WATA BAKWAI CHAPTER 8

WATA BAKWAI CHAPTER 8

  Tun dazun da safe da tazo fitowa ta hango natacce da sauri ta koma dan bata son su hadu. Ya bala.in yin kyau cikin fararen kayan daya saka. Komai farine a jikin shi. Bata sake fitowa ba saida tai sallar azahar. Falon saman tai zamanta tana kallo. Pillow din kujerar ta dauka ta gyara ta kwantar da kanta. Kamshin natacce ya cika mata hanci. Da sauri ta zame filon ta cillar kan kujerar dake can nesa da ita. Wani yanayi takeji data kasa fassara shi. Koya maganan natacce ya fado mata sai zuciyarta tayi wata irin dokawa. Kawai kamshin shi dan naci ya tuna yanayin duminsa da maganar shi da komai nashi. Ammar! Ammar kawai! Ammar shi kadai. Haka take ta nanatawa zuciyarta ko zata daina kaita inda bata da buqata ba kuma a buqatarta. Wayarta ta dauka ta duba lokaci.Tai mamakin jan lokaci haka Kusan la.asar sai ta tsinci kanta dayin murmushi ammar ya kusan dawowa aiki. Tana wata irin kewarsa yau. Sallama taji da karfi ana kiran “Anty! Anty!! Gidan ba kowane??? Cike da mamaki ta mike tana sauka benen zuwa falon kasa. Saurayine matashi mai kimanin shekaru sha takwas zuwa sha tara. Duka bazai wuce shekarunta ba ko zata girme shi bazai shige watanni ba. Kallo daya tai masa taga yanayin kama da suke da natacce sosai. Saidai wannan ko hannun rigarsa bai kama ba a kyau. Kyau! Ta nanata, zuciyarta bata ma ammar adalci dahar tama tsaya kula natacce na da kyau. Murmushi yake mata “lallai banga laifin yaya ba” Dariya tai haka kawai taji ya shiga ranta tana son mishi kirki. “Um kaji zolaya. Zuwa babu sanarwa haka?” Ta fadi. Dariya yai shima “Anty afuwa naso in muku bazata ne. Shisa ko yaya ban fadama ba.” “Bai jima da fita ba shima ta ce tana qarawa da fatan baka kwaso yunwa ba dan bamu da abincinka gaskia” Zaro idanuwa yai ya dafe qirji da “fadin anty! Ke kin fara sakin na hannuna fa!” Dariya sukai gabaki daya. Sai taji ta duk wani iri duk da dawowar ammar farin cikinta ragagge ne. Amman yaron nan yasataji daban. Da yanayin fara.arsa da wasanninsa. “Bara na kira a shigo maka da kayanka ko” Husna ta bukata. Girgiza kai yai yace. “Suna bangare na ai an shigo dasu” Nas ya fadi yana dorawa da. “Gosh am damn tired. Anty barin watsa ruwa” Kamun husna tace wani abu harya wuce da gudu. Gidan ba baqonsa bane kuma yana da bangarensa a ciki. * Mamaki ya cika husna. Banda falo bama ta taba kula da komai a kasan nan ba. Kodan yaushe ma take zaman kasan. Kullum tana can sama a zaune abunta. Bata son natacce. Amman kaninshi ya mata. Yanayin shiriritarsu iri daya data maheer kaninta. Murmushi tai ya debe mata kewar ganin maheer kadan. * Wanka Nas yai. Ya sake kiran mumyn shi yace mata yana gidan yaya ishaq. Saiya huta sosai zai shigo kano. Mumyn shi bata ma wani damu ba. Tasan tsakanin Nas din da yayanshi sai Allah. Yana iya kwana biyu bai kirata ba ya kira yayanshi. Blue jeans ne a jikinshi matsatse. Sai riga fara kal data kama shi. Fitowa yai ya samu husna zaune a falo tana kallo. Kujerar da take opposite ta husna ya zauna. Ba yanda batayi dashi ba akan yaci wani abu yace mata shi bayajin yunwa. Sunata hira yana bata labarin yan school dinsu. Kalar pranks din da ake playing wa malamai da haukan yan makaranta dai. Zaka rantse sunyi shekara da sanin juna. Kamun daga bisani wani comedy a new world cinema ya dauke musu hankali. Dariya suke tayi ta sha su a gaddama wanda yafi wani shirme cikin yan film din. Sam basuji sallamar prince ishaq ba. Tsayawa yai yana kallonsu. Karo na biyu daya taba ganinta tana dariya haka. Murmushi ya qwace masa dabaisan dalili ba. Qarasawa yai ciki sai lokacin suka ganshi. Kaman qaramin yaro naseer ya ruga da gudu ya ruqunqume yayan nashi. Dariya yake da fadin “Naseeru zaka karyani ne bakasan nagaji ba koh?” Sakin shi nas yai kaman zai kuka yace. “Yaya naseeru fa?” Dariya prince ishaq yai sosai. Yasan ya tsani ace masa naseeru. Kallonsu husna take ya qara kyau dayai dariya. Kaman bashi ba. Sai ta tsincin kanta da son boye halin da suke ciki ita da natacce ko dan yaron nan da taji sunansa a yanzun. Already iya zamansu da bai shige awa daya ba taji kaman ta saba dashi. Duk da hakan bazai hanata kashe auren su da natacce ba. “Sannu da zuwa” Ta furta a hankali. Kallonta kawai yake cike da mamaki saiya tuna nas na wajen dan haka yace “sannunki da gida” Wannan shine magana ta farko da suka fara cikin natsuwa da junansu. Sai takejin daban. Tashi tayi ta basu waje su gana da junansu. Sai da prince ishaq ya haura sama yai wanka ya dauro alwala sannan ya sakko kasa. Dan yaga magrib ta kusa. Hira suke shida Nas ya kalle shi a nutse yace “Yaya matarka na da kirki i know babu mai maye gurbin huddy,sai dai zaka samu wadda zaka so kala daban” Ajiyar zuciya ya sauke nas bazai gane ba yayi yarinta da yawa wajen da huddy ta bari babbane. Babu macen da yake zaton zata so shi kaman ita. Ba kuma ya zaton zai sake samun so irin nata. Komai na huddynsa dabanne. Shi din take so. Tasan shi fiye da kowa. Badon kudi ko matsayin shi ba. Sone na tsakani da Allah. Rayuwa kenan. Ba komai da kake mafarki bane zai zamo maka gaskia.1 Bakomai daka tsara bane zai faru. Kana ta tsara rayuwarka kana hango abubuwa da dama. Allah ya gama tsara komai. Tsarin shine Mafi cancanta. Murmushi kawai yai ma nas. Hira suka ci gaba dayi cike da shaquwa. * Tana shiga dakinta kiran ammar na shigowa. Dan haka tai kwanciyarta suka soma shan hira abinsu yana bata labarin wani film da ya kalla a office. Sai da aka kira magrib sannan suka katse wayar da cewan zai sake kiranta can anjima. Ta jima a zaune tana addu.o.i. bayan ta idar da sallar magrib. Dan tana mikewa ana kira. Isha.i dan haka ta sauke nauyi. Jingina kanta tai da gado. Tana sauke ajiyar zuciya. Batasan ta yanda zasu soma magana da natacce ba. Basa magana da ganin juna kullum ma ya ta kare da bugun zuciyarta duk idan sun hadu. Ita da take neman makasar auren nan. Kwankwasawa taji anyi a hankali ta furta. “Shigo” Kaman ko da yaushe kamshin shi ya cika mata hanci. Wannan karin sai taji gajiya ta saukar mata. Batai kokarin fada da yanayin da take ji ba. Kyale kamshin tai ya ratsa ko ina na jikinta. Da sallamar sa ya karasa inda take. A kasalance husna ta amsa. “Nas yace in fada maki saida safe. Ya gaji sosai ya kwanta” Ya fadi idanuwansa na yawo a fuskarta. Cikin sanyin murya tace. “Allah ya kaimu lafiya” Ya amsa da. “Amin” Yana dorawa da “Thank you” Jin tayi shiru ya sashi mikewa. “Good night” Ya fadi bai jira amsarta ba ya fice abin shi. Wani numfashi husna ta sauke da batasan tana rike dashi ba. Wani iri take ji. Wannan kirkin nashi yasata jin daban. Wayar ammar ta katse mata tunanin da take. Dagawa tai tace. “Nawan barin zo. Wanka zan sai mu sha hira”1 Ya amsa da. “Karki dade” Wanka tai ta rigar bacci marar nauyi. Ta dauki wayarta ta kira ammar. Bai dauka ba ya kashe ya kirata. Sunata hira yace. “Tawan ina jin tsoro fa. Jikina yana bani zan iya rasaki har abada” “Hmm nawan. Dan Allah ka daina karyamun zuciya haka. Believe in us mana” Shiru yai na wani lokaci sannan yace. “Bakomai” Hira sukai tayi har bacci ya soma daukar husna. Hakan yasa suka hakura. Tai addu.a. Bacci ya dauke ta. * Prince ishaq harya kwanta yana mamakin karamcin da natacciya taima kanin shi. Shi mutum ne da baya manta alkhairi ko ya yake. Sannan indai kai masa mutunci komin kankantarsa yakan ji dadi. Yana son Nas sosai. Duk wanda ya nuna ma Nas kauna dole ne ya samu karammawa a wajen shi. STORY CONTINUES BELOW Zai kokarin ganin ya mata mutunci gwargwadon wanda taima kaninsa yau. A karo na farko a watannin nan da bacci yazo masa cikin sauki da nutsuwar zuciya. * Sai bayan tayi sallar asuba. Tai wanka tana zaune tana shafa mai, mafarkin da tai jiya ya fado mata a rai. Wani irin dokawa zuciyarta ta shiga yi. Komai ya dawo mata. Mafarki tai ammar da natacce na tsaye kowanne a gefenta. Tana kallon ammar ta nufi natacce ta rike hannun shi gam. Suka tafi abinsu ko juya batai ba duk yanda ammar yake ihun kiran sunanta. Harta gama shiryawa jikinta kyarma yake. Tana ta karyata mafarkin da tai. Ko da ta kwanta. Kasa komawa bacci tai. Tunani ya mata yawa kanta harya soma ciwo. Ko da sukai waya da ammar saida ya tambaya ko lafiya kuwa. Tace masa kawai kanta ne yake ciwo. Zasuyi magana anjima. Fitowa tai daga dakinta zuwa falon kasa. Ganin nas yasa murmushi ya qwace mata. “Um me ake taci haka ba.a neman mutane?” Ta buqata cikin siga ta tsokana. Bakinsa cike yace “Ina kwana anty” “lafiya Nas ya gajiyarka” Tai maganar tana zama kan kujera. Shikam yana zaune kan kafet tsakiyar falon da plate din stuffed cabbage sai mug da coffee a ciki. Saida ya hadiye abinda yake bakin shi sannan yace “haba anty fushi muke fa. Jiya kikai tafiyarki.Inkin manta da yaya ni ai bai kamata a mantani ba. Ko ya kace yaya?” Husna ta mayar da kallonta inda nas yakai nashi sai lokacin ta kula da natacce da haryanzun da tasan sunansa bata shirya daina kiransa da nata ba. Sanye yake cikin wando jeans blue da riga mai dogon hannu baqa. Karo na farko data fara ganinshi da shigar kana nan kaya. Saurin dauke idonta tai daga kanshi kamin mayyar zuciyarta tace yayi kyau. Ga yanda zuciyarta take dokawa fiye da ko yaushe saboda mafarkin da tai ya dameta. Cikin muryarshi dakakkiya yace “Ji bakinka a wajen wato inta mantani kai ba zata mantaka ba. You are nuts” Muryarshi din nan kanta karin matsala ne. Tun dacan ko wani yai magana da muryarsa babba haka saita dago ta kalle shi. Saidai ammar dinta muryarshi sanyi gareta ba kaman ta natacce ba da inyai magana take jin wani abu na miqewa a bayan wuyanta. Sai yanzun zuciyarta ke tattara bangarori da dama da batasan ta kula dasu ba waje daya akan natacce. Hatta yanda yake zama tattare yake da nuna isa da iko irin na jinin sarauta. Dariyar nas ta katse mata tunaninta. “Anty kinji yaya koh?” Ya fadi a tabare da sai da ya sata dariya. “Zo ga waje ki zauna” Prince ishaq ya umarta. ‘ki’ din da yai amfani da ita yasata fahimtar da ita yake kasancewar babu wata mace a wajen. Sororo tai tana kallonshi da wani yanayi data kasa fahimta. Idanuwansa ya kafa mata yako yi sa.ar sauke su cikin nata, sai taji tamkar tana shirin nitsewa cikin wani irin qaton kogi hakan yasata kauda idanuwanta daga cikin nasa. Hannunsa ya miqa mata alamar ta taho ta kalli nas daya zuba musu ido. Saita miqa masa hannunta yana riqeta taji tamkar wayar wuta ta jata zuwa yanayi na daban. Rikon dayai mata sak da wanda yai mata a mafarki. Ga zuciyarta da take zaton natacce dake zaune yana jin harbawar da take yi. “Oh God this is so gross! Nas ya fadi yana dafe kai. Ya dora da “Inta zauna a jikinka dakina zan tafi” Dariya sukai gabaki daya hakan yaba husna damar qwace hannunta daya riqe ta nemi gefensa ta zauna tana murza inda ya taba ko zata cire duminsa da yanayinsa daga jiki. * Komai yake yi saboda nas ne. Baya son da minti daya qaninsa ya fahimci auren nan bai dame shi ba. Koh dan farin cikin da yaga ya samu na ganin kamar komai ya soma dai daita a rayuwarshi. Ya gaji da qaryata zuciyarsa kan cewa yanajin wani yanayi game da yarinyar nan da baisan meye ba. Sai dai daya kalleta zuciyarsa kan doka da tsanarsa da yagani cikin idanuwanta. Zai iya cewa yana ganin tsana data fi tata a idanuwan mutane akansa. Kan mulkin da sam baya gabanshi. Shisa ma ko tunaninsa bayayi. Asalima da akwai abinda zaiyi ya gujema matsayinsa da tuni yayi. Ya kula taji abinda yaji da jikinsa ya hadu da nata.Hakan ya mishi dadi saboda shine fa. Prince ishaq komin tsanar da zata mishi dole taji wani abu game dashi. Yanzun ma ya tabata ne dan yana son ta fara sanin zai iya duk abinda yaso. Kuma saboda nasir. Saida taba tan ya bude masa shafi a zuciyarsa da ya jima da rufewa. Ajiyar zuciya ya sauke. Ta rugasu tashi dan haka bata jira komai ba tai breakfast dinta. Ta samu waje ta zauna. Text ta tura ma ammar taji ko lafiya dan bai kirata ba da safen nan. Kaman ko da yaushe hancinta ya fara jin shi. Bata juya ba. Karasowa yai inda take ya zauna gefenta. Saita tsinci kanta da ce masa “Ina kwana” Cikin babbar muryarshi yace mata. “Kin tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Ta fada tai shiru. Can tace masa. “Nas fa?” Murmushi ya kwace masa jin sunan kanin nashi kawai. Ya kuma ji dadi har zuciyarsa data tambaya. Yana kuma yaba karamcinta na kokarin boye ma Nas halin da suke ciki. A nutse yace. “In yazo adjusting banbancin lokacinmu yana masa wuya. Bacci yake” Su duka zaune suke shiru. Idanuwansu duka kan T.V din yake amman babu wanda hankalin shi yake akai. Kaman yanda komai na jikin husna yake sane da zaman natacce kusa da ita hakan yake a nashi bangaren. Zata iya rantsewa duk da karar t.v bai hanata jin fita da shigar lumfashin shi ba da yake kara ma zuciyarta sauri wajen dokawa. Ba karamun dadin fitowar Nas taji ba dan saiya dauke mata yanayin da take ji. Saida ya karya sannan ya dawo falon. Hira suke su dukansu wayar nas tai ringing. “Ina zuwa pls” ya fadi yana miqewa. Prince ishaq ya maida natsuwarsa kan husna. Cikin muryarsa ya soma magana. “Nakan jima ban ma wani godiya ba. Hakama nema alfarma abune mai nauyi a wajena. Nagode da karamcin da kikai ma kanina. Nagode da boye masa zamanmu. Ina son mu zama friends a iya zaman da nas zaiyi damu. Kome zamu ci gaba bayan nan bai dameni ba.” Miyan dake cikin bakinta taji ya qafe. Harshenta ya mata nauyi. Saboda bata ma san me zatace masa ba. Kai kawai ta daga masa alamar ta amince. Hannu ya miqa mata hadi da fadin “friends?” Tayi jim kamin ta karbi hannun nasa “friends” Ta amsa. Cikin wata murya da ta kasa gane ko tata ce. Murmushi tai masa cike da yanayi da yawa. Shima murmushin yai mata data fahimta tamkar yana son gaya mata a can wani bangare na zuciyarsa yaso ace sun hadu a wani lokaci ba irin wannan ba. “Ishaq” Ya fadi yana zuba mata idanuwansa. Daurewa tai ta rike kallon da yake mata cikin nata idanuwan sannan tace. “Husna” Agogon shi ya duba ya kalli husna yace. “Zan fita bazan jima ba. Ki kula da kanki alright? ” STORY CONTINUES BELOW Dakyar ta hadiye abinda ya tsaya mata a wuya tace masa. “Allah ya dawo dakai lafiya” Amin ya fadi yana mata murmushin da saida dimple dinshi ya fito sosai. Bata taba kula dashi ba. Ko da yake bata kula da abubuwa da yawa akan shi. Sai take jin kaman taci amanar ammar a yanzun nana. Zuciyarta na gaya mata bata kyauta ba. Wani bangare kuma mafarkin datai ya mata tsaye. Haka Nas ya fito ya sameta. Ya tambayeta ina prince ishaq yace ya fita amman bazai jima ba. Nas yace mata zai koma daki zasuyi video chat da friends dinshi ta imo. * Dakinta ta koma tana kwanciya text din ammar ya shigo yana fada mata charge ne baida shi tahau whatsapp suyi hira. “Tawan inajin nisanki da kusancinki a lokaci daya a zuciyata na kasa tantance yanayin kowanne.” Ammar ya rubuto. Murmushi tai ta rubuta masa amsa. “naka yanayin mai sauqine tunda har kana iya dorashi akan kalamai nawan. Ni kadai nasan me nakeji.” “Bazan iya rabuwa dake ba husna kin zamo ni gabaki daya. Ki tausayawa rayuwarmu ki dawo gareni.” Wani daci taji dan a yanzun komai ya kwance mata. Ta rasa mafita. Gaba daya kanta ya kulle. “Hmm ka tayani addu.a ina ta tunani ne nawan.” Alama tagani cewan yana recording voice message. Hakan yasata mika hannu ta dauko earphones dinta kan gado tasa jikin wayar. Voice note din farko ta bude. “In aka yarda daso aka amsa shakuwa bataki shiga ba. Tunda nai miki kin mini naji sai mu killace sirrin juna. Abinda zai fita kan harshe da zuciya ya fita. Ki dan matsar da mayafinki ki ganni daina rufa. Idan naganki cikin shauki sai na daina kwafa. Farin cikinki adona ne fushinki shi na tsana” Wani abu taji zuciyarta nayi. Shi ba ciwo ba. Shi ba tsayawa ba. Tasan ammar. Tasan ammar sosai ta kuma san cewar ko hira suke in har ya soma yi mata waka. To abinda yake ji ya girmama. Muryar prince ishaq ta soma sata manta yanda take bala.in son muryar ammar. Musamman in yana mata waka. Mamaki take akan yaushe ya juye mata zuwa prince ishaq a zuciyarta. Wani voice note din taga ya shigo kamun ta gama budewa wani ya sake shigowa. Kuka ya kwace mata. Kuka take sosai da sosai tana jin zuciyarta kaman zata fado. Yanayin muryarshi a wakar karshe tasan ko ba kula yake ba yana jin ciwo fiye da wanda ita take ji. Sam bataji sallamar prince ishaq ba. Dan wayar ma tana gefe ta cire earphone din ta hada kanta da gwiwa tana kuka. * Ya dawo baiga kowa a falon kasa ba. Gidan yayi wani shiru. Zuciyar shi ta bashi shawara yaje ya duba husna. Ko ba komai sun zama abokai. Koda kuwa na iya zaman Nas ne. Ya fison yai komai yanda ya kamata. Ya kwankwasa yaji shiru ya tura hadi da sallama. Ganinta yai kan gado ta dunkule jikinta. Daga inda yake tsaye yana jin saukar ajiyar zuciyarta. Karasawa yai kan gadon ya dafa mata kafada. Cikin taushin murya yace. “Husna” * Sam bataji shigowar shi ba. Ko kamshin shi bata ji ba yau sai dai dumin hannun shi kan kafadarta. Da yanayin yanda yaja sunanta da halin da take ciki bai hanata jin wani iri ba. Dagowa tai ta kalle shi fuskarta cike da hawaye. Idanuwanta sun canza launi saboda kukan datai. Wata irin kewar huddy ta doki zuciyarsa. Ya danne abinda yakeji ba yanzun banne lokaci. Batare da tunanin komai ba yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta yana fadin. “Menene? Are you ok?” Hannun shi tai kokarin turewa ta a sake fashewa da wani irin kuka. Ta rasa yanda akai ganin shi ya kara karyar mata da zuciya. Gyara zama yai sosai kan gado ya riketa a jikin shi yana fadin. “Shhh husna. Komai zaiyi dai dai. Koma menene it will be alright” Baison kukan mace. Yanayin kukan ta ya dagula mishi lissafi. Husna kam duk wani abu da take ji ne yale fita ta hawayenta. Jitai gaba daya ta wani gaji. Ta zame daga kirjin shi. Gaba daya fuskarta kamshin shi take yi. Kallonta yake. Hannu tasa ta goge fuskarta. Ta kalli kirjinshi gaba daya ta jika masa riga da hawaye ne da wanne tsiya. Duk powder dinta ta goge tas a jiki harda jagirar ma. Kasancewar kayan farare. Ta zaro idanuwa. Muryarta a dishe sosai saboda kukan datai tace. “Dan Allah kayi hakuri. Duk na bata maka kaya” Kallon kirjin shi yai. Ya wani bata fuska da taga ya kara masa kyau yace. “Eww. Gross” Kaman zata sake fashewa da kuka tace. “I am sorry please” Da sauri yace. “Wasa nake fa. Enough, do you want to talk about it? I mean nasan ba hurumina bane. A matsayin aboki” Kai ta girgiza masa alamar aa. Ya sauke wani numfashi. Kukanta kadai ya sa mishi ciwon kai. Ganin shirun yai yawa. Yasa shi fadin. “Kinci abinci?” Ta girgiza masa kai. Ya soma gajiya da amsa masa magana da kai da take yi. Baya so sam.1 Ya share ne yau dan yanayin da take ciki. Mikewa yai sannan yace. “Tam barin watsa ruwa. Ki tashi kema. Kiyi wanka and no more kuka zan dawo ok?” Yanda yai mata maganar cikin umarni zaka rantse da yarinyar da bata fi shekara uku zuwa hudu yake. Karasawa yai daf da ita sannan yadan tsugunno dan ya dai-dai ta fuskar shi da tata. Cikin idanuwa ya kalle ta yace. “Da gaske nake fa. Banda wani sabon kuka zakiyi ciwon kai” Dakyar tace. “Bazan yi ba” Ya furta “Good” Ya fita yana ja mata kofar. Gaba daya ya kara saukar mata da gajiya. Hatta zuciyarta tagaji da aikin tunani. Dakyar ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *