YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 6 BY ANUP JANYAU
(_SPY_🎥)
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani irin taku Kuzeem keyi tamkar wata zakanya, cike da tsagwaron jarumta wacce batada algus. Yayinda Meerah ke gefenta sai Securityâs da ke bayansu, har suka iso bakâin wani kâaton building, wanda a nan ne office dâin L.G Aliyu Iko yake. Cikin sauri Securityâs dâin wurin suka budâe mata kâofa tare da sadda kawunansu a kâasa saboda jin nauyin rashin bata girman da suka saba yi. Dâan guntun murmushi Kuzeem tayi sannan ta shige ciki, ta bar su Meerah tsaye a wurin, don basuda izinin shiga ciki. Daidai lokacin wani Security ya iso wurin tare da shaida musu ana son ganinsu ga baki dâaya, hakan yasa suka bar wurin su dukansu.
Ba shiri Major Khalil yayi saurin dakatar da dariyar da yake yi, yana mai sake tariyo ma kâwakâwalwarsa yanayin kallon da Kuzeem tayi masa kafin ta bar office dâin. Hannayensa biyu ya hardâe a kâirji, tare da jinjina kai yace;
âTabbas akwai tarin maâanoni a cikin kallon da tayi min, tou me hakan ke nufi?. Menene dalilin da yasa aka koresu a hukumar nan?, wanne irin laifi ne suka aikata?, kuma meyasa baâa zauna da ni a cikin meeting dâin da akayi ba?, wanda kâaâida ne duk sanda zaâa zauna meeting irin haka da ni ake zama, amma sai gashi wannan karon baâa neme ni ba. Ba ko shakka akwai lauje cikin nadâi, don haka ya zama dole in binciko ainahin bakin zarenâ.
Yana gama fadâin haka ya bar office dâin da sauri kamar zai tashi sama, yana fitowa harabar hukumar ya hango Securityâs jere cikin layukka sun kâame wuri dâaya, hannayensu a goshinsu alamar Salute, yayinda B.G Atiku Tanko ke tsaye a gabansu fuskar nan tashi a turnukâe babu alamar rahma, tamkar bai tabâa dariya ba.
Tsaye yayi tare da rikâe kâugu yana kallon yanda Securityâs dâin suka daza layukka, sai kuma ya dâauke kansa ya mayar gefe kana ya sake maida dubonsa a garesu, da wani irin sauri ya sake kallon gefe, karaf idanuwansa suka sauka kan su Kuzeem da ke nufosa ita da Bilal. Kallonsu kawai yake yi yana son nazartar yanayin da suke ciki amma ya kasa tantance ainahin yanayinsu, har suka iso ta wurin da yake tare da wuce sa, da kallo ya bi bayansu yana kâiyasta abubuwa da dama a ransa, yayinda su ko kallon banza bai ishesu ba. Kai tsaye wurin Securityâs dâin suka nufa, ko wannensu fuskarsa ba yabo ba fallasa, daidai lokacin mutane hudâun da zasuyi aiki tare suka iso wurin suma, hakan yasa suka jera a tare, kallo dâaya zakayi musu kasan an hadâa zaratan jarumai masu jini a jika, wadâanda ke tsoratar da tsoro da kansa, kâi gudu sa gudu.
Wannan jerawar da sukayi ba kâaramin birge sauran jamiâan sukayi ba, wadâanda ko wannensu tun dâazun sai tambayar kansa yake laifin me wadâannan manyan jigunan hukumar sukayi aka koresu?, saidai sun kasa samun amsar tambayar, yayinda wasu sukayi farin ciki da hakan, wasu kuma suka shiga jimamin lamarin. Suna isowa wurin suka tsaya bayan B.G Atiku Tanko, hakan yasa Securityâs dâin suka shiga sauke hannayensu kâasa a tare, cikin wani irin salo mai birgewa, saidai kallo dâaya zaka yima yanayin fuskokin wasu daga cikinsu kasan sam basu tare da walwalarsu.
Juyowa B.G Atiku Tanko yayi wurin su Kuzeem yana yimusu wani irin kallo wanda suka dadâe da fahimtar maâanarsa, sannan ya maida dubonsa ga Securityâs dâin da ke jere a gabansa, cikin wata irin murya mai amo da sauti yace;
âJamiâai!!!â.
âYallabâai!!!â.
Muryarsu ta kâarade wurin.
âA juya sashen damaâ.
B.G Atiku Tanko ya sake fadâa musu da kâarfi cike da bada umurni. Cikin sauri suka buga kâafafuwansu na hagu a kâasa, tare da yimasa Salute sannan suka juya bâangaren dama. Idan kaga yanda sukayi abun sai yayi matukâar birgeka. Sake tamke fuska yayi sannan ya juyo ya kalli su Kuzeem ba tare da ya furta komai ba yayi musu alama da hannu a kan su tafi. A tare sukayi mishi murmushi sannan suka juya tare da barin wurin suka nufi inda sukayi perking motocinsu. Babu wanda ya sake furta komai daga cikinsu kowa ya shiga motarshi, aka budâe musu get suka bar wurin.
Wani irin iska Major Khalil ya furzar daga bakinsa don ga baki dâaya kansa ya kâulle ya kasa hasaso komai, ya kasa gano bakin zaren, cikin sauri ya nufi hanyar zuwa upstairs, kâofar na budâewa ya shiga, elavotor ya shiga tare da danna 3rd floor, yana tsayawa ya fito ya nufi bakin wata kâofa da aka rubutama *DGN(Director General) Colonel Mansur Iliyas Sani*. Hankali tashe ya murdâa handle dâin kâofar, ya fadâo cikin tamfatsetsen office dâin mai girman gaske da tsaruwa.
Saurin dâagowa wani babban mutum dake zaune cikin office yana danna sytem dâin gabansa yayi tare da kallonsa, sannan yace;
âTaya akayi ka san na dawo?â.
Da sauri Major Khalil ya iso wurinshi tare da jan kujera ya zauna, sannan yace;
âWallahi Uncle bansan ka dawo ba kawai hasashen zuciyata neâ.
Kai ya gyadâa yace;
âMe ke tafe da kai?â.
âWata tambaya nake da ita wacce na san kai kadâai ne zaka iya bani amsartaâ.
Hannu Colonel Mansur Iliyas ya kai ya cire glass dâin idonshi, sannan ya rufe sytem dâin gabanshi yace;
âIna jinkaâ.
âEhm.. dama ina son tambayar laifin me su Kuzeem Yusuf Garba sukayi aka koresu?â.
Major Khalil ya fadâa muryarsa na gargada. Wani kallo Colenel Mansur Iliyas yayi masa sannan ya dâauki glass dâinsa ya kafa a ido, kana yace;
âBan sani baâ.
Sadda kai kâasa Major Khalil yayi don dama yasan zaâa rina, kawai ya yanki tikiti ne amma yasan ba lallai ya samu amsar tambayarsa ba. Hanyar waje Colonel Mansur Iliyas ya nuna masa yace;
âTashi ka fitaâ.
Jiki sanyaye ya mikâe ya nufi hanyar fita, har ya kai bakin kâofa ya ji Colonel Mansur na fadâin,
âKhalil ka daina shiga abinda bai shafeka ba, saboda hakan ci baya neâ.
Cike da jin haushi Major Khalil ya ida ficewa daga office dâin yana kâunkâunai, tare da jin haushin Uncle dâin nashi. Ya rasa meyasa yake masa haka, sam baya basa goyon baya kuma baya ganin farinsa akan duk wani abu da zaiyi, tamkar ba Yayan Mahaifiyarsa ba. Ya sani sarai yafi kowa sanin dalilin korar su kuzeem saboda shine Director General na *DSS* dake kâasar SARBIK ga baki dâaya.
Fuska dâauke da murmushi Kuzeem ta fito daga motarta ta nufi cikin gidan, da murna su Raudah suka yimata sannu da dawowa, ta amsa musu cike da farin ciki, sannan ta gayar da Ammah tare da zama gefenta, bayan Ammah ta amsa gaisuwar ne tace;
âKuzeem wannan faraâar duk ta miye?â.
âYar dariya Kuzeem tayi wacce ta kâara bayyanar da tsantsar kyaunta, sannan tace;
âAbba na nan?â.
Cikin mamaki Ammah ke kallonta sannan tace;
âYana nan, ya dawo tun dâazun kansa ke ciwoâ.
Wata irin mikâewa Kuzeem tayi tace;
âSubhanallah, an kira family dr?â
âCewa yayi baya bukâatarsaâ.
Da sauri Kuzeem ta bar wurin hankali tashe, hakan yasa Ammah ta bi bayanta da kallo har ta fice daga dâakin. Sai kuma ta mikâe tace;
âRaudah ku tashi muje part dâin Abban kuâ.
Kuzeem na shigowa palorn Abba, ta hangosa kishingidâe kan rug ya dâan dâora kansa a kan wani hadâadâdâen titimi, cikin sauri ta iso wurinsa tare da durkâusawa a gabansa tace;
âAbbaâ.
A hankali Abba ya budâe lumsassun idanuwansa, yana ganinta yayi saurin tashi zaune tare da hadâe rai yace;
âMe kika zo yi wurina?, ko wata sabuwar rashin kunyar ce kika zo kiyimin kuma?â.
Saurin girgiza kai tayi tare da rikâo hannunsa, da sauri Abba ya fisge hannunsa daga rikâon da tayi masa sannan ya nuna mata hanyar fita yace;
âTashi ki bâace min da gani Fatima, tun kafin inyi mummunan sabâa mikiâ.
Wasu yawu masu dâaci Kuzeem ta hadâiye da kâarfi, sannan tace;
âKa gafarce ni Abba, na san ban kyauta ba, amma dan Allah ka yafemin ko zan samu rahmar ubangijiâ.
Shiru Abba yayi tare da mayar da kansa gefe alamun baima sauraronta, ganin hakan yasa Kuzeem ta koma gefen da yake kallo tace;
âDan Allah Abba ka daina fushi da ni, kayi hakâuriâ.
Mikâewa Abba yayi, a fusace yace;
âKafin in budâe idanuwana kiyi gaugawar bâace min da ganiâ.
âBabu inda zataje saika yafe mataâ.
Ammah da suka iso cikin palorn yanzu, ta fadâa. Ko kallonta Abba baiyi ba ya nufi hanyar zuwa bedroom dâinsa, da sauri Kuzeem ta mikâe tabi bayanshi, tana isowa inda yake ta rungumeshi ta baya tare da fashewa da kuka, hakan yasa Abba ya tsaya cak, ba kâaramin sukar zuciyarsa kukan nata keyi ba, amma baya jin zai iya kulata.
âAbba na amince zan auri Mr Salame kamar yanda kake bukâata, in har hakan zaisa ka yafemin kuma ka kasance cikin farin ciki na har abada!â.
_*Masoyana ga fa dama ta samu wacce zaku nunamin zallar kâaunar da kukemin a zahiri indai batada algus😅 ga link dâin youtube channel dâita nan, #Anup Janyau Tv. Don girman Allah kuje kuyimin Subscribe ku suburbudâamin like, tare da danna kâaraurawar sanarwa, domin sanar daku a duk lokacin da na dâora shirye-shiryena, nagode #One luv.*_❤️
Saurin kallon Kuzeem Ammah tayi fuskarta dâauke da mamakin jin furucinta. Raudah da Deedee kuwa juyawa sukayi suka fice daga dâakin.
âFatima dagaske kike zaki auri Muâaz Salame?, kodai kin fadâi hakan ne don ki rainamin hankali?â.
Abba ya tambayeta cike da rashin yarda da abinda ta fadâa don yasan halin Kuzeem kaifi dâaya ce, saidai kuma lokaci dâaya yaji tantamar da yake a kanta ta fara gushewa, saboda wani irin farin ciki da ya lullubâe zuciyarsa.
âOver my death bodyâ
Kuzeem tayi saurin fadâin haka a ranta, amma a zahiri cewa tayi.
âHaba Abba! meyasa bazaka yarda da âyar lelenka ba?, tou bari in sake maimaita maka don ka yarda da kyau, na amince zan auri Mr Salame domin ganin farin cikin kaâ.
Tana gama fadâin haka ta saki wani guntun murmushi mai tarin maâanoni, sannan ta bar jikin Abba. Cikin sauri Abba ya juyo ya kalleta, fuskarsa dâauke da wani irin annurin farin ciki, wanda yasa Kuzeem murna a ranta, don ta san kalamanta sun riga sunyi tasiri a zuciyarsa, sannan kuma ta kawar da fushin da yake da ita.
âAlhamdulillah!. Hakâikâa Allah kaine abin godiya. Yar lelenah Allah yayi miki albarka ya faranta miki rai kamar yanda kika faranta min rai, ina matukâar alfahri da keâ.
Abba ya fadâama Kuzeem cikin wani yanayi na farin ciki wanda bai misiltuwa. Kyakkyawan murmushi Kuzeem tayi mishi, a ranta tana mamakin hali irin na mahaifinta, wanda ta dadâe da cin alwashin saita rabashi da wannan halin na son abin duniya.
âWato kin amince zaki auri Muâaz Salame kou?, saboda cikar wani dogon buri na Abbanki, Allah ya kyautaâ.
Inji Ammah tana hararar Abba. Wani murmushi Abba yayi, don sam yanzu ba lokacin bâacin rai ba ne a gareshi.
âHafsa kenan!, ban san sai yaushe zaki waye ba?, ki gane me duniya take cikiâ.
âAbba ya kan naka?â.
Kuzeem tayi saurin tambayarshi don son kawar da wancen zancen, maido da dubonsa yayi a gareta yace;
âKai haba, ai tuni ciwon kan ya wartsake dama na rashin bacci neâ.
âAbba rashin bacci kuma?, me ke hanaka baccin?â.
Wani murmushi Abba ya sake yi, tare da janyo hannunta suka zauna kan kujera. Hakan yasa itama Ammah ta zauna tana kallonsu cike da takaici.
ââYar lelenah duk yanda zanyi miki bayanin kalar damuwar da na shiga akan kâin amincewa da auren Muâaz Salame da kikayi, wallahi ba zaki tabâa ganewa ba, amma dai yanzu komai ya wuce a bar tuna baya. Meya dawo dake gida da wuri haka?â.
Inji Abba da har lokacin murmushi ke bayyane a fuskarsa. Cikin tausasa murya Kuzeem tace;
âAbba na dawo ne saboda ina so muyi wata magana da kai, saidai bansan ko zaka amince ba, duk da dai amincewar ta zama doleâ.
Ba kâaramin fadâuwa gaban Abba yayi ba jin abinda ta fadâa, amma haka yayi kâarfin halin fadâin,
âTou ina jinkiâ.
Dâan lumshe idanuwanta tayi, tare da budâesu a hankali ta sauke su akan Ammah da ke yimata wani kallo, sannan ta maido dubonta ga Abba tace;
âAbba amincewa ta da maganar auren Mr Salame ba wai yana nufin zaâayi auren nan da wata dâaya kamar yanda yake bukâata baâ.
âWhat!?â.
Abba ya fadâa da kâarfi yana mikâewa tsaye cikin wani irin sabon tashin hankali da ya ziyarceshi, sannan ya nunata da yatsa yace;
âKarki rainamin hankali Fatima!, am i your mate?, da zaki zauna kina bani umurni?. Sai yanzu ma nake mamakin kaina da nayi saurin amincewa da ke, Fatima na san halinki sarai kamar yinwar cikina, tun kina kâaramarki idan kika ce baza kiyi abu ba, tou ko me zaâayi babu wanda zaisa kiyi abun nan, balle yanzu da kika girma. Kawai dai kina son ki rainamin wayau ne, da farko kince bazaki tabâa auren Muâaz Salame ba, yanzu kuma kin dawo kince kin amince, tabbas na san akwai shirin da kike yiâ.
Ya kâarashe maganar a zafafe tare da mayar da hannuwansa duka biyu a baya yana kafeta da idanuwansa. Saurin durkâusawa a gabansa Kuzeem tayi tace;
âKa yarda da ni Abba, babu wani shirin da nakeyi, wallahi a hukumar mu ne aka turani wurin wani aikin sirri wanda zai dâaukeni tsawon wani lokaci, wannan dalilin ne ya sanya nake son a janye maganar auren a yanzu, saboda aikin baze yiwu ba idan inada aure, kuma nasan kaima hakan shine kwanciyar hankalinkaâ.
Sai a lokacin kaso 89% daga cikin 100% na hankalin Abba da ya dâugunzuma ya dâan kwanta. Komawa yayi kan kujera ya zauna sannan yace;
âIna bukâatar kâarin bayaniâ.
Kuzeem bata tashi a wurin ba, ta fara korama Abba bayani tun daga farko har zuwa kâarshe. Rai a dâan bâace Abba yace;
âAmma su wadâanne irin marasa hankali da tinani ne?, da zasu tura mace irin wannnan aiki mai matukâar hatsarin gaske, kuma wai har wata jaha. Wannan ai zancen banza ne, to bari kiji sam baze yiwuba, ba zaki je ba…â.
âAbba idan har dagaske kana sona, kuma kana son ganin farin cikina kamar yanda kake fadâa, tou don Allah ka barni in aiwatar da wannan aiki, saboda a halin yanzu babu abinda ke cikin raina, na kuma sashi a gaba sama da wannan aikin, ina so ka sani duk wanda ya shiga aikin hukumar tsaro, mace ko namiji matsayinsu dâaya ne, babu wani bambanci, kuma na riga nayi alkâawalin zan aiwatar da wannan aiki ba gudu ba ja da bayaâ.
Dâan jinjina kai Abba yayi, don ya tabbatar da gaske take, idan har yace zai dakatar da ita daga wannan aikin, to kuwa rayukane zasu bâaci, kâwanda ya samu ya bita a hankali har ta auri Muâaz Salame.
âTou shikenan âyar lelenah, na amince Allah taimaka kuma ina miki fatan nasara a cikin wannan gagarumin aiki da zakiyiâ.
Cike da tsantsar farin ciki Kuzeem ta rungume shi tace;
âNagode Abba, Allah ya barmin kaiâ.
Mikâewa Ammah tayi ta fice daga dâakin, tana nazarin kalaman Kuzeem a ranta. Abba da Kuzeem kam saida suka sake tattaunawa sannan Kuzeem ta bar part dâin, tana sakin wani murmushi. Yayinda Abba ya dâau wayarsa ya dannawa Muâaz Salame kira domin bashi wani babban uzurin da ya shirya.
Ammah na zaune a palornta da su Deedee sunyi shiru suna juya lamarin a ransu, Kuzeem ta shigo, saurin mikâewa Ammah tayi tana yimata wani kallo, sannan tace;
âKin bani mamaki, kuma kin bani kunyaâ.
âKi kwantar da hankalinki Ammah, abinda kike tinani ba haka abun yake baâ.
Kuzeem ta fadâa mata a hankali, sannan ta maida dubonta wurin su Raudah tace;
âSisters ku dâan bamu wuri zamuyi maganaâ.
Mikâewa Raudah da Deedee sukayi tare da barin palorn. Sai a lokacin Amma ta koma kan kujera ta zauna tare da sakin wata nannauyar ajiyar zuciya. hakan yasa Kuzeem ta zauna gefenta, tare da rikâo hannuwanta sannan ta fara yimata bayanin komai.
Wani murmushi Ammah tayi bayan ta gama sauraren Kuzeem, sannan tace;
âSai yanzu hankalina ya kwantaâ.
Kwanciya Kuzeem tayi a kan kujerar tare da yin pillow da lap dâin Ammah ta lumshe idanuwanta ba tare da tace komai ba.
Around 5:45pm Meerah ta iso gidan su Kuzeem hankali tashe don sai a lokacin suka tashi aiki, babu tambayar da batayima Kuzeem ba akan laifin me sukayi?, Kuzeem tace mata batada masaniya kawai dai sunga an dakatar dasu ne daga aiki, amma basu san laifin da sukayi ba, kuma baâa fadâa musu ba.
âWallahi wannan abun wata makâarkâashiya ce aka kâullaâ.
Inji Meerah da ke kuka, zuciyarta har wani zafi take. Dâan cije lips Kuzeem tayi cike da tausayin Meerah ganin yanda take kuka a banza, da tanada damar sanar da ita gaskiyar lamarin da tayi hakan, saboda yanda ta sanya kanta a damuwa duk a sanadinta, hakan yasa take jinta tamkar âyar uwarta.
“Ki daina kuka Meerah, komai daren dadâewa dole na san gaskiya zatayi halinta. Ina baki shawara a koda yaushe ki zamanto mai jajircewa tare da rik’o da gaskiya a wurin aikinki duk tsanani duk wahalaâ.
Kuzeem ta fadâawa Meerah tana kâakâaro guntun murmushi, girgiza mata kai kawai Meerah tayi, don tana cikin damuwa sosai, ba k’aramin shak’uwa tayi da Kuzeem ba, sai k’iyastawa take a ranta yanda zata cigaba da aiki a hukumar ba tare da Kuzeem ba. Dakâyar dai Kuzeem ta samu ta rarrasheta, sai daga bisani Kuzeem ta sanar da ita zatayi tafiya, Meerah tayi mata adduâar sauka lafiya.
*3 days later*
Yau Kuzeem zata bar F.C.T FUNADE zuwa jahar RADDAL. Ba kâaramar damuwa ahalin nata suke ciki ba, don ko kadâan basu son tayi nesa da su, saidai ba yanda suka iya, hakan yasa suke ta yimata adduâoin fatan nasara tare da kariyar ubangiji.
Cikin sanyin jiki Kuzeem ta fito daga dâakinta, don itama ba kâarya ta san zatayi kewar ahalin nata. Sanye take da wata tsadaddar Abaya peach, wacce tayi matukâar amsar jikinta, tayi rolling veil dâin Abayar a kanta, sai wayarta dake hannunta da wata hadâadâdâan hand bag peach color, yayinda Raudah ke biye da ita a bayanta hannunta dâauke da laptop bag dâinta, don tuni aka kaimata trolleynta a boot.
Fadâawa jikin Ammah da ke tsaye a main palor Kuzeem tayi tare da fadâin,
âZanyi kewarki sosai Ammahâ.
Murmushin kâarfin hali Ammah tayi tare da rungumeta a jikinta, nan take taji kâwalla sun taru a idanuwanta, cike da kâarfin hali ta iya fadâin,
âNima haka Kuzeem. Ina rokâon Allah ya baki nasara a cikin wannan aiki da kika sanya a gaba, ya kareki a duk inda kike tare da sauran abokanan aikinkiâ.
âAmeen ya rabbiâ
Kuzeem da su Raudah suka amsa a tare, daga haka su dukansu suka fice daga palorn tare da nufar harabar makeken gidan, kai tsaye wurin Abba da ke tsaye a gefen wata arniyar mota suka nufa, rungumeshi Kuzeem tayi ba tare da tace komai ba, hakan yasa Abba ya shafa kanta yana sakin murmushinsu na manya, sannan yace;
ââYar lelenah Allah ya bada nasara, fatan alkhairi, ki kula da kanki ki kuma kare mutuncinki a duk inda kike, duk da banada haufi da shakku a kanki, amma a matsayina na uba kuma jigo a gareki dole ne in tunasar da ke akan hakan, ina fatan zaki lura dakyau?â.
Kuzeem bata ankara ba taji wasu kâwallah sun gangaro mata a kunci, sai take ganin tamkar rabuwa ce ta har abada zatayi da ahalin nata, a hankali tace;
âInsha Allahu Abbaâ.
Tana gama fadâin haka, ta bar jikin Abba ta isa wurin Raudah da Deedee ta hadâasu su biyun ta rungume a jikinta, sannan tace;
âKu kasance haske a idanuwan Abba da Ammah, Raudah kece babba dan Allah ki kula da Ammah sosai, ki kula da lafiyarta kamar yanda kuka saba, ku daina yin nesa da ita tana bukâatar kulawarkuâ.
Kasa bata amsa sukayi saima wani kâankâameta da sukayi suna kuka mai cin rai, Ammah da ke gefe itama kukan take, ganin haka ya sanya Abba takowa inda suke ya bâambâare su Raudah dakâyar daga jikin Kuzeem, sannan ya ja hannunta ya budâe mata kâofar mota, juyowa tayi ta kalli Ammah da su Raudah tana jin zuciyarta na karaya, sai taji kamar ta fasa tafiyarma, hannu kawai ta dâaga musu sannan ta shige cikin motar, Abba yayi saurin rufe kâofar, tare da zagayawa ya shiga gefen motar don tare da shi zaâa kaita airport, daga haka direba ya tada motar suka nufi hanyar ficewa daga gidan, dama tuni securityâs suka wangale kâaton get dâin. Saida motar ta fice daga gidan kana su Ammah suka koma ciki, zuciyoyinsu cike da kewar Kuzeem.
Koda suka isa airport dâin saida Abba ya sake yimata nasiha, wannan karon kam kuka tayi sosai, dakâyar Abba ya samu ya rarrasheta har tayi shiru. Barin wurin hayaniyar mutane Kuzeem tayi ta dâan koma gefe sannan ta kara wayarta a kunne da alama kira take, tana jin an dâaga kiran tace;
âGani a hanyar zuwa garinku, nan da wasu mintuna zan isoâ.
Banji mai akace mata ba naga tayi saurin ciro wayar daga kunnenta, tare da sakin guntun murmushi tana girgiza kanta, sannan ta bar wurin tana saka wani kyakkyawan face mask a fuskarta. Sai 9:00am jirginsu ya dâaga a duniyar sama wacce tayiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo!.😜
#Anupâ”ⶠâ¶â°