WAYE ANGON CHAPTER 30 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 30 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 


da ita.

Yayin da ita baccinta take hani’an bata san inda zata ce take ba, Karfe uku Nurse ta turo kofar ta shigo don duba patient ‘dinta, yanda tagansu ne abin ya bata mamaki, gefe kumá ya bata dariya, ta fita ta kirawo “yar uwarta ta ce “Zo ki ga wani abu marar lafiya ya warke suka yi dariya” dayar tace “Ikon Allah! Soyayya dadi.” Sukaja musu kofar suka fice suna dariya.

Nannauyan baccin da ya dauké ta bai saketa ba tsabarsai da sanyin asuba ya fara kadata, Sannan ta juya don ta jawo bargo. ta lulluda Kamar yanda ta sabayi da zaran taji sanyi a irin wannani lokacin Zata ja bargonta.

Jinta tayi an matseta ta duba da kyau, kawai ta ganta jikinsa kwance. Wata irin Kara ta saki tayo tsalle ta diro daga kan gadon tana maida numfashi.

Ya farka’ a firgice Shima, ganinta ya yi tsaye tana Binsa da kallo cikin tsananin mamaki, gefe kuma wani takaici da haushinsa ya lullubeta, ta ci gaba da kallonsa Tana harara, kana kallon tsantsar tsanarsa a idonta. Ya tashi zaune ya dubeta yace, “Lafiya? Meya faru?” Tayi, shiru tana harararsa din. Ya miqe tsaye ya tunkarota yana cewa,

“Mabaruka lafiya kuwa? Da sauri taja baya tana: cewa, “Kada ka kuskura ka matso ni, in ba haka ba wallahi sai na rotsa ma kai, mugu, dan iska azzalumi.” Daidai zubowar hawayen da bata san da Zuwansu ba tsabar Takaicin kasancewarta da shi. Ya tsaya cak yana kallonta, ya ce «Me nayi miki na muguntar? Me na kuskure miki? Ta kasa cewa komai sai dai hawayen da ke zirarowa

daga cikin gurbin idanuwanta. Ta dauke kanta daga gare shi ta dubi jikinta har kasa

-ta maida kanta saman gadon don son gano wani abu, bata fahimci komai ba ta dago tana sake kallonsa. Har yanzu idanuwanta da hawaye, ta ce “Ka fada min gaskiya me ka yi min?”

Sam bai fahimce ta ba, yace,Kamar ya?”Ta harzuka ainun ta fada cikin tsawa,idanunta suka yo waje.Ka fada min gaskiya me ya shiga tsakanina da kai a darannan?” Sai a sannan ya fahimce ta. Ya bita da kallo, ya koma ya yi zamansa yana cewa,Oho, tambayi kanki me yiwuwa, shaukin hakan ya mantar da ke. Fadin wannan maganar yasa hankalinta ya Kara tashi, ta harzuqa wasu hawayen suka zubo mata, ta nufo. shi ta cakumo shi tana cewa.Wallahi idan har na tabbatar ka min wani abu na cutarwa sai na kai kararka gurin Allah, mugu, dan iska, macuci wanda bai san darajar soyayya ba, sai ka fada min me ka min.”Ta ci gaba da jijjiga shi tana kuka.Ko motsi ya kasa yi bare ya bata amsa, illa dai kallonta da yake. Ita kuma ba ta fasa ba, har ta koma dukansa a kan kirjinsa hannu bibbiyu tana kuka. Cak ya rike hannunta yana kallonta da jajayen idanunsa, itama shi take kallo, suka ci gaba da kallon-kallo, kowa da ma’anar kallonsa ga dan’uwansa.Shi ya fara magana cikin sanyinsa da saukin kansa ya ce, “Menene haka Mabaruka? Me ke damunki? Ni ne Angonki fa, ni mijinki ne idan har wani abu ya shiga tsakanina da ke wanda ki ke zargi har za ki yi bakin ciki kiyi kuka hankalinki ya tashi har haka, ba fa fyade na miki ba, ni mijinki ne ina da hakki a kanki. Laifi ne don miji ya kwanta gado daya da matarsa?”

Ta harare shi ta ce, “Ni ba matarka ba ce wallahi, karka sake kirana da matarka, har abada ba ni da miji irinka haka kai ma kaje can ka nemi matarka, wacce tayi daidai” da kai amma ba Mabaruka ba.

Ya ce, “Ba zai yiwu ba, tunda har kina matsayin matata dole. ne na kira ki matata, amaryata don ni mijinki ne duniya ta shaida, ni ke da ke ke tawa ce, hakkina mallakata. Kuma dole ne duk sanda na bukace ki in same ki ba tare da kin tuhume ni don me ba, got it?”.

Ji take kamar ta shake shi don haushi, idanunta sun kasa barin nasa, kallon banza tsantsar tsanarsa take ji a ranta da kiyayya.

Ta tofar da yawu gefe ta ce, «Tir da na kasance matarka, Allah ya sauwake, wallahi kyamarka nake ba don kai kazami ba ne illa sai don yanda nake jin tsanarka a raina Ta kwace hannunta daga, jikin nasa ta. Kara cewa

“Kuma sai Allah ya saka min da ka kwanta kusa dani ba da son raina ba, sai don yaudararka da cin amana. Allah ya isa wallahi.” Hawaye suka zubo mata. Ya ce, “Ki daina wahalar da kanki, kina guje wa. auran da aka riga aka daura, Mabaruka ni fa mijinki ne ba yanda ki ka iya. Kiyi hakuri ki saki ranki ki barwa

Allah komai. Ni kuma nayi miki alkawari da kaina zan koya miki sona, zan kuma ririta ki tamkar kwai a hannuna, duk wani abu na jin dadin rayuwa zan ba ki shi ko da ni zan cutu.”Har ya Karashe maganar babu abin da take ji a ranta sai, tukuki, babu magana daya da ta burgeta, cikin maganganunsa sai ma Kara mata tsanarsa da suka yi. Ta durkushe a nan tana jajantawa kanta wannan alakakan, da gaske kenan ya riga ya santa a” ya mace! Da sauri ta mike ta shige toilet.

A iya bincikenta bata ga alamar hakan ba, amman . duk da haka ta kasa fitowa, taci gaba da, kukan tana watsa wa fuskarta ruwa.a Jinta shiru ne’ yasa ya dinga kwankwasa mata kofar

ta fito bata jin zata iya amsawa bare tayi abin da yake so.Tayi banza da shi, iya dukan kofar ya yi amman ta fi budewa Har gari ya waye tar bata fito ba, taci kukanta har ta gaji tayi zaune jagwam hannu biyu a fuska ta rafka tagumi.,Tunda safe su Momy suka zo. hade da breakfast, koda taji motsinsu bata yi alamar fitowar ba, zamanta tayi abinta.

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *