WAYE ANGON CHAPTER 10 BY MARYAM JAFAR KADUNA
Imran yake fada, shin cikinsu waye na gaibun waye tabbas?
Zuciyarta ta cunkushe tai mata nauyi har daci-daci
take ji, madadin kalamansa su sanyaya ranta sai ma suka
Kara ingizata har dai suka gama wayar bata samu wata
nutsuwa ba,
Sha daya da rabi na dare Imran ya dawo, sam mutane
basu bar shi ya huta ba tun yau kenan a gajiye ya shigo
gidan kai tsaye dakinsa ya sauka ya rage kayan jikinsa
ya dan watsa ruwa ya dora jallabiya ya sanyo slipas ya fito.
À filo suka ci karo da Momy, ta ce
“Ka dawo
kenan?”
Ya ce yana sosa keya
“Eh shigowata kenan
mutane suka rike ni.”
Tace,
“Akwai haka kam, hidimar kenan. Abinci fa?”
Ya ce,
“Ban ci ba tukunna, yanzu dai zan ci.
» Ta ce,
“Ok, kaje ga shi can a dining naka kadai na ce a aje can.”
Ya ce,
‘«To ya Jama’a sun fara taruwa ko?” Ta ce, “Ai
kuwa an gaji wasu sun kwanta wasu kuma ga su can suna hira,
Ya yi murmushi ya mike ya nufi dinning din yana cewa,
“Daddy fa bai sauka ba?”
• Ta ce, Eh sai gobe,
mun yi magana da shi a waya har ya zo airport kuma ya
koma, amman idan komai yai clear zai taho gobe in
kuma sai jibin to
Ya zauna yana cewa “Ya kamata dai yana nan aka
daura auran, ban so tafiyar nan America ba ko da ya fada
min sai da gabana ya fadi.”
Ta ce, “Ai ko ko shi haka yace bai so ba. Yafi son
yana nan ake hidimar komai, amman ya ce ko bari ne sai
ya yi yazo ranar daurin auren akwai abokanshi da za suZo wasu ma Turawa ne da Larabawa, yana da kyau kuma
suhadu.
Har ya gama dai suna hirarsu, daga bisani suka yi
bankwana ya shige dakinsa ya kwanta saboda gajiya
bayan ya cire jallabiyar jikinsa.
Dare ya fara, sam! Ta kasa bacci, sai juyi take
damuwarta ta hanata bacci da bakin ciki, tuni Rafiatu
tayi baccinta har tana munshari.
Imran shi kadai ya zama matsalarta da babu shi tana
jin bata da damuwa, duk shi ya kunna wannan fitinar, da
bai ce yana sonta ba hankalinta kwance.
Ya zama kadangaren bakin tulu, yanda Momy ke
sonshi da alama ba ta sonta haka, tunda ta zabi farin
cikinsa a kan nata. Yanzu in ban da don ya kona mata rai
meye na wani Kirkirar party?
Bayan ba shi da tabbacin shine angon. Me yasa bai
hana su ba ya nuna ba ya so? Yana son ta ba shi kunya kenan?”
zuciyarta ta bata shawara, don haka bata yi
tunanin komai ba ta diro daga gadon ta fice daga dakin.
Dakinshi ta tunkara sha biyu ta gota, kofar a bude
take tana taba handle din ta bude.
Bai samu ya yi bacci ba a lokacin yana dauke da iPad
suna magana da wani abokinsa ta social network daga kasar Saudiyya.
Kwatsam! Yaga ta shigo masa, abin ya ba shi
mamaki matuka, yarinyar da ta tsane shi ko kallonsa ba
ta yi, to me ya kawo ta dakinsa a wannan lokacin?
Daga shi sai shortniker ba ko singileti. Ya yi saurin
mikewa yana cewa,
‘”Subhanallah! Mabaruka lafiyarki
ki ka shigo min daki babu sallama?”
Ya jawo
jallabiyarsa ya saka don kare mutuncinsa,
Ya ci gaba “Ba kya tunanin a ya za ki same ni wanda ba zai miki dadi ba?”
Ta zumburo baki daga in da take tsaye jikin kofa tace.
«Ni ina ruwana, wannan ba shine gabana ba.”
Ya yi murmushi ya ce,
“Ok! Naji to meye gabanki?”
Tayi mai banza tana turo baki. Ya sake cewa,
“Mabaruka
menene?” cikin kulawa.
Ta ce tana kumburi
“Magana nake so muyi.” Ya ce,
“Da ni kuma?” Ta yi masa banza. Ya sake cewa makiyin naki?
* Yana murmushinsa mai kyau.
Ta ce cikin fada,
“To in ba da kai ba da wa zan yi?
Dakin wa ka ga na shigo?” Ya ce,
“Kiyi hakuri to dakina
ne, naga ko muryata ba kya son ji bare ki ce kina son magana da ni.”
Ta ce cikin Kufula ba tare da ta kalle shi ba. “Ni ba
nazo nan don in ja magana ba da surutai marar ma’ana
bane kawai nazo ne na taimake ka.
Ya kalleta da kyau ya ce, “‘Ok, bismillah zo ki zauna ga kujera.
“Ya nuna mata kujerar da ke facing din shi. Ta
juyo tana harararsa ta ce,
“Ba zama ya kawo ni ba, ka
daina tunanin zan iya zama dakinka Ya yi murmushi yaCe,
“Maganar ba ta da
muhimmanci kenan tunda a tsaye za a iya yin ta. A zatona tana da girman da za a girmamata,
» Yana rufe baki ta dauka.
“Na gaya maka ban zo nan ba don surutai marar ma’ana ba, ka saurare ni kawai
Ya nisa ya ce,
, “Ok, kin ce ni za ki taimaka, to na gode
kije kawai idan har ba za ki iya zama ba, ba zan iya
saurararki ba kina tsaye ina zaune, kin gane ko?”
Ta harare shi cikin tsananin jin haushinsa har ita zai
wa barazana, don haka ta kulu kawai ta juya fuuuu ta fice
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe