WATA FUSKA CHAPTER 11

WATA FUSKA CHAPTER 11

  A hankali ya soma laluben inda ze qarajin kukan amma shiru be jiyo komai ba, yayi bincikensa sosai amma ba abinda ya gani a kitchen d’in juyawa yayi da zummar komawa d’akin har yakai k’ofar yajiyo k’arar jinjirai da k’arfin Gaske sekace wacce aka tsikara da sauri ya juyo ya kalli k’ofar store d’in kukan taci gaba dayi bil haq da iya kacin k’arfinta tamkar wacce ake ciza dukda yake kana ciwo sautin kukanne alamar bakin a toshe yake da wani abin, da sauri ya juya zuwa store ya soma binciken shi besha wahalar neman taba sabida kukan dataketa k’arayi da sauri ya zaro ta a kwalin yana huci ya kuma haska kwalin da fitilar wayarshi cinnakune a saman zanin datake kai sunkai biyar warwareta daga cikin d’ankwalin datake yayi nanma wani cinnakan ne alamar shi yake cizon ta, riqeta yayi ya soma sosa wurin a hankali yana shhhhhh alamar tayi shiru cikeda tausayawa a kafad’arsa ya d’aurata ya soma sosa mata bayan a hankali be koma d’akin ba yafi 15 mns yana sosa mata wurin a hankali hartayi bacci juyawa da ita yayi d’akin dayabar Ummul ya shiga a hankali, tana zaune tana kuka me ban tausayi….rungume yarinyar yayi ajikinsa yana mata murmushi me k’ayatarwa dabema san yana yiba sosai ya k’urawa yarinyar ido baya ko k’iftawa ba k’aramun kamanni takeyi da late mahaifiyar saba, har acikin baccin yamutsa fuska takeyi alamar tanajin zafin cizon da cinnaka ya mata, har cikin ranshi yakejin wani azababben rad’ad’i akan cizon da cinnaka ya manna wa ‘yarsa….tunda yake a duniya be tab’a jin yana son wani abu ko mutum ko aljan sama dayanda yaji yanason wannan abar ta hannun shiba!!! Ko Ummul dayake so bata kai kwatankwacin san dayakewa wannan babyn ba, kallon ummul yayi yace “Ki Nutsu kimun bayani niba abinda zan miki, yaushe kika haihu naga yarinyar tayi kwar’i sumar kanta kurin ya nuna hakan” d’ago jajayen idanuwanta tayi tace “Watannin Nana khadeeja biyu kenan a duniya, bakwaini aka haifeta kamar yanda na fad’a maka, nafi sati ina b’oyonta akan ance kana raba iyaye da yaransu tunda take bata tab’a yin kuka ba idan na b’oyeta yau, na barwa Allah akan Nana nikam, tunda yake ubangiji ya bayyana maka ita cikin sauk’i shiyasan me yake nufi da Nana, ni bazance maka komai ba illa kurin kaji tsoron Allah mad’aukaki dukkanin abinda kakeyi yana kallonka” Wata iriyar zufa ce take tsatsafowa Ameenu babu wannan shirmen aranshi waishi ya mik’a ‘yarshi shi kenan kuma idan ya bayar baze k’ara ganintaba har abada gashi Alhj Baba ya sanar masa ana kaisu wasu garuruwanne masu kud’in dabasa haihuwa ne ke siyan yara da tsadar dayaga suna siya suna adopting nasu, dukda an sanar masa basa shan wahala ko kad’an amma seyaji a ranshi ko Nawa za’a bashi akan Nana baze iya bada itaba gashi Har Alhj Baba ya gama cinikin kome aka haifa mace ko Namiji kallonta yayi “Ummul Sunan Mamana kika baiwa wannan jinjirar? D’aga masa kanta tayi tace “Wannan shine sunan danaji kace zaka sakawa yarinya idan macece shine nacika maka burin ka” nisawa yayi yace cikin takaici “Da hannuna nake siyar da yarana ummul, bakuma siyar dasu nake dan komai ba sedan ina ganin ina tara uwar dukiya akansu, an sanar mun turawa ke siyan yaran musamman wanda basa haihuwa suna adopting d’insu suna basu gatan daya dace dasu…..yarana sunkai goma sha biyar dana zubar na bada kyauta wasu duk iyayensu aure mukayi wasu matan banza ne wasu hayarsu nakeyi, yanzu dakikace naji tsoron Allah wani tunani yazomun shin idan anje dasu qasashen turwa wane addini ake koyar dasu? Wa danne irin sunaye ake kiransu dashi shin anya zanga annabi kuwa, wani zubin idan akamun haihuwa banako kallon jinjirayrn nake badasu amma akan Nana Khadeeja bazan iyaba ummul, bazan kara siyar da yarana akan wannan abin duniyar ba inada dukiyar dazan rayu acikinta har abada inada gidajen mai iri iri inada kampanin silipas bazan iya qayyademiki adadin abubuwan dana mallaka ba, na dad’e ina tunain cewan had’uwana dake alkhairi ne na jima ina miki kallon ke alherice ashe hakan, Allah na tuba ka yafemun laifuffukana na baya” Dubansa ya miyar zuwaga ummul kan yace “Alhj Baba mutum ne me tsananin san abun duniya, shine ya d’aurani akan wannan mummunan turbar ta banza, yanzu nasan ze iyayin komai akan zan hanashi wannan jinjirar, koda yake dama bayason wanda suka sha nonon uwarsu bare ma wanan watanninta biyu” kallonshi tayi “Sekace abun tsafi Ameen, anya kuwa wasu ke siyan yaran nan kodai tsafi ake dasu?” Kallonta yayi amma beyi magana ba yana nazarin kalamanta ne kurun secen yace “Tunda nake mik’a jinjiraye ban tab’a sanin me akeyi dasuba face abinda na gaya miki Allah ne shaidana, amma kuma ummul maganar kin nan ta zomun da wani tunani, bana mantawa akwai wani yaronmu da yarinyarshi ta haihu da kwana biyu daya kawo jaririn mayar masa akayi akan yasha nonon uwar sa baida wani amfani….wani zubin nikanyi mamakin dalilin sato matan da ake masu tsohon ciki idan sun haihu a kaisu kan hanya a wurgar a dauke jinjirayen duk akan abu d’aya waishi neman duniya kuma bama wannan ba idan suna son jinjiraye babu a k’asarsune? Wlhy ummul nikan jima ina nazqrin abubuwan nan amma yaya zanyi da Alhaj Baba shine gatana banida kowa” shiru sukayi dukkansu suna kallon juna k’arar wayarshi ne ya miyar dasu duniyar dasuke a tare suka kalli screen na wayar *ALHJI BABA* shine rubuce ajikin fuskar wayar…miyarda duban su sukayi akan fuskokin juna bayan da kuran ya yanke lokaci d’aya zuciyoyin dukansu suna lugud’e!!! Murya na rawa yace “Mesa Yake duk wanda ke qoqarin guduwa daganan gidan seyace baya ganin gabansa bare bayan sa, abubuwa da dama dasuka shafi nan gidan ban saniba ummul!!! Wannan tsafin da kika ambata ya rikirkitani koda kuma kinzo da waya ke naki baze shigaba amma ni zan samu wanda nakeso kuma zasu krani, anya babu zancrn ki kuwa anya babu tsafin to amma tayaya? Ni komai na Alhj Baba nasani ki taimakeni ummul ina cikin tsananin rud’u wlhy” shiru sukayi sanda kiran ya k’ara shigowa se gumi yake had’awa tamkar wanda ya had’iyi kunama”…… ************** Koda wasa Nancy bata zata Maheer zezo mata da wannan zancen ba!! Bata burin aurar sa, tunani ya mata waya wannan ya bata damar kiran Mahal ta tbayeshi gameda labarin soyayyar sa akan ta tada, yana amince mata tace yaje yawa Baba iro magana a shirya komai, indai ze aureta karatunta ma zata ajiye, dad’i ya kamashi yace da ita zema barta ta dawo kuma yamata alqawarin farin ciki na har abada….. *Bayan sati d’aya* Maheer yana kwance a parlor wayan Daddh ya shigo masa, d’agawa yayi yana murmushi suka gaisa yace dashi “K’anwar ka tayi muji fa, malam iro ya kirani a waya yana neman izini kozan bada ita, nace duk yanda nace nikam nace a tsarina seta kammala karatunta amma zamu iya tsyar dashi matsayin manemin auren nata” gyaran zaman shi yayi sabida harya dawo zaune yace “Abba wacce daga ciki?” “Kanajin nace malam iro ai kasan Hafsat nake magana ko!!! ” k’irjinsa me yayi wani irin mugun dokawa da tunda yake a ranshi be tab’a jin fad’uwar gaba irin wannan ba, lokaci d’aya ya tsarke ya soma tari sosai “Sannu idan ya fad’a maka ka kirani nanda awanni uku zan shiga meeting yanzu……. Tunda Maheer yake be tab’a shiga wannan tashin hankalin ba, ya jima bega tashin hankali ba irin wannan, se yanzu ya yarjewa kanshi yanawa Hafsat *son so* wanda be tab’a yiwa wani ko wataba yana cikin tashin hankali, yaya Hafsat zata masa haka?? Anya tayi masa adalci kuwa tasan me yakeji kuwa?… Gumice ke tsatsafowa su ummul tako ina, yasan halin Alhj Baba yasan meze iya akan wannan jinjirar yasani zega laifin sane amma bari ya gwada d’aukar wayar tasa,jikinsa ba k’wari ya d’auki wayar ya danna lambar ya kara a kunne+ “BAKA KUSA DA WAYAR NE?” aka buk’aci sani daga d’ayan bangaren…. “Ea Baba bana kusa nashiga bayi gudawa nake tunda nazo gidan, akwai matsala fa Baba” Gyaran zaman hular kansa yayi “Mecece damuwar?” Ya tambaya cikin isa “Baba wai bakwaini ta haifa ashe tun bayan watanni biyu, kaga kuma ni banzoba gashi yarinya har tayi k’wari a hannunta” Tsaki yaja kan yace “Wannan wane irin mugun sakarcine? Bakwaini kuma? kana da labarin cewan na karbi fiyeda rabin kudin wannan jinjiran kuma ka sani ni bana asara sedai idan kai zakayi, kuma a kawomun Uwar zan had’ata da shap shooter ya mata wani cikin shap shap ta haihu a ta maye mana gurbin asarar mu sannan kuma ita jinjirar yaya zakayi da ita? Karka zomun da ita nan kaji na gaya maka wlhy” Muryanshi na rawa yace ze kawotan, kallon Ummul yayi Baze tab’a iya bari wani namiji ya rab’i matar saba, wato shikenan Alhj Baba sabida ya renesa seya hanashi walwala yana nufin iyalansa ma baze bari suyi k’wai ba? Mik’ewa yayi yace “Tashi muje Ummul tashi mubar gidan nan akwai matsala, bazan k’ara cutar miki da rayuwarki ba, bazan yarda wani ya rab’eki da sunan zinaba wai dan ze miki wani cikin, gwandamun in mutu da inganki a wannan halin Alhj Baba bashida imani ko kad’an” koda Bata fahimci kala mansa ba amma ta gano da matsala Naja ma agaba suka sanyata sunsha mamakin gate a wangale suka fad’a motar kuma acikin qalilan lokaci dabefi 50 mns ba suka hau titi da kyau, suna shiga gari Mamaki ya kama ummul ganin ko wane sighn boad zata gani setaga an rubuta masa jos nigeria wato jos ma suke kenan? Lallai ma Ameen namiji munafuki, kai tsaye kano suma nufa acen ya nemi gidan ajiyesu wanda Alhj Baba bemasan yana dashi a kano ba…. Bashida wani wanda ze gayawa damuwarsa amma mutumin farko daya fad’o masa shine Maheer….sun kwana biyu basuyi wayaba kasancewar ya dena amfani da layin da Maheer ya sanshi dashi, lalubar layin yayi ya saka shi ya dannawa Number d’in Maheer kira, yana ganin tak’i shiga ya gano yana london wata iriyar zufa ce ta keto masa, lalubar lambar maheer ta london yayi yae sa’a kuwa ya samu, a wannan lokacin Maheer yana cikin tsananin damuwa akan Nancy, koda yaga Ameen ne yayi mamaki, yafi watanni yana kiram wayansa baya tafiya sam!! Da sallamar sa ya d’aga kiran suka gaisa yace dashi “Kwana biyu Ameenu bana samun wayarka yaya wurin su ummul hope dai lapiya?” Susa kanshi yayi cikeda jin nauyi kan yace “Abubuwa da dama sun faru abokina, dogon labari ne dabazan iya bakashi ba yanzu, naso ace kana gari ne mu hadu gani gaka amma yanzu yaushe zaka dawo?” “Eeeh to akwai abinda zanzo yi Nigeria nanda 3 weeks idan beyi nisa ba, semu hadu daga na dawo idan Allah yasa muna cikin masu numfashi a lokacin” Nisawa yayi “Babu damuwa Maheer amma dai ka sani ina tsananin buk’atarka a yanxu hakan, idan da hali karka wuce sati ukun da kace, bayan wannan idan akwai gidan dakakeda shi a nan kano ina son aron key zanje da ummul gidan akwai damuwa fa” Shiru kan yace “Akwai gidaje ma abokina, zanwa kamala waya seka nemeshi ko, naga kaman hakan yafi kaima zan bashi wayarka” “E hakan ma yayi amma dai a bani motoci guda biyu suma, zan bashi tawa ya ajiyeta a gidan ku kan ka dawo” Maheer be wani tsaurara tambayoyi ba, ya kawai masa fatan Alkhairi….har zasuyi sallama yace STORY CONTINUES BELOW “Kanada labarin en uwan ummul kuwa?” Yana murmushi yace “Ea ai yanzu haka Hafsat tana hannun mu, mun sakata skul anan london, tana yawan damuna akan zancen ummul” “Ka gaya mata ummul tana nan cikin k’oshin lapiya harta haifa mata ‘ya sunan ta Nana khadeeja amma ina kiranta da suna mamina” murna ya masa kan nan sukayi sallama…… ************* Yau dai Islam tana school wannan ne ya baiwa Nancy damar fitowa parlor domin yin kallo sabida da a farko sam sam tadena fitowa sabida wulaqancin da ake mata, wayanta take daddanawa tana chat da Mahal lokaci zuwa lokaci takan saki murmushi zuwa wannan lokacin zuciyarta ta soma shiryawa da Mahal ta aminta dashi matuk’a….Maheer se kallon yanayinta yake wani irin burgeshi takeyi aduk takun dazata yi a wurin shi….zama yayi kusa da ita ta mik’e zaune daga kishin giden da take “Sannu yaa Maheer barka da zuwa” wani irin zuba mata manya manyan idanuwanshi yayi baya ko k’iftawa,ita d’inma shi take kallo basako k’iftawa acikin idansa ta hango k’auna zallah tata, ta hango son fiye da kai, ta hango tausayinta, ta hango d’igon k’aunar ta a had’e da wata zaiba dake cikin k’wayar idansa!! Ta hango Son so acikin idansa, fuskarsa ta bayyanar da yanayin yanda yake matuk’ar k’aunarta ya marairace mata fuskarsa me kyau har hakan yana shirin yin tasiri azuciyar ta kawar da idanta tayi daga dubansa tana yunk’urin mik’ewa ya rik’e hannunta gagam juyowa tayi suka k’ara yin ido biyu dashi ga mamakinta k’walla ta gani a idanshi har yana shirin sauka, lokaci d’aya ta jirkito gaba d’aya zuwaga dubansa tana me wara idanta…….”Bakada lapiya ne yaa Maheer na shiga uku na” muryanshi har rwa yake yace “Kece hafsat, dan Allah ki tausayamun wlhy bazan rayuba idan baki a tawa rayuwar….macewa zanyi matuk’ar kikace zakimun hakan, Naji hukuncin dakika yanke dukdan k’iyayyar dakikemun, na yarda da kiyita k’ina amma ki rayu dani ki taimaki maraicina ki aureni kinji” Kallon ta ta miyar jikin k’ofa ta warce hannunta daga nasa tace “Yaa Maeer kayi hak’uri wlhy bazan iya aurar kaba har abada!! Banason koda rab’ar ka inayi da inada wani iko da nabar muku nan gidan kaida islam d’inka!!! Da inada ikon dena sanyaku biyun nan a ido dana dena, ina rok’on ka yanda kaga nabarka kaima ka barni, ka cireni a ranka kaje cen ku qarata kaida islam, wlhy yaa Maheer Baso a raina, in dai aure ka, ina maka kallon Babban yayana me girman daraja da k’ima ina sonka fiyeda tunanin me tunani a bangaren zamtowarka yaya na, acikin jinina kake yawo yanda kasan dan uwa nayi acikin jinin d’an uwansa, a numfashina kaine nake ja nake fesarwa amma na matsayinka na yaya na, a idonane kurun kake kala biyu wanda hakan bazema maka wani tasiri ba ko kadan!!!! Ka fitar dani a ranta kamun kallon danake maka dan bazan aureka ba”…. Tana kammala fad’ar hakan ta mike ” ummul ta haifi Nana khadeeja inji Ameenu daya mun waya d’azu” da sauri ta dawo ya mata bayanin komai sannan suka rabu zuciyoyin su babu dadi sam… ************** *Bayan sati biyu* Shirin tafiya America yake gun mahaifinsa ze had’ashi da wasu muhimman abubuwa nasa tukunna su wuce Nigeria tare zancen auren Hafsat…tamkar me wani mugun ciwo haka Maheer ya dawo duk ya yamutse sosai kuma…..yana dira tun a airport Abba ya diririce ganin Maheer a rud’e ya yamutse a daddafe sukayi kwana biyar suka juya Nigeria…..kai tsaye gidan su Hafsat suka dira akan maganar auren kai tsaye Maheer agaban Abban shi ya yanki tikitin rashin kunyar shigar da Buk’atarsa tason auren hafsa….mahaifinsa ya nuna rashin dacewar neman aure cikin aure, amma Baba iro ya zak’alk’ale yace sam dama be baiwa Mahal Hafsat Ba be kuma ce dasu komai ba illa su bari se marik’anta sunzo yanzu kuwa tunda sunzo zece dasu sun baiwa wani, Babu yanda Abba beso a nemi izinin yarinyar a tuntub’eta aji ra’ayin taba, tunda ita ta kawo wannan tace tanaso amma k’ememe Baba iro harda kukan munafurci daga k’arshe ma kafewa yayi akan lallai a d’aura auren su yanzu tunda ba wani abin bane kar wata maganar ta k’ara tasowa….. Da Abba da umma ma’auratane masu tsananin girmama junansu…komai zasuyi sesun nemi sha’awar juna anan take y koma mota ya mata waya akan abin da ke wakana, amma ita seta Rok’a akan abari se juma’a idan an sakko masallaci tunda yake yau laraba, haka suka bashi hakuri suka koma kano….. Sosai Abban Maheer suka rok’eshi akan ya janye amma ya kafe su a ganinsu baze iya da mata biyu ba musamman kasancewar su k’awaye kuma duka yara shidai ya kafe kuma ya hana a kira Hafsat akan bazata amintaba sabida kawaicin islam…..mahaifinsa ya kafe akan lallai seya kirata a k’alla ta sani mahaifiyarshi batason d’anta ya gagara samun me yakeso amma ina seda Abba ya kira hafsat, cikin girmamawa suka gaisa yace “Hafsat dama na kirane in shaida miki ranar juma’a zan d’aura aurenki da yayanki Maheer, kasancewar hakanne daidai ina fatan a matsayina na uba zakimun biyayya” Batare datasan me tace ba ta amsa da “Duk hukuncin daka yanke akaina daidai ne abba, fatana zab’in iyaye ya zamto Alkhairi agareni” sosai ya saka mata albarka ya k’ara dacewar “Banason koda su safiyya su sani ko bayan daurin auren se sanda zan baku umarni, sabida haka aci gaba da zama matsayin da ake kai amma aure zan daura idan inacikin masu numfashi jibi juma’a” Tana k’wallah tace “Inshaa Allahu Abba zan kiyaye nagode Allah ya k’ara girma” yaji dad’in adu’arta ya dinga mata godiya seda taji nauyin sama!!!!!! Sake wayarta tayi ta zube a wurin tana sharb’ar uban kakan kuka, wlhy batason auren Maheer, mutumin dayafi son islam akan kansa ma agabansa islam din ke mata cin kashi bazeyi magana, ashe ko yanzu seta duka, wato yayi tafiyane sabida yasan iyayenta sunada kwadayi yayi amfani da kargin ikon dukiyarsa ya tursasa aka bashi ita ko, bayan ga zabin ta…koda ta kira Baba irk tasha zagi sosai bana wasa ba …..yace er b’akin cikice bataso yaci gaba kuma idan ta kuskura tace batason auren Allah ya isa kuma Allah ya tsine mata albarka….badan tasoba ta hakura ta kira maman ta itama kai tsaye ta goyi bayan su baba iro kuka kam ta shashi…. *Ranar juma’a* A babban masallacin juma’a dake jihar sokoto aka d’aura auren Maheer da Hafsat bayan idarda sallan juma’a Bazamu iya fad’ar d’umbin al’ummar dasuka shaida auren ba….. Tun bayan da aka d’aura auren yake cikin fad’uwar gaba, ya hango iyakar gaskiyar Nancy na bazata auresaba kamar yanda ta fad’a!!!!! Ya gagara kiranta, ga farin ciki a qasan ranshi ga kuma tashin hankali a ckin ran nasa, ko yaya zata kallesa? …….Hafsat kuwa tasha kuka su sophie sunyi sunyi sedai tace dasu zazzab’i takeji suka dinga mata sannu…. Alhj Baba ya shiga rud’u da tashin hankali me yawan gaske, neman Ameenu yake hankalinsa a tashe, duk garuruwan dayake tsammanin ganinsa yaje amma ba labarin sa….a gaba ya sanya Babban yaron Ameenu da izgilanchi iri iri dakuma treatening nashi akan hallakar da iyayen sa…dolensa yakaishi gidan Ameenu na kano inda suka tarar baya nan, tsammanin Alhaj Baba zuwa yanzu shine Ameen yabar k’asar kwata kwata don haka ya kud’irta aranshi idan ma ya kamashi har ‘yar tashi ze yanka agabanshi besan haka bane dabe nuna masa ze karbi matar tasaba, kuma matarsa seya wulak’antata ya sanya dukkanin samarin dake masa aiki sun hauta agabansa, duk gatan daya masa ya d’aurasa akan hanyar samun kud’i zema iya cewa gabaki d’aya yafishi samun kud’in gefen wannan harkar yaya ze masa haka?! Duk wani hanyar daze sanya ya ganeshi ya gujeta danko ko kud’ad’e ya dena cirewa ta banking sa to a ina ze samu kud’i? Hankalin Alhj Baba fa ba karamun tashi yayi ba……+ ******************* Ameenu kuwa dabara ya masa, sabida yasan yanda sun tab’a samun yaron dayak’i bada yarinyar sa da matarsa ta hanyar inda yacire kud’ad’e banki ya gano shi, wannan ya sanya yawa abokin shi dasuke huld’ar fata waya wanda dama akwai kud’insa a hannunsa ya tura masa 3 million d’insa acikin acc d’in Ummul dako ATM nata batasan inda yake ba seda yasha wahala ma tukunna ya samu aka mata ATM d’in yake zarar kud’ad’en suna lalurarsu har yanka yawa Nana khadeejah aketa ji da iya, ankuma kaisu asibiti itada uwarta an duba lafiyar su da komai Alhamdulillah….. *************** Tun faruwar wannan lamarin Nancy bata cikin nutsuwar ta, ta rasa dalilinta najin hakan game da Maheer, bazatace ta tsaneshi ba amma sam batajin sansa aranta kamar da, kodan tana jin tsananin takaicin islam ne yasa ko meye dalilin ta oho? Tasani ada ta bautawa san Maheer takuma sha d’awainiyar begenshi amma zuwa yanzu tunani take kaman zallan burgewa ne kawai baso a ranta, ta misibar shak’a da wannan izgilancin daya mata, shime dala kenan ko? Masu kud’i kenan ko? An had’u da kwad’ayayyun iyayenta anje basu abun duniya sun bada aurenta batare da izinin taba sam! Bata masan anayiba, banda Abba ma daya nemi amincewarta Baba iro ko gaya mata beyi ba sanda ta kirashi ma seya nemi tsinemata akan hakk’inta….haka mamanta ma data kirata seta ce ta amince mesa basu ko duba kawaici ba? Kodan islam ai sace noo ko? Wannan auren ta kudiri niyyan wahalar da Maheer akanshi kuma ze ganene….. *************** Sosai suka zanta da Ameenu gameda abubuwan dayake aikatawa da wanda ke gudana a yanzu, Ran Maheer ya b’aci da shashamcin Ameen….ze dinga rayuwa kenan acikin tsoro da b’oyo se kace d’an fashi, sun jima suna meman mafita, basuda dabarar dayafi ya kwashe ‘en kud’ad’ensa ya koma wata k’asar xuwa wani lokaci shida iyalansa wannan kuwa ze d’auki lokaci dan haka gwara su zauna da shiri….Ameenu ya sanya kamala harkan visa dinsu da komai daya shafi barin k’asar. ************** London Koda Jirgin su maheer ya dira a london seda k’irjin sa ya doka yana tunanin yanda ze kalli Hafsat, yana tunanin abubuwa da yawa masu dama….haka ya isa gidan jikin sa ba k’wari ko kad’an da sallamar sa ya shiga cikin parlor d’in inda ya tarar sophie ce zaune tare da Nancy suna kallo sunashan Banana smoothie…a tare suka mik’a suka gayar dashi inda Sophie ta k’arb’i jakar hannunsa Nancy kuma ta k’arbi wacce ya ciro daga bayan shi adaidai lokacin da Islam ke dannowa parlor d’in kai, da sauri har tana had’awa da gudu tazo ta sanya hannu ta tureta ta karb’e jakar hannun shi “Kajimun yarinya da iskanci fa, kina agola dan er masu gida ta karb’i jakar hannun yayanta kekuma asuwa da wani salon karuwan cin zakizo kice sekin karb’a” kalaman na islam ba k’aramun dakarwa Hafsat k’irji sukayi ba gashi turin data mata seda ta fad’i…k’ura mata ido Hafsat tayi ta kasa furta komai yayinda sophie iyayen fitina ta gagara hak’uri tace cikeda tsiwa STORY CONTINUES BELOW “Haba Anty Islam, wannan wane irin mugun furucine kalmar karuwanci ai batada dad’in ji ko karuwar gaske bataso ace mata karuwa bare kuma kowa yasan waye karuwa waye ta k’warai anan, agolanci kuma mu a iya sanin mu Hafsat Abba shine ubanta abinda ya tara mu ya gaya mana kenan cewar er uwarmu ce kuma ershi ce ta jini, kin kama kin matsawa yarinya to kece agola danmu bece damu ke ershi bace kuma kece Tsohuwar karuwa ai kowa ma ya sani” Dire mata lafiyayyen mari Maheer yayi “Ke kinada hankali kuwa? Kina hauka ne? Zaki zauna dan babu cikakken ilmi akanki kina gayawa matana wai itace karuwa” Dafe wurin tayi tana kuka “To yaa Mahii kamata magana mana itama ai tana wuce gona da iri,Ai Abba yace Hafsat k’anwarkace mesa zatace mata karuwa kaki cewa komai kumama har tana tureta ta fad’i Allah ya gank daddy zan gayawa wlhy” ya gaza kalmar daze furta seya kalli islam yace “Karna k’arajin kin matsawa yarinyar nan Salaha, banaso meta miki? Yaya zaki tureta dan zata karb’i jaka a hannuna? Itama ta isa duk abinda su sophie zasumin ita ma ta isa tamun, kinsani batun yauba nasha zaunar dake a d’aki ina miki magana akan abubuwan dakike mata bakyajin magana ne yanzu kinga su gan suke kamar bana tsawatar miki, ki sani wannan karon bazan lamunta ba wlhy, karna k’araji kin tsauwalawa yarinyar mutane sabida ba zamanki takeyi a nan garin ba, matsayin gidan ubanta ne anan banine na kawota nanba me gidan ne ya kawota sannan idan daddy yaji kina mata haka zaku b’ata ne sosai dashi, lastly kalmar karuwanci karna k’ara jinta acikin gidan nan daga yau, baze yiyu ki kalli yarinya acikin gidan suba ki jefeta da muggan kalamai ba, a iya zamana dake da yaran nan bana tunanin sun tab’a yi miki rashin kunya amma yanzu kinjwa kanki sabida haka ki kiyaye…..juyawa tayi tanata kuka sekace wata jinjira ya rik’o hannun Sophie ” Am so sorry sis kinji bazan kara ba” murmushi tamasa taji sanyi daya wanke islam “Yaa Maheer ka isa kamun fiyeda haka, ba komai kayi hakuri abinda nawa Adda islam” rungumeta yayi sannan ya mik’awa Nancy hannunshi wacce tun faruwar abun bata mik’eba daga kishingidar datayi ta fadi, batayi musuba ta mika nata ya mik’ar da ita, kai tsaye cikin faffad’an k’irjinsa ya mannata yace “Am so sorry sister kinji, bazata k’ara ba, zan k’ara tsawatar mata” wani sanyine ya ziyarci hafsat, bazata fad’i iyakar adadin dad’in datajiba daya rungumeta kwantar da kanta tayi saman k’irjinsa haka kurun taji tana buk’atar wadataccen lokaci asaman k’irjin masa, sun kusa 1mn a haka seda Sophie ta gaji da tsayuwa tace “yaa Mahii nakai wannan kayan d’akin ku” sakinshi Nancy tayi tana mejin kunyar sa da sophie gaba daya..karbar kayan yae “Noo bari na k’arisa dasu ciki karki damu” jan hannun Nancy tayi sukai cikin d’akin su “Ke Nan kinga yanda kukai matching da yaa Maheer sanda yae hugging naki, wlhy kun had’u inama zan iya gayamai ince dan Allah ka aureta” dariya sukayi ta d’aka mata duka “Ba wani matching kema ai yayi hugging naki ko? Nima hakanne ko kinaso tun yanzu ki k’aryata kanki da kike cewa ni daku uwarmu d’aya ubanmu d’aya” rungumeta sophie tayi “Ki gama zagayenki yaa Maheer seya aureki,ni danake nice ai ko second d’aya beyi ba ya sakeni kuma beji komai b, amma ke har idanshi ya canja dan yana sankine na sani” Earp ta zare ta tsala mata take suka fara zagaye suna gudu akan seta daketa, nanma maheer da islam sunzo parlor yanata faman rarrashi sabida tana fushi shisa ma ta fito tabaro masa dakin, kallon mamaki suke musu har suka juya zuwa dakin da gudunsa murmushine ya sub’uce masa ganin sunata afka wawta sekace yara….. ******************* Da kanshi yaje ya d’akkota school kai tsaye wani hotel ya wuce da ita itadai batace dashi cikanka ba, bata kuma musa masaba da suka shiga cikin hotel room din daya buk’ata, zama yayi itama ta zauna ta had’e rai sosai da sosai batako murmushi…yafi minti uku beyi magana ba kan daga bisani yace “Hafsat inaso ki nutsu kiji abinda zan gaya miki, da kuma dalilina na kawoki nan” kallon shi tayi amma batayi magana ba yaci gaba “Nasani ban kyauta miki ba, nakuma sani kinada daman zaman mijin dakikeso, amma na tauye miki hakk’in ki dan Allah kiyi hakuri, ki d’auki wannan a matsayin k’addarar mu dama cen ke anrubuta matata ce” Wani kallo ta wurga masa kan tace “Yaa Maheer kaifa me kud’ine koka manta? Me kake tunani daya kaika bani hakuri, yanda ka sanya kud’inka ka siyo igiyoyin aurena haka nakeso kayi amfani da kud’inka da isarka ka siyo hakuri nan dakake bani bawai kayi amfani da bakin ka ba” kallonta yayi ya gagara gare inda kalamanta suka dosa ko kadan “Me kalamanki suke nufi Hafsat?” K’ank’ance idanuwanta tayi “Kai yayane agareni yaa Maheer sabida haka ba rashin kunya a tsakanina dakai, kai mijine agareni yaa maheer sabida haka banida wanda zan girmama sama dakai a duk fad’in duniyar nan, abu d’aya zan sanar maka shine yanda ka sanya kud’i ka siya igiyoyin aurena, to kud’inka baze iya siya maka soyayya naba, da gangar jikina da ruhina bazan mallaka maka ba koda zaka bani dukiya malali gashi tinkiya, kadena tunanin rab’ata yanzu se sanda Abba yayi umarni da asan da zaman aurenmu…..daga ranar daya bada umarnin namaka alk’awarin zan mallaka maka jikina sabida girman Abba, ruhina kuwa baya tare dakai ko kad’an yaa Maheer ka sani kuma idan matarka tana mun izgilanci kana k’yalewa zan mayar da abunne akan kai sabida ya dace tasan meye kalmar halacci” Nisawa yayi zuwa yanzu ya fahimci kalamanta, wato gani take tamkar kud’i yaje ya nunawa iyayenta suka bashi aurenta, in hakane bazata fahimce saba se zuwa gaba, ya gagara furta wata kalma dan kanta ta gaji da zaman ta mike “Ka.miyar dani gida yamma nayi” shi d’inma mik’ewa yayi suka bar wurin gaba daya…. ********* Tana bayansa suka shiga parlor d’in ranshi baya masa dad’i besan wane irin mahaukacin sone yakewa hafsat ba, yana matuk’ar san islam amma bekai haka ba, ko kad’an bayajin wannan zafin zuciyar idan yana tunano ta, bata tayar masa da wani abu dayakeji tun daga kan dan yatsansa har saman kansa duk sanda ya ganta……Islam ce zaune a parlor miyarda dubanta tayi zuwa garesu lokaci d’aya ta murtuk’e fuskar nan…hafsat ko kallon inda take batayiba ta nufi hanyar d’akinsu shi kuwa yayi wurin islam, da tulelen cikinta ta mik’e “Tsohuwar kilaki daga ina kika fito keda mijina?” Juyowa Hafsat tayi sannan ta dawo cikin parlor d’in gaba d’aya tazo daf da ita ta tsaya tace cikin d’acin murya “Da zanyi karuwanci islam kinsan da nayi tun sanda nake taka k’afana daga jami’a zuwa lowcost a k’asa….da zanyi karuwanci da islam da nayi shi tun sanda nake zuwa jami’a tun 7 na safe har shidan yamma batare danaci komai ba ko nasha ko ruwa ba, da zanyi karuwanci islam damayishi sanda nake rasa Naira goma na siyan handout sena zauna da takarda da biro na ari na wasu na kwafa, da zanyi karuwanci islam da nayishi tun sanda nake rayuwar hostel tare da lalatattu irin ku, da zanyi karuwanci islam wlhy danayishi tun sanda kike neman d’aurani a hanyar yinshi, sanda kike hawan jirgi kina zaga duniya, dq zanyi karuwanci dana biyewa Babbar k’awata aminiyata dakowa ya sanni da ita mun tambad’e a tare….Ashe talauci be saka naki karuwanci ba se wadata islam? Ashe wuya da a zaba da rashin sanin madafa be sanyani nayi karuwanci ba se yanzu da Allah ya ‘yantani daga tsananin bauta ya rabani da ita? Ashe tursasasawa be sanyani nayi karuwanci ba se yanzu danake kwanciya in tashi a inda naso babu me tursasamun? Kije makaranta ki koyo ilmin zama da mutane bakisan meye hakk’in d’an adam ba, ke d’in nan bakida mijin dazan nema muyi harkar banza yaa Maheer kuma yaya nane, ko bayan wannan ma nan zuwa gaba kad’an zaki gane cewar inada matsayi har guda biyu awurin shi wanda d’aya kurin kika mallaka…wlhh summa tallahi kika k’ara alak’antani da wannan kalmar sena nuna miki acikin karuwan ma akwai na gida, kuma sekinyi kuka da idanuwan ki wlhy, keda kanki kin sani sam ni Hafsat bana d’aukan raini inadai da hak’uri amma raini kam bana d’aukar shi ko nan dacen” Kuka islam ta saka ta juya gun maheer dayake tsaye tamkar wani statue yana kallon su tace “Honey kanajifa cin mutuncin da wannan banzar kemun amma ka k’yaleta” k’ara murtuk’e fuska yayi “Matsalar baki kenan, kasan me zaka fad’a abinda za’a miyar maka ne baka sani ba, ban miki maganr dena gaya mata wannan kalmar ba? Inaso ma na sani shin yanzu mi kike zargi ko ita?” Shiru babu amsa juyawa yayi zuwa d’akinsu itama Hafsat ta juya aranta tace “wlhy sekunci ubanku, na dena barin kina wulakantani mijin nan ina nima inada hakki akanshi? Wlhy sekinsha azaba awurina akan yaa Maheer muzuba mu gani kuma!!!!!!!!!!!!!”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *