WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 5 BY MARYAM JAFAR KADUNA

Ya yi dariya ya ce “Sorry my Princess, juyo ki karba kici.” Tamkar ba ta gun bare ta amsa, ba yanda ta iya ne yasa take zaune a dakin, dakin ma akan gado, gadon ma kusa da shi har tana jin saukar numfashinsa, ta ce a ranta tir!

Ya ce, “Ok, tunda ba za ki yarda in ba ki ba ni ba ni.” Ya juyo da ita ya mika mata cokalin, ba ta da shirin karba.

Ya ce, “To, idan har ba ki yarda na ba ki ba, ko ki bani wallahi a nan za ki kwana kuma abin da kike tsoro sai ya faru.”

Hankalinta ya tashi ainun idanunta suka yi rau-rau, wallahi ita dai an cuce ta tunda aka hadota da shi bayan an san bata sonsa.

Kawai hawaye suka fara sintiri a kumatunta. Ta jawo cokalin tana Kokarin ba shi, idanunta a rufe taf da kwalla.

Ya fahimceta tabbas ba da son ranta zata yi ba sai don ya matsa mata, jikinsa ya yi sanyi tausayinta ya kama shi kanta na kasa ya dan leka fuskarta.

Cikin damuwa ya ce, “Mabaruka!” Tayi shiru tana shesshekar kuka, ya sake nanatawa a dan rude. ya ce,

“Menene Mabaruka?” Kukan ya soma fitowa.

Ya birkice ainun yana cewa, “Ni ne ko nine na sa ki

kuka? Sorry ba zan kuma ba.” Ta ci gaba da kukanta tana kokarin ba shi hannunta na kusa da bakinshi.

Ya janye hannun yana cewa “Is ok! Is ok! Sorry na fasa wallahi am joking, please ki bar kukan kin ji ko?”

Ba ta fasa miko masa ba, sam ya daina sha’awar ta ba shi din, kukanta ya birkita shi ya tada masa da hankali gefe kuma tausayinta da ya cika masa rai.

Ya tsugunna gabanta tare da riko hannuwanta bayan ya cire hannun daga kan abincin ya rike ta cikin kulawa da damuwa yana cewa.

“Is ok Mabaruka, ki bar kukan na fasa kin ji ko?” Ta daga kai kurum. Ya dan leko ya ce, “Kin bar kukan ko?” Ta sake daga kan ya ce, “Promise?” Ta sake daga kanta:Yace,

“Ba zan sake miki haka ba, bana son kukanki kin ji my angel?” ta dai daga kan.

Ya ce, “Please, say something mana am compused.” Ta ce, “To.” Kawai ya ce “Thanks my Mabaruka.” Ya koma ya zauna idanunsa still a kanta ya ce, “Za ki wuce dakinki in bude miki. kofar ko za ki dan ci abincin sannan.”

Ta dan dago ta kalle shi second biyu ta sunkuyar, haka

nan taji gwanda ta ci ko ya ya ne tunda har ya damu: taci kuma ya barta ta tafi din.

Duk da hakan da ya yi ba burgeta ya yi ba, ta ce a can

Ta ce, “To.” Kawai taja cokalin ta fara kaiwa baki tana ci don dole, sam abincin bata jin dadinsa ko don shi ya bata taci kuma a dakinsa.

Yayin da shi kuma ya zuba mata ruwa a cup ya rike mata yana jiran ta bukace shi ya mika mata idonsa kur a kanta yana jin matsananciyar kaunartà na karuwa.

Ta mika hannu ta karbi ruwan tasha, zata aje ya yi saurin amsa yana cewa “Kawo in rike miki.” Ba ta ce komai ba ta mika masa.

Ta ci abincin sosai da ruwan, dadi ya dinga ratsa shi gashi gata ina ma a gidansa ne.

Ko da ta gama taja tayi zaune ita bata tashi ba ita bata ce komai ba, ya dubeta ya ce “Kin koshi ko?” Ta daga kai kanta a kasa.

Ya sake cewa “Muje in bude miki ko?” Ta ce, “Um!” Kawai ta ce tare da mikewa tana gaba yana baya har bakin Kofa, ya duba baiga kayan ba ya tuna ya jefa bayan wardrove.

• Ya jawota ya dauko ya bude mata yana kallonta cikin fara’a sai da safe ko? Ta ce, “Eh.” Ya sake cewa, “Ko in raka ki?”Tace, “A’a” tare da wucewarta.

Ya yi murmushi kawai tare da binta da kallo har ta tura dakinta ta shige suka yi ido biyu, ya dago mata hannu.

Sunkuyar da kai kurum tayi tare da jan kafarta ta datse.

‘Kan gado ta fada tare da fashewa da kuka, kukan alakakan hada ta da shi, kukan takaicin kasancewarta da . shi a dakinsa, yau cikin darennan.

Duk yanda zuciyarta take azalzala akan kiyayyarsa. Ta ci kuka son ranta daga bisani ta mike ta shige toilet don• wanka, a ganinta akwai datti a jikinta saboda tabata da ya yi shi kuwa a wannan daran ya yi bacci me matukar dadi da mafarkin Gimbiyar tasa cikin walwala da annashuwa.

Washegari tunda safe karfe goma ta bar gidan, koda

*Momy ta tambayeta ina zata je tunda safe ta ce gidan su Rafiatu. Don haka kai tsaye can ta nufa tun kan nataccanta ya tashi. Da zuwanta ta fashewa Rafiar da kuka tana bata

labarin abin da ya faru jiya da kokarin da ya yi.

Ta ce, “Na shiga tara ba uku ba Rafi’a, da Imran ya cutar da ni jiya wallahi da na roki mutuwata a kan na juri kasancewata da shi, tanadina Sulaiman.

Imran ba shi ba ne Angon bare ya kasance da ni.” Ta dube ta ta ce, “Ni fa ba na son hauka Mabaruka da rashin

hakuri, kan dan wannan abin za ki nemawa kanki mutuwa don rashin hankali?”

Ta ce tana kallonta a marairaice “Har yanzu ina Kara

fada ba ki san kiyayya ba, ba ki san dacinta ba a rai.”

‘Gabadaya za ki rasa me ke miki dadi, musamman idan kina ganin wanda ba kya son din bare kuyi rayuwar aure tare, wallahi ba ki san sanda za ki roki mutuwa a kan kasancewarki da shi ba na rantse miki.”

Ta tabe baki tare da kauda kai tana cewa, “Ina neman

tsari da wannan tsanar ko wanda ba ya sona ba na fatan na mishi wannan tsanar.”

Ta ce, “Ba wannan bama Rafia, zullumin gobe nake ya

zan yi idan hukuncin da Alkali ya yanke min wanda bai min dadiba.

Ta ce, “Biyayya mana, ki karbi abin da Allah ya zaba

Hmmmm