakan bazaiwa first love dadi ba.please nablah sake of me jikinta Sai kirma yake tana zubda ruwan hawayen tausayinsa muryarta a dashe tace nasani deeni kataimaka min a rayuwa km zan iya yi maka komai a rayuwa Amman bazan iya kyautar yaran nan Ga kowa ba ciki kuwa har da kai ..
Ni kaina Haka kawai Na tsinci zuciyata da matsanancin kaunarsu tunda Na daura idanuna akansu .kasa samun natsuwa .
Ya zanyi nabaku kennan ni zauna hk ?
Byn tarin wahalar dana Sha akansu .
ahankali ya sausauta rungumar da Yayi mata ya ciro hanky Daga gaban aljihun rigarsa yashiga goge mata hawayen dake tsiyaya akan kuncinta .
bakinsa ya Kai kan lips dinta ya tsotsa yana kallon ‘cikin idanunta .
Lumshe shanyayyun idanunta tayi tasoma kokari cire bakinta Daga nashi .
Jikinsa a sanyaye ya xuba mata rikitattun idanunshi kawai yana kallonta yana imagine dinta.
har sanda zeenat ta dawo dakin hannuta rike da cool food flasks da flasks din ruwan zafi da plate Deeni ya janyo wata Yar karamar stood tsakiyarsu ya bude cool da zeenat tashigo dashi.
miyar dayafi tsana arayuwarsa yasoma cin karo dashi wato miyar kuka wace Tasha naman kaza da kayan kamshi makewa Yayi ya ciro karamar ta sama ya ajiye yacigaba da bude cool yaga tuwan samiviter ne aciki Whit lailon ya ciro tuwon yasaka akan plate ita km zeenat jiki Na rawa ta hada mata tea me kauri ta mikowa deeni.
” ya karba ya ajiye a gefen plet din.
abin zeenat nabashi mamakin sannan km yana jinjina girma al’amarin.
lallai sanadin wayan nan baby’s din Yasa zeenat dinsa tasoma sauya halinta wanda yajima yanasonta dashi . +
Muryarsa a matukar sanyaye yace Bismillah nablah kici abinci .
taki ci ta xubawa masa idanunta ya Mika mata cup din tea shima taki karba.
Yayi shr ya tsura mata rikitattun idanunshi bazaki ci abinci ba ?
Ta girgiza masa kanta alamun eh saboda kina tunani zamuyi poison naki ko ?
Tayi saurin sake girgiza kanta to meyasa bazaki ci ba alhalin nasan kina jin yunwa ?
Muryarta a shagwabe tace nifa bance zakuyi min wani abu ba .. zeenat kawo min spoon.
.
Zeenat ta juya da sauri taje takawo masa spoon ta Mika masa .
mamaki ne yakama zeenat Ganin deeni yasoma tura tuwon samiviter da miyar kuka abakinsa the most abincin dayafi tsana kennan arayuwarsa ballanantana dai miyar kuka wanda ko sunan miyar akafada agabansa Sai ya yatsuna fuska tsabar baya sonta .
Amman yau shine zaune yana ci hankali kwance dago rikitattun idanunshi Yayi masu tsantsar cike da tashin hankali ya daura akan nablah dake zaune tamkar an dasata tare da yi mata alama da spoon din hannunshi .
, zeenat tasoma itama sosai ta tsoma hannuta sbd ganowa datayi lallai nablah bata yarda dasu ba.
tasoma ci Sai da nablah ta tabbatar dayaci sosai hk ma zeenat sannan ta tsoma hannuta ciki tare da yin bismillah tasoma ci ahankali aranta tace idan ma mutuwarce ba zan mutu ni kadai ba Sai dai abarwa ummi baby’s din .
ko tea din ma kin Sha tayi Sai da zeenat Tasha deeni yasha sannan Tasha itama .
deeni ya kalleta yana tabe baki girgiza Kai .
sbd muraran km azahirance nablah ke nuna kuruciyarta a filli . Idan har wani abu zasuyi mata .
Ai tayi kadan ta kare kanta .
number wayar ummi deeni yakira .
Byn kmr minti goma Sai gata tashigo dakin first love yakama ayiwa yarinyar wanka hk fa da duk abinda yadace.ko bakace ba deeni duk za’a yi mata daman wannan tashin hankali ne Yasa nakasa samun natsuwa nayi mata ai nablah tamkar diyar cikina Na dauketa . +
Da zai fita ya janyo hannu zeenat ya nufi dakinsa daita ya rungumeta tsam tsam ajikinshi zeenat yakira sunanta Ina so ki tattaro natsuwa ki sanyawa gangar jikinki sannan ki kwantar da hankalinki da sannu zan shawo kanta ‘cikin sauki batare da wani hargitse ba har ta amince .
domin wannan harbin iskar da kike da tashin hankalin ba zai saka tabada ya’ya ‘cikin sauki ba .
as far as tasan wahalar daukar ciki da radadin haihuwa kema kinsa bazai yiwu a karbi yaran ‘cikin sauki ba.
ki dinga lallabata ta yadda taza yarda ta amince da ba cutar daita da yaranta zakiyi ba ..
narkewa tayi sosai ajikinshi , zanyi komai my hrt matukar yaran zasu zamo nawa Dan wlh wani irin mugu mugun son yaran nake ji ‘acikin zuciyarta .
Nima sun shiga raina zeenat fiyye da ita kanta uwar data kawo su duniya.
Amman duk da hk ba zai yiwu muyi mata dole ba .
tana bukatar rarrashi da caring kema kinsa haihuwar nan is not easy ballanantana irin nata datayi kwana biyu tana abu daya sosai deeni ya kwantarwa da zeenat hankali har ta Dan samu natsuwar zuciya tare da sake jin kaunar yaran daram acikin zuciyarta ..
Kowajen wanka ma kememe nablah taki yarda ummi ta rufe kofa toilet tayi.
Dan kofar a bude aka barta tana hango wutsil wutsul din yaranta akan bed Dan gabadaya atsorace take dasu ummu.
yayinda zuciyar ummi tashiga watsi watsi datashin hankali anya kuwa ba wata maseefar ce ke shirin faruwa dasu ba.
duba Ga yadda nablah ke nuna son yayanta mura mutane da yin kafa kafa dasu …
Daren ranar gabadayansu Daga ummi har oga deeni da zeenat adakin nablah suka kwanna sbd yaran a cewarsu .
bbu wanda ya runtse acikinsu.
yaran Sai kuka suke nablah zaune tana feeding din mazan duka biyu zeenat km tana tsaye tana hada abinci yara a fidda.
shi km deeni yana tsaye rungume da bby girl dinsa yana jijigata sbd kukan datake ya saka mata lips dinsa abakinta yana Dan jijjigata har takoma bacci ya mannata ajikinshi sannan ya koma ya zauna .
Ya jin yadda zeenat ke cigaba da rokon nablah Amman tayi mata banza taciga da feeding din yaranta tana jijiga kafa .zaune kawai deeni yake Dan Bai San me zaice ba .
ya kwantar daita zeenat ta karbi bby daya Daga hannu nablah tashiga bashi abincinsa.
ita dai ummi zuru tayi tana aikin binsu da ido kawai.
sbd al’amarin yarinyar ya daina bata mamakin ya dawo bata tsoro .
Haka ‘cikin daren ummi da deeni sukayi ta mata naci da rarrashi akan yaran .
nablah kema tamkar diyata nake jinki ‘cikin raina sannan km bazan iya takuriki ba Amman idan kinsa yadda yaran nan suke ‘cikin zuciyarta dakin mallaka manasu Kai tsaye bazan taba gajiya gurin rokonki akan kibar mana su ba .
nablah tace uhmmmm azuciyarta , ummi kennan bazaki tabagane value din yaran nan a raina ba .
ni kaina bantabasani Haka yaya suke acikin zuciyar iyayensu ba Sai dayazo kaina .
wayan nan yaran sune duniya ahalin yanzu .. zeenat ma sake saka baki ciki nablah zan kular miki dasu Dan girma Allah kiyi hakuri kibar minsu wlh nafiki bukatarsu sannan Ina rokon ki Dan Allah kibari a dinga sauka da baby’s din nan kasa sbd Yan zuwa barka ..
Wani irin mugun kallo nablah tabi zeenat din dashi sannan tace nifa wlh bazan wani bayar da ya’yana ba .
duk me son ganinsu yazo sama idan ya matsu Amman wlh idan kuka takurani zan ban bar muku gidanku Gobe goben nan , Dan nima wlh atakure nake daku.gaban deeni ya buga da karfi ya tsurawa Dan karamin tsukaken bakinta ido .
Muryarsa a sanyaye yace nablah no duk zance Bai kai hk ba .
Ba Sai kinje koina ba ke zeenat gobe kiyi zamanki anan dakin kawai duk me son ganinki da bbys yazo nan yasameki. jikinta a sanyaye tace to shikennan my hrt.
+
Washegari gidan yacika tap da dangi tana ji yadda kowa yake fadar irin kyawun yaran Amman wai macce ce kawai bata biyo deeni ba suko mazan tamkar an tsaga kara ne dashi .
Ita ko nablah tana kwance su ummi gabadayan sun rasa gane kanta domin ranta a matukar bace yake taki yarda tayi magana da ummi ballanantana wata zeenat.
Barta deeni ko kallo Bai isheta ba sbd magiyar dayake mata akan yaran aranta kuwa kwata kwata batason ta kara daidai da second daya agidan.
tunanin kawai yadda zata gudu take da yaranta ‘cikin sauki batare anganta ba ..
Tundaga ranar duk yazo barka ya nemi ganin baby’s Sai dai subada uzirin Doctor yace bbys din suna bukatar hutu yawan daukar da’ake musu yana saka su zazzabi dare wasu sun yarda da zance Sai dai wasu basu wani amince ba .
km suka dinga cewa iyayi ne kawai irin Na deeni Dan duk sunsa sharrinsa ne …
Sosai ummi ke bawa nablah kulawa ita da yaranta .ta gasata sosai da sosai duk da kasancewar nabla irin matan ne masu tsukaken jiki wayan da da zarar anagama cinsu suke hadewa take Amman duk da ummi Na kula da kasanta .domin zuwa yanzu ta hade gam tamkar ba itace ta haifo Yan uku ba .sosai km take da nuna mata yadda zata kula da yaranta.
Itama nablah duk abinda ummi tasanar tana kiyayewa sbd daman ita can me kaunar yara ce nawasu ma ta bauta musu ballanantana nata .ita kuwa zeenat gabadaya fargaba da tunani hade da tashin hankali ya maidaita wata iri .
tayi wujiga wujiga daita tayi wata irin rama tayi duhu kallo daya zakayi mata kasan tana ‘cikin taskon rayuwa da tsaka me wuya. Yayinda kullun kwana duniya take like da nablah tana yi mata naci da magiya akan tabar mata baby’s din ta .ita km ta rufe idanunta taki wani lokacin idan abun ya isheta tasaka mata kuka .abu goma da ashirin Ga kewa gidansu datake Ga taushin hankali da fitinar zeenat.
Ta fanni deeni ma gabadaya ya susuce ya rame tsaye kawai yake da kafafunsa Amman zuciyarsa cike da rudani .
Tunda akayi haihuwar yagagara fita koina . abokansa sukayita zuwa taya Shi murna karuwar daya samu .
Yayinda ,gida da office takoina ka kalli fuskar jama’a murna haihuwar manager suke .
,sadaka kuwa deeni Yayi shi har bai San iyakacin abinda ya raba ba .hutu sati guda akabawa ma’aikata companies har sai byn suna .
Fk ma yazo ganin baby’s da kyar deeni yasamu ya karbi a gurin nablah yakai masa km har yakai su ya dawo dasu kuka take .tana ganin ya dawo mata da yaranta ta bar kuka datake tana sakin numafashi da karfi da ajiyar zuciya ‘cikin jikin nasa yakaraso gareta yana cizan lips dinsa yace yanzu har rashin yarda takai Haka nablah ?Bazan cutar dasu domin nima sune duniyata kalli yadda kika dawo nablah akan yaran da nabaki ba .wata katuwar harara ta zabga masa sannan ta turo masa tsukaken bakinta gaba bangane yaran da banawa ba?
Kana ganin duk duniya akwai wanda ya isa Yayi claiming din yaran nan nashi ne ? +
Ya Dan yi murmushin takaici ya zauna gabanta ya tsotse lips dinta cike da shaukinki kaunarta yace akwai ubansu km mahaifi ko ba dade zai bayyana kansa garesu Amman dai kafin zuwansa kiyi hakuri ki bar min su.
Ranar da bbys suka cika kwana hudu da haihuwa tafiyar gaugauwa taka ma deeni zuwa abuja tun safe deeni ya tafi abuja amman aranar zai dawo.
,tunda nablah taji zance tafiyar sa .
Ta kasa zaune ta kasa tsaye .
hankalinta Yayi matukar mugun tashi .
Duk ta frigice ..
taki sakarwa ruhinta salama .
Karfe shida daidai
deeni yashigo gidan kai tsaye dakin jikin nablah ya nufa yana bude kofar yayi turus jikinsa a sanyaye sbd ganin da Yayi nablah tsaye rungume da yaranta biyu akirjinta ,sannan km dayan na goye abayanta tana jijiga su tana kuka su ummi da zeenat tsaye akanta sunyi cirkocirko suna dubanta .Dan gabadaya sun rasa yadda zasuyi daita tun barin deeni gidan take a Haka .
baby’s din ma kuka suke sosai tamkar sun San mamansu Na ‘cikin tashin hankali.
ahankali deeni yakarasa shigowa dakin sosai yana bin su ummi da kallo.
kana jikinshi narawa da zuciyarsa gurin cewa lfy ummi naganku hk ?
Ina fa lfy deeni tun safe daka bar gidan nan nake fama daita taki cin taki Sha har zuwa yanzu.
Yanzu km mun shigo dakin munganta goye da ya’yan .
da alamun shirin guduwa take ya runtse rikitattun idanushi dake cike da rudani yana ambatar sunan Allah .
ya kamota ya zauna daita ya karbi yaya duka ya kwantar dasu ya riko hannuta’cikin nashi yana kallon ummi da zeenat tare da yi musu alamar su fita.
Byn sun fita gabadayansu ya Mike yaje ya rufe dakin tare da yiwa kofar key yana dawowa ya rungumeta gam ajikinsa kusan minti goma shabiyar suka dauka haka batare da yace komai ba suna sauke naunauyen ajiyar zuciya da shakar numfashin junansu.cike da tausayinta ya zareta Daga jikinsa yaje ya hado mata tea me zafi yakawo mata ta kar Tasoma sha ahankali Dan yanzu tafi yarda dashi akan zeenat da ummi .
muryasa’cik e da fargaba yace nablah ta dago shanyayyun idanunta tana kallonsa batare da ta amsa.
Meke damunki ?
Tayi shr taciga da kurbar tea .
Ko wani abu su ummi suka miki ?Ta girgiza masa kanta .
Ya kamo tafin hannunta wanda yake empty yasoma murzawa ahankali ahankali tare da tsareta da rikitattun idanunshi.
Muryarsa cike da laushi ya sanyaya ta sosai sannan yasoma mgn a tsanake yace ba ki min alkwarin zaki bani bby
ba?
Ba gori ba ki tuna abubuwan alkhari dana miki nablah akanki Na mari matata ta sunana akanki Na kewa mahaifiyarta gardama Ya’yanki ba’a San usilinsu ba.
ba’a San tushensu ba Amman naji nagani nace karbi ‘cikin jikinki domin Na rufa miki asiri sbd kar duniya ta zage ki . +
,kin tuna sanda kika yi ‘cikin nan ban Kiki ba nayi rayuwa dake tamkar matata ,Na kula dake da abunda ke cikinki . please nablah kada ki canza ra’ayinki akan alkwarin dakika min akan zaki bani su . jikinsa Na rawa yacigaba da cewa wlh idan kika yarda kika amince kika bani baby’s din nan nayi miki alkwarin zan mallaka miki gidan glass gabadayansa zan mallaka miki gidana dake ajawu estate zan maidake makaranta kicigaba da karantunki dakike buri .
zan taimakawa iyayenki Na canza musu rayuwa zan ingata rayuwarki data ahlinki gabadayansu .
haka ya dinga kwadaita mata abubuwan alkhari dazai mata .
nablah Ina son kisan wani abu ko matata ta sunnu bata taba zuwa sabon gidana Na glass ba Sai ke.
bantaba yin rayuwa da wata mace a duniya irin yadda nayi rayuwa dake ba .
Narasa tantancewar kaina da zuciyata shin sonki nake ko km tausayin ne ko km sabo ne Amman mutane da dama idan Na tmbyesu suna gaya min sonki nake.
which’s kema kinsha gaya min haka.
Amman Ina karyata zuciyata nablah ki dubi Allah ki taimaka please ki bani yaran nan sake of me zuciyata tayi rauni dayawa gashi bata iya naci akan abu duk girma Amman yau tsawon kwana hudu Ina binki.
sanadiyar wayan nan yaran bbu abinda bazan iya miki ba arayuwa zan miki komai Na rayuwar duniya r nan .
jan jiyar dake dadin duniya zan saki daukaka acikin duniya.
bazan taba barin ki wulakanta ba.
Duk abinda deeni ya mallaka naki ne hk zuciyar deeni take ce please please nablah ki taimaka please Haka ya dinga gaya mata Ward’s masu dadi da sanyaya zuciya as ended.
Ya zube kasa agabanta Yayi mata neildwon tamkar dai yadda zeenat tayi mata.
ya daura kanshi a saman cinyarta sannan ya sakala hannushi ya rungumeta gam ta baya muryarsa a raunane yace mata.
Dan girma Allah kiyi hakuri ki taimakeni ki rufa min asiri ni badan zeenat ba Dan ummi banason ki kunyata ummi sbd ta rigada tagama gayawa mutane zeenat haihu . Yanzu tunda abin yazama hk Kinfa sa kyautar mana da yaran shikennan ki ba r ya’ya kawai .
Amman Dan sbd dan kada mutane su farga su gane ba yaranmu bane .Ki aro mana su Amman agurin ki zasu dinga kwana a lallaba mutane har ayi suna inyaso byn suna Sai a gayawa duniya da mutane abinda zeenat ta haifa sun mutu har an binnesu ke km kina iya tafiya da yaranki .
Gabanta ya fadi jikinta ya dauki rawa tace to.. to. shikennan Na yarda da wannan .
zan muku alfarma har ta wata daya a gama rurumar suna da barka Sai dai fa wlh da ya’ya zan dinga kwana kmr yadda kace.
zuciyarsa cike da farinciki samun nasara da Yayi yau yace Na amince .
to kira ummi da zeenat ka maimaita agabansu gabadayansu suka shigo dakin byn kiran da deeni Yayi musu ta waya. +
Ahankali cike da natsuwa ya maimaita yadda sukayi da nablah ummi zatayi mgn da zeenat Yayi saurin yiwa ummi sigina da idonsa alamun kada suce komai take kuwa suka yi shiru.
suka hau cewa shikennan mun yarda da wannan tsarin … gabadayansu da ummi da zeenat har deeni suka tabbatar mata da sun Yarda akan tsarin…
Uhmmmm to ko yazata kaya tsakanin deeni da zeenat har uwar gaya ummi 🤔🤔