WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 12 BY MARYAM JAFAR KADUNA

. rafka tagumi tamkar tana jira, tana fita ta maida kofa ta bame bam!

Ta ci gaba da buge-buge duk abin da ya tari gabanta sai ta kai masa duka.

Hankalin Rafi’ar ya tashi, tsoro ya kama ta kar fa ta kashe kanta kamar yanda take bukata, tayo dakin tana bubbuga mata ta bude, tamkar ba ta dakin bare ta amsa. Tana jin ta tana kashe glass din mirror da na drower, yan kwalaban turaranta su Humra ta dinga kashe su.Ta ci gaba da rokonta a kan ta bude don son Annabi,ganin ba za ta bude ba yasa a rikice jikinta har rawa yake ta lalubo lambar Imran.

Shi kuma a lokacin ya fito sai wiage-waige yake, ya yi nan ya yi can yana son gano ina suke? Sam babu nutsuwa a tare da shi.

Kiran da Rafi’ar tayi masa ne a waya yasa da sauri ya dauka ya kai kunne don yasan suna tare da Mabarukar.

Ta fashe da kuka tana cewa “Ka zo ga Mabaruka, nan a daki ta rufe kanta tana ta buge-buge, wai sai ta kashe kanta.”

Ya Kara rudewa, jikinsa ya hau rawa ya ce “A wane gidan?” Ta ce, “A nan gidanku.” Bai sake cewa komai ba ya tura wayar aljihu ba tare da ya ko katse kiran ba saboda tsananin firgita da tashin hankali, da gudu ya shige mota ya jata a guje.

Mintuna kadan suka kai shi gidan, Momy ta fito kenan taga jan motarsa. Tabbas tasan ba lafiya ba, hankalinta ya Kara tashi. Cewa ta ke “Oh ni! Me ke faruwa kuma ina zan yi?” Dukta birkice ta rasa me zata yi. Shi kuwa Imran ya isa gidan a gaggauce ya shige falon.Yana shiga ya kwankwasa mata kofar tare da cewa “Bude mana Mabaruka nine.”

Tana jin muryarsa, sai ta kara wuta a kan abin da take yi. Ya sake cewa, “In dai ni ke sa ki wanna tashin hankalin zan kyale ki Mabaruka, ba na son kiyi asarar ranki, ki yiwa mahaifiyarki ke kadai ke gareta, ki tausaya mata ko don ita kadai ki bari kada ki kashe kanki. Ba zan zama masifa a rayuwarki ba, amman ki bude zan miki duk abin da kike so.”

Iya, nacin ya yi mata amman ta ki sauraronsa, ji yake kamar ya fasa bangon ya shiga ya daukota, har cikin ransa yake jin kukanta wanda da jinsa ta gaji da yinsa, ga fashe-.fashen, abubuwa da take idan ta fasa wani abu har sai ya razana, ji yake kamar a jikinta take fasawa.

Ya ci gaba da dukan kofar yana mata magiya, ya damu Kwarai duk a kansa take wanna haukan, har take Kokarin rasa ranta, meye laifinsa? Meye illarsa? Ko dai yana da wani abu ne na aibu wanda ba kowa ke gani ba sai ita?

Rafi’atu ma bata gaza ba, wajan bata hakuri da lallashi.

-Tun suna jin motsinta da gunjin kukan har suka ji dif!

Hankalinsa ya Kara tashi, toro ya bayyana a tare da shi, zufa ta keto masa, ya hau tambayar kansa meye ma’anar shirun da tayi?

Tsawon awa kenan ana abu guda.

Kai da yaga abin ya wuce misali, ficewa ya yi da sauri ya nemo masu kwance Kofa. Nan da nan kuwa aka kwance

Kofar, har yana buge mai aikin ya fada dakin a rikice.

Kwance ya ganta saman tails, gabansa ya yanke ya fadi. Ya hau jjjigata. Can ta bude ido a wahalce, idanun nata sun rine sun Kankance saboda kuka, muryarta ta dishe ta kasa tsayar da idonta. A rude yake cewa, “Lafiya Mabaruka menene?” Ba ta

¡ya ba shi amsa ba, yum! yum! haka take jin kanta wani iri.

Rafilatu ta fashe da kuka tayi tsaye ta kasa karasawa kusa da ita, tsoronta kar dai wani abu taci ko ta sha.

Shi ma haka ne a ransa, a tsorace ya ce “Me ki ka ci Mabaruka?” Ta kasa ba shi amsa bata san ma da wa take magana ba.

Ya sake nanatawa a wahalce da gajiya ta ce, “Ba komai ban ci komai ba, na gaji yunwa nake ji, ku bani abinci naci yau kwanana biyu ban ci abinci ba.”

Ya juyo yana kallon Rafia cikin farin ciki.

“Ba ta ci komai ba, ina ga kukan da ta dade tana yi ne yas ata gaji, ba ta ma cikin hayyacinta.” In ji Imran.

Ita ma farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta durkuso tana cewa, “Mabaruka!” Ta dago tana kallonta a wahalce, ta ce a hankali “Rafia, Rafiatu ba ni abinci.” Ta ce, “Yunwa ki ke ji?” Ta ce, “Eh.”

Da kanshi ya hado mata tea ya dagata ya jinginar da ita jikinsa kanta saman kafadarshi, a hankali yake bata tea din.

Ta ci gaba da sha, ta sha sosai har sai da yaga ta koshi sannan ya kwantar da ita. Duk dakin ta birkita shi, duk wani abun fashewa ta fashe shi tas! Koda Momy ta dawo taga abin da ya faru har da kwance kofa. Rafia ta ba ta labarin yanda abin ya faru.

Ranta ya baci sosai, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Ta dinga wa Imran fada sosai, kan me zai biye mata ya kyaleta mana taje ta kashe kanta mana, wa ta yi wa?

Ta san dai hukuncinta, shi dai ya dinga bata hakuri, hankalinsa na kan matarsa wacce take barci bata san me ake ba.

Ta shige dakinta tana fada, “Za ki tashi ki same ni, fitsararriyar yarinya kawai marar jin magana.

** **

Sulaiman kuwa wannan ihu da ya dinga yi ba arziki aki sa shi a mota, amman duk da haka kokari yake ya fito shi sai an ba shi matarsa.

Gidan Inna aka kai shi, bai fasa ihun ba.

Sai da aka banka masa magunguna don ya samu bacci ko ya lafa. Baccin kuwa ya dauke shi, nan da nan yana sambatu.

Inna ta numfasa tare da cewa “Dankari! Nan fa ake

Hmmm