YAR MAKIYAYA CHAPTER 17

YAR MAKIYAYA CHAPTER 17 




 Dare yayi saboda haka Habeeb ya koma chan gida tare da umma Hauwa ya bar Suraj tare da Layla, ko da suka iso gida shigowar su living room duk suka yi turus ganin Mom da Dad zaune, as usual Dad yana zaune k’afa d’aya kan d’aya yana kallon news yayinda mom ke zaune tana danna waya. A tare suka d’ago suka aza idanuwan su kan Habeeb ita kuwa Umma Hauwa gaisuwa ta kwasa tayi ciki, shima Habeeb d’in k’arisa wa yayi inda suke ya gaida su cikin ladabi da rusuna wa kuma cikin sakin fuska suka amsa kafin Dad ya cire glass d’in shi yace “Habeeb my son whare is Suraj Ko ba tare kuka fita ba? Tun d’azu muka iso har dare yayi babu kowa sauran ma’aikatan ma basu san da fitan ku ba”. Habeeb cike da mamaki yace “daman bai sanar da ku ba? Amma naji Kamar d’azu yana waya da ke Mom”. Kai mom ta jinjina kafin tace “Bai fad’i komai ba kawai mun yi da shi a kan muna hanya, me yafaru Habeeb akwai wani abu ne?” Ta tambaya tana mai ajiye wayar ta a kan side table. “Mom abun da ya faru shine d’azu ina tare da Suraj Saeed ya zo har gida don ya ci zarafin Layla the thing is Layla ta razana sosai she was in a state of shock shiyasa suka bata bed rest saboda zai iya cutar da ita da d’an cikin ta kuma……” “Layla is pregnant?!!……. How is she now? Ina fatan babu abunda ya sameta? Bai chutar da ita ba dai ko, Habeeb answer me!!” Mom ta fad’a cikin firgici tun bata gama jin me Habeeb yake fad’a ba. “Relax Mom, Lafiyar ta k’alau kuma in shaa Allah da safe zasu dawo Kar ki damu already kin sha gajiyar hanya so kije ki huta mom” Habeeb ya k’ark’are maganar yana kallon Dad wanda ko girgiza bai yi ba da jin maganar hasali ma wayar sa ya d’auka yana k’ok’arin k’iran wata lamba. “Abdoul-malik ! Baka ji abun da yake faruwa bane? Layla has been hospitalised, that too saboda Saeed amma it seems babu abunda ya dame ka”. Mom ta fad’a tana kallon shi. Ba tare da ya d’ago kai ba Dad yace “And hooow is that supposed to be my problem? Eh? Kinga Razia! Don Layla ta ji ciwo ko bata da lafiya so kike in manna a billboard kowa ya sani? I mean to say kin san cewa ni babu hannu na a had’in auren nan in ma me zai faru kin sani bazan yi accepting Layla ba a matsayin suruka ta, in da ace Suraj ne kwance zan shiga damuwa saboda haka pls mun riga mun gama wannan maganar tun a Egypt ki bani lokaci don nayi accepting Layla don har yanzu ban huce ba da k’aryar da kuka yi min! Dad yana kai nan ya mik’e ya fice daga falon ya nufi harabar gidan. Mom kuwa jiki a mace ta zauna kan kujera Habeeb ne ya fara kwantar mata da hankali daga bisani ta nufi upstairs zuwa d’akin ta shima Habeeb a gajiye haka ya kwanta har lokacin Dad yana chan waje. Washegari….. K’arar wayar Suraj ne ya sa ta farka daga nannauyan baccin da take yi, idanuwan ta suka sauk’a kan kujerar da yake kwance se sharar barci yake yi, da murmushi ta taso daga gadon nata zuwa inda yake kwance ta tab’a shi bai tashi ba ta saki murmushi ta zaune kan cikin shi tsabar firgita saida ya kusan jefar da ita k’asa, da sauri ya figo ta jikin shi yana dariya. “Barka da asubah ranki shi dad’e da fatan kin tashi lafiya Mrs. Suraj?” Ba tare da ta amsa shi ba ta rungume shi k’asa k’asa tace “don Allah mu tafi gida ni na gaji”. Zame jiki yayi a hankali ya dube ta kafin yace “Hmmm!… So yanzu kina so ki tafi gida kenan? Idan kuma ya dawo fa?” Ba tare da ta furta komai ba ta d’aga damtsen ta tana nuna mishi alamar k’arfi, hakan ba k’aramin dariya ya bashi ba, ya mik’e yana tattare kayan su ya dubeta yace “bari nayi magana da doctor don tun jiya yake son sallamar mu da dare nine nayi insisting saboda gudun kar wani matsala ya bijiro” kai ta jinjina ta koma ta zauna. Cikin mintina sha biyar ya kammala komai suka suka kama hanyar gida, kafin su isa gida saida suka dank’aro shopping sannan suka k’araso gida. Mom na zaune kan kujera tayi jugum se sak’e sak’e take yi. Tana d’ago kai suka yi ido hud’u da Suraj ba shiri ta mik’e shi ma cike da mamaki ya ajiye jakankunan shopping d’in ya k’araso inda take ya kwashi gaisuwa cike da mamakin ganin ta. Shigowar Layla ne ya sa ta saki murmushi kafin tace “Ohhh Masha Allah y’ata barka da zuwa, duk kun sa na shiga damuwa hankalina bai kwanta ba se yanzu da na ganki cikin k’oshin lafiya” Habeeb ya fito daga kitchen rik’e da tea mug tana dariya yace “Mom kenan ai daman na fad’a miki cewar all is well, gashi Layla ta dawo healthy and Sound”. Murmushi Mom tayi tace “You are right Habeeb”. Ta janyo Layla suka zauna kamar zata Had’iye ta shi kam Suraj tuni ya nufi d’akin su yayi wanka, da kyar Mom ta bar Layla ma ta tafi don ta yi freshening up kafin su ci breakfast……… K’arfe sha d’aya tukunna Layla ta sauk’o da ganin idanuwan ta daga barci ta tashi, Suraj, Habeeb da Mom suna ta hirar su Suka ji motsin tafiyar ta hakan yasa suka d’ago. Ganin yanda take tafe a kasalance yasa Mom tayi dariya gami da girgiza kai, Layla na k’araso wa ta zauna a k’asa ta nad’e k’afa shidai Suraj nashi ido se Murmushi da yake yi kamar zararre. Babu ko sallama ya shigo ya nemi waje ya zauna, Kowa ya gaida shi ya amsa, ko da Layla ta gaida shi bai ko kalli inda take ba se ma mik’ewa da yayi ya bar wajen, duk basu ji dad’i ba amma se suka basar , Suraj kuwa a fusace ya mik’e ya haura stairs ya bar falon saboda b’acin rai, Mom ce tayi wa Habeeb alama da yabi Suraj don yayi comforting d’in shi yayin da ta ja Layla suka nufi garden….. “Suraj pls calm down, don’t take this to heart! Kasan Halin Dad atleast yanzu har ya iya zama under the same roof da Layla, komai zai dawo daidai sannu a hankali” Habeeb ya fad’a yana kallon Suraj A fusace Suraj ya juyo yace “har se yaushe? Har sai yaushe kenan zai ajiye ego d’in shi da pride d’inshi ya yarda cewar Layla is now a part of his family? Kaga Habeeb! Da farko de ni ban ce dole se yazo gida na ba! Na biyu ban tursasa mishi ya yarda Layla surkar sa bace Habeeb for goodness sake me yake damun sa wai?” Murmushi Habeeb yayi yace ” Suraj let it be please komai yayi farko zai yi k’arshe, In shaa Allah zai wuce.” Kai Suraj ya jinjina yace “In Shaa Allah!”….. Kwanaki sun ja, zuwan Dad gidan ba k’aramin affecting Layla yayi ba, bata da walwala sam sedai Mom tana iya k’ok’arin ta na ganin Layla bata shiga halin damuwa ba, sannan duk wani girmama wa Layla tana ba ma Dad. Cikin dare Suraj ya kasa barci se juyi yake yana ta sak’e sak’en yanda zai yi Dad ya fahimci Layla ko da sau d’aya ne. Mik’e wa yayi ya fice daga d’akin Layla kam tayi nisa cikin barcin ta. K’ofar d’akin ya tura a hankali yana k’are ma Dad kallo. “Ahh Suraj my son!come on in, shigo mana ya kuma ka tsaya a kof’a?” Jiki babu kwari Suraj ya k’arisa bakin gado ya zauna yayin da Dad ke zaune kan resting couch yana ta rubuce rubuce. A lokaci guda Dad ya rufe duk abunda yake yi ya dawo kusa da Suraj ya zauna kafin ya duba agogon sa yaga k’arfe sha biyu ne na dare, jinjina kai yace “It’s late amma baka kwanta ba akwai damuwa ne?”. Murmushi Suraj yayi kafin yace “damuwa kam akwai shi Dad, kuma shi yasa na zo wajen ka saboda mu yi maganin damuwar gaba d’aya a wannan daren” zare gilashin sa yayi kafin yace “very well then! Ina jin ka Suraj fad’i damuwar” Suraj ya zame k’asa daga saman gadon ya d’aura hannuwan shi kan gwiwan Dad yace “koda sau d’aya Dad atleast once ina so kayi accepting Layla a matsayin suruka Dad in kayi hakan bazai rage ka da komai ba kuma Layla bata da wani aibu Dad for once give her a chance to be your daughter just once” Ya k’ark’are maganar yana kuka ya d’aura kan shi a cinyar Dad yaci gaba da kuka hakan ba k’aramin tada Hankalin Dad yayi ba don bai tab’a ganin Suraj a wannan Halin ba domin ko lokacin da ya fitar masa jini da majina ma Suraj bai shiga damuwa haka ba don haka ya d’aura hannun sa kan Suraj yana shafa wa kafin yace “Son, look dare yayi sosai yanzu ba lokacin wannan maganar bane dan haka kaje ka kwanta ” D’ago wa Suraj yayi ya dubi fuskar Dad kafin yace “Amma Daaad…….” Dakatar da shi Dad yayi da hannu “look Suraj i need to rest in bazaka damu ba pls leave we’ll talk about this issue later tomorrow” Suraj cikin b’acin rai ya mik’e ya fita yana banbami “daman nasani kawai ina wahalar da kai na ne i knew he will never change!”K’arfe goma masu aiki sun kammala had’a breakfast su mom suna dining kowa yana zaune se ga Suraj ya iso fuskar shi d’auke da fara’a kamar babu abunda ya faru tsakanin shi da Dad ,+ “Good morning!” ya fad’a yana k’ok’arin jan kujera “Morning” suka amsa cike da mamakin yanayin shi. Bai gama gyara zaman sa ba Dad ya d’ago kai yana kallon shi na y’an wasu dak’ik’ai kafin ya nisa yace “Son, where is my daughter? yau baza ta yi breakfast bane?” Duk a tare suka d’ago kai suka watsa ma Dad na mujiya baki a sake cike da mamakin kalaman sa, hasali ma Suraj ji yayi kamar ba daidai yaji maganar ba don haka ya ajiye chokalin hannun sa ya juya da kyau ya dubi Dad yace “Yooo. ……ur daughter….?” Kai Dad ya jinjina kafin ya ce “kwarai! My daughter Layla” Suraj ya dubi Mom da Habeeb su ma hakan suka yi kafin suka maida duban su ga Dad a tare Mom tana masa irin kallon nan na suspense Suraj ya kasa magana yaci gaba da kallon Dad. Mik’e wa Dad yayi yana murmushi ya d’auki plate ya zuba french fries da ketchup ya sa nutella a sliced bread sannan ya d’auki kofin shayin da Mom ta had’a zata sha duk ya d’aura a kan serving tray ya d’auka ya nufi upstairs ya kyale su a wajen, su duk suna tunanin zuwa zai yi yaci abincin a keb’e amma Dad d’akin Suraj ya nufa da wannan abincin. Suraj ya kasa cin abincin da ya zuba ya ce “Wow! Mom Dad is really up to something! Shi da ko jin motsin layla baya k’auna shine har yake tambayar ina take? This is unbelievable Mom!” Mom ta jinjina kai tace ina ga de Abdoul_malik ya kamu da Fever! Yes! Na tabbata zazzab’i ne ke damun shi, bari kuga zan je in duba shi ku kam kuyi breakfast d’in ku ina zuwa.” tana kai nan ta mik’e tayi upstairs zuwa d’akin su don duba Dad. Da sallama ya kwankwasa k’ofar d’akin tana zaune kan kujera ta yi jugum da ita taji k’arar bugun k’ofa don haka ta mik’e tana gyara mayafin kan ta kafin ta bud’e k’ofar, ganin Dad yasa k’irjin ta bugun tara tara babu shiri ta sunkuyar da kai cikin rusuna wa ta gaida shi ta matsa daga k’ofar. “Su…Sur..raj baya nan” ta fad’a cikin d’ari_d’ari har b’ari take yi don tasan yanda Dad ya ke kyarar ta saboda kasancewar ta talaka kuma y’ar Makiyaya. “Ba don Suraj na zo nan ba y’a ta, kowa ya fito karya wa amma baki fito ba shiyasa i wondered why, don haka na kawo miki abinci, ya kamata kici saboda lafiyar ki tafi mana komai”. Zaro idanuwa Layla tayi idanuwan ta kan fuskar Dad bakin ta yana b’ari ta kasa magana tana tunanin a mafarki ne hakan yake faruwa, daidai Lokacin Mom ma tana wajen cike da mamaki take kallon K’eyar Dad wanda bai san ma ta iso wajen ba, wajen zama ya nuna wa Layla babu musu ta zauna ya ajiye mata abincin fuskar sa cike da fara’a yace “yawwa! Kada ki sake zama ke kad’ai ki keb’e kanki ai nan gidan ki ne kina da damar yin komai, nasan ban tab’a nuna na damu da ke ba kuma nayi kuskure na kuma gane Layla Kowanne uba zai so wa d’an sa abu mafi inganci a rayuwa, haka ne ta kasance da ni Suraj d’a na ne sannan shi kad’ai na mallaka don haka na ke k’ok’arin ganin ya bi sahu na i just wanted the best for him amma ban sani ba cewa kawai ina lalata masa yanayin rayuwar sa ne,ni da ya kamata in zama muku role model nine na d’auki darasi………… kada na ja maganar da yawa Layla nazo nan ne in sanar da ke a karon farko cewa ina alfahari da ke kuma kamar yanda nake k’aunar Suraj haka zan k’aunace ki y’a ta, mu mance da abubuwan da suka faru ku cigaba da rayuwa cikin farin ciki, fata na Allah ya muku albarka.” Dad na k’ark’are maganar ya juya zai fita bai yi aune ba yaji an rungumo shi “Oh gosh Suraj me haka kuma?” ya fad’a yana daidaita tsayuwar sa “sassauta rik’on Suraj yayi kafin yace “thank you Dad! Today you have shown me real love a karon farko ka saurari kuka na Dad i promise I’ll never let you down”. Murmushi Dad yayi ba tare da furta ko kalma ba ya fice daga d’akin yayinda Suraj ya maida duban sa ga Mom wanda har lokacin ta kasa yin kwakkwaran motsi saboda mamaki Saida Dad ya koma d’akin sa sannan ta bi bayan shi STORY CONTINUES BELOW K’ofar ta tura a hankali tayi sallama Dad ya amsa da fara’a, kafin ta zauna ta matsa kusa da Dad ta d’aura bayan hannun ta a goshin sa ta d’aga kai kamar mai sauraron wani abu tace “No! You really don’t have fever! In baka zazzab’i kenan me yake faruwa? Domin na tabbata in lafiyar ka k’alau wannan abun da ka aikata yanzun nan da kalaman ka da ka furta ba haka zasu kasance ba” Murmushi Dad yayi a karo na biyu kafin yace “Raaaazia! Kinga ,nasan ban kyauta muku ba duka but tunda na riga na baku hak’uri please maganar ya wuce, i admit na yi laifi, you know Razia na rasa d’ana da farko amma yanzu bazan bari na rasa Suraj ba saboda son kai irin nawa please kema ki yafe min, right now bana buk’atar komai da ya wuce in ga y’ay’a na suna farin ciki.” Hawayen fuskar ta Mom ta share sannan tace “Alhamdulillah!! Abdoul_malik wannan shine abun da na d’ad’e ina muradi , ka saka ni farinciki sosai nagode” Kai Dad ya jinjina yace “Razia i know na aikata kuskure a baya, but now i promise you zan kasance mahaifi na gari kuma abun alfaharin Suraj” Murmushi Mom tayi kafin ta mik’e tace “Barin kawo maka breakfast naka tunda baka ci ba” kai kawai ya jinjina Mom ta fita zuciyar ta fal farin ciki… Cikin wannan satin Layla taga gata ba kad’an ba, Suraj kuwa kusancin sa da Dad ya fi na da don har ayyukan sa yake taya shi, Habeeb ya kammala abunda ya kawo shi har ya shirya koma wa yau haka ma su Mom sun shirya zasu tafi Belel, don haka suka shirya suka fita a tare zuwa Airport Suraj ne ke tuk’in motar yayinda Layla,Mom da Habeeb suke baya suna hira duk da de kalmomi d’add’aya Layla ke tsinta saboda kunya. AIRPORT.. Suraj ya dubi Mom yace “i can’t believe you are leaving too soon we will miss you”. Murmushi Mom tayi ta ce “Look look! If you guys miss me then give me a call se mu yi ta waya har se kun gaji besides ai a Belel muke zaku iya zuwa in condition na Layla gets better, Allah ya muku albarka” Nan suka yi sallama da Su Dad sannan suka koma wajen Habeeb shima suka yi sallama ya kama hanyar Kaduna…… ***** ***** ***** K’arfin ruwan sama ne yayi yawa hakan yasa Suraj ya ja motar sa yayi parking kafin ya juya ya dubi Layla dake barci hankalin ta kwance cikin motar, murmushi yayi ya juya yana dube dube ko zai ga wajen fake wa amma babu saboda haka ya koma ya kwanta jikin kujerar yana kallon yanda ruwan saman ke kwarara kamar da bakin kwarya se lokacin Layla ta motsa ta k’ura masa ido tana kallon sa shi kuwa bai ma san tana yi ba ya lumshe idanuwa, a zaton ta barci yake yi, yamutsa fuska tayi tana dube dube kafin ta hango kwalin biscuits a k’ofar side nashi yunwa take ji sosai don haka ta yunk’ura zuwa side d’in da yake tana ta k’ok’arin d’auka hannun ta bai kai ba, bata ma san Suraj ya bud’e idanuwan sa yana kallon ta ba hannun ta guda ta lank’ayo wuyan sa ta rungume amma duk da haka ta kasa d’aukan biscuit d’in don haka ta hak’ura ta koma seat d’in ta se lokacin ta lura Suraj ya zuba mata ido yana murmushi. Hannu yasa ya d’auko biscuit d’in ya mik’a mata yana ci gaba da murmushi gami da runtse idanuwa ita de kallon sa take yi kafin ta bud’e kwalin ta fara ci. Sun dad’e a wajen kafin ruwa ya tsaya Suraj ya tada mota suka nufi gida. Haka zaman su ya kasance cikin so da k’auna sannan ga girmama juna har tsawon watanni biyu cikin Layla watan sa Hud’u kenan kuma har ya bayyana babu irin gatan da Suraj baya nuna mata, ko wacce rana k’aunar su k’aruwa take yi. K’arfe bakwai na safe wayar Suraj tayi ringing yana kwance da kyar ya zame daga gado ya d’auki wayar amma kafin ya amsa har ta yanke Uncle Ahmad ne ya k’ira har wajen missed calls shida, mamaki da tsoro ne ya kama Suraj hannun shi na b’ari ya k’ira lambar Uncle Ahmad ya kara a kunne yayi sa’a a take ya d’aga amma Suraj ya kasa magana daga b’angaren sa balle ya amsa sallamar da Uncle Ahmad d’in yayi. “Suraj listen, na k’ira in sanar da kai cewa Mai martaba Allah ya karb’a abun sa ya rigamu gidan gaskiya earlier today”. “inna lillahi wa inna ilaihir_raajiuun sune kalaman da Suraj ke furta wa, ya zame k’asa yana kuka Hakan ne ya farkar da Layla daga barcin da take yi mai nauyi a firgice ta sauk’o ta zube gaban sa tana fad’in “na shiga uku! Me ya faru da kai?? Me yasa kake kuka” tana maganar cike da firgici ,gudun kar ta shiga wani hali Suraj ya janyo ta jikin sa yace “Shush! Ya isa haka, it’s ok, yi shiru please”.. Fisge jikin ta tayi gami da mak’e kafad’a tace “A’a! Ni ka fad’a min abunda ya same ka!” ganin ta matsa sosai Suraj ya sanar da ita cewa Mai martaba ne ya rasu, jin haka yasa jikin ta ya d’au b’ari tana addu’a ta rungume Suraj don ya d’an samu relief. “Layla, come on! Tashi mu shirya kafin lokaci ya k’ure barin sa ayi booking flight tickets ya kamata mu tafi” kai kawai Layla ta jinjina Suraj ya fice da sauri ,Layla ce tayi k’ok’arin had’a musu kayan su kafin ya dawo Umma hauwa ma ta shirya don haka suka d’auki hanyar Belel…………..Belel…..+ Sarakuna, y’an siyasa, attajirai daga wasu garurruwan hanyar da mota zata wuce ma se an dage, isowan su ke da wuya aka sallaci Mai martaba aka kai shi gidan sa na gaskiya, Suraj yayi jimamin rashin mutum mafi soyuwa a gareshi domin bai shak’u da Dad ba ma kamar yanda ya shak’u da Mai martaba kuma ko a wajen Sarki ma Suraj ne mafi soyuwan jika a gareshi, abun ka da sarauta tuni aka nad’a uncle Ahmad a matsayin Sarkin Belel da yake shi d’an gargajiya ne sai sarautar ta dace dashi. Kwanci tashi babu wuya ga mai rai, har kwana arba’in na Marigayi Sarkin Belel don haka aka taru a masallaci aka yi addu’o’i da sadaka abun se de ace masha Allah. Suraj na zaune kusa da Mai martaba Ahmad a masallaci bayan sun idar da sallah Uncle Ahmad ya dube shi yace “Suraj! In ka kammala komai ina so ka iske ni a living room d’ina, in so samu ne yanzu kana fita ka nufi chan kawai i will meet you there” Cike da rusuna wa Suraj ya amsa, bayan ya kammala addu’o’in sa ya mik’e ya nufi sashen Mai martaba Ahmadu kai tsaye…. ******* ******* ******** Da Sallama ya tura k’ofar babu shiri yayi turus saboda muryoyin da yaji sun yi gamayyah wajen amsa sallamar sa, gabad’aya family ne a wajen kama daga su Mom, Dad, habeeb,Ameer, Saeed,Layla,Ummin Habeeb, Sapna,Sarauniya Maryam da sauran su. A tsanake ya k’arisa ciki ya nemi wajen zama gefen Habeeb kamar yanda kowa ya zauna. Cikin takun k’asaita Mai martaba Ahmadu ya shigo tare da wasu mutane biyu duk sun sha suit hannuwan su rik’e da suitcase, bayan kowa ya zauna an nutsu Mai martaba ya gyara murya ya fara magana “Aaaaa!… Assalamu Alaikum”. Duk suka amsa masa sallamar sa sannan suks nutsu don jin me zai ce “i know you all must be wondering why i summoned you here at once, toh na k’ira ku nan ne domin ina so in sauk’e wa kai na nauyi tun kafin ya nakasa ni, kun san masu iya magana sun ce *da zafi zafi ake dukan k’arfe* saboda haka i will go straight to the point, akwai wasiyya da Marigayi mai martaba Sarki ya bari kuma yau watanni biyu kenan da ya bani wannan will d’in sannan a gaban wad’annan lawyers d’in aka yi komai, a wasiyyar da ya bari yace “Ranar da na kwana arba’in bana duniyar nan ina so ka tara dukkanin ahali na domin karanta musu wannan wasiyyar, duk abunda suka gani ko suka ji wannan ni nayi niyya kuma sannan kada wanin ku ya nuna cewa an fifita wani kan wani duk d’aya kuke a gare ni” Uncle Ahmad yana kai nan yaja ya tsaya yana k’are musu kallo d’aya bayan d’aya kafin yace “Lawyer please go ahead, zaka iya cigaba da karanto will d’in” Lawyer ya gyara murya ya bud’e suitcase ya ciro wasu files guda uku sannan yace “wad’annan files d’in suna d’auke da takardun Manyan Mansions d’in Marigayi dake garin Abuja d’aya a asokoro d’aya a Maitama district, sannan wannan kuma na Babban multimillionaire company d’in shi ne *Belel holdings* kuma duk ya sa hannu akai cewa ya mallaka wa Mr. Suraj Abdoul_Malik…..” Lawyer bai gama magana ba Suraj da Saeed a tare suka mik’e gami da had’e baki wajen cewa “WHAT??!!”. Hakan yasa kowa d’ago wa Suraj yaci gaba da cewa “oh no! No! No! Please sir ka duba da kyau you must be mistaken, besides bani kad’ai bane d’a a gidan nan ai” ya k’are maganar yana kallon Lawyern ido cikin ido. Saeed da ya kasa zama ya ce “Good! Ko kai ma zaka fad’a, after all ba kai kad’ai bane d’a” Bai ankara ba yaji sauk’ar mari a fuska har saida yaga wuta. “Saeed! Idan baka kiyaye ni ba zan koya maka darasi! Kai kuma Suraj abunda kaji shine gaskiya believe it or not documents d’in da sunan ka aka yi signing d’in su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *