WATA BAKWAI CHAPTER 10

WATA BAKWAI CHAPTER 10

  Yana kwanciya bacci ya samu. Sanda ya tashi lokacin zuhr harya gota dan haka saida ya fara yin sallah sannan ya kara yin wanka.+ Simple yadi yasa fari marar nauyi. Zazzabin daya rufe shi ya sauka sai ciwon kai kawai wanda yasan yunwa ce. Fitowa yai ya samu dakyar ya tura ma cikin shi plantain da irish. A wajen ya zauna yana dan hutawa. Jikinshi ya masa wani nauyi. * Tunda ta tashi bacci ta kunna wayarta suke chat da ammar har saida lokacin sallah yai. Data idar ma ta shirya tai tunanin fita ta duba prince ishaq. Sai taji ba zata iya shiga ba kuma. Ta zauna falon sama tana jira taga fitowarshi. Ga mamakinta daga kasa taga ya hauro sama. Murmushi yai mata da zata iya fahimta a fuskarshi kadai ya tsaya tunda tasha ganin shi yana murmushi. Mayar masa tai ta dora da fadin. “Na dauka kana baccine ai. Ya jikinka?” Saida ya karasa inda take ya zauna. Sannan yace. “Alhamdulillah. Nagode” Kamshin shi duk ya cika mata hanci. “Zan koma wajen Nas yanzun…..” Bai karasa ba ta mike tana fadin. “Bari in dauko in sake kaya inzo” Sai lokacin ma ya kula da kayan da suke jikinta. Doguwar rigace loose sosai da mayafinta nade a kanta. Baice mata komai ba. Ko mintina sha biyar ba a cika ba ta fito sanye da atamfa da doguwar hijab. Sai yaga ta mishi kyau. Jakace maidan girma a hannunta ta kalli prince ishaq tace. “Ka dauko kayanka da zaka sake da brush. Kaga in muka tafi basai mun dawo gida ba” Yatsina fuska yadanyi dan wannan tunanin sam baizo mishi ba. Bai amsata ba ya wuce hanyar dakinshi. Itama bata damu da saiya bata amsa ba. Shadda ya dauko fara da brush dinshi ya kawo mata. Karba tayi batasan lokacin da tace. “Baka da kayane sai farare?” Da wani yanayi a fuskarshi ya amsa sata da. “Ina da. Kawai nafison farare ne” Batace masa komai ba ta dauki jakar suka nufi hanyar fita. Cikin sauri wata hadima ta taho ta tsugunna ta karbi jakar husna. Taso ta hanata ma prince ishaq yai mata wani kallo. Hakan yasa ta sakar mata jakar. Kallon dai ya sake mata dayake nuna alaman “Good” Murmushi tai suka karasa waje. * A hanyarsune yake mamakin yanda akai husna ke karantarshi. Ba saiya bude baki yai magana ba. Tana gane duk wani abu daya dora a fuskarshi. Husnar ma bata kawo zancen a raiba. Ita dai inyai abu kawai tana ganewa. * Shigar su asibitin doc ke musu albishir cewar an samu ci gaba. Bugun zuciyarshi yakai 50. Kuma suna saka ran zuwa anjima inbai rage ba zasu iya masa aiki dan a rage pressure din dake kwakwalwarshi. STORY CONTINUES BELOW Husna ya raka cikin dakin da Nas din yake ya tabbatar ta nutsu waje daya sannan ya koma wajen likitocin sukai masa bayanin yanda komai zai kasancewa. Tambayarsu yai ko za.a iya moving din Nas zuwa india ai masa aikin acan. Suka bashi tabbacin cewar suma zasu iya. Sunada duk likitocin da ake bukata da kayan aiki. Kuma a halin da Nas yake ciki motsa shi ma zai iya kawo wata babbar matsalar. Amman da yanayin ci gaban da ake samu komai zai dai-dai ta da yardar Allah. * Inda yabar husna nan ya sameta tanata danne danne a waya. Ita kam chatting suke da ammar. Tana jin shigowarshi tace ma ammar din tana zuwa. Duka wayar ta kashe ma. Kujera ya ja a hankali ya zauna kusa da husna. Sun jima a haka shiru. Kaman daga sama yace mata “Bani labari” Da mamaki a fuskarta ta kalle shi tace. “Wanne irin labari” Idanuwanshi ya kafa mata sannan yace. “Kowanne iri ma. Nagaji da sauraren bugun zuciyata ne” Idanuwansa sun sa duk tabi ta wani daburce. Ya kula ta rasa me zatace. “How about in tambayeki abu kina bani amsa” Kai ta jinjina mishi alamar ta yarda. Tunani yake danyi. Kawai saiya samu kanshi da son saninta. “Menene full name dinki?” Wata yar karamar dariya yabata. Ta dauka zai tambayeta wani abu mai muhimmanci. Mutumin nan yakan bata mamaki lokaci lokaci. Saida ta gyara zama sosai sannan tace. “Husna Abdullahi” Jinjina kai yai yace. “Tell me more about you” Kallonshi tai tace. “Saidai kaima zaka amsa mun wasu tambayoyi” Tauna maganar datai yake yi. Ya wani daga girarshi sama alamar anya ya yarda kuwa. Can yace. “Alright” Murmushi tai sannan tace. “Su wa sukaima Nas wannan dukan? Me yasa sukai masa?” Shiru yai saboda tambayar tadan tabashi. Saida tai zaton bazai amsa ba yace. “Me yasa kika aureni?” Tambayar tazo mata a bazata. Da sauri ya dora. “Ina son sani zan amsa miki taki tambayar idan naji dalili and please be honest” Yana son sani ne kamun ya amsa mata tambayarta da take sirrin su. Cikin idanuwa ta kalle dan tana so yaga gaskiyar abinda zata fada. Tace. “Sani akai in aureka” Sai yanzun yasan dalilin dayasa ta tsane shi. Kaman yanda akai masa dole ya aureta itama hakane. “Kaifa?” ta bukata a takaice. “Nima haka” Shiru suka danyi. A hankali yace mata “Asalin sarautar garin kano a hannun kakanin kakaninmu take. Kamin daga baya su sarki saif su karba. Bayan lokutta sun shude ne sarautar ta sake dawowa hannunmu bayan rikici da akai mai yawan gaske. Hakan yasa aka zauna sulhu cewa in wannan gidan sukai mulki suka sauka zai koma hannun dayan gidan. Sai zaman lafiya ya samu. Wannan karon in babana ya sauka sarautar hannun su zata koma. Sai dai mutane sun gaji basa son ai hakan suna so inya sauka a bani ne. Wannan shine dalilinsu na son dauke duk wani jini na gidan kan wannan mulkin. Ban taba son shi ba. Bai taba burgeni ba sun dauke huddy akanshi. Hakan kawai daliline dazaisa na tsani komai na cikinsa,gashi yanzun insun sake nasara zasu dauke min Nas. Ansan sune sukeyi ba yanda za.ayi mu dauki wani mataki tunda bamuda shaidar da zamu bayar a kotu. Ajiyar zuciya husna ta sauke tana mamakin kalar wannan rikicin nasu. “Allah bazai barsu ba” Shiru kawai yai. A wajen Nas suka kwana ranar. Ita kan bargunan shikam a zaune. Sati biyu kenan cif. Komai ya sauya musu.A asibiti suke kwana da kusan yini. Ana samun ci gaba a fadar likitoci dan ita kam husna idanuwanta baya ganar mata haka tunda har yanzun nas bai bude idanuwanshi ba. Motsi ma bata ga yayi ba. Harta da numfashi da taimakon na.ura yake yinshi. Abinci sai ta hanci. Husna zatai magana da prince ishaq. Zasu danyi hira tun tanajin wani abu inya riqeta jikinsa harma ta daina. Saboda ba yanda zatayi dashi. Takanji kaman bata kyautawa ammar sai dai a sati biyu harta saba tunda ba wani abun yake mata daya wuce riqeta a jikinsa ba. Kuma ta gaji da qaryata zuciyarta hakan na mata dadi. Tana son qamshinsa da duminsa duka. Ta nemi inda tsanarsa take a zuciyarta ta rasa. Gaskiya mutane da yawa sunyin gaskiya. Karka yanke hukuncin yanda kake ji akan mutum saika zauna dashi tukunna. Ta kula shi din mutum ne mai bala.in yanga. Saidai baya so ai masa. Baya son gaddama. Komai nashi da tsari yake yinsa. Bata san me take ji game dashi ba. Dan yansun komai rudani yake sakata. Tunaninta da yanayin komai. Abu daya take da tabbas a kansa son ammar. Yana nan. Duk da yanzun bata tunaninsa ko da yaushe sai dai da taji muryarsa komai yake dawo mata sabo. Kalamansa nakaita wajaje da yawa da suka kai a soyayya. Danma fadan da suke yawan yi kwana biyu. Ta mishi uzuri saboda ita kanta ta rasa dalilin dayasa take biyo prince ishaq asibitin. Inhar zasu koma gida saiya mata tayin ta zauna itace take kiyawa. Ammar kuma gani yake kaman zai rasata ne. Tsoronshi karta soma kulawa da su. * Prince ishaq kam zai iya cewa abinda ya faru da nas ya tuna masa da alqawarin daya daukar ma huddy a maganarsu ta qarshe a rayuwarta. Yama zai manta. Huddynsa zata so ya samu farin ciki sai dai ko bai mata alqawari ba ba zata mantu a gurinsa ba. Darajar so da en uwantaka ta wuce hakan. Husna baima san me zaice da zuciyarsa a kanta ba. Yakan jima bai yarda ya shaqu da mutum ba. Ko abokai yawanci na karatu ne. Sai na asibitin shi da ya dade da barma Dr.Hashim ragamar komai tun bayan rasuwar huddy. Banda kamala bai yarda da kowa ba da sirrikansa. Shima baban shine sarkin fada. Kusan tare suka taso da prince ishaq din. Zuciyarsa tana da rauni mai yawa ta wannen fannin. Tana da saurin sabo. Koya zakai masa karamci baya mantawa. Yanzun ya saba da hussy kam. Bazaiyi qarya ba sabon da har mamaki yake bashi inyai hange zuwa wasu lokutta can baya. Yanzun aurensu haryana kusan tasarwa wata na biyar. Rayuwar babu wahala. A haka muke ta cinye kwanakinmu. * Sun dan koma gida su huta. Nan husna tabarshi ta shiga ciki abinta. Sai da ta kwanta ta huta sukai waya da ammar sannan. Har zata fito ta tuna. Kausar ta kira ta fada mata abinda ya faru. Ta sha mita cewar batada kirki. Atleast ko da basu zoba zasuyi addu.a. * Yana zaune babban falo yana kallon yanda duniyar take a tashar aljazeera husna ta shigo. Gefensa ta zauna batare data ce masa komai ba. Ya sauke numfashi. Yanayin fuskarsa ta kalla tace mishi. “Yadai?” “Meyasa baki taba kiran sunana bane hussy?Tunda yanzun ana kallon fuskana sunan kuma ya gagara” Ya buqata yana qarasa maganarsa da murmushi. Tun rannan ya soma ce mata Hussy din nan. Sai taji sunan ya mata dadi. Idanuwanta nakan kafet din dakin sai takejin wani iri. Sau uku tana bude baki sai taji sunanshi ya makale akan harshenta. Ba zatai mishi qarya ba dan haka tace “Sunanka yanamin nauyin fadane” Ya wani yatsine fuskarshi mai kyau sannan yace “Nikuma na gaji da zama nameless a wajenki.” Murmushi tai bata dago da kanta ba dai. Yanajin dadin yanda yake da tasiri akanta. Koma wanne irine. Muryarshi can kasan makoshi yace. “Uhum inajinki. Ko sunana ko ki zabarmin wani” Iya zaman sun nan tana karantar halayyarsa. Inba abinda ya bukata tayi ba bawai zai barta bane. “Gentle” sunan ya subuce mata da sauri ta dora da “zan kiraka gentle yayi?” Murmushinsa ne ya bata amsa. Bai sake cewa komai. Jingina yai sosai da kujerar yaci gaba da kallon shi. Yanzun harta soma sabawa da wasu halayen nasa. Yanzun zai mata magana kaman zasuyi hira mai nisa sai kuma yai shiru abinsa. Prince ishaq akwai yanga. Wasu lokuttan sai suyi awa biyu zaune baice mata kanzil ba. Yana magana saita kama ne. Ranar cayai mata su kwana a gida. Yai waya yace koya aka samu canji a kirashi. Taji dadin hakan dan hakurin ammar ya kusan karewa. Aikam har sha biyun dare suka kai suna hira. Charge dinshine ya dauke da basu hakura ba * Badan wannan abin daua faru ba da tuni sun koma kano dan wata daya da yan kwanaki kamata ace sunyi a garin abuja Amman yanzun har suna shirin dosarwa wata uku. Taji dadi sosai da kausar tazo har asibiti ita da mijinta suka duba Nas. Dan kam ya zama qani a wajenta. Ranar da Nas ya cika sati uku a asibiti. Sun dawo gida wajen zuhr. Prince ishaq ya fita yace mata akwai abinda zaiyi. * Kallo take sanda ya dawo. Ya zauna kusa da ita yana wani langabewa. “Gajiya ko?” Ta bukata. Ya daga mata kai. Kallon shi take akwai abinda ya canza mata yau. Fuskar shi tai wani fayau. “Meye babu a fuskarka?” Ta tambaya tana kallon fuskar. Dariya yai. Tajima bataji dariyar nan tashi ba. Itama sai abin ya bata dariya. “Aski nayi fa” Ya karasa maganar yana dariya. Shiru husna tai masa. Haba shisa taga fuskar tai wani fayau. Suna zaune aka kira la.asar. Ya tashi ya nufi masallaci. Itakuma husna tai nata bangaren. Tana yin sallar la.asar tasan zasu iya komawa asibiti don haka ta mike. Wanka ta fito tana kwallia a gaban mirrow ammar ya kirata. Daga wayar tai tasa earphone. Cikin muryarsa mai sanyi yace mata tawan “kaman bakyason kashe auren nan ne ko?” Murmushi tai kaman yana ganinta tace “Nawan ba haka bane.Ka yarda dani wlh na rasa hanyar da zanbi ne har yanzun na kashe auren nan. Kai kasan ina sonka. * Sallah ya dawo. Baiga husna a falon su na sama ba. Dan haka ya nufi bangarenta ya fada mata yai waya da doc din Nas. Komai yana nan yanda suka barshi dazun. Bayajin zasu koma yau saidai zuwa safe inyaso su kwana a wajen shi. Kwankwasawa yai har sau biyu shiru. Ya dauka ma sallah take ya tura dakin da sallama ya shiga. Tana zaune kan stool tana shafa mai jikinta sanye da doguwar riga. Kan kunnenshi take furta komai. * Sam bataji shigowar prince ishaq. Da duk kalma daya da zata fito bakinta sai zuciyarsa tai wani irin dokawa. Lokaci daya ya tuno maganar huddy a wani lokaci can baya “Yayana ka zama mai haquri sai dai karka yarda a wulaqanta mana darajarka ta ko wanne fanni” Yau shi prince ishaq matar da take cikin gidansa da igiyar aurensa ukku a kanta ce take waya da wani qato.1 Har take fada mishi maganganu iri wa.annan. Inalillahi wa ina ilaihi raji.un yame ta maimaitawa a zuciyarshi. Yana fatan dai-dai ta hankalin shi kamun zuciya tasa shi aikata abinda bashi kenan ba. Husna kam hankalinta kwance taketa wayarta. Tashi tai dan ta dauko dankwalin rigar jikinta. Tana juyawa taganshi tsaye jingine da qofa……..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *