YAR MAKIYAYA CHAPTER 18

YAR MAKIYAYA CHAPTER 18 

 Koma wa Suraj yayi ya zauna kafin Mai martaba ya dubi lawyer yace “cigaba pls”. Nan lawyer yayi gyaran murya yacigaba da bayani kamar yanda mai martaba ya rubuta a wasiyyar sa. Saeed na mallaka mishi gidaje na guda uku dake kaduna, sannan Ameer zai tashi da Mansion d’ina dake Yola had’a da babban gidan gona na dake abuja. Wannan dukiyar Marigayi mai martaba ya mallaka wa jikannin sa guda ukku Saeed,Suraj da kuma Ameer. Cewar Lawyer yana k’ok’arin had’a takardun domin sa hannun su. Saeed ne ya fara sa hannu rai a dak’ile ya fice babu ko girmama wa.Ameer kam ko nuna damuwa bai yi ba ya sa hannu a takardun ya koma ya zauna ya k’ura wa Suraj ido ganin ko motsawa bai yi ba har sai da Uncle Ahmad ya ce “Suraj my son what were you thinking? Ka yi signing takardun and take whats rightfully yours!” Jiki a sanyaye Suraj ya mik’e ya karb’i pen yayi signing duk papers d’in sannan ya zauna, daga nan lawyer yacigaba da rabon gado kamar yanda shariah ta tanada. ******* ******* ******* “Dad ni ban san ta inda zan fara ba! Farko yanayin rabon ya tsorata ni, grandpa ya d’auki dukiyar da ta ninka na su Ameer da saeed kusan sau biyar ya dank’a min, daga ganin yanayin su nasan cewa kawai k’iyayya ce zata k’ara shiga tsakanin mu, dad ban san yanda zan yi managing wannan babban company d’in ba, sannan……. “oh come on Suraj!”. Habeeb ya katse shi. “Let them do whatever they want! Mai martaba shi ya mallaka maka dukiyar nan kuma ai ya fi mu sanin kanmmu ma balle halin mu, who cares what they think? ” Dad ya jinjina kai ya dafa kafad’ar Suraj yace “Look son, Habeeb gaskiya yake fad’a maka, sannan kowannen su kowa yana da nashi share d’in kuma na tabbata Mahaifina bai aikata hakan don wai yafifita son ka bane a kan nasu he had his reasons so relax son” Kai Suraj ya jinjina kafin ya nufi d’akin shi Daidai lokacin ne Suka ji Sallama, duk suka amsa a tare fuska cike da fara’a Da k’asaitaccen taku ya shigo, duk su Mom suka mik’e, Ummin Habeeb tace “Finally yau ka cika alk’awari”. Murmushi yayi yace “ai dole na, tunda nayi alk’awarin zan zo”. Dad ya mik’a masa hannu suka gaisa kafin yace “Rasheed! Barka da zuwa! I must say ka sha hanya”. Kai Uncle Rasheed ya jinjina kafin yace “Gaskiya kam na sha hanya,amma tafiyar tayi amfani tunda na had’u da y’an uwa da abokai” duk suka sa dariya su Habeeb da Sapna suka gaida shi haka ma su Mom bayan nan yayi musu ta’aziyya. Dad d’in Habeeb wanda shi ya kasance d’an uwa kuma yaya ga Rasheed yaji dad’in ganin d’an uwan nashi domin kullum sedai su yi waya yana chan Newyork a chan yake da zama. Tare suke sauk’o wa daga bene Suraj se dariya yake da alama Layla ke bashi labarin barkwanci hakan yasa duk su Dad hankalin su ya koma kan Suraj da Layla. A hankali ya d’ago kai ya aza idanuwan sa kan fuskar Layla Saida k’irjin shi ya fara dukan tara tara, Uncle Rasheed bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba. Har suka k’ariso inda yake Suraj da Layla suka gaida shi amma bai amsa ba se hawaye dake gangaro wa daga idanuwan sa hakan yasa duk kowa dake wajen mik’e wa suna mamakin me ya samu Uncle Rasheed all of a sudden “Aaliyah!!!!” uncle Rasheed ya furta baki na b’ari kafin ya k’arisa daf da Layla sedai bai k’ara furta wata kalma ba illah iyaka kallo da yake zuba mata. Da murmushi Layla tace “Layla sunana, ba Aaliya ba, amma me yasa kake kuka?” Ko jin ta baya yi kawai ya zuba mata ido. Ummin Habeeb ce ta k’ariso inda yake tsaye ta dube shi sannan ta dubi Layla kafin tace “Finally yau kaga abunda na shafe watanni ina fad’a maka! In baka manta ba na sha baka labarin Layla in mun yi waya, amma Allah bai yi zaku had’u ba se yau. Kuma gashi cikin ikon Allah you also are shocked kamar yanda nima na girgiza a farkon gani na da Layla.” Dad da Abban Habeeb duk suka had’e baki wajen fad’in “wai me yake faruwa ne?” ” Can somebody just tell me whats going on here?” Dad ya sake tambaya ganin basu bada amsar tambayar farko ba. Ummi ta yi ajiyar zuci kafin tace “da zai fi kyau kowannen mu ya zauna tukunna don maganar ba ta tsaye bane. Babu musu kuwa kowanne ya samu waje ya zauna suka sa su ummi a gaba kowa na jiran jin dalilin da yasa Ummin Habeeb wad’annan maganganu.. ******* ****** ****** “Aaliyah ta kasance baturiya ce y’ar k’asar Birtaniya kuma sun had’u da Rasheed tun yana karatu a Oxford university, ta dalilin Rasheed ne Aaliyah ta musulunta, wanda hakan yayi sanadiyyar rabuwar ta da dangin ta duk da cewa sun kasance masu d’umbin dukiya, Rasheed da Aaliyah sun yi aure kafin ya taho da ita nan Nigeria. Duk abunda ke faruwa babu sanin ko da mutum d’aya daga cikin dangin Rasheed hakan ba k’aramin tayar da husuma yayi ba, a wannan lokacin Abban Habeeb baya k’asar nan yana chan wajen aikin sa a Egypt,Hajiya (mahaifiyar su Rasheed da Abban Habeeb) ta k’i amince wa da Aaliyah a matsayin surukar ta a haka de cikin tsangwama Aaliya ta shafe watanni biyar a gidan, lokacin cikin ta watanni biyu don haka Aaliyah ta buk’aci Rasheed da ya sauya mata gida ko ta koma london hakan ya tada masa hankali domin wannan na nufin ya rabu da gidan su da family kenan don haka yayi watsi da buk’atar ta ita kuma ta fara tattare kayan ta zata bar gidan se aka yi sa’a Abban Habeeb ya yi settling a chan Egypt ya ce ni da Hajiya mu je don haka muka tafi Egypt ni da Habeeb da Hajiya. Watanni bakwai Aaliya da Rasheed suka shafe cikin jin dad’i da k’aunar juna babu abunda Aaliyah ta rasa wajen Rasheed hankalin ta a kwance. Ranar da Aaliyah ta haihu a ranar Hajiya ta koma kaduna kuma a ranar ne aka nemi jaririyar da Aaliyah ta haifa aka rasa sama ko k’asa. Aaliyah kuma ta dage kan cewa Hajiya ita ta d’auke mata y’ar ta kuma, Hajiya kuma ta fashe da kukan makirci hakan yasa Rasheed ya runtse ido ya hau dokin zuciya yana wa Aaliya fad’a a kan ta yi wa mahaifiyar sa k’arya da sharri, hakan shine abinda Hajiya take so don haka taji sanyi a ran ta, duk da cewa Aaliya gaskiya take fad’a ,Rasheed bai yarda Hajiya zata aikata hakan ba don haka Aaliyah ta kwashi kayan ta ta bar gidan, ga ciwon rashin d’iyar ta a ranar da ta zo duniya,ga takaicin Rasheed da yak’i ya fahimci gaskiya. Haka Hajiya ta kwashe shekaru sha hud’u ba tare da ta fad’i gaskiyar abun da ya faru ba sai ranar da ciwon ajali ya kama ta, lokacin duk ta cika da nadamar abunda ta aikata wa d’an ta da Aaliyah a wannan lokacin ne ta fad’i gaskiyar abunda ya faru da jaririyar inda ta bayyana mana cewa wasu maza biyu ta ba wa jaririyar ta biya su mak’udan kud’i domin su yi nesa da ita inda ko k’amshin kaduna bazata ji ba. Haka kuma aka yi. Rasheed na jin wannan maganar ya hau dokin zuciya ya bar gida, ko da Hajiya ta rasu Rasheed da kyar na rarrashe shi ya zo jana’iza nan ma kwanaki uku yayi ya koma Newyork. Abban Habeeb a zaton sa Aiki ne yayi wa Rasheed yawa shiyasa baya zama a kaduna amma sam abin ba haka yake ba Rasheed ya buk’aci kar na sanar da d’an uwan sa abunda ya faru kuma ban fad’a ba se yau d’in nan shima don saboda Layla na fad’a.” Ummin Habeeb ta gyara zaman ta kafin ta cigaba da cewa “Tun farkon da naga Layla fuskar Aaliyah ta dawo min, babu abunda ya raba ta da Aaliyah tamkar an tsaga kara, sannan in aka yi la’akari da shekarun Layla da kuma lokacin da y’ar Rasheed ta b’ata shekaru goma sha takwas kenan such coincidence ba kullum yake faruwa ba”…. Mik’e wa Layla tayi cikin kid’ime wa tace “Aa! Zai yiwu shekarun mu d’aya amma ni a nan aka haife ni kuma baba na kiwo yake yi, a nan na girma kuma zai yiwu nayi kama da ita amma ni ba y’ar ta bane ni inna ta bata raye yanzu kuma ku tambayi Baba na ni y’ar sa ne”.+ Ganin rud’ewar Layla hakan ya sa Mom tace da Suraj ya kai Layla d’akin ta anjima zasu k’arisa magana hakan kuwa akayi Suraj ya tafi da Layla d’aki yana comforting d’in ta. A chan falon kuma Dad ya dubi Habeeb ya umarce shi da ya k’ira Baban Layla nan take Habeeb ya mik’e ya fita don aiwatar da aiken da aka yi masa. “This is going to be tough! Domin yanzu haka in har aka gane Layla y’ar Rasheed ne Baban ta kuma zai shiga damuwa saboda iya rayuwar sa babu abunda ya k’aunata irin Layla ita ce rayuwar sa kuma farin cikin sa, don haka Rasheed kafin kayi taking action kayi tunanin yanda action d’in ka zai yi affecting rayuwar Layla da baban ta. Wannan maganar Abban Habeeb ne yayi ta kafin ya mik’e rai a b’ace ya nufi masauk’in su, ganin yanayin shi yasa Ummin Habeeb ta bi bayan shi kusan a tare ma suka shiga d’aki. “Abban Habeeb, zai fi kyau kayi min bayanin dalilin b’acin ran ka domin a wannan lokacin we all need you with us me yasa ka dawo d’aki?” Cikin b’acin rai Abban Habeeb ya ce “No! Bakwa buk’atan mutum iri na! All those years umman Habeeb! Kun b’oye wannan babban al’amarin daga gareni! Watak’ila da kun sanar da ni, da yanzu Rasheed yana tare da iyalin sa cikin kwanciyar hankali, da bazan bari Hajiya ta aikata wannan kuskuren ba. Yanzu mu k’addara cewa Layla y’ar Rasheed ce, yaya kike tsammanin zata yi reacting? It’s going to affect her life! Tun bata san me duniya ke ciki ba har ta yi wayo tasan ciwon kanta, baban ta shine duniyar ta, farin cikin ta , abokin ta. Umman Habeeb ba zai yiwu karaf d’aya kawai out of nowhere wani ya shigo rayuwar ta yace shi mahaifinta ne ba, in ke ne ya zaki ji? How are you going to react? Wannan ne abunda ke damu na, bai kamata ace Rasheed ya b’oye wannan al’amarin bai sanar da ni ba I’m his brother damn it!!”. Ummin Habeeb bata iya furta komai ba domin ita kan ta tasan bai kamata tun farko iya wad’annan shekarun su b’oye al’amarin ba amma babu yanda zata yi. Habeeb ne ya shigo da sallamar sa, saida ya k’are musu kallo ganin babu wanda ya amsa sallamar sa se ya k’arisa gaban Abban shi yace “Baban Layla da d’an uwan sa su iso Uncle yace in sanar da kai”. Jinjina kai Abban Habeeb yayi sannan ya fice Habeeb na bin sa a baya har zuwa main parlour. Bayan sun gaisa kowa ya nutsu Aka k’ira Layla da Suraj ma duk wajen ya yi tsit na d’an wani lokaci kafin Abban Habeeb ya gyara murya sannan yace “Aaam…… Baban Layla… Abun da nake shirin fad’a maka watak’ila zai b’ata maka rai ko kuma yasa ka shiga rud’ani, amma ina so ka fahimce mu don Allah. Wannan maganar ta shafi Layla ne kuma al’amarin ba k’arami bane gaskiya.” Baban Layla kam tuni ya rud’e da yaji cewa maganar ta shafi Layla, cikin rud’ewa ya ce “Layla? Ta aikata muku wani laifin ko? Tayi wani abun ko? Don Allah kuyi hak’uri zan mata magana”. Murmushi Mom tayi kafin tace “A’a, Baban Layla, Babu abunda Layla tayi, yarinya mai hankali irin Layla babu wanda yake k’orafi a kanta maganar wata daban ce” Kai Baba ya jinjina sannan Abban Habeeb ya cigaba da magana inda ya kwashe duk labarin Rasheed ya basu sannan aka nuna musu hoton Aaliyah abun da yayi matuk’ar tada ma Baban Layla hankali ya mik’e rai a dak’ile yace “wannan maganar kawai almara ce da kuka had’a kuke so ku raba ni da d’iya ta Layla, duk duniya bani da kowa in ba ita ba, bazan yarda ku d’auke min y’ata daga gare ni ba nine kad’ai mahaifin ta!” Baban Layla yana kai nan ya fisge hannun Layla ya jata zai fita daga falon Suraj ya rik’o d’ayan hannun ta shima duk kowa ya mik’e ana bashi hak’uri Uncle Rasheed kuwa ya tafka tagumi ya had’a kai da gwiwa duk hayaniyar kawai ji yake amma bai san inda kansa yake ba. Mai martaba ne ya shigo, hakan yasa wajen yayi d’uf kamar ba kowa, a tare Suraj da Baban Layla suka sake hannun ta da suka rik’e Layla ta rungume Mom tana kuka. Komawa suka yi suka zauna kowa ya nutsu, Mai martaba ya tambayi menene matsalar duk Dad ya kwashe ya sanar da shi duk abunda ake ciki Kafin Mai martaba yayi magana Baban Junaidu yayi firgigit ya mik’e yace “Ranka shi dad’e ina da magana”. Jin D’an uwansa yayi magana ,baban Layla ya katse shi ta hanyar chafko hannun shi suka had’a ido amma da yake Baban Junaidu bashi da kirki se ya fisge hannun sa yace “Ranka shi dad’e Layla ba y’ar d’an uwa na bane kuma zan rantse a kan wannan”. Tsabar firgici Layla bata san lokacin da ta mik’e ba ta ruga wajen baban ta, hannun shi ta rik’e tana zabga kuka “Baba ka fad’a min ba gaskiya yake fad’a ba! Ni kai ne baba na ka fad’a mishi kar yayi k’arya, Kawu ka fad’a mishi gaskiya don Allah”. Haka ta dinga magiya ta kasa nutsuwa tana kai kawo tsakanin Baban ta da Baban Junaidu. “Baban Junaidu gaskiya ya fad’a” Wannan kalmar ita ta fito daga bakin Baban Layla ta doki kunnen Layla hakan yasa kowa ya mik’e yayinda Layla ta maida duban ta ga Baban nata idanuwan ta sharkaf da hawaye tana k’ok’arin tantace wa ko muryar sa taji ko kuma de mafarki ne Layla ba y’ar da na haifa bane”+ Layla bata san lokacin da ta zuba gwiwa a k’asa ba, ji tayi duniyar tayi mata d’aurin huhun goro kawai kallon baban nata take yi yayinda yaci gaba da magana ” na rik’e ta ne tamkar y’ar ciki na saboda a yanayin da na samu Layla ba ni ba wani ma zai yi abun da na aikata” Shekaru sha takwas da suka wuce mun je kiwo ni da Mai d’aki na cikin ikon Allah se nak’uda ta taso mata, don Haka se na ruga inda d’an uwa na Baban Junaidu yake kiwo na k’ira innan Junaidu, domin ta taimaka mata ni kuma na wuce bakin rafi domin na samo ruwa, a daidai wajen ne naji kukan jariri, lokacin yamma tayi da farko ban yi niyyar d’aukar jinjiran ba amma tsananin kukan ta ya matuk’ar sa na tausaya mata don haka na koma na d’auke ta, ina isowa wajen da mai d’akina take na tarad da ta haihu sedai d’an bai zo da rai ba. Hankali na ya tashi matuk’a, nan na basu labarin jaririyar da na tsinta a bakin ruwa, cikin jimamin rashin d’an ta Mai d’aki na ta karb’i Layla ta rungume cewa d’iyar ta ne, wannan yasa muka b’oye wa duniya babu wanda yasan wannan labarin daga ni se d’an uwana da matar sa, ko da muka koma gida ma cewa muka yi y’an biyu Mai d’aki na ta haifa amma d’ayan ya koma, haka muka cigaba da rainon Layla har ta girma, bata nemi komai ta rasa ba, kuma mun bata tarbiyya, daman nasan komai daren dad’ewa gaskiya zata bayyana don haka yau nake fad’a muku wannan. Amma in kuka raba ni da y’a ta ban san yanda rayuwa ta zata kasance ba, bani da kowa yanzu in ba ita ba, ban haifi Layla ba amma bazaku k’arbe matsayin uba da nake da shi ba a wajen ta. Ku yi wa Allah kada ku raba ni da y’ata” Baba ya gama bada labarin ya fashe da tsananin kuka. Shiru kake ji babu wanda ya iya motsa wa se Layla da ta zuba wa uncle Rasheed ido shi ma kallon nata yake yi yana kwalla. Jiki ba kwari ta mik’e ta nufi hanyar fita Suraj ya d’ago yace “Layla!” Ko juyo wa bata yi ba don haka ya mik’e shi da Habeeb suka bi bayan ta… Mom dake zaune ta ja numfashi kafin ta dubi Rasheed da Baban Layla tace “Ku kwantar da hankulan ku, Layla ai y’ar mu ce duk, kuma ko ba komai kai ka fi kowa sanin ciwon Layla kuma kai ka sha wahala iri iri wajen ganin ka tarbiyyantar da ita babu mai kwace maka wannan matsayin, shi kan shi Rasheed na san ba zai fara ba.” Kai Uncle Rasheed ya jinjina kafin ya mik’e gami da dafa kafad’an Baban Layla yace “A baki ne kawai zan iya fad’in ina da y’a amma a bayyane kai ne Uban Layla kuma har abada zaka kasance a haka, bani da ikon raba ka da Layla, sanin cewa ina da y’a, kuma jini nah a raye ma kad’ai ya ishe ni, mutane irin ka yanzu sun yi k’aranci, na gode da rik’on da kuka yi ma Layla ko ba komai nasan y’a ta bata fad’a mummunan hannu ba. Nan fa aka warware maganar Bayan sun ci abinci cikin farin ciki suka sha hirar su har La’asar , Baban Layla da Uncle Rasheed suka sake fahimtar juna sannan, suka yi sallama Baban Layla da Baban Junaidu suka tafi. ****** ****** ****** ****** Shimfid’e take kan koren ciyawar kusa da ruwa kan ta a kan cinyar Suraj yayinda hannun sa ke shafa lallausan gashin kan ta, mayafin ta kuwa ta rik’e a hannun ta, duk idanuwan ta sun yi ja sun kumbura saboda kuka da tasha, daman da kyar Suraj ya lallab’a ta. “Layla!” Suraj ya k’ira sunan ta, a hankali ta d’ago ta zauna sannan ta maida mayafin ta rufe kan ta da shi tana kallon Suraj. “Yamma tayi, ya kamata na kai ki gida, a wannan yanayin bai kamata kina waje ba” Kai ta jinjina ta mik’e, shima mik’e wa yayi ya rik’e hannun ta suka fara tafiya basu yi nisa ba Habeeb ya iske su. Suraj yayi Murmushi yace “Habeeb Bro would you do me a favour? Pls ka k’ira driver ya kawo mana mota, a condition d’in Layla bai kamata ta zama so worked out ba, ni na manta waya na a gida already kum….” Suraj bai gama maganar ba suka jiyo ihu, A firgice Layla ta kwalla ihu “Babaaaaaa!!! Duk suka ruga da gudu suka nufi inda suka jiyo ihun abun da suka gani ba k’aramin d’aga musu hankali yayi ba Layla kam tuni ta zube k’asa a sume Suraj da Habeeb suka had’e baki wajen cewa “AMEEEER???”….. Suraj ko ta kan Layla bai bi ba suka ruga da gudu inda BABAN LAYLA ke kwance shame-shame cikin jini kan shi a kan cinyar Ameer yayinda Ameer d’in ke k’ok’arin zare wuk’ar da ke lume a cikin Baban Laylan. Ameer na hango su Suraj ya ruga wajen da Suraj ke tsaye cikin rud’ani yake fad’in “Suraj please do something! Idan aka cire wuk’ar nan zai zubar da jini matuk’a kuma zai iya mutuwa please mu yi gaggawan kai shi asibiti he has already lost a lot blood!” Tamkar gunki da aka sassak’a haka Suraj ya tsaya idanuwan shi kafe kan Baba dake kwance, jinin ya kalla yaga yanda yake zuba kafin ya maida duban shi ga Habeeb wanda ke durk’ushe gaban Baban. Habeeb ma Suraj yake kallo kafin ya girgiza kai yace “HE’S NO MORE SURAJ!!, ya mutu ,babu ko da d’igon numfashi a tare da shi.” Kai Ameer ya girgiza a firgice yace “No! It can’t be true! Ya zaka ce ya mutu? Mu kai shi asibiti mana!” yana fad’an haka yanufi inda Baban ke kwance ya durk’usa ya kama wuk’ar ya zare sannan ya danne inda jinin ke zuba da hannun shi daidai lokacin ne Baban junaidu ya rugo da gudu yana ihu kamar yayi hauka Habeeb se rirrik’e shi yake yi. Mik’ewa Ameer yayi gami da jefar da wuk’ar ganin haka Baban Junaidu ya d’aga sandar sa ya maka wa Ameer a kai har saida ya daina ganin haske, ganin zai k’ara maka wa Ameer sandar hakan yasa Suraj ya shiga tsakani sandar ta sauk’a a goshin Suraj inda tuni ya fara zub da jini. Da kyar Habeeb da wasu makiyayan suka janye Baban Junaidu, Aka d’auki gawar Baban Layla zuwa gida. Se lokacin Suraj ya koma inda Layla ke kwance shame-shame ya d’auke ta kamar yarinya suka nufi gidan su Layla, Habeeb ya ciccib’i Ameer suka nufi gida domin bai ma san me ake ciki ba. Kafin su isa gida Har labari ya isa Fada cewa Ameer ya kashe Mahaifin Layla, zo kaga tashin hankali wajen su Mom Uncle Rasheed bai jira komai ba ya k’ira waya police suka kama Ameer. Duk da jirin da yake ji Ameer bakin sa bai rufe ba “Suraj! Suraj! I didn’t kill him, wallahy bani na kashe shi ba trust me !! Suraj ka taimake ni please” kalaman da yake ta maimaita wa kenan har Motar police d’in ta bar wajen. Mai martaba kuwa takaicin abunda ake zargin d’ansa Ameer yasa ya yanki jiki ya fad’i shima aka yi asibiti da shi………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *