YANAYIN RAYUWA CHAPTER 8

😔YANAYIN RAYUWA😢😱🌷🌷🌸🌸🌸💐. CHAPTER 8 

 By halimatusadiya saleh Tashi dad yayi yanufi dakinsa,yanata saka da warwara, yarasa meke masa dadi yakasa zaune se safa da marwa yake tayi. Yasan inda yayanshi yana da rai wayen nan abun duk bazasu faruba,kuma gashi yadaura ma usman dauyin da banashi ba. Mom tadago ta bisu da kallo umar dayayi tagumi,zali kuma tana manne da yayanta tana kuka,shiko Usman yadade da sunduma cikin duniyan tunani. Gyran murya tayi,yasa duk hankalin su ya karkata xuwa gun datake, tace ” Usman zaku iyya tafiya ga umar ze taimaka ma awaje dadama, niko kubar ni da zalin.” Basuyi mgn ba yatashi jiki a sanyaye yadaga zali ya kuntar da itta akan carpet na yafita, Umar yabi bayanshi ,dakin su suka nufa. Bawanda yatan kama dan uwansa, toilet usman yashiga ya dauro alwala yafito, Umar na ganin shi shima yaje yayi alwala suka yi nafilla raka’a biyu suka sallame. Sunda de suna mika kukan su ga mahaliccin su kafun umar yatashi yahau bed ya kwanta yanata juyi yarasa meke masa dadi,shi kuma Usman agun yakwan ta yana. Haka rayuwa tayi ta tafi yau kwana biyu da faruwan hakan,inda Usman har yarame yarasa meke masa dadi tunanin safe daban na rana daban. Mom tashiga kitchen dauko plate,tana fitowa suka cikaru da Usman, sunkuyar da kanshi kasa, yace ” Mom bari indan je cikin gari.” ” To Allah ya kiyaye.” Tafada tana binshi da kallo se yanzu taga Raman Usman dun da Umar yagaya mata bata aza yakai hakaba,yana faman barin wurin se ga khalil reke da hola a hannu yana faman gerawa yace ” Brother zan bika.” Kai kawai yadaga mai alaman ok, fita sukayi,maryam dake falo tana kallo ta musu adawo lfy. Daki mom tashiga ta tarar da zali nafaman bude laptop na khalil amma ta kasa,mosen kofa taji yasa ta dago da kanta tace ” Yauwa mom bude min system nan nakasa wlh,yachan za Password.” Murmushi tamata tace ” To imban da abunki,ni inna zansani.” Turo baki tayi ta ajiye laptop din agefe,tana gunguni itta kadai, jijiga kai mom tayi tace aranta,yayan ki nacikin damowa dunke kikina nan kina faman damowa da laptop. Zama mom tayi abakin bed nata tacema zali jekikira min ya Umar,ba musu tatashi tafita dakinsu taje tasame shi yana faman shiri ko inna zaje ohho, salle tayi ta hau kan bad din dakin se lkc ne ma yasan mutum a dakin dun baima ji shigo wanta ba. Ido takura mishi shima ya kura mata, kawar da kanta tayi tace ” Mom fa tana kira.” Yace ” Data aikeki se tace karkiyi sallama koh?” Sauka tayi zata fita tajoya tace ” Intafi ne ko injira ka?” Baice mata kumai ba yabita suka tafi suna issa mom tace ” Zali kije gun aunty hapsat a kitchen,gashi kitafi da plate nan.” Tana fita, mom ta kalli Umar dayake jira tamasa mgn,tace ” Baban yaya, alfarma nake nema agunka,dun Allah kayi biyyaya ga duk abunda zangaya ma badun kumai ba dun muhado muceci marainiyar Allah nan.” Kallon ta yake yana jira yaji wani irrin alfarma take nema. Tadada dace wa ” Kasan me daddyn ku yace ma Usman kuma kasan Usman baze iyyaba yade amsa ne kawai dun yakare kanwar sa, Dan Allah Umar kayarda kace ma daddyn ku zaka auri zaliha, dun mucece ta kasan wacece zuwaira.” Wani nannauyan aziyan zuciya yasauke,dun shi bai taba sammanin ze iyya auren zali ba,kuma alfarma mom tane ma agare shi,yanzu me zece mata yazeyi itta zali intace batason shifa. Haka yayi ta sake sake a zuciyan shi, bamai bashi amsa. Mom ce tace ” Yana ji kayi shiru?” 😔YANAYIN RAYUWA😢😱🌸💞💐💐🌷🌷. By halimatusadiya Saleh. Kallon shi mom tayi tace ” Yanaji kayi shiru.” Dagowa yayi da rinannun idanun sa da suka chanza kalla zuwa red, yace ” Mommm, nayarda Allah yasa shiyafi alkhairi.” Jiyayi kansa yawani sara kaman da gatari ake shirin raba masa kansa,hawayen da basu samo daman fitowa ba dazu,sun gangaro kan kumaton shi, mom ce ta kalle shi cike da tausayawa danta tace ” Babban yaya, kayi hkr dabunda nasaka nasan zakaji zafi,dole ne mucece su dun hakkin mune. ” Tashi tayi tazauna kusa dashi takama kanshi,kuntar da kanshi yayi akan cinyan ta yana kuka kaman karamin yaro,shi babban damuwan sa kar zali tagirma tace batason shi, yazeyi kenan. 💕💕💕💕💕💕💕 Yau yakama laraba da yamma,khalil da maryam ne a setting room suna kallon film,zali da aunty hapsat suna kitchen suna girkin dare,zali nataya ta da wasu abubuwa, ya Usman da ya Umar suna waje suna hira da maigadi. Door bell ne yayi ringing, khalil ne yatashi yaje yabude,babane da su ya Umar, shiga suka khalil ya ma baba sannu da zuwa ya amsa cikin fara’a,maryam tagaishe shi,tawuce dakin mom ta gayamata baba yazo,kafun taje takawu masa ruwa da drink’s. Dakin dad mom tawuce bayan fitan maryam tasanar mai mijin zuwaira yazo, fita sukayi atare, a falo suka tarar dashi shida su ya Umar suna hira. ” A’a babban bako mukayine,sannu dazu baraba susai.” Guri suka samu suka zauna akan sufa,gaisa wasukayi cikin fara’a,inda dad yake tambayan ya lbr yaruwar’sa. Baba yace ” tana lfy,daman nazone batun mgn tafiya da zali naga har ana neman sati biyu da holidayn su bata dawu ba. ” Gyran murya dad yayi kafun yace ” Hakane, naso inzo amma aikine yamin yawa shiyasa bansamu nazu ba. Kuma batun kuma wan mamata gaskiya dan uwan yaki yace shi baze bar kanwansa takuma hannun zuwaira ba,gaskiya abun wahalan datasha abaya ma ya ishe ta haka, shine nikuma nace inhar bayason zali takuma to yane ma mata mijin daze aure ta dun nayi alkawari aure ne kawai ze rabata da gidan ka,yanzu haka yau kwana hudu da mgn amma bece kumai ba,dun sati daya nabashi.” Jinjina kai baba yayi dajin abunda dad yace,kafun yace ” Yanxu yayah yaron waze samo ya auri zali,kuma ma itta zalin nawa take dazaa mata aure yanzu.” Dad amsa amsa mai yace ” ni nariga nayanke hukunci kuma koda yanzu ne yasamo mijin zan aurawa zali,imba haka ba inhar yacika sati bai kawo ba to zata kuma gidan ka.” Wani irin fadowan gaba Usman yaji atake yaji kansa nasarawa , yarasa meke masa dadi aduniya yanaji yana gani zaa tafi masa da yar’uwa kun azzaluman matan nan,taje takashe mai itta inna baze yoba gaskiya. Yana cikin tunani yaji dad yace ” Usman ya mgn mu kasamunne.” Dasauri yadago da rinannun idanon shi ya kalli dad ko mgn yakasa ya kumar da kanshi kasa,da ace su ummi na nan da duk hakan be faru ba. ” Magana nake ma.” Dad yafada asawace,bai dago da kanshi ba balle ya amsa,wani kuka ne yako muce masa mai karfin gaske yace ” Da’a ce baban mu nanan da hakan be faru ba dun baya nan se ku muzguna ma mahaifiyar shi wanda duk duniya baida kaman ta kuma yafi so , amma yau gashi ittace take shan wahala a hannun kanwar sa..” Kuka yaci karfin sa,yana mgn yayi dede da fitowan zali daga kitchen itta aunty hapsat, ai tana ganin yayan ta na kuka ta gudu taje ta rungume shi,suka fara kuka mai rasa jikin mai sauraro,duk jikin su yayi sanyi dajin mgn da Usman yayi. Umar ne yace ” Daddy ni zan auri zali kuma ayau nan,na gummace inrasa farin cikina insaso farin ciki.” Maganan ne yadushi kunnen Usman da zali basu san lkc da suka rabu da juna ba,mamaki ne yacika Usman,itta ko zali tunani take wai itta zaamata aure kuma da ya Umar how come’s. Dasauri dad ya kalli Usman yace ” Ba mgn wasa muke ba.” Tashi Umar yayi yanufi dakin su ya dauko wani shadda da kudin sa ze kai kimanin dubu hamsin da takwaran shine yasa ya mai shida Usman, kafun yarasu yaki dinkawa ne yace se ran auren shi. Wasu zafafan hawaye ne suka sauko mai,ya tona da randa takwaran sa yabashi gashi yau dashi zeyi sadakin matan da ze aura wato zali,fita yayi yasame su kaman yanea yabar su kuwa na binsa da ido banda mom dun itta tashirya abun. Guri yasamu yazauna kusa da dad, yace ” Gashi wannan shine sadakin zali.” Da mamaki yan falon suke kallon shi. By halimatusadiya saleh✨

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *