YAR MAKIYAYA CHAPTER 20 KARSHE

YAR MAKIYAYA CHAPTER 20 KARSHE

  Ameer how could you be sooo stupid? Baka da hankali ne, yaya za’a yi ka yi k’ok’arin hallaka kan ka?” Suraj ya tambaya kafin yaci gaba da cewa+ “Duk tarin matsalolin ka basu kai wad’anda nake da su ba, but na d’auke su a matsayin k’addara, na sani cewa i also have gone mad, amma k’ok’arin k’ona kanka da kayi is a complete and total stupidity Ameer. Ka sa Allah a ranka in shaa Allah komai zai dawo daidai, one more thing! Ina so yanzun nan kayi min Alk’awarin cewa bazaka sake kamanta abunda ka aikata ba ko da kuwa kana wanne irin hali, by killing yourself you are not solving your problems,” Murmushi Ameer yayi sannan ya cire oxygen mask d’in ya rik’e hannun Suraj yace “Ban san wanne irin zuciya kake da shi ba Suraj, you have a very big heart da wani ne nasan ko inda inuwa ta take bazai bi ba, amma kai kuma ka tattare matsalolin ka a gefe kana comforting d’ina ,please Suraj forgive me for all the wrong i’ve done you, Yanzu saboda ni Habeeb ma yana kwance” Suraj murmushi kawai yayi yace “Ameer abunda ya wuce ya wuce , Habeeb is absolutely fine yanzu haka ma ya tashi, Look Ameer, Habeeb ya yi risking rayuwar shi ya ceci naka iya sakayyar da zaka masa shine kada ka sake k’ok’arin kashe kanka” Kai Ameer ya jinjina ya rufe idanuwan sa yana hawaye. ONE WEEK LATER…. “Habeeb yau sati d’aya da tafiyan ta amma duk sanda na farka ji nake kamar yau ta tafi, na sha k’iran Layla amma ko sau d’aya bata gwada d’aga wa ba, ban san ya zan yi ba, wannan shine soyaygar da Layla take yi min kenan, Habeeb farko de ba ni na kashe Baba ba me zai sa ta bani punishment d’in abunda ba ni na aikata ba? Layla ta kwace komai daga gare ni a lokaci guda. I hope the police find the real culprit so that Layla zata dawo gareni, Habeeb my life is incomplete without Layla. Duk da cewa tana nesa da ni, my heart feels her near. Ina samun nutsuwa ne kawai in ina tare da ita in her arms. Ita take cire min duk wani tsoro, ina matuk’ar k’aunar ta da dukkannin zuciya ta, i pray that we remain together forever, may we never part”. Habeeb kai ya jinjina kafin ya amsa da “Ameen”. Sallama suka ji an yi, a tare suka amsa sannan suka maida hankalin su ga wanda yayi sallamar, JUNAIDU ne d’an kawun Layla ya shigo tare da Police hakan yasa duk Habeeb da Suraj suka mik’e daga kujeran da suke zaune suna kallon kallo kafin Suraj ya yi musu iso , kowa ya nutsu sannan inspector ya dubi Junaidu ya ce Ka fad’i abunda ka yi mana bayani d’azu a station”. Baki na b’ari Junaidu ya ce “Ameer ba shi ya kashe kawu na ba, a lokacin da aka yi kisan ina wajen. Baba na shi ya kashe d’an uwanshi, saboda dukiya, da farko nayi shiru saboda bana so a kama Baba na amma naga abunda shiru na ya jawo, na raba Suraj da Layla sannan na tarwatsa farin cikin gidan ku, na kasa samun sukuni, ta b’angare d’aya kawu na ,ta wani b’angaren kuma mahaifi na, amma bazan iya zauna wa nayi shiru ba, Ameer bai yi laifin koma ba Hasali ma taimako kawai yaje yi Baba na (baban Junaidu) shi yayi kisan kuma zan iya rantsuwa a kan hakan”. Suraj kasa ko da d’aga k’afa yayi tsabar mamaki, Habeeb ya ce “i can’t believe how a person can be so rude, ace d’an uwa ya kashe d’an uwansa saboda abun duniya! ” Mik’e wa police d’in suka yi d’ayan su yace Mun riga da mun kama mai laifin kuma ba tare da mun sha wahala ba ya amsa laifin sa, thanks to Junaidu da ya ajiye alak’ar sa da mahaifin shi a gefe ya fad’i Gaskiya da yanzu mun hukunta Ameer akan laifin da bai aikata ba, mu yanzu zamu koma, mun janye duk wani charges against Ameer na kisan da aka yi don haka he is free. “Alhamdulillah! Shine abunda Suraj da Habeeb suke furta wa, duk abunda ya faru Ameer yana tsaye kan staircase yana ji, tsabar farin ciki saida yayi sujood ya gode ma Allah da ya wanke shi daga mummunan zargin da ake mishi. Police suka yi musu sallama sannan suka tafi. Kwanta wa Suraj yayi cikin Lallausan kujerar dake living room d’in yayi ajiyar zuci kafin ya dubi Habeeb da Ameer yace “Na tabbata in har Layla ta fuskanci gaskiyar al’amarin zata dawo gare ni, she will not hold her self back! Habeeb am sooooo…..happyyy!!”. Ameer ya jinjina kai yace “Yes na tabbata Uncle Rasheed zai fahimci kuskuren da ya tafka na raba ka da Layla, ” Wannan daddad’an labarin ya iske su Mom da Mai martaba, sun yi matuk’ar farin ciki , kuma sun gode ma Allah da ya shirya Ameer ya dawo mutumin arzik’i…. ******* ****** ******* Ko da labarin ya riski Uncle Rasheed cewa Ameer ba shi yayi kisan ba, bai sanar da Layla ba, hasali ma duk takardun case dake hannun sa ya b’oye. Dare da rana Layla na jira taji me police zasu fad’a game da kisan baban ta amma Uncle Rasheed a ko da yaushe cusa mata tsanar Ameer yake yi, “Y’ata lokaci yayi da zaki daina b’ata lokacin ki game da Suraj, na tabbata da ya damu da ke da zai yi abunda ya dace. A maimakon ya tsaya da ke ya zab’i d’an uwansa, yanzu haka police sun wanke Ameer daga Laifin da ya aikata an sake shi yana shawagi kamar tsuntsu a cikin daji. Ya kamata ki mance da abunda ya faru ki d’aukaka rayuwar ki” Hawayen da suka gangaro a fuskar ta ta share sannan ta mik’e tsaye tace, “tabbas! Suraj ya tafka kuskuren da bazan yafe masa ba, kuma nayi maka alk’awari cewa zan mance da duk abubuwan da suka faru a baya, zan kuma kula da kaina ko dan saboda abunda ke ciki na nasan tunda kana tare da ni bani da fargaba Abbah.” Wani shu’umin murmushi Rasheed yayi kafin ya juyo ya fuskanci Layla yayi murmushi gami da sa mata albarka….. Suraj har ya gaji da k’iran Layla daga k’arshe ma numbar bata tafiya kullum cikin jiran Layla yake, duk lokacin da rana ta b’ullo zuwa fad’uwar ta babu abunda yake Muradi da ya wuce yasa Layla a ido wannan mafarkin na ganin Layla ta dawo gareshi kullum farautar sa yake yi a barcin sa. Amma ko da kyallin ta babu ballantana na Uncle Rasheed……Watanni sun shud’e, a kowanne rana Suraj sake birkice wa yake yi, he is turning savage, ya zama bashi da hak’uri, rude sannan ko kad’an baya d’aukar nonsense, su ma gidan babu mai shiga gonar sa domin mugun tsoron sa suke yi, Suraj d’in da suka sani a baya ba shi ne Suraj d’in yanzu ba, mutane biyu kawai yake sauraro Har ya yi dariya, Habeeb da Ameer, su kad’ai ya yarda da su. Abu kad’an ke tunzira shi sannan yafi k’aunar zama shi kad’ai. Mom a wani b’angaren ta damu sosai ganin yanda Suraj ya sauya, he has gone totally out of control amma a wani b’angaren tana farin cikin kasancewar Ameer da Habeeb a tare da shi domin tasan ko ba komai sun san yanda suke controlling zafin ran Suraj.+ D’akin Suraj ta shigo amma tsabar duhu saida ta yi tuntub’e, da kyar ta laluma makunnin wutar d’akin ta kunnan. Jingine yake kan gado ya lumshe idanuwa, kunna wutar da Mom tayi ne yasa ya bud’e idanuwan sa. Bin ta kawai yayi da kallo har ta k’arisa inda yake ta zauna a gefen gadon, hannun sa ta rik’e cikin nata kafin ta k’ira sunan shi da sassanyar murya “Suraj…..Son.! Why are you doing this, ruining your life?. Kana ja ma kanka damuwa da rashin nutsuwa, Dukkanin mu k’ok’ari muke muga mun taimaka maka Suraj. All of us are trying to help you with this hard and trying times. Amma a tunanin ka mun zauce ne, haka kake tunani. Na yi kewar d’ana Suraj! I missed the way you used to be, wasu watanni a baya ba haka kake ba. But for some reason ka sauya kwata kwata, dalilin kuwa duk mun sani. Na damu da kai sosai, nakan kasa nutsuwa dare da rana! Amma nasan cewa i can’t stop you now, nor can i fight your fights. Mahaifiyar ka ce ni Suraj nayi matuk’ar damuwa, wad’annan nauyin bazan iya d’auka ba, i can’t take these burdens, i want you to grow up! Grow up and be a man!. Shekarun ka ashirin da biyar amma, so kake mu kama hannun ka kamar yaro ne? Har yanzu akwai lokaci, ka daidaita rayuwar ka. Kayi wannan saboda mu, Ni, Baban ka , Ameer, Habeeb. Muna b’ukatar ka, we all need you and that’s a fact!. Ko wanne dare in zan kwanta, i silently pray for you, in yi addu’a cewa Allah ya ja nisan kwana, cewa Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka farincikin da duk kake buk’ata.” Mom tana kai nan ta mik’e zata fita, Hannun ta ya rik’e yana kuka “Mom nasan na sa ku cikin damuwa sosai, in dai har kuna so na cigaba toh sedai in zan tafi daga Belel, zan yi nesa da duk wani abunda zai tuna min da Layla, Mom watanni shida kenan ina jiran Layla amma ko da so d’aya bata yi tunani na ba da halin da zan shiga, ban san irin zuciyar da take da shi ba, yaya take? Ta haihu lafiya? Me ta haifa? Ban sani ba she snatched my world from me! I will never forgive her for this Mom!”. Mik’e wa yayi ya fice daga d’akin ya bar Mom a tsaye jiki a sanyaye tana magana a zuciyar ta “Suraj ni ma mamakin da nake yi kenan, in har Layla ta san Ameer ba shi yayi kisan ba ai ya kamata ta dawo amma yau watanni shida kenan ko motsin ta babu this dosen’t make sense at all!”. Habeeb da Ameer suna zaune a living room Suraj ya sauk’o, gefen Ameer ya nema ya zauna ya d’auki wayar sa yana duba wa, Ameer da Habeeb basu ce qala ba se kallon sa da suke yi. Habeeb ne ya dubi Ameer yace “Ameer wani abokin mu ni da Suraj ya yi organizing photography exhibition next week kuma ya gayyace ni da Suraj kuma ina da extra I.V me zai hana ka taho kai ma? Ko ba komai zamu samu fresh air atleast zamu huta na kwana biyu. Kai Ameer ya jinjina yace “kayi gaskiya Habeeb, Suraj ya ka gani? Na tabbata zaka ji dad’in tafiyar”. Ko d’ago kai bai yi ba ya ce “Yaushe ne tafiyar kuma wanne gari ne?” Habeeb yayi tsalle ya dawo gefen Suraj yace “GOOD question bro! Tafiyar de next week ne kuma wa are going to Paris!” kai kawai Suraj ya jinjina kafin ya ce “Allah ya kai mu”. Duk suka amsa da Ameen. Wasu Maza ne biyu sanye da suit suka shigo da sallamar su, duk su Ameer suka amsa a tare sannan suka basu wajen zama , bayan an kawo musu refreshments sun nutsu d’aya daga cikin su yace “Na tabbata a cikin ku akwai Mr Suraj Abdoul-Malik right?” Suraj ya d’ago yace “Right! Myself Suraj Abdoul_Malik” Kai Mutumin ya jinjina yace “Well in that case, i am Barr, Hassan Bello and my colleague Emmanuel simpsons. I’m here on behalf of my client Layla Rasheed. Matar ka Layla ta buk’aci saki kuma ta bada kwararan dalilai, ta ce zaman ta tare da kai barazana ce ga ita da rayuwar ta amma in kaga claims d’in ta are false zaka iya kai case d’in zuwa court inda duk zaku samu justice.” Duk Habeeb da Ameer a take suka mik’e Mom da ta fito daga d’aki saida ta jefar da wayar hannun ta, Habeeb ya tara courage d’in shi ya karb’i takaddar ya karanta kafin yace “ta yaya za’a yi haka? Layla da Suraj both Loved each other, suna k’aunar junan su Matuk’a, yaya za’a yi ku taho da wannan false information d’in kuna nema ku nakasa min d’an uwa? This is nothing but a pure lie.” Lawyer ya mik’e ya karb’i file d’in yace “ba mun zo nan bane domin tada hankali, abunda client d’ina ta fad’a shi nake fad’a I’m just her advocate you see.” Duk maganganun da suke yi Suraj jin su yake ko motsa wa bai yi ba, Mom ta kasa kawar da duban ta daga Suraj amma ko a jikin sa kamar bai san suna yi ba, kusan minti talatin Habeeb da Ameer suna k’ok’arin fahimtar da Lawyers d’in amma kamar zuga su ake yi. Har su Dad ma sun shigo sun iske dramar da ake tafka wa. Mik’ewa Suraj yayi ya sa wayar sa a aljihun sa sannan ya dubi Habeeb da duk ya rud’e ya dafa kafad’ar Habeeb d’in ya lumshe idanuwan sa had’e da sauk’e nannauyan ajiyar zuciya ya Kad’a kai yace “No Habeeb Bro……. Please, ya isa haka! Not anymore, bazan iya d’aukar wani tashin hankalin ba, kada ka b’ata yawun bakin ka, bazasu fasa ba har se sun samu biyan buk’ata, haka ma Layla ta riga ta yanke ma kanta hukunci, yanzu lokaci na ne da zan yi abunda ya kamata, abunda ya dace” Habeeb ya zaro ido yace “Me kake nufi Suraj? Me kake k’ok’arin aikata wa? Layla ce fa!” Murmushi Suraj yayi kafin yace “Na san Layla ce, wannan hukuncin da ta yanke ne, kuma nayi mata alk’awari duk abunda ta nema a waje na bazata rasa ba ko da kuwa raina ne, in har yin hakan zai saka ta farin ciki then i am ready to divorce Layla this very moment”. Yana gama rufe baki ya d’auki paper ya karb’i pen ya rubuta saki d’aya ya nad’e ya saka a envelop ya mik’a wa Lawyer sannan yayi signing papers d’in ya bayar. Lawyer ya had’a takardun ya sa a briefcase suka fice Suraj ya haura upstairs A inda take tsaye Mom ta zube gwiwa a k’asa tana furta “Inna lillahi wa inna ilaihir-rajiuun.” Dad da Abban Habeeb zama kawai suka yi babu wanda ya iya furta ko da kalma d’aya tsabar shock….. Da gudu ya k’arisa d’akin sa, numfashin sa sama-sama kamar me asthma ya banke k’ofar ya rufe sannan ya nufi gaban madubi yana kallon fuskar shi, kafin ya doke madubin da hannun sa har saida ya tsage, hannun sa yana zub da jini haka ya nufi bathroom ya saki shower a kansa. “It’s over!!” Wannan kalmar yake ta furta wa in a whisper………… “Ya kamata ki farka a wannan karon Layla Y’ata, Suraj ya riga da yayi nisa yanzu, bazan bar shi haka ba se na koya masa hankali! Har wato yana da ikon da zai rubuta wa y’ata saki? Ya lalata miki rayuwa ya kwace farin cikin ki sannan ya sake ki??”+ Layla bata san lokacin da ta mik’e ba har tana tuntub’e ta nufi wajen da Uncle Rasheed yake tsaye tace “Saki kuma Abbah! A’a wata k’ila baka fahimta bane, Suraj bazai sake ni ba, Suraj bazai min haka ba”. Tsawa Uncle Rasheed yayi mata “LAYLA!! ki nutsu ki saurare ni! In yana k’aunar ki da tuni ya nemi inda kike, sannan ai saki ba k’arya bane, ga sa hannun Suraj, ya kamata ki fahimci cewa ba duk aka zama d’aya ba, kuma ya kamata dama ki yi tsammanin irin haka daga wajen wad’ancan matsiyatan, yanzu sun nuna min cewa basu san mutunci ba!” Yana kai nan ya fice yana murmushi yayinda Layla ta zube kwance a k’asa kan carpet tana kuka mai tsananin tsuma rai, “Suraaaaaajj! Me yasa zakai min haka? Me yasa zaka rabu da ni?? Kenan ka nuna min cewa kai ba namiji bane! Ka rabu da ni da y’ar da na haifa! Ko da sau d’aya baka d’auke ta ba a hannun ka! Me yasa zaka sake ni??….”…… WELL, IT IS SAID THAT SOME LOVE STORIES ARE NEVER MEANT TO BE, SUCH IS THE STORY OF LAYLA AND SURAJ! Littafin Y’ar makiyaya ya zo k’arshe but i can’t call it a happy ending! Rather a sad one, tragic one. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah!! Na gode wa Allah da ya bani ikon kawo k’arshen wannan littafin na y’ar makiyaya bayan zango mai tsawo sosai, littafin da na fara rubuta shi tun 2017 yau na kammala shi, ina fatan saqon dake ciki ya isa ga masu karatu A rayuwa ba komai mutum yake samu ba, sannan duk samun mutum ko rashin sa daga Allah ne. Mai kud’i da talaka duk Allah ne yayi su, kuma basu da banbanci a wajen sa duk bayin sa ne. Munafurci kuma dodone mai shi yake ci, sannan ramin k’arya k’urarre ne. Nasan kuna da tambayoyi da dama! Ku sha kurumin ku Littafin Y’AR MAKIYAYA NE YA K’ARE AMMA BA LABARIN BA DOMIN CIGABAN LABARIN YANA NAN TAFE CIKIN SABON LITTAFI NA MAI SUNA IN SO YAK’I NE……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *