Tare muka ci abincin yana santi, a kullum yakan tambaye ni wai ina na koyo girke-girke, shi wallahi bai taba
•cin abinci irin nawa ba. Na kan ce abin sirri ne amman zan fada maka.
A kan hanya muna mota shi ke tuki, ina gefe dukkanmu mun sha kwalliya, labari muke amman naga ya yi shiru.
Na dube shi na ce, “Ya Imran!” Ya nisa tare da kallona na ce “Lafiya, me ke damunka?”
Ya kalle ni da kyau ya ce, “Kina son ki sani?” Na daga kai tsaye ya ce “Aure nake ‘son yi Mabaruka.”
Na fito da idanu da bude baki cikin murna na ce ” Aure
Ya Imran?” Ya ce, “Sosai, kin yi mamaki?”
Nayi dariya na ce “Dole abin mamaki ne mana, nifa ban taba jin kayi maganar mace ba bare aure, a tunanina ko ma ba za kayi auren ba a rayuwarka.”
Ya zaro ido ya ce, “So ki ke in mutu kenan? Ina! Ba zan iya ba.” Nayi dariya ina kallonsa cikin mamaki na ce, “Don ba ka yi aure ba sai ka mutu?”
Ya ce, “Of course! Son da nake wa yarinyar zai iya hallakar da ni.” Na kalle shi na ce, “Wannan wace ‘yar baiwar ce ka ke so har haka daidai da ranka?” •Ya yi dariya sosai tare da dukan sitiyarin motar ya ce,
**Kina son sanin wacece?” Na ce, “Eh!” Ya ce, *Kin santa ai.”
Na ce, “Na santa! Wacece?” Ya kalle ni a nutse kamar ba zai fada ba sai dai naji kamar daga sama, ya ce “Ke ce mana.
“Na kalle shi da sauri na ce “Ni kuma big bro?” Ya ce,
“Ke Mabaruka.” Yanayina ya sauya na ce «Please! Ya Imran ka daina tsokanata, ka san ba ma haka da kai, ka fada min kawai wacece?”
Na karasa ina dariya fuskarsa ba wasa ya dube ni ya ce,
“Mabaruka!” Na kalle shi tare da amsawa. “Na’am!” Ya ce
“Ba wasa nake miki ba, tunda kin ga ban taba miki irin wannan wasan ba.”
“Wallahi da gaske nake, ina sonki tun ba yau ba, tun
‘kina Sakandire aji daya (SS1), kusan shekara shida kenan, kuma wallahi aurenki zan yi serious (da gaske).”
Fuskata ta sauya sosai, na ce “a,a bari Ya Imran, bana son wasa fa.”
Ya ce, “Na fada miki da gaske nake, kina maida magana
baya. Cikin week din nan zan kai maganar nan gunsu Daddy, ba wani bata lokaci za a yi ba in aure ki in kai ki gidana.
Kin ga shi kenan hankalinki kwance kin san wa za ki aura, Imran din ki ne da ki ke tattali, tun-tuni sai ki zarce na tabbata hakan ba zai miki wuya ba tunda kin saba. “. * Tun da ya fadi maganar nan bakina ya kulle, jikina ya mace, na rasa me ke min dadi.
Har muka je muka dawo ba ni da kuzari. Na zo kwanciya tunanika suka rufe ni, wai me hakan ke nuff? Shin anya Imran yasan so ma kuwa? Kawai don yaga muna dan raha da wasa sai ya ce so wai yana sona?
•Kai! Ina bai san so ba, ni dai nasan ina son Sulaiman don haka gwara tun wuri ta taka masa burki kar abun ya yi nisa a ransa bare su Daddy su sani.
Ban yi tunanin komai ba na tunkari dakinsa ya fara shirin kwanciya ya ganni.
Na wuce shi inda ya bude min Kofar na zauna kujerar da ke dakin na zauna a sanyaye.
” Ya dawo ya zauna kan gado yana facing dina ya ce cikin damuwa my dear me ya faru?
Kalmar ba ta min zafi saboda haka muke kiran junanmu amman wannan lokacin sai naii zafinta sam bata dace ba, ta fito daga bakinsa ba na ce a tausashe.Ya Imran!” Ya ce, “Na’am, menene?”
Na ce, “Magana nazo muyi da kai.” Ya ce, “Ok, ina jin
“ki menene?” Na daga kai na kalle shi ganin yanda ya maida hankalinsa gabadaya gare ni yana saurare.
“Maganar da ka min dazu ce nake son mu tattauna.” Ya ce, “Ok.
” Na ce “Maganar gaskiya Ya Imran ba ka fahimci so ba, ko don baka taba yin shi ba, amman wallahi ba sona ka keba kawai dai mun shaku ne, nima haka ba na sonka.” Maganar ta ba shi mamaki, amman ya ce “Mabaruka kenan! Ke yarinya ce, a tsawon zamanmu da ke ya kamata ki fahimta ko don wasu abubuwa da nake miki, amman da yake yarinya ce ke kin gaza fahimta, har na fito yau na fada miki. Tabbas ina sonki, kuma kema kina sona.
Na dago ina kallonshi nace, “A’a Ya Imran ba haka ba ne, kar maganar nan tayi tsawo mu barta a nan, ka cire maganar so tsakaninmu, don ba zai kasance ba, bana jin sonka a raina, wallahi akwai wanda nake so, don Allah ka fahimce ni.”
Idanunsa suka kada jajir, ni nasan bacin rai ne amman ya dake ya ce “A’a Mabaruka, to ba wani wanda za ki so sai ni, in ma ba ki so to ki Kokarin sa shi a ranki, don jin dadinmu ni da ke, wallahi da gaske nake ni dai ina sonki.” Na mike tsaye na ce, “Don Allah Ya Imran ka bar
tsokanata, wallahi akwai wanda nake so.”
Shi ma ya mike yana cewa “Ba na tsokanarki ni dai ina sonki zan aure ki kema za ki gane hakan a hankali, zan koya miki.”
Wucewa nayi ina cewa, “Ni dai na fada maka ka daina daukar abin wasa, wallahi da gaske nake.
Ya biyo ni zai rufe kofar yana cewa, “Ni ma ba da wasa nake ba, ina sonki ki sa haka a ranki.
Ban iya cewa komai ba na juya nayi wucewata zuwa dakina, ya rufe kofarsa ya koma ya kwanta hankalinsa kwance.
Tun daga wannan ranar alakarmu ta canza da shi, muka rage walwalar da muke da shi duk da yanda yake kokarin ja na. Abu kamar wasa ganin yanda ya dage yana sona.
Hakan yasa na dage nima ina nuna masa ba haka bane ni ba na sonsa, bai gane ba, har na fara nuna masa tsantsar tsanarsa, kamar yanda nake jinta a raina, har kawo yau ba