WAYE ANGON CHAPTER 27 BY MARYAM JAFAR KADUNA
gurin nan ba sai ke? Me za ki je kiyi a gidan to?”
Ta ce, “Ni fa ba zan iya zama ba, don ba abin da zan masa, ai dai nazo yafi ace ban zo ba.”
Daga haka taja hannunta za su wuce.
Ta dubi Sharifa ta ce,Za mu tafi, Allah ya
sawwake.Ba ta amsa mata ba sai dai harara saboda duk saboda ita ne za a kashe mata dan uwa, bata damu ba ta juya abinta.
A bakin kofa suka ci karo da Momy da ta fita raka
Daddy. Wata irin harara tayi mata ta ce, “Ina za ki?” Ta turo baki ta ce, “Gida, na gaji.”
Momy ta wuto cikin dakin tana cewa, “Ba in da za ki, in kin tafi waye zai kular miki da shi? Duk cikinmu wa yake da alhakin jinyarshi in ba ke ba, shine za ki sa kafa ki fice?”Tayi shiru tana fushi, ita bata tafi ba ita bata dawo ba, ganin hakan yasa Rafi’ar ta sakar mata hannu ta dawo ta
zauna don daman bata gamsu ba.Ta sake cewa,
“‘Za ki dawo ko sai nazo na karya miki Katafuwa, daidai ki ke da da ne? ba ki da damar da za ki
je wani guri ba tare da izininsa ba.Fadin wannan maganar ya kara harzukata, dole ta dawo tana cika tana batsewa kamar zata fashe.Tayi zaune Kasa saman tayils din ba tare da ta ce wa
kowa komai ba, suma suka shareta kamar ba ta dakin.Ya lura da inda take zaune, sam bai ji dadin zamanta Kasa kuma a asibiti, ya buda baki ya ce,
“Mabaruka!” Tana jin sa amman tayi kamar ba dashi take ba, kanta na gefe. Sharifa ta juyo ta kalleta. Wai wannan zata dinga wulakanta mata dan uwa? Wacece ita da take jin kanta, har tana jin ita isassa ce?” Tayi kwafa tare da harararta ta dauke kai. Ya sake kiranta. Nan ma ba ta amsa ba. Sharifar ta ce tana kallonsa “Menene Yaya? Me za a yi maka?” Ya ce, “Da Mabaruka nake. Ta tashi daga kasan can akwai matsala zamanta a kasa..” Haushi ya turniketa,kan me zai damu da ita alhalin ita bata damu da shi ba? ‘Sannu’ ba ta hada ta da shi ba, tunda abin ya faru sai
shi zai damu kanshi da ita? Ta fada bata sonsa kuma ta bayyana a zahiri, don haka babu dalilin nace mata, gwanda kawai ya barwa Sulaiman din can su karata.Momy ta ce, “Rabu da ita Imran, tayi ta zama ai ta san akwai illa baka da lafiya kana bukatar hutu.” Zai yi magana ta dakatar da shi “Ya isa haka, koma ka kwanta.
.” Baya son musu, don haka dole ya kyale yayi lamo idanunsa a rufe amman ba abin da yake gani a idonsa sai Mabarukar.Bai san me yasa ba, daga sanda aka daura aurannan wani sonta ke kara ruruwa a ransa matsananci, wanda bai taba jin irinsa ba, a yanda yake ji zai iya komai don
Kwatar matarsa, zai kuma jure komai ba zai yarda ba a kwace masa mata ba alhalin kowa yasan shi ne ANGON. Rafiatu tazo kusa da ita ta dubeta tace, “Mabaruka!”Ta dago tana kallonta, ta ce “Ba kya jin magana ko?”Tayi shiru tana gimtse baki ta ce, “Mijinki ya yi miki magana ki masa banza, ki ki yin abin da ya ce.Wani kallo da tayi mata jin ta ce wai mijinta, tamkar
ta fasa mata baki. Ta ci gaba da cewa,
“To in shi ya yi miki laifi don ya ce yana sonki, ita Momy me ta miki don ta hada aurenku alhalin tana sonki?”Tayi dai shirun taci gaba “To ai kin tashi saboda darajar haihuwarki da tayi, kada ki Bata kanki Mabaruka kan son zuciyarki, ki zama marar da’a da rashin kunya,Allah zai yi fushi da ke saboda rashin yiwa mahaifiyarki biyayya kina bata mata rai gefe kuma ga na mijinki.”
Ba ta da alamar tankawa bare ta tashi din.
“Ba za ki ji abin da nake gaya miki ba, wallahi ni ma zan nesanta da ke, zan kyale ki kije kiyi abin da kike so,ba.zan iya tafiya da wacce bata da da’a ba.Daga haka ta yunkura zata fita:
Da sauri ta tashi ta koma kan kujera ta zauna, sannan ta dawo.Yayi murmushi ya kalli Rafi’ar a hankali bakinsa ya furta”Thanks Kasancewar yanda suke da kusanci da Sharifat da
Mabarukar duk sanda tazo hutu tamkar tagwaye, su kwana tare su wuni tare, su fice yawo wurare-wurare, hatta kayansu wani lokaci iri daya, kan ta dawo zata dinka musu ko kuma ita ta taho mata da su na irin kasarsu. Tamkar tafi kowa murna da aurenta da yayanta, amman tunda ta fahimci bata kaunar dan uwanta har aka zo aka yi wannan rikicin, har ta kai yau tayi
sanadiyyar kusan rasa ransa, amma ko a jikinta, bata daina nuna masa Kiyayya ba, ba ta ko jin kunyar mahaifinsu da ita take nunawa bata son nasu,Don haka ta sire mata a halin yanzu ba wacce ta tsana sai ita, kuma tayi alkawarin ba za ta taba barin wannan auren ya yiwu ba.
Tasan Yayanta mutum ne mai hakuri da sanyin rai, cutarsa zata dinga yi ta hanyar cuzguna masa ta dinga nuna masa tsantsar tsana, shi kuma ba zai dauki wani mataki ba zai kyaleta ne tayi mai isarta koda shi zai cutu,
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe