WATA SHARI’A
CHAPTER 8
Ganin kallonda ake bina dashi yasa duk na tsargu, nayi tsaye a kofar gida kasantuwar babu hanyar shiga,
Ganin nayi tsaye yasa wanda ke bakin kofar duk suka daddare kowa yana kallona, Saurin shigewa gidan nayi gabana sai faduwa yake hankalina ya matukar tashi, Da sauri na shige naci karo da Baba yana kuka sosai kamar karamin yaro,
Hakan ya kara tasar min da hankali matuka,
Wurin Baba na isa tare da gurfanawa k”asa ina kuka,
“Baba meyafaru? mesa kofar gidanmu yake a cike? Mesa kake kuka?” Duka a tare na jefa
masa wannan tambayoyin.’
Bakinshi na rawa yace
“Aishatu ‘yan fashine sun…” ya kasa karisa maganar kasantuwar kuka da yaci karfinsa.
“Baba me ‘yan fashi sukayi? Dan Allah kamin bayani ka daina kukan nan” na fada hankalina a tashe.
Hannunshi ya daga ya gwada min inda aka harbeshi, sai kuma raunuka dake bisa kanshi wanda ban kula dasuba tun shigowata tsabar tashin hankali sai yanzu.
“Na rasa mesa sukazo wurinmu, ni nayi zaton ko sai masu kud’i ‘yan fashi ke zuwa inda suke, sai gasu nan gidan sunzo mana” Baba ya fada bayan ya dafe kanshi saboda wani irin sara masa da yayi,
“Sannu Baba, inma a haka abun ya tsaya ai angode Allah“ na fada cike da tausayin Babana.
“Ba anan ya tsayaba Aishatu, akwai matsala babba, sun d’aure Afrah da Amrah sun tafl dasu…” tun bai rufe bakiba na mike tsaye ina kallon Baba,
“Sun tafi dasu Baba? Wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba wannan cinne ne, turo manasu akayi Wallahi Baba” na kara fashewa da wani kukan ina tunanin furucin Gentle na karshe,
“Lallai babu wanda zayyi wannan aikin sai ita, ko tantama babu itace” na fada a bayyane dukda a zuci naso maganar ta tsaya.
“Wacece ita? Me kike fada ne waima?” Baba ya tambayeni a rikice, Samun kaina nayi da kasa fada masa sai wani irin kuka da nakeyi zuciyata sai tafarfasa take.
“Ki fada min abunda yake ranki Aishatu, bai kamata kiyi shiru ba, waima meya dawo dake daga makaranta bayan kuma jiya kika tafi Ko kin samu labarin abunda ya faru yau d’in ne?”.
Shiru nayi kirjina sai dukan uku uku kawai yake, Hankalina ya kara tashi,
“Baba zan maku bayani amma ka bari sai mutanen nan sun lafa, sirrine tsakanina daku iyayena be”.
Da gudu na karisa dakin mama, na samu dakin cike da mata sai jaje ake mana, hakan yasa nakara fashewada kuka bayan na rungumeta ina sauke ajiyar zuciya, ltakam babu abunda ya sameta alamar basu tabata ba kenan,
A kidime ta janyo fuskata ta kalleni dan a tunaninta ko Amrah ce, saboda bata taba zaton
zata ganni a wannan lokacin ba.
“Mama ashe abunda aka mana kenan, sun tafi mana da Amrah da Afrah, shikenan mama sun gama damu” na sake fashewa da wani kukan.
Sosai mutanen dakin suka tausaya mana, wasu na hawaye wasu kuwa tagumi sukayi kowa da kalar tunaninsa, babban abun mamakin bai wuce yanda kowa yasanmu mabukatane ba amma kuma wai bama barayi masu yawo da sanda ba, ‘yan fashi masu
amfani da binduga sune sukazo gidanmu
Sai wuraren sha biyun dare sannan mutane suka gama watsewa, hakan yasa Baba ya dawo dakin mama ya samemu kowa da abunda yake sakawa, kuka kuwa babu mai
rarrasar wani.
Inda muke ya zauna ya dafa min kafadata,
“Komai yayi zafi maganinshi Allah, sannan kuma dukkanin tsanani yana tare da sauki haka Allah madaukakin sarki ya fada a cikin littafinsa mai tsarki, dan haka dan Allah ku daina kukan nan, bana son wata cuta ta sameku a dalilin haka, insha Allahu Afrah da
Amrah zasu dawo garemu”.
“To muna fatan haka Babansu, Allah ya tabbatar” mama ta fada tare da share hawayenta.
Jikina na rawa na fara labarta masu duk abunda ya faru tun daga farko har karshe babu abunda na boye masu,
Hankalinsu ya kara tashi sosai, sun tausaya min kuma suma sun tabbatarda Gentle ce tayi wannan aiken,
Babbar matsalar yanda take diyar masu kudi, mun tabbatarda ko munkai maganar ga
hukuma babu abunda za,ayi masu.
Yanda mukaga rana haka mukaga dare, ko rintsawa babu wanda yayi a cikinmu, sai koke koke dake tashi wanda har Baba kukan yake yana kara tausayawa rayuwata, saboda yanzu shikenan an rabani da martabata. ‘
Washe gari da sassafe Baba yaje yayi reporting maganar ga ‘yan sanda,
A tak’aice dai saida akayi sati biyu babu ko labarin su Amrah, gashi kuma yanzu har indiyawanda zasu duba Amrah sunzo, likitanta yayi waya yace a kaita za’a nata aiki dan yayi masu bayanin komai, hakan ya kara tayar da hankalinmu, muka rasa duk wata natsuwarmu,
Gashi kuma hukuma ta kas ayin komai akai,
maganarma basu sakeyi ba dukda cikakken bayani da Baba ya masu tun daga
abunda Gentle tasa akamin har ‘yan fashinda suka tafi da kannena biyu.
A ranarda suka cike sati biyun ne aka tsinci gawar Afrah a daidai kwanarda zata shigarda mutum layinmu,
Mutanenda suka tsinci gawar natane suka kawota nade cikin buhu jinajina,
Bayan sunyi sallamah da Baba ya fitane suka shaida masa abinda suka gani,
Amma kuma basu tabbatarda cikin ‘ya’yan Baba bane kawai dai sunyi hasashen hakan
Amma kuma basu tabbatarda cikin ‘ya’yan Baba bane kawai dai sunyi hasashen hakan ne, kasantuwar fuskar dukjinice kallo daya ba za’a iya gane ko waye ba.
A rikice Baba ya kwala mana kira nida Mama, Kodajin kiran muka tabbatarda ba lafiya ba, Dan haka muka fito kofar gida hankalinmu tashe ko dan kwali ban nema ba.
Bayan ya bude buhun ne ya janye yalwataccen gashin Afrah da duk ya baci dajini daga bisa fuskarta,
Baki daya fuskar tayi dameji,
Kayan jikintane ya kara tabbatar mana da daya daga cikinsu ne, ‘Afrah ko Amrah’ saboda mun kasa banbancesu, Jiki na rawa Mama tace
“Ko tantama babu Afrah ce, wallahi Afrahta ce wannan, saboda wannan kayan sune a jikinta, Amrah kuma blue shaddace ta saka ba wannan atamfarba”.
Bansan lokacinda na fasa wani irin ihu mai k’arfl ba, inda buhun yake na tsuguna ina kuka sosai ina kara kallon yanda fuskar Afrah ta koma,
Tam! Na rike buhun ina sauke ajiyar zuciya bayan na nemi hawayenda nake na rasa,
Duk abunda ke faruwa har yanzu Baba ya kasa furta komai,
Saidai kuma kallo daya za’a masa aga tashin hankali karara a fuskarshi.
Muna cikin haka ne wani mutumi yazo, a biye dashi wasu gardawa ne majiya karfi, Cike da izgili mutumin yace “Na gaji da hakuri nikam hakurina ya kare,
Dan haka yau yau din nan zaku barmin gidana,
Shekara biyu kenan ana kan ta uku rabonka da biyan kudin haya,
Dan haka dole ku nemi wurin zama kubarmin nawa yanzu”,
Kallon gardawan yayi yace
“Hame ku shiga ku firfito masu da kayakinsu”.
Da hanzari kuwa suka shiga, mu kuwa kallon mamaki kawai muka bisu dashi, Rashin imaninsu ya matukar daure mana kai,
Basu ko dubi halinda muke ciki ba amma suka ringa jifa da kayanmu,
Hakan ya tabbatar min da cewa wannan ma aikine daga Gentle.
Kara mukaji da karfi Baba ya fadi kasa,
Da sauri Mama ta matsa inda ya fadi din tana kiran sunanshi,
“Abubakar, Abu dan Allah ka tashi, karka tafl ka barmu a daidai lokacinda muke buk’atar taimakonka, dan Allah ka tashi..” kuka yaci karfinta.
Eyyah