YAR MAKIYAYA
CHAPTER 14
Abdul-malik , da nayi shiru ina zaton Wannan fad’an na tsakanin d’a da mahaifi zai wuce, tun yaron nan bai kai haka ba kuke wannan halin dalilin haka na saka shi dole ya biyo ka zuwa Belel living duk abokan sa da wasu muhimman abubuwa na rayuwar shi saboda a rayuwar shi kai kafi komai muhimmanci, amma Baku kwana biyu ba Suraj ya kirani saboda wannan halin naka, Nazo nan nima kasan ba don son zuwan nake ba amma sedai don inga na k’ara had’a kan ka da d’an ka amma maimakon abun ya ragu se yazo yafi na da far more than da. Yau ta kai ta kawo ga har zaka iya yi ma d’an ka illah da har zai kwantar da shi, jiya seda likita ya zo yau kam gashi chan ban san yadda zata kasance ba. Dan Allah Abdul-malik ka taimaka ka zauna da Suraj ko da Sau d’aya figure out your individual differences, your likes and dislikes sannan come up with a solution that will bind you together as one, but kafin nan ina so ka sani zan koma Egypt in kuka daidaita kan ku sannan ka cire wannan ak’idar taka na k’iyayyar d’an talaka kuma ka fahimci muhimmancin soyayya se in dawo, in har na zauna a nan tabbas tunani kad’ai zai kashe ni”. +
Tana kai nan ta juya ta fice daga d’akin Dad yabi bayan ta gami da rik’o hannun ta chak ta tsaya ba tare da juyo wa ba
“Ki saurare ni! Ban yi haka don saboda bana son Suraj ba ,kar ki manta nima da kamar Suraj ban k’i jinin talaka ba,but after what happened to my best friend wanda ya zab’i ya zauna da y’ar talaka naji na tsani talauci, da talaka ,ba se na baki labari ba a idon ki komai ya faru”
Wani Murmushi Mom tayi ta zame hannun ta daga rik’on da Dad yayi mata ta juyo tace
“Mesa kake k’ok’arin chanja topic? Ba maganar da muke ba kenan , talauci da arzik’i Allah ke bada shi ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so don haka in ka duba ko yatsun hannun mu ba daidai suke ba , ta haka ya kamata ka kalli rayuwa, ni ban ga laifin d’ana Suraj ba ,don ya daki Saeed wannan ya tabbatar min da cewa duk rintsi bazai bar wani abu ya tab’a matar sa ba, wannan shi ake k’ira kariya kuma ko gobe Saeed ya aikata abinda yayi ina goyon bayan Suraj hundred percent for ya nuna min shi namiji ne wanda zai iya yak’ar duniya akan abunda yake k’auna wannan kuma shine banbancin ka da shi ,am sorry to say sannan har yanzu ina nan a kan baka ta , Egypt kamar na koma”
Tana gama magana ta juya zata tafi a take tayi turus
Ummi , Habeeb ,Sapna, duk suna tsaye daga gani sun ji komai shikam Habeeb ya kasa danne zuciyar sa , fice wa yayi yana hawaye mom ta Kwankwasa k’ofar Suraj Laila ta taso ta bud’e k’ofar
Jiki a sanyaye ta shige ta nemi wajen zama gefen gadon ta kalle shi diga sama har k’asa yanda yake bacci ,sosai ta tausaya wa halin da ya shiga ,kanshi ta shafa ba tare da ta ce komai ba ta mik’e ta nufi inda Laila take tsaye
“Na sani cewa ke kanki kina cikin takura y’a ta, ina mai k’ara baki hak’uri, Mun d’auke ki daga duniyar ki mai cike da k’auna da kwanciyar hankali Mun kawo ki duniyar da Ke cike da tsananin tashin hankali da firgici, amma ina so ki sani Suraj d’ina na daban ne, ya banbanta da su kada ki guje shi dan Allah, shi kad’ai na mallaka ki kula min da shi y’a ta”
Kai kawai Laila ke girgiza wa kafin ta ce “in Allah ya yarda zan kula da shi ” Murmushi Mom tayi ta sumbace ta a goshi tace “na gode y’ata, Allah ya muku Albarka” Laila ta amsa da Ameen yayinda Mom ta fice daga d’akin, ko da ta fito inda ta bar Dad nan ta iske shi tsaye ta wuce ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi sashen ta dake downstairs……
Da sauri yake tafiya daga gani hankalin sa a d’age yake ainun , sashen mai Martaba ya nufa , masu tsaron wajen suka k’i bud’e k’ofa wai Sarki bai fita ba tukunna. Hankad’a su Habeeb yayi ya kutsa kai ciki babu kowa a babban falo dan haka ya haura staircase zuwa wani falon da Maimartaba ke huta wa.
Tsaye yake ya fuskanci window hannayen sa nad’e a bayan sa ya d’aga kai sama , da sallama Habeeb ya shigo ko gaisuwa bai iya yayi ba ya fara magana
“Wani abu yana faruwa ! Na kasa rik’e wa zuciya na ya kasa, ban sani ba ko nayi daidai amma nidai a gani na ya kamata na fad’a maka”
“Duk abunda yake faruwa ina sane da shi Habeebullah! Ina jira ne inga mai hankali da zurfin tunanin da zai yi k’ok’arin zuwa ya sanar da ni, babu abunda yake boyayye a gare ni “
Cewar mai martaba wanda a yanzu ya juyo kuma ya zo daf da Habeeb ya d’ago shi gami da rik’e hannun shi suka fita tare , ranar duk ya ajiye zancen sarauta gefe da k’afa ya taka har side d’in su Mom ya shiga ,duk inda yabi gaisuwa ake amma babu d’aya da ya amsa kana gani kasan ran shi a mugun b’ace yake shikam Habeeb jan shi kawai ake yi.
Zaro ido Uncle Ahmadu yayi lokacin da ya hangi mai martaba ya nufi sashen su Mom ,ba shiri shima ya taho ya nufi sashen.
Dad na hango shi ya rusuna zai yi gaisuwa mai martaba ya d’aga masa hannu cikin harshen fillanci yace “rik’e gaisuwar ka ! Bana buk’ata”. Habeeb ne ya kwankwasa k’ofa Laila dake takure k’asan gado ta mik’e ta ja mayafin ta sannan ta nufi k’ofar ta bud’e, wani ras! K’irjin ta ya buga domin ganin mai martaba da tayi, durk’ushe wa tayi ta gaida shi ,da kanshi ya d’ago ta yana shi mata Albarka kafin ya maida duban shi ga Suraj dake kwance helplessly yana bacci.
Dad da Unclee zasu shigo Ya dakatar da su ta hanyar d’aga musu hannu sannan yayi musu alama kan su bashi waje simi simi suka juya Unclee Ahmadu kuwa haushin sa yanzu laifin zai shafe shi ko Dad bai kula ba ya fice.
Tari Suraj ya fara yi nonstop wanda yasa ciwon ya fara jini da sauri Sarki ya dafe daidai ciwon ya dubi Habeeb yace “Habeebullah ! Ina so yanzun nan a shirya motoci ni da kaina nake son kai Suraj asibiti wannan babban al’amari ne yana buk’atar taimakon gaggawa , ka kuma k’ira likita yanzun nan!
Ba b’ata lokaci Suraj ya fice , bayan isowar likita da wasu nurses biyu sun bawa Suraj matakin farko na taimako domin numfashin sa ma seizing ya fara haka kawai ,sannan da sauri suka fito da shi zuwa cikin ambulance ,mai martaba bai buk’aci kowa ya bi shi ba banda Habeebullah babu wanda ya tafi tare da shi, Ummi kam kasa ko d’aga k’afa tayi tasan tabbas tunda mai martaba ya shiga lamarin se ran kowa ya b’aci.
Haka suka tafi in convoy motocin security a gaba guda biyu se ambulance sannan motar Sarki tare da Habeeb se wasu guda biyu a baya.
“Ki saurare ni Razia don Allah kar ki tafi”
Ummi ta fad’a tana hawaye
Tafiya ta zama dole ,koma ba komai zan tafi dan in samu relief kad’an domin na gaji da ganin wannan yak’in da ba na k’are ba.”
Tana kai nan ta shafa fuskar Sapna tace “kema ya kamata ki koma d’akin ki , ai bikin ya k’are ko?”
Kai Sapna ta girgiza gami da hugging Mom tana kuka.
Mom ta fice Fati na d’auke da jakar ta su Ummi suka raka ta don babu yadda zasu yi bazasu iya hana ta ba.
Laila kuwa inda suka barta a d’akin nan ta takure tana kuka duk ita tana gani laifin ta ne domin komai ya faru ne dalilin auren ta…I hope now that Dad has nothing left , zai fahimci muhimmancin ahalin sa, wanne hali Suraj yake ciki? Laila fa?….. +
Sapna ita ta d’ebe wa Laila kewa ita ma Washegari tayi mata sallama Cewar zata tafi, Ummi ma dole ne ta koma amma bata son ta tafi ba tare da Uncle Rasheed ya ga Laila ba , amma se aka samu akasi Uncle Rasheed ya tafi tare da Sapna, Ummi ta damk’a wa Fati kula da duk bukatun Laila sannan tayi mata sallama bayan tatafi Laila ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba domin fir tak’i zama a gidan Cewar ta “Saeed zai iya komo wa kuma wannan karon babu Suraj da zai kare ta saboda haka ta matsa wa Fati kan ita gida kawai zata je dan tsoro take .
Fati bata da zab’i illah tayi abunda Laila ta fad’a mata , in just 48 hours entire gida ya ruguje kuma wanda yayi silar faruwar hakan yana chan d’akin sa yana sharholiyar sa.
Ameer kenan! Ba damuwar sa bane to give someone pain!
Saeed kuwa tun da ya sha na jaki a hannun Suraj wutar k’iyayya ta ruru a zuciyar shi, ya sha Alwashin koma me zai faru sai ya tabbatar ko labarin Suraj da Laila ba’a sake yi ba a Belel.
Suraj kuwa tun kawo shi asibitin se yau bayan sati guda ya farfad’o ya dawo hankalin shi.
Mai martaba kuma ya sha Alwashin cewa until Suraj bai dawo hayyacin sa ba ya soke wa kansa komawa kan duty a matsayin sa na sarkin Belel, yana nan a babban gidan sa dake Abuja yayinda Suraj ke d’aya daga cikin manyan asibitin na birnin tarayya, se kuma Habeeb da yake tare da mai martaba.
“Habeeb! Ina Laila ? Me yasa ban ga Mom ba? ” Suraj ya tambaya yana k’ok’arin d’ago wa daga gadon da yake kwance.
“Relax Suraj ! Laila lafiyar ta kalau kullum se ta k’ira she misses you”.
Murmushi Suraj yayi yace “suna tare da Mom ne? K’ira min Mom please”
Shiru Habeeb yayi yana k’ok’arin diverting hirar , Suraj ya fahimci akwai abunda yake b’oye wa dan haka yay Murmushi yace
“Daman na sani! I knew it, yanda naga mom ta fusata nasan wannan hukuncin zata yanke, I just wish ta samu kwanciyar hankalin da take buk’ata a chan , Habeeb tell me waye a wajen Laila? Saeed yana chan ,ga Ameer it’s risky ace an bar min mata a hannun su.
Daidai lokacin mai Martaba ya shigo
“Wa ya fad’a maka tana wajen su? Yanzu haka matar ka tana nan birnin tarayya jiya na sa aka kawo ta, saboda haka ka kwantar da hankalin ka, gida dake Maitama district naka ne halak malak je ka zauna da matar ka ku zauna lafiya ,likita zai sallame ka yau ni zan koma Adamawa Allah ya albarkaci rayuwar ku ya kuma kare ku daga duk wani sharrin mai sharri ” duk Habeeb da Suraj suka Amsa da Ameen yayinda Suraj ya mik’e ya rungume mai martaba cike da murna kafin suka yi sallama ya tafi…
K’arfe Tara na dare suka shigo harabar gidan , Habeeb ke tuk’i Suraj na zaune gefe se trying wayar Mom yake ta layin ta na Cairo amma sam bata d’aga wa duk ya shiga damuwa. Habeeb na parking Suraj ya fito ya nufi main entrance na gidan, tun daga k’ofa ma’aikatan gidan suka tarbe shi gami da kwasar gaisuwa, mata biyu ne d’ayar dattijuwa ce d’ayar kuwa bazaka k’irata yarinya ba Amma ba tsohuwa bace , amsa gaisuwar yayi da sakin fuska ya bi gidan da kallo sannan ya haura stairs Habeeb kuwa ya zube kan kujera ya Furzar da iska yana shafa ciki
“Umma Hauwa akwai abinci de ko? Dan yunwa nake ji a hannu nake yau d’in nan?”
Dattijuwar ta amsa da “eh abinci kam akwai shi, da nayi zaton zaka jira d’an uwan naka shi yasa ban maka magana ba dama madam ma tun abincin safe bata ci komai ba”.
Wani shu’umin Murmushi Habeeb yayi yace “Tab! Wad’annan ki mance da su Umma Hauwa ki bani abinci kawai in ci domin wannan da kika gani in basu kashe junan su da soyayya ba babu abunda zai sa su fito”.
Dariya kawai tayi ta nufi dining table ta fara zuba masa abincin yayinda ya k’arisa ya ja kujera ya zauna ya fara aika loma ba k’akk’auta wa se zuba yake kamar mazari Umma Hauwa tana dariya…A hankali ya tura k’ofar d’akin wanda daman chan ba a rufe yake ba ,da Murmushi ya shigo ganin yadda take kokawar taje gashin kan ta wanda ya chakume baki d’aya, k’arisa wa yayi ta bayan ta ya karb’a comb d’in ya kama gashin yana k’ok’arin taje wa.
Baki ta hangame gami da zaro ido bai ankara ba yaji ta a jikin shi har suna k’ok’arin fad’uwa k’asa , dariya kawai yake yi ya kasa daidaita tsayuwar sa gudun kar su zube k’asa yayi saurin jingina da wardrobe ya ce
“Y’ar fullo irin wannan tarba haka? ” da sauri ta sake shi ta rufe fuskar ta da tafin hannuwan ta tana dariya
“Wai kunya! Kar ki damu I’ll son get rid of it” kallon sa tayi fuska a had’e tace “me hakan yake nufi? Ni kana min hausa da nafi gane wa se kayi ta turance ni ba ji nake ba” dariya ta bashi yace
“Nan gaba zaki fahimta kedai kizo muci abinci dan yunwa nike ji zaunar da shi tayi tace “kai da baka da lafiya ka bari na kawo mana abincin”
“Kinga kiyi zaman ki ni zan kawo mana, yau aiki na ne , ki ci amarcin ki yadda kike so ” ya mik’e sannan ya zaunar ta a inda ya tashin ya fita.
Habeeb na kallon shi ya sauk’o yana Hararar shi bai ce k’ala ba ya fice inda sukayi parking mota, Leda ya d’auko cike ya shigo falon ya sake watsa wa Habeeb harara kafin ya k’arasa inda Habeeb d’in ke zaune yana ta harba loma. Plate ya d’auka da glass cups biyu ya juya zai tafi
“Ahhh haba mana malam! Toh ni baza a bani nawa Kazan ba? Naga de harda ni aka siya ko kuwa so kake kace nayi dakon banza?”
Wani harara Suraj ya sake aika wa Habeeb kafin yace
“Tab! Ai baka isa ba wallahy gwamnati ta hana aikin banza! Wannan kazar kwalelen ka k’arshen karewar ta ma in Allah yasa Mun ci Mun rage ,in Mun rage kenan fa Toh sedai kaga mage tana ci da safe ba de kai ba, lazy man”!!
“Mage fa kace ? Kana nufin kulya , cat?? Yanzu har y’ar mage ta fini daraja don kayi Amarya? Habeeb ya tambaya fuska a dak’ile.
Dariya Suraj ya sa harda zube wa kan kujera yace “You should see your face! Amma d’azu da nace ka d’auko k’i kayi, kace bazaka yi dako wa Y’ar k’auye ba Toh me zaka yi da kazar y’ar k’auye?”
Marairaice wa Habeeb yayi yace ” kaga dan Allah yi hak’uri kaga de na tabbata akwai nawa a ciki kuma kasan yadda nake da kaza dajajatun ni da ita ba wasa in Kana wa Allah ka bani nawa in tafi d’aki da aba ta kaga kana chan kana soyewar ka nima ina chan ina nawa
“Soyayya da kaza?” Suraj ya tambaya yana zare ido yayinda Habeeb ya dake yace Kwarai ma kuwa” kai Suraj ya girgiza kafin ya Ciro Kazan ya bashi sannan ya tafi yana dariya.
Habeeb kuwa ya samu dattijuwa Umma Hauwa nan suka share fagen hira sai labarin k’auye take bashi shi kuwa dariya kamar yayi ciwon ciki.
******* ***** ****
Yana shigo wa suka had’a ido ta sauk’ar masa da the most exclusive Murmushi wanda yasa ya jingina da k’ofa , ba tare da ya d’aga murya ba yace
“You are killing this lover Prince y’ar fullo” k’arasa wa yayi kan resting lounge d’in ya zauna gefen ta sannan ya ajiye abun hannun shi kan side stool ya zuba mata ido.
Wasa kawai take da yatsun hannun ta don duk tana jin a jikin ta yana kallon ta gaba d’aya ta rasa sukuni.
Hannun ya rik’e hakan yasa ta d’ago tana kallon shi.
“Ina ganin Mun manta da wani abu guda, daga k’arshe de Allah ya nufa duk da abubuwan da suka dinga faruwa a kai a kai gashi Mun kasance tare ya kamata muyi alwala muyi sallah raka’a biyu don nuna Godiyar mu ga Allah wanda cikin ikon sa ne muke tare a wannan dare”
Kai ta girgiza tana Murmushi ya mik’e ya nufi hanyar washroom.
Bayan sun idar da sallah sannan kowa ya cika mak’oshin shi Suraj ya tattare ya fita, kan resting lounge ta koma tayi zaune har ya dawo bata sani ba saida hasken d’akin ya d’auke se wani dim light da bai haska d’akin gaba d’aya ba , mik’e wa tayi a d’an tsorace tana juya wa ya d’auke ta chak taji an raba ta da k’asa. A tsorace ta yi wrapping hannuwan ta around wuyan shi ,bai dire ta ko ina ba se kan gado yayi mata rumfa da faffad’an k’irjin shi yayinda ta k’ank’ame idanuwa tana jin zazzafan numfashin sa a kan fuskar ta.
*Na dad’e ina muradin tab’a wannan kyakkyawan fuskar, ina muradin na sumbaci wad’annan kyawawan lab’b’an,Sannan in ji d’umin jikin ki y’ar fullo nah, tsawon lokaci na dad’e ina muradin ki kasance tare da ni,*
Ya fad’a yana shafa fuskar ta har lokacin idanuwan Laila rufe suke……. .
What a night to remember, Suraj da Laila were together for the first time after their wedding a remarkable night for the couple ,thanks to mai martaba don da suna chan Belel da har yanzu bai samu lokacin y’ar fullo ba