WATA BAKWAI CHAPTER 3

WATA BAKWAI CHAPTER 3

rince ishaq kam hannunta yabi da kallo da wani yanayi a fuskar shi.+ Gani yai da gaske takeyi cikin alamar tsoro yace mata “ke meya hakan wai?” Ta ma kasa magana kawai wayyoo mami take kira ta dafe ciki da hannu daya. Dayan kuma ya rike da na prince ishaq dam. Baya son ganin wani cikin yanayi. Hakan na tuna mishi abubuwa da yawa. Tsugunnawa yai Allah ya zuba masa tausayi musamman ma mata. Cikin damuwa yace “Are you okay? wai meke damunki?” Daqyar tace masa “cikina…” Wani abu da ya dade bai motsa ba a jikinsa yaji. Koma menene yafi karfin zuciyarshi. Baisan lokacin daya kai hannun shi kan cikinta ba. “Dai-dai ina yake ciwo? Murdawa yake? Zafi?” Kaman bata masan yanayi ba. Pillow din kujera ya dauko ya ajiye kasa ya samu ya zame hannunshi daga nata. Kamata yai ya kwantar. “Stay right here” ya fada ya mike da gudu har kafarshi ta taka step din farko na benen zai hau sama kawai kamar wanda aka dokawa guduma akai. Ya tuna da alkawarin dayai ma kanshi na kin sake taba wani patient a rayuwarsa. Na barin career din daya so tun yarintarshi. Fasawa yai. Ya sauko da kafarshi. Wajen husna ya dawo da take kwance ta hade jikinta. Ya tsugunna. Muryarshi a tausa she yace mata. “Sannu kinji bara na kira doctor? Or we should go to the hospital? Can you walk? Girgiza masa kai tai muryarta can qasa tace. “zai tafi basaika kira kowa ba.” Hade fuska yai yace “Ban fada miki ba.amin musu ba? Ko yan aikin gidan nan ne basu da lafiya hospital ake kaisu.” Duk zafin ciwon da husna take ji bai hanata harararshi ba. A ranta tace wato ko yan aikin gidan nan. Itama ai ba catai tana da wani matsayi ba. Kaman yanda bata gabanshi bata kuma san me yasa ya aurota ba. Haka itama baya gabanta. Tana kallonshi.Wayar shi ya dauko tana jinsa ya kira. A wajen ya zauna duk motsin da zatai zai mata sannu. Har doc din ya qaraso. Cike da girmamawa taji sun gaisa kuma ya kira shi da prince ishaq. “Prince ishaq” ta maimaita. Daman sunan shi ishaq kenan. Tambayoyi doc din ya soma jero mata yanayin amsarta yasa ya fahimci period ne takeyin nata mai wahala. Yadan rubuta mata magunguna yace bawani abu bane period dinta ne zai dai-dai ta inta sha wannan magungunan. Ya maida hankalinshi kan prince ishaq yace. “You know the rest…. ” “I quit. Sau nawa kuke son in fada maku?” Yai maganar da wani yanayi a muryarsa. Murmushi kawai doc din yayi yana daukar jakarsa. Yace ma husna. “Allah ya kara sauki” Ta amsa da amin muryarta can kasa. “ka tafi da prescription din saika sa a kawomana” Prince ishaq ya buqata. “Alright Nabarku lafiya” Doc din ya fadi yana ficewa. * Kallonta yake a nutse. “sannu ya fada a cikin sanyin murya.” Tana jin shi. Yanda idanuwansa ke mata yawo a jiki. Shiru kawai tayi masa. Bata so yana mata magana. Ita dazai tashi yabarta ma da taso. Jin tayi shiru ga idanuwanta a rufe ya sashi daukar tayi bacci. Ya sauke wani dogon numfashi. Sam baya son matsala. Auren nan matsala ne a wajen shi. Yanzun idan irin wannan yana faruwa shi ya zai yi ne? Jin tunani zai haye masa yasa shi miqewa ya fita daga dakin. Cikin hadiman gidan ya tura mata guda daya don shi baida lokacin dazai bata yana kula da ita tunda bashi ya ajiyeta ba. Kawai dai wata irin zuciya gareshi idan yaga mata cikin rauninsu. Sai yanzun ma kalamanta suke sosa mishi zuciya. Ya rasa meyasa natacciya bata son kallon fuskarsa kuma bata shakkarsa shi. Wato yanda yake kiranta natacciya shiya bata damar ce masa natacce.1 Ko dayake yafi ganin laifin mai martaba a wannan karin. Shi ya takura masa ya aura masa ita kaman yanda yanzun ma yasa shi tafiyar nan da ita.. Sam baya son daukar kaya don ya tabbata shi zata zame masa. Abinda zaije yi abuja yana bukatar sirri kuma mai martaba yafi kowa sanin haka. Dashi kadaine zai zauna hotel abinshi. In yaje gida mutanen da yawa na iya sanin yana garin abuja. Dafe kai yai ya sauke numfashi dai-dai lokacin da wayarsa ta dauki qara alamar kira ya shigo.. Sanin kowa keda ringtone din yasa shi fito da wayar daga aljihunsa ya lumshe idanuwansa sannan ya dannan wayar ya kara a kunne. “Yaya wacece wannan data dauke hankalinka haka? Kar kasa in tsaneta tun kafin inzo…..baka da lokacina sam.” Cewar nasir da yake maganar kamar zaiyi kuka. Yasan babu macen da ta isa ta dauke mishi hankali daga kan kanin nasa koda huddy ce balle wannan natacciyar duk kyan da take dashi kuwa. Kawai dai damuwa ce tai masa yawa. “Haba mana nasir. Wacece ma ta isa? abubuwane sunmin yawa babu lokaci sosai amman everything is gonna be alright karka damu.” “Yaya sune ko? Ba zasu barmu mu huta ma ranmu bane wai? Ko in dawo gida?” Prince ishaq zai iya jin tsantsar damuwar da nasir din ya shiga. Don haka yai kasa da muryarshi yace. “No! Ka tsaya ka gama exams dinka kana jina ko? I am okay! Komai zai tafi dai-dai in shaa Allah” “To fadamun what is going on? ” nasir ya bukata. Prince ishaq ya dafe kai.Sanna yace. “Drop it nasir. I am serious ka kyale maganar nan” “Hmm” kawai ya furta ya kashe wayar. Prince ishaq ya soma tunanin kila dai saiya dinga rubuta abubuwan daya kamata yayi saboda yawan mantuwar da yake yi these days. Ya saba kiranshi a kullum yaji lafiyarsa da yanda komai na rayuwarsa yake tafiya amman a satikan nan ko dan text din baya samun damar tura masa. Bayan damuwar da take zuciyarsa baya buqatar wata damuwar kuma dan haka text kawai ya tura masa ya kwantar mada da hankali. Ji yai iskar wajen ta masa kadan. Ji yake kamar kar nasir su gama exams dinsu ya dawo Nigeria. Zaman shi a England yafi masa kwanciyar hankali. Yasan masu farautar ransu da son gadon mulkinsu duk abinsu zasu bar masa kaninsa in yana can nesa… Asabe tai zaune a wajenta har doc din ya dawo da magungunan daqyar ta tashi tasha.+ Bata jima ba ta samu bacci cike da mafarkin ammar dinta. Bata farka ba sai da yammaci sosai. A hankali ta bude idanuwanta….yanayin yanda taji jikinta ne tasan cewa ta baci ta dan gyara kwanciya da niyyar tashi taga Asabe a zaune cikin ladabi. Tasan ita ta shigo wajenta bayan fitar natacce. “Badai tun dazun kina nan ba?” Husna ta tambaya da mamaki a muryarta. “Ranki ya dade ina nan koda zaki farka ki buqaci wani abu….ya jikin naki?” ta amsa a ladabce. Ita kam bata son wannan girman da suke bata nauyinsa takeji a kunyace tace “da sauqi zaki iya tafiya abinki nagode.” “Ki huta lafia” Asabe ta fadi ta mike ta fice,ciwon da takeji yayi sauqi sosai tashi tai ta nufi dakinta. Kanta tsaye toilet ta nufa ta soma yin wanka don ta tsaftace jikinta. Ta wanke kayan data bata ta dauro towel ta fito. Wata er jaka data zubo abubuwan da tasan zata buqata ta dauko Always dinta ta duba saura guda biyu. Ta dauki daya ta shafa farin almiski a jiki saboda yana dauke karnin jini kuma yana maganin ciwon sanyi da qwayoyin cuta da dama. Bayan ta gama shiryawa tunani take tasan dole ma ta fita shopping tana buqatar kanan abubuwa na amfani. Tsaki taja a fili tasan ba zata taba tambayar natacce zuwa unguwa ba don bai kai wannan matsayin a wajenta ba. Shiru tai tana sake sake. Dazun da mararta ke ciwo sai taji kamar yasa hannu ya taba mata ciki. Wani zafi taji kirjinta nayi. Inba tsabar naci ba inama ruwanshi da ita da har zai taba mata ciki. Tama manta shi nashi hannun data kama ta rukunkume. Dan rainin hankali wato jibi zamu tafi abuja ta nanata a zuciyarta wallahi yama rainani ta furta a fili. Inba raini ba shi yana ma da qafafuwan dazai kwaso yazo wajenta yana fada mata zaiyi wata tafiya kuma har ma da ita. Tunda a nata tunanin bata ga me yasa zai sanar da itaba. Babu ruwanshi da ita. Ko gaisawa basu taba yi ba. Sai tai kwanaki bata ganshi ba. Tome zatai masa in sun tafi taren ko kuma dai salon ya qara takurata fiye da wacce take ciki ne a yanzun? Gabanta taji ya fadi. Kar dai ace so yake sai sunje abuja yace zai hada shimfida da ita. Tunanin hakan kawai yasa taji hawaye sun cika mata idanuwa. Goge su tai. Tana tuna alkawarin datai. Cewar ba zata sake zubda ma auren nataccen nan hawayenta ba. Ko me zai faru kuwa. Tadai san akwai rikici kwance in har abinda take tunani yai shirin faruwa. Wata irin kewar ammar take ji kaman zuciyarta zata fito. Wayarta ta dauko. Tun satin bikinta aka qwace wayoyinta duka aka bata wannan aka kuma sake mata sim babu number din kowa saita yan gida da kuma kausar. Ta sake jin wata tsanar natacce a zuciyarta. So take taga karfe nawa. Dan tana son fita sosai. Idonta yakai kan date din wayar. Jitai kanta ya wani sara. Lokaci daya wani irin jiri ya kwasheta. “06-03-2015” Bangon wajen ta dafa tana kiran “Inalillahi wa ina ilaihi raji.un” babu adadi ko zuciyarta zata samu nutsuwa daga yanayin da ta shiga a wani bangaren kuma tunani yakaita wani lokaci can baya…………..! *** *** Tana kwance kan gado wayarta ta dauki ruri. Jin kidan kawai ya bayyana murmushi a fuskarta. Dagawa tai ta kara a kunne hadi da yin sallama. Ya amsa mata daga dayan bangaren ya dora da. “Haba mana tawan. Sai anjamun aji za a daga wayar? ” Dariya tai wani son shi na sake shigarta tace. “Nawan ni na isa kawai dai….. ” “Kawai dai me?” tanajin murmushin dake muryarshi. Itama murmushin take a kunyace tace. “Nayi kewarka ne nawan” Ajiyar zuciya ya sauke da tanajinta har ta cikin wayar kamun yace. “Idan na fadi nawa a fili zaiyi yawa tawan. In shaa Allah 06 ga watan 03 zan dawo” Lumshe idanuwanta tai saboda hawayen da taji suna mata yawo. Muryarta na rawa tace. “Wata ukku kenan nawan” Sai da yai jim sannan yace. “Tawan ki mun addu.a ke dai. Randa na dawo ba zanyi awa biyu ba za.ai maganar aurenmu in shaa Allah.” Ba zata iya ci gaba da maganar ba. Dakyar tace. “Nawan zamuyi waya anjima” Shima shiru yai na wani lokaci kamun yace. “Babu damuwa. Ina sonki sosai. Take care of you for me” “You too” ta amsa tana ajiye wayar tasan zai kashe……. Cikinsa yaji yana masa qara kuma yasan yunwace tun tea din daya sha da safe bai kuma samun natsuwar qara saka ma cikinsa wani abuba.+ Abinda ya kara bata mishi rai tunanin waccan natacxiyar yarinyar daya fado mishi cikin jerin muhimman tunanin daya kamata ace yanayi. Fada ma kanshi yake cewar auren shi dayake kanta bashi ya nema ba. Saboda haka ba matsalar shi bace. Ya fita hakkinta tunda ya kira mata doc. Ya kuma tura a kula da ita. So baiga dalilin dazaisa ace yana tunanin ko taji sauki ba. Duk da hakan ba bakon abu bane wajen shi in har akan marar lafiya ne. Ita din daice baya so tana kutso mishi kai cikin tunani. Bai baro inda yake ba sai bayan la.asar. kansa tsaye dining room ya wuce. Plantain da qwai yaci yasha fresh milk ya fito. Dakin shi ya shiga ya watsa ruwa ya saka wani farin yadi marar nauyi. Tunawa yai a dining yabar keys dinsa ya fita ya dauko. A babban falo ya hadu da natacciya kallo daya yai mata zuciyarshi ta wani harba. Rabon dayaji ta numfasa masa haka tun huddy. Tayi kyau duk da bayason fadar haka cikin doguwar rigarta abuja style daurin dankwalinta simple sai mayafi. Tunda can yana son yaga mace cikin shigar kaya purple kowanne irine. Lokaci daya yaja wata qatuwar qofa ya kulle zuciyarsa baima san yanda akai qofar ta soma budewa ba. Da alama fita zatayi don akwai qaramin mayafi a jikinta tasa shade shima purple. Cike da mamaki yake kallonta….kaman koda yaushe kanta a qasa ko inda yake bata kallaba asali ma rabawa tai ta wuce kamar baya wajen. Ficewa tai abinta. Murmushi yaji ya qwace masa ya jima rabon dayaji ya bayyana a fuskarsa haka kawai inba mahaifiyarsa yake tare da ita ba ko suna waya da qaninsa.. Yasan ko qofar farko ba zata wuce ba,babu wanda ya isa ya bude mata gate batare da izininsa ba. * Hanyo yi taita bi. Bata san gidan nada girma haka ba sai yau. Daya daga cikin hadiman gidan ta sa ta rakata har kofar gidan. Sai da ta ganta a wajen gidan tukunna zuciyarta da take dokawa tadan dai-dai tu. Tana saka shade in dai zata fita amman ba kowanne lokaci ba. Yauma ta saka ne saboda ya boye idanuwanta dan kallo daya zakai mata ka fahimci ta sha kuka harta godewa Allah. Date din data gani ne ya sake tunzurata ta fita bada izinin mijin da aka daura mata ta fin qarfi ba….duk da sanin hakan ba dai-dai bane bai dameta ba. Tunda ba tada mota a gidan ta yanke shawarar daukar drop zuwa diamond bank ta ciri kudi sannan kuma ta zo stop and shop ta siyi abinda take buqata. Mamakin girman gidan take yi harda titi a ciki kaman na estate dinsu ta dan soma gajiya da tafiya dan ba sabawa tayi ba. Gate tagani a garqame kuma babu kowa a wajen taji wani takaici ya rufeta takai mintina goma a tsaye a wajen wai ko zataga wani ya bullo tasa ya bude mata amman babu kowa. Juyawa tai idanuwanta cike da hawaye tanata qoqarin tarbesu karsu zubo kenan fita ma in zatayi komin buqatarta saita sauke ajinta ta tambayi natacce kenan. Bata kaunar abinda zai hada su magana da juna. Tana son fitar nan kam ko dan gyaran jikinta ma dole ta fita….tafiya take ga nauyi da zuciyarta tai mata. Ko a wanne hali ammar yake? Allah kadai ya sani tana dai da tabbacin tsakanin jiya da yau ya tsaneta! Tasan abinda ya kamata tayi….duk da kashe di da mahaifinta yai mata. Ta tabbata inda shi ya tsinci kansa a halin data tsinta zai fahimci yanda takeji. Da wani sabon qarfin gwiwar data jima bataji shiba ta juya ta shiga gidan. * Prince ishaq kam keys din shi ya dauka ya shiga dakinshi ya dakko system ya dawo babban falo. Yana zaune a falon hankalinsa akan system dinsa husna ta shigo. Ta tsane shi wata irin tsana dabata san kalarta ba ko ganinsa bata sanyi. Ganinsa kuma datai sai yake kokarin ruguza mata dan kwarin gwiwar da take ji. Abin takaicin ma sai da taji gabanta na faduwa. Ga wani kwarjini da taga ya mata. Tsaki taja cikin zuciyarta. Batason wannan abin da yake mata ko kadan. Cikin muryar dabata gane tata bace tace masa “kazo kasa a budemin gate zan fita.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *