YAR MAKIYAYA
CHAPTER 7
An ce kayi k’aryar da zata fidda kai , shin k’aryar Suraj kuwa zata yi aiki? Yaya zai yi ya shawo kan al’amarin,? In har Dad ya gano gaskiya ba k’aramin matsala zata haifar ba domin Laila bata kasance y’ar wani kawun Habeeb ba illah y’ar makiyayi mai kiwon dabbobi a saman tsaunuka.
****** ******** *******
“Who is Laila?”
Dum! K’irjin Habeeb ya harba kamar agogo ,duk da yaji me Dad ya fad’a amma se yayi kamar bai ji ba ya juyo ya sake tambaya
“Na’am, me kace Dad?”
Mik’e wa dad yayi daga kujerar da yake zaune yace
“Yes! Kaji me na fad’a who is Laila?”
Habeeb yasan dole yayi acting kuma ma so fast kafin Dad ya gane komai saboda Idan yasan Laila y’ar talaka ce bazai bari soyayya ta d’aure tsakanin ta da Suraj ba ,gashi yaga irin soyayyar da suke yi dan haka ya k’irk’iro k’aryar sa yace
“Dad Laila y’ar uncle d’ina ne ,kaima ai ka sani ba?” A tsare ya fad’a Amma zuciyar kam kad’an ya rage ta b’alla k’irjin shi ta fad’o k’asa duk gab’ob’in shi sun yi sanyi yana jiran jin me Dad zai ce.
“Alright you may take your leave”.
Cewar Dad a lokaci guda ya koma ya luntsuma cikin lafiyayyen kujerar sa.
Chan k’asan mak’oshin sa Habeeb ya ce “thank you, and. Gud night”. Murmushi kawai Dad yayi ya maida hankalin sa kan TV shi kuwa Habeeb yana fita ya runtuma a guje yayi upstairs bai zame ko ina ba sai d’aki inda ya rufe k’ofar sannan ya jingina jikin ta yana haki.
Ya dad’e zaune a kan gadon yana kallon yadda Habeeb ya kasa nutsuwa gaba d’aya sai haki yake jingine da k’ofa kamar dai yadda yake tun shigowar sa.
“Zai fi maka sauk’i kayi bayanin abunda yake damun ka har yasa ka kasa zama ,don da kasan irin wautar da ni na tafka da sai taka damuwar ta gushe wallahy.” Suraj kenan yake magana yayinda ya takure kai da gwiwa yana kallon Habeeb.
Da gudu Habeeb ya k’ariso inda yake yace ” A’a Suraj na tafka laifi babba ,ka san me na aikata? Na had’u da Dad ya tambaye ni Wacece Laila”
Sunkuyar da kai Habeeb yayi ya rik’e k’ugun sa ya kasa magana Suraj kuwa kamar an mintsina ya chafko Wuyan rigar Habeeb har jijiyan kan shi sun fito yace
“What exactly did you tell him about her? Don’t tell me ka fad’a masa komai?”
Kai Habeeb ya girgiza yace “am sorry Suraj”.
Suraj ya sake damk’e collar d’in Habeeb ya ce “Sorry for what? Tell me baka fad’a masa Wacece Laila ba please” Suraj yana maganar ne Amma gumi da hawaye basu da banbanci a fuskar sa.
Da k’arfin tsiya Habeeb ya iya kwatar kansa daga rik’on da Suraj ya masa sannan ya samu ya shaqi numfashi ya daka wa Suraj tsawa don yaga yana k’ok’arin sake chafke shi
“If only you will listen to what am about to say! Ni ban fad’a wa Dad asalin Laila ba kawai de na ce y’ar kawu na ne, I am sorry ban san me ya shige ni ba na yi Wannan shirmen amma babu yadda zan yi ne there is no other way out, coz Idan nace wa Dad Laila ba kowa bace illa *y’ar makiyaya* zan zamo sanadin rabuwar ka da Laila nasan yadda ya k’i jinin talakawa musamman ma makiyayan nan, am sorry Suraj”
Dariya da kuka duk suka had’e guri d’aya wa Suraj ya zube a k’asa ya kwantar da kansa jikin gado ,shima Habeeb ya zauna gefen shi ya zuba masa ido cike da mamaki kafin yace
“Suraj na kasa gane wa kuka kake ko dariya? I said am sorry it’s not intentionally, babu yadda zan yi shiyasa nace Laila y’ar kawu na ne”
Wata muguwar dariya Suraj ya kece da ,wanda har saida tasa Habeeb ya ja da baya kafin ya share hawayen sa ya yi tsalle ya fad’o kan Habeeb yana fad’in
” *YOU ARE A GENIUS*”!!!! Kasan me? Awa hud’u kafin yanzu I was desperate ban san yadda zan yi ba, I taught I was a terrible liar Ashe akwai wanda ya fini ma iya k’arya, Toh bari kaji d’azu Dad ya tambaye ni Wacece Laila, na rasa me zan ce masa saboda bana so ya aura min y’ar abokin sa khadija ,ban san yadda zan yi ba kawai se idea ta zo min”
Zaro ido Habeeb yayi yace “Toh me kace masa? Kar de na kwafsa maka?” Dafa kafad’ar Habeeb Suraj yayi yace “Aa ai nima k’aryar da kayi masa shi nayi nima, tsoron da naje da b’acin rai yasa na nemi waje a masallaci na fake kawai don kar wanda ya neme ni shine yanzu na dawo, but Nide ba wannan ba pls help me Habeeb”
Cire rigar sa Habeeb yayi ya daka tsalle ya hau gado shima Suraj ya haye suka dinga dariya kamar mahaukata Suraj da kyar yace “ya kamata mu san abin yi” Habeeb ya make shi da bayan hannu sannan yace “haba Malam ! D’azu fa da ka min wani damk’a saida naga wuta ta d’auke, gaba d’aya yanzu kai na babu chaji shine yanzu zaka bijiro da maganar solution? Kawai ka bari zan yi tunani anjima ,in Allah ya kai mu da safe we’ll come up with a better solution”
“You’d better! Saboda in har baka samo min yadda zan yi ba zan sheqe ka and I mean it!
Kashe wuta Habeeb yayi yana dariya yace “no you wouldn’t” Suraj ya girgiza kai yace “yes I would”. Habeeb ya ja bargo ya kwanta kamar bai ji shi ba.2:30am +
“Habeeb! Habeeb!!! Come on ka tashi, ni ina nan na kasa runtsa wa kai se sharara bacci kake yi babu abunda yayi tsalle ya tsone maka ido”
A fusace Habeeb ya zauna yace “Ohohoo! Wayyo Allah! Suraj wai dan Allah baza ka bari nayi bacci na ba? Na fad’a maka zan sanar da kai solution d’in gobe but pls ka bari na kwanta barci nake ji”.
Kwanta wa Habeeb yayi yana mai Jan blanket ya rufu shi kuwa Suraj ya k’ura masa ido ba tare da cewa k’ala ba.
3:00am
“Tsk! Habeeb! Habeeb!! Kai Habeeb dan Allah ka tashi”.
Mirgina wa Habeeb yayi ya koma k’asa ya kwanta ya bar gadon gami da toshe kunnuwan sa da pillow ganin haka Suraj ya mik’e ya d’auki pillow d’in sa ya wurga k’asa kan Habeeb a fusace yace
“Fine! Fine!! Don’t tell me ,after all I don’t need your filthy solution! Me ma zai dame ka kai? Budurwar tawa ce, matsalar tawa ce ,solution d’in nawa ne ! Toh ai shikenan!” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya bar d’akin ya nufi sashen Mom.
Zaune take kan sallaya tana addu’o’i da alama sallah tayi, zama Suraj yayi ta gefen ta ya nad’e k’afafun sa yana jira ta idar, bayan ta kammala ta juyo cike da mamaki tana kallon sa kafin ta dafa kafad’ar shi tace
“Subhanallah! Suraj kai ne a Wannan lokacin?” Ta fad’a tana kallon agogo
Kai ya d’ago yace “Mom cikin Wannan dare ba ke kad’ai kika kasa barci ba nima haka, Mom I don’t know what to do”
“Me yake faruwa Suraj har yanzu baka ce komai ba kawai kana ta k’ara saka ni a duhu.”
Nan Suraj ya kwashe duk yadda sukayi da Dad har da yadda Habeeb ma yayi da Dad mom kam ta kasa cewa komai se yanzu
“Na fahimci komai Suraj, na san dalilin da yasa kayi k’arya dan haka gwara da ka sanar da ni coz zai yiwu dad naka ya tambaye ni kaga bani da ta cewa, yanzu ka je ka kwanta in Allah ya kaimu da safe zamu yi magana, kar ka damu komai zai dawo daidai.” Suraj ya saduda yanzu kam tunda daga Mom har Habeeb cewa sukayi sai da safe dole ya hak’ura don haka ya mik’e ya fice jiki a sake..
Jingine yake a gefen k’ofar ya nad’e hannu a k’irji ,yana jin Suraj ya fito daga d’akin Mom yace “Toh ya? Momma’s boy ka samo solution d’in? Oh ko dai Mom ma tace se da safe? Fad’a min mana me Mommyn ta ce, fad’i mana!
Suraj ya cika tsabar haushi yace
“Oh so kake kaji me tace? Cewa tayi in kashe ka ,yau ni da kai a gidan nan,! Suraj ya bi Habeeb da gudu amma ya tsere saida ya kai d’aki ya tsaya yace
“O boy! Dare ne fa! “. Tsaki Suraj ya ja sannan yace “who cares dallah matsa min in wuce” ya banke Habeeb shi kuwa Habeeb sai dariya yake tayi ya dawo gado ya kwanta.
6:00am
Bugun k’ofa ne ya fara isowa kunnuwan Habeeb da ke saka riga ,da alama wanka yayi, k’arasa wa yayi bakin k’ofar ya bud’e to his surprise Mom ce tsaye tana Murmushi, k’ofar ya bud’e ya bata hanya ta shiga sannan ya rufe , k’arasa wa yayi ya gaida ta ,cike da kulawa ta amsa kafin ta mayar da duban ta ga Suraj wanda bai dad’e da samun bacci ba, d’ago kai tayi ta kalli Habeeb tace ” hope bai dame ka ba last night, don nasan halin sa he don’t give up easily”.
Murmushi Habeeb yayi yace “not at all Mom”
“Yanzu na gama waya da Umma ( mahaifiyar Habeeb kuma yayar Mom) na sanar da ita duk abunda yake faruwa sannan tayi bayani wa Dad naka, yanzu de ta fannin su bamu da matsala amma solution d’in da suka bayar ne da kamar wuya, yanzu ina da wasu ayyukan dazan yi later during breakfast zamu yi magana”. Tana kai nan ta mik’e ta nufi k’ofar fita Habeeb kuwa ya mata godiya yana Murmushi. Har yanzu de bamu ji solution DA Habeeb da kuma Mom suka samo ba, will their solution be the best ko kuwa dai Suraj zai yi hak’uri ya rungumi K’addara?.
******** ******** *******
“Suraj! Come on, tashi ka shirya Mom tana jiran mu downstairs in ka gama mu had’u a chan”,Habeeb na kaiwa nan ya d’auki wayar sa ya fita yana mita
“Mutum an fad’a mishi ya kwanta yayi bacci cikin dare ya k’i se da safe ya ishe mu da minshari tsk” +
Zauna wa Suraj yayi a bakin gado yana murza idanuwan sa,cikin muryar jin bacci yace
“I heard that! Kuma for your information ni bana minshari” gira d’aya Habeeb ya d’aga ba tare da juyo wa ba yace “really? nan gaba Zan saita camera a man ka ta yadda Zan nuna maka how disturbing you are in kana bacci”
Dariya Suraj yayi ya shafa kan shi kafin ya d’auki disposable cup cike da ruwa ya wurga wa Habeeb luckily yayi dodging da sauri ya bud’e k’ofa ya fice kafin ya rufe ya ce “target missed! Suraj bai ce komai ba ya mik’e ya shige bathroom. Cikin gaggawa ya kammala shirin sa don ya k’agu ya had’u da Mom don yaji yadda ta yanke, zaune ya iske su sun zagaye dining table Mom na waya shit kuwa Habeeb ya ma Fara breakfast nashi hankali kwance.
” barka da Asubah Mom” ya fad’a yana k’ok’arin janyo kujerar da zai zauna.
“Morning!” Mom ta amsa a tak’aice sannan ta maida hankalin ta kan wayar da take yi.
Tea d’in Mom ya d’auke ya Fara sha duk da tana waya saida ta tsaya kallon shit, kai ta girgiza ta cigaba da wayar ta Habeeb ya yi y’ar dariya chan k’asan mak’oshin sa yace “lazy lad “. Suraj ya kurb’i Shayin yace “hah! Na ji wannan ma” daidai lokacin Mom ta ajiye wayar ta tsaya kallon Suraj da ko a jikin sa se shan tea d’in yake yi,Murmushi tayi sannan ta Fara had’a wani tace ” Suraj ni da Habeeb Mun samo solution amma kai Habeeb miye naka solution d’in?” Mom ta tambaya ba tare da ta d’ago kai ba.
Gyara murya Habeeb yayi sannan yace
“Solution d’in shine since Dad has been lied to, dole se y’ar makiyaya Laila ta dawo K’anwar Habeeb Laila”
Tea d’in dake bakin shi Suraj ya Furzar gami da zaro idanuwa waje yace
“Kai kayi hauka ne? What do you mean?” Habeeb yace “No! Suraj ba hauka nayi ba amma bamu da wani mafita se hakan, dole somehow kayi convincing Laila ta biyo ni zuwa kaduna na d’an wani lokaci Mom zata taimaka mana mu sa ta a hanya so that Dad bazai yi suspecting wani abu ba Laila dole ta biyo mu, am sure in har Dad ya ganta kai tsaye yanzu wallahy se ya gano cewa bata tab’a zama cikin daula ba trust me ka san halin Dad.”
Mik’e wa Suraj yayi yana girgiza kai yace “ka zo min da impossible task! Laila ta bar Belel wata matsala ce daban sannan Laila ta bar baba ma matsala ce mai zaman kan ta why not come up with a better solution wanda ba se Laila ta bar gida ba ? Habeeb am scared bazai tab’a yiwuwa ba”
“Sedai in Laila bata k’aunar ka tun asali, sedai in dama chan baka da gurbi a zuciyar ta Suraj” Cewar Mom da yanzu ta kafe shi da ido sannan taci gaba da fad’in
” Laila has to change from Laila y’ar makiyaya to Laila daughter of Millionaire Rasheed Ali (sunan kawun Habeeb).
“No no no! I can’t! Saboda son zuciya na bazan bari in kwace wa Laila duniyar ta ba, baza mu tab’a chanja fact d’aya ba ,cewa ita *y’ar makiyaya* ce, and will always be *y’ar makiyaya* no one can change that” Cewar Suraj da tuni ya bar dining table d’in ya koma gefe ya jingina da bango. Mik’e wa Mom tayi ta nufi inda yake tsaye a fuskar shi tace
*also we cannot change the fact that you love her, and will always do! Believe me Suraj I am your mother and I damn know what’s best for you! Ka gwada abunda na fad’a maka in har akwai son ka a zuciyar ta babu makawa zata amince ta tafi kaduna, besides babu abunda zata rasa ko kuma zai cutar da ita ,Ummin Habeeb na nan, ga Sapna (K’anwar Habeeb) bazata samu matsala ba kawai buk’atar mu Laila ta chanja”*.
Suraj ya girgiza kai yace “you can’t change her in just four months! Mom I mean its Impossible!.
Daga bayan su suka jiyo Murya “what’s impossible? Hirar me kuke haka da sassafe?” You both look disturbed akwai matsala ne?
Cikin k’ink’ina da Sosa kai Suraj yace “non..nothing Dad !” Kai Dad ya jinjina ya nemi waje ya zauna yana k’are musu kallo, mom ko kallon shit bata yi ba saboda abunda yayi mata jiya Kai tsaye ta wuce sashen ta yayinda Suraj ya fice daga falon yana sak’e sak’e a ransa ji yake kamar zai nutse cikin k’asa don gani yake Dad ya ji maganar su don sometimes Dad is unpredictable wani b’angaren zuciyar tasa kuwa tunanin yadda zai je wa Laila da zancen da suka yi da su Mom ya tabbatar da kamar wuya ta amince.
Habeeb na ganin fitar Suraj da mota yasan inda zashi , dan haka shima ya hau wata motar ya bi bayan shi ,hoping Laila zata amince…..