WATA MACE CHAPTER 1 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 1 BY SANA S MATAZU

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tun daga bakin ƙofar gidan ta ke jiyo muryarta cike da rauni, waƙa ce take rairawa murya a sarƙe. A haka ta ƙarasa shigowa gidan, mammaki ya kasheta ganin hawaye a idanun Labiba. Bata ƙara tabbatar da mamakinta ba sai da ƙamshi mai ni’ima ya sami masauki a massarafar shaƙar numfashinta. Jiki a sanyaye ta zauna idanunta cikin nata. daidai lokacin da ta ƙara ɗaukar wata waƙar,

“Zamantakewa ba ƙarya ne ba. Cin amanar soyayya, an rabani da me sona”

Jikin Amina ya ƙara sanyi, bata taɓa tunanin akwai ranar da zata ga nadama a idanun Labiba ba, bare kuma zubar hawaye. Lallai masu iya magana sun yi gaskiya, duniya juyi-juyi ce. Tunaninta ya katse lokacin da hannunwan Labiban suka sarƙafo nata hannuwan murya a raunane ta furta,

“Yaya Amina ke ma murnar ki ke yi? Kina cikin masu murna an min saki ɗai-ɗai har guda uku? Kodayake ba kowa ya cuceni ba sai yaya Khamisu da bai sakasu sun je sun daki Yusuf ba da bai sake ni ba. Kaicon rayuwata…”

Numfashinta ne ya soma yin sama da ƙasa, ta kai hannu ƙirjinta ta danne tana taune leɓɓanta na ƙasa. Kafin ta yi wani yunƙuri ta faɗi ƙasa yaraf! A hanzarce Amina ta kai mata ɗauki tana ƙwalla ƙara,

“Yaya Ade ku kawo agaji!”

Daidai lokacin wadda aka kira da Yaya Ade ta ƙaraso, tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi. Kai a ɗage ta kalleta,

“agajin me kuma zamu kawo Yaya Amina? Ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Ɗiyar boya ce fa take gudun auren jinin boya to mene ne a ciki dan ya sauta zata ɗaga mana hankula. Ba a auran ɗiyan boyan mu munka auri yayyunta? Ni kinga tahiyata ma gidan Yusufa naka zuwa ganin waga amarya tasa me karamci. Ance yau danginta sunka kawo gara daga Kano, gara mu hanzarta mu kwashi arziƙi kadda a ayi babu mu. Domin su arziƙinsu na gada ne ba taka haye ba, saudiyya ma zasu tafi aka ce sati me kamawa mahaifinta ya biya musu”

Wannan furucin shi ne ya ƙarasa tafiya da numfashin Labiba, cikin kanta take maimaita,

“Yusufa nawa? Aure? Saudiyya?”

***

Tsayin kwanakinta uku a kwance gado asibiti, bata san inda kanta yake ba. Duk lokacin da zata farka da sambatun kiran sunan Yusuf take farkawa. Allurar bacci kawai ake yi mata ta koma. Aranar kwana na huɗu mahaifiyarta ta zubda hawaye kamar babu gobe, masu ganin laifinta kansu sun soma jin tausayinta. Sai dai wasu ko kaɗan tausayinta be ɗarsu a ransu ba. Hasalima gani suke yi bata girbi abinda ta shuka ba.

A hankali take rarraba idanunta tana ƙarewa inda take kallo. Tabbas nan ɗin ɗakin jinya ne, bata yi mamaki ba duba da yanayin data riski kanta. Sannu ƴan ɗakin suke jeramata tana amsawa da kanta kamar ƙadangaruwa. Idanunta ta ji sun mata nauyi, gaɓɓanta na amsawa amma hakan be hanawa kunnuwanta sauraran abin da ke fitowa bakin Yayanta Khamis ba,

“Ni na rasa irin wannan masifa ta Labiba wallahi. Tun da an yi saki har guda uku ta haƙura mana yanzu saboda Allah wa gari ya waya. Ki duba fa, kwanata shida ita da gawa marabarsu numfashi. A ranar ma da abin ya faru ba dan zuwan Amina ba ƙila sai dai mu riski gawarta..”

Maganar ta katse sakammakon sallamar da aka doka, ɗaukacin mutane sun kai su goma sha biyar ne a ɗakin, abin ka da ƴar dangi. Labiba ƴar dangi ce gaba da baya. Amma kuma kash kafataninsu aka rasa me ƙumajin amsawa. Bakunnansu sunyi musu nauyi. Hannatu ce ta yi karaf ta amsa gudun aji kunya. Labiba kuwa tun sallamar ta shaida mammallakin muryar, domin ko giyar wake ta sha Yusuf da abin da ya mallaka daban suke a rayuwarta. Sai dai ta gaza buɗe idanunta waɗanda ta kulle tun lokacin da ta ji sallamarsa. Ƙwarai tana fargabar buɗewa ta ganshi da abin da zai ƙarasa tarwatsa duniyarta.

“Sannunku da zuwa”

Ƴan ɗakin suka soma faɗa, suna harhaɗa kalmomin kamar masu koyo. A kunyace Yusuf da amaryarsa suka bi su daki-daki suna kwasar gaisuwa. Ummi ta yi tsaye ƙiƙam idanunta na yawo a kan mahaifiyarta. Sai lokacin ƴan ɗakin suka farga da ita suka soma faɗin ta ƙaraso wajenta su gaisa. Ko gezau bata yi ba, tana dai kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. Aunty Shukura kamar yadda suke kiran amaryar mahaifinsu, wadda a yanzu suke jinta kamar ita ta haifesu, ta miƙe tare da riƙo hannun Ummi da Khalifa ƙaninta. Sai dai ko taku uku ba su yi ba ta ji yaran sun warce hannunsu. Ta juya cike da mammaki, sai ga hawaye na zuba a idanun Ummin, ta soma taku a hankali a hankali da baya tana girgiza kai. Daga bisani ta kwasa a guje tana furta,

“A’a Aunty!” Shi ma Khalifa da tsamin baki irin na wanda hausa bata gamsheshi ba ya juya yana faɗin,

“Bajani ba Anti zasu yi min irin dukkan da suka yi wa Abbanmu!”

Ya ƙarasa yana ajiye yatsansa manuni akan Khamis yayan mahaifiyarsa. Kunyar duniya ta luluɓe Khamis ganin ƙaramin yaro na alamtashi da mummunar ɗabi’a. Bai taɓa tsanar biyewa shirman ƙanwarsa da mahaifiyarsa irin yau ba. Garam! Ummi ta rufo ƙofar da ƙarfi, bayan ta ja hannun ƙaninta. Sautin ya yi daidai da bugawar zuciyar Labiba. Cak numfashinta ya yi fitar burgu. Gaba ɗaya ɗakin aka ɗauki salallami, cewar Ade matar Khamis.

“Labiba ta cuci kanta. Ɗiyanka! Ɗiyanka na cikinka na gudunka? Mi ake da wanga ɓataciyar rayuw..”

Kallon da Yaya Khamis ya wurga mata ne ya sanya bakinta mutuwa, sai lokacin hankalinsu ya koma kan gadon da take. Suka fahimci bata numfashi. Da hanzari Huraira ta kira likita, ya soma ƙoƙarin daidaita numfashinta. Nan da nan ta farfaɗo, sai dai ba abin da take yi sai surutai tilas aka yi mata allurar bacci tare da sallamar duk wanda ya ke cikin ɗakin. Jiki a sanyaye suka fito yuu! Zuwa harabar asibitin anan suka riski Shukura na lallashin Ummi. Yusuf kuma yana riƙe da Khalifa. Ana haka Amne ta ƙaraso da Hajja ƙarama. Ɗiyar Khamis. Tana ganinsa ta kama dariya tamkar mahaifinta ta kama zilo, duk da ƙarancin shekarunta. Hannu ya miƙa zai karɓeta, amma ƙiri-ƙiri Amne ta hanashi ita. Nan kuwa yarinyar ta tsanyare da kuka tana mimmiƙewa. Yaya Khamis ne ya karɓeta ya miƙa masa duk da mugun kallon da Amnensu take jefa masa. Ade kuwa sai ƙunshe dariya take yi. Yarinya na zuwa hannunsa ta yi tsit tana wangale baki.

Basu wani jima ba, saboda yadda wajan ya soma ɗinkewa da dangi, kuma kowa ya zo bakinsa baya shiru game da Yusuf da matarsa, karo na farko ya kafa TARIHI cikin zuri arsu. Dan haka Shukuran duk a takure take, ganin haka yasa  ya yi musu sallama tare da ajiye kayan dubiya har leda uku. Duk suka rakashi da idanu, basai an yi musu bayani ba shadar jikinsa kanta abar kallo ce. Yaya Ade ce ta janyo ledar tana bubbuɗewa bakinta na furta,

“Masha Allahu. Ka ga gidan karamci da sanin darajar ɗan Adam”

Mugun tsakin da Amne ta ja ya ankarar da ita kadda ta yi kwaɓa, domin ta ga Amnan ta kawota bakin maƙoshi. Da hanzari Khamis ya fita yana jin wani ɗaci a zuciyarsa. Tabbas shi ne sillar komai shi ya tarwatsa farin cikin ƙanwarsa da tuni tana tare da yaranta koda babu muradinta. Nadama da danasani suka shiga kai kawo a zuciyarsa. Komai ya soma dawo masa daki-daki kan rayuwar ƙanwartasa. Dole ne ya nema mata farin ciki ya ayyana hakan a ransa. Dole ya sake tuntuɓar Jawwad su daidaita ko ƙari ne ya yi masa kan miliyan gudar da ya gindaya masa.+

***

“Haba Jawwad mata fa na ke baka ka aura, amma kana jamin rai kamar wanda zai yi min abu kyauta! Ban da ma dai ƘADDARA ya za a yi na nufeka da wannan batun, bayan kana da TAMBARIN da baka cancanci zama da ita ba…”

“Dakata Khamis, wai dole sai na auri ƙanwarka? Ni gaskiya ba zan iya auren ɗiyar boya ba, kuma duk TAMBARIN da nake da shi ya kai nata ne? Ko ka manta duk abin da namiji ya yi adone? Ina ce kafatanin danginmu babu mace mafi ƙasƙanci kamarta a yanzu? Kodayake naga alamu ita data tashi gado, sai ta gado surukarta baƙin jini maimakon farin jini irin na mahaifiyarta. Kodayake babu haufi ai duk boya dai sunanta boya babu wani bambanci…”

“Dakata Jawwad kadda ka zagarmin mahaifiya, miliyan ɗayan da nace zan baka ce ta yi maka ƙaranci ga auren ɗiya kamar Labi..?”

Ƙarasowar Kabir wajen ne ya dakatar da su daga muhinmiyar maganar da suke yi, duk da shi Jawwad anasa ɓangaren ya so su ci gaba, koba komai zai suluɓe daga auren da ake son maƙala masa amma Khamis ɗin ya dinga togewa. Tilas ya haƙura, amma kuma yana barin wajen ya soma ƙyanƙyasawa Kabir ɗin kanun zancen. Kwaliya ta biya kuɗin sabulu ta ɓangarensa domin ya sami makamin shiga nasa gidan. Ko babu komai zai hayaƙa tasa giwar.***

Zaune take a babban fallon da zai sadaka da ainihin cikin gidan. Tun fitowarta asibiti ta ƙara zama wata shiru-shiru fiye da baya. Ita da kanta mamakin kanta take yi game da sauyen-sauyen da aka samu kan wasu ɗabi’unta. Hawayen da ya kwaranyo mata ta goge tana jan ajiyar zuciya.

Fawwas ne ya shigo kamar an jehoshi, ƙiƙam ya tsaya a kanta yana ƙunƙuni.

“Wai ki je in ji Uncle Jawwad yana sitroom yana jiranki”

Bata ɗago ba, bare kuma yaron ya sa ran samun amsar data dace. Ficewa ya yi yana turo baki tare da sakin maganganu waɗanda tasan a baya koda kuɗi aka haɗashi bai isa ya furta mata su ba. Amma yanzu wanda be kaishi ba ma zai mata haka. Tunaninta ya tsinke lokacin da Yaya Khamis ya shigo yana hucci.

“Ke Labiba dan iskanci ana son rufa miki asiri shi ne zaki watsa wa mutane ƙasa a ido? Yaron nan yana zaune yana jiranki tun ɗazu amma saboda baƙin halinki kin yi banza da shi. To wallahi ki sani ba zan ɗauka ba, nagaji da halinki…

“Yaya Khamis mana..”

“Bana son jin komai, ki tashi ki fita ki bani waje, kuma ki ka sake ki ka yi masa abin da zai tunzurashi ke ki ka sani domin shi ne makamin komawarki gidan Yusuf..”

Da mamaki ta ajiye kallonta a tsakiyar idanunsa, ya jinjina mata kai cike da ƙwarin guiwa yana ajiye murmushi a saitinta. Wani abu ta ji ya daki ƙirjinta, jikinta a saluɓe ta miƙe tana tattara guntuwar natsuwar data rage mata. Dogon hijabi har ƙasa ta saka ta fito tana bin bango kamar wata munafuka. Ɗaya bayan ɗaya mutanan gidan duke kallonta suna watsawarwa har ta isa wajan da aka tanadarwa baƙi. Yana zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karkaɗawa.

A tsaye take tana kallonsa ƙasa-ƙasa, bai ko kalleta ba. Sai murmushin gefen baki da ya ke saki. Tsaf ya ƙare mata kallo ta cikin zumbulelen hijabinta, tana da ƙira mai kyau. Ko ba komai zai kwashi rabonsa ya ƙara gaba. Tunda komawa gidan Yusuf ne muradinta ko ba komai zai zame masa makamin nufarta idan ya so ita ma ta fito da TAMBARIN da yayanta yake masa gori akai.

“Labibah!”

Ya kira sunan da wani irin sauti, gaba ɗaya yanayin jikinta ya nemi ya sauyawa. A hankali ya tako inda take yana zagayeta. Dubanta yake a kaikaice, hancinsa yana sansanar wuyanta.

“Labiba ki bani dama, ni kuma zan faranta miki fiye da duk WATA MACE dana taɓa mu’amalanta. Wollah zan baki shika tun wanshekaran da anka kawomani ke gidana!”

Gabanta ya ƙara tsananta bugu, yayinda ta ji hannunwansa sun sami zarcewa wasu sassa na jikinta. A ƙaugace ta janye jikinta ta ɗaga hannu ta kifa masa mari, kafin ya ankara ta ƙara masa biyu zafaffa. Tana hucci ta yi baya, tana me zuba masa jajjayen idanunta. Sai kuma ta kwasa zuwa cikin gida a guje tana rusar kuka me cin rai.

Dai-dai shigowar Yaya Khamisu, suka yi karo da shi bata waiwayo ba, ya juya kafin ya yi wani yunƙuri yahango Jawwad yana niyyar fice a hayaƙe. Gabansa ya sha,

“Jawwad kun daidait..”

“Dakatamin Khamis!”

Ya katseshi a tunzure, ya ɗora da,

“Tun asali kasan halin ƙanwarka bata da mutunci bata san ƙimar mutane ba. Ina laifina dana rufa asiri zan yi wa kaina runton zunubi akan ƙaddararta. Amma wannan be isheta ba har tana a zarfi ɗora hannu kanfuskata. To kasani ka kuma shaida mata wallahi bashi ta ci kuma sai ta biya ko ba yau ba. Aure kuma ba zan yi ba ka nemi wani. Miliyan guda kuma na cinyeta bisa ƙasƙantani da ta yi ta mareni ba wai dan sun isa fansar lafinta ba ta jirace ni. Fuu! Ya yi gaba ya barshi nan a tsaye kamar status. Dafe kai ya yi yana jin wani ɗaci a ƙasan ransa. Yasan waye Jawwad tunda ya furta zai aikata. Wani takaicin Labiban ne ya ƙumeshi. Hakan ya tunzura shi ya fita daga gidan ba tare da ya yi magana da kowa ba. Kai tsaye gidan mahaifinsa ya shiga rai a ɓace ya nufi sasshin mahaifiyarsu yana sababbi. Babu ko sallama ya hau rattaba bayani,

“Wallahi amna na gaji d iskancin wanga ɗiya. Tunda aure nata sunka muntu nike hidima wa ita amma gani take mu munka kashe mata aure. Na yi faffutukar neman wanda zai aureta asirinmu ruhe na samu Jawwad ya amince. Babu mai zarginmu game da shirinmu saboda dama shi yana da TAMBARIN sakin mata a zuri’armu. Salin ahalin sai ta koma ɗakinta. Shi ne take shuka masa halin nata ya fasa. Bayan na zare kuɗi har miliyan guda na bashi toshiyar baki!”

Abokiyar zamanta data sako kai ta yi baya tana riƙe haɓa, saɗaf-saɗaf ta nufi babban tsakar gidan inda suke taruwa suna shan iska. Mata da maza ne a tare ƴaƴa da jikoki, tun asali harabar wajan hirarsu ne tun suna ƙuruciyarsu. Dama kuma tun mutuwar auren Labiban wajan ya koma gurin kafa dandalin hirarta. Dan haka yanzu da sabon labari ya samu, a hanzarce Mama Saude ta taho tana baza musu labari.

“Khamisu baka da hankali ina ga, mi ka damunka ne wai kan wannan ƙanwa taka? Kasan zaman da mukan yi cikin gidanga shi ne ka taho kana mana bankaɗa haka? Shin auran nata waka kasoshi bakai ba? Dan hakanga kai ne me ɗaukar duk lalurinta”

Ɓata rai ya yi yana jin takaicin Amnan tasu, idan shi ne me hannu cikin mutuwar auren Labiba ai ita ce jagoransu. Duk wani iskanci data shimfiɗa a gidan da sa hannunta…

“Ta shi mu je gidan na ganta!”

Bai musa mata ba, suka fito tare. Tunda suka doshi wajan tasan maganar ta isar musu, domin laɓe a gidan abun ado ne. Dan hakama ta shiryawa yadda zata taresu. Gab da zasu fita ne, Inna Sa ade ta yi dariya,

“Ɗiyan boya kuma da kuɗi aka haɗa a aureta, su da ake sayensu yau su suka sayen miji”?

Bata barin ta kwana, dan haka ta juyo fuskarta a cike da murmushi.

“Ai kinsan shi zamani riga ne, wadda ta yi maka daidai ita ka ke maƙalawa. Tun yaushe ake haɗa mazajan ɗiya da gida da mota ke sai yanzu ki ka san wannan martabawar?”

Sai ta juya ta barsu shanye da baki, Hajiya Amne kenan haka take bata taɓa bari a fahimci rauninta. Ta iya tafiyar hawainiya. Masifaffiyar mace ce ta ƙin ƙarawa, bata ɗagawa kowa ƙafa. Lokacin ƙuruciyarta ba ƙaramin mulki ta zuba a gidan ba, gata dai ba jinsin matan aure ba. A baiwa ta ke amma kuma idan ta murɗa kambunta sai ta so za a baki kwana. Maigidansu har ya mutu yana shakkar ɓata mata rai. Ta zamewa matan gidan ƙadangaran bakin tulu. To har zuwa yanzu da kowa yake zaman gashin kansa, ƙarƙashin inuwar ƴaƴa bata sake zani ba, idan ka ce mata kulle zata ce maka cas! Kuma baka taɓa fuskantar inda ta dosa saboda ita ɗin ƙuli-ƙuli ce.

Tun da suka shiga gidan bata tankawa kowa ba ta wuce sashin ɗiyarta, sautin muryarta ta karaɗe kunnuwanta,

“Yusufa mijina. An rabani da mai sona. Sun rabani da yarana. Na bani ni ƴar Amne”

Ras! Gaban Amne ya faɗi, ta ƙarasa tana rungumota jikinta, hawaye shar wani yana bin wani tana share mata. Cikin kunnuwanta ta dinga raɗa mata maganganu masu taushi tare da alƙawaruruka masu girma. A haka ta samu ta yi shiru tana ajiyar rai. Sannu a hankali matan Khamis ke shigowa suna kawo gaisuwa ɗaya bayan ɗaya idan ka ɗauke Yaya Ade. Jinjina kai ta yi bayan amaryarsa ta ƙarshe ta gaisheta ta wuce,

“wato Khamisu matarka Ade ta raina ni ko?”

“ki yi haƙuri Amne ƙuruciya ce!”

“Hakan kake faɗi kodayaushe amma zan yi maganinta”

Ta furta tana datse harshe, tana tuna girman amintar dake tsakaninta da mahaifiyar Ade wadda ta kasance abokiyar zaman mahaifiyar Yusufa. Duk ita ta ƙara rura wutar tsanar Yusufan a ranta har suka kawo wannan gaɓar amma kuma ta lura ɗiyarta ta fi kowa takurawan Labiban tabbas zata ɗauki matakin da zai ɓata ran kowa. Juyawa ta yi zata gyarawa Labiban kwanciya sai ta samu bacci ya ɗauketa. Amma kuma abin mamaki surutai ta ke yi tana faɗin sunan Yusufa. Da mamaki take duban yayanta, ya ɗaga mata kai,

“Amne ni dai zan biya miki saudiyya ki je ki yi wa Labiba addu’a ko zamu samu sassaucin wannan masifa. Haka take in tana bacci to Yusuf ne a bakinta haka ma idan idonta biyu waƙar Yusufa ce a bakinta!”

Girgiza kai ta yi daga bisani ta yi shiru tare da gyara mata kanta dake kan cinyarta, a hankali ta saki ajiyar zuciya tana tuna komai daki-daki.Gudu yake kamar zai tashi sama, wani irin yanayi yake ji a ƙirjinsa wanda bashi da bambanci da zubar garwashin wuta. Kamar almara ƙafafunsa suka soma yi masa nauyi. Ya yi ya yi ya motsasu amma tamkar dutse haka suka zame masa. Durƙushewa ya yi yana cije leɓɓensa. Da dukkan ƙoƙarinsa yake san motsasu, yana san faɗamusu su ingizashi zuwa gaba kafin abinda zuciyarsa yake ɗarsa masa ya afku. Yana jin dukkan dammamakin daya mallaka suna kuɓcewa da wata irin nadama.

Ƙasar wajen da yake tsugune ne ta soma wata irin girgiza. Idannunsa ya buɗe da wani irin matsanancin tsoro, wanda ya bayyana har kan laɓɓansa da suka soma rawa. Kafin ya yi wani yunƙuri fuskar da ba zai taɓa mantawa da ita ba ta bayyana. Ita bata yi sama ba, kuma bata yi ƙasa ba. Tsoro ya kamashi matuƙa, ‘dama ana mutuwa a dawo’ ya ayyana aransa. Sai dai tunaninsa ya rabu gida biyu lokaci ɗaya kamar yadda lokaci ɗaya fuskar ta rabu biyu.

Ɗaya tana ɓanagaren dama, cikin shiga ta kammala ɗauke da murmushi, a gefenta korayen ganyayyakine suna linƙaya da wani irin fure mai ƙayatarwa. Ɗayar kuwa murtuk take, kanta a tsefe ya mimmiƙe, ga wasu irin huddoji da suka ɓuɓɓurma. Wasu irin macizai na fitowa ta ciki suna haurawa zuwa saman gashinta. Wuta ce me tsananin zafi take fitowa ta bakinta. Huccin wutar ne ya bugeshi yasa dukkan hannuwansa yana karewa. Bakinsa na rawa ya furta,

“Zahidaht!”

Wata irin dariya mummunar fuskar ta yi, yayinda kamillaliyar ta ɓacewa ganinsa.

“Kaiconka Kabir!”

Motsawa yayi yana yin baya da wani irin taku, da dukkan kumajinsa yake fatan ya ɓacewa ganinta amma ya kasa motsawa. Binsa ta cigaba da yi tana dariye me amsa kuwwa sai, huccin bakinta na cigaba da ɗumama yanayinsa.

“Kamar yaune Kabir, kamar yau ne zaka zo inda nazo!”

Wani wawwakeken rami ne ya bayyana a bayansa, shi ya tilasta masa tsayawa har ta riskeshi. Bawai dan bazai iya motsawa ba, bawai dan yana gudun wahala ba yana jin zai iya faɗawa ramin domin ya kuɓuta. Amma ba hakane muradinsa ba. Muradinsa kawai ta dafa kafaɗarsa ta ce,.

“Kabir na yafe maka!”

Wata shaƙa ta yi masa me matuƙar zafi, take ya soma kakari yana yunƙirin ƙwacewa. Amma ya kasa aiwatar da komai. Wutar ds take bakinta ta hura masa. Komai ya ɗauke masa, yana jin yadda duniyarsa take sauyawa, sai dai bashi da wani ƙoƙari. Tunkuɗashi ta yi ramin bayansa. Ya soma tafiya a hankali, yana jin yadda idanunta suke ɓacewa daga ganinsa. Kafin ya kai ƙasa ya hangi kamilalliyar fuskarta cike da murmushi, ta rikiɗe da wani irin yanayi me kama da tausayi tana furta,

“Kana da sauran lokaci, zaka iya gyara kuskuranka Kabir. Ka gyara kafin zuwan ranar nadama!”

A gigice ya farka yana kiran sunanta da ƙarfi, Jawwad ya miƙe yana buga tsaki,

“gaskiya ni ana ƙwarata wallahi da aka haɗani kwana da mahaukaci!”

Ihu ya cigaba da yi yana kururuwar data haddasawa mutan gidan fitowa. Hannunsa na kan wuyansa yana kakari, kafin kace kwabo gaba ɗaya sun cika ɗakin wasu kuma na daga waje suna kakabin lamarin. Sai dai jin sunan Zahidaht da yake kira ya basu amsar dalilin ihun. Baba Ɗangaladima ne ya riƙoshi suka fito, faɗi ya ke,

“ki yafe min Zahidaht dan Allah!”

Mtsss! Abokiyar zaman mamansa ta ja tsaki tana mitar an katse musu baccinsu. Labiba kuwa tana gefe amma tsoro da mamaki sun cika zuciyarta. Kabir ne yau yake kururuwar yafiya daga Zahidaht bayan bata duniya. Wani tunani ya ɗarsu a ranta tana ayyana ita yaushe ne zata nemi yafiyar Yusuf. Baba Muttaka ne ya yi magana kowa ya koma sashinsa, saboda yadda ƙananun maganganu suka soma tashi. Sai dai hakan be hana ƴan habaice-habaice tashi ba.

Labiba tunda ta koma sashinsu takasa komawa bacci gaba ɗaya nadama da danasani sun rufeta. Idan haƙƙin Yaya Zahy na yawo da Kabir har haka ita ina haƙƙin Yusuf dana yaranta zai kaita? Gabanta ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. Bata yi aune ba har aka kira asuba. Tunda ta idar da sallah tana zaune kan darduma har gari ya yi haske. Babu abinda take yi sai tunanin rayuwarta ta baya. Wata irin nadama ce take lulluɓe da zuciyarta bisa tunaninta na zama *WATA MACE* kafin zuwan wannan rana. Turo ƙofar da aka yi ne yasata maida hawayenta, sai dai mamaki ne ya kasheta ganin shigowar Yaya Ade sashinta karon farko tun dawowarta gidan.

“Laby kin tashi?”

Da idanu ta bita, tana son jin zuciyarta ta ƙaryata mata ba Yaya Aden bace take mata magana da sanyi haka. Sai dai duk yadda zuciyarta take matsewa da yanayin ta kasa samun amsar datake buƙata. Runtse ido ta yi tana aro juriya.

“Aunty Ade na tashi!”

“Ki fito to, ki yi kalaci akwai taron family yau”

Murmushin dake kan fuskarta be ɓace ba, sai yanzu ta samu amsarta. Ashe wannan saƙon ne tafw da ita shi yasa ta tako ɗakinta. Da idanu ta rakata har ta ɓacewa ganinta tana jin yadda zuciyarta take matsewa. Lumshe idanu ta yi tana tuna komai daki-daki.1

STORY CONTINUES BELOW

MAFARI.

Ahalin Malam Bukar Saɓalo, babban ahaline da ke ɗauke da al’umma masu yawa. Asalin Malam Bukar Saɓalo mutumin garin Sakwato ne, haifaffen cikinta gaba da baya. Shi ɗin baƙin bafulatani ne, ɗan asalin wani ƙauye ɗaya daga cikin ƙananun hukumomin jahar. Allah Ya azurtashi da matan aure huɗu, da yara maza guda goma sha biyu rigis. Sai kuma Mata su takwas waɗanda dukkansu suna gidajen mazajensu cikin kwanciyar hankali.

Malam Bukar cikakken Malamine mai bada taimako, ta fannoni da dama. Shi ɗin manomi ne na gaske, ga kiwo, kuma ɗan kasuwa ne dan bai tsaya iya noma ba, ya haɗa da kasuwancin su kalwa gyaɗa da injinan sarrafa kanta gyaɗar. Haka kuma yana da alfarmar samun kwangiloli ta ɓangaren gwamnati da dama. Hakan yasa ya yi suna sossai cikin garin Sakwato. Babban mutum ne mai dattako ga taimako da kuma jin ƙan na ƙasa da shi. Babban ɗansa shi ne Yusuf wanda suke masa laƙabi da ɓaure, saboda bashi da abin faɗa sai Allah Ya bashi ƴaƴa da yawa sama dana Malam. Hakan ya sa sa’aninsa suke yi masa inkiya da wannan suna kuma ya bishi.

Sai mai bi Masa Sani wanda suke yi wa laƙabi da Ɗangaladima. Sai kuma na ukunsa Musa suna kiransa da Ɗan ƙwairo. Akwai Ibrahim da Khamis. Sadisu da Muttaƙa sai Lawali da Jamilu da da Audu da kuma auta Mu’azu. Dukkan iyalansu kama daga kan mata har zuwa maza akwai haɗin kai mai ƙarfi tsakaninsu. Sai dai kishi na tsakanin zuƙatan mata wanda su ma ƙarfin ikon maigidan bai basu damar asassar da shi a cikin gidan ba.

Ya ɗora iyalansa kan turba mai kyau har zuwa lokacin da mutuwa ta ɗauke shi. Musamman ta ɓangaren karatu, ya basu damar yinsa gwargwadon ƙarfinsa daga mazan har matan. Sai dai yaransa mata basa zurfin ilmin boko, ƴa mace na da shekara sha biyu yake aurar da ita haka kuma namiji baya haura shekaru ashirin. Yakan wadatasu da jarin da zasu yi sana’a a gidajensu. Kuma wannan ɗabi’a har ya mutu yana jadaddawa yaransa maza da su tafi a kanta.

Su ma ɓangaren mazan ya wadatasu sossai, daga fanin karatu, da tarbiya haka kuma masu sha’awar kasuwanci babu wanda bai samarwa madafa ba, sai dai abin da ke haɗashi da yaran nasa shi ne yawaitar aure-aure tun suna da ƙananun shekarunsu. Ya sha zama ya nusar da su yadda ya zauna da mahaifansu su huɗu kacal amma kuma kash ya lura aure-aure kamar ajininsu ya ke.

Hakan yasa ya soma tunanin shin ta yaya zuri’arsa zata kasance a waje ɗaya? Tunaninsa ya ta fi kan gina babbar shiyar da zata zamo majingina ɗaya cikin zuri’ar. Tabbas burinsa ya cika domin kafin rasuwarsa sai da ya samar da babbar shiyar da ta zamo matattarar iyalansa maza gaba ɗaya.

*ƊAN SAƁALO ESTATE*

Babbar shiya ce data tara kafatanin ƴaƴansa maza da iyalansu. Akwai ɓangaroro masu dams cikinta, kama daga kan makaranta, masallaci da kuma ɗan ƙaramin wajen kula da lafiya _clinic._ An ɗauki tsayin shekaru uku da rabi ana gina wannan shiya, sannan ta kammala. Wani iko na ubangiji wata ɗaya da kammala gininta ya amsa kiran mahallicinsa kuma ba a shafe wata biyu ba matansa suka dinga bin bayansa ɗaya bayan ɗaya. Wannan ahali sun shiga tashin hankali ƙwarai da gaske. Daga bisani suka rungumi ƙaddara kowa ya kama iyalansa tare da ƙarfafa zumunci mai ƙarfi tsakaninsu da ahalinsu.

Shekaru sun ja sai dai kuma kash, ɗabi’ar nan ta aure-aure na ƙara linƙaya cikin wannan ahali. Baba ɓaure wanda ya kasance babba cikinsu, ɗan kwangila ne da ya shahara cikin garin Sakwato da wasu ɓangarori nata. Haka kuma bai bar sana’ar mahaifinsu ba ta kalwa wadda suka haɗa kai da ɗan uwansa Ɗangaladima suke yi tare.

Ɓangaransa ne a farkon shigowa. Yana da matan aure guda huɗu da kuma boya guda huɗu yana kuma da yara guda sittin da takwas ƙanana da manya da kuma masu tasowa. Waɗansu mahaifiyarsu ta fita waɗansu kuma mahaifiyarsu tana nan. Hajiya Gajiya ita ce matarsa ta farko tana da yara goma sha biyu. Sai Hajiya Lubba me yara takwas. Sai Hajiya Asiya me yara goma. Hajiya Lawisa ita ce me yara huɗu kacal Suwaiba da ƙananta Hannatu Amina da Zahidaht da kuma autansu Mustapha.

Baba Ɓaure bai tsaya iya nan ba yana da bayi guda huɗu. Duk cikin bayinsa guda huɗu babu mai haihuwa, sai guda ɗaya da suke kira da Amne wadda ta mallaki yara guda goma tara maza ras sai mace ɗaya mai suna Labiba. Kaf matansa babu wadda bata kishi da Amne sakammakon ita ce fitilar cikin gidan. Mulki take bugawa son ranta. Tsayayyar mace ce kamar namiji, dirarriya mai kyan fassali gata da tsayi da jin kai uwa uba kuma ƴar gayu ce ta ƙin ƙarawa.

Ɓangaren Baba Ɗangaladima shi ma matansa huɗu ne rigis, da farko kasuwanci ya kama sakammakon anan yafi ƙwarewa. Ya tara dukiya mai yawa kafin Allah Ya aiko masa da ibtila’in karayar arziƙi wadda ta zamo sillar durkushewarsa ya rungumi noma gadan-gadan. Sai dai duk da haka dukiyarsa bata kai ta sauran ƴan uwansa ba. Matan auransa su huɗu ne da boya guda biyu. Babbar Hajiya Hauwa mace mai tsanin haƙuri da sanin yakamata. Tana da yara shida, Adamu shi ne Babba wanda yake auren ɗiyar Babban Ɗanƙwairo wadda suke kira da Yaya Asabe asalin sunanta Amina. Wasu ma kan kirata da Yaya Aminan.. Tana da tsananin kirki da sanin ya kamata. Sai mai bi masa Mu’azam Aisha da Mardiyyah sai kuma autansu wanda ya kammala karatunsa wato Yusuf takwaran baba ɓaure. Sai abokiyar zamanta me yara biyar Hajiya Muwaddah, Ade ita ce Babba a yaranta. sai ƙananta Hamsa’u da Huwaila da Amra da kuma Jidda. Sai sauran matan guda biyu da suke da ƙananun yara guda goma sha bakwai jimila.

Gidan Baba Ɗangaladima, gida ne da ake gudanar da ƙazamin kishi wanda har ya ɓacci. Hajiya Hauwa ita ce babba sai dai kuma kash ta kasance ita ce koma baya. Idan suna yi mata wani wulaƙanci, sai ka ɗauka boya ce. Domin su sun fi nuna kishinsu ga boya fiye matan ahalinsu. Kodayake duk sanda wulaƙancin abokan zamanta ya motsa, sukan goranta mata da asalin mahaifiyarta boya ce duk da cewa auranta da maigidan auren zumunci ne.

Hajiya Muwaddah ita ce tauraruwa a cikin gidan gaba da baya, kuma kanta a haɗe yake da matar baba ɓaure Hajiya Saadatu wadda suke kira da Amne. Karansu suke ci babu babbaka. Sau tari Hajiya Hauwa ita ce da girki amma kuma bata da kwana a gidan, haka kuma duk lokacin da ta yi miya babu mai ci daga matan gidan har yaransu. Ba kuma dan bata iya ba kawai tsabar ƙiyayyace da yadda maigidan ya ɗaukaketa a ransa saboda karamcinta kafin ayi kutu-kutun da aka fitar da ita daga ransa gaba ɗaya. Idan ta kwana da miji to rantsattsen rabone ya rantse haka suke tafiya tun daga ƙuruciya har suka manyanta. Kullum ta kan nusar da yaranta muhimmancin haƙuri da kuma juriya.

Ɓangaren baba Ɗanƙwairo su ma tubarkallah akwai iyalai da ya wa. Matansa uku ne yana da yara ashirin da takwas sai ɓangaran Baba Iro baba Muttaƙa da sauransu. Dukkan sassan suna da yara da yawa amma babu kamar waɗanan sassa guda uku. Haka sassan suka kasu har zuwa sassa goma sha ɗaya. Daga bayan gidan akwai wajen kiwo wanda Baba Iro ya ƙware a wajen. Sossai yake fitar da shanu da awaki musamman alokacin babbar sallah. Yana kuma kiwon kaji da fitar da kifaye.

Kaf wannan ahali sun tsayawa yaransu matuƙa wajan karatun boko da addinni. Sai dai kuma suna riƙe da wannan al’ada tasu guda ɗaya. Mace da zarar ta haɗa shekaru goma sha biyu cif a duniya to sukan haɗata aure da namiji ɗaya cikin ahalin me shekaru goma sha takwas idan sun fahimci fitinanne ne, idan kuma yana da natsuwa sukan bar shi ya kai matakin shekaru ashirin. Sai dai yaran nasu ba acikin gidan suke zama ba, bayan aure yaran maza kan cigaba da karatu. Haka kuma me sha’awa cikinsu ya kan bar matarsa ta ci gaba da karatu. Amma kuma matan duk da ƙarancin shekarunsu basa aure sai sun haɗa saukar alƙur’ani mai girma. Wasunsu hadda wasu kuma biye suke yi. Wani ikon na Allah mahaddatan sun fi yawaita daga cikin matan. Hakan ce ta cigaba da kasancewa cikin wannan a hali har shekaru suka ja.

***

Baba ɓaure dai kamar yadda yake babba cikinsu to takowane fanni kuma Allah Ya girmamashi. Yana da ɗumbin dukiyar da shi kansa ba zai iyakance adadinta ba. Domin shi suke nunawa a makwafin mahaifinsu a komi. Yakan taɓa ɓangaren abin da ya shafi siyasa, shi ya sa samun kwangila bata yi masa wuya. Haka kuma duk kwangilar da gwamnati zata bashi ba ya karɓar ko sisi sai ya kammala an tabbatar da ingancinta daga bisani ya karɓi haƙƙinsa.

Hakan kuma bai saka masa ƙyashi ko hassadar ƴan uwansa aransa ba. Duk wani biki da ake gudanarwa a zuri’arsu shi ya ke ɗaukar nauyin kayan ɗaki, bayan biki shi ya ke ɗaukar hidimar karatun mazan. Zai basu muhalin zama da matansu, idan suka kammala karatu zai nema musu aiki, ya kuma ɗorasu turbar kan gina nasu muhalin koda ba zasu tashi daga nasa ba, domin yana basu ne iya mudun rai har ka gina naka ka danƙa masa nasa.

Matan da aka aurar kuma duk shekara bayan ya fitar da zakka, yakan raba musu naira dubu ɗari-ɗari da sunan su ja jari. Waɗanda mazansu ba su basu damar ci gaba da karatu ba kuma ya kan ƙara musu da dubu hamsin akan dubu ɗarin.

Baba Ɗanƙwairo ne me ɗaukar hidimar gara duk bikin da za ayi, baya gazawa.. Shi kuma Baba Iro duk wani yaro da za ayi wa bikin shayi (kaciya) a zuri’arsu shi yake bayar da rago da kuma kajin da za a buƙata tun daga kan ƴaƴa har jikoki.

Wannan al’adace ta mutanan Sakwato, sossai suke suke kashewa ɗiyansu kuɗi wajen bikin shayi. Kamar wani biki, wasu ma har anko suke yi, dangi kuwa sukan himmatu wajen kawowa yaro kyautuka, kaji awaki da sauransu. Da zamani ya ratso kuma bidi’a ta ƙaru hadda masu kekuna da abin da ba a rasa ba. Abu dai sam barka.

Tabbas ɓaure wani jigone a cikin zuri’arsa, hakan yasa suke ƙaunarsa da dukkan zuciyarsu. Sai dai duk wannan ƙauna da suke yi masa babu wanda ya taɓa yi masa takwara cikin zuri’ar daga ƴaƴa har jikoki in ka ɗauke Baba Ɗangaladima.Tabbas saka sunan Yusuf ya ƙara mutuntaka da ƙimarsa a idanun ɗan uwansa.

Tun da aka haifi Yusuf ɗin Hajiya Hauwa kuwa, aka kuma tabbatar da sunansa baba ɓaure bai taɓa gazawa wa hidimar yaron ba. Kama daga kan ragon sunansa har sutura da komai nasa har ya isa sawa makaranta. Kyautuka kuwa har ya zamo Hajiya Hauwa na ƙorafi kan wannan kyautuka da yake masa. Wani ikon Allah kuma Yusufa ya taso da tsananin haƙuri kamar mahaifiyarsa ga farin jini da tsananin kunya. Duk inda baba ɓaure yasa ƙafa to zaka sami Yusuf a waje. Kaf ahalinsu sun sa da wannan.

Hakama take a ɓangaren Baba Ɗangaladima yana tsananin ƙaunar Yusuf sama da kowa cikin yaransa. Wannan ƙauna da Baba ɓaure da ɗangaladima suke masa ta ƙara rura wutar tsanar Yusuf da mahaifiyarsa Hajiya Hauwa a zuciyar abokiyar zamanta Hajiya Muwaddah da kuma Hajiya Amne wadda ta kasance aminiya gareta kuma mace ƴar gaban goshin Baba ɓaure acikin matansa. Kowa yasan amintar dake tsakanin Hajiya Muwaddah da Amne, domin akansu aka soma samun ɓarakar aurattayya na yaran gidan.

Lokacin da aka so haɗa Adamu yaron Hajiya Hauwa da Bilkisu ɗiyar da Amne take riƙo bayan fitar mahaifiyarta. Ƙiri-ƙiri ta nuna hakan bazai yi wu ba. Haka kuma aka so haɗa Khamis yaronta da ɗiyar Hajiya Hauwa ta nuna bata son wannn zance ba sai dai a haɗashi da Ade ɗiyar aminiyarta Muwaddah. Su suka asassa dalilan sauya tsarin auratayya a gidan. Tun daga lokacin aka suuya, bisa ƙi da kuma son rayuwan wasu cikin zuri’ar.

Adawarsu da ƙaunar da ake yi wa Yusuf ta cigaba da ƙabura sossai har girmansa. A ganin Hajiya Amne idan Labiba ƙaramar ɗiyarta bata sami wannan ƙauna daga mahaifinta ba to kuwa Khamis babban ɗanta shi ya kamaci wannan ƙaunar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *