YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 6 BY ANUP JANYAU (_SPY_🎥)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 6 BY ANUP JANYAU

(_SPY_🎥)

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani irin taku Kuzeem keyi tamkar wata zakanya, cike da tsagwaron jarumta wacce batada algus. Yayinda Meerah ke gefenta sai Security’s da ke bayansu, har suka iso bak’in wani k’aton building, wanda a nan ne office d’in L.G Aliyu Iko yake.  Cikin sauri Security’s d’in wurin suka bud’e mata k’ofa tare da sadda kawunansu a k’asa saboda jin nauyin rashin bata girman da suka saba yi. D’an guntun murmushi Kuzeem tayi sannan ta shige ciki, ta bar su Meerah tsaye a wurin, don basuda izinin shiga ciki. Daidai lokacin wani Security ya iso wurin tare da shaida musu ana son ganinsu ga baki d’aya, hakan yasa suka bar wurin su dukansu.

Ba shiri Major Khalil yayi saurin dakatar da dariyar da yake yi, yana mai sake tariyo ma k’wak’walwarsa yanayin kallon da Kuzeem tayi masa kafin ta bar office d’in. Hannayensa biyu ya hard’e a k’irji, tare da jinjina kai yace;

“Tabbas akwai tarin ma’anoni a cikin kallon da tayi min, tou me hakan ke nufi?. Menene dalilin da yasa aka koresu a hukumar nan?, wanne irin laifi ne suka aikata?, kuma meyasa ba’a zauna da ni a cikin meeting d’in da akayi ba?, wanda k’a’ida ne duk sanda za’a zauna meeting irin haka da ni ake zama, amma sai gashi wannan karon ba’a neme ni ba. Ba ko shakka akwai lauje cikin nad’i, don haka ya zama dole in binciko ainahin bakin zaren”.

Yana gama fad’in haka ya bar office d’in da sauri kamar zai tashi sama, yana fitowa harabar hukumar ya hango Security’s jere cikin layukka sun k’ame wuri d’aya, hannayensu a goshinsu alamar Salute, yayinda B.G Atiku Tanko ke tsaye a gabansu fuskar nan tashi a turnuk’e babu alamar rahma, tamkar bai tab’a dariya ba.

Tsaye yayi tare da rik’e k’ugu yana kallon yanda Security’s d’in suka daza layukka, sai kuma ya d’auke kansa ya mayar gefe kana ya sake maida dubonsa a garesu, da wani irin sauri ya sake kallon gefe, karaf idanuwansa suka sauka kan su Kuzeem da ke nufosa ita da Bilal.  Kallonsu kawai yake yi yana son nazartar yanayin da suke ciki amma ya kasa tantance ainahin yanayinsu, har suka iso ta wurin da yake tare da wuce sa, da kallo ya bi bayansu yana k’iyasta abubuwa da dama a ransa, yayinda su ko kallon banza bai ishesu ba.  Kai tsaye wurin Security’s d’in suka nufa, ko wannensu fuskarsa ba yabo ba fallasa, daidai lokacin mutane hud’un da zasuyi aiki tare suka iso wurin suma, hakan yasa suka jera a tare, kallo d’aya zakayi musu kasan an had’a zaratan jarumai masu jini a jika, wad’anda ke tsoratar da tsoro da kansa, k’i gudu sa gudu.

Wannan jerawar da sukayi ba k’aramin birge sauran jami’an sukayi ba, wad’anda ko wannensu tun d’azun sai tambayar kansa yake laifin me wad’annan manyan jigunan hukumar sukayi aka koresu?, saidai sun kasa samun amsar tambayar, yayinda wasu sukayi farin ciki da hakan, wasu kuma suka shiga jimamin lamarin. Suna isowa wurin suka tsaya bayan B.G Atiku Tanko, hakan yasa Security’s d’in suka shiga sauke hannayensu k’asa a tare, cikin wani irin salo mai birgewa, saidai kallo d’aya zaka yima yanayin fuskokin wasu daga cikinsu kasan sam basu tare da walwalarsu.  

Juyowa B.G Atiku Tanko yayi wurin su Kuzeem yana yimusu wani irin kallo wanda suka dad’e da fahimtar ma’anarsa, sannan ya maida dubonsa ga Security’s d’in da ke jere a gabansa, cikin wata irin murya mai amo da sauti yace;

“Jami’ai!!!”.

“Yallab’ai!!!”.

Muryarsu ta k’arade wurin.

“A juya sashen dama”.

B.G  Atiku Tanko ya sake fad’a musu da k’arfi cike da bada umurni.  Cikin sauri suka buga k’afafuwansu na hagu a k’asa, tare da yimasa Salute sannan suka juya b’angaren dama. Idan kaga yanda sukayi abun sai yayi matuk’ar birgeka. Sake tamke fuska yayi sannan ya juyo ya kalli su Kuzeem ba tare da ya furta komai ba yayi musu alama da hannu a kan su tafi.  A tare sukayi mishi murmushi sannan suka juya tare da barin wurin suka nufi inda sukayi perking motocinsu. Babu wanda ya sake furta komai daga cikinsu kowa ya shiga motarshi, aka bud’e musu get suka bar wurin.

 

Wani irin iska Major Khalil ya furzar daga bakinsa don ga baki d’aya kansa ya k’ulle ya kasa hasaso komai, ya kasa gano bakin zaren, cikin sauri ya nufi hanyar zuwa upstairs, k’ofar na bud’ewa ya shiga, elavotor ya shiga tare da danna 3rd floor, yana tsayawa ya fito ya nufi bakin wata k’ofa da aka rubutama *DGN(Director General) Colonel Mansur Iliyas Sani*.  Hankali tashe ya murd’a handle d’in k’ofar, ya fad’o cikin tamfatsetsen office d’in mai girman gaske da tsaruwa.

Saurin d’agowa wani babban mutum dake zaune cikin office yana danna sytem d’in gabansa yayi tare da kallonsa, sannan yace;

“Taya akayi ka san na dawo?”.

Da sauri Major Khalil ya iso wurinshi tare da jan kujera ya zauna, sannan yace;

“Wallahi Uncle  bansan ka dawo ba kawai hasashen zuciyata ne”.

Kai ya gyad’a yace;

“Me ke tafe da kai?”.

“Wata tambaya nake da ita wacce na san kai kad’ai ne zaka iya bani amsarta”.

Hannu Colonel Mansur Iliyas ya kai ya cire glass d’in idonshi, sannan ya rufe sytem d’in gabanshi yace;

“Ina jinka”.

“Ehm.. dama ina son tambayar laifin me su Kuzeem Yusuf Garba sukayi aka koresu?”.

Major Khalil ya fad’a muryarsa na gargada.  Wani kallo Colenel Mansur Iliyas yayi masa sannan ya d’auki glass d’insa ya kafa a ido, kana yace;

“Ban sani ba”.

Sadda kai k’asa Major Khalil yayi don dama yasan za’a rina, kawai ya yanki tikiti ne amma yasan ba lallai ya samu amsar tambayarsa ba.  Hanyar waje Colonel Mansur Iliyas ya nuna masa yace;

“Tashi ka fita”.

Jiki sanyaye ya mik’e ya nufi hanyar fita, har ya kai bakin k’ofa ya ji Colonel Mansur na fad’in,

“Khalil ka daina shiga abinda bai shafeka ba, saboda hakan ci baya ne”.

Cike da jin haushi Major Khalil ya ida ficewa daga office d’in yana k’unk’unai, tare da jin haushin Uncle d’in nashi. Ya rasa meyasa yake masa haka, sam baya basa goyon baya kuma baya ganin farinsa akan duk wani abu da zaiyi, tamkar ba Yayan Mahaifiyarsa ba. Ya sani sarai yafi kowa sanin dalilin korar su kuzeem saboda shine Director General na *DSS* dake k’asar SARBIK ga baki d’aya.

Fuska d’auke da murmushi Kuzeem ta fito daga motarta ta nufi cikin gidan, da murna su Raudah suka yimata sannu da dawowa, ta amsa musu cike da farin ciki, sannan ta gayar da Ammah tare da zama gefenta, bayan Ammah ta amsa gaisuwar ne tace;

“Kuzeem wannan fara’ar duk ta miye?”.

‘Yar dariya Kuzeem tayi wacce ta k’ara bayyanar da tsantsar kyaunta, sannan tace;

“Abba na nan?”.

Cikin mamaki Ammah ke kallonta sannan tace;

“Yana nan, ya dawo tun d’azun kansa ke ciwo”.

Wata irin mik’ewa Kuzeem tayi tace;

“Subhanallah, an kira family dr?”

“Cewa yayi baya buk’atarsa”.

Da sauri Kuzeem ta bar wurin hankali tashe, hakan yasa Ammah ta bi bayanta da kallo har ta fice daga d’akin. Sai kuma ta mik’e tace;

“Raudah ku tashi muje part d’in Abban ku”.

Kuzeem na shigowa palorn Abba, ta hangosa kishingid’e kan rug ya d’an d’ora kansa a kan wani had’ad’d’en titimi, cikin sauri ta iso wurinsa tare da durk’usawa a gabansa tace;

“Abba”.

A hankali Abba ya bud’e lumsassun idanuwansa, yana ganinta yayi saurin tashi zaune tare da had’e rai yace;

“Me kika zo yi wurina?, ko wata sabuwar rashin kunyar ce kika zo kiyimin kuma?”.

Saurin girgiza kai tayi tare da rik’o hannunsa, da sauri Abba ya fisge hannunsa daga rik’on da tayi masa sannan ya nuna mata hanyar fita yace;

“Tashi ki b’ace min da gani Fatima, tun kafin inyi mummunan sab’a miki”.

Wasu yawu masu d’aci Kuzeem ta had’iye da k’arfi, sannan tace;

“Ka gafarce ni Abba, na san ban kyauta ba, amma dan Allah ka yafemin ko zan samu rahmar ubangiji”.

Shiru Abba yayi tare da mayar da kansa gefe alamun baima sauraronta, ganin hakan yasa Kuzeem ta koma gefen da yake kallo tace;

“Dan Allah Abba ka daina fushi da ni, kayi hak’uri”.

Mik’ewa Abba yayi, a fusace yace;

“Kafin in bud’e idanuwana kiyi gaugawar b’ace min da gani”.

“Babu inda zataje saika yafe mata”.

Ammah da suka iso cikin palorn yanzu, ta fad’a. Ko kallonta Abba baiyi ba ya nufi hanyar zuwa bedroom d’insa, da sauri Kuzeem ta mik’e tabi bayanshi, tana isowa inda yake ta rungumeshi ta baya tare da fashewa da kuka, hakan yasa Abba ya tsaya cak, ba k’aramin sukar zuciyarsa kukan nata keyi ba, amma baya jin zai iya kulata.

“Abba na amince zan auri Mr Salame kamar yanda kake buk’ata, in har hakan zaisa ka yafemin kuma ka kasance cikin farin ciki na har abada!”.

_*Masoyana ga fa dama ta samu wacce zaku nunamin zallar k’aunar da kukemin a zahiri indai batada algus😅 ga link d’in youtube channel d’ita nan, #Anup Janyau Tv. Don girman Allah kuje kuyimin Subscribe ku suburbud’amin like, tare da danna k’araurawar sanarwa, domin sanar daku a duk lokacin da na d’ora shirye-shiryena, nagode #One luv.*_❤️

Saurin kallon Kuzeem Ammah tayi fuskarta d’auke da mamakin jin furucinta. Raudah da Deedee kuwa juyawa sukayi suka fice daga d’akin.

“Fatima dagaske kike zaki auri Mu’az Salame?, kodai kin fad’i hakan ne don ki rainamin hankali?”.

Abba ya tambayeta cike da rashin yarda da abinda ta fad’a don yasan halin Kuzeem kaifi d’aya ce, saidai kuma lokaci d’aya yaji tantamar da yake a kanta ta fara gushewa, saboda wani irin farin ciki da ya lullub’e zuciyarsa. 

“Over my death body”

Kuzeem tayi saurin fad’in haka a ranta, amma a zahiri cewa tayi.

 

“Haba Abba! meyasa bazaka yarda da ‘yar lelenka ba?, tou bari in sake maimaita maka don ka yarda da kyau, na amince zan auri Mr Salame domin ganin farin cikin ka”.

Tana gama fad’in haka ta saki wani guntun murmushi mai tarin ma’anoni, sannan ta bar jikin Abba. Cikin sauri Abba ya juyo ya kalleta, fuskarsa d’auke da wani irin annurin farin ciki, wanda yasa Kuzeem murna a ranta, don ta san kalamanta sun riga sunyi tasiri a zuciyarsa, sannan kuma ta kawar da fushin da yake da ita.

“Alhamdulillah!. Hak’ik’a Allah kaine abin godiya. Yar lelenah Allah yayi miki albarka ya faranta miki rai kamar yanda kika faranta min rai, ina matuk’ar alfahri da ke”.

Abba ya fad’ama Kuzeem cikin wani yanayi na farin ciki wanda bai misiltuwa. Kyakkyawan murmushi Kuzeem tayi mishi, a ranta tana mamakin hali irin na mahaifinta, wanda ta dad’e da cin alwashin saita rabashi da wannan halin na son abin  duniya.

“Wato kin amince zaki auri Mu’az Salame kou?,  saboda cikar wani dogon buri na Abbanki,  Allah ya kyauta”.

Inji Ammah tana hararar Abba. Wani murmushi Abba yayi, don sam yanzu ba lokacin b’acin rai ba ne a gareshi.

“Hafsa kenan!, ban san sai yaushe zaki waye ba?, ki gane me duniya take ciki”.

“Abba ya kan naka?”.

Kuzeem tayi saurin tambayarshi don son kawar da wancen zancen, maido da dubonsa yayi a gareta yace;

“Kai haba, ai tuni ciwon kan ya wartsake dama na rashin bacci ne”.

“Abba rashin bacci kuma?, me ke hanaka baccin?”.

Wani murmushi Abba ya sake yi, tare da janyo hannunta suka zauna kan kujera.  Hakan yasa itama Ammah ta zauna tana kallonsu cike da takaici.

“‘Yar lelenah duk yanda zanyi miki bayanin kalar damuwar da na shiga akan k’in amincewa da auren Mu’az Salame da kikayi, wallahi ba zaki tab’a ganewa ba, amma dai yanzu komai ya wuce a bar tuna baya. Meya dawo dake gida da wuri haka?”.

Inji Abba da har lokacin murmushi ke bayyane a fuskarsa. Cikin tausasa murya Kuzeem tace;

“Abba na dawo ne saboda ina so muyi wata magana da kai, saidai bansan ko zaka amince ba, duk da dai amincewar ta zama dole”.

Ba k’aramin fad’uwa gaban Abba yayi ba jin abinda ta fad’a, amma haka yayi k’arfin halin fad’in,

“Tou ina jinki”.

D’an lumshe idanuwanta tayi, tare da bud’esu a hankali ta sauke su akan Ammah da ke yimata wani kallo, sannan ta maido dubonta ga Abba tace;

“Abba amincewa ta da maganar auren Mr Salame ba wai yana nufin za’ayi auren nan da wata d’aya kamar yanda yake buk’ata ba”.

“What!?”.

Abba ya fad’a da k’arfi yana mik’ewa tsaye cikin wani irin sabon tashin hankali da ya ziyarceshi, sannan ya nunata da yatsa yace;

“Karki rainamin hankali Fatima!, am i your mate?, da zaki zauna kina bani umurni?.  Sai yanzu ma nake mamakin kaina da nayi saurin amincewa da ke, Fatima na san halinki sarai kamar yinwar cikina, tun kina k’aramarki idan kika ce baza kiyi abu ba, tou ko me za’ayi babu wanda zaisa kiyi abun nan, balle yanzu da kika girma. Kawai dai kina son ki rainamin wayau ne, da farko kince bazaki tab’a auren Mu’az Salame ba, yanzu kuma kin dawo kince kin amince, tabbas na san akwai shirin da kike yi”.

Ya k’arashe maganar a zafafe tare da mayar da hannuwansa duka biyu a baya yana kafeta da idanuwansa. Saurin durk’usawa a gabansa Kuzeem tayi tace;

“Ka yarda da ni Abba, babu wani shirin da nakeyi, wallahi a hukumar mu ne aka turani wurin wani aikin sirri wanda zai d’aukeni tsawon wani lokaci, wannan dalilin ne ya sanya nake son a janye maganar auren a yanzu, saboda aikin baze yiwu ba idan inada aure, kuma nasan kaima hakan shine kwanciyar hankalinka”.

Sai a lokacin kaso 89% daga cikin 100% na hankalin Abba da ya d’ugunzuma ya d’an kwanta. Komawa yayi kan kujera ya zauna sannan yace;

“Ina buk’atar k’arin bayani”.

Kuzeem bata tashi a wurin ba, ta fara korama Abba bayani tun daga farko har zuwa k’arshe. Rai a d’an b’ace Abba yace;

“Amma su wad’anne irin marasa hankali da tinani ne?, da zasu tura mace irin wannnan aiki mai matuk’ar hatsarin gaske, kuma wai har wata jaha. Wannan ai zancen banza ne, to bari kiji sam baze yiwuba, ba zaki je ba…”.

“Abba idan har dagaske kana sona, kuma kana son ganin farin cikina kamar yanda kake fad’a, tou don Allah ka barni in aiwatar da wannan aiki, saboda a halin yanzu babu abinda ke cikin raina, na kuma sashi a gaba sama da wannan aikin,  ina so ka sani duk wanda ya shiga aikin hukumar tsaro, mace ko namiji matsayinsu d’aya ne, babu wani bambanci, kuma na riga nayi alk’awalin zan aiwatar da wannan aiki ba gudu ba ja da baya”.

D’an jinjina kai Abba yayi, don ya tabbatar da gaske take, idan har yace zai dakatar da ita daga wannan aikin, to kuwa rayukane zasu b’aci, k’wanda ya samu ya bita a hankali har ta auri Mu’az Salame.

“Tou shikenan  ‘yar lelenah, na amince Allah taimaka kuma ina miki fatan nasara a cikin wannan gagarumin aiki da zakiyi”.

Cike da tsantsar farin ciki Kuzeem ta rungume shi tace;

“Nagode Abba,  Allah ya barmin kai”.

Mik’ewa Ammah tayi ta fice daga d’akin, tana nazarin kalaman Kuzeem a ranta.  Abba da Kuzeem kam saida suka sake tattaunawa sannan Kuzeem ta bar part d’in, tana sakin wani murmushi.  Yayinda Abba ya d’au wayarsa ya dannawa Mu’az Salame kira domin bashi wani babban uzurin da ya shirya.

Ammah na zaune a palornta da su Deedee sunyi shiru suna juya lamarin a ransu, Kuzeem ta shigo, saurin mik’ewa Ammah tayi tana yimata wani kallo, sannan tace;

“Kin bani mamaki, kuma kin bani kunya”.

“Ki kwantar da hankalinki Ammah, abinda kike tinani ba haka abun yake ba”.

Kuzeem ta fad’a mata a hankali, sannan ta maida dubonta wurin su Raudah tace;

“Sisters ku d’an bamu wuri zamuyi magana”.

Mik’ewa Raudah da Deedee sukayi tare da barin palorn.  Sai a lokacin Amma ta koma kan kujera ta zauna tare da sakin wata nannauyar ajiyar zuciya. hakan yasa Kuzeem ta zauna gefenta, tare da rik’o hannuwanta sannan ta fara yimata bayanin komai.

Wani murmushi Ammah tayi bayan ta gama sauraren Kuzeem, sannan tace;

“Sai yanzu hankalina ya kwanta”.

Kwanciya Kuzeem tayi a kan kujerar tare da yin pillow da lap d’in Ammah ta lumshe idanuwanta ba tare da tace komai ba.

Around 5:45pm Meerah ta iso gidan su Kuzeem hankali tashe don sai a lokacin suka tashi aiki, babu tambayar da batayima Kuzeem ba akan laifin me sukayi?, Kuzeem tace mata batada masaniya kawai dai sunga an dakatar dasu ne daga aiki, amma basu san laifin da sukayi ba, kuma ba’a fad’a musu ba. 

“Wallahi wannan abun wata mak’ark’ashiya ce aka k’ulla”.

Inji Meerah da ke kuka, zuciyarta har wani zafi take. D’an cije lips Kuzeem tayi cike da tausayin Meerah ganin yanda take kuka a banza, da tanada damar sanar da ita gaskiyar lamarin da tayi hakan, saboda yanda ta sanya kanta a damuwa duk a sanadinta, hakan yasa take jinta tamkar ‘yar uwarta.

“Ki daina kuka Meerah, komai daren dad’ewa dole na san gaskiya zatayi halinta. Ina baki shawara a koda yaushe ki zamanto mai jajircewa tare da rik’o da gaskiya a wurin aikinki duk tsanani duk wahala”.

Kuzeem ta fad’awa Meerah tana k’ak’aro guntun murmushi, girgiza mata kai kawai Meerah tayi, don tana cikin damuwa sosai, ba k’aramin shak’uwa tayi da Kuzeem ba, sai k’iyastawa take a ranta yanda zata cigaba da aiki a hukumar ba tare da Kuzeem ba. Dak’yar dai Kuzeem ta samu ta rarrasheta, sai daga bisani Kuzeem ta sanar da ita zatayi tafiya, Meerah tayi mata addu’ar sauka lafiya. 

*3 days later*

Yau Kuzeem zata bar F.C.T FUNADE zuwa jahar RADDAL.  Ba k’aramar damuwa ahalin nata suke ciki ba, don ko kad’an basu son tayi nesa da su, saidai ba yanda suka iya, hakan yasa suke ta yimata addu’oin fatan nasara tare da kariyar ubangiji.

Cikin sanyin jiki Kuzeem ta fito daga d’akinta, don itama ba k’arya ta san zatayi kewar ahalin nata. Sanye take da wata tsadaddar Abaya peach, wacce tayi matuk’ar amsar jikinta, tayi rolling veil d’in Abayar a kanta, sai wayarta dake hannunta da wata had’ad’d’an hand bag peach color, yayinda Raudah ke biye da ita a bayanta hannunta d’auke da laptop bag d’inta, don tuni aka kaimata trolleynta a boot. 

Fad’awa jikin Ammah da ke tsaye a main palor Kuzeem tayi tare da fad’in,

“Zanyi kewarki sosai Ammah”.

Murmushin k’arfin hali Ammah tayi tare da rungumeta a jikinta, nan take taji k’walla sun taru a idanuwanta, cike da k’arfin hali ta iya fad’in,

“Nima haka Kuzeem. Ina rok’on Allah ya baki nasara a cikin wannan aiki da kika sanya a gaba, ya kareki a duk inda kike tare da sauran abokanan aikinki”.

“Ameen ya rabbi”

Kuzeem da su Raudah suka amsa a tare, daga haka su dukansu suka fice daga palorn tare da nufar harabar makeken gidan, kai tsaye wurin Abba da ke tsaye a gefen wata arniyar mota suka nufa, rungumeshi Kuzeem tayi ba tare da tace komai ba, hakan yasa Abba ya shafa kanta yana sakin murmushinsu na manya, sannan yace;

“‘Yar lelenah Allah ya bada nasara, fatan alkhairi, ki kula da kanki ki kuma kare mutuncinki a duk inda kike, duk da banada haufi da shakku a kanki, amma a matsayina na uba kuma jigo a gareki dole ne in tunasar da ke akan hakan, ina fatan zaki lura dakyau?”.

Kuzeem bata ankara ba taji wasu k’wallah sun gangaro mata a kunci, sai take ganin tamkar rabuwa ce ta har abada zatayi da ahalin nata, a hankali tace;

“Insha Allahu Abba”.

Tana gama fad’in haka, ta bar jikin Abba ta isa wurin Raudah da Deedee ta had’asu su biyun ta rungume a jikinta, sannan tace;

“Ku kasance haske a idanuwan Abba da Ammah, Raudah kece babba dan Allah ki kula da Ammah sosai, ki kula da lafiyarta kamar yanda kuka saba, ku daina yin nesa da ita tana buk’atar kulawarku”.

Kasa bata amsa sukayi saima wani k’ank’ameta da sukayi suna kuka mai cin rai,  Ammah da ke gefe itama kukan take, ganin haka ya sanya Abba takowa inda suke ya b’amb’are su Raudah dak’yar daga jikin Kuzeem, sannan ya ja hannunta ya bud’e mata k’ofar mota, juyowa tayi ta kalli Ammah da su Raudah tana jin zuciyarta na karaya, sai taji kamar ta fasa tafiyarma, hannu kawai ta d’aga musu sannan ta shige cikin motar, Abba yayi saurin rufe k’ofar, tare da zagayawa ya shiga gefen motar don tare da shi za’a kaita airport, daga haka direba ya tada motar suka nufi hanyar ficewa daga gidan, dama tuni security’s suka wangale k’aton get d’in. Saida motar ta fice daga gidan kana su Ammah suka koma ciki, zuciyoyinsu cike da kewar Kuzeem.

Koda suka isa airport d’in saida Abba ya sake yimata nasiha, wannan karon kam kuka tayi sosai, dak’yar Abba ya samu ya rarrasheta har tayi shiru. Barin wurin hayaniyar mutane Kuzeem tayi ta d’an koma gefe sannan ta kara wayarta a kunne da alama kira take, tana jin an d’aga kiran tace;

“Gani a hanyar zuwa garinku, nan da wasu mintuna zan iso”.

Banji mai akace mata ba naga tayi saurin ciro wayar daga kunnenta, tare da sakin guntun murmushi tana girgiza kanta, sannan ta bar wurin tana saka wani kyakkyawan face mask a fuskarta. Sai 9:00am jirginsu ya d’aga a duniyar sama wacce tayiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo!.😜

#Anup⁔⁶ ⁶⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *