WATA MACE CHAPTER 5 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 5 BY SANA S MATAZU


                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji, Yusuf ya sami sauƙi sossai. Har an sallameshi. Sai dai rayuwarsa ta sauya sossai, ya yi bala’in ƙara zama me sanyi fiye da baya. In kaga haƙoransa sun buɗe to murmushi ne amma ba dariya ba. Ita kanta Shukura ta ga sauyi sossai a tattare da shi na wasu ɗabi’un amma kuma shaƙuwarsu na nan. Lokacin da aka sallamoshi gidan mahaifinsa ak wuto da shi, domin ya ƙuduri aniyyar ya bar GIDAN MATARSA har abada. Dan haka ba shi da wajen zama da ya wuce baranda, kodai yana karatu ko kuma suna waya da Shukura. Wannan damar Labiba ta samu ta maida tagar dake ɗakin Amne ta sama wajen zamanta. Kodayaushe idanunta yana kansa, duk wani motsi nasa yana tafiya da yanayinta zuciyar n matsewa da wani irin abu da takasa fahimtar tausayine ko kuma ƙiyayya ce.

Kamar kodayaushe yana zaune, ita kuma idanunta na kansa. Tunani take yi ta ya ya zata isa wajensa ta nemi yafiyarsa? Tabbas tana kallon yadda rayuwa take wujijjiga Kabir ya ƙare ya lalace, bata fatan kwatankwacin hakan ya faru da ita. Tunaninta ya katse daidai lokacin da motar Yaya Adam ta shigo harabar gidan, yana buɗewa yaranta suka fito cikin shiga me tsafta da sha’awa wani abu ya gindaya ta tsakanin haƙarƙarinta. Da ido take dubansu, tana jin kewar abinda ta bari a baya na matsa ƙirjinta. Wannan gatan suka rasa daga gareta. Wannan kulawar da kowane ɗa yake alfahari da ita suka yi kewa. Lallai bata kamaci amsa sunan uwa ba, duk da cewa UWA UWA CE koda kuwa ta buzuzu ce amma kuma ba kowane ya ke amsa sunanba. Ƙwalla ta share sakammakon dafata da aka yi tana juyawa suka yi ido huɗu da Husnan baba Mu’az, bata san yaushe ne ta shigo ba, kawai sai ta sami kanta da rungumeta tana gunjin kuka. Abin ya bata mamaki matuƙa, a tarihinsu babu komai tsakaninsu da ita da hanatara da kyara. Yau kuma sai ga akasin hakan, lallai duniya juyi-juyi ce,

“Husnah na yi kuskure a rayuwata wanda gyarashi yake da matuƙar wahala..”

“Ba me wuya bane Labiba matuƙar kin saka wa zuciyarki zaki gyara ɗin, babu wanda ba ya kuskure sai dai ba kowane yake da rabon gyarawa ba!”

Wasu ƙwallan ne suka sake kwaranyo mata, ta goge mata tare da zama a kusa da ita,

“Labiba sau tari muna aikata kuskure amma sai mu karaya a hanyar gyarawa. Ƙwarai duka kuskure kuskure ne, amma kuma gyarashi babbar rabauta ne. Nasani da ciwo ƙwarai gyara abinda ka bari, amma kuma a kwai rib…”

Gani ta yi gaba ɗaya hankalinta na kan taga, ta kai idonta kai sai ta hango Ummi kan cinyar mahaifinta tana ɓalɓala dariya da waya a kunnanta. Ko ba a faɗa Husna ta  sani da Shukura ya haɗasu suke waya, kallon juna suka yi yayinda Labiba ta dafe ƙirjinta da yake barazanar buɗewa. Da wani irin zafi me ƙuna, duk da bata san me ya ke faruwa ba tana jin wata irin sarewa da rashin madafa miƙewa Husnah ta yi ta barta domin babu abinda zata iya faɗa mata ya wanke wannan raɗaɗin.+

***

Soyayya tsakaninsa da Shukura sai abinda ya ƙara ƙaimi. Cikin ƙanƙanin lokaci manya suka shiga lamarin aka tsaida magana. Babu wanda ya dakatar dashi domin suna san rage masa raɗaɗin abinda ya yi kewa. Babu kuma wanda ya bi ta kan Labiba domin suna san nuna mata kuskuranta. Hasalima an hana kowa sanar musu abinda yake wakana.

Sossai Yusuf ya saki jiki ya soma neman na kansa, mahaifinsa ya bashi jari me kauri duk da mahifin Shukura ya so ɗorashi akan nasa kasuwanci amma ya nuna baya buƙatar wannan mutuntawa domin ansha shi ya warke. Ƙaramin gida ya kama haya da guminsa, kuma mahiafinsa ya amince da hakan. A hankali ya cigaba da hidimominsa a gefe guda kuma Yaya Amina na tara masa lefe duk da mahaifin Shukura ya ce baya buƙatar komai idan ka ɗauke sadaki. Kuma Baba Muttaƙa ya biya naira dubu ɗari, amma da ƙyar suka karɓi hamsin. Soyayya suke cike da mutuntawa, bata da abin tambaya sama da yaransa tare da ƙarfafa masa guiwa kan fusknatar ƙalubalan rayuwa.

A kwana a tashi ya rage saura kwanaki bakwai bikinsa. Duk wani shirye-shirye a gama shi. Babu abinda su Labiba suka sani domin yanzu ba fitowa take ba daga ita har Amne kamar amare haka suke wuni cikin ɗaki. Babu wanda baya murna da auren Yusuf. A gefe guda kuma ya soma tunanin yadda zata kayya masa tsakaninsa da Labiba. Shi kam ba shi da burin sakinta ko dan karamcin mahaifinta. Amma kuma yana jinjina wace irin rayuwa zasu gudanar.

***

Da ɗan gudu irin na yara Khalifa ya fito daga sashin da ya kasance na Yusuf ɗin. Binsa ya ke yana san ƙwace wayarsa a hannunsa. Shi kuma sai dariya yake yana faɗin,

“Aunty Cukula”

Daidai hanyar da zata sadashi da sassan Amne ya ja burki, yana jin baya muradin taka ƙafaffunsa a wajen gara ya aika wani yaron. Kamar ance tsaya sautinta ya ratsa kunnansa.

“Wallahi Labiba matuƙar ina numfashi ba zaki komawa auran faƙirin yaron can ba. Yarinya babu zuciya ba komai ke kullum magana ɗaya. Ba Yusuf ba Ɗangaladima ma uwatasa kurwar ɗiyana kur wollah”

Runtse idanu ya yi yana jin zagin da ta aunawa mahaifinsa na zaga kowace gaɓa tasa. Babban takaicinsa mahaifiyarsa data zaga tana kwance ƙasa. Tafiya yake ko gabansa baya gani, yana son maida Labiba ba dan so ba, sai dan mutuntakarsa amma kuma baya jin akwai abinda ya isa taɓa mutuntakar mahaifansa. Kai tsaye ɗaki ya wuce yana jin ƙirjinsa na suya, koda Khalifa ya dawo kawai amsar wayar ya yi yana daka masa tsawa. Kamanin Amne dake yawo kan fuskar yaron na saka masa wata irin shakka da kokwanton kadda ya kwaso halinta. Sai dai tuna sunan da ya saka ma yaron na bashi wani irin tabbaci da yake jin nasarar tasa ce. A daran bai kwanta ba sai da ya gana da Baba Muttaƙa kuma ya fahimceshi.

STORY CONTINUES BELOW

***

Babban ɗakin taron shaƙe yake da tarin ahalin, haya-haya hayaniya take tashi sakammakon hira irin ta ƴan uwantaka da wasu ɗaiɗaiku suke gudanarwa. Yusuf yana daga gefe yana duban kowa daki-daki. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa. Daga hagu Labiba ce zaune kusa da Amne, sun keɓe kansu kamar wasu mumunai, amma kuma idanun Labiba na kan Yusuf. Hango Ummie ta yi cikin wasu kaya ƴan kanti masu kyau da tsada. Zuciyarta ta ɗokanta da san jin ɗumin ƴaƴanta, gaba ɗaya wani tsoro da shakkar Amne ya fita a ranta balantana barazanarta. Gadan-gadan ta nufeta, daidai lokacin da yarinyar ta iso tsakiyar ɗakin taron. Caraf ta riƙe hannunta, ta juyo tana dubanta. Kallonta ta ke yi irin kallon nan na bansanki ba, ko kuma wace ce ke? Gaba ɗaya mutanan sai suka zubo musu idanu, yarinyar ta juya tana ƙoƙarin fuzgar hannunta. Bakinta na rawa ta furta,

“Ummie ni ce fa!”

“Ke ce Mamarmu me saka Abbanmu kuka ko?”

Tamkar ɗaukewar nefa haka komai ya ɗauke mata, zuciyarta ta tsaya cak tana wani irin matsewa. Bata gagara tsayar da hawayen fuskarta ba, ta kuma kasa gaba ta kasa baya. Ummie ta zame hannunta ta juya tana wani irin taku cike da nutsuwa da kawanciyar hankali. Abin sai ya bawa mutane mamaki tamkar wata babba. Nan da nan ƙus-ƙus ya soma ya tashi, Labiba da idanunta suka yi nauyi ta soma tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. A haka Amne ta ƙaraso ta ja hannunta tana huci suka zauna.

Bayan buɗe taro da addua’a Baba Muttaƙa ya miƙe ya miƙe ya soma gabatar da abinda suka samu na riba da kuma alkhairi a cikin zuria’ar. Daga nan ya ɗora da bayanin yaran da suka sami gurbin karatu a bana da waɗanda ake sa ran futowar sakammakonsu. Sannu a hankali ya gangaro kan abinda shi ne maƙasudin taron baki ɗaya. Bayan dogon jawabi game da al’ammuran da suka gudana daga kan Kabir Yusuf da Labiba da kuma marigayiya. Ya yi jan hankali sossai kan yadda da ƙaddara da kuma yin fashin baƙi kan ma ana ta sirranta sirrin gidan aure. Ƙwarai abinda ya kamaci sirrantawa amma ba irin zama na Zahidaht da Kabir ba, domin akwai cutarwa. Ya fito ƙarara ya nuna illar dake tattare da abinda ya faru, tare da nusar dasu kan abubuwan da suka kamaci ɓoyewa. Ƙwarai akwai abinda ya kamata a sakayashi a zamantakewa kamar sha anin yau da gobe bisa yanayin rayuwa. Samu da rashi duka na Allah ne. Mu amalar zamantakewa da sauransu. Daga ƙarshe ya ja hankalin iyayen sossai domin su ne suka bada ƙofar afkuwar hakan. Babu yadda za ayi ƴa ta kawo maka kokenta kan gidan auranta ka ƙi sauraranta, domin yana daga kuskuran da suka aikata akan Khameesat wanda ya zamewa Zahidaht makamin riƙewa na cewa koda ta zo gida ba za a dubeta. Tabbas miji abin mutuntawa ne amma kuma ba ya nufin komai nasa da zai aikata babu kuskure ciki ba, akasari abinda yake daƙilar da ƴa mace shi ne yarda da kuma yaƙini da iyaye suke lulluɓawa ƴaƴansu akan mazajansu ne. Sau tari nan ne mafarin matsalar sai kuma ta caɓe a dinga dama kaza. Gaba ɗaya jikin mutanna wajen ya yi mugun sanyi. Ba kamar Yaya Amina da ta ke ganin tafi kowa laifi domin ta san halin da Zahidaht take ciki amma ta ƙunshe bakinta. Tana kuka tana komai ta miƙe tana neman yafiyar kowa na wajen kan wannan kukskuran data aikata. Kuma triyan-tiryan ta miƙe ta na me koro musu bayanin asalin halin da Zahidaht ta kasance a gidan Kabir.

Babu wanda bai koka ba, ta kuma ɗora da irin azabtarwa da Yusuf ya sha wajen Labiba, domin wasu lokutan a gidanta yake cin abinci idan ta hanshi duk da baya faɗa mata dalili sai dai izgilanci irin na Labiba kam bata damar bayyana mata koda bata tambayeta ba. Cike da ƙarfin guiwa take roƙonsu,

“Baba ba wai ina so a rabasu bane, amma ku yi adalci. Adalci fa nake magana iyayenmu. Ku daure ku ajiye zumunci da sanayya a gefe ku bawa Yusuf zaɓi karon farko a tarihin zuri’armu ku bamu damar mallakar haƙƙi irin ƴaƴa!”

Gumi sossai iyayensu maza suke sharewa, sai yanzu idanunsu ya buɗe kan kuskuransu na tauye wasu haƙoƙƙi n yaran nasu. Tabbas biyayya ga iyaye wajibi ne amma babu hallacinta ga abin hallita yayin saɓawa ubangiji. Baba Ɗangaladima kuwa kai kawai yake jinjinawa yana hango hikimar ubangiji na ɗaukar ran Baba Ɓaure domin ya fi su zafi.  Yusuf yana gefe kamar mutum-mutumi zuciyarsa wani irin bugu take yi, yana jinjina wahalar da Zahidaht ta sha duk nasa me sauƙi ne. Sai yau ya ji abinda ya dane shekara da shekaru a game da ita na motsa masa. Wata irin tsanar Kabir ce take zagaya kowace jijiya ta sa. Da yana da iko da ya fitar da Kabir daga zuri’arsu ko hakan ya sassauta masa abinda yake ji, amma ina ba a sauyawa tuwo suna.

Labiba tamkar kazar da aka tsamo cikin ruwan sanyi haka ta kasance. Tun abinda Ummie ta aikata mata, ga kuma ƙari daga Yaya Amina. Daga ita har Amne a ɗarare suke gani suke kowa kallonsu yake yi kuma hakane, duk da cewa sun san gaskiya ta faɗa amma hakan be hana su ji zafinta ba. A ƙasan ransu kum suna kiranta ‘munafuka’.

“Yusuf”

Muryar Baba Muttaƙa ta dira a kunnansa, ya ɗago idanunsa jajjur kamar gauta. Ga jijjiyoyin kansa duk sun ɗaga. Wannan ya bawa masu kular cikinsu damar sanin yana cikin yanayi mara daɗi.

Murya can ƙasa ya amsa da,

“Na’am Baba”

Murya a kaurare Baba Musa ya yi magana,

“Yusuf ka ɗago magana zamu yi da kai”

Wannan karon da wani irin karsashi ya ɗago murya cike da ladabi,

“Ina jinku Baba duk abinda ku ka yanke ni me biyayya ne a gareku!”

Gaba ɗaya sai ya sanyayyar musu da jiki, amma hakan ba zai sa su shiga haƙƙinsa ba.

“Yusuf zaɓi muke baka a matsayinka na wanda aka zallunta. Shin mene ne ra ayinka akan ƴar uwarka Labiba?”

Gaba ɗaya sun ɗaureshi da jijiyoyin jikinsa, da ido yake duban kowa. Idonsa ya tsaya akan nata data kafeshi da su. A idanunta yake hango gazawa, magiya da neman yafiya da kuma nuna cewa bazan kuma ba ka tausayamun. A idanun danginsa kuma yana hango, ka ji kanmu wannan dama ce da muka samu daga ahalinmu karo na farko a tarihinmu kadda ka bari ta kuɓuce mana. Zuciyarsa kuma na tuna masa. Waye Baba ɓaure, karamci da sadaukarwarsa. Bai kamata ya zamo me yankakken baya ba. A gefe kuma yana jin wace rayuwa yaransa zasu yi babu mahaifiya? Zuciyarsa ta raya masa Shukura fa?”Na sauwaƙe mata shika ɗaya biyu uku, idan ta sami miji ta yi aure!”

Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki salati, da yawa suna san suga sun rabu amma basu taɓa tunanin zai yanke ɗanyen hukunci haka ba. Mahaifinsa kuwa dafe kai ya yi ido jawur. Amne ba tare da nadama ko dana sani ba ta rangaɗa guɗar da ta ba kowa mamaki, miƙewa ta yi tana furta,

“Tafi Nono fari…”

Bata gama ba Labiba ta ƙwala ihu ta yanke jiki ta faɗi tana jan numfashi da ƙarfi amma ya kwace mata ta sume. Da hanzari ƴan uwa suka yi kanta, amma Amne ta ce kadda wanda ya taɓa mata ƴa. Khamis ta dakawa tsawa ya saɓeta a kafaɗa kamar yarinya suka yi waje aka nufi asibiti da ita.

Bayan fitarsu wajen ya ruɗe, masu kuka na yi masu Allah ya ƙara na yi. Tsawa Baba Ɗangaladima ya daka musu, sossai ya yi wa Yusuf faɗa tare da nuna masa illar abinda ya aikata sai dai bakin alƙalami ya bushe. Nasiha ya ƙara yi musu me ratsa zuciya tare da gargaɗi kan tasowar wata fitina. Anan aka fitar da waɗanda zasu kai lefan Yusuf washegari, cike da fushi da kaushin murya kuma ya bawa Kabir da Jawwad damar tsayar da hankulansu su nemi matan aure. Daga bisani aka rufe taro da addua’a musamman ga Zahidaht da Khameesat tare da jigon gidan baki ɗaya.

Babu wanda ya bi ta kan Amne da zuri’arta suka hau shirya-shiryan biki. Sai lokacin Amne ta sami labari, nan ta shiga zage-zage da surfa rashin mutunci son ranta. Babu wanda ya biye mata.

Kabir kuwa gaba ɗaya ya fita hayyacinsa ya koma abin tausayi. Ko zama cikin ƴan uwa ya kasa yi, mahaifiyarsa tun tana hantararsa har ya koma bata tausayi ta soma jansa a jiki tana nuna masa ya maida al amuransa ga ubangiji. Sossai ta tsawatar masa kan yin azkar da azumin nafila. Aikuwa ya kama babu hannun yaro, sai ya soma jin wata irin nutsuwa na bibbiyarsa ga kammala da kwanciyar hankali. Tsakaninsa da Jawwad gaisuwa, iyayansu kuwa kullum sai ya je ya gaida kowa. Ya tattara komai ya watsar ranar da babu aiki baya zama. Mahaifinsa yake bi suna noman rani abin gwanin ban sha’awa. A wajen aikinsu akwai wata yarinya Ramlatu data nace tana sonsa, duk da sun taɓa rayuwar banza da ita yana jin ita ɗin zai aura ya huta domin ita ta dace da shi kasancewar tana da tabo kamar shi. Allah bashi sai su haɗu su tuba su gyara rayuwarsu.

Biki ya kankama kowa na hidimarsa. Ana gobe ɗaurin aure aka sallamo Labiba, kwata kwata bata san abinda yake faruwa ba kuma babu wanda ya faɗa mata. Dan haka ta cigaba da hidimarta bata kula kowa ba, tana shan magungunanta kamar yadda likita ya gwada mata. Da yamma ana shirin walima ta dinga kallon mutane da rashin fahimta amma bata tanka ba har kowa ya fice ya barta nan zaune.1

Washegari aka ɗauro aure aka kai amarya. Shi ma Labiba bata sani ba, saboda ta tashi da zazzaɓi da mugun ciwon kai.

Kwana biyu tsakani mutanan gidan suka tashi da hidima saboda kawo gara da za ayi daga gidansu Shukura. Duk abinda ake yi Amne ta sani amma tana gudun faɗawa ɗiyarta gudun halin da zata shiga. Tana lura da yanayin da take ciki wasu lokutan sai dai ta ganta tana sharar hawaye, ga yawan firgita idan tana bacci tana kiran sunan Yusuf ɗin. Abin tun baya damunta har ya soma damunta.

***

Da yamma duk gidan kowa ya daɗe, yaya Amina ta shirya ta nufo gidan. Tana san zuwa ta duba Labiban amma kuma tan shakkar tarbar da Amne zata yi mata. Amma kuma ƙasan ranta tana jin ba laifi ta aikata ba. Zata yi komai dan kawo haske a rayuwar Yusuf.

***

MUN DAWO LABARIN.

***

Tun daga bakin ƙofar gidan ta ke jiyo muryarta cike da rauni, waƙa ce take rairawa murya a sarƙe. A haka ta ƙarasa shigowa gidan, mammaki ya kasheta ganin hawaye a idanun Labiba. Bata ƙara tabbatar da mamakinta ba sai da ƙamshi mai ni’ima ya sami masauki a massarafar shaƙar numfashinta. Jiki a sanyaye ta zauna idanunta cikin nata. daidai lokacin da ta ƙara ɗaukar wata waƙar,

“Zamantakewa ba ƙarya ne ba. Cin amanar soyayya, an rabani da me sona”

Jikin Amina ya ƙara sanyi, bata taɓa tunanin akwai ranar da zata ga nadama a idanun Labiba ba, bare kuma zubar hawaye. Lallai masu iya magana sun yi gaskiya, duniya juyi-juyi ce. Tunaninta ya katse lokacin da hannunwan Labiban suka sarƙafo nata hannuwan murya a raunane ta furta,

“Yaya Amina ke ma murnar ki ke yi? Kina cikin masu murna an min saki ɗai-ɗai har guda uku? Kodayake ai ke ce ma me bada shaida amma ba kowa ya cuceni ba sai yaya Khamisu da kuma Amne da basu sakasu sun je sun daki Yusuf ba da bai sake ni ba. Kaicon rayuwata…”

Numfashinta ne ya soma yin sama da ƙasa, ta kai hannu ƙirjinta ta danne tana taune leɓɓanta na ƙasa. Kafin ta yi wani yunƙuri ta faɗi ƙasa yaraf! A hanzarce Amina ta kai mata ɗauki tana ƙwalla ƙara,

“Yaya Ade ku kawo agaji!”

Daidai lokacin wadda aka kira da Yaya Ade ta ƙaraso, tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi. Kai a ɗage ta kalleta,

“agajin me kuma zamu kawo Yaya Amina? Ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Ɗiyar boya ce fa take gudun auren jinin boya to mene ne a ciki dan ya sauta zata ɗaga mana hankula. Ba a auran ɗiyan boyan mu munka auri yayyunta? Ni kinga tahiyata ma gidan Yusufa naka zuwa ganin waga amarya tasa me karamci. Ance yau danginta sunka kawo gara daga Kano, gara mu hanzarta mu kwashi arziƙi kadda a ayi babu mu. Domin su arziƙinsu na gada ne ba taka haye ba, saudiyya ma zasu tafi aka ce sati me kamawa mahaifinta ya biya musu”

Wannan furucin shi ne ya ƙarasa tafiya da numfashin Labiba, cikin kanta take maimaita,

“Yusufa nawa? Aure? Saudiyya?”

***

Tsayin kwanakinta uku a kwance gado asibiti, bata san inda kanta yake ba. Duk lokacin da zata farka da sambatun kiran sunan Yusuf take farkawa. Allurar bacci kawai ake yi mata ta koma. Aranar kwana na huɗu mahaifiyarta ta zubda hawaye kamar babu gobe, masu ganin laifinta kansu sun soma jin tausayinta. Sai dai wasu ko kaɗan tausayinta be ɗarsu a ransu ba. Hasalima gani suke yi bata girbi abinda ta shuka ba.

A hankali take rarraba idanunta tana ƙarewa inda take kallo. Tabbas nan ɗin ɗakin jinya ne, bata yi mamaki ba duba da yanayin data riski kanta. Sannu ƴan ɗakin suke jeramata tana amsawa da kanta kamar ƙadangaruwa. Idanunta ta ji sun mata nauyi, gaɓɓanta na amsawa amma hakan be hanawa kunnuwanta sauraran abin da ke fitowa bakin Yayanta Khamis ba,

“Ni na rasa irin wannan masifa ta Labiba wallahi. Tun da an yi saki har guda uku ta haƙura mana yanzu saboda Allah wa gari ya waya. Ki duba fa, kwanata shida ita da gawa marabarsu numfashi. A ranar ma da abin ya faru ba dan zuwan Amina ba ƙila sai dai mu riski gawarta..”

Maganar ta katse sakammakon sallamar da aka doka, ɗaukacin mutane sun kai su goma sha biyar ne a ɗakin, abin ka da ƴar dangi. Labiba ƴar dangi ce gaba da baya. Amma kuma kash kafataninsu aka rasa me ƙumajin amsawa. Bakunnansu sunyi musu nauyi. Hannatu ce ta yi karaf ta amsa gudun aji kunya. Labiba kuwa tun sallamar ta shaida mammallakin muryar, domin ko giyar wake ta sha Yusuf da abin da ya mallaka daban suke a rayuwarta. Sai dai ta gaza buɗe idanunta waɗanda ta kulle tun lokacin da ta ji sallamarsa. Ƙwarai tana fargabar buɗewa ta ganshi da abin da zai ƙarasa tarwatsa duniyarta.

“Sannunku da zuwa”

Ƴan ɗakin suka soma faɗa, suna harhaɗa kalmomin kamar masu koyo. A kunyace Yusuf da amaryarsa suka bi su daki-daki suna kwasar gaisuwa. Ummi ta yi tsaye ƙiƙam idanunta na yawo a kan mahaifiyarta. Sai lokacin ƴan ɗakin suka farga da ita suka soma faɗin ta ƙaraso wajenta su gaisa. Ko gezau bata yi ba, tana dai kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. Aunty Shukura kamar yadda suke kiran amaryar mahaifinsu, wadda a yanzu suke jinta kamar ita ta haifesu, ta miƙe tare da riƙo hannun Ummi da Khalifa ƙaninta. Sai dai ko taku uku ba su yi ba ta ji yaran sun warce hannunsu. Ta juya cike da mammaki, sai ga hawaye na zuba a idanun Ummin, ta soma taku a hankali a hankali da baya tana girgiza kai. Daga bisani ta kwasa a guje tana furta,

“A’a Aunty!” Shi ma Khalifa da tsamin baki irin na wanda hausa bata gamsheshi ba ya juya yana faɗin,

“Bajani ba Anti zasu yi min irin dukkan da suka yi wa Abbanmu!”

Ya ƙarasa yana ajiye yatsansa manuni akan Khamis yayan mahaifiyarsa. Kunyar duniya ta luluɓe Khamis ganin ƙaramin yaro na alamtashi da mummunar ɗabi’a. Bai taɓa tsanar biyewa shirman ƙanwarsa da mahaifiyarsa irin yau ba. Garam! Ummi ta rufo ƙofar da ƙarfi, bayan ta ja hannun ƙaninta. Sautin ya yi daidai da bugawar zuciyar Labiba. Cak numfashinta ya yi fitar burgu. Gaba ɗaya ɗakin aka ɗauki salallami, cewar Ade matar Khamis.

“Labiba ta cuci kanta. Ɗiyanka! Ɗiyanka na cikinka na gudunka? Mi ake da wanga ɓataciyar rayuw..”

Kallon da Yaya Khamis ya wurga mata ne ya sanya bakinta mutuwa, sai lokacin hankalinsu ya koma kan gadon da take. Suka fahimci bata numfashi. Da hanzari Huraira ta kira likita, ya soma ƙoƙarin daidaita numfashinta. Nan da nan ta farfaɗo, sai dai ba abin da take yi sai surutai tilas aka yi mata allurar bacci tare da sallamar duk wanda ya ke cikin ɗakin. Jiki a sanyaye suka fito yuu! Zuwa harabar asibitin anan suka riski Shukura na lallashin Ummi. Yusuf kuma yana riƙe da Khalifa. Ana haka Amne ta ƙaraso da Hajja ƙarama ɗiyar Khamis. Tana ganinsa ta kama zilo, duk da ƙarancin shekarunta. Hannu ya miƙa zai karɓeta, amma ƙiri-ƙiri Amne ta hanashi ita. Nan kuwa yarinyar ta tsanyare da kuka tana mimmiƙewa. Yaya Khamis ne ya karɓeta ya miƙa masa duk da mugun kallon da Amnensu take jefa masa. Ade kuwa sai ƙunshe dariya take yi. Yarinya na zuwa hannunsa ta yi tsit tana wangale baki.

Basu wani jima ba, saboda yadda wajan ya soma ɗinkewa da dangi, kuma kowa ya zo bakinsa baya shiru game da Yusuf da matarsa, karo na farko ya kafa TARIHI cikin zuri arsu. Dan haka Shukuran duk a takure take, ganin haka yasa  ya yi musu sallama tare da ajiye kayan dubiya har leda uku. Duk suka rakashi da idanu, basai an yi musu bayani ba shadar jikinsa kanta abar kallo ce. Yaya Ade ce ta janyo ledar tana bubbuɗewa bakinta na furta,

“Masha Allahu. Ka ga gidan karamci da sanin darajar ɗan Adam”

Mugun tsakin da Amne ta ja ya ankarar da ita kadda ta yi kwaɓa, domin ta ga Amnan ta kawota bakin maƙoshi. Da hanzari Khamis ya fita yana jin wani ɗaci a zuciyarsa. Tabbas shi ne sillar komai shi ya tarwatsa farin cikin ƙanwarsa da tuni tana tare da yaranta koda babu muradinta. Nadama da danasani suka shiga kai kawo a zuciyarsa. Komai ya soma dawo masa daki-daki kan rayuwar ƙanwartasa. Dole ne ya nema mata farin ciki ya ayyana hakan a ransa. Dole ya sake tuntuɓar Jawwad su daidaita ko ƙari ne ya yi masa kan miliyan gudar da ya gindaya masa.Haba Jawwad mata fa na ke baka ka aura, amma kana jamin rai kamar wanda zai yi min abu kyauta! Ban da ma dai ƘADDARA ya za a yi na nufeka da wannan batun, bayan kana da TAMBARIN da baka cancanci zama da ita ba…”

“Dakata Khamis, wai dole sai na auri ƙanwarka? Ni gaskiya ba zan iya auren ɗiyar boya ba, kuma duk TAMBARIN da nake da shi ya kai nata ne? Ko ka manta duk abin da namiji ya yi adone? Ina ce kafatanin danginmu babu mace mafi ƙasƙanci kamarta a yanzu? Kodayake naga alamu ita data tashi gado, sai ta gado surukarta baƙin jini maimakon farin jini irin na mahaifiyarta. Kodayake babu haufi ai duk boya dai sunanta boya babu wani bambanci…”

“Dakata Jawwad kadda ka zagarmin mahaifiya, miliyan ɗayan da nace zan baka ce ta yi maka ƙaranci ga auren ɗiya kamar Labi..?”

Ƙarasowar Kabir wajen ne ya dakatar da su daga muhinmiyar maganar da suke yi, duk da shi Jawwad anasa ɓangaren ya so su ci gaba, koba komai zai suluɓe daga auren da ake son maƙala masa amma Khamis ɗin ya dinga togewa. Tilas ya haƙura, amma kuma yana barin wajen ya soma ƙyanƙyasawa Kabir ɗin kanun zancen. Girgiza kai ya yi cike da takaicin halin ƴan uwan nasa, duk abinda ya faru ba zai zama ishara garesu ba. Hasalima wata ɓarnar suke da niyyar aikatawa lallai wannan karon ba zai bari ba, tillas ne ya nuna musu kuskuransu.+

***

Da Yamma Khamis be haƙura ba ya sake bin Jawwad majalisa. Tunda ya hangoshi ya ke kumbure-kumbure. Kabir yana gefe da carbi me dannawa a hannunsa. Gefe kuma yana amsa wayar Ramlatu da yanzu sun daidaita. Tahowar Khamis ɗin yasa ya yi mata sallama. Sai dai kafin ya ƙarasa har ya soma jin tashin muryoyinsu, dafe kai ya yi yana ƙarasawa amma sai ya riski Khamis na killar Jawwad. Abinka da ƙarashen taba da giya, muryarsa a shaƙe yake faɗin,

“wallahi ba zan aureta ba, ana dole ne? Ƙanwarka ɗin banza kuma miliyan guda na ci na yi haniƙan wallahi bazan biya ba”

Zaburowa ya yi zai kuma dukansa, Kabir ya riƙeshi suka wuce yana tausarsa,

“Haba yaya ina maka kallon me hankali amma kana biyewa shasshancin Jawwad. Saboda Allah ya kuke so iyayanmu su ji idan suka riski abinda kuke yi?”

Sai lokacin wata kunya ta rufeshi, wautarsa yake gani ta biyewa muradin Labiban amma kuma farin cikin mahaifiyarsa yake so domin yanzu tafi kowa burin Labiba ta koma ko ta huta.

Duk abinda ya ke faruwa akan idon Tukur me ɗinkin takalmin da Jawwad ya bawa wankin takalma. Da fari ya so ya ƙi karɓa saboda yamma ta yi. Amma abinda ya faru ya tabbatar masa da cewa arziƙi ne ya ke bibiyarsa. Matsawa ya yi tare da tattaro dukkan nutsuwarsa,

“Sannu bawan Allah, ga shi na gama”

Karɓa ya yi tare da bashi haƙƙinsa, amma be matsaba sai ma ƙara marairaicewa ya yi fuskar tausayi yana jajjantawa  masa a haka suka rabu.

Tunda Tukur ya koma gida ya shiga tunanin yadda zai mallaki miliyan guda cikin ƙanƙanin lokaci. Tabbas nesa taso masa kusa. Amma kuma ta ina? Tsakar dare ya miƙe kan yagulalliyar tabarmarsa yana juyi, Lado abokinsa ya kawo masa bugu da ƙafa yana magaggi tureshi ya yi yana ayyana ya kusa fara kwana a kan irin gadon nan na bakin titi. Wata dariya ta ƙwace masa ya soma shirya yadda tsanin nasararsa zai kasance.

Cikin kwana biyu ya maida majalisar su Jawwad wajen zamansa koda ba ɗinki, a hankali ya soma saka musu baki idan suna hira. Musammman sha anin Jawwad ya dinga koɗashi da kambamashi tun baya kulawa har ya zamana suna wasa da dariya. A hankali ya soma shigo da labarai musamman kan halayyan mata da wasu mazan a gidan aure. Ya nuna yadda matarsa take zalluntarsa a zahiri yayinda akasin hakane a baɗini. Abinda ya ja hankalin Jawwad kenan ya soma bashi labarin yadda shi mata basa juyashi.  Sannu-sannu ya soma bashi labarin nasa auran har zuwa batun Labiba. Cikin abinda be gaza sati biyu ba Tukur ya soma mafarkin burinsa na gab da cika.

***

Amaryar Shukura soyyaya auke me tsafta da angonta. Ta rungumi yaransa sossai ta maidasu tamkar nata. Ummie idan suna wani abun sai ka ɗauka ƙanwarta ce ba ɗiyar miji ba. Kamar kullum yau ma suna zaune suna buga lido bayan ta gama yi musu ƙarin karatun alƙur’ani. Mahaifinsu ne ya shigo suka miƙe cike da girmamawa da tsantsar kulawa suka nufeshi. Khalifa ne ya rungumeshi yana faɗin,

“Abbiey sannu da zuwa”

Ummie kuma ta riƙe jakar kayansa, murmushi ya saki tare da shafa kansa. Wani abu na tsirga masa. Bai taɓa sanin mene ne aure na haƙiƙa ba sai ƴan kwanakin nan? Bai taɓa jinsa a cikakken uba ba sama da zuwan Shukura cikin rayuwarsa ita ɗin alkhairinsa ce. Idanu ya sauke a kanta ta haskeshi da murmushin da ya fi buƙata.

Ɗunguma suka yi zuwa ɗakinsa, da dabara da wayau ta janye yaran bayan ta haɗa masa ruwan wanka. Yana fitowa ya shirya cikin jallabiya, gab da zai bar ɗakin wayarsa ta yi ƙara ya ɗauka yana amsawa. Bayan sun gaisa daga ɗaya ɓangaren ya furta,

“Baba na tura musu kuɗin komai ya daidaita”

Magana aka sake yi ya rusuna kamar yana gabansa,

“Sunan Mamarmu za a saka Baba, insha Allahu ƙarshan wata nan komai zai kammala. Inshaa Allah! Na gode Baba Allah Ya shige mana gaba”

Sauke wayar ya yi tare da ɓoyayyar ajiyar zuciya, wani irin nishaɗi ne yake zagaya kowaace gaɓa ta jikinsa. Wai yau shi ne zai mallaki gidan kiwon kaji nasa na kansa. Godiya yake ga ubangiji da kuma mahaifinsa. Uwa uba kuma Shukura da ta zamo wani tsani a rayuwarsa. Bazai taɓa mantawa da karamcinta ba. Kafin bikinsu ne ta shawarceshi da batun ya gwada kiwon, da fari ya nuna mata turjiya kan hakan amma ta dinga nuna masa kowa da wajen da ubangiji ya ajiye masa nasibinsa. Kamar wasa ya soma wanda hadda taimakon kuɗinta a ciki naira dubu goma. Allah Ya dubeshi yasa masa albarka, fitar farko ya yi asara saboda be san kan kasuwancinsu ba amma fita ta biyu sai gashi an maida abinda aka rasa. Cikin ikon Allah sai gashi guri ya haɓaka. Wajen ɗinkinsa ma ya buɗe ɓangaren horar da masu sha’awa sossai wajen yake tafiya. Takai ta kawo ma shi baya ɗinkin in ba na manya ba, sai dai ya yanka yaran su haɗe yana dubawa. Tabbas ya yadda babu abinda ya gagari ubangiji.

Cikin nutsuwa ya nufo fallon yana jin nishaɗin kasancewa da ahalinsa.2

***

TUKUR…

Cikin ƙanƙanin lokaci ya tattara duk wani abinda yake buƙata ya ƙara gaba. Domin dai Jawwad ya saki jiki dashi ainun. Babu abinda be samu ba game da Labiba abu guda ya rage masa shi ne yadda zai tunkareta.Tsaye yake a harabar ƙofar estate ɗin, gab ɗaya jikinsa ya yi sanyi na abinda ya ke tunanin aikawa. Yana jin ana faɗin girma da mutuntakar ahalin amma be yi tunanin sun kai haka ba. Lallai aikin gabansa babbane.  +

   Wata zuciyar na faɗa masa ya juya, wata kuma na sake jadadda masa a’a ya je. Yana nan tsaye yana jiran gawon shanu sai ga Khamis. Ɗas! Gabansa ya faɗi, domin ya shaida fuskar dan haka da ƙwarin guiwa ya nufeshi suka gaisa. Fuskarsa na nuna rashin sanayya. Ganin hakan yasa Tukur ya gyara ya gabatar masa da kansa, da kuma maƙasudin zuwansa. Jim Khamis ya yi kamar me nazari, sai kuma ya saki murmushi ganin nesa ta zo kusa ko babu komai zai huta da mitar Amne uwa uba Labiba dake iƙirarin sun kashe mata aure. Juyowa ya yi yana dariya,

“Ka ce kun daidaita da ita ko?”

“Eh mun daidaita ita ce ma ta ce na zo wajenka!”

Ya faɗa ƙirjinsa na dukkan uku-uku, tunda ya soma magana da Khamis ɗin ya ke jin kamar asirinsa zai tonu. Har waigawa ya ke ko zai ga zuwan Jawwad a tsautsayi.

“Madalla to zan yi magana da iyayanmu sai in shaidamaka ranar da zaku turo. Amma mene ne sana’arka?”

“Eh dama ni ɗin ba wata sana’a ce da ni ba wankin takalmine amma babu abinda zai gagara tunda cikin miliyan guda ɗin da tace zaka bani zan yi hidimar komai kafin wa’adin auranmu ya cika!”

Da mamaki yake dubansa, “kan haka kuka shirya auran naku?”

“eh ta ce min kai ne me alhakin bayar da kuɗin kamar yadda aka so yi kan Jawwad!”

Ganin zai ɓalo masa ruwa yasa ya dakatar da shi tare da karɓar lambarsa. Har ya juya zai tafi sai ya dawo,

“bari na kira maka ita ku gaisa”

Da ace Khamis ya lura zai ga firgicin dake tattare da fuskarsa amma ina hankalin na can. Kai tsaye gida ya shiga ya turo masa Labiban shi kuma ya zauna suna tattaunawa da Amne.

“Amne Labiba ta samu wanda zata aura sun ma daidaita!”

Ba tare da damuwar komai ba ta yi hamdala, dan har ga Allah ta gaji da koke-kokenta. Shi kuma Khamis ganin fara arta yasa be faɗa mata ga auren da Labiban zata yi ba, tunda bata san Yusuf ɗin har gobe zata iya dakatar da ƙudurinsu. Amma ya ɗauki alwashin miliyan guda ɗin da za a fitar acikin kuɗinta za a fitar dan ya gama asara.

Koda Labiba ta nufo ƙofar gida sai da ta jima sannan ta gano Tukur ne me magana da ita. Bayan sun gaisa ya dubeta yana washe baki, ta ɗan ja tsaki miyau-miyau ɗin fuskarsa ya fi komai bata haushi. Amma ta dake ta ji dame ya zo ba laifi dai suturrasa ƙyalau da ita kuma me tsada.

“Malama Labiba ni dai sunana Tukur. Sana’ata ita ce…Yayanki ya sameni kan buƙatarku kuma na amince insha Allahu babu wata matsala”

  Da farko kallon tsana da nafi ƙarfinka take yi masa, amma jin maƙasudin auran yasa ta ɗan saki murmushi. Lallai Yaya Khamis na ƙaunarta tunda yana san cikar burinta. Basu wani jima ba, suka yi sallama bayan ya karɓi lambarta. Kai tsaye gida ta shiga tana fara’ar da mutanan gidan suka jima basu ganta a kan fuskarta ba.

Da murmushi ta shiga ɗakin Amne,

“Yaya Khamis na gode!”

Ta furta tana lanƙwasa ƴan yatsunta. Da idanu yake dubanta yana mamakin yau Labiba ce yake girmamashi haka sai tuna cikar burinta take muradi zata yi komai.

“Yauwa Labiba cikin kuɗinki zan ciri kuɗin nan wannan karon!”

“Wane kuɗi ku ma?”

Amne ta tambaya da sauri, cikin hanzari Labiba ta tareta domin ta fahimci Khamis ɗin kuma bata son Amne ta watsa shirin,

“Wasu kaya ne nagani ina so, da shi ya yi alƙawarin zai siya min to kuma kinga ga hidima zata taso mu tunda ina da su gara ni na siya ɗin”

Jinjina kai Amnen ta yi , su kuma suka saki ajiyar rai a tare suna kallon juna.

“Ka cira idan ma sun ɗara haka babu matsala”

***

Cikin ƙanƙanin lokaci maganar auren Labiba ta kankama. Tukur ya aiko magabatansa anyi komai cikin mutunci. Kuma be ɓoye asalinsa da sana’arsa ba. Baba Muttaƙa ya jinjina saboda sanin wace ce ɗiyarsu amma ganin ita ta turoshi kuma ga yayyunta maza basu tanka ba yasa suka sanya wa abin albarka. Anyi komai cikin mutunci. Tukur ya yi rawar gani akwatuna huɗu ya yi mata da kaya masu madaidaicin kuɗi. Sauran kuɗin kuma ya acewarsa ya kama haya ya yi ƴan ɗinkuna da abinda ba a rasa ba. Murna yake sossai shi ma zai shiga sahun ma’aurata lallai rabon kwaɗo ba ya hawa sama be taɓa tunanin zai  sami wannan dama ba. Yusuf da ya sami labarin auran Labiba ya ji mata daɗi ko ba komai zata huta da tsangwamar dangi. Sai dai ƙasan ransa yana tausayin wanda zata aura ɗin.

Ana gobe ɗaurin aure yasa Shukura ta shirya ta kawo yaran, tsaf da su tare da gundumuwar naira dubu hamsin ya ce a bata. Ƙwarai ya ba kowa mamaki. Labiba kuwa hakan ya ƙara mata ƙaimin komawa gidansa. Wai Yusuf ɗinta ne da yin kyautar dubu hamsin? Lallai jin daɗi na jiranta. Balantan tunda ta sami labarin sana’ar Tukur ana tsegumi a gidansu ya hanata sukuni amma data tuna dalilin auren sai ta watsar da su ta cigaba da sha’aninta. Hata ƴan jere da suka dawo sai da suka yi tsegumin ƙauyen Geza kuma unguwar da za a kaita tsohuwar unguwa ce, gidajen ƙasa sun fi yawa nata gidanma na ƙasane da shafen sumunti. Koda Amne ta yi ƙorafi sai ta nuna shaci faɗi ne kawai, domin ya nuna mata gidan da zasu zauna a wayarsa daya kama a gabatowar bikin kuma acikin unguwar Geza ne ba ƙauyen Geza ba. Domin dai a saninta cikin Sakwato akwai unguwa Geza kuma kuma akwai ƙaramin ƙyauye da mazauna cikinsa suke zuwa cirani cikin Sakwato. Batun sana’a kuma ƙiri-ƙiri ta ƙaryata bayan kuma bakinta dana Tukur ɗin sun yi magana ya tabbatar mata da hakan wanda har zaginsa ta yi a wajen. Amma kuma ta bashi haƙuri gudun kwaɓarta ta yi ruwa. Abinda ya ƙara tsumata jin makarantar da Yusuf ya maida ƴaƴanta, makaranta me tsada da kyau ga yaran ɓulɓul dasu gwanin ban sha awa.

Hidima ake sossai, Amne ma ba a barta a baya ba.

Ranar Asabar da misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Labiba da angonta. Da yamma aka ɗauki amarya aka nufi ƙauyen geza da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *