WATA BAKWAI CHAPTER 1

WATA BAKWAI CHAPTER 1

Tunda abokansa suka rakoshi suka gama surutunsu da kawayen amarya bai ce uffan ba. + Asalima bazai iya maimaita magana daya da suka fada ba dan hankalinsa ba akansu yake ba. Kallan yarinyar da take zaune kan gadon ya keyi baima san me zai soma fada mata ba.Ko kalar fuskarta bai sani ba tana zaune kan gadon lullube da mayafin da bashi da niyyar bude mata. A hankali kaman mai koyon magana yace mata. “Sannunki” Tafi mintina biyar a zatansa ma bataji ba sannan cikin rawar murya tace masa. “Nagode” Hannunta tasa tana sake gyara mayafinta dai-dai lokacin da idanuwansa suka sauka kan hannayen nata da suka sha kunshi. A gefe guda kuma zuciyarsa ta dauke shi ta watsa shi wani lokaci can baya. *** *** Da gudunta ta karaso inda yake. “Yayana kaga kunshina yayi kyau?” ta fadi da murmushi a fuskarta. Shima murmushin yai mata yana fadin. “Kai kai gaskiya baiyi kyau ba”

Fito masa da idanuwanta tayi lokaci daya ta tabare fuska tana shirin yin kuka. Yana dariya yace. “I am sorry. Just kidding, yayi kyau sosai. Waye yai maki?” Juya bayanta tai alamar tayi fushi. Rufe idanuwansa yai ya bude su a hankali in ba itaba bai fiye son yawan magana ba. “kinga bara nai tafiyata since fushi kikeyi” ya fadi yana mikewa. Riqo masa hannu tai sai da yaji wani abu har cikin kansa. Bayaso tana rike masa jiki musamman in babu tsammani yaji hannayenta a jikinsa. Muryarsa can kasa yace. “let go of my hand huddy” Sake makalo shi tai. Saida yai mata tsawa sannan ta sake shi ta ruga kuma. Yasan tabarar huddy kamar yunwar cikinsa. Kuka zatai kuma bashida zuciyar binta ya lallabata dan tana rikita masa kai da yawa. *** *** Idanuwansa da suke rufe ya bude. Hakan yasa zuciyarsa dakatar da inda ta dauke shi takaishi. Sauke su yai kan yarinyar da take zaune kan tanqamemen gadon dakin.

Wani abu yaji ya soke masa zuciya. Jiyai sam bazai iya jurewa ba ya fice daga dakin yaja mata kofar a hankali. * Taji fitarsa. Kwantawa tai kan gadon ko kaya bata da kwarin tashi ta sake. Kuka ne tayi shi har bata zatan tana da sauran hawayen da suka rage mata. “Sannunki” shine kalmar da tunaninsa ya bashi ya furta mata a darenta na farko a matsayin matarsa. Wato kaddara dabance. Bata taba zatan auren wani bayan Ammar ba. Fadar sunansa kawai a tunaninta yasa zuciyarta wani tafasa. Ta gama tsanar mutumin nan tun kamin ma taganshi. Ya rabata da ammar dinta. Wai duk ma matan kano ya rasa wa zai aura sai ita. Dan tsabar rashin adalci da rashin sanin darajar SO. Kunshin hannunta ta kalla da bata ga amfaninsa ba can gefen zuciyarta ta tuno wani lokaci tayi kunshin jan lalle suna zaune da ammar. *** *** “Babyna ina son kunshi sosai. In munyi aure zaki dinga yimin” ya fadi cikin karamar muryarsa da take so. Murmushi tai a kunyace hadi da fadin. “Saika biya tukunna” Dariyarsa yai mata ya wani juya idanuwansa da yasan duk idan yayi yana burgeta sannan yace. “Karki samu damuwa lokaci ne zaki fadamin ma.anar wannan maganar” “Yaushe kenan?” Ta fadi muryarta da alamar dariya. “uhm zakiyi bayani ne yarinya” ya karasa shima da dariya a muryarsa. *** *** Wani radadi taji zuciyarta nayi tasan ta rasa Ammar da soyayyar nan tashi mai tsaya mata a rai. Yanzun duk kulawar nan da alkawurransu sun tashi a banza? A wata daya kacal wani yazo ya ruguza masu soyayyar da sukai shekaru suna ginawa?

Ya tarwatsa musu farin cikinsu saboda sonkai irin nasa. Ta tsani koma waye wannan. Kanta taji yana mata wani irin ciwo ga zuciyarta da take mata zafi. Haka tai kwance shiru tana duk wata addu.a datazo bakinta ko zata samu saukin radadin da takeji. A hankali bacci ya dauketa cike da mafarkin Ammar. Ya rasa kwanciya zaiyi ko zama ko kuma tsayuwa. A duk yanda yai zuciyarsa sam babu dadi. + Auren nan ya sake fama masa ciwukansa yasa suna zubda jini. Da su umma sunsan bashida sauran zuciya mai numfashi ta bangaren soyayya balle kuma aure da basu matsa masa ba. ko da yake harda laifin yarinyar da bata gaya musu bata son shi ba. Shi kam yayi iya kokarinsa na kaucewa auren fin karfinsa akai. Itama yasan kwadayin abin duniya ne yasa ta nace ma aurensa. A wata dayan da akasa na bikinsu. Kin zuwansa yaga kalar fuskarta kawai ya isa ya tabbatar mata da bai amincewa aurenta ba. STORY CONTINUES BELOW Amman saboda naci da kwadayi irin na matan yanzun saida ta bari aka daura masa ita. Inda huddy ta sha banban da sauran kenan. Zuciyarsa ta fada masa. Dafe kai yai. Baya son wannan matsayin nasa da wanda yasan yana shirin samunsa a lokaci na gaba. Yasan bakomai bane zai zabarma kansa amman ya dauka cewar atleast matar dazai spending rayuwarshi da ita shi zai zaba. Bawai daukarta za.ai a lika masa bada son ransa ba. Gaba daya kansa yai masa nauyi. Neman wanda zai likama laifin abinda yake faruwa dashi yake kuma a yanzun babu wadda tafi dacewa irin yarinyar can dako sunanta ma bai sani ba. Inma an taba fada a gabanshi bai rike ba dan bata ransa. Baya mata kallan komai sai yar katsalandan da kara masa matsaloli fiye da wanda zuciyarsa take ciki. Gani yai sai juye juye yake yi ya kasa bacci. Ga ciwon kai na damunshi yama manta cewar tun abincin safe ne a cikinshi da ummansa ta takura masa ya zauna yadan ci. Bacci sam yaki yazo. Dan haka ya tashi ya shiga bandakin shi ya dauro alwala.

Hakanne kawai zai masa maganin wannan tunanin da ya addabe shi. Kuma yasan zai samu nutsuwa ko yaya take. * Bude idanuwanta husna tai. Kanta ya wani sara mata. Lokaci daya komai ya dawo mata. Dacin da take ji a zuciyarta yana nan daram. Wayarta ta lalubo kan gadon, jikinta ya mata wani irin nauyi. Bata san ta makara ba saida ta duba agogon wayarta taga karge bakwai saura mintina sha biyar. “Lallai nasha bacci” ta fadi a hankali. Sai da kanta yadan saki sannan ta mike zaune. Taja tsaki. Wata kofa ta bude daga cikin bedroom din taga hanya ce. Ta rufe ta nufi wata ta sake budewa taga dakin canza kayane. Ta juya idanuwanta. Ta sake bude wata taci karo da tankamemen toilet. Duk haduwa irin ta gidansu da gidajen yan uwa da take zuwa bata taba ganin kayataccen ban daki irin wannan ba. Duk da tsanar gidan da maishi da tai yawa a zuciyarta bai hana ban dakin burgeta ba. Wanka ta fara yi sannan tai alwala. Sai bayan ta idar da sallah sannan yunwar da takeji ta soma addabarta. Rabon cikinta da wani abu tun safiyar jiya. Sai da ta gama shiryawa cikin wani less ruwan toka duk da ba wata kwalliya tayi ba kayan sun karbi jikinta. Fridge din da yake can gefen dakin ta nufa ta bude cike yake da kayan alatu. Fresh milk ta dauka da apple dan ba ma.abociyar cin abu mai nauyi bace. Musamman da sassafe haka. Bayan ta kammala ta dauki katan mayafi kalar kayanta ta lulluba sannan ta koma kan gadon ta zauna. Ta kudurta a ranta koda wannan Nataccen zai shigo kaman yanda ta yanke shawarar kiransa dashi tunda ba sunansa ta sani ba. Kuma ba damuwa tai da hakan ba. Bata shirya ya kare ma halittarta kallo ba. Auren kaddara ne ta riga ta runguma ko da da hannu dayane. Bata san iya lokacin data dauka ba kamin taji an kwankwasa kofar a hankali. Gabanta taji ya fadi a sanyaye tace shigo. Zuciyarta na dokawa ga mamakinta wata mata ce mai matsakaicin shekaru ta turo kofar hadi da sallama. Amsawa husna tayi. Har kasa matar ta tsugunna ta ce. “Ina kwana. Fatan kin tashi lafiya” Wani irin nauyin matar ya kama husna. Ko bata haifeta ba zatayi kanwa da ita. A kunyace ta amsa. “Ranki ya dade ko kina bukatar wani abu?” matar ta tambaya wadda har lokacin tana tsugunne. Cikin sanyin murya tace mata. “A.a bana bukatar komai nagode. Ya sunanki?” “Sunana asabe ranki ya dade. An shirya abinci ko da kina bukata nazo ingani. Dan lokacin tashin yarima daga bacci baiyi ba.” 1

Sai da tai jim sannan tace. “A.a nagode da kulawarki malama asabe. Kije kawai” “Hutawarki lafiya ranki ya dade ” Asabe ta fadi tana mikewa ta fita daga dakin. Husna ta yamutsa fuska alamar komai yai confusing dinta. Wannan girmamawar da matar take mata yai yawa. Duk idan tace ranki ya dade din nan sai taji wani iri. “Yarima” Ta nanata tana tabe baki. “Wa abbana ya auramin ni husna?” tai tambayar da batasan mai bata amsarta ba. Zuciyarta tace mata. “da kin maida hankali lokacin da ake miki bayani ai da kinsan kowaye.” Girgiza kanta kawai tayi. Tagaji da komai ma. Tagaji da tunani kan wannan auren tunda an riga an daurashi. Takuma gaji da tambayoyin da babu mai bata amsarsu. Hade kai da gwiwarta tai tana sauke wani dogon numfashi…… Ya sha bacci sosai dan jiya da dare sam bai samu wani baccin kirki ba. + Babban falo ya fita hankalin shi a kwance. Bai zaci ganinta a falon ba. Zuciyarshi ta wani doka a yan mintina kadan ya manta da damuwarsa idanuwansa suka natsu wajen aika masa da saqonni kyawun yarinyar da take zaune a falonsa. Hankalinta gaba daya yana kan kallan da take da alama ma bata san shigowarsa ba. Wannan ce natacciyar da aka aura masa kenan to kyawunta bazaisa yaji komai ba yake fadawa kansa. Dan ya tsani makwadaita masu son abun duniya. Kujera ya samu ya zauna can nesa da ita. sai lokacin ta dago ta kalle shi ta sake maida hankalinta kan T.V din kaman baya wajen. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Sam bai saba mace ta kalle shi tai kaman baya nan ba duk min ajinta kuwa. Yana da kyau shima yasan hakan. Duk macen data kalle shi saita qara kallansa amman ta wani basar kaman bashi bane zaune a wajen. Ballantana kuma in tasan koshi waye yanzun zakaga yarinya nasan yai mata magana ta shishshige masa. Well nasan kudina da kuma matsayina yasa kika nace saikin aureni ya fada a zuciyarsa. Yasan zata juyo ne ta sake kallanshi. Ga mamakinsa miqewa tai ta gabanshi ta wuce batare da tayi koda yunqurin nuna yana wajenba tai gaba abinta. Shi ya bita da kallo cike da mamaki yau shi prince Ishaq mace take wucewa kamar baya wajen.

Lallai akwai aiki a gidan nan. Zai iya jure komai dan tun daga huddy zuciyarsa ta daina numfasawa kowacce mace amman banda shariya. Izzarsa da mulkin da yake yawo a jininsa bazai jure halin ko in kula ba. Shi ya kamata ya share mata not the other way round. Domin ita ta nace ma aurenshi bawai shi ya nace ma ta ba. * Husna kam ganin natacce da tai a falo ba qaramin girgizata yaiba. Kyakkyawa ne naban mamaki. Kallo daya zakai masa ka fahimci hakan. Duk da kiyayyar da take masa tasan yafi ammar kyau amman hakan bashi bane zaisa ya burgeta. Dan yanaji da kudi da kyau ba shi zaisa yai mata katsalandan da fin karfi ba. Kyawunsa baya gabanta tunda shine silar rabata da farin cikinta. Taga alamar yana ji da kanshi sai dai itama hakan take. Ta dawo dakinta ne tabar masa falon saboda karta sake kallan shi ya dauka burge ta yai. ”Babyna bana son inji kince kina kallan indian film kar kije kiga wanda yafini kyau” maganar ammar ta fado mata. “Hmm kai bakasan zuciyata ta kulle ba bata ganin kowa sai kai dear idanuwana ne kawai suke ganinsu.” Wannan shine amsar data bawa ammar a lokacin amman gashi yanzun tana hada kyawunsa dana natacce. 1 Haushi ta bawa kanta hadi da alqawarin zatai qoqarin qin sake kallan fuskar natacce in Allah yaso ya yarda balle harta dinga hada shi da ammar. * Washe gari da safe wanda shine kwananta na biyu a gidan natacce. Ta tashi zuciyarta da nauyi da wata irin kewa ta ammar data addabeta. Jinta take kaman bata da rai a wasu wajajen na jikinta. Komai tana yinsa ne dan anayi. Tun jiya bata qara ganin natacce ba ko yana ina shi yasani dan baya gabanta. Ta kammala duk abinda zatai ta fita zuwa babban falo ko zata dan shaqi banbantacciyar iska da wacce take a dakin baccinta. Ta tako kenan text ya shigo wayarta. Ganin kausar ce yasa ta dubawa taga tana tambayar ko tana lafiya. Wani murmushin takaici ya tokareta. Reply take rubuta mata tana tafiya.

Karo taji takaiwa wani abu dabata san komeye ba saboda rubutun da takeyi yasa bata kallan inda zata saka qafarta. Wani irin qamshi mai sa natsuwa ya doki hancinta. Sai lokacin ta kalla taga inda kafadarta ta doka. Faffadan qirjinsa taci karo dashi da sauri ta daga kanta tako sauke idanuwanta cikin na natacce da yake mata wani irin kallo da yasa ta jin gwiwoyinta sun mata nauyin gaske. Ga wani irin kwarjininsa da taji ya cika mata zuciya. Lokaci daya ta sadda kanta qasa tana kallan takalmin qafarsa. Zuciyarta na barazanar fitowa daga qirjinta. A dake yace mata “ki dinga kallan hanya karkiji ciwo.” Wani haushi taji ina ruwanshi da ita shi baisan ta tsane shi bane ba. Ta tsani yanda deep voice dinshi tasa tsikar jikinta tashi. A hasale tace “nagode bana buqatar tunawarka.” Kamin ya bata amsa ta wuce ba tare data sake kallan inda yake ba. * Dakinta ta koma ta zauna kan gado tana maida numfashi kamar wadda tai dambe. Duk jikinta ya mata wani iri. Ga idanuwan natacce da takeji har yanzun kaman yana cikin nata. Hakan yasata saurin rufe idanuwanta ta bude su. Wasu hawaye masu dumi suka bi fuskarta. Ta goge in shaa Allah ta daina zubda ma natacce hawayen aurensa dayake kanta. Tasa hannu ta goge hancinta ko zata goge kamshin sa da take ji har lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *