YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU
(_SPY_🎥)
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun bayan kammala sallar asubah Kuzeem bata koma bacci ba, ta dukāufa aiki a system dāinta wanda ya dāauketa tsawon wani lokaci, daga baya ta buge da online shopping inda tayi siyayya me yawan gaske, don dama ita tana daga cikin mutanen da suka yarda da online shopping saboda yafi musu saukāi, musamman ma ita da batada wani lokacin kanta, saida ta kammala komai kana taje tayi wanka ta shirya cikin wata blue gown, mai masifar kyau da tsada, tare da feshe jikinta da tsadadden turarenta mai shegen dadāi da kāamshi wanda ke narkar da zuciyar duk wani wanda ya shakāi kāamshinsa.
Wurin Binta dake baje kan gado tana sharar bacci ta isa ta tayar da ita tare da bata umurnin ta tashi tayo alwala ta gabatar da sallah, daga haka ta fice daga dāakin, kai tsaye gaban kāatuwar Tv plasma dake palorn ta nufa ta kunna, kana ta dāau remote ta dawo kan kujera ta zauna, sanja cannel tayi tare da dāan lafewa a jikin kujerar tana kallon news dāin daki-daki. Tsawon 7 minutes sai ga Binta ta iso palorn hannunta rikāe da wayar Kuzeem da aka kira, gyara zamanta tayi sannan ta karbāi wayar tare da dāaga kiran, a hankali ta furta,
āMorning Sirā.
Daga haka tayi shiru, bansan mai aka ce mata ba naga ta dāan wulkāita kyawawan idanuwanta harta kai dubonta zuwa ga agogon bangon dake dāakin, sai kuma ta dāauke idanuwanta ta lumshesu kana tace;
āMeyasa zaāayi haka?, shin baāa yarda dani ba ne ko me?ā.
Dāan shiru tayi don ba kāaramin bāaci ranta yayi ba, idan ta cigaba da magana zaāa iya samun matsala duk da ko yanzu ba wai zata kāi fadāin abunda ke ranta ba ne, saida ya kammala maganar da yake, kana ta budāe idanuwanta tare da sakin wani guntun murmushi tace;
āSir, idan zanyi abu ina yinshi ne da dukkan zuciyata kuma kun dadāe da sanin hakan, so banga dalilin da zaisa a rikāa bibiyar lamurran da suka shafeni ba, saboda ni naji na gani na kuma amince da wannnan aiki, duk da kuwa na san akwai tarin kāalubale a cikinsa, maganar gaskiya Sir banji dadāi ba ko kadāan, kuma nayi mamaki matukāaā.
A yanda ta kāarashe maganar zaka tabbatar da ranta yana a bāace, ta sanadin hakan ne ma yasa bata jira jin abinda zai sake fadāa mata ba ta katse kiran tare da wulla wayar gefenta, ita mutum ce mai saurin dāaukar zafi musamman ga abunda taga alamar akwai cin zarafi a cikinsa, dama tun jiyan da ta fahimci akwai wata a kāasa dauriya kawai takeyi, saboda bata son aikin ya fice mata a rai don ta riga tasa kanta, kuma ta dāaukarma kanta alkāawalin duk tsanani duk wuya bazata ja baya ba. Tana jin wani kiran ya sake shigowa wayarta amma tayi banza ta cigaba da kallon news dāin da take.
8:00am Rabson da Bash suka iso Estate dāin, don jiran fitowar Kuzeem saidai har 9:30am tayi basuga alamar zata fito ba, hakan yasa suka kama hanyar zuwa asibitin su Saimah a cewarsu ko ta tafi tun dāazun. Suna barin wurin Saimah ta iso, horn tayi aka budāe mata get dāin kana ta kunna kan motarta cikin Estate dāin, bayan tayi perking ne ta fito daga motar tare da budāe back seat ta ciro wani hadāadādāen basket na alfarma, kana ta nufi hanyar shiga gidan.
Mikāewa Kuzeem tayi jin anyi Knocking door, gently ta isa wurin kāofar ta budāe, nan idanuwanta suka sauka kan Saimah, kusan a tare suka sakar ma juna murmushi kana ta dāan matsa gefe don ta bata damar shigowa cikin palorn, bayan Saimar ta shigo ne Kuzeem ta maida kāofar ta rufe kana suka isa cikin palorn, Saimah na fadāin,
āNa kiraki baki dāaga baā.
Saida Kuzeem tayima kanta masauki akan kujerar da ta shi, sannan tace;
āIna wani abune a lokacin, saisaā.
āOkay ai na manta agogo sarkin aiki kikeā.
Inji Saimah tana harararta, Kuzeem dai bata ce mata komai ba ta maida hankalinta kan wayarta da sakāo ya shigo.
āGa fa abinci nanā.
Saimah ta sake fadāamata, a hankali Kuzeem ta kai idanuwanta kan basket dāin kana ta dāauke tace;
āSaidai Binta, ni sai zuwa anjimaā.
Wata hararar Saimah ta sake bāalla mata tare da tabāe baki kana ta janyo basket dāin ta ciro plate da spoon ta zubama Binta abincin. Kuzeem kuwa mikāewa tayi ta nufi kāofa, yayinda Saimah da Binta suka bita da ido har ta budāe kāofar palorn ta fice.
Murmushi wata arniya dake tsaye wurin balcony tayima Kuzeem, tare da fadāin,
āGood morning Maāam!ā.
Fuska ba yabo ba fallasa Kuzeem tace;
āMorning, how are you?ā.
āIām fine Maāamā.
Ta amsama Kuzeem har lokacin fuskarta na dāauke da murmushi, sannan ta nuna mata wata mota dake ajiye a gaban gidan tana fadāin,
āGa kayanki sun iso Maāamā.
Sai a lokacin Kuzeem ta kai dubonta wurin motar da wani saurayi keta faman jido wasu manyan bags yana ajiyewa a wurin.
āOkay thanksā.
Kuzeem ta fadāa cike da kulawa. Wani murmushin arniyar ta sake yi, na jin dadāin tarin siyayyar da Kuzeem tayi a wurinsu, wacce ta kashe makāuddan kudāadāe.
āAlways welcome Maāamā.
Arniyar ta sake fadāawa Kuzeem, daga haka ta nufi wurin motar, yayinda Kuzeem ta rufa mata baya, cike da girmamawa saurayin ya gaida Kuzeem ta amsa mishi, sannan ta bashi umurnin shigar da kayan cikin gida, bayan ya gama ne, Kuzeem ta sake musu godiya inda suma suka yi mata godiyar kamar ba gobe, sannan suka tada motarsu suka bar wurin.
Kuzeem na shigowa cikin palor Saimah ta wulgo mata wani kāaramin pillown kujera tare da bāalla mata uwar harara tace;
āWallahi matar nan bakida kirki ko kadāan, yanzu fisabilillahi muna zaune zaki wani turo muna kāaton gardi a cikin dāaki yana muna shige da fice?, haka kawai mun barbaje muna shakāatawa ya wani zo ya kallemu tas a banza da wofi, nidai wallahi kin cuceniā.
Murmushi Kuzeem tayi, saboda Saimah na dāaya daga cikin mutanen da ke sanyata farin cikin dole, duk irin yanayin bāacin ran da take ciki.
āKuzeem!ā.
Saimah ta kira sunanta da kāarfin gaske, tana kallon Mom Eshmal da Mom Arif dake tsaye bakin kāofar palorn ko wace hannunta dāauke da muciya, yayinda Mom Eshmal tasha wata uwar dāamara tana girgije-girgijen rashin mutunci da tijara.
āSu waye ku?, me kuke shirin aikatawa?ā.
Saimah ta tambayesu tana mikāewa tsaye, saidai bata yarda ta matsa daga inda take ba don kadāan take jira tayi wuf cikin dāaki. Kuzeem kuwa kyawawan idanuwanta ta wulga akan extension wire dake jikin dāaya daga cikin socket dāin palorn.
āUwarki da ubanki zamuyiā.
Inji Mom Arif tana wani tsikare dāan kwalin wata arniyar shadda dake jikinta, kana suka fara takowa zuwa cikin palorn, har lokacin Kuzeem na tsaye a wurin ta basu baya, kuma ko alamar motsawa batada. Wata shewa Mom Eshmal tayi tace;
āHeeee! lallai yarinya, to maza ki juyo kiga maza bisa kanki, ahayye nanaye yau zan nakkasa banza, billahil azim yau saina sanja maki kamanni kin zama abun kwatance, daga lokacin nasan bazaki sake gigin shisshigi akan lamarin kowa baā.
Kamar kāyaftawar ido Kuzeem ta fisgo jibgegiyar extension wire dāin, sannan tayi saurin juyowa ta fuskancesu dakyau, don so take yau dāin nan ba sai gobe ba, ta koya musu hankalin da nan gaba sai sunji shakkun yima wani mahalukāi kallon banza, ballantana har suyi yunkāurin illata shi. Mom Eshmal na kāokāarin magana ba zato ba tsammani taji saukar waya a jikinta, ai ba bāata lokaci ta saki muciyar hannunta tare da kai hannunta saitin da Kuzeem ta lafta mata wayar, ganin abinda ke faruwa yasa Mom Arif tayo cikin Kuzeem saidai tun kafin ta kāaraso Kuzeem tayi wuf ta koma ta bayanta sannan ta dagargaje ta lafta mata wayar itama a tsakiyar bayanta, wani shegen ihu ta saki abunka da jan buzu jiki baison wahala😂. Kuzeem kuwa kallon Saimah tayi cikin wata dakakkiyar murya tace;
āRufemin kāofar can Saimah!ā.✍️
*Tashin hankali mai remote*😂💔
Cikin sauri Saimah ta isa wurin kāofar ta rufe, tare da waro idanuwanta waje tana kallon Kuzeem da ta nufi wurin su Mom Eshmal. Ba kāaramin tashi hankalin Mom Eshmal yayi ba, ganin dagaske fa Kuzeem keyi jibgarsu zatayi, sai kawai marin da ta sakarmata jiya ya dawo mata a rai, wanda fadāin azabar shi baya misiltuwa. Mom Arif da bakinta bai gama mutuwa ba tace;
āKuttmar uban chan! ke mu zaki daka?, lallai yarinyar nan ashe kuwa kaf danginku zasu kāare rayuwarsu a prison, wallahi kin taro fadāan da yafi kāarfinki gaba da baya, yau sai munga wanda ya dāaure miki kāugu…ā.
Kuzeem bata yarda ta bata damar kāarashe maganar ba, ta kai mata wayar a jiki, wani irin dukāewa Mom Arif tayi a kāasa, tana sakin wata kāarar azaba, don ba kāaramin shigarta dukan yayi ba. Ganin haka yasa Mom Eshmal rugawa zuwa hanyar fita, Kuzeem ta fisgota da kāarfin tsiya ta dawo da ita baya, tare da sakar mata extension wire dāin a jiki, bata jira sun gama tantancewa ba ta aniya jibgarsu kamar donshi aka turota duniya, saboda a lokacin zuciyarta ta riga ta kawo har wuya, abubuwa biyu ne suka tarar mata a lokaci dāaya, wanda ko wannensu ya haddasa mata matsanancin bāacin rai.
Wani irin ihun neman ceto su Mom Eshmal suke, suna ba Kuzeem hakāuri, amma ko jinsu batayi don idanuwanta sun riga sun rufe, jibgarsu kawai take, ga babu damar wani ya jiyo ihunsu daga waje, saboda tsarin ginin Estate dāin daban yake da sauran gidaje, kuma ko banza akwai tazara tsakanin gidajen. Ganin abun ba na kai sake ba ne, ya sanya Saimah saurin isowa wurin Kuzeem ta rikāeta tana fadāin,
āNa shiga uku!, Kuzeem ya isa haka manah!, karki manta fa ba a hukumarku kike ba, kuma wadāannan mata ne ba maza ba balle kiyita jibgarsu haka, don Allah ki barsu karki jimusu rauniā.
āSaimah Idris Garba! wallahi kiyi gaugawar sakina ko in hadāa dakeā.
Ai tun kafin Kuzeem ta rufe baki Saimah ta daka uban tsalle tayi baya, jin yanda Kuzeem ta kira cikakken sunanta kai tsaye, cikin wata kalar murya mai cike da zallar bāacin rai. Ta san bakāar zuciyar Kuzeem da kuma shakāiyancinta, ba kāaramin aikinta ba ne ta hadāa da itan ta jibga, daga baya ta dawo tana bata hakāuri.
Binta kam sai murmushin jin dadāi take ganin yanda Kuzeem ke jibgar su Mom Eshmal, sai kuka suke kamar wasu kāananun yara, sai ta rinkāa tuno kalolin azabar da tasha wurin Mom Eshmal, shiyasa ko kadāan bata tausaya mata ba, amma ta dāan tausayawa Mom Arif saboda tana dāan kyautata mata wani zubin. Plate dāin abincinta ta janyo ta fara ci hankali kwance.
Kuzeem bata daina dukansu ba saida taga sun galabaita har muryarsu bata fita sosai, wayar ta jefar a kāasa, kana ta hardāe fararen hannuwanta a kāirji tana jifarsu da wani dāan iskan kallo tace;
āBa ku kāananun āyan tasha ba?, masu degreen iskanci da tijara?, to yau ga mai masters da phd a gabanku, dama kunsan ance gaba da gabanta kou?ā.
(Feeyaya dake labāe a bakin kāofa ta lekāo tace *Aljani ya taka wuta*🌚😂💔💃)
āWallahi tallahi!, duk cika baki ne muke, don girman Allah kiyi hakāuri ki yafe muna, billahil azim daga yau har lokacin da zaki bar gidan nan ko kallonki bamu sake yi, balle har muyi miki wani abunā.
Inji Mom Eshmal tana zubda kāwallah masu dāauke da azaba. Wani shuāumin murmushi Kuzeem ta saki, kana tace;
āWadāannan kalaman nadamar, ba a yanzu nake bukāatar jinsu baā.
A tare sukayi saurin girgiza mata kai alamar gamsuwa. Sauke hannunwanta tayi tare da pointing Mom Eshmal da yatsanta tace;
āDaga wane kāauyen kika fito?ā.
Murya na rawa Mom Eshmal tace;
āRISAM…ā.
Dāan waro idanuwa Kuzeem tayi tace;
āWow! amma ko kadāan bakiyi kama da mutanen Jahar RISAM ba, saboda kowa yasan sunada halin dattako, ilimi, sanin darajar dāan adam, da tausayi, sai kuma gashi ke ko dāaya bakida a cikin duka halayen, da alama dai CI RANI kuka zo a jahar kou? huh!ā.
Ba kāaramin sukar zuciyar Mom Eshmal kalaman Kuzeem sukayi ba, amma hakanan ta daure tayi shiru tare da sadda kanta kāasa tana sauke wahalallar ajiyar zuciya. Kuzeem kuwa dubonta ta mayar kan Mom Arif tana kallonta shekāekāe tace;
āKefa jan kāosai daga ina?ā.
āAsaliiā.
Mom Arif ta fadāa muryarta na rawa, don har wani zazzabāi takejin yana neman rufeta, tsabagen azabar da tasha, don tafi Mom Eshmal jin jiki saboda fatarsu ba dāaya ba, fuskarta har wani ja tayi kamar kāosai. Rikāe kāugu Kuzeem tayi tare da dāage mata gira dāaya tace;
āAu! ai ni na dāauka daga gidan shugaban kāasar SARBIK kika fito, a yanda naji kina ikāirarin dangina zasu kāare rayuwarsu a prison, ashe-ashe!ā.
Ta kāarashe maganar tare da kāyalkāyalewa da wata dariyar shakāiyanci, yayinda suka bita da kallo kawai, don kalaman Saimah na dāazun sun gama tabbatar musu da Kuzeem jamiāar tsaro ce, wacce suka alakāantata da soja. Saida ta gama dariyar ne ta maida dubonta kan Mom Eshmal tace;
āWato ke azzaluma an baki amanar āyar marainiyar Allah, amma kin cinye saboda mugun hali da rashin ilimin islama, don mai ilimi bazaiyi abunda kikayi ba. Yawwa bari in tambaye ki, yanzu alal misali, ke na cire misalin ma, a zahiri nake nufi. Yau ki fadāi ki mutu ko mijinki ya mutu, ya zamto kinbar āyarki shin zaki so ayi mata irin zaluncin da kikayima wannan yarinyar?ā.
Ta kāarashe maganar tana nuna Binta dake cin abicinta hankali kwance, tamkar babu abinda ke gudana a wurin. Saurin girgiza kai Mom Eshmal tayi tace;
āAāah wallahi bazan so abinda zai tabāamin Eshmal baā.
āSaboda ita ce dāiyar da aka haifa kou?, ita kuma Binta daga sama ta fadāoā.
Shiru Mom Eshmal tayi tare da sadda kāanta kāasa tana jin wani radāadāi a zuciyarta.
āTou ki kwantar da hankalinki, a yau dāin nan zan mikāata a wurin Mamanta wacce ta san zafintaā.
Cikin wani irin matsanancin tashin hankali maras misiltuwa Mom Eshmal ta dāago tana kallon Kuzeem kana tayi saurin yin kneeling tare da fadāin,
āDon girman Allah ki rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa miki naki, wallahi in kika maidata gidansu mijina yaji abinda nayi mata saki na zaiyi, banida kowa a duniyar nan sai shi, kuma wallahi ina balaāin son mijina, nasan a matsayinki na āyar uwata mace bazaki so aure na ya mutu ba, wallahi nayi nadama bazan sake aikata haka wa kowa ba, zan zamo managarciya mai kyautatawa kowa da wanda na sani da wanda ban sani ba, kuma na miki alkāawalin zan rikāe Binta tsakani da Allah, zan kāaunaceta tamkar yanda nake kāaunar āyata Eshmal, bazan sake cutar da rayuwarta baā.
Yanda Mom Eshmal ke zubda kāwallah tana maganar zai baka tabbacin tayi nadama ba kadāan ba, saboda hankalinta a mugun tashe yake, a halin yanzu ta daina jin radāadāin dukan da Kuzeem tayi mata sai wannan maganar da ta fadāa mata.
āYanda kika cutar da ita ba laifin tsaye balle na zaune, dole ne kema saikin dāandāani irin radāadāin da taji, kuma ko ba komai ina so wannan ya zamo izina ga sauran mutane masu mugun hali irin naki. Sannan wannan nadamar da kike ikāirarin kinyita ba don Allah kikayi ba, azaba ce da kuma kāaunar mijinki yasa kikayi ta, so yanzu kinada damar rokāonta gafara akan abinda kika aikata mata, kafin tayi miki nisan kiwoā.
Kuzeem ta kāarashe maganar tana jifarta da wani mugun kallo. Saurin rikāe kāafafun Kuzeem Mom Eshmal tayi tare da fashewa da wani matsanancin kuka tana fadāin,
āKi taimakeni Kuzeem! karki min haka, na rokāekāi kiyimin alfarma ko sau dāaya ne, wallahi har ga Allah nayi nadama maras misiltuwa, dama sharrin shaidāan ne, yanzu kuma na gane kuskure naā.
Tana gama fadāin haka ta mikāe da sauri ta isa gaban Binta tace;
āBinta ki yafe min kinji kou?, wallahi bazan sake cutar da ke ba, ki yarda daniā.
Kasa cewa komai Binta tayi don zuwa yanzu ta fara jin tausayin Mom Eshmal. Cike da tausayi Saimah ta iso wurinta tare da dafa kafadāarta tace;
āKi kwantar da hankalinki, insha Allah zatayi miki wannan alfarmar, amma ki tabbatar kin gyara kuskurenkiā.
āBafa zan sanja kāudurina ba, dole ne saita girbi abinda ta shuka, a lokacin ne zatayi nadamar gaskiyaā.
Kuzeem ta fadāa tare da nufar hanyar bedroom, a yanda tayi maganar dukkansu sunsan cewa babu alamar wasa a ciki, daga Mom Eshmal har Saimah duk saida jikinsu yayi sanyi.
āDon Allah ki nema min alfarma a wurinta, ta taimaka ta rufamin asiriā.
Inji Mom Eshmal cikin sanyin murya da mutuwar lakkar jiki, girgiza kai Saimah tayi tace;
āKarki damuā.
āNagodeā.
Mom Eshmal ta sake fadāama Saimah tare da mikāewa, itama Mom Arif mikāewa tayi fuskar nan tata ba alamar rahma, wani kallo ta watsawa Mom Eshmal kana ta nufi hanyar fita ta budāe kāofa ta fice daga dāakin, yayinda Mom Eshmal ta rufa mata baya.
āMom Arif!, dan Allah ki tsayaā.
Dakatawa Mom Arif tayi daga tafiyar da take, tana jifar Mom Eshmal da wani kallo, cike da dauriya tace;
āDon Allah kiyi hakāuri Mom Arif, wallahi bansan reshe zai juye da mujiya baā.
Cike da tsiwa Mom Arif tace;
āKinga malama, don Allah ki rufemin bakinki, wallahi Mom Eshmal Allah ya isa tsakanina dake, nayi dana sanin saninki a rayuwata, haka kawai ina zamana kin ja anmin dukan da tunda Nenne ta haifeni baāa tabāa min irinshi baā.
āNa yarda kice duk abinda zaki ce, amma ina so kiyi hakāuri Mom Arifā.
Wani kallo Mom Arif ta watsa mata kana taja dogon tsaki tayi gaba abinta.
Saimah kuwa wurin Kuzeem ta nufa, tsaye ta tarar da ita gaban mirrow hannuwanta rungume a kāirjinta, stool taja tare da zaunawa tana kallonta tace;
āKuzeem na san wannan ba halinki ba ne, son ganin mutum ya wulakāanta ya tozarta, wallahi baiwar Allah nan ta bani tausayi, don girman Allah ki rufa mata asiri kinji?ā.
Banza Kuzeem tayi da ita tamkar bata ji abinda take fadāa ba, hakan yasa Saimah ta marairaice ta cigaba da fadāin,
āDan Allah zakiyi Kuzeem, ba don halinta baā.
āNajiā.
Kuzeem ta fadāa can kāasan makāoshi, murmushi Saimah tayi tace;
āYauwa āyar lelen Abbaā.
Hakan yasa Kuzeem tayi wani murmushi ba tare da ta shirya ba, wanda yayi sanadiyar lotsawar dimples dāinta, kana ta juyo ta kalli Saimah tace;
āAmma fa idan yarinyar takāi amincewa da cigaba da zama a wurinta, wallahi bazan mata dole baā.
āNa yarda, ina zuwaā.
Inji Saimah tana murmushi, sannan ta mikāe ta fice daga dāakin ta koma wurin Binta, hannuwanta ta rikāe tace;
āBinta kin yarda da Kuzeem?ā.
Cikin sauri ta gyada kanta alamar eh, Saimah na cigaba da murmushi tace;
āTou tace in rarrasheki ki koma wurin Auntynki, bazata sake cutar dake ba, kuma Kuzeem tace bata so kikāi amincewa, nima dai bazanso ki kāi amincewa ba, kinga dai Auntynki harda kuka tayi kuma tayi nadama, ko baki yarda da tayi nadamar ba?ā.
Binta na kāokāarin magana idanuwanta suka sauka kan Kuzeem dake tsaye a bayan Saimah. Dāan tabāe baki Kuzeem tayi tare da barin wurin ta nufi wurin manyan bags dāin da ke ajiye palorn ta fara budāewa, domin duba siyayyar da tayi.
āNa yardaā.
Binta ta fadāa tana murmushi. Rungumeta Saimah tayi tace;
āTou kin amince zaki koma wurinta?ā.
āEhā.
āYawwa kāanwata ina ji dakeā.
Kāyalkāyalewa sukayi da dariya, sannan Saimah ta mikāe ta nufi wurin Kuzeem suka cigaba da duba kayan a tare, kayan sawa ne tsadaddu kuma hadāaddāun gaske, saidai Abaya da dogayen riguna sunfi yawa, saboda Kuzeem tafi son yin shigarsu, sai kananan kaya, da su mayukkan shafa, turarukka, takalmi, jikkuna, da dai sauransu. Kayane masu yawan gaske wadāanda a kāalla har ta bar RADDAL bata gama sanyasu ba. Sai bayan sun gama duba kayan ne, Saimah tayi serving dāinsu abincin suka fara ci a tare.
******
āWai Abokina lafiyar ka lau kuwa?, tun jiya na rasa gane kanka, ga baki dāaya ka sauya kamar wani abu na damunkaā.
Hisham ya fadāa yana kallon Miswar dake zaune bayan boot dāin wata mota dake cikin garejin nasu. Wata nannauyar ajiyar zuciya Miswar ya sauke tare da furzar da wata iska daga bakin shi, kana yace;
āHisham bazaka fahimce ni baā.
āKamar ya bazan fahimce ka ba?, nidai ka fadāamin miye damuwar?, ka san dai tun lokacin kāurciya bama bāoyewa junan mu komai, so banga dalilin da zaisa kazo ka sanja muna tsarinmu a yanzu baā.
Ya kāarashe maganar shima yana hawa boot dāin. Dāaga kai Miswar yayi yana kallon sama tare da sakin wani murmushi, hakan yasa Hisham ya bisa da kallo baki sake.
āWannan yarinyar!ā.
Miswar ya fadāa a hankali, yana lumshe idanuwansa. Cike da mamaki Hisham yace;
āYarinya?, wace yarinyar kenan?ā.
āMiye na tambaya Hisham?, bayan kasan wacce nake nufiā.
āAu wai kana magana ne akan yarinyar jiya?, hege ashe kaima ka ganta?, shine ka wani rufe idanuwaā.
Inji Hisham yana bāalle murfin robar ruwan swan da ke hannunsa.
āIna kāaunarta!ā.
Ai Hisham da ya kai gorar ruwa a bakinshi baisan sanda ya ciro gorar ba tare da furzar da ruwan da ya zukāa yana zaro idanuwa waje yace;
āKamar banji da kyau ba Abokinaā.
Kāyalkāyalewa da dariya Miswar yayi wacce tayi sanadiyar bayyanar fararen hakāoransa masu dāauke da wata siririyar wushirya a tsakiyarsu, wacce tayi balaāin masa kyau. Lallausan sajen shi ya shafa yana tsagaita dariyar da yake yace;
āTou duk lokacin da ka shirya ji dakyau sai kazo in sake maimaita makaā.
Shima Hisham dariyar yayi yace;
āWallahi ka bani wata amaryar dariya, yanzu kai don Allah bakaji nauyin fadāin wannan kalmar ba?, ka kuwa yima yarinyar nan kallon tsaf?. Hmmm! Abokina tun wuri ina me baka shawarar kayi gaugawar yakice soyayyar wannan yarinyar a cikin zuciyarka, don kuwa tafi kāarfinka nesa ba kusa ba, kai da ganinta kasan ita dāin matar manya ceā.
Sauka Misawar yayi daga kan motar, sannan ya rungume hannuwansa a faffadāan kāirjinsa yace;
āGa dukkan alama baka san miye asalin so ba Hisham, kawai dai kana yin shi ne kara zube. Tou ina so kasan shi so na gaskiya babu ruwanshi da kyau, nasaba, mulki, kudāi ko chanchanta, muddin tana sona bazata tabāa kallon rashin dacewar mu ba. Wallahi tinda nake a rayuwata ban tabāa jin ina son abu ba kamar yanda nake mugun mahaukacin son wannan yarinyar ba, ina jin wani babban alāamari a tattare da ita wanda na kasa gano miye maāanarsa. Hisham koda zata kāini to ni bazan tabāa daina so da kāaunarta ba har kāarshen rayuwata, domin kuwa soyayyarta a cikin jinina take yawoā.
Kai Hisham ya girgiza cike da mugun mamakin abokin nashi, yasan waye Miswar tun kafin su kawo haka, babu ruwanshi da harakar mata balle har yayi soyayya da su, akwai kyawawan mata dake sonshi har dāiyan masu fadāa a ji amma bai tabāa kulasu ba balle har yayi soyayya da su, sai gashi yau shi da kanshi yake furta kalmar so ga wacce batama san da wanzuwar shi a cikin duniyar ba.
āLallai abokina kayi nisa baka jin kira, to Allah ya tabbatar da alkhairiā.
Inji Hisham yana rikāe habāa.
āAmeen Abokina, kaidai kawai ka zuba ido kayi kallo zaka sha mamakiā.
*****
*_F.C.T FUNADE_*
āMaganar gaskiya Sir Kuzeem tayi fushi mai tsanani, ya kamata a bata hakāuriā.
Cewar wani mutum yana kallon B.G Atiku Tanko, wani murmushi yayi yace;
āNa rasa gane meyasa Kuzeem take da saurin dāaukar zafi tamkar nine na haifeta, yanzu miye mafita?ā.
Dariya L.G Aliyu Iko dake gefensa yayi yace;
āZan kira Kuzeem dāin anjimaā.
Wani uban burki Major Khalil dake kāokāarin shiga Office dāin na B.G Atiku Tanko yaja, tare da janye hannunshi daga jikin handle dāin kāofar, a hankali ya furta,
āKamar naji an ambaci sunan Kuzeem?ā.
Jin alamar zaāa budāo kāofar office dāin ya sanyashi saurin barin wurin yana maimaita sunan Kuzeem a ransa.
********
āWannan wanne irin shirmen banza ne?, taya zaku bari ta shammace ku?, na san halin Fatima kamar yinwar cikina da, ga dukkan alama kunyi sakacin da har ta gano kuna bibiyarta saisa ta sanja takuā.
Inji Abba da ke tsaye a tsakiyar palornshi, wayarshi kare a kunne alamar waya ce yake, dāan shiru yayi yana sauraron su Rabson kana yace;
āZan baku dama ta kāarshe, da zaran kunyi sake da ita shikenan kwangilar ta wuce kuā.
Yana gama fadāin haka ya ciro wayar daga kunnenshi tare da katse kiran.
āAlhaji me kake shirin yi ne?ā.
Ammah ta tambaya, don tun dāazun take tsaye a palorn tana sauraren wayar da yake ba tare da ya sani ba. Saurin juyowa yayi ya kalleta, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace;
āHafsa wannan bai shafe ki baā.
āBan gane bai shafeni ba Alhajiā.
āKamar yanda kika ji na fadāa miki ba!ā.
Abba na gama fadāin haka ya nufi hanyar bedroom dāinsa ya bar ta nan tsaye, girgiza kai Ammah tayi tare da furta,
āAi idan kasan wata baka san wata baā.
Daga haka ta juya ta fice daga dāakin tana danna wayarta, har ta lalubo number Kuzeem.✍️
#Anup💋āøā¶ ā¹ā°