bakin ciki da auransa?”
Ta dago ta dubeta fuska share-share da hawaye,
“Gwanda a hada ni da mutuwata yafi min farin ciki da nutsuwa, koda kullum tana daukar numfashina.
Na fada miki ba na sonsa Rafia, amman kin kasa ganewa, wallahi mutuwa zan yi.”
Kasa furta komai tayi sai dai ta bi ta da kallo, abin nata
ya fara wuce misali sai kallo.
Kan ta ce wahi abu taga mikewarta, tana kokarin sa
takalma idonta a rufe.
“Mabaruka ina za ki je?” Rafia ta tambayeta a hanzarce.
Ba ta jin za ta iya bata amsa, ta wuce ta gabanta da sauri. Ba ta tsaya ba itama ta rufa mata baya.
A baranda ta samu cimmata, ta juyo da ita da karfi tana cewa “Wai lafiyarki, ina za ki je?” Yanayinta ya sauya gabadaya.
Ba abin da ka ke gani a idonta sai bakin ciki, idanun
• nata sun sauya launi, hatta fuskarta ta sauya.
Ta tsura mata ido cikin tsananin fushi tana kallo, uffan takicewa. Ita ma ta kura mata idon tana jiran amsarta.
Tsawon dakiku suna haka, kawai sai ta sake juyawa tayi gaba a hanzarce. Ita ma Rafi’ ar ta sake binta.
‘Wani mai adaidaita sahu yana sauke wata mata da sauri ta shige cikinsa, ganin yana Kokarin jan mashin din ya tafi Rafi a tayi saurin shigewa itama.
Mai Adaidaita sahun ya ce, “Ina za kuje?” Rafi’ar ta bita da kallo don son jin ina zata je. Ta yi masa shiru.
Ya sake nanatawa, ta ce “Kai ni ko’ina ma.”
Ya juyo yana kallonta cikin mamaki, “In kai ki ko ina?
Lafiya kike?”
Ta ce, “Lafiya nake, ka kai ni duk in da ya maka.”
Rafi’a ta dube shi ta ce, “yi hakuri Mallam, bari mu sauka bata da lafiya. ” Yaja ya tsaya.
Ta jawo ta da karfi ta fito.
Suka yi cirko-cirko suna kallon-kallo a tsakaninsu.
Tsaki kawai taja tare da wucewa.
Tamkar za su tashi sama tana tafe tana biye da ita suna fada, ta ce “Wai har ina za ki je Mabaruka? Ya kamata ki saurare ni.” Ta tsaya tare da juyo wa a fusace ta ce “Ai bina ki ke, ki sa ido ki gani.” Daga haka ta juya ta ci gaba da tafiya abinta. Abin da ta gani ne ya girgizata, idanunta suka fito, tsoro ya bayyana tattare da ita.
Ganin Mabarukar tayi tsakiyar titi, manya-manyan motoci da mashina sun sa ta tsakiya sai faman horn suke mata. Ta hada go slow, amman ko a jikinta taja tayi tsaye tamkar mahaukaciya.
Da wani irin gudu ta falla wanda ba ta san tana da shi ba, da zuwa ta fincikota da wani irin karfi suka dawo bakin titin, mutane daga ma su zaginta sai masu tir da ita.
•Ita kuwa Rafi’ar saboda tsabar haushi ji take tamkar tai ta falla mata mari. Ta dubeta cikin fushi ta ce da ita.
“Ba ki da hankali ko kina hauka? Auren dole hauka ne ko kanki aka fara? Kina son ki kashe kanki ko Mabaruka?” Tanke ta kasa cewa komai, illa wani takaici da take ji a
•ranta, me yasa Rafi’atu take son zama matsalarta?
Ta ci gaba “Wallahi na kusa raba hanya dake tunda kin canja kin juya halinki, kawai don an aura miki wanda ba kya so, meye laifin mahaifiyarki har za ki ga laifinta? Ba zan ya hada hanya da marar biyayya da da’a ba.”
Don fadin wannan maganar kawai sai ta fashe da kuka, taja da baya ta fadi kasa tim! tamkar karamar yarinya yayayyiya.
Nan ta hau shure-shure tana kuka, abin ya daina ba
Rafilatu haushi illa takaici da jin haushi. Wai me Mabaruka take son zama? Tsakiyar titi cikin mutane take nuna halinta?
Momy kuwa tunda ta fita sai kawai ta hau motarta ta wuce gida, a kokarinta na ta dan samawa Mabarukan wani abu don jin dadinta, musamman abin da tasan zata bukata a. asibitin, ba da jimawa ba ta juyo.
Zata shiga dakin suka hadu da Imran da ledar magungunansa, sai wata ledar shake da su fruits jikinsa har rawa yake yi.
Suka tura Kofar dakin da Mabaruka take suka shiga a tare, amma suna shiga suka ga wayam! Dakin babu kowa.
Suka bi junansu da kallo cike da mamaki, kowa so yake ya tambayi dan’uwansa ina Mabarukar?
Wata Nurse ta shigo ganin shigowarsu, ta ce “Marar lafiyar nan ku ke nema?” Suka hada baki da sauri suka ce Eh.” Ta ce, “Yanzunnan naga sun yi nan ita da wacce ku ka zo tare, har sun shiga mota naga sun sauka sun wuce kuma.”
Bai san sanda ya saki ledar ba ya runtuma a guje har
•yana ture Nurse din. Mamaki ya cika Momy, tayi sake da baki tana tambayar kanta ta fita ina to za ta je?
Su kuwa suna can tana ta bige-bige da ihu saman titi, mutane sun mata caa kowa na kallonta, was na tambayar Raff’ar me ya faru?
Ba ta jin za ta iya ba daya daga cikinsu amsa, takaici ya cika zuciyarta, ta dinga zubar da hawaye tana gogewa, saboda abin da Mabaruka take ja musu saboda shegiyar kafiyarta.
Ta tsaida Adaidaita sahu, da kyar ta samu ta tura ta ciki ta rirrike ta tamkar hauka sabon kamu, a kan ita wallahi ba inda zata je sai ta kyaleta an kasheta a wannan titin.
Gidan Momyn suka sauka, ta jata suka shige ciki. Still dai ba ta fasa shure-shuren ba, ita a lallai sai ta mutu.
Koda ta shigar da ita dakinta bata fasa ba, taja ta jingina da bango ta dubeta ta ce, “To ci gaba da yi har ki kashe kan naki don Allah.”
Karshe ma fitowa tayi ta dawo falo tayi zamanta tare da
Hmmmm