WAYE ANGON CHAPTER 4 BY MARYAM JAFAR KADUNA
daga cikinsu take yi ba. Haka nan dai cikin sanyin jiki ta
danne tare da kaiwa kunne tana sallama.
Daga can ya ce,
“Kina ina ne ba mun yi da ke yau
za ki dawo gida ba?” Ta yatsina fuska tace,
“Ni gaskiya na fasa ba abinda zan yi a gidan.
Ransa ya baci,
“Zan ci mutuncinki fa Mabaruka! Kin
maida ni abokin wasanki ko? Tun yaushe mu kai
maganar nan da ke? To ki maida hankali wallahi ki taho
yanzunnan ga Jama’a nan
sun fara taruwa ana
tambayarki, na fada miki. ” Daga haka ya datse layin.
Zuciyarta ta cunkushe tayi shiru ta rasa me zata yi.
Rafi’a ta ce, «Ya kuka yi da shi?”‘ Ta fada mata komai, Tace,
“Ai ba damuwa sai mu wuce tunda an kusa gamawa.
• Nina ma manta da yau ne wa’azin, duk damuwarki ta rikita ni.»
Sai da suka gama sannan suka fito. A kan hanyarsu
Ne a ka sake kiranta. Wayar na hannun Rafi’atun ta duba
taga Mama (Maman Mabarukan), don haka da sauri ta miko mata tana cewa “Karbi Mabaruka, Mama ce.
Harararta tayi ta Kara yin gaba, har wayar ta yanke ba
su dauka ba. Sai a karo na biyu ganin Mabarukar taqi
karba yasa ita ta dauka. Suka gaisa da Maman ta ce, “Ina
Mabarukanne?” ta ce,
«Gata nan wai taki karba ranta ya
baci.
“Maman ta ce, “Ki bata wayar.” Tace, “To.
Ta mikawa Mabarukan ta amsa tana zobara baki.
Daga can ta ce,
“Zan ci ubanki fa Mabaruka, wacce irin
kafaffiyar yarinya ce ke wai? Kina son ki bani kunya
ko? Jibi daurin aure amman ba kya gida, wacce tsiyar ki
ke yi a waje?”
Mabaruka ta ci gaba da turo bakin ba tare da ta ce
komai ba. Maman ta ci gaba da cewa, “Wallahi, kiyi
marmaza ki taho yanzunnan, tun kafin ranki ya baci.
Zan turo Imrana yazo ya dauke ki, kina gidan su Rafiar?”
Cikin gunguni ta ce,
“A’a muna saloon,
.” Ta ce, “Tò
zai kira ki ki fada masa inda kike.” Daga haka ta yanke
layin.
Haushi, takaici da bakin ciki suka tokare ta. Sakin
wayar tayi tayi gaba abinta cikin tsananin fushi. Rafi’ar ta tsugunna ta tattara wayar ba tare da ta ce komai ba,
sannan ta biyo bayanta. Tafiya kawai suke ba me
magana har suka iso.
A kofar gida suka gamu da Baban, ya fito da butoci
za suyi alwalar sallar Magriba tare da mutanansa.
Ya kirata taje tana bata rai, ya dubeta a tsanake ya ce,
“Menene naga ranki a bace?” Bata jin akwai amsar da
zataiya ba shi. Ya kara nanatawa. Ta ce “Ba komai, kaina
ne yake ciwo.
Ya kalleta tsaf! Ya fahimci ko menene, amman ya ce,
“Ciwon kai kuma a wannan lokacin bai kamata ya dame
ki ba. Ke da ke Kokarin zuwa gidan masoyinki?”
Ta kalle shi kallon bai san me yake ba. Shi a
tunaninsa har wani farin ciki zata yi? Da babu wata
harkalla a daura auren da shine zata yi farin ciki,
amman wannan auren da cikinsa yake da fitintinu.?
Ya katseta “To ki je ki sha magani. Tun dazu a ke jiranki har an gama taron amman akwai sauran Jama’a
cikin gida ki isa kwa gaisa.
.” Bai gama rufe bakinsa ba ta juya ta wuce don ta gaji da maganarsa.
Gidan ya fara daukar harama da ‘yan biki, ‘yan
kauyensu duk cikin mutanen babu dangin Mamanta ko
daya, daga nashi sai na Inna matar Babanta, su ke ta. hidimarsu.
Da shigarta ma su tsokanarta nayi ma su janta nayi,
babu wanda ta saurara suka shige dakinsu ita da Rafia.
Ta fadi zaune jagwab tare da dafe kai ta ce, “Na shiga
uku ni Mabaruka, da gaske dai ne?” Idanunta suka yi
rau-rau zata yi kuka. Kafin Rafiatu tayi magana wayarta
ta hau kuka ta duba, Imran ne. Ta kai kunne tare da cewa
“Hello!”
Daga can ya amsa suka gaisa yana tambayarta
“Mabaruka fa? «Ta ce, “Gata nan kusa.” Ya ce, “Ok! Ki
ce mata gani nan kan hanya ina zan sameta?” Ta ce,
‘Muna nan gidan Babanta.
Ya ce, “Ok, ga ni nan na kusa.” Ta ce,
“To.” Tare da
kashe wayoyinsu, ta dube ta ta ce, “Ga Imran nan kan
hanya ya kusa.”
Ta dube ta da rinannun idanunta ta ce, “‘Wai yazan yine Rafi’a? ina zan sa kaina?”
Tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, ta ci gaba
“Shi ya kira ni lallai in taho nan ita ma ta kira ni lallai in
tafi can, har ta turo shi ya tafi dani wai ya ake son nayi?
Sò suke su birkita min kwakwalwa don Allah??
‘Ta cè, “‘A’a wannan duk mai sauki ne, tunda mun zo
nan din ya gan ki sai ita ma muje can din tunda ita uwa
ce mace, me yiwuwa akwai wasu abubuwan da zata ba
ki daman abin da ya kamata kenan daidai wannan
lokacin kina tare da ita, don yi miki shiri mai kyau
wanda shi Baban ba zai yi ba, ko kin zauna a nan ba abin
da zai miki, to gwanda maki tafi can din kawai.
Ta jingina da bango tare da cewa,
“Oh! Ya Allah ka
kawo min dauki cikin gaggawa, kai kadai ka san me
kenan, kai kadai ka san abin da zai faru. Ya Allah ka
kawo min komai da sauki.”
Gidan a cunkushe yake da Jama’a, daman ga shi a
kuntace. Dakuna biyu ne ko kitchen babu.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE www.Dailynovels.com.ng