WATA MACE CHAPTER 4 BY SANA S MATAZU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ƙara ƙanƙame wayar ta yi a kunnanta, hawaye masu zafi na zubar mata. Maganganun Yaya Amina na shigarta, kowace gaɓa amsar saƙon take bawai dan ta gajiya da yawan amsar ba. Amma kullum ana kira mata lokaci-lokaci tana san sanin yaushe ne?+
“Zahidaht!”
Ta faɗa da murya mai amo,
“Nasan ke ake zallunta, amma hakan ba zai sa in ƙi baki haƙuri ba, wata rana sai labari. Duk wani yunƙuri da zaki yi yanzu ba shi da wani alfanu. Labiba ta riga da ta bugawa ahalinmu tambarin da ya zame mana baƙin fenti”
Lumshe idanunta ta yi tana jin tsanar hallayar Labiba har cikin ranta. Ita kuwa ba dan an tabbatar mata da ta haɗa uba da ita ba a yau da ta yi shellar ta cire Labiba daga cikin ahalinta, ƙila koba komai ta samu sassaucin tata rayuwar auran, domin ta lura da ita Kabir ke amfani matsayin makamin kassara ƙumajinta. Ido ta sauke akansa lokacin da ya sawo kai ɗakin. Tabbas a buge yake kuma ba zata yi sakaci ya daketa a hofi ba.
***
Kai kawo yake yi tsakanin ƙofar shiga gidan da sitroom, gaba ɗaya rigarsa ta jiƙe da gumi. Ba komai ke ɗaga masa hankali ba face kukan karnukan da ke tashi. Kwanansa a waje ba matsala bane, sai dai be san illar da zasu yi masa ba. Ya sake duban agogonsa, a yanzu ya share awa uku kenan yana kiran wayarta tare da buga ƙofar gidan. Babu ɗaya da ta yi cikin abu biyu zuwa ukun da yake buƙata. Buɗe ƙofar ko kuma amsa wayarsa ya san halin da ɗiyarsa ta ke ciki kawai ya wadace shi basai ya kwana gidan ba. Haka saƙwanin magiyar da ya ke jera mata babu wanda ta amsa masa. Kansa ya ci gaba da sarawa idanunsa suka kaɗa.
Zuciyarsa ce ta doka da wani irin karsashi lokacin da ya ajiye kallonsa a bangon gidan. Wata inuwa ya hanga doguwa tana nufoshi, idan ba gizo idanunsa suke yi masa ba hadda leda a hannun inuwar. Duk wata addu’a da ya taɓa sani a rayuwarsa ya shiga karantowa.
Jikinsa ban da karkarwa babu abinda ya ke yi, kamar almara ya ji sautuka biyu a daidai lokacin da ya fitar da tsamanin ya yi gamo,
“Baban Khalifa me kake yi anan, ga dare ga kuma karnunkan nan marasa kirki?”
Garam! Sautin zare sakatar gidan ya sauka a kunnansa. Ajiyar zuciya ya saki, yana ajiye kallonsa a saitin maƙocinsa Malam Ali,
“Wallahi Ummi na siyowa magani, ina ga bacci ya ɗauke Mamanta, amma ga shi nan ta buɗemin ƙofar!”
“Asha”
Ya furta da fuskar alhini, domin su ɗin sababbu ne wajen jin yana buga ƙofa duk lokacin da zai dawo. Tun suna yi wa matarsa uzuri shi da maiɗakinsa har suka dangana abin da rashin tarbiya. Ba yau ne farau ba da zai share awoyi yana haƙƙilon buga ƙofa, sai dai duk lokacin da tsautsayi zai haɗaku ka tambayeshi zai yi ƙoƙari wajen kare iyalinsa ta hanyar uzururruka da yawa,
“ni ma dubiya ce na je, kuma na rasa abin hawa da wuri, ayi mata ya jiki don Allah. Sai da safe”
“Na gode Allah Ya kaimu”
Tana tsaye ƙyam tana sauke masa kwandon harara, ba tare da ya kalleta ba ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan. Ummi na kam kujera duk ta sauya yanayi. Ban da rawar sanyi babu abin da take yi. Da hanzari ya ɗagota sai amai, tun tana yi da ƙarfinta har ta kwanta jikinsa. Tana tsaye tana kallonsu sai huci ta ke, bai bi ta kanta ba ya gyara yarinyar ya bata fresh milk da magungunanta. Ya kaita ɗaki cikin ƙannanta tare da tofesu da addu’a ya fito. Bai nufi wajen abinci ba, yana da yaƙinin bazai samu ba, leda guda ya ajiye gabanta ya wuce ɗakinsa da guda. Babu kunya ta ɗauƙa ta wuce tana ƙunƙuni.
Sai da ya tabbatar da cikinsa ya ɗauka sossai, sannan ya miƙe ya ɗauro alwala ya hau abin sallah. Ya jima yana kaiwa ubangiji kukansa daga bisani ya yi shirin kwanciya. Juyi ɗaya biyu ya kai hannu sashin da ya kamata ace anan take amma wayam! Babu alamunta, ya san za a rina abu ne da bai kamata ace ya yi mamaki ba, amma kuma ya zai iya da yanayinsa? Shi kam ko karan hauka ya ci je shi ba zai kai kansa ɗakinta ba domin yasan ƙamshin mutuwa zai shaƙo. Runtse idanu ya yi yana jin wani irin abu a ƙasan zuciyarsa, a haka bacci ya yi awon gaba da shi…
***
“Yaya Amina ki zauna mana”
“In zauna Laby? Ai banga wajen zama anan ba, zuwa na yi in duba Ummi dan jiya tare aka kaisu kyamis da Nazir ɗina”
Ta faɗa tana ajiye mazaunanta kan kujerar da ta fi aminta da ita, sai dai zumbur ta miƙe sakammakon zama kan malellen fitsari har da ɗigon kashi. Kallonta take da zallar mamakin hallayarta, ji take kamar ta shaƙeta ta mutu kowa ya huta da baƙin cikinta, dariya take tana ƙarawa cike da nishaɗi,
“Wallahi yaya Amina bata jin daɗi, amma da sauƙi”
“Ina Baban nata?”
Ta faɗa tana nufar hanyar ɗakinsa, domin tasan anan ne zata sami sa ida. Sai dai bata ƙarasa ba saboda abin da kunnuwanta suka jiyo mata.
“Rabona da shi tun jiya dana horashi da tsayuwar awoyi a waje”
Mamaki ya daskarar da ita, bata bari ta cigaba ba ta tanka,
“Labiba wai yaushe zaki sauya ne?”
“Sai ranar da ɗan uwanki ya sauya kashin awaki. Wato ni gandun laifi ko? Hmmm! Ai wallahi naso karnukan jiya sun manna masa hauka! Ban da wulaƙancin ƊA NAMIJI awa nawa ina jiransa? Daga siyo maganin Ummi mutum ya shuri awa biyu da rabi”
“Amma dai Labiba baki da mutunci, kin tambayi dalilin jinkirinsa ne? Saboda kin samu mutum lako-lako sai ki dinga zuba wuƙalancinki son ranki. Kina sane fa da yadda ƴan kwanakin nan ake fama da wannan zazzaɓin ma maja, to tabbas jiya agun magani ya ja lokaci saboda Baban Nazir ya je kai Nazir allura tare suka dawo shi ya sauke su a gida a mashin ɗin sa”
Turo baki ta yi kamar shantu,
“ya dai sauke su ya tafi hidimarsa, ai wallahi tunda Baba Ɗangaladima ya bani goyon bayan rufe ƙofa idan ya wuce ƙarfe tara, wallahi ya dinga kwasar takaici kenan! Ni da GIDANA ba zan ɗauki tijarar ƊA NAMIJI ba. Naga alama idan na biyeku wahala zan sha,kawai ku komai sai ku ce mutum ya yi haƙuri wata rana kuwa sai dai a riski gawar mutum haƙurin ya kashe shi”
Galala take dubanta yaro da wayau, tabbas ta yi nisa bata jin kira sai dai addu’a. Duk yadda ake faɗar hauka da gaɓoncin Labiba bata kawo ya kai haka ba, tabbas ta ƙara sallama mata da hallayarta. Da gudu ta shigo ɗakin tana shassheƙar dariya, faɗawa ta yi kan kujerar da mahaifiyarta take kai,
“Ummi kin ga yaya Shukura zata dokeni ko!”
Ta furta tana ɓuya a bayan mahaifiyar tasu. Gyara zaman gilashin idanunta ta yi tana murmushi,
“Wasila ba kwa jin magana ko? Wai Shukura bata girmeki ba, amma kin mayar da ita abokiyar wasanki. Haka zaku tafi Sakwaton ku je kunata saka Yaya magana ko?”
Da hanzari ta sauko ƙasa, ta tanƙwashe ƙafafu tare da zuba dukƙan hannayenta a fuskarta. Ta marairaice fuska kamar wata me neman taimako, tare da kama kunnuwanta dukka biyun.
“Na tuba Ummi kimin rai, dan kina iya cewa ba za a je dani ba kadda a je a dinga sa miki wannan farin tsohon naki magana”
Duka ta kai mata, ta kauce tana dariya da buga ƙafa, daidai shigowar mahaifinsu ta tafi da gudu ta ɗaneshi. Har lokacin dariyar take yi. Ummi kuwa ta shaƙa sai ƙwafa take yi,
“Ummin yara ke da mutuniyarki kuma yau?”
“Abbu wai dan na ce farin tsoro shi ne fa..”
“Wannan da ki ka maƙalƙale ne farin tsoho rasai..”
Ummin ta tareta, ai kuwa daga Shukura har Abbun da Wasilar suka kwashe da dariya suna kyakkyatawa. Sai ta miƙe ta bar musu ɗakin. Sai da suka tsagaita sannan mahaifin nasu ya dubi yaran. Ɗakin mahaifiyar tasu ya nuna musu da hannu, Shukura ra noƙe kai tana taɓe baki. Wasila kuwa sai ta mirgina kai kamar marayan ɗata tare da haɗe hannaye biyu. Sai dai yadda Abbun nasu ya yi yasa suka ƙara kwashewa da dariya. Sai kace wani yaro. Daga ƙarshe dai suka ɗunguma zuwa ɗakin baki ɗayansu. A zaune suka sameta tana gyara takardu.
Sai suka tsaya turus kowa na shakkar matsawa kusa da ita, Wasila ce ta zaga ta baya ta ɗane wuyanta tare da sakalo hannayenta dukka biyun. Ai kuwa da hanzari Shukura ta zauna a gabanta tare da rike hannayenta dukka biyun. Abbu kuwa sai ya tanƙwashe ƙafa tare da kama kunnuwansa yana kashe mata ido. Gaba ɗaya sun dabaibayeta ta kasa motsi. Kowane da irin motsin da yake wanda ya ke nuna mata nadamarsa. Dan haka sai ta sare,
“bazan haƙura ba!”
Ta furta tana ƙunshe dariya. Wasila ta yi wani zilo,
“Ummi Abbu fa cewa ya yi in dai baki haƙura ba…” saita ɗora hannunta kan bakinta tare da furta”au suɓul da baka!”
Dungureta ta yi da hannu,
“Me ya ce?”
“Wai dama wannan ƙawar taki data liƙe masa ita ce..”
But! Ta bige bakinta, ai kuwa suka kwashe da dariya. Itama sai ta biyesu tana dariyar dan sai lokacin ta ankare da abin da ta yi, gaba ɗaya suka haɗa baki suna faɗin,
“Ta haƙura ta haƙura”
Shukura ce ta kama hannun yar uwarta,
“Sililiya mu je mu ƙarasa haɗa kayan tafiyarmu!”
Fita suka yi suka bar iyayen nasu, ya muskuta tare da ƙureta da kallo,
“Anya zani Sakwaton nan kuwa Hadiza? Kwanaki uku babu ke kusa da ni akwai gyara!”
Ya ƙarasa yana langaɓe kai kamar ƙaramin yaro. Hannu tasa ta kama kunnansa tare da murɗawa a wasan dare. Shi kuma hadda wata ƴar ƙara irin da zafin nan,
“Love da zafi fa”
Zare idanu ta yi tana kallon ƙofa wai kadda yara su ji. Dariya ya yi tare da shafa kuncinta,
“Oya kin iya cutata da kunya kin iya bigeman bakin ɗiya dan tace zan auro wayis ko?”
Duk sai suka saki dariya su duka biyun. Haka suka kasance wajen cin abinci ma cike da farin ciki ba abinda suke sai hirar tafiyar su Shukura.
Alhaji Abdurrahman asalinsa mutumin Sakwato ne, matarsa Hajiya Hadiza ita ma ƴar asalin garin ce. Aikine ya kawoshi Kano yana koyarwa a B.U.K. Mutum ne mai rufin asiri, bayan aikin gwamnati yana haɗawa da kasuwanci lesuna da shadodi. Daidai gwargwado ya tsayawa yaransa kan tarbiya. Yaransu biyu, Shukura ita ce babba tana matakin level one tana karantar business admin. Sai Wasila mai bi mata tana matakin ƙarshe a makarantar secondary. Sun jima Allah bai basu haihuwa ba, dan haka suna ƙaunar yaransu sossai. Saidai ƙaunar da suke musu bai dakusar da hoɓbasar ɗorasu kan kyakkyawar tarbiya ba. Matarsa mace ce mai kirkir ga kawaici da kunya, komai ɗayansu zai yi ya kan yi shawara da ɗaya. Zamansu gwanin sha’awa. Duk shekara sukan shirya tare da iyalansa a can garin Sakwato suke yin sallah su gaisa da ƴan uwa. Wannan karonma suna shirya-shiryan tafiyane shi yasa su Shukura suketa zumuɗi.
Tun da ya rage saura kwana biyu tafiyar suketa shiri. Sun yi soye-soye da dama na dangin kayan fulawa da sunan tsaraba. Washegari da sassafe suka ɗauki hanya cike da farin ciki. Suna tafe suna hira da mahaifinsu a hanya. Akwai fahimtar juna sossai tsakaninsu da iyayansu haka ko damuwarsu basa iya ɓoye musu. Gefin la asar suka sauka. Nan da nan ƴan uwa suka shiga hidima da su, musamman da suka kasance masu san jama’a kowa nasu ne. Shukura da Wasila gidan Baba Magajiya suka sauka saboda ɗiyarta Asiya, sossai suke mutunci da ita kuma akwai shaƙuwa tsakaninsu.
Bayan gaishe gaishe da hirar yaushe gamo, kowanensu ya miƙe yana neman huce gajiya. Washegari da su Shukura aka ɗauki azumi, ranar da zasu zo ne dai suka ajiye saboda halin tafiya. Tare da Asiya suka shirya kayan buɗa baki, komai ya yi musu yadda suke buƙata, ana gab da shan ruwa Asiya ta soma neman yaron da zai kai wa Yusuf kayan buɗa baki amma ta rasa. Tilas tasa hijabinta da zumar kai masa da kanta. Shukura ce ta yi zuruf ta bita, tare suka jera tana yi mata ƙorafin data zauna ba nisa zata yi ba. Dariyar wasa ta saki tana faɗin,
“kodai ba kya son in je in miki kwacen saurayi. Ai na ji Gwaggo ta ce kullum ke ki ke aika masa da buɗa baki!”
Dukan wasa ta kai mata,
“zuciyata na riga na bada riƙonta ga Ahmadina shi kansa ya san da zamansa taimako kawai nake yi!”
Dariya suka sa gaba ɗayansu, Shukura tace,
“Yauwa sis ni kuwa ina zamu kai ɗinkinmu? Mun zo da lace da atamfa da kuma shada wadda zamu yi anko mu uku hadda ke”
“Baki da matsala wajen tela zamu…”
Daidai lokacin suka ƙaraso bakin ƙofar shagon Yusuf, samu suka yi yana alwala. Sai da ya kammala suka gaisa Asiya ta miƙa masa kayan buɗa baki. Karɓa ya yi yana zuba mata godiya da sa albarka. Idanun Shukura kan ɗinkunan shagon tana yaba fikirar mai shagon.
“Baƙuwa muka yi ne..”
“Eh daga Kano suka zo, zama mu kawo ma ɗinkinsu anjima ayi haƙuri mun zo a ƙure baƙi ne..””
Sai lokacin Shukura ta sauke idanunta akansa, ɗas gabanta ya faɗi. Wani irin kwarjini Yusuf ɗin ya yi mata. Mamaki take zuƙeƙen saurayi haka ya ɓige a ɗinki, lallai bashi da girman kai. Da hanzari ya ɗauke kansa jin yadda zuciyarsa ta buga lokacin da suka haɗa ido,
“Ke baƙuwa ba ki iya gaisuwa ba, a haka zan yi miki zuran layin ɗinkin?”
Firgigit ta ɗauke idanunta daga ƙaramin hoton Yusuf da yaransa data zubawa ido, shi ma ya lura da kallon da takewa hoton. A ranta kuwa tana ƙisima ƙila ƙannansa ne ko ɗiyan yayyunsa. Sai ta ji hausarsa ta bata dariya, ta kuma burgeta. Karon farko da ta ji daɗin hausar Sakwatawa domin ta maidasu ababben tsokanarta har faɗa suke yi da Asiya. Murmushi ta yi tana jin kunyar rashin gaisheshi da bata yi ba. A kunyace ta gaisheshi suka wuce. Rakasu ya yi da idanu wani irin yanayi na saukar masa. Suna tafe Shukura ta kasa haƙuri,
“wai Asiya wannan ne telan?”
“Shi ne me kika gani!”
“Ba komai”
Ta bata amsa a taƙaice. Haka suka ƙarasa gida, bakinta ya yi mata nauyi akwai abubuwan da takeson tambaya da yawa akansa amma kuma tana jin nauyin tambayar Asiyan domin dai ita dai mamaki take yi, matashi kamarsa yana ɗinki kuma Asiya ta ƙara tabbatar mata da family nasa babban family ne a garin Sakwato. Suna shiga gida suka yi alwala suka yi sallah. Daga nan suka baje anata hidimar buɗa baki tare da hirar yaushe gamo. A haka aka kira sallahr isha’i matan suka bi jam’i mazan kuwa suka wuce masallaci.
Ƙarfe tara daidai, suna zaune a tsakar gida saboda zafi da suke ji sakammakon ɗan ɗagawar hadari. Hira suke a hankali wani yaro ya yi sallama,
“Assalamu alaikum. Wai gashi in ji Yusuf”
Amsawa Asma’u ta ti haɗe da karɓar kwanukan, fes dasu a wanke. Murmushi ta yi tana yaba tsaftar Yusuf ba su taɓa bashi abin ɓuɗa baki ba, ba tare da ya wanke kwanon ba. Sai yaron ya miƙo mata leda baƙa. Ta karɓa tana mamaki, kafin ta yi magana ya furta,
“ya ce don Allah kadda a dawo dasu, hijabaine na Muhammad ne babu yawa sai kuma Gwaggo”
Kafin ta sami zarafin magana yaron ya fice, Gwaggo na ƙwalla kira ko ya juyo saboda ya gargaɗeshi. Wasila ce ta yi zuruf ta buɗe ledar sai ga ɗinki daidai da autan Gwaggo Muhammad Arif. Sai kuma hijabi dogo mai kyau da tsari. Sossai abinda ya yi ya faranta ransu. Ko ba komai ka gaishe da me gaisheka koda ba zai amsa ba. Haka suka cigaba da hira, wanda rabinta Gwaggo ta ɓige da bata labarin halin kirkin Yusuf da yi masa addu’ar samun mace tagari. Domin tasan komai da yake faruwa da shi kasancewar tana da ƴar alaƙa da Amne ta siye da siyarwa.
Sossai Shukura ta tsume tana mamaki da al’ajabin irin rayuwar da yake yi da iyalansa. Iya tausayi ta tausayi ta tausaya masa. Ji ta yi gaba ɗaya hirar ta gundureta ta rasa abin da yake mata daɗi. Jan Asiya ta yi suka koma ɗakinta. Wasila kuwa ta baje tana kakabin halin Labiba. A wajen kwanciya dai Shukura kasa jurewa ta yi ta muskuta tana duban Asiya,
“Wallahi Asiya sai na ji ina ƙaunar in ga matar mutumin nan haka kawai”
Kallon mara wayau ta yi mata, sai kuma ta gimtse fuska,
“uwar karambani ki yi mata me?”
“Ko ɗaya bani da abin da zan yi mata, kawai so nake na ganta”
Murmushi ta saki,
“kinyi sa a gobe Gwaggo zata aikeni unguwarsu wajen surukarsa sai mu san dabarar da zamu yi mu shiga gidan”
Lumshe idanu ta yi tana ƙiyasta Labiba a zuci da idanunta. Washegari da safe suka kammala duk wani aiki daya danganci gyaran gidan. Shukura tsaf ta zage aka yi komai da ita. Duk yadda Asiya ta so ta huta ƙi ta yi. Wasila kuwa gado ta ɗare tana sharɓar baccinta. Misalin ƙarfe sha ɗaya suka karɓi aiken Gwaggo suka ɗauki hanyi. Tafe suke suna hira Asiya na ƙara nuna mata wasu wuraren tare da bayaninsu. Sha ɗaya da arba’in a fallon Amne ta yi musu. Basu wuce mintuna goma ba suka yi abinda ya kaisu suka fito. Tunda suka fito Shukura take bin Asiya da ido. Ta matsu ta ganta a gidan Labiba. Suna gab da shiga kwanarsu suka yi kiciɓis da shi ya fito hannunsa riƙe da Khalifa. Da murmushi kan fuskarsa yake ƙarasowa wajansu. Asiya ta saki ajiyar zuciya. Domin gaba ɗaya kanta ya ɗaure tana tunanin yadda zasu shiga gidan su awa? A mutunce suka gaisa, Shukura da take ƙoƙarin sunkuyar da kai ƙasa yake zolaya,
“Bakuwa me rowar gaisuwa!”
Duk suka yi dariya, ta miƙa hannu tana faɗin,
“Fine boy ina mamanka?”
Babu jinkirtawa ya miƙa mata Khalifan, daketa zuba ƙamshi. Can ƙasan ansa yana gode wa Allah da ya yi masa wanka duk da kukan da yake yi. Domin ko sisi bame siyansa haka suka wayi safiyar. Idanunsa akan Shukuran daya nace da kallonta,
“Allah Asiya yau dai sai kin shiga gidan iyalina!”
Dariya ta ɗanyi, kasancewar ya sha yi mata tayin hakan tana dojewa. Ba musu ya yi musu jagora suka rankaya suna taɓa hira shi da Asiyan. Da sallama suka shiga, daidai lokacin ta fito banɗaki daga ita sai zani ɗaurin ƙirji. Kanta babu ɗankwali sai kitson da ya kasance rabi a kitse rabi a kwance. Ummi da ta ke zaune kan abin sallah ta nufo mahaifinta. Ita ma tanata zuba ƙamshi. Hannunta ya riƙe, ya sauke idanunsa kan Labiba da take dubansu a yatsune. Lokaci daya takaici da kunya suka yi masa rufdugu. Ya dubeta murya a tausashe,
“Maman Ummi baƙi ne damu”
Sai da ta mula tukuna ta tanka,
“Nagansu!”
Daga haka ta sa kai ɗakinta. Asiya ta yi wa Labiba kallon kin gani ko? A sace ya kallesu sai dai ganin babu sauyi kan fuskokinsu yasa ya ɗan ji dama-dama. Jagora ya yi musu zuwa ɗakin nata duk da bashi da kyan gani. Haka suka zauna a tsume babu wata mutuntawa. Ganin babu sarki sai Allah suka yi masu sallama suka wuce. Shukura dai ta ƙara tabbatar da maganar Asiya saidai zuciyarta bata bar mamakin wautar Labiba ba.+
STORY CONTINUES BELOW
***
Cikin ƙanƙanin lokaci Yusuf da Shukura suka yi wata irin shaƙuwa. Har ta kai yana bayyana mata matsalar da yake fuskanta da Labiba. Kodayaushe takan nusar dashi yi mata uzuri tare da ƙarfafa masa guiwa wajen ɓoye sirrin gidansa. Ta ɓangaranta kuwa tun dawowarsu Sakwato ta kasa gane yanayin da zuciyarta take ciki tsakanin ƙaunar Yusuf da kuma tausayinsa. Sukan ɗauki lokaci suna waya da shi, ko shi bai kirata ba ita zata kirashi. Haka Ummi yakan haɗasu awaya suna gaisawa. Duk lokacin da zasu yi aike Sakwato kuwa zata tsarma wani abu ta ce da Asiya a aikawa Yusuf ya ba wa Ummi tun tana yi mata tsiya har ta sa mata ido.
Shi ma a nasa ɓangaren gaba ɗaya ƙaunar Shukura da ɗabi’unta ya zagaye zuciyarsa ya hanashi sakat. Sai dai yana tunanin yadda zai wanye da Labiba. Ba ya waya da ita sai yana waje, haka yakan gargaɗi Ummi kan faɗawa Mamanta tana waya da Aunty Shuu! Kamar yadda take kiranta. Sossai ya maida hankali kan sana’arsa Allah alhakeem kuma ya sa masa albarka, yana samu sossai domin har mashin irin na matasa ya saya. Ummi ya sauya mata makaranta zuwa ta kuɗi, haka kuma ya buɗe center yana yi wa yara training kan ɗinki, tare da siyar da form kan farashi mai rahusa. Nan da nan wajen ya karɓu sossai.
***
“Kai ma Jawwad kasan halina wallahi, ai tunda ta nuna min ita muguwa ce ni nafita iya mugunta. Wallahi bazan bari ta samu abinda take ƙulafuci ba. Ba dai haihuwa take buƙata ba, to kuwa matuƙar ba zan ci dukiyarta ba ba zan daina zama sanadin zubewar abin da take muradi ba. Na lura akwai shigar ciki a tare da ita kuma shi ma sai ya bi rariya”
“Amma Kabir zuwa yanzu fa ya kamata ace mun saduda, Mun soma girma ni wallahi tsoronma na yi aure na haihu nake yi kadda a rama kan yarana. Gashi gaba ɗaya dangi sun ɗoramin karan tsana, in samu ko ƴar bazawara ma abani an ƙi. To dangi ma sun ƙi ni ina ga waje. Kai gara kai babu wanda ya fuskanci haƙiƙaninka sai matarka”
“Ka cika yawa Jawwad kana nufin wai yanzu kai tuba zaka yi? Mtsss! Ni ka zo ka rakani in karɓo maganin kawai…”
Da sauri Zahidaht ta yi baya ƙirjinta na dokawa, ko ba a faɗa mata ba yau ta gama fahimtar Kabir ne sanadin ɓarinta. Hannunta tasa ta toshe bakinta, a ƙoƙarinta na maida kukan daya taso mata. Kaicon rayuwar son rai irin ta Kabir ashe duk wahalar da take sha shi ne sanadi. Kuma tsabar rashin imani bai taɓa tausaya mata ba. Sake runtse idanunta ta yi ta juya zuwa ɗakinta tana daddafa bango. Yau tana hango KUSKURANTA matuƙa wajan sakayawa ahalinta aihinin waye mijinta. Tana jin tashin motarsa wani zazzaɓi ya sake rufeta. Sai dai yau ta ƙuduri ko zai yankanta sai ta ga bayan ƙudurinsa. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa ta hau bincikar lokokin da ya ke ajiye magunguna. Ta himmatu wajen binciken Allah ya bata sa ar abinda take san gani ta gsnoshi. Ɗauka ta yi tana murmushi tana share hawaye,
“Kabir na sami makamin yaƙarka da izinin Allah”!
Ta yi furucin kamar tana gabansa. Juyowar da zata yi idanunta ya sauka akan nasa idanun. Take ta firgita sai kuma ta gimtse. Hannu ya miƙa mata fuska babu annuri. Ta ja baya tana furta,
“wallahi bazan bayar ba domin shi ne hujjata ga Baba Ɗangaladima..”
Bata karasa ba yasa hannu ya hankaɗata, ta yi hantsile gefan gadonsa ya daki cikinta. Ta ƙwala ƙara ta zube ƙasa. Kanta ya yi a kiɗime amma bata ko motsi. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba.
***
Kwanaki biyu kenan suna tafka tsiya da Labiba saboda fuskantar yana waya da mace. Rashin mutunci take zubawa son ranta. Sai dai ko ɗaga kai baya yi ballantana ya dubeta. Hasalima shi a waje yake wayarsa gudun fitina amma haka zata leƙo ta baranda tana jifansa da duwatsu kamar wata yarinya. Wani lokacin kuma ta kule gidan sai dai ya kwana a waje.
Kamar kodayaushe yau ma yana dakalin ƙofar gidan yana waya. Shukura ce take bashi labarin sakammakon jarabbawarta suna ta nishaɗi abinsu. Zuwa lokacin daga shi har ita sun fahimci suna san juna amma sun gaza bayyana hakan. Kamar amafarki ya hango tahowar Labiba tana sanɗa zata rufe masa ƙofa. Saurin miƙewa ya yi ya shammaceta ya tura ƙyauran. Aikuwa ta yi taga-taga zata faɗi ya tarota jikinsa. Hannu tasa ta turashi ya bige da bango kansa ya fashe daga gefan goshi.
“Ash!”
Ya furta yana sauke wayar, daga can Shukura na tambayarsa lafiya, kafin ta sake magana ta tsinkayo muryar Labiba tana aunamasa zagi,
“Wallahi Yusuf baka isa ba ka na yi min waya da karuwanka A GIDANA!”
Hannu yasa ya tankaɗata saboda yadda kansa yake zubar jini. Gefe ta yi tana hucci su Ummi sun yi cirko-cirko suna kallonsu. Kai tsaye waya ta ɗauka ta dannawa Amne kira ta fashe da kuka. Ƙarya da gaskiya ta zauna ta shirya mata. Ga Yusuf nan ya yi mata mugun duka saboda ta kamashi yana waya da budurwa. Aikuwa kamar jira take, tana katse kiran ta kira Khamis tana rattaba masa buƙatarta. Babu jinkiri ya kwashi yayyanta maza na ƙasa dashi su biyar suka nufi gidan. Lokacin da suka je Yusuf yana tsaka da waya da Shukura tana bashi haƙuri kan abinda ya faru Labiba kuma tana ɗaki da yaranta. Basu yi wata-wata ba suka rufeshi da dukan kawo wuƙa. Mamaki ya kasheshi kan dalilinsu na dukansa. Tun yana ɗaukar abin a wasa har ya soma ƙoƙarin kare kansa.
“Me na yi muku?”
Shi ne abin da yake faɗa, sai dai sunƙi bashi damar da zai fuskanci laifinsa. Cikin mintuna goma suka sassaɓa masa kamani yadda baya zato. Tun yana motsi har ya zama sai dai ido. Acan ɗaki gaba ɗaya Labiba ta tsorata, domin tana kallon komai ta taga. Ummi kuwa banda kuka da kiran Abba babu abin da take yi.
“Labiba kwaso kayanki mu tafi!”
Ras! Gabanta ya faɗi, ita fa ba cewa ta yi azo arabata da mijinta ba. Kawai dai taso a ɗan tsoratashi ne ya daina waya da mata. Sai yanzu ma ta gano wautarta na kiran Amne tunda tasan ƙudurinta kan auransu. Dakewa ta yi ta fito tana ƙunƙuni tare da tallewa Ummi ƙeya. Sai dai tana fitowa ta tsandara ihu,
“Na shiga uku Yaya Khamisu kun kashe shi wallahi sharri na yi masa!”_Kowane sauyi ya kan amsa sunansa sauyi amma ya kan zo da sauƙaƙƙawar cikar mutuntaka matuƙar baya tafe da sauyin nagarta._+
Tsabar takaici kasa cewa komai Khamis ya yi. Kafin ya farga ta ɗauki waya ta kira Yaya Adam tana kuka. Bata ɓoye masa komai ba, hankali tashe ya bata tabbacin yana hanya. Sai dai duk yadda taso zama agidan har zuwan nasu bata samu ba. Ƴan uwanta suka tasa ƙeyarta tana kuka tana komai. Aka bar Ummi zaune gaban mahaifinta dake halin MUTUWA DA RAYUWA.
A kiɗime yaya Adam ya ɗaukeshi suka wuce asibiti mafi kusa. Ummi kuwa yaya Asabe ce ta tafi da ita. Ana shiga da Yusuf asibiti Kabir na shigowa da Zahidaht. Ka tsaye wajen taimakon gaggawa aka wuce dasu. Dukkansu basu san inda kansu yake ba. Baba Ɗanƙwairo da Baba Ɗangaladima nan da nan suka nufo asibitin. Gabaɗaya hankalin zuri’ar a tashe yake domin babu tabbacin halin da suke ciki. Jimawa kaɗan likita ya nemi ganin wani babba cikin dangin Zahidaht, Baba Ɗangaladima ne ya wuce gaba. Sai dai bayanin da likita ya yi masa ya kiɗimashi. Zuciyarta ce ta kumbura. Faɗa sossai likitan yake yi bisa sakacin da aka yi a take ya bayyana masa ana buƙatar ayi mata aiki da gaggawa domin cikin jikinta ya jirkita tana zubar da jini idan san samu ne suna buƙatar fitar da shi. Hankali tashe ya nemo Kabir domin ya saka hannu. Jikinsa a sanyaye ya sa hannu aka wuce da ita Kabir banda kuka babu abin da yake yi.
Wani irin yanayi yake ji akan Zahidahr. Gab da za a shiga da ita ta farka, babu wanda ta nema sai Kabir. Lokacin da ya zo kasa haɗa idanu da ita ya yi. Gashi ta kasa magana, so take ya kalleta koda sau ɗaya ne ko zai fahimci saƙon da ya ke cikin idanunta amma ya gaza. Lumshe idanu ta yi, wasu hawaye na kwaranya a kwarmin idanunta da suka sake cikowa maimakon zurmawar da kowa ya santa da ita. Wani abu ta ke ji da ba zata iya kwatanta yanayinsa ba, tunda take a rayuwarta bata taɓa jin yanayin ba. Haka aka turata aka wuce da ita. Yana jin yadda idanuwanta suke yawo akansa, sai dai nauyi da yake ji bazai bari ya aikata umarnin zuciyarsa akan nata ba. Sossai yake muradin su haɗa idanu sai dai lokacin da ya nufaci hakan ya makara…
Bangaren Yusuf suka sake komawa, shi da sauƙi ya farfaɗo amma ya sami karaya a hannunsa na dama. Sai kuma karaya a cinyarsa ta hagu. Ana tunanin dole sai dai a turashi asibitin ƙashi na Kano. Cikin ƙanƙanin lokaci asibitin ya ɗinke da ƴan uwa da abokan arziƙi. Sai dai kowa ka dubi fuskarsa jingum yake. Shuɗewar awa biyu da mintuna likitocin da suka shiga da Zahidaht suka fito suna sharce gomi. A karo na biyu suka nemi ganin makusancinta. Wannan karon bayan Baba Ɗanƙwairo hadda Kabir aka shiga. Sai da bayanin da likita ya yi musu ya girgizasu. Zahidaht dai ta amsa kiran mahallicinta. Sossai iyayen suka kiɗime da tashin hankali. Kabir kuwa a guje ya fito, Jawwad da ya shigo asibitin kenan ya riƙeshi yana tambayarsa ba’asi. Sai ya saka kuka tare da dunƙule hannunsa yana bugawa a bango.
“Jawwad ta mutu! Ta tafi ta barmin komai ta barni in ci tsiyata”
Kuka ya sarƙeshi ya durƙushe awajen. Sossai yake kuka tare da tonawa kansa asiri bisa abubuwan da yake yi mata. Babu abinda ya ɓoye. Jawwad ne ya janyeshi yana toshe masa baki. Iyayen kuwa ko takansa ba wanda ya bi aka ɗauki gawarta zuwa gida. Banda shassheƙar kuka babu abin da yake tashi cikin estate ɗin. Tabbas mutuwar ta girgizasu. Musamman Yaya Asabe gani take kamar Zahidahn ta mutu da ƙulinta aranta na hanata bayyanawa zuri’arsu halin da take ciki. Sai dai kukan da Kabir yake yi yana maimaita shi ne sillar mutuwarta ya ɗauki hankalin ahalinsu. Da yawa masu zuciya kusa nan suka shiga aibatashi, wasu kuwa shiriya suke nema masa. Duk sai Jawwad ya ji ya muzanta domin dai abokin ɓarawo ɓarawone musamman da shi Akuyarsa ta fi ta kowa kuka. Da yawa ma suna ɗora laifin kan cewar shi ya kangarar da Kabir ɗin.
Jikin Labiba ya yi bala’in yin sanyi, gani take kamar Yusuf ma mutuwa zai yi. Nan da nan ta shige can cikin ɗakin Amne ta ƙunshe kanta. Banda kuka babu abin da take yi tare da danasani. Burinta kawai san sanin halin da Yusuf ɗin yake ciki. Sai dai bata sami fuska wajen kowa ba. Tun dare aka haɗa gawar Zahidaht wshegari da safe aka ɗauketa zuwa gidanta na gaskiya. Iyaye da ƴan uwa na kokawa tare da kyautatta mata zato bisa haƙuri da juriyar ibadarta ta gidan aure. Koda aka je maƙabarta da ƙyar Baba Muttaka ya bari Kabir ya kamata aka sakata cikin gidanta na gaskiya, sai dai yana sakata ya yanke jiki ya faɗi dole aka wuce asibiti da shi domi karɓar taimakon gaggawa. Da yawa daga cikin mazatan gidan asibitin suka wuce dan ganin halin da Yusuf yake ciki. Ba laifi jikin da sauƙi, kuma likitocin sun sami tattaunawar data kamata ana tunanin basai an kaishi Kano ba.
BAYAN KWANA UKU!
Kwanaki ukun makokin sun zo wa zuri’ar a hagunce, da yawa daga cikinsu babu walwala a tare da su. Shukura da mahaifanta takanas suka zo gaisuwa tare da duba jikin Yusuf. Sossai ya ji daɗin karamciɓ mahaifinta da karar da suka nuna masa. Hakan ya ƙara mata ƙima da kwarjini a idanunsa. Kabir dai an sallamoshi amma jininsa ya yi mugun hawa saboda tunani. Kwata-kwata ya tsangwani kansa baya zama wajen da mutane suke zaune. Idan ya zauna kuma ya dinga surutai kenan. Bacci kuwa sai da mutane a kusa da shi suna rirriƙeshi saboda firgita ya ke yana kiran,
“Gata nan! Gata nan!!”
Duk wannan taƙadamar da ake yi Labiba na gida tana fama da ɗacin rai, ko bakin ƙofa Amne ta kasa ta tsare ta hanata fitowa balantana ta sami damar dubo Yusuf. Gabaɗaya mazan gidan sun saka mata idanu suna sanin ganin iya gudun ruwanta. Matan kuwa sun sami aikin yi. Tabarmar zaman makoki ta koma dandalin gulma.
Tun daga ranar da Yusuf ya farfaɗo yake tunanin hukuncin da ya kamaci Labiba a zuciyarsa. Idan ya zauna tunani sai yake hango shin wace rayuwa yaransa zasu yi BABU MAHAIFIYA. Sai dai idan ya tuna WA YAKE AURE ya kan ji ya tsani kansa. Kamar kodayaushe jingine yake da gadon da aka kwantar da shi, yaya Adam da shigowarsa ɗakin kenan ya dubeshi da kulawa,
“Yusuf kana buƙatar wani abu ne?”
Shiru bai amsa masa ba, sake maimaitawa ya yi amma kuma bai motsa ba. Da sassarfa ya ƙarasa tare da girgizashi. Ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi,
“Yaya yaushe ka shigo?”
Haɗe fuska ya yi yana dubansa,
“Lokacin da ka tafi duniyar tunani. Look Yusuf nasan ba tunanin kowa ka ke yi ba sai na Labiba. Ba zan hanaka tuna matarka ba amma wallahi tun wuri ka sauyawa kanka taku. Yau kwananka nawa a cikin asibitin nan cikin mawuyacin halin da ita ce silla? Amma babu ƙafarta babu ta mahaifiyarta ballantana wani makusancinta. Wannan bai isheka ishara ka fahimci wa ka ke aure ba?”
Ƙansa a ƙasa idanunsa taf da hawaye, muryarsa ta yi rauni sossai ya furta,
“Ku yi haƙuri komai lokacine!”
Mamaki ya kashe Adam ɗin, domin a tunaninsa sakin Labiba zai yi amma sai ya ga saɓanin hakan,
“Yusuf wace irin zuciya ce da kai?”
“Yaya ba a gyara ɓarna da ɓarna. Kamar yadda ba a nunawa sakarai illar sakarci ta hanyar sakarci. Yadda ake tafiyar da wanda ya jahilci hanya bisa tafarkin da ya kamata hakane ya kamaci Labiba. Mu kasance masu uzuri agareta koda zai kai karo saba’in ba aibu bane!”
Baba Ɗanƙwairo da ya shigo ɗakin jinyar ya furta,
“Allah Ya albarkaci tunaninka Yusufa!”
Tsabar takaici kasa cewa komai yaya Adam ɗin ya yi yasa kai ya yi ficewarsa. Shi kuwa lumshe idanu ya yi yana ayyana gejin da ya kamata ya ɗauki mataki a kanta ba wai yanzu ba.