WAYE ANGON CHAPTER 21 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 21 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

dashi, dangane da wuyar rayuwa na talauci, Mun yi yawon haya gida-gida a lokacin kudin hayar ma gagararmu yake sai dai mu biya rabi kan ya Kare zamu harhada da”‘ yan kasuwancin da muke ni da shi mu biya.

Tun bayan barin wajen aikinsa inda yake wankin hula. Kwatsam sai ga wani sabon kamfani an bude ana neman ma’aikata

Don haka bai yi wasa ba yaje cikin sa’a aka dauke shi aikin. Ba laifi albashin da albarka, na daya na biyu ana uku ya harhada ya sai fili.

Muna nan dai rayuwa ta fara sauki shi kanshi ginin yana yin shi gutsin-gutsin in an samu ayi, yanayin dai ginin talaka bai gama ginin ba aka samu matsala a kamfani aka kulle, don haka sai dai ya koma sana’ar wankin hularsa.

Haka dai rayuwar ta ci gaba da gangara mana ganin mun kusa gama ginin mahaifiyarmu ta rasu, to gadona da shi nayi amfani na sayar da dan abin da ke gareni daga kayan daki da ‘yan canjina na tattara na ba shi ya Karasa ginin. Daki biyu ne shi daya ni daya, muka tare hankalinmu kwance, lokacin Mabaruka na yayeta. Ban fasa sana’a ba ina yi mu kanci abinci da kyau shima ya kawo abin da ya samu, don haka sai rayuwa tai mana sauki, ga shi ba yawon haya a gidanmu ne ga

sana’a muna yi ni da shi. Wata rana, ranar Asabar ina zaune ina yankewa

Mabaruka farce ya shigo da kaya niki-niki a hannunsa, na bishi da kallo ina cewa.

“Malam daga ina haka afujajan da kaya?”

Ya zauna tare da mike kafa yana cewa,

“Ke dai bari, daga kasuwa nake.Na ce,

“Kasuwa kuma?”Ya ce,Eh! Na bude na gani.

Atamfofi na gani har guda uku, sai leshi daya da hijabi da takalma sai “yan kayan shafa. Na dago ina kallonsa na ce, “Wadannan kayan fa?” Ya ce,Kanwarki taja min sayensu, naki ne.

“‘Na ce,Ban fahimta ba, wace kawar?” Ya ce,

“Ku fa mata akwai ku da basarwa, wace Kanwa ki ke tunanin zan kawo miki? Abokiyar zama mana wacce Mabaruka zata

sami “yan kanne.'” Ya fada yana jan Kafar Mabarukar yana mata wasa.

Idanuwana- suka fito na ce,

“‘Aure ka ke nufin za kayi?” Yayi dariya ya ce, “Yawwa ‘yar gari ashe kin gane,

aure fa. Jibi take tarewa.Matuka raina ya baci, saboda ganin ya raina min

wayau, yana kallon wuyar da muka sha na rayuwa duka yaushe muka fara samun sauki, amman ko shekara bamu kulla ba ya fara zancan aure.Wai har jibi zata tare, kenan an daura aure tunda har ana maganar tarewa? Na dai daure na ce “An daura kenan?”

Kai tsaye ya ce, Wallahi yau mako daya kenan,

anjima masu yin farar Kasa za su zo su dan shafa mata a dakin, in ya yi ragowa kya samu.

Na ce, Allah sa alkairi, na gode da fenti ita dai da da yake sabuwa ce a mata tafi bukata.

” Ya ce,Ah to ba laifi bana tunanin ma zai isa.

Na Kara cewa, Amman kana ganin adalci ka min  a daura maka aure ba ka sanar da ni ba sai ana jibi tarewarta Sannan  zaka sanar min?”Ya ce,Kiyi hakuri bana son ki tayar da hankalinki ne, amman yanzu tunda an riga an yi damuwarki da sauqi

: “Daga haka ya mike yasa takalma ya fice.

•Koda amarya ta tare nasha mamakinsa matuka, kiri-Kiri ya canza baya jin komai gabana yake rawar jikin

matarsa kamar bai taba aure ba.

Hatta cefane ya fara canzawa idan ranar girkina ne sai ya dauko Naira dari ya bani ya ce ba shi da lokacin” zuwa kasuwa in sai abin da zan siya ayi maneji Idan kuma ranar girkinta ne haka zai shigo da ledoji

fal da kayan miya, kaji da cefane ko kifi tayi girki gaje-gaje ta juye musu a ledar da naman ni ta bar min saura a tukunya.

Duk idan nayi magana ya hau fada, ai ba ni da hakuri shi ma ba daga shi ba ne kawai dai abin da ya sani ita ta shigo da kafar dama shi yasa. duk ranar girkinta aljihunsa yake jinsa da nauyi. Wata ranar girkina zai fita da safe ya miko min Naira dari ya ce “Ga shi nan in sai kayan miya yana saurine.Naki karba na ce

“Ka ba yaro ya siyo ai ba a rasa mai

siyowa ba, ba lallai sai ni naje na siyo ba.”

Ya ce,Wane yaron nake da shi zai siyo?” Ya jefo min ya wuce yana cewa, “In kin ji yunwa kin siyo.” Yai ficewarsa.

Dole tunda ina jin yunwar da rana tayi na dauka naje na siyo wake gwangwnai dayan da dan barkono da manja na dawo na girka.

‘Abincin nan da na gama na ba Binta matarsa ko kallonsa bata yi ba bare taci, ni dai naci haka zalika shima da ya dawo na kawo masa ya ce a koshe yake. To a ranar ta karbi girki tun da ya shige dakinta ban Kara jin motsinsa ba.Washegari tunda safe ya fice, ashe kasuwa yaje sai gashi da kaya dam a hannunsa, ya wuce dakinta ya kai

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *