WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

SAUYI.

Haihuwar Labiba ta kawo sauyi da yawa a rayuwar aurenta da Yusuf. Sossai zahirin hallayarta ta fito kowa ya sani. Muguwar ƙazantar data zame mata jiki ta bayyana. Ɗakinta baya zaunuwa saboda zauri ga ƙarnin miyau. Domin tana tashi daga bacci shi take soma tsartarwa a jikin bango. Tun yana kauda kai har ya zamana ya soma tankawa amma babu sauyi ko kaɗan sai ma izgilanci da rainin wayau data tsiri yi masa. Hakan ya asassa musu rabuwar ɗaki kowa ya zamana yana da mallakinsa.

***

Duk abinda ya ke faruwa game da ƙazantar Labiba Amne ta sani sarai, amma bata taɓa kadda baki ta yi mata magana ba hasalima hakan ya yi mata yadda take so ko ba komai Yusuf zai ƙara ƙuntata da baƙin ciki. Watan Ummi goma a duniya Allah Ya sake bata rabon ciki, tabbas samuwarsa ta ƙara asassa komai na rayuwarta. Iskanci kala-kala da an yi magana ta ce cikine. Tun ba ajin kansu har ya zamana iyayensu maza sun soma shiga cikin lamarin domin sassanci. Baba ɓaure dai kodayaushe yana bayan Yusuf saɓanin mahaifinsa. 

***

A safiyar wata Asabar Yusuf ya tashi da sassafe. Nazira ɗiyar Yaya Asabe da tazo musu hutu yasa ta kira masa Labiba ta tafi da ɗan gudunta tana tsale. Tana shiga ta sameta a kwance kamar mataciyya. Kauda kai ta yi tana gunguni dan Nazira akwai rashin kunya. Ƴar ƙara ta yi, wadda ta haddasawa Labiban farkawa, a tunzure take duban yarinyar da haushin tadata da ta yi. Nazira kuwa baya ta yi tana ɗan turo baki. Tsittt! Kake jin sautin fitar miyan bakinta, bai sauka ko ina ba sai a bangon ɗakinta. Nazira data shigo ta ja baya tana kyaɓe baki. Idanunta ƙur a kan bangon da Addahrta ta zubar da miyan. Ɗauke kai ta yi tana yatsuna fuska. Karaf a kan idanun Labiba, ta maka mata harara,

“Dan ubanki ni kike kyaɓewa baki?”

Ja da baya yarinyar ta yi tana zare idanu, domin tasan matuƙar ta shiga hannunta mai ƙwatarta sai ubangiji. Bata sami nasarar guduwa ba ta cafkota.

“Ba dake nake ba?”

Da sauri yarinyar ta toshe hancinta saboda hamammin bakinta daya doketa. Daidai lokacin da take kicin-kicin ƙwacewa Yusuf ya jiyosu ya tako zuwa ɗakin badan ransa ya so. Sai dan sanin zata iya illata masa yarinya kafin zuwansa.

“Laby cikamin yarinya!”

Ya furta da fuskar shanu.

“Idan anka ƙi hwa?”

“Zan ɗauki mataki fiye da tsamaninki!”

Kallon uku kwabo ta watsa masa, ta cuno baki tana karkata kai.

“Da anka yi man wanga tutiya, banda wannan lokaci kajiya”

Wani ƙululu ne ya tokare masa maƙoshi, da ƙyar ya haɗiye miyan daya tattaro, bai san yaushe ne Labiba zata sauya ba? Ba haka ya ga KOWACE MACE na yi wa mijinta ba. Wai shin jarrabta siyanta ake da Labiba ta kwaso duk wasu makaman raini ta zuba akansa? Ba tare da ya tanka mata ba, ya juya ya kama hannun Ummi da Nazira da zumar su bar ɗakin,

“Allah ka rabani da lusarin namiji!”

Saukar kalamanta kamar aradu cikin kansa, a fusace ya juyo ya watsa mata wani kallo muryarsa na rawa,

“Ba ki ji ya daɗin halinki ba, ɗiyan boya kawai”

“Uwa taka ma ai tsattson boya ce..”

Jifa ya kai mata da takalmin ƙafarsa, ya kuwa yi nasarar samunta a bakinta. Ta ƙwalla ƙara tana riƙe wajen. Take leɓɓen ya fashe kafin ajima ya kumbura ya yi suntum da shi. Ta kuwa shiga surfa masa zagi ta uwa ta uba, ganin idan ya biye mata sai ya iya yi mata dukan da zai nakasata ya sa ya fice da niyyar bar mata gidan gaba ɗaya. Nazira da take riƙe da Ummi tana kuka ta yi sakare tana kallonsu. Farga ya yi da yarinyar ya juya kawai ya fita gudun yin abin kunya.

***

Cikin Labiba na ƙara girma ƙazantarta ta ƙaru fiye da baya. Nazira da take tayata aiki ta tattara kayanta ta gudu saboda masifarta. Cikinta na gab da haihuwa gwamna mai ci ya bawa Baba ɓaure kwangilar gina babbar kasuwar da ta kasance a tsakiyar garin sakwato. Wadda ta haɗa kowane nau’in kaya na kasuwanci. Kasuwa ce da aƙala ba a kasaraba aka yi itifaƙin zata ci naira miliyan ɗari da hamsin da ɗoriya. Sossai wannan kwangila ta fito da martabar duk wani ɗan cikin *ƊAN SAƁALO ESTATE.* Nan da nan Baba ɓaure ya soma gudanar da gwangilar cike da ƙarfin guiwa.

Yusuf na ɗaya daga cikin ma’aikatan da aka ɗauka, kuma yana cikin waɗanda aka ba wa babban matsayi a wajen. Safiyar da zai fita aikin haka suka rabu da Labiba da zagi uwaka ubanka kare baya ci ba. Ji ya yi kamar bazai fita ba saboda ɓarin rai.

Tunda ya bar gidan kansa ya ke ciwo, ga jiri da yake ɗibarsa lokaci-lokaci. Haka ya daure ya tuƙa machine ɗinsa har zuwa inda ya ke san zuwa. Aharabar ma’aikatar da ake gudanar da kwangilar da wan mahaifinsa ya karɓa ta gina babbar kasuwar MARWAKH ya samu ya yi matsuguni. Tun daga nesa ya hango Baba ɓaure yana zagaya wajen, ya zuba masa idanu, tsoho mai karamci da sanin ya kamata. Tarin dukiya bai ɗora masa girman kai ba, kamar yadda ɗiyarsa ta ɗorawa kanta. Sau tari yana jin kamar ya saki Labiba ya huta, sai dai kullum yana tuna karamcin mahaifinta da kuma furucin mahaifinsa,

“Labiba ɗiyatawa ce, ni naka ɗaurama aure da ita. Amanatata naka baka, ni zaka duba ba ita ba!”

Ajiyar zuciya ya saki, ya taka akan duga-dugansa, daf da yayan mahaifin nasa ya ƙarasa tare da rusuna ya gaisheshi. Daga bisani ya cire rigarsa ya saka ta ma’aikata kamar kowa. Cikin hanzari ya shiga sahu, aka soma loda masa suminti a kwano yana ɗauka kamar kowa. Nauyin sumintin ya danƙarar da dogon wuyansa, har ya bada wata ƙara ƙas! Cije laɓɓansa ya yi yana jin ɗaci a ƙasan ransa, sai dai kuma wata zuciyar na tuna masa,

“da haka kowa ke mallakar gumin hallak!”

A haka suka shari awa huɗu suna aikin gini, wasu na ɗaukar bulo, wasu na kwaɓin suminti wasu kuma na ɗaukar kwaɓin suna kaiwa masu dasa harsashin gini. Nan da nan suka ci ƙarfin aikin domin sun kai kimanin su ɗari da hamsin. Sallah da cin abinci kaɗai ya ke tsayar da su. A haka suka kammala. Daga bisani suƙa soma bi layi sahu-sahu ana rarrabamusu haƙƙinsu na ranar. Kowannansu da naira dubu uku ya tashi.

Hannu yasa ya karɓi nasa kason, farin ciki na zaga zuciyarsa. Idannunsa na kan kawun nasa, yana yaba hallayar dattijon har gobe. Tabbas samun irinsa sai an tona. Ba kuma shi kaɗai ba da yawansu sai sun yi godiya bayan sun karɓi kuɗin, ba don komai ba sai don karamcin shugaban nasu. Sau tari idan sun yi aiki irin wannan na kwangila ga su kuma da yawa, maimakon a basu dubu ɗaya da ɗari biyar ko dubu biyu na yini da aka sani ana biyan kowane magini. Wato raba kuɗin biyu da wasu suke yi, suna yi musu tinƙahon suna da suna da yawa shi yasa aka rage farashin. Shi baya yin haka.

Haka kuma ɗabi’ar sauya ma’aikata a washegari baya yi. Wanda akasari haka ƴan kwangila suke yi, in ma dai waɗanda suke da hanya ko kuma in baka yi sammako ba a ɗauki wasu a yi maka tinƙaho da cewar aikin kwangila babu jira. Akasari maginan da suke aikin kwangila suna fuskantar wannan matsin na ragin haƙƙinsu, ga hantara da kyara daga shugabaninsu. Ga kuma fitar sassafe gudun a sauyasu da wasu. Wsu na jurewa hakan kasancewar rashin aiki da ya yawaita, duk wajen da ake aikin kwangila irin na gini baya rasa matasa masu zuciyar nema a wajen. In ma sun san wani, in ma kuma haka siddan su zo neman dacewa dan samun hasafi.

Sai dai shi nasa fanin ba haka bane, Baba ɓaure akwai karamci, mutanan da ya soma aiki da su, har agama da su yake aiki. Kuma yakan ninka musu kuɗin aikinsu tare da tunatar da su muhimmancin wadata iyali. Shiyasa duk wajan da ake aikinsa zaka ga tururuwar matasa.

Da murna da komai Yusuf ya wuce gida, a hanya ya tsaya ya siyi shinkafa kwano ɗaya ta hausa, sai shinkafar tuwo rabin kwano saboda yasan Labiba na ƙaunar wainar shinkafa.  Ummi da Nazira kuma ya siya musu alawa da biscuit da bobo. Wasai ya ke jin ransa ko ba komai ya fi ƙarfin gidansa. Duk da ƙasan ransa yana jin takaicin yadda suminti ya yi masa kanta a hannu tare da maida fatar hannun nasa me kausji da wani irin tauri na ban mamaki. Haka ƙafafunsa tafin ƙafar duk ya tsattsage duk kular da yake bata da man kaɗanya. Duk wannan takaicin be hanashi yin walwala ba saboda ya siyi abinda za su ci. Sai dai tun daga bakin ƙofa gabansa ya soma faɗuwa. Kafe machine ɗinsa ya yi, tare da yin shahadar ƙuda ya shiga. Take idanunsa suka sauka akan yanyyamun ƙudan da suka cika mazubin kashin yara. Da sauri ya ɗauke kai, zuciyarsa kamar ta fito dan takaici. Tana zaune a can gefe, daga ita sai ɗaurin ƙirji, ga mangwaro take sha. Ummi na kwance a ƙasa bako riga ƙuda na binta. Ga hannunta a baki tana sha, bisa dukkan alamu yunwa ta ci ta cinyeta. Da gudu ya nufoshi,

“Abba sannu da zuwa!” Sauban yaron Yaya Adamu ya faɗa yana ɗaneshi. Shafa kansa ya yi, yana jin ƙuncinsa na raguwa. Babu suturar kirki a jikinta bare kuma yasa ran za ta sakawa Ummi. Ya sake kallon Sauban yaron ya bashi sha’awa tsaf da shi. Hannunsa ya riƙe sossai cikin nasa.

“Saubahn ina Mamanka?”

Mtsss! Tsakin Labiba ya shiga kunnuwansa, ta miƙe yuu! Ƙudaje kuwa suka ce sallamu alaikum. Ɗauke kai ya yi. Ya soma ƙarewa tsakar gidan kallo. Ya ma rasa ta ina ne zai soma. Allah Ya yi shi da mugun tsafta. Dan haka ya zage ya gyara ko’ina tsaf duk da gajiyar daya kwaso. Bai nufi ɗakin girki ba, gudun ganin abinda zai iya sa shi amai. Ummi ya kama ya yi mata wanka, ya kaita ɗakinsa wanda yake fitar da ƙamshi mai daɗi. Daga bisani ya yi dabarar dafa musu indomie suka ci tare da ita, nan da nan ta ware tana ɓangala dariya sai ta ɓingire ta kama bacci. Sai da ya mula sannan ya nufi ɗakinta. Tana zaune kai babu ɗankwali ga tulin kayan wanki, zauri kuwa ba a magana kamar banɗakin ƴan makaranta. Shinkafar ya miƙa mata da sauran canjin, ta karɓa a lallace.

“Ka fanshi kanka da…”

Kafin ta ƙarasa idanunta suka nuna mata shinkafar gida, ƴar hausa. Wata ashariya ta ƙundumo ta maka masa tare da tattara shinkafar ta jefa masa. Bata sauka ko’ina ba sai kan fuskarsa. Ta tarwatse a tsakar ɗakin. Take ya soma bin shinkafar da idanu, kwanyarsa na lissafomasa tarin wahalhalun da ya sha wajan samar da ita. Komai ya shiga zuwar masa daki-daki kamar a lokacin ya ke aikin. Zuciyarsa ta ƙuntata matuƙa karon farko ya ji yana muradin sauke fushinsa akan Labiba tun auransu. Kyawawwan maruka guda uku ya shimfiɗa mata akan fuska, yana huci ya nunata da yatsa,

“Zan juri komai Laby amma banda wulaƙanta ƙumajina!”

Daga haka ya fice ya bar mata ɗakin tana kuka da ɗura masa ashariya kamar ɗiyar maguzawa. Ashariya ta shiga auna masa kwano-kwano. Hajiya Hauwa dake kwance a kabari, ta dinga ambata tana ɗurawa zagi. Gani ya yi ba zai iya juraba ya zage kwanji ya jibgeta son ransa. Ai kuwa da himma ta tattara ta nufi gida. Amne ta dinga surfa ruwan bala’i ta kuma yi rantsuwa duk ranar da ya kuma dukkan mata ɗiya to yayyunta zasu rama mata.

Baba ɓaure ne ya nuna mata bata isa ba, ya kuma ja kunnan Labiba da kakkausar murya kan zagar masa iyaye. Tare da yi wa Yusuf ɗin nasiha mai ratsa jiki kan haƙuri da iyali. Nauyinsa ya koma ji sossai, saboda me doki ne ya koma kuturi shi da ya kamata ace ya tsayawa Labiba amma shi yake goyon bayan Yusuf. Ƙima da mutuntakarsa sai ta kuma ƙaruwa a idsnunsa dama dangi baki ɗaya. Tun daga lokacin Labiba ta shiga fefan dangi, aka watsata. Da anga kina ƴar rashin kunya ga miji za a soma dangantaki da ita, har abin ya soma zama abin fitina cikin ahalin.Baba ɓaure ya tashi haiƙan, wajen gudanar da aikin kwangilarsa. Ba’a ɗauki wata biyu ba gaba ɗaya birni da kewayen garin suka san da mashahuriyar kasuwar. Saboda yadda ginninta ya soma fantsama ko’ina ka zauna batun ake yi. Wani abin burgewaa sisi bai karɓa ba na aikin ya ce sai ya kammala. Wannan ya ƙara masa ƙima da martaba a idan gwamna sossai.

A ɓangare guda kuma ƴan adawa nata ƙoƙarin dakusar da hoɓasarsa, amma kuma Allah bai basu ikon yin nasaraba. Cikin watanni ƙalilan aka kammala ginin kasuwar, gwamna ya haɗa gagarumin taro tare da karrama shi da wasu cikin makusantansa. Aka bashi lambar girmamawa tare da yabawa aikinsa. Sai dai kuma kamar yadda gwamna ya buƙata shi ne, ya zo gida ya amshi kuɗin aikin kwangilarsa ba za a bashi su gaban bainar jama’a ba.

Haka taro ya tashi farin ciki cike da zuƙatan makusanta. Yusuf kansa yana cikin masu farin ciki, domin ba kaɗan ba ya dama a wannan kwangila ya samu daidai gwargwado haka duk wani matashi dake kewayen unguwar dama cikin estate ɗinsu.

Bayan sati biyu a safiyar Littinin Baba ɓaure ya yi wa iyalansa sallama. Ya shirya ya tafi karɓo haƙƙinsa kamar yadda aka buƙata. Sai dai tun safe har zuwa magarba babu shi babu labarinsa, hakama wayoyinsa basa shiga. Amne ce ta soma ankarar da mutanan gidan halin da ake ciki, domin ita ɗin mace ce mai kulawa da lamarin mijinta. Tunda ya tafi take bibbininsa a waya, balantana kuma da take tunanin kuɗi zai amso ko banza tana da kaso mai tsoka. Saidai bata samun wayar, tun abin yana cinta ita kaɗai har ta fito ta nunawa mutanan gidan wayarsa fa bata shiga. Nan fa hankula suka soma ɗagawa aka shiga cuku-cukun neman ina ya tsaya. Sai dai kash duk iya ƙoƙarinsu babu labarinsa. Kafin wayewar gari labarin ɓatan Baba ɓaure ya kewaye cikin ahalin baki ɗaya.

Baba Ɗangaladima ya fi kowa shiga tashin hankali, sai dai ya fi kowa nuna musu dauriya domin shi mutum ne mai kawaici. Sai yamma suka sami zuwa wajen gwamna sai dai abin tashin hankalin an basu tabbacin bai zo ba. Tashin hankali wanda ba a samasa rana. Wannan ahali sun ga tashin hankali koke-koke kuwa babu yara babu manya. Haka suka dawo guiwa a sage duk da kwantar musu da hankali da gwamnan ya yi tare da alƙawarin sa wa a bincika. Kwana ɗaya biyu uku, babu wani sauyi, ba bu shi babu dalilinsa.

Ta ɓangaren gwamna ma kuma duk ƙoƙarinsu babu wani cigaba sai ban haƙuri da yake wa iyalan. Addu’a kuwa basu san iyakar wadda suka yi ba, suka saka aka yi. Hakama mutanan gari kowa yana nuna alhininsa. Kwanansa biyu da yini aka kira wayar Baba Ɗangaladima tare da buƙatar maƙudan kuɗi kan za a badashi ko kuma zuwa washegari a sami gawarsa. Sossai hankalinsu ya tashi, domin bada kuɗin da aka buƙata tamkar durƙushewar ahalinsu ne domin gaba ɗaya dukiyarsu bata gaza hakan ba. Haka suka shiga cuku-cukun samun kuɗin amma abu ya faskara. Koda labari ya isa ga kunnan gwamna sai ya buƙaci su barshi da alhakin hakan. Sun ji daɗi karamcinsa sossai da sossai. Abinka da aikin gwamnati, ba zasu ce ga yadda aka yi ba, su dai sun wayi gari suni ganshi an kawoshi har ƙofar gida da asuba a wata baƙar mota aka tafi.

Ƴan uwa sun cika da murna da farin ciki musamman da ya kasance lafiyarsa ƙalau, babu wani rauni tare da shi. Kwana biyu ƴan uwa na jelar zuwa ganinsa, aranar kwana na uku ne suka tashi da tashin hankali sakammakon jikinsa da ya rufe da zazzaɓi sai kuma ƙafaffunsa da ya zamana basa motsawa ko kaɗan. Babu jinkiri aka wuce asibiti da shi, binciken farko likitoci suka tabbatar da an yi masa allurane mai nakasa gaɓoɓin jiki daga nan kuma sai kisa. A bayanin nasu sun tabbatar da zasu yi iya ƙoƙarinsu wajen dakatar da allurar, gwamna kansa ya shiga tashin hankali domin yana da yaƙinin don a ɓata sunansa a ka yi.

A ranar ya soma cuku-cukun nema masa visa domin tafiya egypt, cikin kwana biyu zuwa uku aka kammala komai. Tare da Baba Ɗangaladima aka tafi, kwanansu biyu dai jiki ya ƙi daɗi aranar kwana na uku ya amsa kiran mahallicinsa.

Iya tashin hankali ahalin sun shiga, haka aka yi cuku-cukun ɗauko gawarsa zuwa gida nijeriya wadda ta shari tsawon kwana biyar da clearing da komai suka iso tare da rakiyar tawagar amintattun gwamnati. Cincirindon mutane ba a cewa komai saboda tsabar yawansu. Da ƙyar motocinsu da ambulance ɗin da aka turo daga wani asibitin gwamnati wadda ta ɗauko shi suka iya wucewa. Bawan Allah mai halin gaskiya da amana ko da rai ko babu yana cikin zuƙatan mutane. Koke-koke kawai ake ji yayin da ƴaƴansa da kansu suka ɗauki gawar mahaifinsu zuwa cikin gidan domin haɗa shi. Zuƙata sun raunana matuƙa a wannan rana. Hajiya Amne da abokan zamanta sun zabge lokaci guda. Surukan gidan da jikoki ne ke iya taɓuka wani abu, suma ɗin a sanyaye. An shirya yin jana’izar ana idar da sallar azahar saboda ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa da suka roƙi alfarma.

Baba Ɗangaladima baya iya ko magana, haka ma Yusuf Labiba kuwa sumanta uku tana farfaɗowa. Hakan ya jaza mata naƙuda gadan-gadan a ranar ta haifi cikin jikinta, yaro ɗan firit da shi bakwaini. Haka aka yi masa sutura aka sadashi da makwancinsa na gaskiya. Ba wani zama aka sake yi ba, tunda anyi na baya. Har zuwa lokacin Labiba na sashin mahaifiyarta bata koma gidanta ba. Ƴusuf kuwa bai bi ta batunba, ganin har lokacin mutuwar bata gama sakin ahalinsu ba.

Mutuwarsa ta sanyaya jikin ahalinsu da dama. A  kuma lokacin ne Zahidaht ta zo ita da Kabir da Jawwad kuma a wannan zuwane ta tubure kan bazata koma ba. Duk da cewar iyayan nasu basu tambayeta dalili ba, amma kuma ramarta ta matuƙar tsoratasu. Ta ƙanjame kamar ba wace ta bar nijeriya ba. Kowa ya goyi bayanta, da aka matsa mata da san sanin dalili sai ta nuna musu ta fison kusanci da ahalinta ne. Mahaifiyarta kam bata yadda ba, binta kawai take da ido tana fatan ta sami sararin keɓewa da ita.

Dole Kabir yana ji yana gani ya haƙura ya barta, sai dai bisa turasassawar mahaifansu ya soma neman transper domin fara aiki a ƙasarsa sakammakon ya kammala karatunsa har ya soma aiki. An yi cuku-cukun karɓar transper zuwa ƙarshan shekara ya tattara ya dawo. Dawowarsa yasa ya rage yi mata abubuwa da yawa saboda idanun yan uwa. Sai dai kuma ta yi nadamar  dawowawarsu gaba ɗaya, domin  sai da ta zama ƙofar data bashi lasisin ƙuntata rayuwarta. Ta hanyar kisan mummuƙen da yake yi mata.Yusuf ya yi wa Labiba abin da bata taɓa zato ba, ranar data cika sati aranar ya yanka ƙaton ragonsa ya kuma shaidawa duniya ya maidawa ɗansa sunan Baba ɓaure. Kowa ya yi matuƙar farinciki musamman Amne, nan da nan wasu suka soma kiran yaron da suna Khalifa. Wasu kuma Yusuf takwaran Yusuf ɗan Yusuf jikan Yusuf, amma kuma masu kiransa Baba baure sun fi yawa. Sai dai Labiba ta fututtuke tace Khalifa sak za a kira mata ɗa.

Kwanci tashi mutuwar ta bi jikinsu gaba ɗaya, sai dai alhini irin na sabo. Amma banda Baba Ɗangaladima dan shi kamar zuƙarsama ake kullum cikin rama. Haka su Yusuf zasu tasashi gaba su yi ta bashi baki.

Lokacin da Labiba ta koma gidanta sai ya zamana ƙazanta ta ƙaru, da an yi magana ta hau zuba rashin kunya tana faɗin ba a tausayinta ba a ganin gwarnai ta yi. Tun Yusuf na kauda kai har ya soma kai ƙararta wajan mahaifinsa. Saidai kullum bayan Labiba yake bi, bawai dan wani abu ba, sai dan tuna cewa kadda dangi su ce ƙasa ta rufewa mahaifinta idanu ana yi mata badaidai ba.

Shi kuma duk ƙanƙantar laifi idan ya aikata mata, zata kira Amne da Khamis ta shirya ƙarya da gaskiya su kirashi ba tare da jin ta bakinsa ba su ci mutuncinsa son ransu. Yusuf sarkin haƙuri sai dai ya bada haƙuri, amma kuma abin na cin ransa gaba ɗaya ya zabge ya rame. Ga wata uwar ƙasumba da ya ajiye, haka kuma fatarsa ta ƙara duhu idanunsa sun zurma ciki sossai sun fidda wani kogo daya ƙara fito da aihinin sirrintakar hancinsa.

Cikin ƙanƙanin lokaci raini mai ƙarfi ya shiga tsakaninsa da Labiba, bata shakkar ta zageshi a gabansa hakama gaban abokansa da ƙawayenta. Har abin tinƙaho ya zamo mata sai yadda ta ke so ake yi agidan. Abinci idan ya kawo mata ƴar hausa ba zata dafa ba, idan kuma ƴar gwamnati ce to ba zata girka mai daɗi yadda zata yi armashi ba. Hasalima abinci ƙarshansa babbakewa cikin tukunya musamman data soma chats ya zamana yana ƙara ɗauke mata hankali. Sangarta kala-kala, wandunan kashin yaro kuwa bata wankewa sai sun taru ta kule a leda ta watsar a bola. A haka Khalifa ya shekara ɗaya da watanni Ummi kuma nada shekaru biyu da watanni.

***

MUSABABI.

A haka zamansu ya miƙa, sai dai yau da gobe taƙi gaban wasa. Duk ƙumbiya-ƙumbiyar Yusuf sai da dangi suka fahimci baya jin daɗin zama da mstarsa. Saida ya zamana babu wanda bai san matsalarsu ba. Duk inda aka zauna taro manya ciki kan ƙoƙarin bata shawara, musamman kan ƙazanta amma ƙarshe sai dai ta zagesu tas ta ƙara gaba abinta. Cikin tsakanin aka yi musu rabon gadonsu, dukiyar da aka samu ta girgiza mutane da dama, basu taɓa tsamanin dukiyar mahaifin nasu takai hakanba.

Kowace ɗiya mace saida ta tashi da naira miliyar arba’in da gida guda ɗaya banda kadarori. Shi kansa Baba Ɗangaladima abin ya shallake tunaninsa, bai taɓa kawo ɗan uwansa ya kai haka ba. Su Khamis nan da nan aka shiga faccaka da kuɗi, masu wayau ciki suka kafa sana’a wasu kuma suka shiga sharholiyarsu yadda suka ga dama.

Zahidaht na ɗaya daga cikin waɗanda suka bada dukiyarsu a juya musu, ƙwarai taso bawa Yusuf ya juya mata domin shi ne koma baya acikin ahalinsu amma mahaifiyarta ta fututtuke ta nuna bata lamunta ba. Sai dai hakan baisa ta fasa niyyarta ba, a ɓoye ta siya masa sababbin kekuna aka gyara shagon dayake haya aka zuba masa su. Tare da bashi naira dubu hamsin ya kafa jarin kayan ɗinki a shagon. Ranar ya yi kuka irin wanda bai taɓa yi ba, ta kuma roƙi alfarmar ya zama sirri daga ita sai shi da mahaifinsa da yaya Asabe suka sani. Sauran kuɗin kuma ta dunƙule ta miƙasu ga mijin Yaya Asaben ta ce ya juya mata, anyi takarda da shaidu da komai kuma gaban jagororin gidan.

Wannan abu data yi ya ƙuntata ran Kabir kamar ya yi hauka, domin shi ya baje sai lallaɓata yake yi, salon kulawa kala-kala yana tsarin ta gama zuwa hannu har mota sai ta siya masa. Aikuwa ranar data miƙa dukiyarta ga Yaya Adam kaɗan ne bai yi hauka ba, ga Jawwad na ƙara tunzurashi. Ranar yini suka yi a club ya sha syrup ya yi tattul ya nufo gida, duka ya yi mata na fitar hankali tare kyakkyawan gargaɗi kan ta amso kuɗin amma ko a ƙafar silifas ɗinta kuma ba wanda ta kai wa ƙara. Ta yi alƙawarin tunda Yaya Asabe bata goyi bayanta ba, ba zata taɓa buɗe baki takaiwa wani ƙararsa ba. Duk ranar da ubangiji ya nufa zasu fuskanci wa suka bata matsayin miji to zasu fuskanta ba tare da takai ƙara ba. Ƙila hakan ya ankarar da su KUSKURAN da suka tafka daga su har ita. Musamman data ga yadda lamarin Labiba da Yusuf yake tafiya sai ya ƙara mata ƙarfin guiwar cewa, ko ta kai ƙara dai bayan Kabir za a bi.

Ɓangaren Labiba kuwa, duniya sabuwa dal gareta, gidan da suke zaune ciki nan ne ya zama gadonta. A ranar da aka mallakamata shi a ranar ta tsira Yusuf ya bata takardunsa domin suna hannunsa. Fes ta ke jin ranta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta dinga wasa da dukiya. Gwala-gwalai ta siya, a je gidan biki a yi ta iyayi ana ɗaga kai. Ta sake kayan ɗaki biy biyu, wato ya zamana two bedroom. Sai dai kayan basu je ko’ina ƙazanta ta nakasusu, musamnan da ya kasance na dubai ta saka. Su kuwa suna buƙatar kulawa. Haka kayan kallo da duk wasu nau’in kayan amfanin gida ta sauyasu kamar wata amarya ga danƙareriyar waya.

Ƙawaye kansu sababbi ta sake ƴan yayi. Ganin tana ɓarnar kuɗi ne, Amne ta ƙwace kuɗinta ta damƙawa Khamis yayanta aka soma juya mata da yake harkar gwala-gwalai yake yi. Kwatsam Zahidaht ta je mata da shawara kan me zai hana ta ba wa Yusuf kuɗinta ya juya mata, ranar da uwaka ubanka suka rabu. Har tana goranta mata me ya hana ita ta ba nata mijin tata dukiyar? Wannan abu ya ba ta mamaki ƙwarai da gaske, domin me ɗaki shi ya san inda yake masa zuba. Ta sha alwashin badan alƙawarin da ta yi wa zuciyarta ba, da sai ta bambancewa Labiba tazarar dake tsakanin Kabir da Yusuf.

A taƙaice dai Labiba sai ta miƙe ƙafa ta sake sabon zubin rashin mutunci. Girki bata yi saita ga dama, take away take yi ita da yaranta. Hidimar dangi kuwa idan ana yi matuƙar bata ƴan ɗakinsu bace sai ta mula take zuwa. Yusuf ya zame mata hoto bashi da ƴancin tsawatar mata zata ci zarafinsa, agaban ƴaƴansa. Tun Ummi bata fuskanta har ta soma fuskanta domin ta yi wayau ta shiga shekara ta biyar Khalifa kuma huɗu. Idan ta zauna a waje sai ka ji tana,

“Ummunmu tana sa babanmu kuka!”

Idan yaro ta samu suke wasa sai dai ka ji tana tambayarsa,

“Mamanka tana sa babanka kuka?”

Haka ma idan babbane ba take masa wannan tambayar. Ranar data yi wa Nazira tambayar a gaban Yaya Asabe ba ƙaramin kaɗuwa Yaya Asaben ta yi ba. Ta ja Labiba ta dinga yi mata faɗa tare da nusar da ita KUSKURAN da take aikatawa na yin komai gaban yara. Ta nuna kamar ta ji, amma koda suka dawo gida mugun duka ta yi wa Ummin wanda ya fusata mahaifinta ya zage ƙarfinsa ya naɗa mata nasa dukan. Ai kuwa ta ji jiki matuƙa.

***

Kamar yadda muka sani a al’ada ƙaratowar azumi kowane magidanci yana hoɓɓasa a gidansa. Hakama Yusuf ya kasance mai tsayuwa tsayin daka wajen ganin ya wadata gidansa, sai dai wai a banza man kare in ji ƴan magana. Ko kaɗan bai ɗaɗa Labiba da ƙasaba hasalima a raine ta karɓi kayan. Har aka yi azumi huɗu biyar zuwa goma bai san samun abin buɗa baki daga gidansa ba, sai dai Asiya yarinyar da yake haya a shagon gidansu tana ƙoƙarin kawo masa kunu Alla bashi shi kuma yana siyen ƙosai da dabino. Sossai yake mutunta Asiya da mahaifiyarta bisa karamcinsu.

Lokacin da aka shiga hidimar sallah sai ya zamana aiki ya soma rincaɓewa Yusuf, ɗinkuna sun soma yi masa yawa baya samun dawowa da wuri, amma abin takaici duk lokacin da zai dawo sai ya samu ta garƙame gida da sakata. Idan ya yi magana kai tsaye zata ce,

“Gidanka ko nawa?”

Tun ba ajin kansu game da hakan har ya kai ga ya kai ƙararta, sai dai ga mamakinsa kadda baki Baban nasa ya yi ya tambayeshi,

“Yusuf tun nawa ka ke fita?”

Ya bashi amsa da cewar,

“Baba asuba ne”

“Ka dawo nawa”

Sai da ya yi jim, sannan ya amsa,

“Ina kai biyu saboda yanayin aikin namu!”

Kai tsaye mahaifin nasa ya maida dubansa kanta,

“Labiba ƙarfe nawa ki ke so ya dawo?”

Babu kunya ta amsa,

“ko bai sha ruwa gida ba Baba kadda dai ya wuce tara!”

“Yusuf”

Mahaifinsa ya kirashi da kaushin murya, ya amsa kansa a ƙasa yana jin wani irin raɗaɗi da ɗaci tun daga ƙasan zuciyarsa,

“daga yau idan ka wuce tara a waje Labiba zata rufe gidanta!”

Ɗas! Gabansu ya faɗi su duka, Labiba maimaita kalmar take cin ranta,

‘Gidanta! Gidanta!! Gidanta!!!’

Tana ji kamar Baban magana ya faɗa mata, amma suita dake tare da yi masa godiya suka nufi gida. Tun daga wannan rana Labiba ta sake samun lasisin cin fuskar Yusuf son ranta. Haka aka kusa gama azumi gaba ɗaya yana kwannan shago, ya zamana tun kafin maɗinka su soma kwanan shago shi ya soma. Saboda idan ya dawo, sai ya shefe mintuna sittin yana bugu da kiran waya amma ba zata ko ɗaga ba. Kuma ba zata buɗe masa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *