YAN ARABIC COMPLETE HAUSA NOVEL

YAN ARABIC COMPLETE HAUSA NOVEL 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cin cirundan d'alibai ne nake hanga a  can nesa dani wanda suka hau layi- layi amma yawansu baya bada damar a gane a layi suke,dik girma irin na filin dake bayan I.C .T na wannan makaranta d'aliban k'ok'arin cikeshi sukeyi, kasance war  d'alibai ne mabanbanta courses wasu hira suke wasu kuwa gajiya tasa ko hiranma basayi gasu dai tsaye suna  jiran layi yazo Kansu ko wanne hannunsa rik'e da credentials d'insa kana ganunsu dai kasan masu neman Admission ne.
Yawancin matan a zazzaune suke wasu a tsugunne .

Can gefan titi motar tai parking ya juyo ya kalleta da D'an mirmishi a kan fuskansa yace" To Nahnah Khadeejah ga skul d'inku kuma wad'an nan tarin jamaa'r da kike gani dikka masu neman Admission ne kamar ki don haka yanzu cikinsu zaki shiga saiki Tambayi ya'n Department d'inku kema kibi layi"

Dafe baki tai cike da tsoro tace "yanzu yaya dik wannan tarin muta nan kar b'ar Admission letter zasuyi to ta yaya zan samu karb'a ayau"?

Mir mishi ya k'ara yi yace" To ai dik ba course d'aya kuke ba kowa department d'insa daban don haka in kin je zaki ga kowa data windows d'in da zaki ga masu basu"

"Tom yaya saina dawo" ta bud'e murfin motar tana fita,
Kud'i ya d'auko 2k ya mik'o mata"ungo wannan ki rik'e a hannunki don neman wani kud'in ko in kin fara jin yunwa don zaku iya kai yamma"

Karb'a tai tana fad'in "Tom yaya na gode"

A hankali ta k'ara so wajan k'irjinta nata dukan uku uku don ita jama ar yawansu yana bata tsoro ,gefan dataga matan suna zaune ta k'arasa da sallama abakinta " السلام عليكم" wasu daga cikinsu sun amsa mata yayin da wasu suke bidirin gabansu wasu kuma binta sukai da kallo irin kallon nan da mata kewa y'ar uwarsu mace musamman idan tai babban wanka,😜

Gyaran murya tai cikin sanyin miryanta tace"Don Allah ina Tambaya ne"
"OK Allah yasa mun sani"
"Don Allah *YA'N* *ARABIC* nake nema"
"To gaskiya sai dai ki matsa can gaba kad'an kiyi Tambaya nan dik babu su"
Gaba ta k'ara kad'an ta k'ara Tambaya nan wata dake zaune agefe tace "gamu nan "
K'ara sawa tai kusa da ita ta zauna tare da mik'a mata hannu sukai musabaha tace" nima *YA'R* *ARABIC*ce zan amshi Admission letter ne"
Kallonta tai sosai tace"Ok kice y'ar uwace kinga duk way'an nan ma department d'inmu d'aya" ta fad'a tana nuna sauran y'an Matan dake gefe,dik mik'a musu hannu tai sukai musabaha"
Nan suka ci gaba da zama suna jiran a fara raba musu letter n.


Khadeeja Alk'adi yusuf haifaffiyar garin sakkoto ce y'a ta goma sha bakwai acikin gidansu kuma ita ce autarsu,
Mahaifinsu Alk'adi Yusuf tsohon Alkali ne a babbar kotun Shari ar musulunci ta garin sakkoto Dattijo ne me cikar kamala da addini yana da mata biyu da ya'ya' goma sha bakwai maza goma sha biyu mata biyar,
Babban D'ansa Namiji ne Yaya babba kenan sai na biyunma na miji ne yaya Sani sai ta uku mace Aunty sai ta hudun Aunty Amina ta biyar ma mace ce Aunty jamila bayan Aunty jamila saida aka haifi maza hud'u sannan aka k'ara haifar mace agidan wato juwairiyya daga nan aka k'ara maza shida sannan aka haifi auta Wato Nahnah khadeejah, y'ar gata ce sosai agidansu don dikkan yayyanta mata an musu aure mazanma duk sunyi aure mutum

DOWNLOAD HERE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *