WATA BAKWAI CHAPTER 2

WATA BAKWAI CHAPTER 2

Ya sha bacci sosai dan jiya da dare sam bai samu wani baccin kirki ba. + Babban falo ya fita hankalin shi a kwance. Bai zaci ganinta a falon ba. Zuciyarshi ta wani doka a yan mintina kadan ya manta da damuwarsa idanuwansa suka natsu wajen aika masa da saqonni kyawun yarinyar da take zaune a falonsa. Hankalinta gaba daya yana kan kallan da take da alama ma bata san shigowarsa ba. Wannan ce natacciyar da aka aura masa kenan to kyawunta bazaisa yaji komai ba yake fadawa kansa. Dan ya tsani makwadaita masu son abun duniya. Kujera ya samu ya zauna can nesa da ita. sai lokacin ta dago ta kalle shi ta sake maida hankalinta kan T.V din kaman baya wajen. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Sam bai saba mace ta kalle shi tai kaman baya nan ba duk min ajinta kuwa.

Yana da kyau shima yasan hakan. Duk macen data kalle shi saita qara kallansa amman ta wani basar kaman bashi bane zaune a wajen. Ballantana kuma in tasan koshi waye yanzun zakaga yarinya nasan yai mata magana ta shishshige masa. Well nasan kudina da kuma matsayina yasa kika nace saikin aureni ya fada a zuciyarsa. Yasan zata juyo ne ta sake kallanshi. Ga mamakinsa miqewa tai ta gabanshi ta wuce batare da tayi koda yunqurin nuna yana wajenba tai gaba abinta. Shi ya bita da kallo cike da mamaki yau shi prince Ishaq mace take wucewa kamar baya wajen. Lallai akwai aiki a gidan nan. Zai iya jure komai dan tun daga huddy zuciyarsa ta daina numfasawa kowacce mace amman banda shariya. Izzarsa da mulkin da yake yawo a jininsa bazai jure halin ko in kula ba. Shi ya kamata ya share mata not the other way round. Domin ita ta nace ma aurenshi bawai shi ya nace ma ta ba. *

Husna kam ganin natacce da tai a falo ba qaramin girgizata yaiba. Kyakkyawa ne naban mamaki. Kallo daya zakai masa ka fahimci hakan. Duk da kiyayyar da take masa tasan yafi ammar kyau amman hakan bashi bane zaisa ya burgeta. Dan yanaji da kudi da kyau ba shi zaisa yai mata katsalandan da fin karfi ba. Kyawunsa baya gabanta tunda shine silar rabata da farin cikinta. Taga alamar yana ji da kanshi sai dai itama hakan take. Ta dawo dakinta ne tabar masa falon saboda karta sake kallan shi ya dauka burge ta yai. ”Babyna bana son inji kince kina kallan indian film kar kije kiga wanda yafini kyau” maganar ammar ta fado mata. “Hmm kai bakasan zuciyata ta kulle ba bata ganin kowa sai kai dear idanuwana ne kawai suke ganinsu.” Wannan shine amsar data bawa ammar a lokacin amman gashi yanzun tana hada kyawunsa dana natacce. 1 Haushi ta bawa kanta hadi da alqawarin zatai qoqarin qin sake kallan fuskar natacce in Allah yaso ya yarda balle harta dinga hada shi da ammar. * Washe gari da safe wanda shine kwananta na biyu a gidan natacce. Ta tashi zuciyarta da nauyi da wata irin kewa ta ammar data addabeta. Jinta take kaman bata da rai a wasu wajajen na jikinta. Komai tana yinsa ne dan anayi. Tun jiya bata qara ganin natacce ba ko yana ina shi yasani dan baya gabanta. Ta kammala duk abinda zatai ta fita zuwa babban falo ko zata dan shaqi banbantacciyar iska da wacce take a dakin baccinta. Ta tako kenan text ya shigo wayarta. Ganin kausar ce yasa ta dubawa taga tana tambayar ko tana lafiya. Wani murmushin takaici ya tokareta. Reply take rubuta mata tana tafiya. Karo taji takaiwa wani abu dabata san komeye ba saboda rubutun da takeyi yasa bata kallan inda zata saka qafarta. Wani irin qamshi mai sa natsuwa ya doki hancinta. Sai lokacin ta kalla taga inda kafadarta ta doka. Faffadan qirjinsa taci karo dashi da sauri ta daga kanta tako sauke idanuwanta cikin na natacce da yake mata wani irin kallo da yasa ta jin gwiwoyinta sun mata nauyin gaske. Ga wani irin kwarjininsa da taji ya cika mata zuciya. Lokaci daya ta sadda kanta qasa tana kallan takalmin qafarsa. Zuciyarta na barazanar fitowa daga qirjinta. A dake yace mata “ki dinga kallan hanya karkiji ciwo.” Wani haushi taji ina ruwanshi da ita shi baisan ta tsane shi bane ba. Ta tsani yanda deep voice dinshi tasa tsikar jikinta tashi. A hasale tace “nagode bana buqatar tunawarka.” Kamin ya bata amsa ta wuce ba tare data sake kallan inda yake ba. * Dakinta ta koma ta zauna kan gado tana maida numfashi kamar wadda tai dambe. Duk jikinta ya mata wani iri. Ga idanuwan natacce da takeji har yanzun kaman yana cikin nata. Hakan yasata saurin rufe idanuwanta ta bude su. Wasu hawaye masu dumi suka bi fuskarta. Ta goge in shaa Allah ta daina zubda ma natacce hawayen aurensa dayake kanta.

Tasa hannu ta goge hancinta ko zata goge kamshin sa da take ji har lokacin. Baisan yanda akai bakinsa ya furta masa abinda zuciyarsa take tunani ba. + Sam ba kalaman da kunnuwan natacciya ya kamata yaji bane ba. Karon datai dashine ya tuna masa wani lokaci shida huddy hakan yasa shi yin irin furucin da yai wa huddy. A karo na biyu da ta kalle shi ta sake dauke idanuwanta daga fuskarshi tamkar wacce taga wani naman ruwa. Baisan abinda yasa hakan ya sake bashi haushi ba. Meye a fuskarsa da ta kasa jure kallanshi. Who is she da zata kalle shi kaman shi din ba kowa bane. Shin zaima iya tuna tsawon lokacin da wata mace tai masa magana da irin yanayin da natacciya tai masa. Wai me take ji dashine? Kyau? In kyaune shima ai yana dashi kuma bayajin tafishi. Babu macen da zata ki girmama shi ko da bata son shi ballantana wadda ta like ma aurensa. Well koma menene zai sauke mata shi. Ba.ai macen da zata share prince ishaq ba ko da kuwa baya sonta ne dole ita ya burgeta. Kawai ta bata mishi rai. KiranNasir ne ya katse mishi tunanin da yake ya dauka yana fadin “mutanen england.” STORY CONTINUES BELOW “Yaya ni nayi fushi fa yau kwana nawa baka kirani ba? Tun ranar daurin aurenka” Yasan bai kyauta ba kam. Musamman da nasir din ya fada mishi kwananshi biyu asibiti bashida lafiya ga exams zasu fara. “Afuwan Kanina hidimomi ne sukaimin yawa shisa kaga ban kiraka ba. Ya jikinka?” “Hmm it is alright” nasir ya fada ya dora da “Alhamdulillah naji sauqi. Ya gajiyar biki? Ya in-law dina? Kadai fada mata nace she should take care of you ko?” Sai da yai dim sannan yace “duk lafiya ya england? Ya karatun?” “England gata muna ciki yaya,karatu yayi zafi mun fara exams jiya, na qagu inzo gida duk nayi kewarku.” Murmushi yai yana qaunar qaninsa kaman me duk a gidansu jininsu yafi haduwa in baka sani ba bazaka taba cewa baba kawai suka hada mama kowa data shi ba. Shaquwarsu zata baka mamaki. Cikin taushin murya Nasir yace masa. “Are you really ok? I mean is she making you happy? If not yanzun na biyo available flight inyo gida” Duk da wasan da yake yi bai hana prince ishaq yin yar dariya ba. “Nas kai din nan ko!” ya fada da fara.a a muryarshi. Haka suka ci gaba da hira na zuwa wani lokaci kamin suyi sallama. * Rayuwa take badan tanajin dadin ta ba. Jinta takeyi kamar wata zombie. Kaman wayar da take da full charge amman babu ko sim balle kai tunanin samun network. Ga wani ciwon kai da baya sauka bata kuma damu data sha mishi magani ba. Ga kirjinta data soma tunani sai ta dinga ji yana mata wani ciwo dakyar take tsugunnawa. Yau kwananta bakwai cir a gidan natacce amman sau uku magana ta taba hadasu. Shima kuma duk kamawa hakan tayi. Ta wanni fanin ta gode masa dabai yunqurin aiwatar da komai ba akanta da batasan yanda zata dauki hakan ba. Kuma ta tabbata ba karamun rikici zasuyi ba. Ta soma mamakin dalilin da yasa ya aureta.

Menene amfanin rabata da ammar ya kawota nan ya ajiye bayan ta kula bama damuwa yai da itaba. Lokaci daya taji ta qara tsanar shi. Yanzun takan fita babban falo ta zauna banda nan bata zuwa kowanne fanni na gidan saikuma in zataci abinci. Idan kewa ta dameta ta gaji da kallo Suna dan hira da su Asabe. Hadiman gidansuna da kirki kuma suna matuqar bata girma. * Yauma kaman ko da yaushe yunwa ce takaita dakin cin abincin. Tana shiga zuciyarta ta doka da qarfi. Ta tsani a gani na hudun nan datai masa zuciyarta ke son fitowa daga kirjinta. Abu na farko da ya fara zuwa tunaninta shine kamshin sa da ta kasa mantawa. Inba sharri bane irin na zuciyarta daga nisan da yake sai taji kaman ta jiyo kamshinsa. Yana zaune kan daya daga cikin kujerun dining room din jikinsa sanye da wata alkyabba Ja. Hannunsa rike da apple din dayake gutsura da wani irin yanga. Ta kula duk ganin da tai masa da alkyabba a jikinsa. Saurin sadda kanta qasa tai kamin ta gama fahimtar kyawun da yayi. Da juyawa zatai ta koma daki idan ya gama ya fita saita dawo. wata zuciyar tace nataccen zaki gudarwa? Qarasawa tai taja kujera ta zauna. Ko kallonta baiyi ba inma yaji alamar ta shigo bai nuna ba ko a jikinsa. Apple dinshi yake tauna hannunsa daya kan tablet din shi da take kan table din wajen. Kawai sai taji jikinta har wani kyarma yake ta kuma rasa dalili. Ga zuciyarta nata dokawa. Yanayin da takeji bata tunanin wani abu zai iya zama a cikinta. Dan jitai ya wani kulle ma. Haka ta dauki kankana guda daya da aka yayyanka da cokali mai yan yatsu tasa a bakinta. Sai lokacin taji idanuwansa na mata yawo a fuska. Bugun da zuciyarta takeyi ya karu. Sam taqi ta dago kanta duk da abinda idanuwanta keson yi kenan. * Yanajin shigowarta da zamanta wajen. Ta kasan ido yaga ta dauki kankana. Ya dago da kanshi ya kafa mata idanuwansa. Kallanta kawai yakeyi yanda take tauna kankanar ma a yangance take yinsa. Kanta a kasa. Badai ta dago ta kalle shi ba ballantana ma yai tunanin zatai mishi magana. He is confused yanzun. Ya soma tababar anya kuwa kwadayine yasa ta nace wa auransa? To inba kwadayi bane menene dalilinta da ba zata nace bata sonshi ba? Kuma inda kwadayine zata dinga shishshige masa tana cusa kanta kaman yanda yan mata sukanyi masa. Sai dai ya kula inda da yanda zatai karta ganshi ma gaba daya datayi. Bata san koda kallan fuskarshi. Tana yi kaman ma bata san yana waje ba duk idan sun hadu. Hakan baqon abune a wajen shi bazai boye ba. Yana daya daga cikin mazan da suke matukar son kulawa. Wata irin zuciya gare shi. Yanajin rashin huddy fiye da ko yaushe ya tuna wani lokaci suna zaune. *** ***

“Ke kaman baki taba ganina ba.” Dariyar nan tata da yake so tai masa tace “yayana ni bana gajiya da kallan ka fa. Kana da kyau sosai.” Murmushi yai miqewa tai idanuwansa a kanta tace “kace fa zaka koyamin doki.” “Ban manta ba huddy zan koya maki ba yauba kinga nagaji yanzun ki tafi wajen Nasir.” “Um um yaya nasir bazai yi hira dani ba yana karatunsa ne fa” ta qarasa maganar a tabare. Komai na huddy ya masa yana son yarinyar wani irin so da yake ji har jininsa ko dan akwai yan uwanta ka ta jini tsakaninsu ne shisa. Tana rikita shi da yawa ya qagu watanni shiddan daya rage musu ya cika ya dauke kayarsa. * Wata ajiyar zuciya ya sauke. A friend circumstances and fate give us nothing more than chat, phone calls, text messages and sharing pictures. + Three good years of sharing secrets, sharing each others ups and down, laughter and happiness, of emotionally being there for each other. And today mark the exact of three months without hearing anything from you. I have nothing to start from… No address to go and look nothing more than a phone number that is no longer going through and a first name that thousands own. I don’t know if you are okay dee…… And i don’t kbow if i will ever stop wondering or worrying. Two things are still certain and i mean very certain to me. In will love and pray for you like a sister wherever you are. Dead or alive Dee. And….. And i will never stop searching with the little i have i will never stop searching and hoping!!! Ajiyar zuciyar dayai ne yasa husna dagowa ta kalle shi. A dai dai lokacin da shima ya dago daga tunanin da yake. Ganin ta yasa shi tuna cewar yafa rasa huddy. Wannan wata ce data shigo rayuwarsa ba tare da amincewarsa ba. Kaman ko da yaushe saurin sauke idanuwanta tai kaman irin taso taga wani abune kuma ta fahimci baya wajen. Husna kam bata san dalilin daya sa ya sauke ajiyar zuciya ba haka. Kaman irin ya tuna wani nisantaccen abu. Yanayin yanda ya kalleta da kuma yanda fuskarsa ta sauya lokaci daya ta daure mata kai. Ya kalleta da sanayya a farko kaman taga yaso yai murmushi ne dayan yanayinne bata fuskanta ba. Kema kike wahalar da kanki akan natacce zuciyarta ta fada mata. Miqewa tai tabar wajen ba tare data yarda ta sake kallan shi ba. Ya dafe kanshi. Baya son matsala amman da duk taku daya dazaiyi dan ganin ya guje mata da taku biyu da zatai don samun shi. Dakinshi ya koma da fita zaiyi yaji sam ya fasa. *

Kwance yake kan gadonshi maganar mai martaba na masa yawo a kwanya. So yai ya tafi abuja abinsa yadan bar wannan shiga hanci da qudundunen da natacciya taiwa rayuwarsa. Yadan samu nutsuwa ko ciwon kan da ke yawan damunshi zai masa sauqi. Ko zai daina ganin natacciyar yarinyar can tana saka mishi jin rashin huddy. Amman Mai martaba yace bazai tafiyar wata daya ba tare da iyalanshi ba. Ko yaushe ta shigo rayuwarshi da har zata zama iyalanshi oho. Shi baima san ta yanda zai fara ce mata ta shirya zasuyi tafiya ba bayan ko kallan fuskarshi bata son yi. Bakuma ya son shige mata saboda bai manta da yanayin da tai masa magana ba rannan. Komai zai iya faruwa in har ta sake daga mishi murya. Bai saba baba. Ba kuma zai fara daukar hakan daga wajenta ba. Gashi jibi yake son tafiya abuja din. Ya gama shirya komai. Beside akwai abubuwan da yake son aiwatarwa da ba zasu yiwu ya soke tafiyar ba sam. STORY CONTINUES BELOW Duk da bata da wani matsayi a wajen sa. Darajar igiyar aurensa da take kanta ya wuce ace ya aika hadimai sun fada mata sako irin wannan. Yanda baya son raini yake ji da izza baya son ya raina wani ta ko wanne fanni. Dafe kai yai ya zama dole ya fada mata duk da baisan kalar zaman da zasuyi ba. “Kalar zaman da kukeyi anan mana. Ko wa yai harkar gabanshi” Zuciyarshi ta fada masa. * Yau satinta biyu kenan a gidan nan da take wahalar kiransa na aurenta. Tun ranar da ta hadu da natacce a dining bata sake ganin shi ba. Hakan yafi mata kwanciyar hankali. * Tana zaune tana kallo kamshinsa ta soma ji wanda tun randa tai karo dashi ta kasa mantawa. Ita kadaima in ta fito babban falo ko taje dining dan neman sharri irin na hancinta sai taji taji kamshinsa. Jin kamshin ya fi na ko yaushe karfi yasata sanin da gasken shine ya shigo. Cike da takaici ta ci gaba da kallonta zuciyarta na dokawa da sauri sauri. Duk da tasan shine ya shigo bata ko motsa ba balle tai yunqurin kallan inda yake. Tadai son nesa da ita zai zauna in zaman yazo yi kenan. Jin zamansa gefenta kan kujerar da take yasa zuciyarta wani irin dokawa da karfin gaske. Hannu tasa ta dafe kirjinta dan zata iya rantsewa natacce dake zaune gefenta yanajin yanda zuciyarta ke dokawa. “Ki shirya zamu je abuja jibi in Allah ya kaimu.” Ya furta muryarsa a dake kuma can kasa. Husna kamar zata kurma ihu. Akan me muryarshi zata dinga tayar mata da tsikar jiki. Saboda me zaizo gab da ita ya zauna bayan kamshinsa takurata yake. “Lallaima wannan ya qure rainin hankali sallama bata hadasu,gaisuwa bata hadasu sai yau zai wani ce mata ta shirya zasuje abuja jibi kaman wani ubanta.” Zuciyarta ta saka mata.

Shiru tai ta kyale shi tai kaman bataji shiba ma. Kanta akan tv. Tasa hannu ta dafe kirjinta kaman yana mata ciwo. * Wani abu yaji ya tokare masa wuya wai wannan yarinyar me take ji dashine haka da zai mata magana ta share masa. Yar wacece ita da kamar shi zai mata magana tai kaman bataji shi ba. Muryarsa a dake can kasan makoshi yace mata “bana magana amin shiru.” Miqewa tai da niyyar bar masa wajen gaba daya. Cikin wani irin zafin nama yasha gabanta saida ya tsoratata. Ganinta tai can like da kasa dan ta tabbata in fuskarshi zata kalla sai ta daga kai. Saboda dogo ne. Kanta a faffadan kirjinshi ya tsaya. Kanta ta sadda qasa bata san ganin shi batasan yana mata magana ba taqi ya fita harkarta ba ya kasa gane hakan. “Matsa in wuce ta fada” muryarta na rawa kanta a qasa. “Look at me… ki bani amsar maganar danai miki” Ya buqata yana zuba mata idanuwansa. Ji yake kamar ya kwada mata mari sai ta dago ta kalle shi. Baya son maimaita magana. Ko yaita fadar abu daya ka kasa ganewa. Bata mishi rai hakan yakeyi ba kadan ba. Wannan natacciyar yarinyar ta kasa gane level din hakurin shi yakai karshe. Numfashi yake ja yana fitar dashi a tsanake ko zai controlling bacin ran da yake ciki. Husna tana jin hawaye na shirin zubo mata. Sam bata son takura ya kasa gane takura mata yake. Kaucewa tai ya sake tare hanyar yaga alama yarinyar nan tana gwada haqurinsa. Batasan waye prince ishaq ba harda rashin huddy ya sake mayar dashi haka. Shi ya sashi zama so cool din nan. Da kudi akace tai masa hakan ba zatayi ba. Gab da ita ya kara matsawa yau kome take ji saita sauke shi ta kalli fuskarsa. Yanajin hucin lumfashinta a kirjinsa. * Husna kam zuciyarta ci gaba tai da dokawa tunda take bata taba yin kusa da namijin daba muharraminta ba haka. Ammar ne yake mata yawo a kwanyarta ga kuma qamshin natacce daya addabeta so take ya kauce ta wuce yaqi. Taga alama inba abinda yace tayi ba bazai barta ba. “Ba zani abuja ba kabani hanya in wuce.” Ta fada da sauri dan batason yaji yanda muryarta ke rawa. Murmushi yai duk da baikai zuciyarsa ba. “I didn’t asked you ko zakije ne. Nace ki shirya. And ki kalle ni kibani amsa” Ya fada idanuwansa nakanta. Ta soma qulewa a hasale tana shirin yin kuka tace “wai kai wanne irin natacce ne ka qyale ni nace ba zani ba!” Kuma sam taki dago fuskarta ta kalle shi. Lumshe idanuwanshi yai ya bude su a hankali. Akwai rigima kenan ya fada cikin zuciyarsa. Hannunsa yasa ya dago mata haba cikin idanuwanta ya kalla. Ji tai duk wani karfi na jikinta yana narkewa. Duk wata gaba ta jikinta ta mata sanyi. “In kina so zaman lafiya you have to take note of three things. Ba.amin magana cikin hargowa. Bana magana aimun shiru. Bakuma nason gardama da maimaita abu.” Ya karasa yana kallonta deel cikin idanuwa. Husna tana jib dumin hannun shi dayake kan habbarta a ko ina na jikinta. Kamar habar tata tana da wani dangantaka da sauran inda take jin dumin nakai mata. Hannu takai da niyyar ture mishi nashi dai-dai lokacin da mararta ta wani irin murda mata sai da ta ji lumfashinta ya na neman daukewa. Hannunshin da zata ture ta kama ta rike gam tana kiran “Wayyo mamina….” Ji tai abin bawai na wasa bane ta sake kama hannun shi ta riko dam tana yin kasa. Takan sha wuya ba kadan ba lokacin period dinta sai dai yau saura kwana biyu take tsammani ga abin yazo mata a bazata…..!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *