WAYE ANGON CHAPTER 6 BY MARYAM JAFAR KADUNA
‘saboda ciwo.
Tana kukan ta ce, “Don Allah Momy ki tausaya min
ki janye maganar auran nan, wallahi ina cikin tashin
hankali kar ki sa ni cikin masifa, ban taba son Imran ba
ko sau daya a rayuwata.
Shine mutum na farko da na fara tsana, wallahi ko
muryarsa ba na son ji bare in gan shi, har ta kai ni kuma
ga auranshi. Wallahi zan cutu Momy, don Allah ki janye
ki bar ni da Sulaiman.
Ranta ya baci, ta ci gaba da harararta, taja tsaki
“‘Maganar banza kenan, ni so ki ke in yi magana biyu?
Tun yaushe sadakinki ya zo hannu! Ko so kike girma da
mutuncin da Babansa yake ganina da shi ya zube?
Tun yaushe muke maganar nan? Na fada miki na
nanata miki, wallahi ba ki da miji sai Imran, shi na zaba
miki, ban ga aibunsa ba, nutsuwa, hankali da tarbiyya ga
ilimi, to me kuma a ke nema?
Ina da tabbacin wallahi babu gidan da za ki samu
kwanciyar hankali da nutsuwa sai gidansa. Imran yana
sonki, yana tausayinki, ya kuma damu da ke. To don me
za ki ce ke ba kya sonsa? Alhalin an halicci zuciya da son
mai kyautata mata!
Don haka ki sa shi a ranki, ki so shi ki dauka tuni shi
ne mijinki. Ko yau na fadì na mutu wallahi ban yarda ki
auri wani ba sai shi, shi nake so da shi na yaba
Mabaruka ta zauna rajab! Saman lafiyayyan gadon
mai lallausan zanin gado, ta ce “Ni kuma ba za ki duba
abin da nake so ba, zuciyata take so ba? Taki ki ke
dubawa?
Momy zuciyata zata yi daci, zan dawwama da kunci
karshe ciwo ya kama ni na mutu. Sulaiman shi kadai
nake so, duk abin da ki ka lissafo na Imran, Sulaiman
yana da shi har ya fi shi.
A gidansa ne zan fi samun kwanciyar hankali da jin
dadi, shine kadai zai ba ni farin ciki ba Imran ba.”
Ta kalle ta da kyau ta ce,
“To ni kuma ban amince ba,
idan har ni na haife ki ya zama dole ki bi abin da nake so
kiyi kuma.
.” Ta ce,
“To shi kuma wanda ya za6a min
Sulaiman waye shi gare ni in ke Mahaifiyatace?”
Kai tsaye ta ce,
“Ubanki mana. Hakan yasa ban
yarda da za6inshi ba nawa nake so.
Ta ce, “Shi mahaifina ne shi na saba mishi kenan ke
Nabi abin da kike so?”
“Kwarai kuwa, don ni na haife ki nayi renon cikinki,
nasha wuya wajen haihuwarki ko na mutu ko na rayu,
haka na haife ki naci gaba da renonki ko na ci ko ban ci
ba sai na ba ki kinci kin sha fa.
Duk bai gabansa, sai ya ci sau goma ke bai ba ki kin
ci sau biyu ba, amman ni bani ci ke ba ki ci ba asalima
nafi son ke kici akan ni naci. Nafi sonki a kanshi, yanda
yake sonki nafi damuwa da ke a kan shi.
Koda wasa ma ba za ki hada uwa da uba ba, Annabi
ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci uba sau daya,
don haka dole ni za ki wa biyayya kafin shi in har kina
neman albarka, kuma zabina ba aibu ba ne alkhairi ne
gare ki, ba make kadai ba har ga mahaifin naki.”
Ta dafe kai ta Kara fashewa da kuka har yanzu ta kasa. fahimtarta, shin ya zata bullo wa al’amarin nan?
Anti Karima ta shigo kanwar Momy ce ta bisu da
kallo, sannan ta ce “Har yanzu dai maganar nan ba ta
kare ba Mabaruka?”
Ta dago tana kallonta da jajayen idanunta, tà ce
“Yaushe za ta kare Anti, bayan ni kadai nake hango
tashin hankalin da za a jefa ni.”
Ta zauna tana cewa,
“‘Auran Imran dinne tashin
hankali? Ke ba ki gani kin san kuwa irin jin dadin da za
ki samu gidansa? Ko kayan da ya hado miki-ya isa ki
sauke makamanki uwa uba gidan da ya kera miki
saboda ke kadai kawai yana sonki yana kyautata miki,
kuyi aurenku ku fita Kasashe jin dadinku da hutu.
Amman duk wanna bakya hangowa kin
gwammace ki auri wancan Talakan Malamin
Makarantar wanda kafin albashinsa yazo ya cinye su da bashi?
To me yaci ya ba ki ya ba abokiyar zamanki? Ga uwarsa ga kanwarsa, to bare mu in muka zo me zamu
samu gidan bushe ke bushe? Duk ba ki duba wannan ko
Mabaruka?”
‘Ta kalleta kamar ta mare ta, ta ce “‘Wannan ni ba shi
ne gabana ba, ba shi nake so ba. Ni shi nake so shi kadai,
shine farin cikina da kwanciyar hankalina.
Arziki kuma wannan na Allah ne, zai iya azurta mu.
Shi Imran din da ku ke magana ba zai iya min abin da
Sulaiman din zai min ba, ba shi da abin da nake so daga
gare shi.
Gidansa zai zame min tamkar akurki, dukiyarsa bata
taba burge ni ba wallahi, don ba za ta bani farin cikin da
nake so ba.
Ta ce,Ke yarinya ce sakarya, za ki gane gaba ba ki
da hankali tukunna, wake kai kansa ga talauci? Kowa
yana neman tsari dashi,
Domin kuwa Annabi (S.A, W) ma yana neman tsari
da shi, kowa inda zai huta yake so. Son banza shirme akwai abin da ya kai kudi? Ai so shi ne kudi, in da kudi
komai lafiya daidai ne, kudin su ne za su bada farin ciki
HMMm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe